You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yadda likitan da kanshi ya kira ta, duk kuwa da ayyukan da suke gabanshi. Kuma ba haka suka yi ba, sun yi ne cewa ita za ta kira shi ƙarfe takwas, amma abun mamaki, shi da kanshi ya kira ta.


Kawar da mamakinta ta yi ta hanyar miƙewa tsaye, ta ninke sallayar ta ɗora a bakin gado, sannan ta doshi barin ɗakin, zuwa na Modu.


A takure ta same shi, ya haɗa kai da guiwa, yana ta wani irin kuka mara sauti, sai dai shessheƙarsa kawai ake ji.


Cikin kiÉ—ima ta iso gare shi. Hannunta a ka take faÉ—in,


"Ya Noor me ya faru da kai?"


Tunani yake, mafarki ne wannan yake yi. Irin zuwan da Amrah ta saba yi masa a mafarki ne ita ma Maryama ta masa. Hakan ya sa ya ƙi ɗago kanshi, yana mai tsananta kukan da yake yi.


"Ya Noor me kake ne wai haka? Ko wani abu yana maka ciwo ne?"


A nan ɗin ma bai ɗago kanshi ba. Haka kuma bai rage sautin kukan ba, sai ma ƙarfafa shi da ya yi.


Hankalinta ne ya daÉ—a tashi. Ta sa hannunta tana mai dafa kafaÉ—arshi, a hankali take É—an bubbugawa.


"Zan yi fushi ma in tafiyata, tu da dai ba za ka min magana ba."


Taba shin da ta yi ne ya ba shi tabbacin ba mafarki yake ba. Ya dago kansa, da idanuwansa da suka gama rinewa.


A kidime ta zaro idanuwanta tana kallon bakinshi. Ta ce,


"Yaa Boor me ya samu bakinka? Na shiga uku? Ko wani abu ya faru ne?"


Daina kukan nashi ya yi, ya dora dukkanin idanuwansa gare ta, yana bin ta da wani irin kallo, mai cike da zallar jewarta da ya yi.


"Yaa Noor talk to me. Me ya faru da labbanka duk suka farfashe?"


"Yo ni na ciccije su."


Ya fada cikin halin ko'inkula. Farin cikinshi dai da ta dawo garr shi. Ita kam ba ta masa nisa kamar yadda Amrah ta masa ba.


"Me ya sa za ka ciccije labbanka?"


Ta tambaue shi, cike da al'ajabi.


"Ba ke ce kika ki zuwa ba? Ni kuma na ji haushi, na keta riga ta, na kuma ciccike labbana."


Ya fashe da dariya, yana mai sadda kanshi, wai ya ji kunya.


Samun kanta ta yu da murmusawa. Har cikin ranta ta tausayawa masa. Wani irin dadi ta ji ya ziyarci zuciyarta. Ashe har Annur ya damu da ita haka? Kodai ya fara ba ta matsayi ne kamar Amrah?


Ba ta samo wannan amsar ba ta juyo muryarsa yana fadin,


"Ke kika ce ba za ki taba yi min nisa ba, za ki zame min madadin Amrah."


Habarta ta dafe da hannun dama, tana tuna ranar da suka yi wannan maganar da shi, tamkar hankalinshi ba ya gare ta. Amma ga shi har bai manta ba, har ma ya fara yarda cewa babu Amrah. Lallai ta yarda sosai da Dr. Sandra. Ta amince cewa Lost of Memory shi ne bbsvbar damuwar Annur. Bayanan da ta mata cewa makusanci yake nema, wanda zai nuna masa dukkanin soyayya, ya ba shi dukkanin kulawar da wani masoyi zai samu daga wurin masoyiyarsa. Yau ga tabbaci ta gani. Har Annur na ambatar za ta zame masa madadin Amrah.


"Ko jiya ma ta zo min a cikin barci, ta ce da ni wai in dauka cewa ke ce ita, in moyar da duk wata soyayyarta gare ki, wai in dai ina so ta yi farin ciki. Farin cikin Amrah nake so! Duk abin da zai faranta mata rai ina biye da shi, hakan ya sa na mata alkawari cewa zan miki kauna, sai dai ba kamar wacce nake mata ba. Ta yarda da hakan, kuma ta bace da ganina, hade da raubtsuwar ba za ta taba dawowa a gare ni ba har abada."


Kuka ya fasa a daidai nan, yana mai kallon wuri daya, tamkar wanda yake tunkwa da wani abu.


Tun sadda ya fara maganar take kallon shi, kallon mamaki. Wai kodai Annur ya warke daga hauka ne? Wannan kalaman da yake mata, mahaukaci ba zai taba iya yin su ba.


A hankali take jin duk wata damuwarta tana rarewa izuwa farin ciki. Kaunar Annur na shiga duk wata kusurwa da ke cikin jikinta. Soyayyarsa na ambaliya a jini da dukkanin jijiyoyinta.


Ji take ta manta ma da wata damuwa da take cikinta. Maganar auren da ake so a hada ta da Deedah nna disashewa daga cikin zuciyarta. Tana canzuwa da farin cikin da Annur ya jefa ta a ciki.


"Kawai a zo a mana aure..."


Ta tsinkayo muryarsa ya fada, yana mai sadda kanshi kasa, alamun jin kunya.


***


*My pipu how was this chapter? Was it nice? In ga hannuwan wanda ta ma dadi...lol.*


*To kar dai a manta da kankaro mutunci.*


*Masu mutunci ku karkata ku kankaro shi.*


*Ni ma sai in karkata in kankaro muku dogon shafi irin na yau.🤗😘😃*


*Ku kuma ghosts masu hancin yalo, ku ci gaba da labe, Allah yana ganinku. Kuma insha Allahu gobe sai kun tashi karanta next oage dina chajin wayoyinku ya kare. Ehen. Masu hakoran bera kawai.😏🤒*


*Jinjina ga yan RAZ NOVELLA 1&2. Ina kaunarku all fisabilillah. Iya wuya ana tare.*


Thanks all.


Pinky durling💞
RAZ 2
[9/6, 11:23 PM] Princess Amrah✍🏻💞: *🅰MRAH NAKE SO!♥*


_(Labari mai taba zuciya, soyayya, sadaukarwa da kuma ban tausayi)_


Sadaukarwa ga masu cutar amosanin jini (Sickler)


Na Amrah A Mashi
(Princess Amrah)
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*


5⃣6⃣


Wattpad: PrincessAmrah


***


A bakin wani gidan gona suka faka motarsu. Tun sadda suke shigowa cikin dajin Sans ke son yin magana. Yana son sanin ina za su je da suke keta daji irin haka. Sai dai ya yi shiru ne saboda ya san wasu ba su son yawa magana. Zai haƙuri har su isa ɗin, don ya ga iya gudun ruwansu.


Taimaka masa ya yi matashin ya fiddo keken daga bayan motarsa, ya ajje a daidai ƙofar gaba da ya buɗe ma Sans, sannan ya tallabo shi ya ɗora a bisa keken.


Bayan ya zauna daram ya rufe murfin motar, sannan ya ringa tura shi har suka isa daga bakin ƙofar, ya hau ƙwanƙwasawa. Babu jimawa sai ga wasu matasa sun fito, ɗaya na magagin barci, ɗayan kuma yana ma wancan saurayin sannu da zuwa.


"Yax. A kama shi a shigar ciki, zan gyara parking É—ina."


"To Oga."


Wanda aka kira da suna Yax ya faÉ—a, yana mai kama keken Sans, haÉ—e da shigar da shi cikin gidan.


Bayan sun ƙarisa tangamemen falon, Yax ya ce da ɗayan abokinsa,


"Esien, taimaka kawo mishi ruwa ya sha. Da alama yana jin ƙishi, ga bakinsa nan duk a bushe."


Bai musa ba Esien, ya nufi inda fridge yake, ya ɗauko masa ruwan roba, mai tsananin sanyi, har da raɓa.


Miƙa ma Sans ɗin ya yi bayan ya buɗe, bai karɓa ba, sai cewa ya yi,


"Ina jin zazzaɓi sosai a jikina, ba zan iya shan ruwa mai sanyi ba. Kuma ga magungunana nan a cikin aljihu ina son sha, ba a sha da ruwan sanyi."


Wancan matashin da daidai shigowarsa kenan ya ce,


"Esien kawo masa mara sanyi don Allah. Wanda ba a saka a fridge ba."


Ya ƙariso gaban Sans, da faɗin,


"Sannu ko?"


Kai kawai Sans ya jinjina masa.


Esien na kawo masa ruwan ya ɓalli magungunanshi ya sha. Sanann ya ce,


"A ina zan yi wanka? Ku taimaka min, duk jikina babu daÉ—i."


"Yax, ka dafa masa ruwan zafi yanzu. Da alama akwai zazzaɓi sosai a jikinsa, bai kamata ya yi wanka da ruwan sanyi ba."


Cikin bin umurnin wancan matashin ya miƙe, ya ƙarisa cikin kitchen domin ɗora ruwan zafin.


"Ka kwantar da hankalinka. Ni sunana Farouk Sardauna, you can call me Bobby. Za ka iya ci gaba da zama a nan tare da wa'yannan bayin Allahn, duk yarana ne, har sadda ka samu wurin zuwa."


Kansa kawai ya jinjina ma Bobby. Yana mai samun dukkanin nutsuwarsa da ya rasa a baya.


Sai da Yax ya haÉ—a mishi komai sannan ya sanar da shi ya haÉ—a masa, ya tura shi har toilet É—in, sannan ya bar shi ya yi.


Bayan Yax ya dawo, Bobby ya ce da su,


"Ina son ku nutsu mu yi magana da ku."


"To Oga."


Suka haÉ—a baki wurin faÉ—i.


"Wannan da kuke gani, ina son duk wani girma da za ku ba ni, shi ma ku ba shi. Ku girmama shi, ku ɗaga darajarshi, matuƙar kuna son ganin farin cikina. Duk wani abu da yake da buƙata, ku tallafa masa, tunda kun gan shi gurgu."


Cikin gamsuwa Esien ya ce,


"Mun maka wannan alƙawarin Oga."


Yax ma ya ce,


"Deal!"


Tafa hannunsa ya yi Bobby, ya ce,


"Shi ya sa nake alfahari da ku a kodayaushe. Kuna faranta min rai sosai. Duk abin da zan nunar muku da ina so kuna aikata shi."


Yax ya ce,


"Ai Oga dole ne mu faranta maka, saboda kai ma kana faranta mana. Ka duba ka ga, ba wani aiki sosai muke yi a gidan gonar nan ba, amma duk sadda Dadynka zai zo ka ringa koÉ—a mu kenan, yana mana kyautukan ban mamami. Tsakaninmu da kai sai dai godiya kawai."


Murmushin jin daÉ—i ya yi, sannan ya shiga É—akin da kayanshi suke, wanda idan ya zo gidan yake sakawa.


Wasu kayan sanyi ya fiddo ya É—ora a bisa gado, ya feshe su da turare, sannan ya dawo falon.


Ya tarar har ya fito daga wankan Sans, hakan ya sa ya tura shi izuwa É—akin da ya fito daga shi É—in.


Mai ya gwada mishi ya shafa, sannan ya ba shi kayan, yana mai fita daga É—akin.


Abincin da ya tsaya ya siyo ne ya koma ya ɗauko daga cikin mota, ya mimmiƙa ma su Yax nasu sannan ya ajje ma Sans nashi gefen kujera, shi ma ya hau cin nashi.


Ƙarar keken Sans da suka ji ne ya tabbatar musu cewa ya fito, duk suka ɗaga kawunansu suka kalle shi. Sosai kayan jikinshi suka amshe shi, tamkar dama can nashi ɗin ne.


Bayan ya iso gaban Bobby ya fasa kuka, yana mai runtse idanuwansa.


Da sauri Bobby ya ajje robar take away É—in, yana tambayar Sans dalilin yin kukan nashi.


"Kawai ina jin daÉ—in halaccin da ka min ne. Har ma ban san ta hanyar da zan bi don na gode maka ba."


GyaÉ—a kansa ya yi Bobby, cike da tausayi ya ce,


"Ka daina kuka in don wannan ne. Har ga Allah ka shiga raina, a lokaci guda na ji tausayinka ya shiga duk wata gaɓa da ke cikin jikina. Karɓi wannan."


Ya miƙa masa wani hankici babba, mai ɗauke da tambarin tutar USA.


"Share hawayenka, kar kuma na kuma ganin koda É—ison hawaye ne ya fito daga idanuwanka."


Karɓar kuwa ya yi Sans, yana mai share hawayensa, da hankicin.





"Yauwa ko kai fa. Yanzu sai ka ci abincinka. Daga nan sai ka samu ka kwanta, ko za ka samu ƙarfi-ƙarfi a jikinka. Gobe da safe zan dawo insha Allahu, zan kai ka asibiti."


Godiya Sans ya sake jaddada masa, sannan ya fara cin abincin, zuciyarsa na cike da ƙaunar bawan Allahn da ya ba shi taimako ba tare da ya san cikakken asalinsa ba.


***


Bubbuga shi ya ji an yi, a lokacin da kanshi yake bisa guiwowinsa, yana saƙe-saƙe haɗe da zancen zuci.


Ɗago kan nashi ya yi, yana kallon mai taɓa shi ɗin. Dadynshi ya gani sanye da farin glasses, yana sakar masa murmushi.


"Ya ƙarin haƙuri?"


Dadyn nashi ya faɗa, yana mai ƙoƙarin gyara zamansa a kusa da Sans.


Share guntuwar ƙwallarsa ya yi, ya ce,


"Haƙuri an gode Allah, Dady."


Yana mai jin nauyin Dadyn nashi, wanda shi kanshi ya kasa gane dalilin hakan.


"Allah Ya ji ƙan Farouk, Ya sa ya huta. Ka yita haƙuri ka ji? Na sani, akwai zafi da raɗaɗi. Akwai ciwo mai tsanani, mutuwar babban aboki. Amma ka daure, ka kai zuciyarka nesa. Ba wai gaggawar tafiya ya yi ba, lokacinsa ne ya yi."


Dady ya ɗan yi shiru daga nan, yana karantar yanayin ɗan nashi, wanda hakan ya ƙara sagar masa da jiki.


Cikin kwantar da hankali ya ci gaba da faÉ—in,


"Dukkan mai rai mamaci ne, Annur. Yanzu ina Amrah take? Ka manta irin soyayyar da kuka yi da ita? Ka ga kuma, a hakan Allah ya ɗauki rayuwarta. A haka ka ci gaba da rayuwa kamar kowa. Ka jure, ka yi haƙuri, duk da dai kalar ƙalubalen da ka fuskanta a lokacin da ta rasu. Ba na so a kuma ƴar gidan jiya Annur. So nake ka miyar da komai ba komai ba. Ka ci gaba da yi ma Farouk addua, har sadda kai ma taka mutuwar za ta zo ta ɗauke ka."


Tun daga sadda Dady ya fara yi mishi maganar Amrah yake jin gabanshi na faɗuwa. Shi da bai santa ba, bai taɓa ganinta ba, amma ya ci gaba da rayuwa a idanuwan duniya a matsayin shi ne asalin masoyinta. Sau da dama shi kanshi yakan zauna ya yi tunani; makomar rayuwarsa a duk sadda wancan ƙullin ya kwance. Ga shi abokin shawarar nashi babu shi a yanzu, ya kwanta damarsa. Kodai zai fito ya fallasa kanshi ne? Ya tambayi kanshi. Da sauri wata zuciyar ta inigiza shi haɗi da kwaɓar kanta, cewa kar ya yi. Ta ya zai ci gaba da rayuwa a duk sadda asirinsa ya tonu? A ina zai ci gaba da zama? Dama Allah ne gatanshi Bobby ne gatanshi, tun ma kafin ya dawo gidan su Annur ɗin. To babu Farouk yanzu, ya zai yi? Zai rufe bakinshi salin-alin ya ci gaba da rayuwa a gidan. Sai dai ya tsara ma kanshi, cewa babu shi babu kayan maye har abada. A duk sadda zai ga mai yi ma zai Ƙoƙarta kwaɓarsa, saboda shi ya ga illarsa, a zahiri ba nesa da shi ba.


***


Cike da ƙarfin hali take taya Mama aikin haɗa kalaci. Raba-da-rabi take jin daɗi a zuciyarta. Nan daɗi, can kuma haushi; Auren dole da ake son a mata. Daɗin kuwa na kalaman da suka fito daga bakin Annur ne, masu cike da zallar nishaɗantar da zuciyarta, da duk gaɓɓan jikinta.


Bayan sun gama duka ta kai a É—akin Abba, ta samu har ya gama shirin fita Office, kalacin kawai yake jira.


Gaishe shi ta yi cikin girmamawa, banza ya mata, ko kallon inda take bai yi ba.


A zatonta ko bai ji ba ne, hakan ya sa ta sake É—aga sautinta, ta gaishe shi.


Bai mata magana ba, sai ma Hammad da ke daidai shigowa É—akin da ya ma magana, cewa ya je ya kira Mama.


Jiki babu ƙwari ta fice daga ɗakin, wasu irin zafafan hawaye na fita daga idonta. Tun daga jiya take kuka, babu ci babu sha, sai famar ciwon kai, wanda panadol ya kasa saukarwa.


A bisa faffaɗan gadonta ta faɗa. Haushin kanta take ji sosai, ta yadda zuciyarta ta kasa aminta da zaɓin iyayenta. Ba ta ga laifin Abba ba, ko kaɗan. Da gaske ko ita ce ba za ta taɓa aikata abin da take so Abban nata ya yi ba. Bai kamata ba, a yadda kawu Imrana ya yi hidima da Abbanta, kuma ya iya ya tinkare shi da zancen wai ba ta amince da auren Deedah ba.


Muhammad da shi kanshi bai ji daɗin abin da ya faru ba, bayan ya kira Mama zuwa ɗakin Abba, ya lallaɓa ya shiga ɗakin Mamar da shirinsa na makaranta, ya ɗauko wayarta, ya ɓoye a cikin rigarsa. Da sanɗo da sanɗo yake tafiya, har ya fita daga part ɗin nasu, ya nufi wani part da ke can baya, inda babu kowa.


Lambar Kawu Imrana da aka rubuta ma Yaya Imran ya gano, babu shakka bare tsoro, ko kuma tunanin wani abu, ya latso kiranshi. Har ta tsinke bai É—auka ba, ya sake kiransa, tana daf da tsinkewa Kawu Imrana ya É—auka.


Sallama ya yi, haÉ—e da faÉ—in,


"Hajiyar Maryam barka da safiya. Ya tashin iyali?"


Sai a yanzu Muhammad ke jin faɗuwar gaba duk da kasantuwarsa ƙaramin yaro. A haka ya daure, ya ce,


"Kawu ina kwana? Ni ne Muhammad."


"To to to madallah da Muhammadu. Ya kuka tashi da iyayen naka?"


"Suna lafiya."


Ya faÉ—a a hankali.


"Lafiya dai ko É—ana?"


Kawu Imrana ya faÉ—a, cike da mamakin kiran da Muhammad É—in ya masa da sassafen nan.


Magana Hammad ya hau yi masa ƙasa-ƙasa, yana yi yana waigen gefe da gefensa, gudun kar a kama shi yana yi.


Sai da ya yi kusan wayar minti bakwai, kafin suka yi sallama da kawun nashi, haɗe da lallaɓa komawa ɗaki.


Ya ci sa'a kuwa har yanzu Mama tana tare da Abba, hakan ya sa ya lallaɓa ya miyar da wayar. Sai dai kuma ya manta shaf, domin kuwa yarinta ba ta bar shi ya tuna goge kiran ba.


Fitowa ya yi fuskarsa a sake, haÉ—e da nufar É—akin Maryama.


A kwance ya same ta, tana ta faman kuka mai sauti.


Ƙarisowa ya yi ya zauna a bakin gadon, cike da tausayin tilon ƴar uwarsa, mai ƙaunarsa, mai son farin cikinsa fiye da nata. Riyawa yake a ransa, duk yadda zai yi dole ya yi, don ganin ya kuɓutar da ita daga wannan mawuyacin halin da take ciki. Ya fara hawa hanya a yanzu kam, yiwuwar abun kawai yake jira.


Bubbuga ta ya yi a hankali, yana faÉ—in,


"Yaya Maryama..."


"Leave me Muhammad!"


Ta faÉ—a da Æ´arfi, cike da takaici.


Duk da ya ji haushin tsawar da ta masa, amma bai yi zuciya ba, ya sake faÉ—in,


"Na miki alƙawari in dai ina raye to babu wanda zai miki auren dole. Wanda kike so shi za ki aura."


Tashi ta yi zaune tana kallon shi.


"Ta yaya?"


Ta haɗa wannan kalaman biyu, da ƙyar da jibin goshi, duk da ba ta san ta yadda ta tsamo su daga cikin bakinta ba.


"Just wait, you'll see."


"Kar ka yi koma menene Hammad. Kar ka ja min, ina zaman zamana. Ka bari kawai, mu barwa Allah lamurranSa, Shi ne kawai zai iya magance mana."


Kanshi ya gyaÉ—a mata, da murmushi ya ce,


"Ba zan ja miki komai ba Yaya Maryama, I promise you."


Kanta ta gyaÉ—a da hawaye kwance a bisa fuskarta, ta ce,


"Allah ya tabbatar."


Kafin ya sake faÉ—in komai ya ji muryar Mama na kiransa, cewa ya fito Abba ya wuce da shi makaranta.


Tashi ya yi, ya mata ba-bye, sannan ya fice daga É—akin, yana jin zuciyarsa wasai, tamkar babu wata damuwa a cikinta.


***


A yi maneji da wannan, iya wanda ya samu kenan.


Do comments
Do votes
and then share with your family and friends.


Thanks all


Pinky Durling
RAZ 2
[9/7, 12:29 AM] Princess Amrah✍🏻💞: *🅰MRAH NAKE SO!♥*


_(Labari mai taɓa zuciya, soyayya, sadaukarwa da kuma ban tausayi)_


Sadaukarwa ga masu cutar amosanin jini (Sickler)


Na Amrah A Mashi
(Princess Amrah)
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*


5⃣7⃣


Wattpad: PrincessAmrah


***


Tun daga sadda Fiddou ta karɓi soyayyar Mahmouda yake duk iya ƙoƙarinsa na ganin ya koya mata son shi. Ya ɗan samu nasara kaɗan ba mai yawa ba. Domin kuwa a yanzu har murmushi takan yi duk sadda suke tare. Ko a gida ma yakan faɗo mata a rai har ta samu kanta da murmusawa. Sai dai kuma murmushin yakan gushe daga saman fuskarta, idan ta tuno da Modunta, wanda take ma mutuwar so.


A tsawon wannan lokacin, har manya sun shiga maganarsu, an tsaida zancen auren nasu, wata É—aya mai zuwa.


A yanzu ne Aunty Sahiya ke nadamar abubuwan da ta kasance tana ma Fiddou. Ta tabbatar cewa cin amana ne fa take yi, kuma ba za ta so wata ƙanwarta ta faɗa tarkon matar yayanta ba, kamar yadda ta ringa cutar da Fiddou, ƙanwar mijinta uwa ɗaya uba ɗaya. Duk wata biyayya da ya kamata ƙarama ta ma babba, haka Fiddou ke ma Aunty Sahiya. Amma ita ta kasa karɓarta a matsayin ƙanwarta, ta kasa kyautata mata kamar yadda ita Fiddou ɗin take ƙoƙarin kyautata mata.


Zaune take a É—aki Fiddou É—in. Ta rafka tagumi tana mai tunano tsawon lokutan da suka shuÉ—e, na zamantakewarta da rayuwarta da Modu. Shirmensa kawai take tunawa, da kuma sunan Amrah da ke yawan fitowa daga bakinsa.


Sosai ta yi zurfi da wannan tunanin, hakan ya sa ruwan hawaye ya fara sauka a bisa kumcinta.


Gyaran murya ta yi Aunty Sahiya, bayan ta ƙarisa shigowa ɗakin ta nemi wuri ta zauna, a kusa da Fiddou ɗin.


Zabura ta yi Fiddou, ganin Aunty Sahiya ta shigo ɗakinta, kuma har ta nemi wuri ta zauna. Ta tabbata ba alkhairi ne a tattare da zuwan nata ba, sai tarin wulaƙanci da take tunanin zai fito daga bakinta.


Da dukkan hannuwanta ta sa tana share hawayen, haÉ—e da furta,


"Sanu da shigowa Aunty Sahiya."


Abin da take tsammanin faruwarsa sam! Ba shi ne ya faru ba. Sai saɓanin haka da ta gani. Murmushi ne shimfiɗe a fuskarta, tana mai ƙara kallon Fiddou, cike da yanayin tausayi.


"Yauwa Fiddou. Kukan ne halan har yanzu ya ƙi ƙarewa?"


Mamaki bai bar Fiddou ta iya furta komai ba, sai kallon al'ajabi kawai da take bin ta da shi.


"Ki yi haƙuri Fiddou, komai yai yi hwarko yana da iyaka. Kuma dukkan tsanani yana tare da sauƙi."


Ba ta taɓa tsammanin Aunty Sahiya ta san hakan ba, haka kuma ba tai tsammanin akwai ranar da Aunty Sahiya za ta iya fuskantarta da irin wannan kalamin ba.


"Fiddou magana nake son yi da ke, ta fahimta. Hwatar za ki mallaka mini dukkanin nutsuwa da hankalinki."


Nannauyar ajiyar zuciya ta sauke, ta ce,


"Insha Allahu. Ke nake saurare."


Matsowa ta yi daf da Fiddou, ta ce,


"Gahwara zan nema a wurinki Fiddou. Na sani, na san ni ɗin ban zama ta gari a gare ki ba. Tunda na auri Yayanki Labib ban taɓa yin wani abu da nuhin hwarin cikinki ba, duk da kuwa naki ƙoƙarin na ganin kin ba ni girmana.


Ki sani Fiddou, na yi da na sani, da na sani mara misaltuwa. Sai yanzu nake jin haushin kaina; rashin kyautata mikin da na yi, duk da kuwa ke ɗin kina da buƙatar mai kyautata miki.


Don Allah Fiddou ki yafe min, wallahi na yi alƙawarin hakan ba za ta sake hwaruwa ba."


Tana dakatawa a nan, da sauri Fiddou ta tsugunna a ƙasan Aunty Sahiya, tana kallon yadda take kuka, kuka mai tabbatar da ta nadama.


Hannunta ta saka Fiddou, ta ringa share mata hawayen, tana faÉ—in,


"Ki daina kuka Aunty Sahiya. Wallahi komai ya wuce. Allah Ya yahe muna baki É—aya."


Da haka suka rungumi juna, cike da ƙaunar junansu, tamkar babu wani abu da ya taɓa shiga a tsakaninsu.


***


Sosai rayuwar Sans ta sauya, daga baƙin ciki zuwa farin ciki. Duk wani abu da zai nema yana samu, tamkar sadda yake gidansu. Kulawar da su Yax ke ba shi, ko shi ne Ogan nasu iya wanda za su ba shi kenan. Sosai suke girmama shi, duk da kasantuwarshi gurgu, ba ya neman komai ya rasa a rayuwarsa.


A lokacin da Sans ya cika wata guda a gidan ne, Bobby ya fara ƙoƙarin karkatar da shi, ta hanyar koya masa shan cyrup, da niyyar duk wata damuwa da yake cikinta za ta gushe, izuwa wata duniyar ta daban.


Daga farko sam! Sans bai yarda da hakan ba. Dalilin da ya sa ya butulce ma Bobby kenan, ya kuma ƙi karɓar wannan tayin nasa. Sai daga baya ne sadda damuwar tunowa da iyayenshi ta addabe shi, ya ringa tunanin tilon ƙanwarsa Yamaira, kwatsam Bobby na zaune da shisha a gabanshi, da kuma karan sigari a hannu yana zuƙa, sai tarin kwalaban cyrup a gabanshi, ya shanye wasu, bai fasa wasu ba.


A zaune ya same shi ya yi mankas, amma bai fara fita daga hayyacinsa ba.


Ƙoƙarta sauka daga keken nasa ya yi, saboda a tsawon wannan kwanakin har asibiti Bobby ke kai shi, inda yake da wani nurse abokinsa, yake ma Sans treatment.


"In har da gaske kake cewa wannan abun zai gusar min da damuwar da nake ciki, shirye nake da ɗanɗanawa, a karon farko na rayuwata. So da dama nakan tuno da rayuwata ta baya, in tuno da kyautatawar da na samu daga wurin iyayena. To kuma lokaci guda na rasa su, sun tafi sun bar ni ni kaɗai a duniyata. Don haka dole in fantsama wata rayuwar ta daban, saɓanin wacce nake a kai sadda suke raye."


Hannu ya ba Sans suka tafa Bobby, yana faÉ—in,


"Ko kai fa abokina. Yanzu na ji magana. Ungo wannan. Ina mai tabbatar maka da zarar ka fara shan shi yau, to gobe kai za ka kawo kanka da kanka cewa in ƙara maka."


Karɓar kwalbar ya yi Sans. A daidai zai kai kwalbar bakinsa, wani tunani ya faɗo masa a rai, cewa kar ya sha, ya yi ƙoƙarin kwaɓar zuciyarsa, da kuma ta abokinsa, a kan wannan mummunan halin. Wani sashe na zuciyarsa ne ya gargaɗe shi, kan cewa matuƙar fa bau aminta da wannan tayin ba, lallai zai dauwama a cikin damuwa, kamar yadda Bobby ya faɗa masa a baya.


A bakinsa ya

Please Login or Register in order to submit comment