You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dai addu'a kawai, don kuwa ba wuya ta zautu, barinma dai ta tsakani da Allah, wacce babu surki ko kaɗan a cikinta.🤧


Where are the lover birds? Kun ji waƙar soyayya wadda Maryama ta koyawa Modu ba? Haha! Ƙirƙirarra ce daga bakin Amrah marubuciyar, ta ƙirƙira ta musamman don takwararta Amrah.🤣


Thanks all my fans. Ina ƙaunarku all fisabilillah😘😍


Comment, vote and share with your family and friends.


Pinky durling
RAZ 2
[8/30, 3:57 PM] Princess Amrah✍🏻💞: *🅰MRAH NAKE SO!♥*


_(Labari mai taba zuciya, soyayya, sadaukarwa da kuma ban tausayi)_


Sadaukarwa ga masu cutar amosanin jini (Sickler)


Na Amrah A Mashi
(Princess Amrah)
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*


5⃣0⃣


Wattpad: PrincessAmrah


Wannan shafin naku ne baki ɗaya ƴan NAGARTA WRITER'S FANS GROUP. Musamman Meinerh, Ummu Ikhram, Ummu Aysher and Janaaht. Sannunku da rero baitocin Amrah😂 kun ƙoƙarta fa irin sosai da sosai ɗin nan😍😘. Ina yin ku sosai, ina ƙaunarku all fisabilillah.


***


Tunda ya bar wurin gabansa ke dukan uku-uku. Sosai yake ji kamar wani abu zai faru, sai dai kuma ya kasa tantance menene zai faru ɗin. Tausayin mahaifiyarsa da ƙanwarsa tilo yake. A wani sashen na zuciyarsa kuma tunanin halin da mahaifinsu yake ciki yake. Tunawa ya yi da kalaman Abbun nasa na ƙarshe, da kuma sautin harbin bindiga da ya ji, wanda ya kasa fita daga cikin kunnuwansa. Ko dai an kashe Abbu ne? Ya tambayi zuciyarsa. Rashin samun amsa daga gare ta ya sa ya gaggauta kawar da tunanin daga zuciyarsa, gudun kar ya kai wa bango karo ba tare da ya sani ba.


Tashin hankalin da ke akwai yanzu kamar ma ya fi na É—azu. Guje gujen da al'umma ke yi domin su tsira da rayukansu har ya fi na É—azu. To a hakan zai samu mai siyan wayarsa?


Ƙara sauri ya yi da haka har ya isa titi. Abun hawa ma babu, kowa neman ceto yake. Tafiya ya ci gaba da yi a hankali saboda gajiyar da ya yi. Sai kuma ya tuno da halin da ya baro mamansa da ƙanwarsa a ciki; yunwa da kishirwa. Cikin sauri ya ci gaba da takun nasa, har Allah ya haɗa shi da wani mai taxi ya zo wucewa. Saurin dakatar da shi ya yi, amma ina, cike take da al'umma, wasu kan wasu. Har sun yi nisa kuma sai ga su sun dawo, cikin tausayi dreban ya kalle shi haɗe da furta,


"Idan za ka iya daurewa da zaman matsatsi mutum ukun nan da ke gaba su gyara maka ka zauna, ko a kan É—aya ne. Ya fi tsayuwa a nan É—in, cikin tsananin tashin hankalin nan"


Bai ko ba shi amsa ba ya buÉ—e motar, suka gyara masa ya zauna a kan wani.


Ta titin suka bi kai tsaye, saboda sojoji ne rinkis a bakin hanyar, masu tsaron mutane. Duk inda suka gitta sojoji sai sun musu bincike kafin su bar su su tafi.


Sun yi tafiya mai nisa kafin motar ta tsaya musu. Dreban ya yi ya yi ta tashi amma ta ƙi tashi, hakan ya tabbatar masa da cewa mai ne ya ƙare. Kansa ya dafe cike da takaici da faɗuwar gaba. Hawaye ke neman fitowa daga idonsa, saboda a tsakiyar daji suke, suna daf da shiga cikin Maiduguri. Dama kuma plan ɗin Sans kenan, su ƙarisa cikin gari ya samu mai siyan wayarsa, saboda babba ce sosai, mai tsada.


Cikin wata irin murya dreba ya labarta musu abin da yake faruwa. Salati aka É—auka duka motar, barinma matan da ke ciki, kuka suka fasa mai nuna tsantsar tashin hankalin da suke ciki.


Babban abun takaicin kuma babu soja ko ɗaya a kusa kusa, wata ƙila sai gaba ko suna cin karo da soja. A tsorace suke su duka, tsoronsu ma kar kar ƴan ta'addan su ɓullo musu ta tsakiyar daji, sun tabbata sun tashi aiki daga nan.


Mazan da ke cikin motar ne suka firfito, a tunaninsu wai ko za su samu wata mota ta zo wucewa a taimaka musu a samo mai ko za su samu barin dajin. Matan kuma cikin motar suke zaune. Zuciyoyinsu a dagule, sun ga samu sun ga rashi.


A ɓangaren su Yamaira kuwa, tun bayan tafiyar Sans jikin Aunty ya ƙara tsananta. Dafe take da ƙirjinta, tana jin tsananin ciwo a cikinsa. Dama haka ulcer take mata, matuƙar ta ji yunwa mai tsanani to akwai matsala. Ta ringa shan wahala kenan tana aman jini, har sai ta samu ta ci abinci, ta ɗora da maganin da take sha; ulcer kit. To yanzu babu ma abincin bare maganin. Ga ƙishi ko yawu babu a bakunansu.


Ba Yamairah kaÉ—ai ba, hatta sauran mutanen da ke wurin hankulansu sun tashi da ciwon Aunty. Sun dawo kanta baki É—aya, suna tausaya mata. Ga shi duhu har ya fara, an rasa samun mai fita daga wurin don ganin halin da ake ciki.


Suna cikin haka suka fara jin ƙarar motoci, hakan ya sa suka ƙara firgita, suka dabaibaye juna, banda sautin ajiyar zuciya babu abin da ke fita a tsakaninsu.


Kamar a mafarki suna fara jin sautin bindiga, ga ƙarar taku ana kusanto cikin kangon.


"Ga wasu nan."


Suka jiyo muryar wani matashi ya faɗa, hannunsa riƙe da bindiga.


Nan fa ake yin ta. Daga masu sakin fitsari sai masu sakin zawayi. Abin da suka jiyo labarinsa ne daf da su yanzu. Nan fa suka sadaƙas, dukkansu suka kwakkwanta a ƙasa.


Bataliyar mutanen ce ta shigo, su kusan talatin ko ma fin haka, kowanne riƙe da bindiga, fuskokinsu a doɗe, ƙwayar idonsu kawai ake gani.


Wani babba daga cikinsu ya sa duk suka tashi zaune, kusan al'umma arba'in ne, duk suka É—aÉ—É—ago suna kuka.


Ƴan matan da ke ciki suka fitar, su shida, ciki har da Yamaira. Mutum biyu suka tisa ƴan matan gaba suka wuce da su, sauran kuma aka saita bomb kusa da wani dutse, ba tare da kowa ya sani ba, sannan suka bar wurin.


Kuka sosai iyayen yaran ke yi, a ganinsu su sun tsira, yaran ne kawai aka tafi da su. Baki ɗaya Aunty ji tai gwara ma mutuwa ta zo ta ɗauke ta, zai fi mata sauƙi fiye da wannan halin da take ciki. Ga ciwo ya addabe ta, ga kuma uwa uba ƴarta da aka tafi mata da ita, ba ta san halin da take ciki ba. Sans ma ya tafi fin awa biyu, babu shi babu alamunshi. Mijinta ma babu labarinshi. Wannan fa shi ake kira da shiga uku! Sunan Allah suke ta ambata kawai, shi kaɗai ne Zai iya fitar da su daga halin da suke ciki.


Wata irin ƙara suka ji a kunnuwansu, kafin wurin ya kama da wuta, ta mamaye kaf ilahirin wurin, har ma ta kai nesa da kangon. A take duk suka mace, ko gawarsu babu alamarta, saboda wuta ta gama soye su.


***


Washe gari da misalin ƙarfe goma na safe ya ɗauki wayarsa, safe da ƙirjinsa, ya latso kiran Maryama. Sau kusan biyar yana kiranta amma ba ta ɗauka ba. Haka ya sa ya ajje wayar, a fili ya furta,


"Please help and pick my call Maryam. I seriously neet to hear your voice. Am missing you so badly."


Ya dafe kansa, hawaye na zirara daga idanuwansa.


Annur da ke gefensa ya ce,


"Na rasa gane kanka Guy. A maimakon ka ji da ciwon da yake damunka, ka tsaya ta wata mace, macen ma wacce sam ba ta damu da kai ba. Me zai hana ka fita a harkarta?"


GyaÉ—a kansa ya yi Bobby, ya ce,


"Ba za ka gane ba ne guy. I love Maryama har ma ban san ta hanyar da zan misalta maka ba. Maryam is my choice, ina ƙaunarta, kamar idan na ji muryarta zan samu sassaucin ciwon nan da nake ji tun daga zuciyata. And...I want to tell her something before..."


Ajiyar zuciya ya sauke Annur, haÉ—e da dakatar da shi ya ce,


"To Allah kyauta maka. Ni bara na tashi, wurin aiki zan je."


"Ok guy, please pray for me, Allah sa Maryama tai picking call É—ina."


"Ameen."


Annur ya faɗa cike da tausayin abokinsa, wanda ya gama ramewa a ƴan kwanaki ƙalilan, kamar ba shi ba.


Ci gaba ya yi da kiran Maryama amma shiru ba ta ɗauka ba, shi kuma ya kasa haƙuri.


*


A gefensa take zaune, tana jera alphabets a gabanshi, fuskarta ƙunshe da murmushi.


A-M-R-A-H ta jera, ta ɗago tana kallonsa, shi ɗin ma fuskarsa ƙayace da murmushi, wanda ke ƙara bayyana kyawunsa.


Muryar Mama ta ji tun daga nesa tana faÉ—in,


"Maryama wayarki na ta ringing fa tun ɗazu. Zo karɓi ga ta."


Miƙewa ta yi Maryama, a daidai bakin ƙofar ɗakin ta karɓi wayar da fara'a, a lokacin ma har ta tsinke.


Koda ta duba 12 missed calls ta gani, baki a sake take dudduba mai kiran, duka mutum É—aya ne. A bayyane ta furta,


"Bobby!"


Kafin ta fara tunanin ajje wayar sai ga wani kiran nasa ya sake shigowa. Ajiyar zuciya ta sauke sannan ta ɗauka, da sallama ƙunshe a bakinta.


"Maryama mutuwa zan yi, ki taimaka ki saurare ni, wata ƙila maganar ƙarshe ce za mu yi da ke."


Wannan maganar tasa ba kaÉ—an É—in karyar da zuciyar Maryama ta yi ba. Take ta ji hankalinta ya tashi, duk da ba sonsa take ba. Muryarsa kawai idan ka ji ta isa ta tabbatar da ingancin maganarsa, lallai bai da lafiya, akwai abin da yake damunsa.


"Lafiya Bobby, me ya same ka?"


Ta faÉ—a cikin rawar murya.


Runtse idanuwansa ya yi duka biyun, ya ji daɗin saurarensa da za ta yi, ko ba komai jin muryar Maryama kaɗai kan saka shi cikin shauƙi, shauƙin ƙauna.


"ÆŠaya daga cikin manya manyan munanan halayena ne Maryama, smoking ne ya ja min, shi ya kai ni a wannan mugun ciwon da nake, wanda ba lallai na ci gaba da rayuwa ba."


Canza wayar ta yi daga kunnen dama zuwa na hagu, idanuwa a buÉ—e tamkar yana a gabanta, ta ci gaba da saurararsa,


"Maryam ina ƙaunarki, ke ce mace ta farko a rayuwata wacce na fara so tsakani da Allah, haka kuma ba na ji akwai wacce zan so bayanki. In short, na tabbata ina daf da mutuwa, ba zan samu kamarki ba har na koma ga Allah maɗaukakin sarki. Alfarma ɗaya nake nema a wajenki, wacce ita ce silar kiranki ma baki ɗaya."


Sosai take tausaya masa. Ita É—in dama uwar hawaye, babu wuya kuwa ruwan hawaye ya fara sintiri daga idanuwanta zuwa kumcinta.


"Akwai wani abokina, sunansa Annur, ina so na sadaukar masa da soyayyarki, saboda ba ni da tamkarshi a duk cikin abokaina. Ƙaunar da nake masa ta sa nake son sadaukar da abin da na fi matuƙar so a rayuwata, ke kenan. Don Allah ba don ni ba Maryam, ba don halayena na banza ba. Ki taimaka ki amince da wannan buƙatar tawa, ki auri Annur, dama gidansu an daɗe ana so ya fitar da matar aure ya yi aure. Kar ki watsa min ƙasa a ido Maryama, zan baki lokaci ki yi tunani, idan har ina da sauran numfashi zuwa gobe zan kira ki. Na bar ki lafiya."


ya tsinke kiran, ba tare da ya jira me za ta kuma faÉ—i ba.


Sandarewa ta yi a zaune tun sadda ta ji buƙatarsa. Har cikin zuciyarta tana tsananin jin tausayin Bobby, tana jinsa har cikin zuciyarta. Sai dai kuma ta rasa dalili, ta rasa a wane babi yake a zuciyarta. Duk da hakan, ba ta jin za ta iya amincewa da wannan buƙatar tasa. Ba za ta taɓa iya auren fake Annur ba. Mutumin banza, wanda ya zauna a wani gida don yaudara, a matsayin asalin yaron gidan.


Modu da ke zaune gefenta duk sai ya sha jinin jikinsa. Ya kasa yi mata magana, saboda halin da ya ganta a ciki.


Haka kawai yanayin nata sai ya tuno masa wani sashe na rayuwarsa. Sosai ta tuno masa wani lokaci da ya shuÉ—e, a tsakaninsa da Amrah. Lokacin da yana Cyprus suna waya, ciwonta ya tashi, bayan sun yi waya take shaida masa halin da take ciki, har ma an kwantarta asibiti. Ya shiga damuwa sosai, kuma yanayinsa ya sauya. Shi ya sa yake kallon Maryama a matsayin wacce masoyinta yake cikin damuwa, damuwa mai tsananin gaske.


Sosai yake jin kansa na sara masa. A duk lokacin da zai tuno da wani abu na rayuwarsa, take zai ji kansa na masa ciwo, komai yana juya masa, zuciyarsa na masa tuƙuƙi, abun ba ya misaltuwa.


Ganin halin da yake ciki ya sa Maryama ƙarfin halin wartsakewa, cikin dakiya ta ce,


"Ya Noor miye ne kuma? Ko ba ka da lafiya ne?"


Idanuwansa a runtse ya ce,


"Ba ke ce ba..."


Ya yi shiru ba tare da ya ƙarisa zancen ba.


"Ni ce me? Faɗa min ko kuma mu ɓata."


"Ke ce kike kuka. Kuma kin ƙi ki faɗa min ko me aka miki."


Murmushi ta ƙirƙiro na dole, ta ɗora fararen idanuwanta da suka rine zuwa launin ja a cikin nasa. Wani irin kallo take masa mai kashe jiki. Ta ɗan tauni leɓonta, sannan ta ce,


"Ba wani abu ba ne ba fa. Tsakuwa ce ta faÉ—a min a ido."


GyaÉ—a kansa ya yi alamar a'a, bai yarda ba. Bai kuma faÉ—in komai ba, sai dai har yanzu bai daina jin wani iri a zuciyarsa ba.


*


Cikin murya ƙasa ƙasa ya ce,


"Yaya idan babu damuwa, so nake ka ba ni auren Fiddousi."


Ba yayan kaÉ—ai ba, ita kanta Fiddou tsayar da kukan nata ta yi ta É—ora idanuwanta a kansa. Ta gagara furta komai, sai dai bakinta na motsi, alamar tana son yin magana.


"Tun daga ranar da na kaɗe Modu da mota, na hwara ɗora idanuwana a kan Fiddou, na kamu da ƴaunarta, ƙauna mai tsanani. Tun ranar na saka ta a zuciyata. Sai dai kuma na bar abun zaune a raina, ba don komai ba sai don soyayyar da na ga tana yi wa Modu. Ta sadaukar da komai nata saboda samun lahiyar Modu. Ta shiga tsananin damuwa a lokacin da aka hwaɗi matsalar Modu. Wanann dalilin ne ya sa na yi shiru, na ci gaba da dakon sonta. Soyayyar maso wani na ɗawainiya da duk wani saƙo na zuciya da gangar jikina.


Abin da ke ƙara ingiza soyayyar Fiddou a cikin zuciyata shi ne, tausayinta da nake. Ina matuƙar tausayawa rayuwarta. Sosai farin ciki ya yi ƙaranci a rayuwar Fiddou. Baƙin cikin da take ƙunsawa zuciyarta ya fi farin cikin yawa. Wannan tausayin nata da nake shi yake ƙara rura wutar ƙaunarta a cikin zuciyata.


Dalilin da ya sa na daure na hidda zancen daga zuciyata ganin Modu ɗin ya tahi, dangi nai sun tahi da shi, na tabbata ba zai taɓa dawowa inda Fiddou ba. Soyayyar da Modu ke ma Amrah ba za ta taɓa bari ya so wata ɗiya mace ba, koda kuwa a ce bayan ya dawo hayyacinsa ya tabbatar da bata raye ne. Idan ma ya yarda ya auri Fiddou, rayuwa da shi za ta mata wahala. Ga uwa uba al'adunmu da nasu ba ɗaya ba. Akwai abin da za ta yi mai a ganinta ba komai ba, shi kuma a gare shi komai ɗin ne.


Ina so na shiga rayuwar Fiddou. Ina so na hwaranta mata. Ina son bata hwarin cikin da duk ta rasa a rayuwarta. Ina son gusar da damuwa da baƙin cikin da ta cusawa rayuwarta. Don Allah yaya kar ka ce mini a'a. Kar ka butulce wa buƙatata."


Yana direwa nan ya miyar da kallonsa ga Fiddou. Cikin marairaice murya ya ce,


"Fiddou...!"


Ta dakatar da shi da hannu. Hakan ya sa ya yi shiru, ya ci gaba da bin ta da kallo.


"Ashe ba don Allah ne kake taimakona ba? Ashe don da wata manuhwa ce a ranka yas sa kake kula da ni? To na ji, ya ishe ka haka nan. Don Allah ka tashi ka tahi, ni ba ta kai nake ba..."


Kuka ya ci ƙarfinta, da ƙyar ta iya dakatar da shi, ta ce,


"Annur nake so! Annur zan aura! Babu wani a zuciyata bayan Annur."


Ta shanye ruwan hawayenta, ta ci gaba,


"Idan ma ka zo da wasu kalamanka na yaudara ne don in cire Modu daga zuciyata to ka lallaɓa ka tallabe su ku tahi tare. Ko Modu ya so ni ko ya ƙi ni, in dai zai aure ni bani da damuwa. Rayuwa da wani bayan Modu dai ce ba zan iya ba. Matuƴar na auri wanda ba shi ba, lallai za a neme ni a rasa, don kuwa zan tafi inda ba zan sake ganin wani ba, har rayuwata ta idasa a can."


"Ba ma za a yi haka ba."


Mahmouda ya faɗa haɗe da miƙewa,


"Bari in tahi Yaya. Babu komai, Allah ya haÉ—a kowa da rabo nai."


Kama hannunshi ya yi yayanta ya zauna, ya ce da matarsa ta kawo ma Mahmouda ruwa, ya sha su yi magana.


***


Washhh Allah na! Na gaji. Ba laifi na sha typing fa. Ma haɗe wani lokacin, for now dai kam, na gama.😀


Thanks masoyana.😘


Kar ku manta fa a ringa yi ana kankaro mutunci ta hanyar dangwala tauraruwar nan ta hannun hagu.😀


Pinky durling
RAZ 2


[8/30, 7:35 PM] Princess Amrah✍🏻💞: *🅰MRAH NAKE SO!♥*


_(Labari mai taba zuciya, soyayya, sadaukarwa da kuma ban tausayi)_




Sadaukarwa ga masu cutar amosanin jini (Sickler)


Na Amrah A Mashi
(Princess Amrah)
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*




5⃣1⃣


Wattpad: PrincessAmrah


***


A nan inda suke har duhu ya fara, rana ta fara ƙoƙarin faɗuwa. A wannan lokacin kam matan da suke cikin motar ma kuka suke. Su kansu mazan ba ƙaramin jarumta suka yi ba. Kowannensu ya buga uban tagumi, ana zancen zuci.


Tagumin ya rafka shi ma Sans. Ya fara tunanin halin da ya baro mahaifiyarsa a ciki, da kuma yadda take shiga tsananin ciwo idan ulcer'rta ta tashi. Da kuma ƙanwarsa Yamaira, ta daɗe da jigatuwa ita ma.


Bai san sadda ya fashe da kuka ba. Kuka mai ƙarfi, mai cike da zafafan ruwan hawaye.


"Yaro ka yi haƙuri ka ji? Be strong. You're a man, don't act like a woman. Just look at how the women are crying, and you, kai ma kukan kake. What's the different between you and them? There's no! Don Allah ka yi haƙuri, mu taru mu dage da ambaton sunan Allah, muna sanar da shi halin da muke ciki. Mu haɗu mu ma matan can nasiha, tare da nusar da su cewa kuka babu maganin da zai mana baki ɗaya."


Wani dattijo da suka zauna a gaban mota tare ne ya ma Sans wannan maganar, cike da ƙarfafa masa guiwa.


Rage ƙarfin kukan nasa ya yi Sans. Ya dubi mutumin da idanunsa da suka kaɗa suka yi jajur. Cikin wata disasshiyar murya ya ce,


"Baba ya zan yi? Mahaifiyata na can cikin wani hali, yunwa da ƙishi har suna neman galabaitar da ita, ga shi kuma dama tana da matsananciyar ulcer. Ƙanwata ta jigatu, har tafiya ma ba ta iyawa da kanta. A cikin kunnuwana na ji harbin bindiga, wanda ya kawo ƙarshen wayar da nake yi da Abbuna. Na baro su ne cikin wani tsohon gini, da nufin in samu masu siyan wayata, ko zan sama musu wani abu su saka ma cikkunansu. Baba ga ni a nan, mota ta tsaya mana, mun rasa mafita. Ba dole na yi kuka ba?"


Kansa ya gyaÉ—a dattijon, sosai ya tausayawa yaron, musamman ma jin har da yarinya budurwa, yadda Æ´an ta'addan suka dage tafiya da Æ´an mata, abun ba a magana.


Cikin sanyin murya, mai nuna kwantar da hankali, dattijon ya ce,


"To ai ba kuka za ka yi ba, haƙuri za ka yi ka bar wa Allah lamurranSa. Ya san halin da muke ciki, kuma Shi zai fitar da mu. Idan Allah Ya sa mun samu taimako, mun samu man da zai fidda mu, na maka alƙawarin ni zan ba ka kuɗi daga aljihuna ka nemi wani abu ka siya musu, ba ma sai ka siyar da wayarka ba. Akwai kuɗi a hannuna, ni ma motar tawa lalacewa ta yi, wani aiki ya shigo da ni garin, ashe tsautsayin wahala ne ya shigo da ni."


Godiya sosai ya masa Sans. Daga nan suka ci gaba da ambaton sunan Allah, suna masu ƙanƙan da kawunansu.


Kamar an ce Dreba ya É—aga kanshi zuwa titi, tun daga nesa ya hango wata hilux na dosowa daga cikin garin Bama. Kuma dukkan alamu sun nuna cewa ta sojoji ce. Hakan ya sa ya gaggauta sanar da sauran, suka tashi a tare suka nufi bakin titin.


Hannuwa suke ɗagawa su duka, cikin sa'a kuma hilux ɗin ta tsaya, wacce sojoji ne maƙil a cikinta, har a bodinta.


Tambayarsu suka yi abin da ke faruwa, take suka zayyane musu komai, da kuma tsawon awannin da suka É—auka a wurin.


Babu wani tiyo wanda za su sa a zuqo mai, hakan ya sa Ogan nasu ya umurci sojojin da ke cikin motar, da su koma cikin bodi, wancan matan su shigo ciki, mazan kuma su yi skwatin a bodin. Da babu gwara ba daÉ—i.


Abin da ya faru ɗin kenan kuma. A haka suka ƙarisa cikin garin Maiduguri.


Suna shiga garin suka sassauka, a take dattijon nan ya ciri kuɗi masu yawa ya miƙawa Sans, ya masa fatar alkhairi sosai, tare da jaddada masa cewa sai ya bi a hankali wurin shiga garin Bama, musamman ma yanzu da dare ya yi.


Godiya ya masa Sans, sannan ya tari mai mashin, ya kai shi wata restaurant mai kyau. Abinci mai rai da lafiya ya sa aka masa take away, kusan wanda mutum goma za su ci, shi bai ma da nutsuwar cin abincin, ruwa kawai ya sha, sannan ya sai musu lemuka da yawa, ya kama hanyar tafiya.


Kai tsaye tashar mota ya dosa, inda zai samu motar Bama. Sai dai kuma a rashin sa'a, bai samu motar ba. Ga su nan jere birjik, amma duk sun ce ba za su shiga Bama a wanann lokacin ba, saboda abubuwan da suke wakana a can É—in, duk suna da labarinsu.


Kuka yake sosai Sans ya marairaice fuska, ya zaro duka sauran kuɗin da mutumin ya ba shi, wanda za su kai darajar naira dubu ashirin da biyar. Dubu ashirin ya fitar daga ciki, sannan ya miƙa su ga wani dreba, ya ce ya taimaka masa ga kuɗin duka, ya taimaka ya kai shi. Firfir mutumin nan ya ce ba zai je ba. Wayarsa ya zaro daga aljihu, ya haɗa da kuɗin yana kuka, ya ce ya taimaka ya kai shi. Baki ya washe mutumin, ya ƙare ma wayar kallo. Babba ce ba ƙarama ba, sosai za ta yi kuɗi idan zai siyar.


Cikin murya ƙasa ƙasa ya ce,


"Na amince zan kai ka, amma bisa ga sharaÉ—in a bakin gari zan ajje ka idan mun isa, ba zan shiga ciki ba."


Saurin É—aga kansa ya yi Sans, ya ce,


"Na amince wallahi."


HaÉ—e da hanzarin É—aukar ledojin abincin, ya bi bayan mutumin suka isa wurin motarsa.


Yana jin yadda abokan aikinsa ke masa magana kan cewa kar ya je, amma ina, bai ko saurare su ba ya ƙeƙashe, suka kama hanyar Bama.


***


Ruwa mai sanyi ya kora Mahmouda, yana mai tsananin jin ɗaci da raɗaɗi a cikin zuciyarsa. Me ya sa Fiddou za ta masa haka? Dama abin da ya jima yana ji ma tsoro kenan. Shi ya sa tun asali shi bai yarda da soyayya ba. Bai kuma taɓa shiga ƙanginta ba sai a yanzu.


"Mahmouda ka yi haƙuri da duk kalaman da ka ji sun fito daga bakin Fiddou ka ji? Yarinya ce. Ita har yanzu gani take kamar soyayya da mahaukaci zai yi riba a gare ta, wanda kuma sam, hakan ba mai yiuwa ba ne a gare ta. Ina so ka ci gaba daga inda ka tsaya, tunda dai duk tsiyarta ai ba za ta taɓa ci gaba da rayuwa a haka babu aure ba. Na tabbata Modu ya tahi kenan, ba zai dawo gare ta ba. Ka ba ni daga nan zuwa mako guda, zan tari kawunmu da maganar, na tabbata zai tsawatar mata, zai kuma aura maka ita, saboda ni kam har ga Allah na yarda da nutsuwarka."


Nannauyar ajiyar zuciya ya sauke Mahmouda. Ya kalli ƙofar da ya ga Fiddou ta shiga, bai ko hange ta ba. Murmushin ƙarfin hali ya yi, haɗe da furta,


"Amma

Please Login or Register in order to submit comment