You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gashi na manta da Annur zai kira ni. Subhanallahi!"


Ta matuƙar jin haushin hakan, damuwarta ma ɗaya plan ɗinsu da yake neman lalacewa.


Kamar ta latsa kiransa, saboda kiran da ya mata ya fi ƙarfin talatin. Ga kuma na Jiddah, wanda aƙalla zasu kai uku ko huɗu. Sai na Bobby guda biyu, na wata lamba guda biyu.


Rasa wanda zata fara kira ta yi, hakan ya sa kawai ta fasa, ta cire daga silent, sannan ta nufi ban É—aki domin É—auro alwala.


Tun tana ciki ta fara jiyo kira a wayar, bata fito ba har sai da ta kammala alwalar duka, a lokacin wayar har ta tsinke an sake kira.


Lambar Annur da ta yi saving da sunansa ta gani, hakan ya sa ta sauke ajiyar zuciya, haÉ—e da É—aukar wayar.


"Assalamu alaikum."


Ta faÉ—a cikin sassanyar muryarta, wacce ke nunar da ta tashi daga barci.


Nannauyar ajiyar zuciya ya sauke, bai san sanda ya saki murmushi ba, yana mai matuƙar jin daɗin muryar tata. Tun bayan wayarsa da Bobby ya kasa barci, maimaita kiran Maryama kawai yake amma bai dace ba, sai yanzu da ya riga ya cire tsammani.


"Maryama kina lafiya? I've been calling your number baki É—auka, I hope all is well."


"Zan iya sanin da wanda nake magana?"


Ta furta cikin salon jan hankalinsa, dan ta tabbatar ba zai ɓoye mata ba, dole zai mata bayanin kansa.


"Ye..yes, why not? Am Annur Iqra Al-Hussein. Na kira ki ne, akwai maganar da nake so mu yi."


Gyara zamanta ta yi bayan ta zare wayar daga chaji, ba tare da tunanin komai ba ta ci gaba da saurarensa.


"Ina fatan zaki bani aron lokacinki, ki saurari kalamaina, ki ji abin da nake tafe da shi. Amma fa sai kin daure, saboda abin da yawa, zai iya É—aukarmu tsawon lokaci."


"Ina saurarenka."


Ta faÉ—a a hankali, ta ma cire tunanin karatun da zata yi, saboda a ganinta, wannan wata dama ce ta zo mata, wacce ta jima tana tsumayenta.


"Maryama! Kin tashi kuwa?"


Ta jiyo muryar Mamanta, tana tinkarowa É—akinta.


***


A inda take zaune ta haɗa kai da guiwa ta fara jiyo takun mutane. Daga kanta ta yi ta kalle su, Mahmouda ne da ƙannen nan nasa, suna mata kallon tuhuma, suna son sanin dalilin kukan da take yi.


"GiÉ—e ba kuka zaki yi ba. Allah ne Ya É—ora mai wanga laluri, kuma shi zai yaye mai."


ÆŠaya daga cikinsu ta faÉ—a, tana jin tausayin Fiddou.


Ta buɗe bakinta zata mata magana ke nan likita da nurse suka shigo, hannun nurse ɗin riƙe da takarda.


"GiÉ—e ga reffer letter É—inai nan. Ku É—aukai ku kai asibitin gwamnati. Na kira abokina na sanar mai yanzu, ku tahi dai, Allah Ya bashi lahiya."


Mahmouda ne ya karɓi takardar, yana son sanin dalilin yi ma Modu reffer ɗin.


"Gata nan zata yi ma bayanin komai. Kai ina ganin hwa mun gama da kai, ina Æ´an sandan nan suke? Su taho ka yi signing, dan ya warke da duk abin da ka damunshi wanda ya danganci banka tai da ka yi, sai Æ´an raunukan da ba za a rasa ba.."


Sauke ajiyar zuciya ya yi Mahmouda. Yana jin zuciyarsa ta samu sassauci, yanzu kam zai zauna zaman ta'aziyyyar mahaifiyarsa ba tare da tunanin komai ba. Sai dai kuma me? Yana tsananin tausayin Modu, gashi kuma bai san abin da yake damunsa ba.


"Mun gode ƙwarai Dr. Ka taimaka muna ƙwarai da gaske, Allah Shi saka ma da alheri."


Fiddou ta faɗa tana ƙoƙarin shanye hawayenta.


"Babu komai ai. Allah Ya bashi lahiya, Allah Ya taƙaita abin."


Amin suka amsa da shi su duka da ke wurin, kafin likitan ya juya, Mahmouda ya bi bayansa.


Kun ga ɗan ƙaramin haukan da Annur ya yi ko? wai duk gudun kar ƙullinsa ya warware. Ya manta cewa dare dubu na ɓarawo, rana guda tal ta mai kaya. Duk irin mugun abun da mutum yake aikatawa, dole akwai ranar tonuwar asirinsa, akwai ranar dana sani, akwai lokacin da zai fallasa, kowa ma ya san da halinsa


gaisuwa ta musamman gare ki Queen miemie.


Jinjina da fatan alkhairi ga Æ´an group É—in Nagarta writers fans. Ina yinku irin totally É—in nan, fi sabilillah.


Kamar yanda na faɗa maku, ba kullum ne zaku ringa ji na ba, sai dai zan yi iya ƙoƙarina, dan ganin kuna samu akai akai.


Thanks all.


Pinky durling
RAZ 2
[8/30, 3:49 PM] Princess Amrah✍🏻💞: *🅰MRAH NAKE SO!* ♥


(Labari mai taba zuciya, soyayya, sadaukarwa da kuma ban tausayi.)


Na Amrah A Msh
_(Princess Amrah)_
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*


_Sadaukarwa ga masu cutar amosanin jini (sickler)_


3⃣5⃣




Cikin tsarguwa ta gaggauta janye wayar daga kunnuwanta, ba tare da ta kashe ba. Ƙoƙarin amsa kiran Maman tata take, sai dai tana gudun bincike irin na Mama, babu wuya za ta gano cikin halin da take.


"Maryama kin tashi kuwa?"


Ta sake jin muryar Mama, saboda bata riga ta kunna hasken É—akin ba dama.


"Ehh, ehh na tashi. Har alwala ma na yi Mama."


"Ok masha Allah! A yi sallah kafin a fara karatun ko? Za ki fi jin daÉ—insa sosai."


"To." kawai ta faÉ—a haÉ—e da latsa switch na wayar, ta kashe ta baki É—aya.


Miƙewa ta yi tana jin kamar ƙafafuwanta ba za su iya ɗaukar gangar jikinta ba. Ko kaɗan ba ta yi tsammanin zuwan Mamanta a daidai wannan lokacin ba.


Dafe kansa ya yi a daidai sanda yake jin kalaman Mama. Gabansa ne ya tsananta duka, yana tunanin yanda zai yi kuma.


Sake kiranta ya yi amma ya ji a kashe, bai san sanda zazzafan hawaye ya fito masa ba, duk iya jarumtar dannesan da yake yi.


"Shi kenan na san by now boka ya yi zuciya. Ya zan yi ne ni Annur? Am totally confused, I've no idea on what to do, help me out ya Allah!"


Sallarta ta fara bisa kafet, tana mai ƙoƙarin cire rauni daga zuciyarta. Bayan ta gama ta hau karatu sosai, tana jin yanda natsuwa ke daɗa sauka ga duk ilahirin jiki da jininta. Lallai karatun Al'Qur'ani wani abu ne, wanda babu tamkarshi, wanda ke dakar da zuciyar mutum, yake saka natsuwa sosai a cikin zuciya.


Ta jima tana karatun kafin ta sadaƙe, ta miƙe ta kawo raka'a biyu, a lokacin ƙarfe uku na dare kenan. Bayan ta gama ta yi addu'a sosai, ta ma iyayenta, sannan kuma ta kai kukanta wurin Allah, a kan wannan aiki da take son yi. Tana son Allah Ya taimaka mata, ya kawo mata mafita, kar wani abu ya faru da su har su gama.


Kwanciya ta yi da addu'a a bakinta, ta tofa wa kaf ilahirin jikinta, da hijabi a jikinta bata cire ba, barci ya yi awon gaba da ita.


Kwalbar codein ya fiddo daga cikin deep freezer É—insa, ya jijjiga ta sosai, sannan ya É—aga kansa ya kwankwaÉ—e, yana son damuwar da ke cikin zuciyarsa ta kau.


Sigari a fiddo daga lakar bed side nashi, ya bata wuta, sannan ya hau zuƙarta, yana yi hawaye na fita daga idanuwansa, hawayen neman mafita kawai, dan ya tabbatar matsala ta auku, babba ma ba ƙarama ba.


Washe gari.


Da ruwan sama aka tashi kamar da bakin ƙwarya. Tun bayan da aka kammala sallar asuba ruwan ya sauko, da ƙarfi sosai, irin mai haɗe da iska ɗin nan.


Baccin safe take mai cike da jin daɗi. Tana jin daɗin baccin matuƙa, ko farkawa ba ta yi ba tun da ta yi sallah ta kwanta.


A hankali ta fara buɗe idanuwanta, tana jin yanda zuciyarta ke mata rauni, wanda ta rasa dalilin hakan. Ta sani, duk sanda ake ruwan sama daɗi take ji a zuciyarta, tana son yanayin sosai, ba wai lallai sai tana barci ba, ko idonta biyu ma. Amma a wannan gaɓar, saɓanin haka take ji. Ga tsananin duka da zuciyar tata take yi, tana tuna abin da ya faru bayan ta gama sallar asuba.


*
Da ƙyar ta iya buɗe idanuwanta, saboda barcin da yake cikinsu, na tashin da ta yi.


Miƙewa ta yi bisa kafafuwanta, tana hamma haɗe da miƙa, ta nufi hanyar banɗaki.


Alwala ta É—auro sannan ta hau bisa kafet, ta fara da raka'atainil fajr sannan ta yi sallar asuba, a lokacin ruwa ya fara saukowa a hankali, ana yayyafi, ga iska sosai ana yi.


Bayan ta gama ta yi adhkar, sannan ta cire hijabin nata, ta haye bisa gado ta kwanta.


Ta jawo bargo zata lulluɓa kenan ta ji fitsari take ji, hakan ya sa ta miƙe ta yo sannan ta dawo. Abin da ba ta saba yi ba kenan, ko kaɗan ba ta yarda ta kwanta ba tare da alawala ba, ko da kuwa bayan sallar asuba ne irin na yau.


Gabanta ne ya faÉ—i, ta dafe zuciyarta, tana tunanin dalilin faruwar hakan, sai dai kuma ta gagara ganowa, take ta kawar da komai, ta haye gado ta kwanta abinta.


Bakinta ta buɗe zata fara addu'a, sai hamma ta zo mata, ta ƙarisa salatin da take yi haɗe da hammar, sannan kawai ta juya ta ci gaba da baccinta.


*
Ƙoƙarin motsa hannunta ta yi amma sam! Ta kasa. Ta gwada ɗaga gangar jikinta nan ma ta kasa komai. Gabanta ne ya tsananta faɗuwa, ta fara tunanin abin da ya same ta, sai dai ta rasa gane komai, tunanin mummunan mafarkin da ta yi kawai take.


Ƙyafcin ido kawai take iya aikata wa, daga ba shi ba kuwa, komai ta kasa yi, bakinta take so ta buɗe ta ƙwala wa mamanta kira ma ta kasa.


A hankali ta fara jin wani nannauyar abu na fita daga cikin zuciyarta, yana saukowa har bisa gangar jikinta, tun daga bisa kanta ya ringa tafiya, har sai da ya iso bisa tafin ƙafarta. A daidai nan ne ya fice da ƙarfin gaske, ta ji wata irin azaba wacce tun da take a rayuwarta ba ta taɓa jin irin ta ba. Kamar an ɗauki garwashi an watsa mata a tafin ƙafar haka ta ji.


Tun bayan fitar abun kuma ta ji ta koma daidai, hannun na ta ma ya É—agu, sannan a hankali ta tashi zaune, tana tunanin abin da ya same ta.


Ba ta san sanda hawaye mai zafi ya fara mata kwaranya ba. Hankalinta a tashe ta dafe ƙirjinta, ta runtse duka idanuwanta, tana karanto addu'a a bakinta.


Sai a yanzu ma take tunanin abin da ya faru da asuba. Ashe fa ta manta babu alwala ta kwanta, saɓanin ko yaushe, yanda ta saba a rayuwarta ko bata sallah to ba dai ta kwanta ba ta da alwala ba.


Addu'a sosai take yi, tana kuma samun natsuwa sosai, tana jin sassauci a cikin zuciyarta.


"Assalamu alaikum."


Muryar Muhammad ce ta saka ta buɗe idanuwanta, tana kallonsa cikin shiga mai kyau, ya saka farar shadda da baƙar hula.


"Yaya Maryama lafiya na gan ki haka?"


Ya faÉ—a yana bin ta da kallo, saboda yanayin da take ciki dole ne a fahimci ta yi rashin natsuwarta ne.


"Uhmm...babu komai Hammad. Ba dai har ka shirya ba."


"Na shirya Yaya Maryama. Ke kawai nake jira."


"Ok ka koma a falo ka jira ni ina zuwa."


"To."


Kawai ya faɗa sannan ya fita, har ya ɓule daga ɗakin bai daina waiwayenta ba.


Wanka ta shiga daga nan, a ranta tana tunanin halin da ta shiga yau. Lallai mai rai ba wata tsiya ba ne. Cikin lokaci kaÉ—an komai na ta ya juye, ta gagara ko da motsi. Yanzu fa idan mutuwa ce ma a haka za a ce ai an kwana da ita lafiya, aka wayi gari babu ita.


A kasalance ta gama shirin. Ta saka baƙar abaya mai adon pink. Sannan ta ɗaura ɗankwalin a kanta, ta fiddo ƙaramin mayafi pink ta ɗora a bisa gado.


Falo ta fito jikinta sukuku, sai ƙoƙari take dan ganin ta koma daidai amma hakan ya gagara. Fargaba ce haɗe da tsoron Allah mamaye a cikin zuciyarta.


"Ina kwana Mama?"


Ta faÉ—a da sassanyar muryarta, tana saita dubanta zuwa ga mahaifiyarta.


"Lafiya ƙalau Maryama. Kin sha barci. Ai tun ɗazu Muhammad ke son zuwa ya tashe ki nake hana sa. Wai ya ƙagara ku tafi haka nan."


"Ai fa dai na ga alama Mama. Tun da ga shi nan har ya shirya tun É—azu. Allah dai Ya sa zakwaÉ—i ma ya bar shi ya karya."


"Ya ci ƴar guntuwar doya. Kin ga sauran nan ya ƙulle a leda wai zai tafi ma Abdul-Ahad da ita."


Dariya sosai Maryama ta kece da ita. Da gaske Muhammad ya bata dariya. Wato shi ya rasa ma abin da zai kai wa Abdul tsaraba sai soyayyar doya, wadda ta riga da ta gama hucewa.


"Nawawo for this boy. Kai yanzu fi sabilillahi wannan doyar ce zaka kai ma ƙaninka tsaraba?"


Matsowa ya yi kusa da ita yana murmushi.


"To Yaya Maryama ai ya fi na je masa haka nan ko? Amma idan na kai masa doyar nan na tabbata zai ji daÉ—inta."


Su dukansu dariya suke a wannan gaɓar, har shi kanshi Muhammad ɗin dariyar yake.


Miƙewa ta yi za ta ɗauko kalacinta ta ji wayarta na ringing. Aunty Islam ta gani a rubuce, hakan ya sa ta koma ta ɗauki kiran da sallama a bakinta.


Kusan mintinsu biyu suna waya, kafin ta juyo ga Mama ta ce,


"Wai a gidansu zamu same su. An fara yi masu aikin gida ne yau, tun jiya da dare mijin ya ce kawai ta je can gida. Har kira na ma ta yi da wata lamba a cikin daren ban É—auka ba. Ga shi nan za ta turo min address yanzu."


Mama ta ce,


"To ba damuwa ai. Sai ki hanzarta, na tabbata yanzu za ku ga Mallam Ado ya zo É—aukar ku."


Kitchen ta nufa ta zubo doya a plate, sannan ta É—auko lemon 5 alive haÉ—e da cup a hannunta.


Zama ta yi tana ci a hankali, fiye da rabin tunaninta yana ga abin da ya faru yanzu. Ta na son kiran Jiddah ta sanar da ita komai, sai dai kuma yanzu babu lokaci, dole sai idan sun dawo.


Ba ta gama ci ba Mallam Ado ya yi sallama. Yana Shaida masu cewa ya iso, su same sa a waje.


Tashi ta yi ta mayar da kayan kitchen, sannan ta shiga É—aki ta yafa mayafinta ta fesa body spray ta fito.


Bankwana su ka yi wa Mama, sannan su ka fice daga gidan, zuciyar Muhammad sayau take, yana tsananin jin daÉ—in ziyarar da za su kai ma Abdul.


***


Annur kuwa tun da sassafe ya shirya cikin ƙananan kaya ya fita, ko sallama bai tsaya ya yi ma Momy ba kawai ya kama hanyar gidan su Farouk Sardauna.


Kiran Bobby É—in ya yi a waya, bai ko tsaya ya É—auka ba ya fito, dan ya san dalilin kiran nasa.


Buɗe motar ya yi ya zauna a gaba sannan ya rufe. Ya kalli yanayin abokin nasa, yanda duk ya bi ya susuce a cikin ƙanƙanin lokaci.


"Annur wannan fa damuwar da ka saka kanka a ciki sam! Ba ita ce mafita ba. Dolenka ka zama jarumi, ka ƙoƙarta mayar da komai ba komai ba, sannan walwalarka za ta dawo. Amma idan kana cikin wannan halin, ba ka tsammanin su Momy za su iya fahimtar wani abu? Lallai dole za su fahimta."


Duk da tuƙi yake amma hakan bai hana shi kallon Bobby ba. Ɗan lumshe idanuwansa ya yi, sannan ya mayar da kallon na shi ga tuƙinsa, ya ce,


"Duk yanda zan yi dan ganin na kawar da wannan damuwar na kasa. Haka kawai nake jin gabana na faÉ—uwa, kamar komai ya kusa dagule wa. Ina fargabar haÉ—uwarmu da boka, dan ba ni da hujjar da zan kare kaina a wurinsa."


Ajiyar zuciya ya sauke Bobby, a tsanake ya ce,


"Haka ne. Amma kuma ai dole ya maka uzuri. Shi kansa da yake aiki da tsafi tun farko ya ce yarinyar ta gagae shi, bare kuma kai da ba ka taki komai ba?"


"Haka ne Farouk. Maryama kam ta yi nisa ba ta jin kira. Ta riƙa sosai a ibada, ban kuma ga abin da zai iya dakatar da ita ba."


"Ina ga kawai abin da ya kamata, idan da yanda zai yi ya canza salon aikin baki ɗaya sai ya taimaka mana. Wannan dokar ta true love gaskiya dole a karya ta, saboda fa zuciya ba ta da ƙashi. Ba ka isa ka tanƙwara ta a kan abin da ta gani tana so ba."


Da wannan firarrakin suka isa wurin bokan. Kai tsaye suka zarce tare da aikata duk yanda su ka saba idan sun je wurinsa.


Zama suka yi a ƙasa, Bobby ya masa kirari sai ga shi ya ɓullo, yana kallonsu su duka biyun.


Murmushi ya saki da ƙarfin gaske. Ya dunƙule hannuwansa duka biyun sannan ya buɗe su.


"Ka yi aiki mai kyau, ban taɓa tsammanin yiuwar aikin nan ba. Daga farko na ji haushinka sosai, saboda wahalar da ka ba ni, kuma a banza. Sai dai na daure a ƙarshe, sai ga shi kuma mun yi nasara."


Ido buɗe suka kalli junansu, suna matuƙar mamakin kalamansa. Su da su ka yi zaton zai balbale su da masifa, amma sai su ka ji akasin hakan, hasali ma yabo ne ya fito daga bakinsa.


Page din nan ya ba ni wahala. Sai da na rubuta fiye da rabi ya goge😭 da ƙyar na samu maimaita shi. Amma duk da hakan dai ya sha banban da na farkon.


Thanks my fans, ina jin daÉ—in yanda kuke bibiyata.


Saƙon ta'aziyya ga masoya Irfan. Ina mai taya mu jaje na rashin jarumin labarin MH da mu ka yi😧 na sha kuka kamar ba gobe, har nake jin mutuwar kamar da gaske ne ta faru. Sai dai kuma ba abun mamaki ba ne, saboda mutuwa ko kalmarta kawai ka ji wani tashin hankalin ne. Fatanmu dai Allah Ya sa mu yi kyakkyawan ƴarshe, ya kyautata makwancinmu.


Ina jajen ƙawata XARAH BB. Ban san ina kika shige ba, ta yiu kuma ɗan Baba ne ya ɓoye mana ke.😂 Allah Ya bada lafiya amin.


Pinky durling
RAZ 2
[8/30, 3:50 PM] Princess Amrah✍🏻💞: *🅰MRAH NAKE SO!* ♥


(Labari mai taba zuciya, soyayya, sadaukarwa da kuma ban tausayi.)


Na Amrah A Msh
_(Princess Amrah)_
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*


_Sadaukarwa ga masu cutar amosanin jini (sickler)_


3⃣6⃣


Assalamu alaikum.
Na samu ƙorafi daga wasu cewa; wai duk karatun da Maryama ta yi kuma sai asiri ya kama ta?


Abin da nake so ku gane shi ne; a duk duniya babu mutum sama da manzon Allah, (SAW). Shi ne mafi daraja, ma fi soyuwa ga Allah MaÉ—aukakin Sarki!
Shi ne wanda ya fi kowa ilimi, kuma ya fi kowa aiki da shi.
Shi ne wanda ya fi kowa ibada, kuma yake kiyayewa.
To kuma asiri ya kama shi. Shin mu waye da asiri zai gagara kama mu? Shin Maryama wace iriyar mutum ce, wacce asiri zai gagara kama ta? Kar ku manta, an jima ana ƙoƙarta asirin ya kama ta, amma ya gagara shigarta, saboda kariya.
To lokaci É—aya kuma Allah Ya jarrabe ta, Ya shagaltar da ita, sam! Ta gagara yin abin da ta saba yi. Kenan dai ba abun mamaki ba ne dan asiri ya kama ta.
Masu wannan tunanin, ku yi haƙuri ku zuba min ido. Ni na san kan labarina, na kuma san yanda ya kamata.
Please and please, ku zuba min ido kawai, ku dai aikinku karatu ne. Ku bari har sanda na kammala, duk mai ƙorafi ƙofa a buɗe take. A daidai lokacin an ga yanda ƙarshensa zai yi kenan.
Fatan za a fahimce ni.
Wanda na ɓata wa ya yi haƙuri.


***
Cikin É—aga sauti bokan ya ce,


"A yanzu kam an gama komai. Duk wata damuwa ta ka ta ƙare Annur, saboda an samu nasara a kan yarinyar, duka soyayyar da kake mata an fitar, aiki kuwa zai gyaru sosai yanzu."


Murmushi suka saki su duka biyun a tare, duk da ba su san dalilin faruwar hakan ba, sai dai su na ji a jikinsu akwai dalili.


"Ku ajje abin da za ku ajje, ku tafi, an kammala da aikinku. Ina mai tabbatar ma ku da cewa asirinku ba zai taɓa tonuwa ba. Wannan ɓoyayyen al'amarin ba zai taɓa fallasuwa ba."


Kuɗi ya ciro daga aljihunsa Annur, ya dire su a gaban boka, sannan suka miƙe su duka biyun, suka nufi barin gidan.


A mota har rige rigen magana suke, Annur ya ce,


"Ko ta ya wannan aikin ya faru?"


"Tambayar da ke cikin zuciyata kenan. Amma dai wannan ba shi yake gabanmu ba. Fatanmu dai aiki ya yi, kuma ya yi ɗin. Faƙat."


Hannu suka haɗa suka tafa da ƙarfi, duk wanda zai kalle su zai tabbatar da tsantsar farin cikin da suke cikinsa.


***


Tun daga sanda aka ba Fiddou reffer letter take rusar kuka. Tana son zuwa gidansu ko dan a ji daga gare ta, amma kuma ba ta son tafiya ko yaya ta bar Modu. Tun washe garin da suke asibiti ta je gida ta É—auko kaya, ba ta sake komawa ba. Yayanta dama ya yi tafiya, matsarsa ce kawai, kuma ba ta damu da ita ba bare har ta nemi jin halin da take ciki.


Tagumi ta buga a bisa teburin da take zaune, sai Modu kwance suna jiran likita. Kimanin awarsu biyu kenan a asibitin, sai dai da yake asibitin gwmanati ce, akwai layi sosai, dole sai sun bi har a zo kansu. Ita babban tsoronta ma kar Modu ya farka, dan ba ta san yanda za ta yi da shi ba.


Da haka har aka zo kansu. Irin kujerar ɗaukar marar lafiyar nan ce ta yi magana aka zo da ita, mutum biyu su ka cicciɓa Modu suka zaunar a ciki, sannan su ka tura shi har cikin Ofishin likitan.


Zama ta yi bisa kujera tana fuskantar likitan, damuwa ce danƙare a cikin zuciyarta, tana ƙoƙarta danne hawayen da ke fita daga idanuwanta.


"What's his problem?"


Muryar likitan ta dawo da ita hayyacinta.


Takarda ta miƙa masa, ta ce,


"Mu ne Dr. Huzaif yat turo daga Amana clinic. Ga takarda tai nan."


Karɓa ya yi likitan yana dubanta, ya ce,


"Mi da ba ki shigo ba tun É—azu? Ai ban san kun iso ba giÉ—e."


Shiru ta yi bayan ta sadda kanta ƙasa, dan ba ta ji ko kaɗan tana da ra'ayin yin doguwar magana. Damuwar halin da Modu yake ciki kawai ta ishe ta. Ga kuma zullumin abin da zai faru.


"Gado za a ba shi."


Ya faÉ—a bayan ya ajje takardar bisa teburinsa. Ya É—auko abin awon zuciya ya É—ora a saitin zuciyar Modu, yana jin yanda ba ta tafiya yanda ya kamata.


"GiÉ—e na cikin matsala mai girma. Ina gudun kar zuciya tai ta mutu, wato ta tsaya cak!..."


Yana neman ci gaba da magana Fiddou ta dakatar da shi da hannu.


"Halan wane irin likita kake? Mi da ba ka san irin maganar da za ka hwaÉ—i ma mutane ba? Yanzu idan aka yi gawa biyu hwa? Ba ka gudun maganar da kai yi tana iya tsaida bugun zuciyata? Halan ka san irin darajar da Modu gare shi a cikin zuciyata?"


Kuka sosai ya ci ƙarfinta. Kalaman likitan take ji suna ratsa duk wata gaɓa ta jikinta. Tsoro take kar maganarsa ta tabbata.


"Haba i haƙuri giɗe!"


Ya faÉ—a yana murmushi, kamar ma bai damu da munanan kalaman da Fiddou ta jefa masa ba.


"Kwantar da hankalinki ke jiya. I'll try my best dan ganin giɗen ga ya samu lahiya. Likitan zuciya nike, na miki alƙawarin ba shi kulawa iya ƙarhina."


Sai a sannan ta É—an samu sassauci, amma duk da hakan ba ta daina yin kuka ba.


Nurses ya kira cewa su ba Modu É—aki, kuma Amenity za a ba shi, saboda mutum mai matsalar zuciya ba ya son wurin da za a yawaita hayaniya, ko kuma mai cinkoso da yawa.


Bin bayansu ta yi Fiddou, a daidai wannan lokacin ta daina kukan, sai dai kukan zuci kawai take, wanda da shi ta gwammaci tai ta yin mai ƙarfi.


Gyare yake É—akin tsaf, su na shiga wani lebourer ya shigo da bed sheet da pillow case, ya shimfiÉ—a a gadon, sannan aka kwantar da Modu a kai.


Bayan sun bar É—akin ne aka bar ta daga ita sai Modu. Hakan ya sa ta tashi ta É—an rufe shi da blanket, sannan ta fara haramar tafiya gida.


Ta Offlishin likita ta fara biyawa, ta shaida masa cewa za ta je gida, idan akwai wani abu da ake buƙata sai a rubuta mata yanzu kafin ta tafi.


Babu komai ya shaida mata. Yanzu jiran farkawarsa kawai yake, saboda akwai abin da yake son ji daga gare shi.


"Dr. Ya na da taɓin hankali hwa. Halan mi za ka ji daga garai?"


Ta faÉ—a cikin muryar tausayi.


"Duk da haka akwai dabarar da zan ringa yi mai, sannu a hankali za mu yi shaƙuwar da da kai nai zai hwaɗa min damuwa tai."


Shanye kukanta ta yi, ta ce,


"To shi kenan likita. Ina hwatar hakan. Bari in

Please Login or Register in order to submit comment