You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Tun da safe na so in taso kuma, sai kuma muna wani bikin ne, ƙanwar mijin yayata ake ma aure, yayar tawa ta ce ban isa in taho da wuri ba, sai dai in bari har da yamma sannan in taho sai in kwana a nan ɗin."


Jiddah ta murmusa, ta ce


"Sannu to ai mun gode da hakan ma."


"Angon naki ne wannan? Na ga kun yi matching sosai."


Kallon juna suka yi Jiddah da Deedah. Deedah ya ce mata,


"Namu za ki zo next insha Allah."


Kunya sosai Jiddah ta ji, ta masa hararar wasa.


Bayan sun isa gidan amaryar, sai da Hadiza ta fita sannan suka yi bankwana, Deedah na ce mata duk matsakar da gare su kar ta ji komai kawai ta kira shi, insha Allahu zai musu koma meye.


Tare suka shiga cikin gidan, Jiddah da Hadiza. A lokacin duk an gama watsewa, wanda za su kwana kawai suka rage, sai kuma Dr. Islam da mutanenta; Hammad da Abdul-Ahad.


*


Sosai suke nishaɗi a gidan amaryar, kusan ƴan mata takwas ne za su kwana, babu iyaye a cikinsu duka iyayen sun gama tafiya. Sai famar tsokanar Maryama suke, murmushi kawai take sakar musu, a wani ɓare na zuciyarta kuma ba ta daina al'ajabin zoben nan ba. Haka kawai take jin faɗuwar gaba tunda al'amarin zoben ya kasance. Ta rasa dalili.


Gama sallarta kenan Jiddah ta ninke hijabin ta miƙo ma Maryama.


"Oya take your hijab. Kar sai bayan biki ba ki ga wannan hijabin naki na gado ba ki ƙwala min kira a waya."


Murmushi kawai ta saki, ba tare da ta furta komai ba. Saboda ita kam yadda jikinta ya gama saɓulewa, ko yawaita surutu ma ba za ta iya yi ba.


"Wannan Jiddar tunda suka iso sai wata fara'a take da na kasa fahimtar dalilinta."


Saudat ce ta yi wannan maganar, tana latsar waya tamkar ba ita ce ta yi maganar ba.


Caraf Hadiza ta ce,


"Ah to ba dole ku gan ta a cikin nishaÉ—i ba."


ÆŠago kai Saudat ta yi tana murmushi, ta ce ma Hadiza


"Gist me ƙawata. Wani abu ya faru ne?"


Hadiza ta saki murmushi tana kallon Jiddah, ta ce,


"In faÉ—a ko kar in faÉ—a?"


Banza ta mata, tana sakin guntun murmushi.


"Tunda ba za ki yi magana ba to bara kawai in tona. Tare take da Habibin nata fa, su suka ma É—auko ni da kansu. Wannan ango nata ko tsageran ango. Baida kunya ko É—iris."


Duka É—akin suka kwashe da dariya, har da Maryama.


"Hadiza sharri ko?"


"Ba wani sharri Jiddah. Ai wani mayen kallo da na ga yana miki na jima ina mamaki. Har da kunyata ba ku ji ba."


Dukan wasa Jiddah ta kai mata. Ta ce,


"Kina nufin muna gaba kina baya amma har kin hangi muna wani irin kallo? Hadiza fear God wallahi."


"To na ji. Amma dai wace irin soyayya ce ba ku yi a gabana ba? Malama ni fa har sai da na ji ina ma a ce ba mu iso ba. Saboda ina kallon ku ina ƙara koyon soyayya."


Sosai suke dariya. Suna matuƙar jin daɗin hirar tasu. Har dare ya nisa amma ba su sani ba. Dama tun wuraren takwas Kawu Marwan ya aiko musu da take away na chips da kaji da yawa yadda zai wadace su.


Cikin muryarta da ta gama disashewa da kuka ta ce,


"Wai ni kam Hadiza ina Fiddou ne?"


"Fiddou ta yi aure Maryam."


Cikin mamaki Maryama da Jiddah suka kalle ta.


"Ta yi aure? Yaushe? Wa ta aura?"


Duka a jere Maryama ta yo ma Hadiza wannan tambayoyin.


"Yau ɗin nan aka ɗaura mata aure. Ai shi ya sa ma ban zo da wuri ba. Aunty Sahiya ta ce bai kamata in taho tun safe ba tare da na tsaya har a ɗaura aure ba. Ta auri wani Mahmouda. Yauwa, ƙila ma za ku san shi. Ta ce min wai shi ne wanda ya taɓa kaɗe Modu da mota."


Murmushi Maryama ta saki, wanda yake kai tsaye tun daga cikin zuciyarta. Da biyu ta yi murmushin. Na farko ta jiye ma Fiddou daɗi da ta yi aure. Na biyu kuma ko ba komai ta huta da alƙawarin da ta ɗaukar mata, kan cewa Annur da kanshi zai koma ya aure ta.


"Amma kuwa na ji mata daÉ—i sosai wallahi. Allah ya sa alkhairi ya ba su zuria ta gari."


"Ameen Jiddah. Daga nan kuma sai ina? Sai gidanki."


Ta yi dariya.


Haka dai suka ci gaba da hira sosai har kusan uku na dare sannan suka yi barci. Da asubar fari kuma ɗaya daga cikin ƙawayen amarya mai suna Humaira ta tashe su. Sai masifa suke mata amma ta hau yi musu dariya, wai ai dama gidan amarya ba wani barci ake yi sosai ba. Hakan dai suka daure duk suka miƙe, suka jira lokacin sallah ya yi sannan suka gabatar.


*


Ba wani abu aka yi ba washe gari asabar. Kawai dai sauran tarkacen amarya da ba a kawo ba ne aka ƙarisa kawo su. Ƴan matan suka jejjera mata, sannan duk wani jere da manyan suka yi ranar jere da suka ga kamar bai yi ba, suka bi duk suka gyaggyara shi. Gidan su Maryamar ne aka yi guntun taro, shi ɗin ma don kar a ce ba a je gidan amarya an yi wani abu ba ne.


Da yamma suka fara warwatsewa har Hadiza ma ta tafi, ya rage daga Jiddah, Saudat sai Afrah kawai suka yi saura. Share mata ko'ina suka yi suka mata goge-goge. Toilets duk inda aka ɓata suka bi suka goge shi.


Misalin tara na dare motar da za ta É—auke su ta zo, wadda Deedah ya turo kawai don ya musu wayo ya samu su tafi ko zai samu shan hira da masoyiyarsa. Hakan kuma sai ya ma Jidda da Maryana daÉ—i, koba komai za a kawo ango ba a gaban su Afrah ba, tunda ba su san komai game da shi ba.


Ƙarfe tara da rabi Abba, kawu Imrana da kuma Uncle Marwan suka iso gidan, tare suke da Annur da ya sha wankan wani dakakken yadi kalar ruwan madara, an ƙawata ɗinkin da surfani shi ma irin kalar, ga hula kalar kayansa wadda ta yi matching sosai. Fuskar nan tasa mai cike da walwala ta yi fayau, sai famar sakin dariyar yaƙe yake, wacce in ba ita ɗin ya yi ba, babu wanda zai kalle shi ya ce mahaukaci ne.


A rufe falon yake, suna ciki su biyun Maryama da Jiddah suna hira, Jiddah na daɗa ƙarfafa mata guiwa a kan rayuwar aurenta. Tana mata nasiha cikin hikima kan yadda za ta zauna da mijinta, duk da kasantuwarsa mara hankali. A ƙarshe ta ce mata,


"Maryam ahir ɗinki da fitar da sirrikan aurenki. Kin ga dai mafi kusanci a cikin ƙawayenki da ke ni ce ko?"


Maryama ta É—aga mata kai.


"To ko ni kar ki taɓa yin kuskuren faɗa min rayuwarki ta aure. Shi sirri sirri ne. Wannan al'amarin a tsakaninki da mai gidanki ne kawai. Duk wata ƙawa da za ta buƙaci sanin wani abu game da auratayyarki, ki kwaɗa mata maganar da ba za ta sake gigin tambayarki ba."


"To insha Allahu zan kula sosai."


Kafin su sake cewa komai suka ji knocking. Hakan ya tabbatar musu da cewa Annur ne aka kawo, tunda dama kawu Imrana tun É—azu ya kira Maryama, cewa da kanshi zai kawo ango.


Da sauri Jiddah ta yafa mayafinta sannan ta isa falo ta buɗe ƙofar. Murmushi ta saki tana mai buɗe musu hanya su wuce. Sosai ta yi mamakin yadda Annur ɗin ya ɗau wanka, ya sha kyau sosai. Har ƙasa ta gaishe su, kafin Kawu Imrana ya ce da ita ta shiga ta kira Maryamar.


Tare suka fito, fuskar Maryama lulluɓe da tafkeken gyale, Jiddah ta daho ta har suka ƙariso falon. Daga ƙasan Kawu Imrana suka zauna su biyun, tare da miyar da hankulansu ga iyayen nasu.


Uncle Marwan ne ya fara da faÉ—in,


"Zan fara da godiya ga Allah maɗaukakin sarki, da Ya nuna mana wannan gagarumar rana, mai albarka a gare mu baki ɗaya. Haƙiƙanin gaskiya ba ni da bakin da zan iya yi miki magana Maryam. Domin kuwa kin gama mana komai, kin yi jihadi mai girma na zaɓen Annur a matsayin mijin aurenki na din-din-din. Allah Ya saka miki da alkhairi. Allah ya baku zaman lafiya ya kuma ba Annur ɗin lafiya."


Ya juya da faraa ya fuskanci kawu Imrana, ya ce,


"Alhaji Imrana na gode ƙwarai da wanann halacci ko in ce jihadi naku. Haƙiƙanin gaskiya samun dattijawan kirki kamar ku sai an tona. Kuka aurar da ƴarku mai cikakkiyar lafiya ga Annur da ya kasance ba mai hankali ba. Allah ne kawai zai iya saka muku. Na gode ƙwarai, Allah ya bar zumunci."


Murmushin dattako suke saki su duka ukun, kawu ya ce,


"Ai wannan tamkar yi wa kai ne. Fatar mu dai kawai Allah ya ba su zaman lafiya. Shi kuma wancan É—in Allah ya toni asirinsa. Insha Allahu Annur zai samu lafiya, da kansa zai koma gidansu gaban iyayensa."


Abba ya ce,


"Allah ya yarje mana."


Ya dubi Maryama da ta sunkuyar da kanta cikin gyale tana ta famar kuka ya ce,


"Maryam na san mun ba ki tarbiyyar kirki, tun yarintarki har kika girma. Ina so ki yi amfani da iliminki na addini da kuma na zamani, ki bi mijinki sau da ƙafa, ki masa biyayya, kar ki dubi cewa wai mai laruri ne, babu ruwan Allah wallahi. Matuƙar kika saɓa ma mijinki to tsaf za a rubuta miki zunubi. Duk da yake a haka, to Aljannarki a ƙarƙashin tafin ƙafarsa take. Ki kiyaye, ki ba shi dukkanin kulawa tamkar yadda za ki ba mai cikakkiyar lafiya. A ƙarshe, sai in ce na yafe miki duniya da lahira. Allah ya miki albarka ya ba ki zaman lafiya da mijinki. Kar a fallasa sirrin aure Maryam. A kiyaye."


Kuka take yi sosai, tana jin yadda ƙaunar mutanen ke daɗa shiga cikin zuciyarta. Har ma dai Abbanta, da duk zafin da ya ɗauka da ita ya sauke shi.


"To mu bari mu tashi mu tafi. Ƙawar amarya a nan za ki kwana ne?"


Cikin zolaya kawu Imrana ya yi wannan tambayar yana kallon Jiddah.


"A'a kawu. Yanzu ni ma nake son tafiya."


"Ah to madalla. Sai mu tafi tare ai mu sauke ki."


Dariyar yaƙe ta yi, tuna cewa Deedah ya ce zai zo ya kai ta gida da kanshi, har ma ya shiga ya gaishe da ƴan gidansu.


Kama Maryamar ta yi suka nufi É—aki. Uncle Marwan kuma ya kalli Annur da tun É—azu yake ta wasa da kafet É—in É—akin yana bin zanensa.


"Annur! Duk da na san cewa ba ka kasance mai lafiya ba, amma hakan ba zai hana ni yi maka nasiha a matsayina na maɗaurin aurenka ba. Ka kula sosai, don Allah ka yi haƙuri da matarka, duk wuya duk runtsi kar ka taɓa butulce mata, ka ga dai yadda ta sadaukar da rayuwarta a kanka, ba tun yanzu ba. Ka riƙi Maryam da amana, ka tsaya tsayin-daka wurin ba ta farin ciki, tun daga yanzu har zuwa sadda za ka dawo cikin hankalinka. Na tabbata hankalin Maryama ba za ta taɓa barin ka ka wulaƙanta ba."


Tamkar yana magana da gunki haka ya yi. Sai dai ci gaba da wasanshi kawai da ya yi, yana sakin murmushi. Amma fa bai É—ago ya kalle shi ba.


Fitowar Jiddah ya sa duk suka miƙe, a lokacin har text ta gaggauta yi ma Deedah, cewa Abbanshi ya ce da kansu za su miyar da ita gida.


"Ta shi ka bi ta ta kai ka É—aki."


Uncle Marwan ya faɗa, yana kallon Annur. Babu musu kuwa ya miƙe, ya bi bayan Jiddah da ta masa jagoranci har zuwa ɗakin.


Tana fitowa suka fice, dama Uncle Marwan ya kawo musu ɗaya daga cikin masu gadin gidanshi, tunda ya san cewa dole suna da buƙatar mai kula, kasantuwar ba wani tsayayyen namiji a gidan. Bayan sun fita mai gadi ya rufe gidan, yana ɗaga musu hannu.


***


*Kun ga unexpected post ko? Ko ni ban tsammaci za ku same shi ba gaskiya. Kuma ba laifi ya yi tsawo, har ma ya zarce ma tunanina. Idan kun ji daɗinsa, please and please pray for me; Allah ya biya min dukkanin buƙatuna na alkhairi, da sauran ƴan uwa musulmai.*


*Dan-dan-dan-dan-dan-dan!😀 Ga amarya Maryama ga kuma angonta Annur. Ko ya wannan rayuwar aure za ta kasance?*


*Mu je zuwa dai.*


*Ina daÉ—a gaishe ku masu mutunci. Ku ci gaba da aikinku, ladar ku na a hannuna, zan ba ku ita ta hanyar ci gaba da kawo muku zura-zuran pages...lol.*


Thanks all.


Pinky durling💞
RAZ 2
[9/18, 4:14 PM] Princess Amrah✍🏻💞: *🅰MRAH NAKE SO!♥*


_(Labari mai taba zuciya, soyayya, sadaukarwa da kuma ban tausayi)_




Sadaukarwa ga masu cutar amosanin jini (Sickler)


Na Amrah A Mashi
(Princess Amrah)
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*




6⃣6⃣


Wattpad: PrincessAmrah


***


Ji ta yi an dafa ta, hakan ya sa ta dakata daga kukan da take yi, ta ɗago kanta tana kallon yadda ya yaƙe bakinsa yana mata dariya. Tozalin da ya yi da rinannun idanuwanta da ke zubar da ƙwalla ya sa shi dakatawa da dariyar, tamkar bai taɓa yin murmushi ba.


"Me aka miki? Ko ni ne?"


Ƙirƙiro murmushi ta yi tana kallon shi cikin ido, ta ce,


"Ba kai ba ne Yah Noor, tsakuwa ce ta faÉ—a min a cikin idanuwan."


GyaÉ—a mata kai ya yi, sannan ya ce,


"Ki yi haƙuri kin ji. Za ki warke insha Allahu."


Sassanyar murmushi ta saki, ta ce


"Allah ya yarje mana. Yanzu ka samu ka yi wanka, ga kayanka can a cikin wardrob da Mama ta aiko da su É—azu, sai ka sauya na jikinka."


Kallon ta kawai yake a tsayen da yake, bai san yadda zai yi ya yi wankan ba. Mallam Mai gadi ne ke masa dama ko a gida.


Kallon da yake mata ya sa ta gano manufarsa, cewa ba zai iya ba. Ta ce,


"Ba za ka iya yi ba? Well. Bari in ɗauko maka da koda jallabiya ce sai ka canza. Amma ai ba za ka kwana da wannan kayan ba, ba ma za ka taɓa jin daɗin barcin ba."


Ta miƙe tsaye. Tafkeken gyalen da ke jikinta ta ɗora a bakin gadon, ta gyara zaman rigarta, sannan ta isa bakin wardrobe ɗin. Wata jallabiya ce ta ɗauko masa kalar coffee brown. Bayan ta rufe wardrobe ɗin ta dawo kusa da shi, ta ajje kusa da inda ta ajje gyalenta, sannan ta ce masa,


"Ina zuwa."


Ta fice daga ɗakin, ta nufi nata. Cikin kayanta ta duba ta ɗauko wata rigar barci mai ɗan tsawo, za ta wuce guiwa. Sauya na jikinta ta yi da rigar barcin, sannan ta sako hula mara nauyi, ta zumbulo hijabi har ƙasa ta dawo inda yake.


Kamar wasa ta tarar har ya cire na jikinsa ya saka jallabiyar, ya yi tsaye ƙerere gaban madubi yana kallon kanshi. Mamaki ta yi sosai, sai kuma ta saki murmushi, ta ƙarisa gabanshi tana faɗin,


"Inye, angon ba. Har ka canza kenan. Ka ga yadda ka yi kyau kuwa? Yanzu ka san me ya rage?"


Ya gyaÉ—a mata kai yana murmushi.


"Wannan."


Ta zira hannunta a gaban madubin, ta É—auko turaren oud al'abyad. Feffesa masa ta yi sannan ta fesa ma kanta, ta miyar ta ajje tana fuskantarsa.


"Mu kwanta ko?"


"A ina?"


Ya ce da ita a hankali yana kallon ta.


"A can mana."


Ta gwada masa gado, haÉ—e da yi masa hararar wasa.


Isa ya yi bakin gadon, ya kwanta tare da takure kansa, sannan ita ma ta isa ta kwanta daga gefensa. Wani irin yanayi take ji sosai, mai cike da shauƙi da farin ciki. Sai a yanzu ne take daɗa tabbatarwa, cewa da gaske an ɗaura mata aure da Annur. Sakin murmushi ta yi a hankali ta zira hannunta bisa cikinsa, ta tallabo shi a jikinta. Wani irin yar! Ta ji a jikinta, hakan bai sa ta sake shi ba, sai ma ƙara rungume shi da ta yi tsam-tsam, tana jin yadda nutsuwa ke sauka a duniyarta. A haka barci yai awon gaba da su duka biyun, barci mai cike da mafarkai kala-kala, duka masu tsantsar daɗi da nishaɗi. Asubah da gari Marnoor.


*


Idanuwanshi tsaye suke ƙyam bisa ƴar madaidaiciyar wuƙar da ta yi aƙalla mintuna goma sha biyar a hannunsa. Hawaye yake saki, mai cike da ƙunar zuciya da tashin hankali.


"Rayuwa ta juye min baki ɗaya. Na rasa duk wani farin ciki da jin daɗina. Walwala ta ƙaurace min. Mutuwa ce daidai ni a wannan lokacin, ita ya kamata a ce ta zo ta tafi da ni, sai dai kuma har yanzu ta ƙi zuwa, don haka dole ni na jawo ta da hanzari, ta zo inda nake."


Ya saki kuka da ƙarfi, ba tare da ya ɗauke idanuwansa daga kan wuƙar ba. Kuka yake sosai har da shessheƙa, yana jin yadda zuciyarsa ke tafarfasa, take karanto masa cewa kashe kanshi ne kawai zai zame masa alkhairi, shi ne kawai zai saka ya samu sassauci. Duk wani ɓangare na zuciyarsa da zai ƙoƙarta kwaɓarsa tare da kawo masa haramcin mutum ya kashe kanshi, sai ya kwaɓe shi, inda ke ƙara tunzurasan kawai yake biye mawa.


Da ƙarfi ya ɗaga wuƙar haɗe da caka ma cikinsa ita, ya saki wani irin razanannen ihu, tare da zubewa ƙasa. Sosai jini ke malala daga cikinsa, idanuwansa a rufe.


Ihun Sans baki ɗaya sai da ya karwaɗe farfajiyar gidan, har ta ɓangaren da mai gadi yake. Sai dai kuma tazarar da ke akwai daga farfajiyar zuwa cikin gidan akwai ɗan tsayi, hakan ya sa mutanen cikin gidan ba za su ji ƙarar ba.


Mallam Ya'ulle mai gadi ya ce da Habu mai wankin mota,


"Kamar daga ɓangaren Annur fa wanann ihun ya fito."


Habu cikin kiÉ—ima ya ce,


"Ko tantama babu daga can ne. Da alama ba lafiya."


Suka miƙe su duka biyun, suka tinkari ɗakin Sans. A halin da suka gan shi ne suka daɗa gigita. Yadda jini yake kwance male-male a wurin, ga kuma Sans da ko alamar numfashi babu a tattare da shi.


"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un! Habu maza-maza ka kira Yallaɓai da Hajiya, Allah dai ya sa yana raye."


Cikin kuka sosai mallam Ya'ulle ke wannan maganar, yana kai kanshi saitin ƙirjin Sans, ko zai ji fitar numfashi.


A guje Habu ya isa falon, ya samu Momy ce zaune, sai su Hanan da Janan da suka zo hutu yau. Dalilin ma da ya sa su Momy É—in ba su koma gidan su Maryama wurin biki ba kenan a ranar.


A yadda Momy ta ga Habu ne ya tabbatar mata da ba lafiya ba. Miƙewa ta yi cikin kiɗima, ta ce,


"Habu me ya faru...?"


Bai ko jira ta dire tambayar tata ba, ya ce,


"Hajiya babu lafiya. Annur ga shi can kwance cikin jini, kamar ma ba ya numfashi ko kaÉ—an."


Ido buÉ—e momy ta dafe kanta, da sauri da sauri ta ji gabanta na faÉ—uwa. Ta ce,


"Habu me kake faÉ—a ne haka?"


"Hajiya ba wannan ba ne ya kamata ki yi, sai an gaggauta kai shi asibiti, domin a ba shi taimakon gaggawa, idan ma yana raye kenan."


Shi kanshi kuka yake sosai, su Hanan ma hankalinsu ya tashi, Janan ta nufi É—akin Dady ta sanar masa. A kiÉ—ime Dady ya fito shi ma, ko riga babu a jikinsa sai singlet, yana faÉ—in


"Ku ba ni mukullin mota."


A hakan ya fice zuwa É—akin Sans, ya tarar mai gadi sai famar kuka yake, ya kasa zaune ya kasa tsaye.


"Ya Salaam! Annur me ya faru haka? What's wrong with you? Cakar ka ta yi wuƙar? Sai dai haka kam. Mallam Ya'u ku taimaka ku kamo min shi a kai mota, insha Allahu Annur ba zai mutu ba, zai tashi da kafaɗunsa."


Cicciɓarsa suka yi suka kai mota, a lokacin har su Momy da ke ta ruzgar kuka sun isa bakin Prado ɗin. Bayan an saka shi suka shisshiga ciki, kai tsaye suka nufi Nadda Hospital.


*


Sai shida da rabi ya samu damar tashi, kasantuwar hidimar biki akwai gajiya sosai. Da ƙyar ta iya buɗe idanuwanta, ta sauko daga bisa gadon a hankali, sannan ta nufi toilet. Alwalla ta ɗauro sannan ta fito tana tsane ruwan hannunta a jikin rigar barcinta ta silk.


Hijabinta ta ɗauko ta saka sannan ta tada sallar, a lokacin har gari ya fara yin haske-haske. Bayan ta sallame ta yi addu'o'i sosai, sannan ta fara niyyar tashin Annur. Har ta ɗaga hannunta za ta ɗan bubbuga shi, sai kuma ta tuno cewa, psychologically ba a son tayar da mai mental illness daga barci. Sosai hakan ke ƙara rikita ƙwalwarsa, saboda an dakatar da wani jin daɗinsa. Fasawa ta yi, ta jawo blanket ta rufe shi, saboda sanyi-sanyin da ake yi, kasantuwar an kwana ana shara ruwan sama.


Komawa ta yi ta kishingiɗa bisa tafkeken kafet ɗin da ke baje daga gefen gadon, sannan ta zaro wayarta da ke jikin caji. Text take son ta tura ma iyayenta na godiya, da kuma sauran mutanen arziƙi da ƙawayenta na ban-gajiya. Iyayen nata ta fara tsara ma text mai matuƙar ma'ana, ta musu godiya na hidima da ita da suka yi tun haihuwarta har izuwa girmanta. Sun ciyar da ita, shayar da ita, suturtar da ita, sannan kuma suka ilimantar da ita ba tare da gajiyawa ba. Sun ba ta duk wani farin ciki da ya kamata iyaye su ba ma yaransu, har ma sun zarce. Sun ba ta tarbiyya mai kyau, wacce ta zam abar alfahari ga kowa, ake son koyi da duk halayenta. Sannan a ƙarshe suka ba ta farin cikinta, ta hanyar aura mata mutumin da take da muradin taimaka masa, da kuma tsantsar ƙaunarsa.


Tana gama rubuta text din ta sharr hawayen da suka sauko mata. Ta ɗan yi jim! Ba tare da ta sake kallon wayar ba, saboda jikinta da ya yi sanyi, iyayenta da kuma Hammad ƙaninta, kuma abokinta ta tuna, cewa ta rabu da su kenan fa sai dai idan ta je ganin gida.


Ta daɗe a haka kafin ta wartsake, ta musu sending message ɗin a tare. Kawu Imrana ta fara rubuta ma nashi, na tsayuwar da ya yi ga rayuwarsu, tun ma kafin su zo duniya. Sannan a ƙarshe ya goyi bayanta ɗari bisa ɗari, ta hanyar tsayuwa tsayin-daka ganin an aura mata farin cikinta. Ba ta da hanyar biyansa, addua ce kawai za ta masa. Ta nemi gafararsa a kan butulce ma zaɓinsa da ta yi, ya yi haƙuri ya gafarta mata.


Text guda ta rubuta na ban-gajiya, ta yi sharing ɗinsa ga duka contacts ɗinta. Datarta ta buɗe saboda ta jima ba ta hau charting ba. A hankali charts suka ringa shigo mata, wasu daga ciki na taya ta murna ne, mafi rinjaye dai groups ne da take, saƙuna da yawa saboda jimawar ta ba ta hau ba. Kamar wasa ta ga shigowar saƙon Dr. Hamdan, tamkar a mafarki haka ta shiga cikin saƙon nasa, ta hau karantawa.


Ce mata ya yi ya ji ta shiru, kuma ya kira ta tun ranar da suka yi magana amma ba ta ɗauka ba. Tun bayan da suka yi maganar nan bai san dalili ba ya ji abun ya masa tsaye a rai, ya ji tausayin mara lafiyan sosai. Idan har za ta samu lokaci, to ta daure ta kawo shi Maidugurin, ya mata alƙawarin duba lafiyarsa sosai. Idan kuma tana ga kamar abun da sauƙi sosai, to ta jira shi, akwai Seminer da zai je Kano nan da sati uku, in ya samu yadda yake so zai zo Katsinar wurin wani abokinsa. Idan kuma bai samu zuwa ba, to sai su same shi a Kano ɗin.


Sosai Maryama ta ji daɗin hakan, farin ciki ya kasa ɓoyuwa daga fuskarta, gani take kamar ma har Annur ɗinta ya warke ne. Saboda yadda Dr. Sandra ta rinƙa ƙawata Dr. Hamdan ta tabbatar cewa gwani ne.


Miyar masa da saƙon ta yi, cewa za ta jira shi ɗin har ya zo, tunda dai ta bi shawarwarin Dr. Sandra sosai, ta kuma ga ci gaban hakan.


Kashe datar ta yi bayan ta tabbatar saƙon ya je masa, sannan ta miƙe bisa ƙafafuwanta, tana jin yadda daɗi ke ziyartar zuciyarta. Kallon Annur ta yi a karo na biyu, ta saki murmushi, ganin yadda ya haƙiƙance barcinsa yake.


Falo ta nufa kai tsaye, ta hau dudduba yadda komai na falon ya tsaru, sai ta ji ya ƙara birge ta sosai. Daga nan ta wuce ɗayan bed room ɗin, wanda ya kasance nata, shi ma ta sake duddubawa, komai ya yi

Please Login or Register in order to submit comment