You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tasan da sharadi na ta zabi barin dakin ta don ta farauta ran yar uwarta na zumunci.
Zumuncin ma daga sama don ba zan matan da lokacin tafiya ku waje ba naje lagos kan mutumin nan ya taimaka min sabuwa da kanta ta hana shi ya taimaka sai barene can daban taba sani ba ya taimake mu.
Wai yau wa yan nan mutanen Jimmai ta jawo min cikin a hali har ta zabi farin cikin su da nats nan gaba me kake tunanen za,a yi a gidan nan idan ina lamuntan haka na faruwa tun yanzu.
Gaskiyane daddy na fahinci abinda kake ji kuma kake nufi a kan wanan magana zamu zauna da mama mu fahinci juna yana fadin haka ya mike sauran ma mikewa sukayi suna mara mai baya bayan sunyi sallama da mahaifin nasu.
Tuki yakeyi hankali a tashe gabaki dayan su cikin motan babu wanda ke iyayiwa wani magana sai faman sake sake suke a ransu.
Nauyayyan ajiyan zuciya Habbib ya sauke lokaci guda yana fadin yau danine a matsayin ka bros yarinyar nan ba zata kara kwana min a gida ba.
Don ba zan yarda kan auren wata mace na uwana ya mutu ba ga banza ni bansan abinda mama take nema a gurin wa yan nan mutanen marasa mutunci .
Don naji ana fadin ko wurin bukin wullakanci suka so yi mata a lokacin salma ne tare da wasu suka taka masu birki.
Duk maganan da yan uwan keyi a motar Umar baiyi magana ba har lokacin gaba dayan su sun fahinci baya cikin dadin rai a lokaci.
Gidan shi ya nufa inda suka samu mahaifiyar su saidai sunyi rashin sa,a tana da baki yan uwanta sun ziyarce ta a lokacin.
Suna jin muryan su da kalaman su har inda suka tsayar da motar su part din mu suka shiga kai tsaye har lokacin ba wanda yake iya yiwa wani magana.
Mama Asma,u dake ta wajen kofa tana wayane taga shigowan su gidan har shigan su part din akan idon ta haka ya bata daman sace jiki zuwa wurin su ba tare da yan uwan nata sun sanda haka ba.
Ta shiga wurin su suka gaisa ta danyiwa umar din murnan aure da yayi sai kuma ta kare da fadin saidai kuma wanan abin bai kawo kallo ba.
Ace sanadin wanan auren yaya tabar nata dakin da tai shekara da shekaru a cikin sa haka bai taba faruwa a tsakanin su da Alh ba sai akan wanan bakin auren haka.
Don mu auren baki yake a gurin mu don shine sanadin wanan abinda ya faru saidai yannen nawa basa son gaskiya don basu lurar da ita gaskiya sai kara dulmiyar da ita sukeyi.
Mama mun sani shine abinda ke kara daure muna kai ace da girman su mama wanan abin yake faru haka ko yaushe a tsakanin su.
Yanzu sun tsameni cikin al,amarin su zasuyi abu ban sani ba don fadin gaskiyana danake masu yasa ake abubuwa bada sanin nawa ba.
Ko wanan auren naka ban san dsshi ba sai ji nayi daga sama don ban dauka abune da zai yuyu ba a tsakan zurian mu dasu.
Sai gashi ashe har hurdi Alh yayi mata amma yaya ta rufe ido har ta yarda wanan abin ya faru tsakanin su haka.
Yau ma din ninaje gidan mahaifin naku dan in mata ban gajiyan buki sai hjy maryam ke dan tsegunta min abinda ke faruwa wanda banji dadin hakan ba.
Naso ganin Alh aka ce min bai tashi ba yana kwance har lokacin haka yasa na shiga neman inda yaya din take nazo.
Saidai banji dadin zaman ta a inda na sameta ba don tun yanzu an fara samun matsala don yarinyar bata son zaman yaya a nan din.
Gidan ubanta ne nan din da bata son hakan habbib ya fada rai bace cool down mana habbib, umar ya fada yana kada kafan shi cikin takaici.
Don shi kadai yasan yadda yakeji a lokacin wayan shi daya dauki kara ne ya tsaya dubawa cikin mamaki yayi received din wayan yana mamaki a ranshi na kiran danayi mai na bazata.
Haka yasa ya fara tunanen wata kila wani ba lafiya ko wani abin ya taso tasa nake neman shi a layin shi sai ya dauka yana fadin .
Zahra ya lafiya ko tambayan nasa ya bata min rai saidai na dake ina fadin lafiya kalau yaya mu kiraka ne kawai muji lafiyan ka gasu Abdul suna son jin muryan ka na fada a kunyace don Nafisa na gurin zaune tare damu ta kura min ido tana sauraren mu.
Ya dauki lokaci yana waya da yaran shi hankali kwance yayin da su mama Asmau suke dan tataunawa dasu Aliyu kan zancen da sukeyi da farko.
A karshe yace suba maman su waya duk a cikin harshen turanci yake magana dasu nice mai dan kokarin koyawa yaran harshen hausa don kada su taso basu iya ba.
Saiko zuwan fauziya yanzu ba karamin taimakona zuwan yarinyar yai min ba lokacin.
Na karbi wayan ina sauraren shi yace i miss you Zahra how far ya Abbati na amsa a sanyaye da muna lafiya ya Amaryan ka kuma ?
Dan murmushi yayi babu amsa yana tambayana baku dai da matsalan komai ko ko a turo maku kudi zaku sai wani abin ?
Babu abinda zamu saya yaya we are ok mun gode yace take care of your self and the children nace in sha Allahu yaya .
Kaima ka kula muna da kan ka yana fadan hakan mukai sallama na kashe wayana ina jin zuciyana ba dadi a lokacin.
Badon komai bane sai don tunanen shi can yana more rayuwan shi da wata mace can ta daban mu muna nan ya barmu a cikin maraicin shi.
Gashi ba lafiya nake dashi ba don ban gama helling a jikina da akai min aikin wurin cire baby har yanzu ban gama warwarewa ba sosai.
Da kyat suka samu zama da mahaifiyar su kan hujjan da mahaifin su ya kafa game da komawanta dakin ta.
A take hjy ta hau fada inda take shiga ba nan take fita ba karshe ma sai nuna masu tayi ai mamune ta jefo masu bakin asiri daga can har haka ya kasance a tsakanin su.
Kai amma dai mama idan wanan halin zaki ci gaba dayi gaskiya akwai matsala babba don kina daukanwa kanki nauyi ne.
Ina wanan maganan kin san shi tun kan ayi auren nan da kika matsa ayi din kin amince da hakan ke nan .
Yanzun kuma zaki dauko wani zancen daba shi ba mama ki dora kan matar da bata ma san anayin wanan abin ba a nan.
Wai kai habbib haihuwana kayine ko me da kake kokarin nuna min kuskurena a kowani lokaci na dauko zancena.
Mama kiyi hakkuri abinda kikeyi ne wani lokaci ke kanki kinsan ba daidai bane sai kuma ki yarda shedan ya rudeki a ciki.
Don Allah mama ki bar wanan yarinyar ta koma inda ta fito tunda dai itace duk ta jawo wanan matsalan a tsakanin ku da daddy .
Inyaso mu lalaba daddy ya hakkura ya mayar dake dakin ki don Allah wanan abin kunyan ya, , ,
Habbib kabar falon nan tun kan na sabawa rayuwan ka anya kuwa yaron nan baya shaye shaye zaman shi a turai tana magana idon ta yana kan babban nasu umar.
Dan murmushi yayi yana dagawa habbib hannu yace bai shan komai mama halin turai dai ya kwaso na fadan gaskiya ga ko waye idan bukatan hakan ya taso ayi.
Mama gaskiya yake fadi don a kan auren wata can ba zamu taba yarda ke naki auren ya samu tangarda ba muna kallo.
Nan ko ta hau fada tana fadin na gane yan uwanane baku kauna a tare dani don an riga da an zuga ku akansu.
Don haka ku barni da yan uwana komai zai faru ya faru ba matsalan ku bane.
Ta mike har takai kofa ta juyo tana fadin kai kuma babawo sai ka shirya shiga gurin amaryan ka don ban fahinci manufar ka ba na kin shiga gurin ta.
Nan dai shima aka haushi da fada da tashin hankali da kyat ya samu fada mata mama zanyi yadda kikace insha Allahu .
Tana fita daga falon ta nufi hanyar shiga part din tun daga nesa ta hango part din a saye har takai ta tura kofan taji shi a rufe.
Da mamaki ta dan tsaya tana buga kofan shiga part din har ta gaji ba wanda ya bude kofan mamakine ya cika mata zuciyan ta lokaci guda.
Ta rasa yadda zata fassara wanan abin ko dai yarinyar ta fita unguwane bata sani ba.
To waima wani unguwa kuma yarinyar da bata wani kwanaki da shigowa gida ba har zata fara fita haka unguwa.
Tana tsaye tana wasi wasi a kofan daidai lokacin aka bude kofan dayan part din gaba dayan sune suka fito a part din kamar yadda ta barsu a ciki su uku.
Da mamaki suke kallon mahaifiyar nasu wace take tsaye a rakube kofan part din samira din a cikin damuwa.
Lafiya mama Aliyu yayi saurin tambaya yana isa gurin da sauri wallahi na fito kawai na samu kofan a rufe yanzu
Daga inda umar yake yace kamar ya kofa a rufe mama ya takowa zuwa wurin da take tsaye da mamaki fal a fuskan shi.
Yana zuwa ya fara dukan kofan a cikin wani irin hasala can yaji ana kokarin bude kofan habbib kan lokacin har ya kai wurin motar shi don shi haushin hakan bai bari ya tsaya jin meke faruwa ba a wurin.
Wata yar bakar yarinya ce ta bude kofan a hasale tana fadin wai waye ke damun mu da dukan kofa hakane don Allah anty tana kwance fa.
Tana karasa budewa sukai arba da umar dake tsaye a hasale cikin wani kakausar murya yace ke waya baki umurnin rufe kofa haka gidan nan ?
Ta fara dan inda inda tana fadin dama dama anty ce tace in rufe bata son damuwa zata kwanta.
Anty waye anty a gidan nan kuma ya tambaya da mamaki karara a fuskanshi da sauri hjy tace samira take kira da anty ai.
Yace a hasale common bude kofan nan kada kiyi gigin kara rufe kofa a gidan nan da rana yana fadin haka ya juya rai bace da sauri ya bar gurin.
Aliyu dake tsaye ya kalli mahaifiyar tasu yana fadin mama shiga a cikin wani irin sanyin murya yake magana rai bace shima.
Sun kama hanya gaba dayan su an rasa wanda zaiyi magana daga cikin su sai Aliyu ne ya iya fadin amma wanan yarinyar bata da kunya mamane ta rufewa kofa ko me ?
Ita ta rufewa mana baka san halin zurian hjy sabuwa ba ko wanan ma ai kadan mama ta fara gani wurin su.
Ka daina fadan hakan Habbib kamar baka damu da halin da mahaifiyar mu ke ciki ba don Allah.
Mama a yanzu idan ka kula dabara na kokarin kubce mata ne don in ka kula duk abinda takeyi ba a cikin hayacinta takeyin sa ba umar ce yana sauke numfashi.
Kaike daukan hakan yasa suke kokarin gara ka aiko shi daddy ya dawo daga rakiyan halin su ne yanzu duk wanan damuwa ne ke damun ta don bata taba zaton daddy zai iya mata haka ba gaskiya.
Ya juya wurin Umar da kyau yana fadin yanzu kaine zaka kawo karshen wanan matsalan gaba daya nake gani.
Hannun shi daya kare fuskan shi dashi ya sauke yana kallon dan uwan tare da fadin as how zan kawo karshen abin ?
Kwarai kuwa ya kara fada yana jijiga kai kafin ya fara fadawa dan uwan nasa maganan abinda yake gani shine mafita kan mahaifiyar tasu dasu nan gaba.
Gaba dayan su shiru sukayi kowa na nazarin zancen a ranshi can Aliyy yace kana ganin mama zata yarda da wanan hukuncin kada kuma wani abu ya biyo baya a karshe.

Nafisa dake zaune ta kurawa tv dake aiki ido tun zaman ta a wurin take faman tunane a ranta.
Gaskiya ita yanzu gida take muradin zuwa wanan zaman kadaicin haka ya ishe ta ace mutum ko rana baya gani balle dan adam kana cikin gida a kulle jiddadun alaina baka ganin komai a garin.
Tana mamaki na yadda bata ga mun damu da fita ba dagani har maria dake wuni a tsaye tana muna aiki a gida.
Na fito daga daki ina daye da wani bakin wando da ya dan zarta wuyan kafana kadan sai dai bai sauka min ba kasa.
Sai rigan daya dan sauko min har kysan gwiwa mai umberal sai dai ta kare min kallon yanayin shigana take fadin.
Wai ke fatima haka kuke zama wanan garin zugu zugun ba fita ba komai kullun mutum a gida.
Har mama wai tana ganin wani daula da jin dadi kuke ciki nan ashe abin ba haka yake ba ma ashe .
Yawo kike son fita tace min tun zuwa na garin nan baki fita ya kai sau biyu ba gaskiya idsn mutum ba yazo yaga yadda kuke rayuwa ba dole idan ya ganki yayi zaton duk komai na yaya yana hannun ki ai...


ZAINAB IDRIS MAKAWA
17/11/2021, 07:20 - 🤐🤐🤐: Sauraren maganan nafisa nakeyi kamar a mafalki don azaton su ashe a cikin daula nake sai abinda naga dama nake a gidan dan uwan su.
Ke nan wanan zuwan ya fara wankeni daga zargin da suke min ke nan a baya ni dai nasan su matane dole gidan wani zasu su zauna kamar yadda nake zaune a gidan dan uwan su.
Tabbas ko wace mace sai tayi irin wanan rayuwan da yan uwan miji wata rana dan dama ma ni nawa dangin mijin yan uwanane amma basu raga min ba a cikin zaman mu don wani dalili nasu can da suka ratayawa zaman namu.
Hakane kuma suma nasan ko wace zata fuskaci irin nata kalubalin daga yan uwan mazajen su kamar yadda suke min suma.
Don hakane na nake hakkuri da komai ina danne abinda duk Nafisa take min na takalan bakina don kawai ta samu madogara ga kudirin ta gareni.
Kallon ta nayi bayan gama tunanena ina fadin Nafisa ke nan ai kin san dama idan mace tana zaune kalau da mijin ta hakan mutane kanyi zato gare ta.
Sai su dauka tana zaune tana juya mijin ne ita son ranta sai abinda taga dama takeyin shi a gidan basu dauka hakkuti da jarircewan wasu matan ne yake kaisu ga hakan.
Nafisa idan kinyi wa zaman mu da yaya adalci ni ko shi har yau ba wanda ya taba korafin wani a gidan mu da sunan rashin jin dadin zamantakewa da dan uwan shi.
Nafisa ke kin sani ba wai bamu samun sabani bane a tsakanin mu kwarai muna samu saidai hakkurin da Allah ba kowane a cikin mu ya hana har mu bada kafa a fahinci hakan.
Ke dai yanzu ganauce kinzo kinga rayuwan da muke a gidan nan daga ni har yaran mu ba wai wani abin duniya da kuke tunane bane yaya yake sakar muna, muna yadda mukaga dama a gidan nan .
Rayuwa muke na sese wa sese da zama rufawa junan mu a siri yadda ya dace duk wata macen kwarai ake bukatan samu hakan a wurin ta.
Yanzu kinga ke nan zaki koma gida da hujjan kan abunda idon ki ya gane maki a zaman mu gidan nan .
Wanda kuke ganin kamar wani daulan duniya nake cikin shi zaune a nan tace da sauri wa kike tunanen zan fadawa hakan ?
Bawai ina nufin ki fada kai tsaye bane ai Nafisa kawai na tabbatar da idan magana makamancin haka ya taso a kan mu kina wurin zaki bada shedan abinda kika gani wa idon ki ai.
Sai lokacin naga ta danyi murmushi kadan a fuskanta tana fadin kwarai kuwa don ni din dai ganauce don ban zaci hakan ba gaskiya a zaman ku.
Duk da dai ba a gane tsakanin miji da mata sai Allah amma dai duk da hakan na fahinci dan wani abin yanzu kan zamantakewa na aure wanda a baya ba haka na dauki abin bani.
Mun kai wani lokaci muna jefawa juna magana a dunkule da sunan hiran salma wanda kowan mu ya gane nufin dan uwa.
Rashin dawowan yaya har sati hudu yasa na fara shirya yadda zan fara karatuna don dama mun gama magana dashi haihuwana ne ya tsayar dani kan hakan amma na dade da applying anyi komai.
Nafisa kan iya gajiya ta gaji da zama wuri daya don bata saba da hakan ba ita ni har mamaki take bani don idon ta yanzu ya matukar budewa kamar ba yar gidan kawu bace ita.

Muryan hjy sabuwa ce ya tayar dasu ranan daga barci don kamar a hanya tayi sallah asubahi a yadda tayi sakkon zuwa gidan cikin rashin mutunci.
Bada kowa take wana jidalin ba saida hjyn su yaya tana fadin yo jummai ai bansan makira kike ba sai yanzu.
Haka kawai kin wanko kafa kin dawo gidan yara cikin ki kin zauna don kawai ki batawa Samira jin dadin auren ta.
Ashe kin yarda an hada wanan auren ne don ki yaudaremu ki samu daman da zaki dawo gidan danki ki zauna ki kasa ki tsare don sheri.
Budan kofan da akayi yasa ta tsaya ta dan dakata da maganan ta don ganin wanda ke fitowa a part din lokacin.
Hjy jummai ce ta bude kofan tana kallon hjy sabuwa da mamaki hakan bai hana hjy sabuwa fasa fada abinda take fadi ba a lokacin.
Tana fada ta nufi cikin part din a hasale tare da fadin tabbas kuwa na sheda don ga zahiri nagani yau hjy jummai kinsan kunya kuwa ?
Ki rasa inda zaki tare sai a gidan yarinyar dake ganuwan amarci da mijin ta kinzo don rashin ta ido kin zauna masu a gida kin hanasu rawan hantsi a gida don kawai kina takama gidan danki ne nan.
Hjy sabuwa irin sakkaiyan da zaki mun ke nan bayan duk abinda ya faru sanin kanki ne a dalilin auren yarki ya faru dani.
Ni zakizo ki watsawa kasa haka ga ido tunda farar safiyan nan haka a gidan nan .
Naki dai ki daina cewa sanadin samira hakan ya faru dake don Allah kada makiya suji su canfa min yata ga banza.
Yo koma hakan ne yanzu ke daidaine ki dawo nan ki tare masu nan ne kawai gurin zama a cikin gidan nan kome ?
Wallahi jummai kinban kunya don ban zaci hakan da wuri a gareki ba koma me kika shirya ai kya bada lokaci ko ?
Hjy da imani da mamaki ya cika lokacin kasa magana tayi don jin abin take kamar a almara wai duk gwagwalmayan da take sha duk akan auren yar sabuwa irin sakaiyan da zatayi mata ke nan da farar safiyan nan.
Samira da bata son auren ta ya balgace ne takewa uwar nata magana kamar a fada haba umma yakamata abi abin nan a tsanake bada tashin hankali haka ba.
Ta juya wurin yar tana fadin barni in fada mata gaskiya idan bakanta ya kamatane ?
Mama wai me ke faruwa hakane a gidan nan muryan wa nakeji cikin rashin kamun kai zai shigo muna gida da safen nan da masifa haka ?
Wanan wata irin bakuwace haka mai kaifin harshe mara tunanen gidan mutane tazo da safen nan take wanan nuna tarbiyan haka gareki.
Aliyu ne da sauran yan uwanshi da dawowan su ke nan daga masallaci basu dade da shiga ba suke jin muryan hjy sabuwa komai da take fada a kunnen sune.
Allah ya nufa za,ayi wanan abun a gaban su yayan su yace su kwana a nan don da safe zasuyi sammako zuwa gurin wani dan uwan su daddy su a kauye.
Gaba dayan su juyowa sukayi a inda suke jin maganan suna kallon su da mamaki.
Dan kame kame hjy sabuwa ta farayi don batayi tsamanin gaba dayan su har shi umar din yana gidan ba a lokacin.
Au kuna ciki ashe tace ba wanda ya amsats sai shi umar din ne cikin sanyin murya yake fadin mama meya faru ne haka wai da safen nan ?
Wanan matar tazo muna da jidali gida babawo sarakuwan kace fa mahaifiyar samira amaryan ka .
Wani kallo yaiwa hjy sabuwan don harga Allah matar ta sake mai ga baki daya don ba haka yasanta ba a baya gaba daya yaga ta sauyamai ga gani.
Wani kallo yai mata bai iya magana ba ya juya zai bar dakin ba tare da yace da ita uffan ba sai jin muryan ta kowa dake falon yayi tana fadin .
Babawo ko ban baka mata ba a matsayin uwarka nake balle na wanke diya na baka do dole alakan mu dakai ya karu a yanzu.
Ta fada a gadarance tana kallon shi kamar mai bashi umurni tace ban san matsayin daka dauki yata ba a wurin ka don har yanzu kwanan ka nawa a garin nan tana cikin gidan ka tace ko gaisuwan ka bata samu.
Ban san dalilin hakan ba tunda ba mutum mutumi na kawo maka ajiya ba a gida mace ce lafiyaya na dauka na baka aure.
Tunda ta baci sunan shi yaja ya tsaya wuri daya yana sauraren maganan da take fada mai ba tare daya juyo inda take ba har zuwa lokacin data tsayar da maganan ta.
Sai lokavin ya juyo gareta jin ta tsaya da maganan da take koro mashi ya dan murmusa kafin yace hjy zanso ki gyara kalaman ki kan komai nan gaba ko abin zai zo maku da sauki.
Yar ki bata fadi karya ba don har yanzu ban san tana gidan nan ba don bamu je an muna gwaji ba a tsakanun mu a tantance lafiyan ta.
Me kake nufi da fadan hakan gwaji gwajin me kake nufi zakuyi tuhumar yar nawa kake dawani cuta ko me kuma ?
Eh a ka,idana sai anyi wanan gwaje gwajen an tattance tsakanin mu kafin in tabatar da komai a gare ta.
Uwarka jummai gatanan za, a gwada ka kalli tsaban tsakiyan idona babu kunya kake furta min wanan maganan gwajin ko me ?
Nasaran da kake koyi dasu sunci abu kazan kazan su wa zaka kawowa wanan bakin akidar naku

Please Login or Register in order to submit comment