You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

iya zama babba a gidan nan.
Yana fadin haka ya juya yabar wurin sauran ma basu dade ba suka shigevwurin mahaifiyar su photon da aka fasa dauka ke nan dasu.
Ina shiga dakin Amma tana zaune an kewayeta da kwanonin abinci a gaban ta tana fisgan nama a bakin ta mukai sallama muka shigo.
Tana hadewa take kokarin magana ashe kafa yayi sauki har kin samu fitowa yau nace ina zama dana sani da ban fito a yanzu ba ai.
A jaka fada idan kayi magana ace baka da gaskiya da ke da waye yanzu kuma ta tambaya tana maida dubanta gare ni.
Ban bata amsa ba sai kokarin hayewa kujeran da nakeyi don in mike kafana dana dan tako yake min zugi a lokacin tunda ba wani fita nakeyi ba sosai.
Kafin muci gaba da magana sai ga Aisha ta shigo tana fadin kai mutumiyar wanan shiga haka kamar wata balaraba dake wallahi bakiga yadda kika tafi da imanin mu ba a gurin lalai hajiyan ki tana ji da budurwan nan nata.
Ido naga Amma ta kyat min sai kawai nayi dan murmushi na gane may take nufi na basar da maganan da Aisha take min ta zauna a kusa dani tana fadin .
Amma dai ba a kasan nan aka sai maki wanan rigan ba wallahi duk kin fimu mu haduwa baki ga yadda sallama ta tsuke fuska ba da tana muna sallo a cikin nata sai gashi sun ga naki ya cunawa nasu din.
Ranan hira mukayi da Amma da Aisha sosai do ban fito ba saboda nauyin da kafan ke mun yasa na dade a zaune a gurin.
Da yamma lis na fito don komawa part din mu a daidai lokacin Ahmed ke fitowa daga wurin Alh da yazo gaida shi da sallah.
A yadda na hango kofan falon da takalman maza da yawa ya nuna cewa Alh yana da baki a lokacin.
Tun daga nisa Ahmed dake kokarin saka takalma yake min murmushi abinda bai taba yi mun ba sakin fuska.
Haka yasa nima na mayar mai da martanin murmushi a fuskana na tunkari inda yake ina fadin Ya Ahmed barka da sallah.
Yana kallona a wani yana da ban iya fassarashi yace yau kanwatace haka a cikin kwaliya kamar wata yar sarkin larabawa ?
Wai ya Ahmed kayan sunyi min kyau ne kowa sai yabon kwalliyata yakeyi yau dama ai kaida mamu kuke hanani kwalliyan ai dama na iya abina tun a gida.
Yanzu dai barin nuna maki kyaun da kikayi gyara in dauke ku photo dake da fauziya ku gani nan yayi ta daukan mu photo muna dariya.
Sai ganin mutane na fitowa fallon wanda yaran gidan ne su uku sai wasu biyu da van sani ba a bayan su naji daga cikin bakin na fadin .
A a Ahmed ashe baka tafi ba ya dan yi dariya so guilty yana fadin wallahi wanan kanwar tawa ne ta tsayar dani da shiririn tan ta.
Nan ya tafi ya barmu da wayan shi muna kallo a cikin sa sai da muka gama naba fauziya ta kaimai inda nake hangen su.
Kwana biyun ranakun sallah mun sha gasan kwalliya a gidan wanda akeyi kamar ko wani gida da ke da yan mata duk da ban kai su shekaru ba ina tsone masu ido.
Har na bar fita ranan na uku ga sallah da safe sai ga mamu a dakina ta tsaya daga kofa tana fadin ki shirya idan mun gama girki muje wurin babba asibiti yau.
Wani irin tsale nayi ina murna da sauri nabi bayan ta ina tambayan ta may za a girka don in dora da wuri mu gama.
Tace tuwo don kin san shi tafi so don yanzu tana cin abinci har da yunwa yaso yai mata illa saboda rashin kulan da bata samu sosai a can.
Haka na zage nayi aiki mamu tana duba min har na gama muka shirya gaba dayan mu zuwa asibitin .
Mun fito ne daidai lokacin da baki ke zuwa gidan na sheda su kannen kawu ne su kawu bala da kawu suleiman muka tsaya muna gaisawa dasu a wurin .
An dan taba yar magana tsakanin su da mamu wanda ni ina bakin motar ta banji abinda suke magana akai ba tazo ta shiga muka tafi.
Ashe mun bar baya da kura a gidan don Amma ce ta aika suzo gaba dayan su tana son ganin su wanda dama suna da niyar zuwa sai dai ba a lokaci daya sukan zo ba don haka ta nemay su a wanan lokacin.
Duk da kiran bai daga masu hankali ba don takan nemay a haka idan wani magana mai muhinmanci ya taso gare ta daya shafi kowan su .
Sai da suka shiga wurin dan uwan su suka taba hira dashi suka fito zuwa jin kiran da tsohuwar ke masu a lokacin.
Su shiga sun samay ta zaune da diyan ta mata su biyu a lokacin suna dan maganan su ba mata shigowan su aka fara gaisuwa a tsakanin su.
Bayan gaisuwa da yar hiran lokaci kawu bala ya fara magana akan neman da mahaifiyar tasu take mashi a lokacin.
Sai kowan su ya natsu yana sauraren dalilin kiran a cikin ladabi gaba dayan su suna kasa zaune har matan sun sauka ka kujeran sun zube a kasa kamar yadda yayyu su sukayi.
Dan kallon gefen Alh sani tayi tana fadin zanso kafin in fara magana a kira min matan ka gaba dayan su do suma maganar ta shafe su.
Alh sani yaji wani iri don yana zaton irin iya shegen da iyalin ke yawan yi ne a lokacin wani abu ya shafi tsohuwar har zatai magana.
Don Amma bata da yawan magana kan sarakanta ga duk wani abinda suke mata tana kokarin kawar da kai don kada suga takurawan ta gare su.
Kawu sulaiman yace maimuna ko bata gidan nan don muna shigowa naga fitan ta tace asibiti zasu gaida kakar yarta da aka kwantar tun kan ayi sallah ko ?
A kira min ita ta dawo don wanan maganan ya shafi kowa na ahalin nan shiya saka na kiraku yanzun ma.
Wayan shi ya ciro daga cikin Aljihun shi ya fara neman layin mamu din a daidai lokacin da muna zaune na makale manjo muna yaushe rabo da ita.
Sai ga kiran mijin ta ya shigo mata yana fadin ta dawo gida yanzu hajiya tana neman ta da gagawa haka kuma bayan ya gama waya da mamu ya kira sauran matan nashi a waya.
Mamu bata kara lokaci ba ta mike tana fadin mu je gida tana ganin wanj abi ne ya taso a fida don Alh ya kirata cewa gwago tana neman ta.
Ta juya gurin da nake tana fadin ko kinyi wani abin ne da wani ban sani ba da sauri nace ni ko part din Amma ban shiga ba yau.
Haka muka fito ba don naso ba muna nufi hanyar gida tayiwa manjo alkawarin dawowa dani wani lokacin i wuni a gurin ta.
Ko da ta dawo har Alh yayi mata kira biyu da cewa ita fa ake jira tana fadin gata gida a na karshen kiran.
Bahan ta shigo ta gaida su ta samu wuri ta zauna kamar yadda kowa yake zaune a falon kafin Amma ta fara magana tace.
Dalilin kiran ku anan ba wani abu bane sai dalili kamar biyu don haka na bukaci kowa yazo don zancen ya shafi kowan ku nan wanan dalilin yasa na kira harda matan ka kai yaro don haka take kiran shi kasancewar shi dan farko a gare ta.
Ta sake fadin kun san dalilin wanan kiran yanzu gaba dayan su falon suka amsa da a, a banda hajiya jummai dake cika tana batsewa ta dauka maganan ta za a yi da farko.
Tace zancen nasan wasun ku zasu jishi kamar almara kamar kuma tatsiniyar sai dai gaskiyar magana zan fada maku.
Sai da ta dan nisa kafin tace yaron nan Umar ne ya samay ni da wata maganan da ban taba kawo rai gare shi ba kwanakin baya.
Kafin ayi sallah na daure ne na hade maganan don ku sha ruwa lafiya zuciyar ku da sanyi ta kara da fadin sai dai ina son ko wanin ku bayan kunji ni ku yarda da kaddara kamar yadda nayi tunane a baya.
Jummai da tun ambatan Umar ta tsurawa hajiyan ido tana kallon ta da son jin may zata fada gamay da danta data tara su haka wuri daya koma mainene tasan magana ce mai tsauri.
Amma taci gaba da fadin ya samay ni wata rana yake fada min wai yana da aure a can har matan tana da ciki yanzun haka maganan nan da nake maku.
Ba hjy jummai da ke mahaifiyar shi ba gaba daya sun kadu a falin don ji abinda tsohuwar ke fadi tace ba iya zancen ke nan ba lokacin da taji kawu bala yana fadin shi umar din dai hajiya.
Tace aban haushi abin takaici da yaron nan ya dauko muna wai matar tashi arniyace don bata sallah kuma a haka yake son abinshi.


ZAINAB IDRIS MAKAWA
16/11/2021, 22:52 - 🤐🤐🤐: BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM ALLAHUMA INNI AS, ALUKAL HUDA WAL TUKA WAL FAFA WAL LUDAIINA, , , , , ,


Gaba dayan su ba mai iya furta komai sai innalillahi wa inna alahim raji, un bamunan su ke iya ambatawa.
Da kyat hjy jummai ta iya furta hajiya wanan maganan ina ya fito haka wani sabon sherin kuma ake son kulla wa diya don kawai anga sun dawo kasan nan lafiya cikin wadata.
Ke dakata don Allah a nan wa kike fanin zai kullah wa umar sheri a cikin mu ko hajiyar ce zata kulla mai wanan sai Amma tayi murmushi tace in banda abin jummai sunan kin haifi yaron nan saudaki ne kawai amma baki fini son shi da shakuwa da shi ba.
Ina nan zaune yaron nan ya samay ni fuskan shi da yanayin sa a cikin damuwa kwana biyu na shiga damuwa sosai sai daga baya yake labarta min damuwan shj dana damay shi da tambaya.
Farkon wljin wanan maganan vun yar kakabun nan na fara ji A ruwa take min wanka da jurwaye da zancen.
Da sauri mamu tace Sayadi kuma gwago ina ta jiyo wanan maganan itako babban magana irin haka ?
Allah masani ke dai yar nan anan ta samay ni cikin damuwan rashin walwalan shi kwana biyu kin san itace abokiyar firan nawa wani lokaci ina magana shine take fadin wai kai sai kuma ta kasa fadin abinda na fada mata ranan don ganin idanun da sukai mata yawa lokacin.
Ehh lalai wanan yarinyar takai shu,uma har sherin yakai gun yarana haka a hasale kawu bala yace ke jummai ki bari mu fuskanci matsalan da ya kunnu muna kai ki daina muna wanan shirmay.
Ko ta fada yanzu ai ba abin mamaki bane don kila a wani wurin ta samu labarin don yanzu maganan duniya ba boye yake ba mama Altine yayan mama hadiye ke fadin haka.
Yanzu naji inda wanan sherin ya tafito a gidan nan dama ko ba,a fada ba kowa yasan a rina har bakin cikin yakai haka ban sani ba.
Ke jummai na fada maki ki daina muna wanan shiman may ye na bakin ciki da diyan ki ina abinda yai yaran ki shiyayi yar nan da kike son zargawa magana.
May ye abin zargi a cikin maganan nan Bala sadauki da kansa yazo ya samay ni da zancen yana son in roka mashi gafaran ku.
Tun fara maganan Alh sani bai iya furta komai ba sai zufa yake yayin da kanshi yake duke zuviyar shi tana batun bugawa a lokacin.
Sai mama hadiye ta katse mai tunane da fadin yanzu may ake ciki da wanan zancen mai daure kai yaya.
Sai lokacin Alh sani ya dago kai yana fadin may ko ake ciki hadiye illar yaje ya nemi wasu iyayyen tunda ya nuna yana dasu cikin duniya .
Ni dai na zamay hannu ga duk wani alamari Faruq a gidan nan yaje ya nemi iyayyen shi can duniya ce fadi gare ta ke kuma jummai kin kai ga yadda kike so Allah ya isar min a gare ki yana fadin haka ya mike yana sharan hawayen dake barazanan zubo mashi a idanuwan shi.
Ba hajiya jummai duk wani wanda ke falon a lokacin ya tausayawa Alh sani da kuma firgita da kalamin Alh sani daya furtawa hjy jummai.
A hankali hawayen bakin ciki ya fara zo mata na nadama tana fadi a cikin kuka yanzu may ye nawa a cikin wanan zancen don Allah.
Yaron yanzu ne ka haife shi baka haifi halin shi baka shedan dan yau har kina kokarin dora laifi kan yar mutane sai Amma tace .
Balle zancen yar nan dutse ne don zaman su da arna take magana na kwabe ta ashe bamu tsira da zancen ba.
Yaya yanzu mainene abin yi don Alh ya tashi a cikin fushi bai tsaya an samo ma maganan mafita ba.
Tunda ya riga ya aikata har an kai ga rabo ai sai a san yadda za a gyaro maganan yanzu kuma mama Altine ke magana don su din yayyun mahaifiyatace yasa nake kiran su da mama sabanin yaran gidan da suke kiran su da gwago.
Ni banga wani abin bata lokaci ba ai gaskiyan Yaya din daya ce duniya da fadi yaje tunda dangin matar shi sun fi mai da zaiyi abu gaba gadi babu sanarwa.
Amma ta dan girgiza kai tace zanso muji ta bakin umar din don ya fada muna dalilin shi na yin haka ba tare da sanin mu ba saboda kada mu yanke mai hukunci a cikin duhu .
Yanzu sai mu bari har wani lokaci idan mun kara tataunawa akan zance sai mu sake zama sai maganar gaskiya wanan yaton bai kyauta muna ba wallahi.
Hjy Jummai kamar ruwa ya cita a gurin don zaune take tun bayan da zance ya tabbata gaskiya shi yazo da wanan maganan mai kama da tatsuniya a wurin su.
Da dadaya suke ficewa a falon kowa ranshi a bace da wanan zancen da yazo masu na bacin rai inda hjy jummai ta bi bayan su kawu Bala ta fice a cikin wani yanayi.
Duk ido matan dake falon suka bita dashi lokaci daya kowa yasan irin halin tashin hankalin da take ciki a lokacin don duk wata uwan da tasan zafin dan ta bata kaunan wanan abu ya faru dashi.
Bayan kamar yan dakiko mama Altine ta fara magana tana fadin irin abinda akewa gudu ke nan wallahi.
An sosa wa hjy maryam rai don zuciyar ta fari yake kal kan wanan zancen don tasan komai na iya faruwa tsakanin hjy jummai da maigidan su a yanzu.
Tace dama idan kace baka son ran yaro ya baci kai naka sai yafi dubu bace don yaya bata son afadi laifin yayan ta ko kadan.
Don haka ne ko kaga yaro yana abu a gidan nan kaidai iyakan ka ido yau ina alfaharin da ake muna yaranta sune gida su suka iya, , , ,
Haba anty maryam wanan magana bai dace ba don wanan abu ya shafi kowan mu a nan sannan duk mu nan iyayye ne idan daji bai gama cin wuta ba ba aiwa kukuture barka don babu bare a nan yanzu cikin mu.
Mama hadiye ta amsa da wanan haka yake gaskiya indai baka tausaya ba bakace kuma gwai ba ai ba.
Tace ba haka nake nufi ba kowa a nan yasan halin yaya akan rashin son a fadi gaskiya akan diyan ta shine nufi na.
Sun dauki lokaci ana magana a wurin kafin su watse kusan lokaci daya mamu da hjy maryam suka fito daga part din.
Hjy maryam bata daddara ba tace maimuna baki gane nufi na ba zakice baki jin zafin yawan gorin da alfaharin da ake muna gidan nan ne.
Don kawai mu an maishe banza a gidan nan damu da yaran mu ana daukan mu damu da babu duk daya ne a gidan nan.
Kai duniya amma wanan maganan naki baiyi ba wallahi Allah ya kyauta tana fadin haka ta shige ta barta tana hadiyan kili bibin dake cin ta lokacin don ita kan a wurin ta hakan yai mata dadi taga kurin zuwa turan yaran da ake mata ga tsaraba turai ta samu dan ta ya jajibo mata arniya a matsayin sarakuwa a gida da gari duka.

Hajiya Jummai a har gitse ta shiga shiyan ta dama kiris take jira ta fashe da kuka don ba karamin daurewa tayi ba na controling din hawayen kada su zubo a gaban makiyan ta.
Jin sheshekan kukanta yasa su salma saurin fito da sauri a rude suke suna tambayan abinda ke faruwa sai dai ba baki kuka kawai take rusawa zaune.
Wanan ya tayar da hankalin salma ta daga waya tana kiran yayyun ta tana fadi suzo gida babu lafiya hjy ce daga an kirata part din Amma ta dawo masu tana kuka cikin tashin hankali take maganan.
Umar din data kirashi tana fada mai yace shi yana lagos tun da safe baya gari a cikin zuciyar shi cewa yake am fasa kwan ke nan shike nan Amma ta fasa kwai a gidan.
A rude su Aliyu suka shigo gidan kowa ya gansu yasan hankalin su a tashe yake dan sun dauka wani rikici ne ya faru a gidan sun shiya cin mutunci yau ga ko waye don basu iya jure ganin mahaifiyar su a kullun cikin bacin rai hakana.
Mama may ke faruwa ne haka may ya faru dake kuma mama ta kasa basu amsa daidai lokacin sisters din ta suka iso suma.
Tambaya daya suke mata suma ta kasa basu amsa saida suka matsa mata da kyar ta iya bude baki tace yau ni Alh ke jawa Allah ya isa akan babawo.
Salati suka saka lokaci daya suna fadin may yai zafi haka kuma har yakai ga furta hakan gareki kuma ?
Wai ashe babawo yayi auren arniya a can ban sani har tana dauke da cikin shi yanzu haka yaron nan bai fada min ba asan mafita sai a bakin kakarshi nake ji.
Salati suka saka tare da fadin aure arniya kafira mara sallah kuma a can ko a nan ne ai ya jawo muna abin kunya gare mu.
Yanzu ina babawon yake ne dayan yar uwar nata ta tambaya Salma tace bros yana lagos tunda safe.
Ta juya tana fadin kinji ba nasan duk wanan abin ba a banza bane mahasda sunyi muna yawa a tattare damu.
Haba mama may ya kawo zancen hassada ga wanan zancen da ya shafi bros a can kawai yayi aure sai kuyi mai fatan alheri ciki ai yanzu bros shiba yaro bane zai iya yin abinda yake so.
Habbib ne da ya fara gajiya da irin halin mahaifiyar su yake fadin haka yace ni banga abinda zai sa ki wani tayar da hankalin ki haka ba sai dai in akan kalamin daddy ne ?
Shi daddy may zaisa ya furta hakan don kawai ke kika haifi bros ko may yana da incin da zai auri wace yake so yanzu ai.
Balle auren yau fa kusan shekara hudu kenan da yayi shi komai kuma bai faru ba gare shi so ni banga wani abin tayar da hankali ba a nan ?
Kallon shi sukayi suna fadin kun san da wanan zancen baku fadawa mahaifiyar ku ba amma ko kunyi kuskuren boye mata dai .
Mama may ye a ciki don yayi auren shi a can ba a can yake zaune bane zai zo nan yayi aure ne kuma idan matan nan basuyi mashi ba fa.
Sai lokacin tace ni ba abin bakin ciki gare ni duk da naji haushi wanan zancen amma wai yadda aka tara kowa ake fadin wanan maganan kamar kaina aka fara hakan gaban maryam da maimuna fa Alh ya kirani suke fada min.
Amma ai mashi auren gata a cikin dangi kamar kowa a mutunce ai zaifi yaya arniya kafira zata shigo cikin mu da sunan sarakuta ?.
16/11/2021, 22:55 - 🤐🤐🤐: BISSIMILLAHI RAHAMANI RAHIM YA HAIYU YA KAIYUMU BIN RAHAMATIKA YA ASTA GIS, , , , ,

Yinin ranan ya kasa bude wayogin shi tun lokaci da salma ta kirashi tana fada mai halin da mahaifiyar su take ciki yace bai gari ya kashe wayoyin nasa.
Can ya mike ya fito ya nufi mota ba inda zai tafi haka yasa ya nufi beach don ya sha iska a can tafiya yake a bakin beach din hannayen shi duka biyu a cikin aljihun wandan shi sai dan kafan wandon daya tankwashe su kada ruwa ya bata mai.
Kusan awa daya ya dauka a haka bai kaiga samo ma kanshi mafita ba a lokacin can yaja ya tsaya a guri daya yana fadin.
Imposible imposible yana girgiza kanshi a hankali, nan ya fara tunane baiga dalilin hana shi abinda ranshi ke so a yanzu ba saboda wani akida can da bai sabawa addinin shi ba.
Shidai yasan ba zai iya auren wata yar hausawa ba yanzu a yadda yake ganin su lulube ko yaushe a cikin hijjab gani abin rufe fuska da suke wani amfani dashi suna rufe fuska wanda bai san dalili su na yin hakan ba ?
Kai ya girgiza daya tuna harda wanan yar ficiciyar yar maimunan wai rufe fuska take wa mutane ko may take boyo oho ?
Sai kuma yaja guntun tsuki lokacin daya tuna yadda na fito babu wanan abin rufe fuskan gaba daya sun yi mamakin ganin irin surar da Allah yai min.
Ko shi yasa Alh ke ji dani a cikin yayan gidan kamar yadda mama ke yawan korafin yana mun tsuki ya kara ja yana fadin how comes maimuna ta samu ya haka kamar halfcase wai ?
Ita kanta maimuna inya tuna lokacin data tashi ai haka take da zuben kyau how he wish shima yasamu yara kyawawa haka a rayuwan shi kamar yadda diyan maimuna suke biyo ta da kyawo.
Maimuna maimuna ya furta maimuna you deceved all this care wurin Alh don ya tuna suna secondary maimu din tana da hali mai kyau wanda tun a lokacin maza ke rushing a kanta.
Mama why baki hakkuri don yarinyar nan tafiku da komai da maza ke so a wurin mace don idan ba don wanan alakan auren ta da mahaufin shi ba daya sa yanzu bai sakar mata fuska da can mutumiyar shi ce sosai a baya don kusan tashin su daya tare sukai karatu.
Idon shi ya dan kara runtsewa iskan teku na bugun shi tare da guguwan ruwan dake fesowa har

Please Login or Register in order to submit comment