You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yafi da nan ko mutuwa akace yayi aiba abin mamaki bane ga ubangiji yanzu suka ce hakane.
Amma ta juyo tana fadin a kira shi umarun yasan da zancen ciwon yar nan don kada muyi abu a cikin duhun kai tunda yanzu yana da hakkin sanin hakan .
Ba bata lokaci kawu ya sake ciro wayan shi ya kira umar din sai da wayan ya kusa tsukewa ya daga yana gaida mahaifin nasa tare da bashi hakkurin rashin zuwa kwana biyu.
Kawu yace ba matsala Allah ya tsare muna ku a duk inda kuke ya amsa da amin sai kawu yace dama na kirakane in sheda maka zancen ciwon yatinyar nan .
Da sauri Umar din yace wace yarinya ke nan daddy a cikin damuwa ya tambaya ?
Fatima yar gurin maimuna da zaka aura muna asibiti da ita tun dazun da safe aka kwantar da ita ba lafiya .
A cikin wani irin murya ya cewa kawu daddy Allah ya bata lafiya ina porthacourt yanzu zuwa safe zan dare zamu sauka insha Allahu.
Daga haka suka kashe wayan lokacin dakin yayi tsit kowa na sauraren abinda zai bada amsa a wayan.
Umar ko yana aje kiran daddy ya sauke ajiyan zuciya a hankali don hjyn su bata dade da kiranshi ba tana fada wai akan auren nan idan daddy su matsa sai anyi zasu iya samun matsala dashi.
Hakkuri ya ba mahaifiyar tasu yana fadin mama ki kwatar da hnkalin ki na fada maki nasan abinda nakeyi fa kwanan ma zamu koma America don haihuwan merry ya kusa insha Allahu mahaifan ta sun matsa mu dawo can.
Babawo yanzu da bakin ka kake fada min mahaifan matar ka sun matsa ma akan ku dawo can mai kake nufi da hakan a can kake nufi zata haihu ba nan ba ?
Ke nan mu nan bamu da wani darajan da matar ka zata haihu a gaban mu sai ka dauketa ka mayar can wata kasa.
Yaya kake son inyi da mutanen arzikina a nan auren ka ban samu yin wani shagali ba ga haihuwan kuma ka dauko wanan zancen ka aza to ban yarda da wanan shawaran ba.
Ya samu ya bata hakkuri tana bambami har katse layin abu goma da goma sun taru sun mashi yawa a kai ga mahaifin merry koda safe ya kirashi ya kara jaddada mashi akan ya kawo masa yarshi kada ya bari ta haihu a Nageria.
Ga kuma abinda mahaifiyar su ta fada yanzu ga kuma daddy da nasa matsalan ya kunnu kai hakan yasa ya dafe goshin shi bai karasa jin meeting din da sukeyi da abokan harkan shi na can.
Yana fitowa kai tsaye airport suka nufa don jirgin da zai taso zuwa Abuja na yamma zasu bi dama ya fito da shirin sa gaba daya.
Sai misalin bakwai saura ya iso kano gidan shi ya nufa kai tssye sallah ya tsaya waje yabi jam,i kamar yadda yake idan yana cikin unguwan.
Sai da aka fito ya shiga gida inda ya samu merry zaune ga kida na tashi tana dan ciye ciyen ta tana bin wakan wani iri yaji a ranshi ba dadi gaskiyan daddy da yake kyamatan merry a daidai lokacin daya dace bawa ya kusanta kanshi da ubangiji yakai kukan sa gare shi.
Ita a wanan lokacin ne take zaune tana bin rudin shedan yana kara zuga ta itako merry tana ganin shi taso yunkurawa ta tashi zuwa gare shi saidai nauyin da tayi ya hanata tashin.
Bai nufo inda take ba sai gurin speaker dake sake sautin ya kashe ya juyo zuwa gurin ta tare da dan dukawa ya rankwafo ya sunbace ta tare da fadin wanan kidan yayi yawa merry baki ganin is time for prayer's now.
I send my pray to god of heaven since morning wani addu,a kuma kake son inyi a wanan lokacin sai kuma idan zan kwanta idan na samu time sai inyi.
Kai ya girgiza yana fadin merry you have to fear god at dis situation you are yace weat Omar what d you mean with dis word ?
Don a zauna lafiya yace nothing ya fara balle maballen rigan sa yana kokarin shigewa dakin su da suke a kasa don saboda condition din merry hawa saman yana mata wuya yanzu.
Bin bayan shi tayi da kallon tare da fadin weat woo what dis man mean with me now ?
Shabi he want me to pray like him, d holl day no rest for humanbeing at all.
Yeeeeee sai ta ja tsuki tana ci gaba da gunguni a fili ita daya tare da kwalawa mai aikinta na kitchen kira.
Tazo da sauri da dan bujen ta tana fadin madam kina nemane tace eh ki kawowa maigidana abinci ya dawo.
Ta amsa da fafin yes ma ta juya zuwa kitchen din da sauri ta tana rawan jikin bin umurnin madam din gidan.
Ta dawo tana jera abincin sai gashi ya fito a cikin wasu kaya sai kamshin turare yakeyi yana gyara hannun rigan shi yace zan fita i will right back in thirty mins .
Tace how about your food is ready yana saman table kallon gurin yayi tare da aikawa mai aikin kallo yayi saurin kawar dakai gurin.
Ya fara tafiya take tambayan shi ina zaka haka ne kake sauri ?
Yace kai tsaye asibiti a dan firgice ta sake tambayan shi wirin wa yace yarinyar nan daughter din step mum take asibiti don shi baya karya kai tsaye yake maganan shi idan ya tashi.
Weat for me zan je in duba ta yarinyar da uwar ta suna da kirki gaskiya ba zan iya mantawa dasu a rayuwana ba.
Dole ya ja ya tsaya yana jiranta sun iso subitin a daidai lokacin su mamu sun dawo da kawu kawo min abinci na tashi suna rarashina inci abincin yayi sallama a kofan dakin bayan sunyi waya kawu ya gaya mai dakin da muke.
Da fara,a fuskan Amma tana fadin lale marhabin da maigidana babban giwa har an da, , , ,
Ganin merry tafe a bayan shi yasa ta gimtse maganan da ta kasa karasa a bakin ta tana kawar da kanta gare shi.
Yi yayi kamar bai gane may Amma ke nufi ba dayin hakan ya karkata gurinta yana kai mata ruguma ta dan duki bayan shi tana fadin kana son haka kazo da aanan jelar taka nan .
Ai da kazo kai daya dakaga runguma mamu dake duke tana gyara min kwanci don nace na gaji da kwanciya ta gefe daya.
Ta dago da sauri tana masu sannu da zuwa oh sister inlaw may ke faruwa ne haka tana nufowa gurin da nake kwance take wanan maganan.
Idanuna na lumshe a daidai lokacin data karaso inda nake ina jin wani irin ba dadi a raina koba komai merry na nuna min kulawan matsayi na kanwar mijin ta .
Ni yanzu da wani ido zan kali matar nan da wanan hadin da kawu ke son min da mijin ta wasa da dariyan da muka dinga yi a gidan su ranan da muka kai masu ziyara ne ya fado min.
Ban san lokacin da wasu hayeb tausayin kaina ne kona merry wani hali zata shiga idan taji za a hadani da mijin ta ?
Saukan hannun ta naji saman jikina tana dan tabawa tare da fadin eyyah sorry my dear ban sani ba sai yanzu da dear ya dawo yake fada min.
Ganin ina hawaye yasa merry kai hannun ta saman fuskana tana share min hawayen a hankali tare da min sannu da jiki.
Ta juya gurin mamu tana tambaya may ke damuna ne haka muma ta bata amsa da fever ne ya kama ban dade kwance ba ai.
A daidai lokacin ya juyo yana gaida kawu kafin ya juya wurin mamu yana fadin ina wuni ta amsa da kadawo lafiya.
Ya hanya ce Alhamdullahi ya mai jikin fa ashe bata jin dadi haka har asibiti ?
Wallahi tun daren jiya zazzabin ya fara har gashi sai da aka hada da asibiti ya dan tsura min ido can yace sannu ko idana suna a lumshe sai marry dake bakin gadon da nake zaune ta dafani tana fadin brother din ki na gaishe ki.
Kai kawai na gyada ba tare dana bude idona ba ya juya gurin Amma yana fadin yanzu may likita yace ?
Amma ta tabe baki tana fadin ciwo haka ba cin abinci ba dadin jinya gare shi ba don nasan harda yunwa na damun yar nan ace mutum tun jiya baici abinci ba a cikin sa sai ruwan leda kawai ake dura mai a jiki.
Dan shiru dakin yayi kafin ya furta zamu koma don akwai gajiya a jikina yanzu na dawo daga tafiya kiran daddy dazun yasa na nace barin inzo in duba ku ?
O to ai da ka sani baka zo ba tunda bamu da albatkacin da zaka zo nan don mu yanzu.
Kallon Amma ya danyi ya girgiza kai kafin ya juya yana fadin merry ta tashi su tafi ta yunkura ta tashi da kyat tana fadin get well sson my dear takai mi dunbata a hannu.
Ina jin shiru yasa na dan bude ido naga daga ni sai Amma a dakin mamu bata cikin dakin haka yasa na gane ta dan rakasu ne don kawu ya fice tun shigowan shi nasan ba komai ya fitar dashi daga dakin ba sai ganin merry a kusan tsirara take da shiganta don dan rigace armless ba hannu rigan ta saya mata iya cinyar ta.
Nayi mamakin yadda yaya umar ya ke iya fita da ita haka a cikin mahaifan shi ba tare da yaji nauyin hakan ba.
Sai da mamu taga wucewan su ta juyo zuwa dakin tana fadin gwoggo bai dace kina wa Umar haka ba sai matar tasa ta tsargu da rashin kulatan da bakuyi alhalin tasan matsayin ku gare ta.
Yo yayi haushin mana idan yai fushi yabar zuwa muna da ita gida man idan akwai abinda baki a duniyan nan ingsnshi tare da kafiran yarinyar nan bai son muyi fushi dashi ya kwaso muna ita.
Shiko umar suna shiga mota merry ta fara korafin wai may grandmother din shi take nufi da ita ?
Ko haka halinta yake ne kamar na mum din shi bata son mutane itama shiyasa fa take son wanan step mum din nasa don tana da friendly lokaci daya.
Iska ya furzu jinta kawai yake zuciyar tana faman da sake sake a kan yadda zasu kwashe da merry idan wanan zancen ya fito fili don yaga son da takewa mutanen bana wasa bane saboda duk halin da take tana arba da mamu koni zata washe.


ZAINAB IDRIS MAKAWA
16/11/2021, 23:08 - 🤐🤐🤐: BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM, , , , ,


Tun dasowan shi gida zuciyar shi take cike da tunanen wanan al,amarin bai taba gaskata yarintana a fili ba sai yau din da yai min kallon tsaba.
Tsuki yaja yana gyara kwanciyar shi tare da lumshe idanuwan shi ya rasa gane dalilin nacin daddy akan sai ya auri wanan yarinyar wanan ai wahala kawai daddy yake son dora min.
Yarinyar da ma kila yanzu take shirin fara period din ta ko ta fara ma ai wanan bada wani dadewa ba can.
Juyi ya kara yi sai jin hannun merry yayi a saman jikin shi tana sauke numfashi tare da fadin mey yasa bakai barci ba dear ?
A hankali ya sauke numfashi yana kai hannun shi saman cikin ta ya dan shafawa sake tambayan shi tayi may ke damun zuciyar ka haka ?
Yace nothing kai tsaye tare da dan sunsunan wuyar ta yana lumshe idanuwan shi a hankali.
Sai dai ba wanda yai magana itama merry kamar yadda ya makaleta haka ta manne a jikin shi a haka barci ya dauke su.
Washe gari ma akwai damuwa a tare dashi sai dai yayi kokarin boyewa merry din abinda ke damun shi a wanan dan takin yan cikin halin damu iri iri.
Ga na tafiyan merry da suka sashi gaba ita da mahaifanta ga hjy shi tace ba zancen tafiyan merry din a gurin ta da kuma umurnin bijirewa mahaifin shi data umurceshi yayi ga mahaifin su dake son yayi mai nasa biyayyan kuma.
Wanan abin ne ya taru yai masa yawa a zuciya ya kasa samun natsuwa a tare dashi a cikin dan yanayin da ake.
A gagauce yayi breakfast ya fito don merry na ciki kwance bata tashi ba tun barcin daren jiya din akidar tace bata tashi sai kusan sha biyu ko sha daya da wani abu na safe.
Duk da yasan ba wani itin hurdan nan a tsakanin shi da Nasir abokin shi amma sai yau yaji yana bukatan shawaran Nasir din don shi yafi kwanta mai a rai duk cikin wa yanda yake mu,amula dasu yanzu
Yana fita gidan ya kira layin Nasir sai da Nasir yayi mamakin ganin nomban Umar din dake kiran shi yau yasan tun suna yara suke tare dashi.
Zuwanshi kasan waje ne yayi sanadin raba karfin abotan su sosai suka dan rage yawan hurda da juna da farko Nasir kayi kokari ya neme shi a layin sai ya kasance ba kasafai yake daukan wayan shi ba.
Hakan ne yasa Nasir din ya fita batun shi shima ya hakkura da lamarin umar din a tafi a hakan ko wanan dawowan da Umar yayi kasan bai wuce sau biyu da suka hadu ba dashi.
Shi yasa yanzu da yaga kiran umar din yake mamakin kiran nasa a yanzu din don hakada mamaki ya dauki wayan nasa yana sallama gare shi.
Umar da zuciyar shi ke cike da kunci da takaici daya taro mashi a zuciya sai tunane barkatai a yanzun yana ganin ta hanyar Nasir kadai ya rage mai ya samu mafita da tashi shawaran don shi a bangaren shi abubuwa sun taru sun masa yawa.
Ta yadda ya kasa lalubo don bai son yai wa kowa daga cikin mutanen nan uku butulci a rayuwan shi.
Sallaman Nasir ne ya katse shi a lokacin yaji yana amsa wayan tasa daga bangaren shi amsa sallaman yayi tare da fadin Nasir kana ina ne ya bashi amsa da ina gidana umar lafiya ko ?
Yace kajirani ina hanya yanzu gani tafe gidan daga haka ya kashe wayan yana ci gaba da tukin motar.
Da lalube da tambaya ya samu ya isa gidan Nasir ya isa ya tsayar da motar a kofan gidan ya fito sai da ya dan tsaya yayi tunanen abinda zai fadawa Nasir din ya danna remote din motar tashi motar ta rufe.
Kallon gidan yayi gidsn na a rufe haka yasa ya dubi wayan shi na laluban layin Nasir din yana ganin kamar ya fita dayaga bai zo ba.
Nasir kana inane gani na iso kofan gidan naka a samu get a rufe .
Nasir ya bashi amsa da ina ciki ai tunda kace kana tafe ban fita ba ina jiran ka gani nan fitowa yanzu.
Cikin yan seconds sai yaji ana budan kofan gidan Nasir ne ya fito daga ciki yana washe baki da ganin umar din yana mamaki.
Umar din dake tsaye a cikin wata shada gizna mai kalar ruwan kasa dinkin rigan mai dan karamin hannu din kin bai sauka kasa sosai ba sai gaban rigan da akaiwa dan karamin ado da aninaya kalar shaddan.
Hulan dake kanshi kalan kayan ne yar karama da gani daga waje yazo dasu sai takalama bakake masu daukan ido ga kamshin turaren sa da yakeyi.
Ganin Nasir din da fara,a shima ya yana dan fara,a a fuskan shi wanda bai hana dinbin damuwan nasa ya boyo a fuskan shi ba.
Nasir ya kalle shi yana mika mai hannu tare da fadin abokina yanayin ka ya nuna min akwai damuwa a tare dakai mana yau.
Dan murmyshin da baikai ciki ba ya kara kakarowa a fuskan tashi yana rike da hannun Nasir din yake fadin gani dai Nasir yau garin babu dadi a gurina.
Nasir ya sake hannun nasa yana fadin subbahanallahi mu shiga daga ciki mana mu tsaya nan waje muna magana don naga maganan mai muhinmanci ne sosai ke rafe dakai.
Umar yace kasan yanzu kai magidanci ne ba zan so shiga gidan ka kai tsaye haka ba Nasir.
Nasir dai yayi murmushi yana fadin ka wuce hakan a wurina umar har abada ko da ka yar da Friendship din mu ni ban yar ba a guna don haka ka shigo kawai ciki malam nan kamar gidan ka ne ai in ga zumunci.
A tare suka shiga falon Nasir din wanda umar din kalamin Nasir yasa yaji ba dadi a ransa don gaskiya ya sake abokin shi na kwarai mai kaunar shi tun farko.
Suna shiga Umar ya fada a saman kujeran farko na shiga falon yana lumshe idanuwan shi a hankali kallo daya zakai mai kasan yana cikin tashin hankali.
Nasir ya tsura mai ido ya kasace masa komai har tsayin dan lokacin kafin ya dago ya dawo kujeran dake fuskantan na umar din.
Yau yanayin abokin nasa ya bashi tsoro don yasan halin sa idan abu ya damay shi sosai yake ganin sa hakan .
Da kyat nasir ya bude baki yace mai wai lafiya mayke faruwa ne haka abokina don yanayin naka ya fars rikitani gaskiya.
Maimakon Umar din ya bashi amsa sai ya koma kwantar da kanshi saman kujera ya daga kai sama tankar wanda ke tunane.
Naris daya kura mai ido yakai hannun shi saman kafadan shi yana fadin be a man abikina ka fada min abinda ya faru ko zamu samo mafita.
Saida umar ya sauke ajiyan zuciya ya dago kai yana kallin nasir din tare da fadin Nasir ina cikin tsaka mai wuya akan mutun uku daddy da mama da kuma matana dana fadama na aura tana nan ta biyo ni da tsohon ciki tun bayan tahowana.
Nan dai Umar din ya labarta mai komai dake faruwa dashi wanda ya rasa shawo kan matsalan da kan shi.
Nasir ya jinjina kanshi yana fadin lalai abokina kana cikin matsala sosai sai dai idan mun kwantar da hankali mukabi maganan a sannu ko wani zamu samu mafita akansa da yardan Allah.
Jin hakan ya sa umar din yadan fara samun natsuwa yace na rasa yadda zanyi ne Nasir don mama tana kan bakanta auren sauran yan uwana bai daga mata hankali ba kamar nawa.
Nasir ya murmusa yana fadin tana da nata dalilin in kayi la,akari da halin su na mata akan kishi don kaga ba wani shiri bane sosai a tsakanin diba ga yadda ita maimuna din ta auri daddy yanzu.
Umar wanan bai isa ya tayar ma da hannkaliba haka har yanayin ka ya nuna kamar wani abin tashin hankaline ya samu haka.
Umar yace maganan ka gadkiyace don yadda da farko mama ta matsa muna mu dawo kasan nan mu kwatar mata inci a gurin daddy da kishiyoyin kai har Amma abinda take fada muna a kanta muna can babu dadi in gajarce maka.
Sai bayan mun zo ne din muka samu abin ba haka yake ba don da farko har ina mamakin sauyawan ita maimuna din ga yadda mama ke fada muna maganan ta muna can.
Sai gashi mun samu maimunan tana binta sauda kafa saidai ita mamadin bata bukatan hakan don tana ganin wai don a kuntata mata ne maimunan ta shigo gidan.
Tsuki Nasir yaja yana fadin wanan ku maza ba damuwanku bane ai akan wanan bamu da matsala nake gani yiwa daddy biyayya gare ka ya zama dole amma fa sai ta hanyar yiwa mama hikima ka nuna mata kana bayan ta a yanzu dari bisa dari ka yarda da maganan ta .
Ta haka ne har a sannu ka cikawa daddy nasa burin a boye ta hanyar yiwa daddy bayanin gaskiya.
Sai maganan matar ka da zamu fahintar da mama kada wani matsala yazo ya faru da meery din a nan a kuka da ita har daddy kai masa wanan bayanin tunda ita mama ai dole ta yarda shawaran da daddy ya yanke a gidan sa.
Umar da yai kasake yana sauraren Nasir din ya nisa sannu a hankali tare da kada kanahi alaman gamsuwa da maganan Nasir din.
Sai da yaji Nasir yace ina dai fatan ba zaka ha,inci daddy ba ga wanan manufan nasa zaka rike mai amanan yarinyar kamar yadda yake rikonta shi a gidan sa?
Murmushin karfin hali Umar yayi a fuskanshi yana fadin don wanan kada ka damu nasan ta yadda zanyi in farautawa daddy din rai a kan ta idan na inganta rayuwanta kamar yadda nasan shi daddy ke hasashe a gare mu.
Ya marauraice murya yana fadin yarinyar fa karamace sosai Nasir ina zan kaita yanzu ina jiyewa kaina ranan da merry zata fahinci hakan Nasir a raina.
Nasir da yai shiru yana sauraron abokin nasa da yake fadin zaiyi auren yarinyar ne a bisa umurnin mahaifin shi shima kawai.
Can Nasir ya nisa yana fadin Nasir naji maganan ka a yanzu kan yarinyar sai dai ni shawaran da zan baka shine ka rike amana aure yafi gaban wasa wallahi.
Dole ka ba yarinyar nan hakkinta daya rataya a wuyanka koda kuwa ranka ba zai so hakan ba sai ka cire son zuviya a ranka komai zai zo maka daidai.
A fusace ya juyo yana fadin bani da ra,ayin yin mata biyu a raina nasir kafi kowa sanin wanan tsarin nawa tun muna yara banda ra,ayin yin hakan a rayuwata.
Nasir yayi murmushi yana fadin a dai bi wanan a sannu yanzu domi aure wani babban sha,ani ne sosai.
Waya Umar da yai kara ya hanashi magana da nasir din ya bi wayan dake aje a gefen shi da kallo yaga merry ce ke kiranshi lokacin ta tashi bata gamshi a gida ba.
Bai san lokacin da ya saki guntun tsuki ba ya bar wayan bai dauka ba har ya tsunke.
Nasir ya kalle shi yana fadin kayi hakkuri a bokina mu hwada wanan mu gani ko zai fishemu ga wanan maganan kaga daga baya sai mu san yadda za a bullowa sauran magana yanzu a samu ita merry din ta bar kasan nan tukun.
Saboda hakan ne ake son auren yar kasanka don wani tsari na al,adan mu nan kaga a wani fannin mama tana da gaskiyanta .
Don ka riga da kayi kuskure tun farko na auro bare baren kuma yar a halul kitabi da bata sallah kamar mu sai dai shi kaddaran mutum bai wuce shi.

Da safe aka sallamoni daga asibitin don sunga zazzabin ya sauka sosai yasa suka ban sallama muka dawo gida a daidai lokacin da mamu ke shirin zuwa dubani.
Sai gamu mun dawo

Please Login or Register in order to submit comment