You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

baga ya dauki hanyar gidan yaya umar din dan juyowa nayi ina kallon shi yace kada ki damu kanwata nasan abinda nake ai ba kaiki zanyi ba dauko shi zamuyi fita zamuyi tare.
Idan mun tsaya sai ki koma bay ina fatan bamu takura maki ba dai nace babu komai yaya nagode ya dan juyo yana fadin da may kuma ?
Ban iya bashi amsa ba har ya fita daga motar ya shiga gidan nikuma na fito na koma baya na zauna.
Ina nan zaune na hango su sun fito suna magana kamar kullun yau ma yana saye da kananan kaya a jikin shi bakar rigace da anini daidai damtsen hannun sai farin wando daga ksa da bakaken takalma.
Kodai ban sanshi ba da sosai zan iya cewa naga ya fada sosai ya danyi duhu kaina na kawar daga kallo su har suka karaso bakin motar.
Tun daga nesa ya ya kalli Aliyu yace yaya haka kuma baka kaita gida bane ko yaya yace na ratsene mu dauke ka sai mu wuce idan mun sauke ta.
Daga haka baiyi magana ba muna karya kwanan gidan muka hango motar daddy a wajen gidan.
Daddy ya dawo gida ke nan yace a waje Aliyu ya tsaya da mota na fito na barsu ciki bayan fitana Aliyu yace yarinyar nan bata da lafiya fa.
Yana magana ya balle mota ya fito ba tare da yayi magana ba sai daya dira kasa yace fito mu shiga muga daddy kafin mu wuce.
Koda nashiga su hajita maryam nagani ta rako wasu kawayen ta zasu tafi suka tsuro min idanuwan su na shige ba tare da na gaidasu ba don nasan gulmana akeyi.
Shigowa su ne ya hana suyi maganana kallon ya koma gare su ikon Allah shi wanan ma badamu ba uwarshi na can tana ciwo don auren shi .
Shi yana nan yana yawo da amaryan shi a gari lalai zamani kuwa maganan uwarshi ne an gama dashi sannu kawai sukace masu suka shige kai folon mahaifin su kai tsaye.
Sun samay shi yana shirin fita kuma yana ganin su suka tsayar dashi dole ya zauna suma suka samu wuri suka zauna a kasa.
Dan shiru ne kafin umar din yace daddy munji abinda ya faru tsakanin ka da mama da safe ya sai ya kara sunkuyar da kai cikin ladabi yace don Allah daddy kayi hakkuri mama ta dawo dakin ta.
Ya dubeshi da mamaki yace umar ai ban koreta ba zabi na bata kuma taga hakan yafi mata don haka ko jummai zata dawo gidan nan sai ta gane kuren ta tayi nadama.
Ku kankuma sai kunyi min alkawarin amincewa da zabina gare ku ba zaku watsa min kasa a idon duniya ba.
Zaku riki matayen ku bisa amana ba zaku wullakanta diyan mutane ba kamar yadda suma iyayyen su sukaga mutuncina suka bada su Amana.
Umar yace daddy ai kasan bamu taba maka musu ba ga duk abindaka umurcemu muyi yace na sani umar sai dai mahaifiyar ku tasha alwashin sai ta raba wanan auren danaku dana salma ga baki daya.
Har tana ikirari salma tafito su tafi da ita na nuna idan salma tabisu bani ba ita a duniyan nan.
Aliyu yai saurin fadin daddy abin baikai can ba ai su salma sun mayar muna da yadda akayi adaiyi hakkuri daddy don Allah.
Sun dan kara bashi hakkuri yace sai yayi shawara nan yake fada masu zancen tarewan matan su gobe don ba za a tsaya jiran komai ba.
Sun mai godiyan dole kafin su fito zuwa gidan da mahaifiyar su take itama su bata hakkuri kamar yadda suka ba mahaifin su din.


ZAINAB IDRIS MAKAWA
16/11/2021, 23:13 - 🤐🤐🤐: YA AR-RAMANIN AR RAHIM YA HAYYU YA KAIYUMUN, , , , , , ,


Ina shiga part din mu na samu baki a part din mama saude da umman su Atika sai Atika da manjo da Addahna da wasu mutum biyu dana sani a azare.
Ina ganin su na fashe da kuka maimakon farin ciki jikin umman Atika na fada na darji kuka na wanda duk wanda ke falon sai da yai hawaye.
Daya daga cikin kannen manjo da suka zo tare tace ki share hawayen ki yar nan aure ba mutuwa bane abin farin cikine tunda kikaga har munzo murnan haka.
Ya kamata ace farin cikin ganin mu kikayi sai kuma ki aza muna kuka haka maza ki share hawaye ki daina wanan kukan haka.
Yadda tace hakan nayi don yadda take magana umurnine take bani a lokacin haka yasa nayi saurin dakatar da kukan da nakeyi din.
Umma ta dan bugi bayana tana fadin ai saiki saka mu jin ba dadin zuwan mu nan nidakewa Atika fatan samun nasara irin haka har yaushe zaki tsaya kina kuka.
Duk wata uwa yana cikin farin cikin zuciyar ta yau ace ka kai yarka aure haka cikin lumana aike ba karamin sa,an aure kikayi ba yar nan.
Tashi ku shiga ciki da Atika kuci abinci nasan ke take jira ta kasa cin komai tun da muka iso.
Mikewa nayi muka shiga daki nida Atika nan saida mukai kukan mu muka share hawaye muryan Aisha ne ta shigo tana fadin yanzu mai kumshi tazo zamuyi dama ai nace naki yana nan kamar yau akai maki shi.
Saida ta kalli Atika ta dan rage tsawo tana fadin ance kun fita tare da ya Aliyu dazun dana shigo nace gurin photo ya kaini nayi.
Photo kuma wani irin photo ke nan ko kuma harda photo zakuyi ne na amarya da ango wai ?
Ango da uwargida zamuyi ba photo na harareta ina fadi tare da ya Aliyu muka fita ashe haka yake da saukin kai sosai .
Wani dadi taji tana kaiwa zaune tare da fadin don Allah da gaske kikeyi A ruwa ?
Harara na kara aika mata nace a,a a wuta don Allah tafi nama fasa baki labarin ta rungumoni tana fadin haba yar kanwata fada min don Allah yadda kukayi dashi mana.
Yayi maki magana na don Allah ta fada tana tsurenu da idanuwan ta tana son jin amsa daga bakina.
Kai na girgiza mata nace ko daya bai mun maganan ki ba wallahi ya dai bani shawara sosai kuma naji dadin hakan da yai min don ya kwantar min da hankalina kadan.
Rarashi na take wai in dan fada mata abinda yace mun nace ki bari kema zai fada maki ai idan kun hadu.
Hannuna ta kama tana fafin haba yar kanwata kin san fa bamu haka dake a gidan nan keta hannun damanane aru wai fatima.
Na kara hararanta nace ba zaki daina kirana da sunan nan ba ko ?
Bakina ya saba hakan saboda Amma dake yawan kiran sunan kulun nace ni rabu dani don Allah na kashe wanan sunan dai tace naji matar yaya.
Ashe baki son kiji komai ke nan gara ma bakin ki ya saba da kirana da kanwar yaya din zaifi maki sauki.
Ni ba wani abu yace min ba magana kawai yai min akan inda zanje shine ya ban shawara kawai.
Ina fadin haka nakai kwance tace waike ko kina shirin wankin amare da za ayi muna gobe ?
Yi nayi kamar ban jita ba na kyale ina kallon gefen da nake kwance ina tunane a raina.

Suna zaune a dan karamin falin gidan yayan su gidan da hjy su take zaune duk kansu su uku ne a zaune suna fuskantan mahaifiyar tasu da suke zaune ita sisters din ta duka uku.
Tace kundai ji abinda mahaifin ku yai mun ko saboda ku har wanan yar banzan salma zance tafito mu bashi gidan shi taki fitowa.
Ba wanda ya iya magana daga cikin su sai habbib da yakai iya kuluwa da zancen yace.
Amma mama kema kina da laifi gaskiya yau kuke da daddy bai taba cewa ki barmasa gidan shi ba sai kan wanan zancen .
Mun fada maki ki kwantar da hankalin ki tun farko tun abin nan bai kaiga haka ba kinki kwantar da hankalin ki.
Abi abin a sannu cikin hikima da muke shirya kin dai san ba son abin nan muke ba dukan mu muna hakane saboda farin cikin ki.
Amma mama kikaki bin shawaran mu har abin yakai ga muni haka garemu dake don daddy ya hau fiya da yadda kike tsanmani gaskiya.
Yayi ta hawa mana shine may don ya koreta gidan shi akace nufanshin ta aka katse ko may ?
Look mama rabi wanan magana ne tsajanin mu da mahaifiyar mu don ba zamu so wanan abinda ya faru yayi tsauri ba don Allah ina rokon ku idan ba zaku tayamu kwantarwa mahaifiyar da rai akan zancen nan ba kuyi shiru.
Babawo ni zaka fadawa haka ko kin fimu son tane zaka nuna min yau ka tuna uwa daya uba daya suka haifemu don haka ba zaka nuna min son ta ba yanzu.
Kuna son ta aka hada kai daku akai mata waban cin fuskan da yankan kauna wai har kanwarku ne za a dauka a hada da almajirin gidan ku don rainin wayau ?
Please mama ciki hade hannayen shi habbib ne ke magana na rokeki kamar yadda dan uwana ya rokeku ku fitar da bakin ku ga wanan zancen don Allah.
Ba zasu fitar ba ai bansan kunzo nan kuyi muna rasgin kunya bane da kuka koyo a kasan turai.
Karya tafada ba gaskiya bane bakin ku hade da mahaifin naku don a tozartani haba mama ya kamata ki fahince mu yanzu mafa mun zauna da daddy akan maganan nan ya kidaya muna sharudan shi akan in har kince ba zamubi zabin shi ba gare mu a bakin auren ki.
Mama yaya kike son muyi da zuciyar mu wanan abin fa don farin cikin ki muka yarda mukayi shi ba wai son ran mu bane Aliyu ya fada shima rai bace.
Tace haka yace yace kwarai kuwa don mun zauna dashi da baba balarabe ya kara jaddada muna hakan da yamman nan.
Kallon juna sukayi sai hjy rakiya tace ya kamata Alh yai muna uzuri tunda muma muna hakki a kan ku ai.
Musanman salma da akaiwa wanan bakin hadin dakai babawo di yan matar shi cefa yayiwa gata amma mu namu ya bata mata asali.
Habbib ya kalle ta yace kada kuce haka mama don salma tana son mijin ta munyi magana da ita tana son mijin ta.
Kabar wanan zancen wai salma nason mijin ta uwar tace kabar wanan kazamin zancen habbib .
Yace wallahi mama da bakinta ta fada muna da muka zauna da ita bawai mun tursasa mata ta fadi ba.
Kallon juna sukayi kafin uwar tace zanko halaka yar iska idan tace wanan dan almajirin take kauna mutum da naki jinin shi a duniyan nan.
Haba anty ki bar fadin haka don Allah tunda yanzu ya zama surikin ki nifa naga ku bar Alh kawai yayi iko da iyalin shi yadda yake son yi shine saukin mu.
Ki samu ki koma dakin ki don zaman nan ba zai fishe ki ba tun mutane basu farga da hakan ba.
Bazata koma ko ina ba Asmau idan bamu samu sabani dake akan wanan zancen ba a wurin nan may nake ?
An gaya maki kowa irin kine da namiji ke takawa kina kurun don ruwan cikin tsiya nina rasa inda kika kwaso halin nan kamar ba Auta ta haifeki ba.
Ku tashi muje umar daya mike yace da sauran ku tafi mana mai bakin zuciyar tsiya dama nasan bayan ubanka kake ai.
To bari kaji muddin ina raye yar iskan yarinyar nan ba zata shigo min cikin zuri,ana ba .
Amma anty da kin kyale kamar yadda sukace suna bin mahaifin nasu a hankali ne ba a san manufan su ba ai.
Su kan sun fice sun barsu a nan ba wanda yaiwa dan uwa magana daga cikin su har suka shiga motan da suka zo a ciki.
Saida safe hjy keji wai ranan ne tarewan amare don Alh ya aiko ma kawun su da yayan su yace a fada masu yau salma zata tare gidan mijin ta tare da sauran Amare.
Don haka yake sanar dasu idan akwai mutum biyu daga bangaren su da zasuzo da dare akai salma dakin ta.
Yayan nasu ya kare masu bayani hjy tace yasha karya wallahi babu inda salma zata gidan wanan mijin da zuciyar ta bai amince dashi ba.
Yayan nasu yace kinga jummai tashin hankali yanzu ba naki bane zan tafi in samu kawo a gyara zancen nan naku ki koma dakin ki ki kai yarki aure kikuma tari sarakan ki da zasu shigo hannun diyan ki.
Maimakon ta saduda sai kawai tace amma yaya in kun min haka baku min adalci ba sam yadda yake tunanen banda amfani a gidan yanzu ya koreni sai idan yazo da kafan shi zan koma don nasan barazana yakeyi bazai kai mu aure bani gida ba.
Hjy Rabi tace ni dama nasani wanan kamay kamay da yakeyi don dai ta dawone barazane kawai yakeyi .
Nan dai suka kananaye shi da dasin bakin mata har yaji ya gamsu da maganan shi bai neme kawun nasu da sukejin maganan shi ba.

Ina kwamce dakin mamu inda na mayar gurin zamana a yanzu sai ga mamu ta shigo ta bude wardrobe din ta tana fito da kaya a ciki sabbi an dinka su ta zube saman gado a gefena .
Atika ta tashi ku shiya tana nuna kayan da zan saka a lokacin tare da mata bayanin sauran kayan lokacin da zanyi amfani dasu.
Sannu a hankali gida ya fara cika da mata yan wunin buki ko wani bangare yan uwan iyayyen mu mata ne suka cika shi idan an debe part din hjy da ba wani nata wanda yazo daga mata har mazan su.
Kawu tun safe ya maida salma part din Amma inda dukkan mu muka taru a can nayi mamakin ganin har sunyi karfin hslin gaiyato abokan su sunzo ashe.
Bangare na daga ni sai Atika da Allah ya rufa min asiri tazo muke dan kus kus din mu mu biyu.
Yan uwan kawu birni da kauye sun cika gidan fam sai faman kuskus ake na zancen hjy da bata gidan lokacin.
Karfe biyu akayi mothers daya da wankin amare sai lokacin ne mukaga yan uwan mazajen salma da ikilimi ashe sadiq din shagon kawu ne shima sun dade tare tun yana karami sai dai baikai Ahmed bunkasa ba a wurin.
Amma shima yana da rufin asirin shi gwargwadon hali don sun ginu daga Alh sosai shida Ahmed din yanzu.
Hjy maryam tayi kuka tayi korafi saidai fin karfin yan uwa da iyayye ya hanata motsawa ta saida hali.
Karfe hudu sai ga su mama hadiye sjn shigo suna fadin maza mu shirya kawu yana neman mu a falon shi.
Kusan a tare muka shiga falon bisa jagorancinn Amma mama hadiye mama Atine da matan kawu balarabe sai hjy maryam da mamu Addah da gwaggon Aisha daya.
Kowa ya samu wuri ya zauna yayin da nake manne gurin Amma gwaunin ban tausayi dani kawunan mu suna a duke.
Kawu ya dan dauki lokaci yana rubutu saman fararen envelop guda biyar sai kawu balarabe da kawu mustapha zaune a gefen shi.
Can ya dago kai yana fadin hajiya kunyi hakkuri ina rubutu koda kuka shigo ya fara gaisawa da mutanen wirin kafin ya dora da godiya ga Adda da gwaggon Aisha a karshe.
Ya kira sunan salma da rakiya sai Aisha da ikilima nice ta karshen kira nace na,am kawu ina wuni cikin dakusasshen muryan da ya gaji da kuka lokacin.
Ya amsa da kyat yana kallona tausayi yakeun don dai tausayin nake bashi sai dai ba yadda zaiyi ne don hakan ne mafita a gare mu baki daya.
Yace diyata har yanzu kukan bai kare bane kiyi hakkuri haka musulunci ya gadar damu mu raya sunna a tsakanin mu karfafa zumunta a tsakanin yan uwa musulmai.
Ya kare da kiyi hakkuri kinji na gyada kai kawai ba bakin magana gare ni shashekan kuka nake saukewa a hankali daga inda nake zaune.
Dago kai yayi ya kallemu dukan mu yace da farko zan fara da godiya da Allah ya nuna muna wanan ranan mai albarka ranan da ya nufa a cikin kudin tarihin ku zamu kaiku gidan mazajen ku lafiya.
Nasiha yayi muna mai kashe jikin bawa a gurin yayin da falon yayi tsit ga baki daya na dan wani lokaci ana sauraren shi.
Ya kare yana saka muna albarka tare da fatan zaman lafiya a tsakanin mu da mazajen namu yace a tsarin su ba zancen saki ko yaji a gidan nan din haka kowa yaje ya zauna lafiya da mijin shi.
Salma ya kalla yana miko mata envelop dake dauke da sunnanta tare da fadin wanan sadakin ki ne hannkin ki ne don haka muka yanke shawaran bawa kowan ku ga hannun ta don sadaki ba abin wasa bane.
Haka yai ta kiran mu daya bayan daya yana mika muna envelop din dake tare a gaban shi wanda muka samu yana rubutu a kai.
Bayan ya gama bamu ne yace yanzu sai ku shiya ga balarabe ga mustapha da gwaggonin ku zamu kaiku dakunan ku kfin yamma ya karayi.
Ke fatima ina ganin gobe zaku bar kasan nan ko zuwa jibi da fatan zakiyi amfani da tarbiyan da muka doraku akai.
Kada kikaga bamu kusa ki dauki wani tarbiyan daba namu ba ki dorawa kanki a can.
Shigan ki gidan dan uwanki yana nufin wani haskene a rayuwan shi daya manta a baya ke zakiyi kokarin dawo muna da akidun mu da al,adun mu a acikin zurian shi.
Don haka ashe aikine babba ja a gaban ki aka doraki kiyi ba kamar sauran da su mazajen su basu cunkushe da wasu al,adun a gidajen su ba.
Kawu balarabe ya karbe da fadin kindai san wanan kafiran matar tashi sai kin ture wasu al,adu nata kada ki yarda al,adunta yayi tasiri a gare ku ko kadan kiyi kokarin kafa naki akidan addin nin a zukatan duk na tare daku.
Kibi mijin ki sauda kafa yinayi bari na bari sai a zauna lafiya a tsakanin ku kuka mai tsuma rai nakara fashewa dashi a wurin saida naba kowa dake gurin tausayi Amma ma kukan ta fara tana fadin ko zaku barta gida ta kwana biyu alabashin daga baya idan yazo sai su tafi.
Kunga ko yanzu ba lafiyane a jikin ta ba a hakan kuke tunanen kaita cikin wanan halin ?
Dan murmushi kawu Alh ya sake yayi da kawu balarabe yace haba babba mai zaisa a barta gida bayan mijin ta yana gari ?
Daga haka kowa na falon ya shiga yi muna nasiha kawu yace mu tashi mu shiga muyi bankwana da iyayyen mu su bamu mintuna talatin a fito.
Kowa ya tashi a guri mamu na zaune kanta a duke tana zubar da hawaye a fuskan ta kawu mustapha yace kiyi hakkuri maimuna tashi kije kuyi sallama da yar ki ko ina take Allah ya tsare muna ita.
Kuka nake darza sosai a part din mamu saman jikin manjo mamjo din tana tayani .
Haka mamu ta shigo ta samay mu da bata kukan ana bata hakkuri sosai takardan hannuna na miko mata wanda kawu ya bamu tace dashi zaki sayadi hakkin kine a cikin sa.
Kaina gyada nace mamu ki aje a wurin ki tunda va abinda dashi a can ki karba Addah tace don kada ya salwance a wurin ta .
Basu tsaya jiran komai ba ko kebewa bamu samu yi da mamu ba haka su mama hadiye suka shigo suna fadin wai in fito kowa na waje ni ake jira.
Kukan da nakeyi naba kowa tausayi mota na samu a bude kawu balarabe ne maija kawu Alh yana zaune a gefen shi.
Amaren na zaune baya jeep din dukkan su sai kuka sukeyi kawu mustapha yana jan dayan motan dasu gwaggo Addah ke ciki harda su mamu da Hjy maryam su kawu sunce sufito su rakamu dakunan mu.
Aka dauki hanya damu zuwa gidanjen mazan mu sai fatan alheri a gare mu ga sauran mutanen da aka bari basu je ba.


ZAINAB IDRIS MAKAWA
16/11/2021, 23:13 - 🤐🤐🤐: EID MUBARAK YAN UWA ALLAH YA MAIMAITA MUNA NA BADIN BADADA AMIN, , , , , ,

Allah sarki rayuwa aure yakin mata gishinkin rayuwan mace muna kallo abinda bamu taba kawowa a ran mu ba yau ya faru damu wai gidan aure za,a kaimu wanan fitan da mukayi gida.
Gidan salma aka fara zuwa nan muka samu gidan a cike da yan uwan Ahmed da sukazo daga garin su can jahar katsina.
Daga gidan salma sai gidan Rakiya gidan yana rufe babu kowa daga bangaren hjy ko Alh do bukin ba tsari akayi shi duk yan uwa nacan gidan kawu Alh.
Itama dai an mata nasiha sosai muka fito zuwa gidan Ikilima yan uwan sadiq sundan cika gidan daga jahar sokoto dama abokan arzikin shi.
Sai gidan Aisha inda muka samu yana gida da wasu abokan shi mutum uku bamu fita ba hjy Asmau tazo da kawayen ta da matan kawun su suna bada hakkuri .
Mun fito tare dasu ana raha sukace zasu riga isa gidan umar kada acisu tara hakan akayi don sun rigamu isa gidan.
Su suka tare mu ina jin mota ya tsaya na kara makalewa a jikin Addah ina rusa kuka haka Addah ta rikeni muka fito daga cikin motan.
Ta dan tsaya dani tana rada min a kunnena abinda zan karanto bissimilah kafa goma sha uku sai falaki da nasi da kulhuwallahu uku uku kowa harsu kawu aka tsaya daga kofa.
Muna shiga ina jin mutane na fadin masha Allah gida yayi kyau kusan duk gidajen sun fadi hakan bawai a nawa kawai suke fada ba.
Kawu ya riko hannu na yana fadin ina part din yata din yake aka nuna mai har dakin suka kaini su uku dashi sai kawu balarabe da Addah.
Ya zaunar dani saman gado tare da dafa kaina yana jero min addu,oi suna amsawa da amin yakare ya dan bubuga min baya yana fadin inyi shiru insha Allahu wanan auren zai zamo min alheri a rayuwana.
Zai wuce na riko hannun shi ina kuka tare da fadin kawu kada kutafi ku barni don Allah kawu yaya umar ba sona yakw ba dukana zasu dinga yi don Allah kawu kada ku wuce ku barni a gidan nan da kyat ya iya bambare hannun shi daga nawa yana share hawaye shima.
Nace wayo Addah na Addah kada ki tafi ki barni kema Addah mutuwa zanyi wallahi idan kin tafi kin barni.
Itama kukan

Please Login or Register in order to submit comment