You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Atika kamar ta biyo mi take ji tazo ta ganki sai mahaifin tane dai ba lafiya sosai shima tunda yai wanan hatsarin motar bai kara samun lafiya ba.
Duk sai naji ba dadi a raina don ban manta da irin halarcin da mutanen suka nuna min ba dan zama a azare danayi.
Ina like da su muna ta hira sai ga mamu ta shigo dakin a cikin hijjab din ta tana fadin watau sayadi ba zaki barsu su hutaba kin cika su da surtun tsiya tun dazun.
Ki barsu su huta har zuwa gobe tunda ba yanzu zasu koma ba sai babba ta gama ganin likita.
Manjo da ta koma min shiru shiru yanzu bata son yawan hayaniya tace ki rabu da ita tayi kewan mu ne yar nan.
Ki tashi ki kaiwa gwaggo abincin ta kin barshi a kitchen tun dazun yana sanyi manjo tace watau dai kin kore muna ita da wayau ko ?
Ina shiga part din Amma na samay ta zaune tana jan tasbaha itama na kai abincin inda muke ajewa zan wuce tace dawo yan nema yau kinga kakan ki zumudi ya hana ki tsayawa to ba inda zaki sai na more ki a nan nima.
Kinga dauko min ledan can dake aje dazun maigidana ya shigo min dashi wai ya dawo ikko haka yake tafiyan shi ba salma shi sai dai idan ya dawo mutum yaji.
Ina daukowa nace Amma wani maigidan ki ya kawo maki ko mijin ki ya dawo ne ?
Tace ja,ira kin taba ganin inda aka mutu aka dawo duniya yayan ku dai umaru ne wai ya je ikko ya kawo min tsaraba .
Na bude ledan kaya ne irin na kurmi a ciki kwakwa abarba ayaba da sauran tarkacen kurmi shake da ledan baco mai girma.
Tace ki dabarwa uwar ki don nasan ko yakawo masu nasu ba deban masu jummai zatayi ba sai dai ta aje idan ya rube ta zubar.
Nace kinga ko Amma dama duk manjo ta rame sosai da gani basu bata kulawan daya dace a can .
Amma tace yar nan ke nan azamanin nan ai diya mace kadai tasan zafin uwarta wanan sarakan zamanin babu abinda suka sani banda su mayar da uwar miji banza.
Nace bandani Amma nikan yadda naga su umma saude nawa manjo bani fatan inyi wanan rayuwan da sarakuwata.
Anya A ruwa zaki ko samu hakan gurin sarakuwar ki don babu alaman hakan zai samu sai dai gyaran Allah.
Nace ji Amma kamar kin san wanda zan aura har ki san halin uwarshi kina mun mugun fata haka ?
Tace cikin dariya kai yaro man kaza yo ni ai har na hango sarakuwar taki ko a idona idan baki sani ba san nan ke din nan da nake gani kayya a dai bar zancen don Allah.
Nace Amma Allah dai ya bar muna ke kiga auren namu nan da shekara goma mai zuwa kilama da dan hayi don ni nan kawu yace min sai na zama babban likita a gidan nan.
Kinga kuwa ai ba zancen yanzu akeyi ba ke nan tace hakane fa kinga dauki kayan ki kaiwa uwar ki kafin wa yan nan sarakunan kwadan su fito su saka maki ido.
Nace to sai da safe Amma tunda dau naga yau baki son hiran tamu dake ke tafi can tace min wa zakiwa tako hankalin ki na gun kakar ki sarai.
Na fice ina dariya da kayan a hannu na ina sauri in koma part din mu in fara ba manjo ta sha lemo da ayaba.
Na samu mamu ta gyara masu guri da zasu kwanta inda manjo tace ita a kasa zata kwanta bata hawa gadon da aka gyara masu din.
Haka yasa aka kayar mata da katifa a kasa ta kwanta a nan sai gani na shigo sai dana nunawa mamu tace in kai kitchen in aje har da safe mm ace barin dibawa manjo lemon ta dan sha.
Washe gari nayi sa,a ba zuwa school ranan a na public holiday sai aka hada muna meettime break din mu don haka zamu zauna gida na kwana biyu ke nan.
Ga mamu tayiwa merry alkawarin zamu shigo muga gidan su idan Allah ya yarda ranan ko dana tashi tun safe ban zauna ba ina aiki a part din.
Na gama abinci ne mamu ke fadin nace su Aisha su shirya don nayiwa matar yayan ku alkawarin yau zaku shigo wurin ta don ta matsa da maganan baku je ba.
Take na daure fuskana don ban son zuwa gidan ni dai har ga Allah kyaman su ma nake ji daga matar har mijin saboda arnarcin su sai nakw ganin kamar shima arne ne .
Tunda irin kayan da yake yawan sakawa irin na kafirai nake ganin kamar shi shiyasa ranan da naga yana alwala a wajen gidan mu zaije masallaci saboda gulma har tuntube nake ina waigen shi ko ya iya alwalan.
Ko ba zaki je bane kin tsaya kina wani tunane banza naki kuma kada inji ance ga abinda kikayi na rashin mutuncin a gidan nan.
Mamu ni ina ruwana dasu muje kawai mu gaida su mu fito har zan tsaya wani rashin ji kuma mamu ni yanzu na bar rawan kai fa tunda na girma.
Sai da na dan zauna wurin su manjo muka dan taba hira na shiga wanka yadi da ya kawo wa Amma tsaraba ta dinka ta vani shina saka a jikina.
Don ban taba saka shi a jikina ba sai yau na dauko na saka saboda kawai in kara burge su Addah na saka su san rikon arzikin da ake min a gidan kawu din.
Dinkin da yadin ya kara fito min da surana karara a fili ni kaina dai sai da nasan yau nayi matukar kyau sosai ba kadan ba.
Na kama jelar gashina nayi gawo dashi na nade guri daya na cushe shi san nan na daura dan kwali a kai.
Sai dana gama kallon kaina tsab na dauko sabon hijjab dina na aza saman kayan ya sauko min har kasa sosai ya rufe min kwalliyan dana bata lokaci inayin sa.
Muryan su Aisha ne a falin mu suka shigo na fito kallo na sukayi gaba dayan su Aisha tace kai amma dai fatiman nan.
Wallahi ni ban taba ganin wace ta auri hijjab kamar ki ba a duniya yanzu wanan fitan da zamuyi shine kika dauko wanan jibgegen hijab din kika saka kamar mai zuwa islamiya.
Ke kullun gaki sai kace rainon kauye dake ke kullu banga ranan da zaki waye ba wallahi kamar ba a cikin kano kike ba.
Naja na tsaya ina kallon ta a raine kafin in ce ke ba zaki gane ba Aisha may zanwa kwalliya yanzu tunda ba saurayi nake nema ba a waje.
Ki bari lokacin kwaliyana yana zuwa idan na gama neman illimina lokacin zan faso duniya ta san dani kinga lokacin masunsunina zaizo.
Kinga ko yaga surata a lokacin babu komai domin a yanzu bayyana sura bashi zaisa ka samu kasuwa ba ni dai fatana Allah ya ban na gari .
Yanzu dai ke kadai ne zakka a cikin mu zaki bimu da wanan zunbulelen hijjab din haka kamar matar uztazu.
Baki na tabe lokacin mamu na fitowa tana jin zancen mu dasu tace idan kunbi ta wanan sai ku shekara a nan tana cin ku da wanan baki nata.
Kunga ku kula idan kunje banda sai da hali don Allah kada naji anyi wani abin asha a can.
Daga haka muka fita na rike hannun fauziya don da ita zamu tafi su samir sun fita da kawu tunda safe.
Tare da Amma muka fita don ta samu wanda zai sauke mu a can tunda muka fito yaran hjy maryam suka ganmu suka tsura muna ido.
Murja tace kada ku fada masu inda zamu yanzu zasu fadawa uwar su zancen muna fita sai ga Aliyu zai fita mamu ta tsayar dashi tayi mai magana bamuji mai tace mai ba sai yace muzo mu tafi.
Har zamu zauna a baya sai naji mamu tace ke Aisha ki dawo gaba ki zauna sai su su zauna baya.
Haka mukai zaman motar sai faman kalle kalle muke na kauyanci a motar ga sanyi ga kamahin turare a ciki.
Shiru motar yayi kowan mu na gudun yayi wani dogon motsi da ba daidai ba sai can yace ke wanan hijjab din haka kamar matan malam fa ?
Haka kikaga yan uwan ki ke kullun kamar mai zuwa tafsiri dake nayi dan murmshi don na fahinci dani yake saboda ni kadaice mai hijjab a cikin mu.
Duk rawan kaina ina dan shayin yaran hjy jummai kaf din su musanman tu lokacin da naji sun taimawa mamu nake ganin mutuncin su a idona saidai ba ruwana dasu ne sai gaisuwa.
Ya dab bugi sitiyarin motar yana fadi yarinya duk zaki bar wanan ne nan gaba sai lokacin na bashi amsa da fadin ai ban fatan in bari yaya don shine tsaron mutunci na.
Ganin hakan yasa da ya sauke mu nayi mai godiya kamar yadda kowa yai masa zuciyana fam da mamakin sakar min fuskan da yayi yau ko dai don ba a gida muke bane ?
Ban ankara da inda muke ba sai da na fito daga motar tsarin gidan ya tafi da imanina sai naji kamar a mafalki nake ganin kaina a ciki.
Bani kadai ba har dasu wayayon sai da gidan ya tafi da imanin su tun a waje suka fara santin gidan dan baya naja kadan ina fadin ku ku tsaya ..
Ni dai wallahi naji tsoro ace wanan katafaren gidan wai na dan kawu ne to a ina ya samu kudin dayayi wanan gidan haka ?
Kunga kuzo mu koma mucewa mamu bamu samay su a gida ba zaifi muna alheri don ni wallahi na tsorace da wanan gidan tun bamu shiga ba gabana wallahi faduwa yake yi sosai.
Ke dan Allah mu shiga may ye na wani tsoro kamar sai damu za ayi akace maki yau sai mun ga kwam wallahi.
Aisha ke maganan tana fadi ta jawo hannun fauziya dole nima nabi bayan su inda ya Aliyu ya nuna muna hanyar shiga gidan.
Cirko cirko mukayi a wajen kofan kowa na tunane nace yanzu sallama zamuyi ko may kun dai san ba gidan musulmai mukazo ba.
Ke kika mai dashi kafiri ko jiya daya shigo Amma tayi mai tayin fura cewa yayi yana azumin thursday ne.
Nace kika sani ko nasu na kafirai yakeyi kin san suma fa suna azumin su akace .
Wai ke aka ce maki yaya din shima kafirine kamar matar shi nace in ba kafiri bane yaya ya zauna da wace bata sallah da sunan aure.
Ni kinga kallo daya da matar shi nake masu fa shiyasa ki yazo part din mu yana sallama ban karbawa don ance baida kyau ka karbawa kafiri.
Gashi da girman kai da jiji da kai ko kana gaidashi sai yayi kamar bai sanka ba kullun ba sakin fuska dashi da dan uwan nan nasa guda kusan halin su daya nake gani.
Ke ni ko kannesa su salma bance yana sake masu ba balle mu naja wani tsuki nace ni ban san may yasa mamu ke son hurda dasu ba in anyi magana tace dan uwan tane may ne may ne.
Aisha ta ja tsuki tace ke don Allah muna neman hanya kin dami mutane da surutu nace maganin yan gulma ke nan sai kun shiga an baku giya yau zaku gane baku da wayau ai.
Aisha ta wurga mi harara tace dkn Allah A ruwa raba mu da wanan zancen banzan naki nace a, a ba aruwa ba a wuta ko amma zan kashe masu wanan sunan banzan ne a bakin su.
Zaune yake yana kallon duk abinda mukeyi tsab ganin bamu da niyar nocking mun tsaya muna budan ido yasa shi ya taso ya bude kofan fuskan shi a daure tamau.
Yana fadin kai wai su waye hakane kunzo kun cika mutane da surutun tsiya tun dazun.
Mu mm mune yaya Aisha ta fada tana dan inda inda tare da fadin ina wuni yaya ?
Bai amsa ba sai juyawan da yayi ya bar muna kofan a bude ga wani sanyi daga ciki yana bugun fuskan mu daga waje.
Ni kan dariyan keta ne ya kamani lokacin ban san har nakai wurin da sai an taka step ba sai jina nayi zan fadi kasa murja ta rikoni ta baya.
Ku zauna tana ciki yace ba tare da ya juyo inda muke ba ya shige ciki yana shiga mukabi falon da kallon gulma ido gulma hanci gulma ko ina mun baza shi sai kallon kallo mukewa junan mu.
Shiru muna zaune kamar ba wanda ya kula da zuwan mu har na fara hasala a raina sai jin muryan merry mukayi tana fadin.
Wawoo yau prity ce a gidan namu sun fito rike da hannun junan su yana saye da three quarter da farar riga a jikin shi ita kuma wani dan riga iya cinya armless ne saye a jikin ta sai cikin jikin ta dayai tsini ya dago rigan.
Tana zuwa ta sake hannun shi ta rugume ni ta sake ta rugume su Aisha kamar yadda tayi min din ta juya wurin shi tana fadin yau kaga su sisters a gidan mu sun kawo muna ziyara.
Ya danyi dariyan yake yana juyawa zai bar gurin tace idan ya shiga ya turo mata mai aiki daya ta bamu abin sha.
Satan kallon Aisha na danyi kadan ina mata alaman kada mu sha komai a gidan ban don ni na gama tsorata da su gaba daya sai sake sake nake a raina.
Ina kuma mamakinwai matace ke aiken miji haka a gaban mu ko kunya baiji to ina zaji kunya nace fitowan ma nan da falon saida ya rakota.
Shigowa yar aikin mai guntun buje itama ya katse min tunane na ta shigo tana gaida mu cikindan rusunni.
Kallon kwalban nayi ban gane kwalban lemun ba shiba fanta ba ba kuma cock ba da wani leda an rufe saman shi da gani dai kaga abin maye.
Tace mu sha mana sai muka kama kallon juna suna tuna zance na kafin mu shigo gashi ko ya zama gaskiya.
Hira sosai muke kwasa da ita tana bamu labarin kasar su har dai muka dan sake jiki da ita tace ita fa tana son rawa don haka kowan mu sai yayi mata rawa tagani.
Kida ta saka duk ya gauraye gidan sai nake mamakin yadda mijin bai damu ba ya kyale take wanan tabaran haka da alama dai yau taji dadin zuwan namu din sai take jin mu kamar wasu kawayen ta can.
Su kuma Aisha uwayen rawan kai sai suke ganin zatace basu waye ba yasa suke biye mata suna ta hauka.
Suna rawan sai gashi ya fito saye da wasu tufafin ya sauya kayan sun mashi kyau sosai sun fitar mai da kurciyar shi fili ta mika mai hannu wai yazo suyi rawan ko mai ya rada mata sai tayi dari ta sunbance shi yana dan dariya ya juya ya fita sukaci gaba da rawan su nan.
Ganin ya fita gida nima na mike nace haka ake rawan sai tace sai fa na cire hijjab a jikina za a ga rawana.
Naki nan suka kamani da kokawa sai da suka cire min hijjab din wai in taka hakana ina cire hijjab din nan kuma suka shagala da dada kyau danayi wai ina boye kaina.

ZAINAB IDRIS MAKAWA
16/11/2021, 23:07 - 🤐🤐🤐: BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM HASBUNALLAHU WANI,IMAL WAKEEL, , , ,


Yana tsaye daga kofan falon da waya a hannun shi yanayi ya tsura muna ido da mamaki yake kallon rawan da mukeyi din duk mun shagala mun buge da rawa bamun ya dawo ciki ba a lokacin.
Merry sai tafa muna take da hannayen ta duka biyu a hankali ya tako zuwa wurin remote din ya dauka ya kashe kidan.
Gaba daya muka mike muna mamakin abinda ya tsayar da kidan kuma juyowan nan da zamuyi mukai arba dashi ya daure fuska tamau kamar bai taba dariya ba a rayuwan shi.
Merry ta tako zuwa gare shi tana fadin why dear zaka kashe muna redio muna enjoyed din kan mu zuwan yaran nan gidan nan yasani yau na shiga nishadin da tun zuwa mm a kasan nan ban taba shigar shi ba tana magana tana kokarin kwanci saman kafadan shi.
Dan ture merry yayi ya yana fadin why merry why kin san hakan mu ba al,adan mu bane zaki saka yaran nan rawa kija muna hatering gun iyayyena.
Rawan kawai na nishadi da suke tayani yi diya bafa gun fati naje dasu ba da kake wanan maganan haka ya kara daga mata hannun yatare da fadin please, .
Daga haka ya shige ciki ya barmu zaune tsuru tsuru muna boye fuska ni dai kasa wani mosti nayi tunda na samu na saka hijjab dina a jikina na dunkule bayan Aisha.
Ina ganin merry ta bishi nace ku tashi mu fice don Allah kun jawa mutane abin kunya Aisha duk jece kika jawo min haka wallahi na fada a dan hasale.
Merry ta fito da dan murmushi a fuskanta tana fadin mu saki jikin mu nan fa gidan dan uwan mu ne taga mun tsorace dashi ta kai zaune tana fadin shi haka yake baison abin jin dadi a rayuwan shi sai idan shi yaso.
Can sai gashi ya fito bai ko kalli inda muke ba har yakai kofa ya dan juyo yana fadin ku fito in sauke ku gida idan kun tashi.
D way yadda yai maganan umurni yake bamu kowan mu ta mike da sauri muna shirin tafiya merry mamaki ya kamata ta take fadin don may zaka kore min abokan nishadina kuma kai ba zama zakayi a gidan ba.
Bai kulata ba sai ficewa yayi daga gidan mukan har mun daga kowa na kokatin daukan jakkan shi nidai hannun fauziya na riko muka fito tana biye damu da tikeken cikin ta a baya tana fada dashi.
Yana cikin motar dake rufe lif a lokacin muka karaso wurin motar muka tsaya ya sauke glass din motar yana fadin kanwata zagayo ki shigo nan gaba wurina da cewan fauziya don ita yake kallo yana magana.
Ban san lokacin da bakina yace zamu iya karasawa gida ai ba nisa don islamiyan mu ma yana gaba da nan.
Shoutup ban tambaye ki ra,ayin ku ba yace da sauri na rufe bakina muka fada bayan motar da tsoro da mamakin shi ashe yana iyawa matar shi haka yadda nake ganin su a soye kullun.
Maimakon ya mike damu hanyar gida sai ya dauki hanyar da zai fitar damu daga unguwar gaba daya.
Kallon kallo muka fara yi kasa kasa na radawa Aisha da ido ina kuma zai tafi damu haka ?
Sai muryan shi mukaji yana fadin sayar daku zanyi kin san ni dan yankan kaine ai ko baki sani ba yace ba tare daya juyo ya kalle mu ba.
Sai ya ja tsuki yaci gaba da tukin motar shi shiru na wani dan lokaci yace idan ni ba kafiri bane aike da kika buge da rawa yanzu kin dauki hanyar zama kafiran sallon kuje gida ku fada kunyi rawa a gidana ace zata koya maku kafirci.
Duk wanda naji wanan maganan a bakin shi sai na bata maku rai dukan ku baku san halina ba ko ?
Kina wani boyewa a cikin wanan abin kullun ashe shedaniya ce ke ko bai fada ba nasan dani yake fada nidake cikin hijab din ya kama ina rawan shakiyanci.
Ya furzo da iska daga bakin shi ta yadda muke iya jin sa bai kara magana ba sai daya tsaya a bakin wani katafaren shago da akaiwa manyan haruffa rubutu.
Ina dan kallo wurin naji yacewa fauziya barin maku tsaraba kuje dashi gida ko yana kallonta tare da fadin wa yan nan yan shagalan sun kwaso ki sun barki zaune.
Ya fita ya zagayo ya budewa yarinyar nata bangaren ya rike mata hannun suka fara tafiya a nan ya barmu zaune tsuru tsuru a cikin motar.
Murja ta fara magana tace ashe gaskiyar fatima da ki kace bahagon mutum ne sosai gashi ko ya nuna muna yau din.
Ni wallahi da nasan yana nan da banyi rawa ba har ya zargemu wai muna karya da uztazanci a fili.
Shiru nayi ban iya furta komai ba sai lokacin da naji Aisha ta fadi hakan na dago kai daga kallon wajen da nakeyi nace bafa daku yake ba dani agolan gidan su yake kukan ai kannen sa ne bai maku fada .
Ba yazo ya samay ku da farko kuna rawan ba baiyi fadan ba sai Aisha tace ke kila fa don yaga yadda mumun ku da hjy su suke yasa yayi gudun fitina.
Muna nan ciki zaune sai ga wani yazo da uniform din wurin yana fadin wai ance ku fito ku shiga daga ciki yana fadi ya juya abin shi.
Bin mutumin nayi da kallo sai kuma na juyo nace ku shiga ni ba inda zanje Allah.
Kallona sukayi kawai kafin suce mukan zamu shiga mu dibi rabon mu suna fita zuciyana ta bani in bisu muga gudun shi.
Da sauri na samay su har sun tura kofan sun shiga nima nabisu yana rike da hannun fauziya yace kowa ta dauki duk abinda take so.
Tsayawa mukayi muna shawara a tsakanin mu kunga mu dauki biscuit da sweet kawai koda bibiyu ne kada yaga haukan mu ko muyi kauyanci nace enyyeh kawai.
Ban tsaya ko inaba danaga sun nufi sashen kayan zaki nikan na nufi sashen wasu kaya dana hango.
Dogayen riguna mai tsaron wurin yana ganina ya taso yana fadin hjy a tayaki dubawa ne nace eh kawai nan ya shiga zakalo dogayen riguna masu tsadan gaske har guda biyar.
Nace sun isa na nufi gurin turamay nace ya zaba min ya dauko masu tsada gaske ni dai ban hana ba guda hudu na zaba nace ya saka a basket din ya bini da kallon mamaki na fuske sosai.
Sai na koma wurin turare da man shafi ina dubawa nan ma mai tsaro yace bari na zaba maki daidai da jikin ki ya zabar min turare masu tsadan gaske da kamshi na juya kowa sai kallona yake yana mamaki.
Daga haka na nufi gurin mai lissafi nan na samay su harshi suna jirana Aisha da murja suna ganina ido waje sun bude baki suna kallona da mamaki na iso inda suke tsaye.


Please Login or Register in order to submit comment