You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da hakan kawu ya fadi lamarim mahaifiyar ku a yanzu sai addua don abin nata kara yawa yakeyi ko yaushe.
Kafin su fita suka aje magana kan za,a bincikeni yaushe ne zan koma don su sani a shiryawa tafiyan mu don sun amince na koma harda yaran gaba daya can har zuwa lokacin da zan kara sakewa .
Naji dadin wanan halarcin da sukai min din don dama yadda za a rabani da yarana nake ji dashi nake kwana nake tashi a raina.
Sai gashi abin yazo min da sauki sosai ba bata lokaci na shirya na koma London nida yarana inda za a dinga kulawa damu a karkshin oga mansur mijin Ramla.
Mun tafi mun bar hjy da tarin dukiyan da take fada a kanashi inda bata san can ma dan nata ya bar arzikin da bata taba tsamanin irin sa ba gareshi.
Don aikin yaya ba karamin samu sukeyi ba wanda yake harkan international samu yake kamar ba gobe a kullun.
Sosai na mayar da hankalina ga karatuna inda nake tare da maria sai manjo da na wuto da ita don kara debe min kewa.
Hakan baiwa hjy dadi a ranta ba sai jefa magana takeyi tana fadin wai rashin tsoron Allah yasa aka turani in koma don ansan abinda aka kitsa na koma na wawashe abinda aka bari a can tunda nan babu halin ci a gareni.
Itace tace nayi ta haihuwa kamar bera dama mun san abinda muka shirya a kanshi merry sawun barawo kawai ta taka.
Duk da ina samun kulawa a bagare daban daban daga yan uwa da abokan arziki na yaya umar hakan bai hanani kewan mijina ba muna tsaka ga exam din shiga matakin karshe na haifo dana mai kama da ubanshi sak wanan ba inda ya ragewa yaya umar shi wurin kama.
Tun fitowan shi na fara kiran shi da habibi da kuma wanan sunan oga mansur yayi mai huduba watau umar faruq.
Gida basu samu labarin haihuwana da wuri ba don nina hana a fada ba saboda komai ba sai don in dan samu natsuwa don hjy na iya tayar da fitinan in dawo tunda na haihu ayi suna a nan gida.
Ban damu da fadan kowa ba a yanzu idan ma har koyone na koyi halin boye sirina a wurin uban diyana.
Tunda labarin haihuwana yazo kunnen hjjy ta dan bada lokaci sai kuma ta matsa sai in dawo gida a raba gado tun tana boye hakan da farko tana fadin in kawo yaron dana haifa su gani har dai ta gaji ta fara fadin in zo asan inda kowa yake zaifi.
Kin dawowa nayi nace duk abinda sukayi daidai ne a gareni ba don komai naki dawowa ba sai don yarana da nake jin kishin kishin din za, a rabani dasu wai idan muka dawo gida haka yasa na share kowa nayi zama tare da yarana a can .
A haka na samu labarin wai hjy dai zaman yaki ta tare yanzu a gidan mu kuma tana amfani da babbar motar da yaya yake amfani dashi.
Duk wanan bai dameni in dai ina tare da yarana hankalina yana kwamce gasu da jikjn girma sunyi wani girma hausa ma ya fita bakin su.
Kodana kara karatuna na samu aiki a can ta hanyar oga mansur mutumin kirki da bai gazawa damu ga business da mukeyi nida mamu ina shiga kashe ina saro kaya in turo nan kano yaya Ahmed yana kula min da sana,a ta.
Bani nazo gida ba saida na share shekara biyar da watani a can koshi don ciwon Amma da aka buga min bata da lafiya na shigo.
Lokacin na kara bunkasa na zama wata wayyaya dani ko dole yanzu yaji shakkan takani kamar yadda ake min a baya.
Don a karskashin WHO nake aikina idona ya bude sosai bani daukan raini a gurin kowa a yanzu.
A bangaren merry kuwa tunda ta samu ta bar Nigeria a furgice bayan barin ta gidan lokacin da abin ya faru ta koma America a firgice tana nadaman abinda ta aikata din har labarin rasuwan yaya yazo mata gashi bata san inda yakai mata yarta ba ya rasu kuma.
Gashi taji labarin ana neman ta a Nigeria ido rufe kan zargin kisan mijin ta da tasa yan bundiga suka zo har gida sukai mai.
Wanan dalilin yasa ra boye kanta ga kowa bata yarda ta kara waiwayan yar nata ba ga rashin ya ga rashin mijin da tayi don bata san abin zai kai ga kisan shi ba.
Hakan ya jawo mata gaba da yan uwan mahaifiyar ta da suka bata shawaran ayi kidnaping din yaran sai ya fito mata da yarta a bashi yaran shi sai gashi plan din ya basheta.
Mun iso Nigeria mun samu Amma abin ba dadi don jikin ya matsa mata sosai tun rasuwan yaya data saka damuwa a ranta.
Muna da sati biyu da zuwa Allah ya karbi rayuwanta mukayi wani babban rashi tsohuwar arziki a cikin mu.
Duk da Amma tsohuwace saida wanan mutuwan nata ya taba kowa na halin don anji mutuwanta sosai a gidan.
Saida komai ya lafane sai ga yaya habbib ya tsiro da wani zance wai yana son a daura muna aure dashi ya maye min gurbin dan uwan shi.
Wani sabon tashin hankali kuma ke nan don hjy naji ta hau bakin ta da bala,i ga kuma matar kawu balarabe da ta fito da nata bala,in ina muka fito nida mamu.
SARKA MAI RIKICIN GANGAN ina wuta su sakani na dawo bauchi wurin gaisuwan umma da ta rasu na samu wanan fitinan kuma duk ina jin su ban samu ba kowa amsa ba.
Sai ji sukayi kawai na koma na bar kasan koshi da kyat kawu ya yarda na koma don shi ya amince da zancen yaya habbib din.
Har London yaya habbib ya biyoni da zancen na nuna mashi hakan ba zai yuyu ba saboda me ya tambaya nace ko ya manta da wace yake aure yar uwata ce ita.
Ko bayan hakana yasan zancen da ba zai taba yuyuwa garenu bane don hjyn shi bazan sake zama a karkashin ta ba har abada.
Wanan amsan dana bashi yasa shi har zuka wai idan hakane sai dai in bashi yaran su dama suna daga min kafane don haka tunda ban yarda ba zasu dauki yaran su yanzu .
Nan kuma na nuna mai bai isa ba muka rabu baram baram dashi babu dadi haka yasa na samu sa,ida ga lamarin su.
Iyakata nazo mu kwana biyu da yara mu koma ina kula da abina tunda Allah ya hore min abinyi yanzu ban damu da dukiyan yaran ba don da aka raba cewa hjy tayi saidai su su rike na yaran a wurun su har yara su girma.
Wanan shine labarina mai cike da rikici har mai rabawa yazo ya rabamu da yaya hjy bata barni na huta ba saida taga na fita zancen komai da yaya ya bari a duniya kafin ta dan sarara min.

Ina rokon duk wanda na batawa rai kan wanan littafin da ya yafe min sai mun sake haduwa a wani littafin kuma kurakuren mu Allah ya yafe muna baki daya.
Ina kara mika gidiya ga dinbin masoyana da so da kaunar da suke nuna min da hakkuri da halina banda abinda zance a kullun sai godiya a gare ku da fatan alheri.
Yau gashi sanadin rubuta novel rayuwana yakaini inda ban taba zato ba a sanadin ku na tsuci kaina a kasan Europe.
Masayona ku tayani yiwa wanan boyar Allah da a sanidiyarta Allah ya ingata rayuwana ku tayani yi mata godiya tare da addu,a ita da ahalin ta a baki na godewa kowa da kowa ina godiya a gareku har kullun masoyana ubangiji Allah ya rufawa kowa asiri a rayuwan shi Amin.
SARKA FADI KIRICE MAI RIKICIN GANGAN

Downloaded From https://tknovels.com.ng


Please Login or Register in order to submit comment