You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Downloaded From https://tknovels.com.ng 🎲🎲 TUDUN DAFAWA🎲🎲



Rubutawa...
Mummyn Fadyl (Fatima Muhammad Adamu)

Tallafi (Maryam Abdullahi gwaram)

*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION*
    *[onward together]*
*{we give the reader's of ours the best out of the bests,, our inks are melodious and dropping a kinda lights to reader's}*
```THE PEN OF LOVE😘 HEAT TORCHING❤ TEAR OF SORROWS😭 CURDLES😊 GIGGLES😁 AND MARRIEGE THINK💑```
*```JUST GIVE US FOLLOW..**


Bismillahirrahamanirrahim.!! Allahumma salli Ala sayyadina Muhammad, wa Ali Muhammad, kama sallaita wa rahimta wa barakta ala Ibrahim wa Ala Ali Ibrahim innaka hamidun majid.....
Assalamu Alaikum enai muku gaisuwa da fatan alkhairi...

Wannan shafin nakine my mentor

*Real mum Afrah*


Fitowa ta 0⃣1⃣



Kuka takeyi bilhaqqi tana fadin harsai yaushe  ne xamuy farin ciki MAMA harsai yaushe xaki daina jin tsoron UMMA LAMI? Harsai yaushe xamu samu TUDUN DAFAWA? Kukan da yaci qarfintane yasata tsagaitawa domin baxai barta takai qarshen zancen nata ba....... Shiru ne yaratsa tsakaninsu can sai Mama ta nisa  tace, baxan gaji da tunasar dake muhimmancin haquri ba akullum ina gaya miki, kiyi haquri! Kiyi haquri tabbas kobayan raina baxaki tabe ba, kuma zakiga ribarsa.

Taci gaba tana shafa bayanta tare  dacewa meye acikin duniyar nan diyata, idan pa mukayi haquri watarana xa'a wayi gari bama nan, itakanta Umman taku baxama xatai a duniya ba... Nafison inga kina farin ciki, ganin annuri a fuskan ki shike bani kwarin guiwa..

Share hawayenta tayi tana murmushin yaqe Wanda ake cewa yafi kuka ciwo, tace shknn Mama Allah yashige mana gaba... Qarar banko qofar da akayi ne tare da daga labule, ya sasu saurin dago kai su kalleta, cikin qaraji, isa dakuma daga murya tace ke wato Aiken da. Nai miki tun tuni xua kasuwa ki kiramin Bbn Ku Ashe bakije ba, kinzo kinzauna keda uwarki kuna kitsa munafurci ko?

To wlh ninan dakuka ganni LAMI QAYA (tafadi tana nuna kanta) nayi muku nisa kuna cin darajar Abu daya Dana jima da qarasa tarwatsa Dan farincikin da ya rage muku inga tafadin iyayi.,..... Kinbar kallo nane kosai na makeki da idanunki kamar ma dujjal....

Kitashi yanxu basai anjima ba kiwuce tajuya tai tsakar gida fuuuuuuuuuuu.... MAMA ce tai qarfin halin cewa NANA tashi kije ko Allah yamiki albarka, yanxu kidawo karki tsaya ahanya kinga lokacin islamiya takusa.

Fitowarta keda wuya xatai waje suka kusa bangajan juna itada AYASHE aminiyar Umma lami, gaisheta tayi amma taqi amsawa saima kallon banxa data bita dashi tayi ciki ita kuwa tayi waje...

Lami tana hangota ta yashere haqora tana fadin muyi cikin daki, suka shiga cikin murya qasa qasa Ayashe take cewa LAMI wnn maganin dana karbo miki sunansa tafaru taqare,, tajuya tana leqe leqe (alamar munafurci) snn taci gaba da fadin sai cikin dare xakiy wanka dashi amma kiraba kashi biyu dayan kuma kisawa MAL.HABU anashi ruwan wankan sauran bayanin xanji daga bakinki, Shewa sukayi suka tafa, Umma lami tace mata nagode Aminiya tah Allah yabarmu tare gobe xanxo xakijini.......

          Tafito daga dakin suna qara tattaunawa, Mama tana tsakar gida tana Alwalan sallan la'asar taga fitowar Ayashe,saida gabanta yafadi, zuciyarta ta tsinke, A'uxubillahi minal~shaidanirrajim shine abinda tafada, don kua tasan xuwan Ayashe gidan yawanci bayan tafiyar ta sharri ne ke biyowa baya, qaqalo murmushi tayi tare da fadin aaahhh Ayashe kece a gidan namu? ya yaran?  Mtswww Tsaki Ayashe taja tace mata kedai anyi jarababbiya me kutsa kai ba kwarjini, kiyta bin mu2m yana banxa dake amma kikasa haqura dashi? To nidae kurwata Kur! Tayi wucewarta..

Kallon Mamaki Mama tabita dashi a ranta tana cewa Allah yashiryeku nidai baxan Gaza gurin nema muku shiriya ba, ta tashi tai shigewarta daki ta tada sallah.......

Lami bayan ta dawo daga rakiyar Ayashe ne ta tunada Layar data karbo shekaran jiya dama abunda yahanata amfani dashi rashin samo wnn maganin wankanne amma 2nda ansamo shknn faduwa taxo dai dai da xama, murmushi naga tayi tare da fadin yanxukam nakusa inyasar da kwallon mangoro inhuta da Quda lallai Zynab qarshenki yazo a gidannan. Ta nutsu tanajin kara2n da dayar xuciyarta ke mata na gargadinta karfa kimanta Lami Zynab tamiki dukkan halacci itace silar xuciyanki gidannan ta aminta dake har kika auri mijinta Anya ta cancanci haka daga gareki bayan kin rabata da farin ciki ta wato mijinta? Shin zaki iya 2na rabon Mal.Habu da shiga dakin ta? Shin zaki iya 2na rabonda Yayiwa NANA kallon diyarsa ta cikinsa? Anya Lami son kannaki baiyi yawa ba?

Amma inaaaaa sheidan yariga da yagama buga mata ganga gurin ganin tacimma burinta naganin tazauna ita kadae da yaranta guda biyu kuma Agola a gidan Mal.Habu.

Tafiyarta takeyi cikin Nutsuwa kanta yana qasa tana ta 2nanin rayuwarsu itada MAmanta basuda 'yanci ko kadan Mama kamar ba zaman Aure takeyi ba, ita kuma kamar ba gidan Ubanta ba, baxata iya cewa ga iya shekarun da ake deba rabonta dataga  dariyar mahaifinta agurinsu ba, don indai kaganshi da fara'a ko kuma yana dariya, to fa yana tare da UMMA Lami ne,..

Sau da dama kuma zaka ganshi a zaune shikadae yanata qunci ko kuma yayi shiru yana 2nane~2nane komenene hakan??

Kubiyoni muje.

Sainaji comments daga gareku.

😍😍🤝🏼Anatare
(Mummyn fadil) CE.






🎲🎲 TUDUN DAFAWA🎲🎲


Rubutawa.....
Mummyn fadyl (Fatyma Muhammad Adamu.)

Tallafin Maryam Abdullahi (gwaram)


*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION*
*[onward together]*
*{we give the reader's of ours the best out of the bests,, our inks are melodious and dropping a kinda lights to reader's}*
```THE PEN OF LOVE😘 HEAT TORCHING❤ TEAR OF SORROWS😭 CURDLES😊 GIGGLES😁 AND MARRIEGE THINK💑```
*```JUST GIVE US FOLLOW..**

Wani abun sai Ikon Allah kenan Metsaga ido ba zafi...

JINJINA GA MASU BIN NOVEL DINA I heart u all😉......

Fitowa ta 0⃣2⃣



MU WAIWAYA SHEKARUN BAYA DASUKA SHUDE

Shin menene sanadin wadan nan abubuwan dasuke faruwa?


Asalin Mal.Habu mutumin Jahar katsina a qaramar hukumar jibiya, a unguwar bakin kuka, Mahaifin shi Mal.jafaru yakasance Dan kasuwa ne da yake saida kayan masarufi cikin rufin asirin Allah, yanada matarsa daya mai suna Marka, mata me mutunci dakuma karamci, yanada yara uku, nafarko Amina Wanda yanzu take unguwar qoqi da aure tareda yaranta biyar, sai mai bi mata, mal. Habu saikuma autarsu Habiba ita kua tana zaune a unguwar Dando, da yaranta shida......

Mal.Habu yakasance shikadae namiji agurin iyayensa hakan yasa mahaifinshi yadaura duk wata Buri akansa, hakan yasa tun yana qarami yake tusashi gaba suke xuwa kasuwa tare......

Mal.Dahiru maqoci ne ga Mal. Jafaru, kuma shine mahaifin zynab, yanada matanshi guda biyu, Zuwaira dakuma Hafsat..

Mal.Dahiru shekarasa Goma sha biyar da aure tareda Hafsat mahaifiyar zynab amma ubangiji bai Axurtasu da samun haihuwa ba, hakan yasa aka matsanta mishi akan ya qara aure, yaso ya bijire saboda shibaiga naqasu atareda matarsa hafsat ba,saboda tana mishi biyayya iyaka gwargwadon iyawarta takuma son farin cikinsa, amma iyayensa suka matsanta masa, tareda yanke hukuncin hadashi aure da 'yar gidan Innan sa Zuwairah.....


Bayan tarewar Zuwairah a gidan abubuwa da dama sun faru marasa dadi saboda zuwaira batada kirki da kawaeci don kua gani take Mal.Dahiru Hafsat ta mallakeshi duba da yanda yake qaunarta.

Hakanne yabata damar wulaqanta ta son ranta dakuma hadata fada da surakanan ta tahanyar sharri dasauransu....

Ana cikin haka kwatsam Allah yabawa Hafsa ciki😊fari. Cikin Mal.Dahiru baxai misaltu ba, zokuga tashin hankali gurin Zuwairah..... Tayi yawon gun bokayen harta gaji amma dayake zakaranda Allah yanufa da cara ko ana muzuru ana shaho sai yayi......

Watarana Hafsat ta tashi da ciwon naquda ba'a dadeba Allah yasauketa lpy, inda ta sunkuto diyarta mace, saidae ko kallon fiskar Diyar batayiba sakamakon yankowar jini a take rai yayi halinsa,😭😭.

Allah sarki Mal.Dahiru yaga gigicewa tamkar zautacce haka yakoma, duk mugunta irinna Zuwairah saida ta koka, aka dauki jaririya aka wanketa Snn aka shirya Hafsat xua makwancinta na gaxkiya.......

Ranar suna aka radawa yarinya suna ZAINAB, ba ai wani taro ba saboda jimamin halinda ake ciki, cikin kirsa Zuwaira ta karbi riqon jaririyar, India ake shayarda ita dan yen Nonon Shanun ingantacce, yarin yarda ta taso cikin gatan mahaifinta dakuma qunqatatawar kishiyar uwa, sakamakon ganinda takeyi tamkar Mal.Dahiru ninka soyayya yayi xuwa ga diyartashi..

Alokacinda Zainab takeda shekara sha takwas a duniya lokacin shikuma Habu yanada shekara Ashirin da Tara, Sakamakon Amintar dake tsakanin maqotan nan guda biyu yasa suka yanke shawarar hada yaransu Aure, Bawanda yayi musu akan wann hukuncin.... Kasancewarsu dukan biyun masu biyayya ne.....


Mama da Mal.Habu bayan tarewarsu a unguwar Bachaka, shaquwace me qarfi tashiga tsakaaninsu tareda Amincewa da juna, Mama tanada kyawawan halayenda kowani namiji yasameta baxaiyi tirr da itaba, Mal.Habu shima yana iya bakin qoqarinsa gurin ganin ya kyautata mata....
Tun tarewarsu a unguwar maqociyarci ta shigo domin su gaisa, asan juna, shigowarta Yayi dai~dai da shigowar Mal.Habu... Barka da shigowa Mallam shine abinda mama tafada Barka da gida zainabu, a ah baquwa mukayi ne? Mama ta tambaya, Bayan ta kalli matar tana mamakin ta don't daga gani tasan kan bariki, qarewa ko ina kallo takeyi kapin ta saki malalacin murmushi snn tace, eh wlh kuna lpy? Mama tace haba dai a tsatstsaye aikya xauna ga guri, tamiqa mata kujera. Samun guri tayi ta zauna suka qara gaisawa, nan take gaya mata ita maqociyarsu suce kuma sunanta Lami, kapin Mama ta amsa mata, Mal.Habu yakirata, ta tashi tashiga daki, nuna mata kayanda yasayo mata daga kasuwa yayi, tayi murna matuqa tareda code mishi, kayan marmarin ta debo takawo wa Lami, tanata wutsil wutsil da ido alamar. Miyon ta ya tsinke😜...

Kekuwa Zainab inajin labarinki a unguwar nan da irin kirkin mijinki da kuma hidimarda yake miki, Allah yajiqan Hashimu (mijinta daya rasu) tafashe da kukan munafurci, Mama CE ta hau aikin rarrashinta tareda bata baki har tasamu tayi shiru....


Tundaga wnn ranar yakasance LAMI tana shigowa Mama akai akai zumunci me qarfi ne yashiga tsakaninsu, inda Mama take riqe da ita zuciya daya itakua Lami a gurinta abun bahaka yakebaa, don kua Ahalinda take ciki tagama kwadaitua da auren Mal.Habu.....

Lami hatsabibiyace tanada yara biyu Isa dakuma Sadiya,Wanda mijinta yarasu yabarta dasu, Sam Isah halayyar mahaifiyarshi bata burgeshi,sabanin Sadiya wacce halayyarta daya da Lami Wanda akafi sani da LAMI QAYA SOKI UBANKOWA...


Lami CE durqushe gaban bokanta Wanda Aminiyarta CE Ayashe tahadata dashi me suna Boka MAYE megani har hanji take sanar mishi* nipa matsalata yanxu baiwuce inganni a gidan Mal.Habu ba, Lami nagaya miki wnn abun dakamar wahala matsawar bawai kin kawo adadin kudadennan ba ,saboda dashi xa'a sayi kayan aikin da xa'a rabawa aljanu.,, Snn abunda Nagani jiya bayan tafiyarki shine Zainabu pa tanada ciki 😳😳😳😳. Gwalalo ido Lami tayi tareda fasa wani uban qara tace ciki tunkapin ni inyi? ( kujifa kamar matarsa)🤔

To Yanxu yaxa'ayi don Allah ka fara zubar da cikin xannemo kudin wancan aikin ma,bakin zaninta takunce taciro kudade tamiqa mishi... Shikuma yamiqo mata qullin magani yace taxuba mata a abun shaa.. Snn yadaka mata tsawa!! tashi kificemin da gani, ga Aljani HASBABU ya iso..

Tashi tayi aguje tanufi hanya tana waige waige harta isa gida, cikin tashin hankali tahada wuta a murhu tadaura ruwan dumi nan danan ta dama kunu taxuba garin maganin aciki tanufi gidan MAMA.......

KUBIYONI MUJE


😍😍😍🤝🏼Anatare
(Mummyn Fadyl) CE

Wattpad@fatimamuhammadadamu



🎲🎲TUDUN DAFAWA🎲🎲

Rubutawa....Mummyn Fadyl (Fatima Muhammad Adamu).

Edited by Real mom Afrah.


*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION*
*[onward together]*
*{we give the reader's of ours the best out of the bests,, our inks are melodious and dropping a kinda lights to reader's}*
```THE PEN OF LOVE😘 HEAT TORCHING❤ TEAR OF SORROWS😭 CURDLES😊 GIGGLES😁 AND MARRIEGE THINK💑```
*```JUST GIVE US FOLLOW..**

Kwarin guiwar Ku shike qaramin kuzari da kuma qara riqon alqalamina dai2 har abada baxan manta da karamcinku gareni ba.
INTELIGENT WRITER'S ASSOCIATION,

JATTKO NOVELS,
KUNDIN QADDARA FANS,
YOUNG MOTHERS,
GWANAYE
'YAN UWAN JUNA
GROUP OF NOVELS

dasauran da ban ambata ba, u really mean alot to me....




Uhmmm Sannu sannu kwana nesa Tsayuwa kishiyar Tafiya......


Fitowa ta 0⃣3⃣


..,......Shigan ta gidan tasamu Mama tanata Amai gaba daya ta galabaita, gashi babu komai a cikinta saboda haka yunqurin aman yake bata wahala, Lami CE tai saurin isa gareta ta taimaka mata da ruwa da wanke bakinta snn ta taimaka mata suka xauna akan tabarma, Sannu Zainab, yauwwa Lami kece tafe da ranannan? Wlh ingayamiki nadan dama kunu ne gashinan bayawa nace bari inxubo miki nasanki nason kunu, Murmushin jindadi Mama tayi snn tace Allah sarki kamar kinsani kuwa wlh daxu nagama rayawa a raina nake fadin Idan naji qarfin jikina xanbada surfen gero sai indama insha don shikadae ke xama acikina, Tabe baki Lami tayi snn tace Wai ko Zainabu anya baciki ne gareki ba?

Uhummm kawai Mama tace mata, Lami tace gaxkiya namiki murna sosae, Allah ya raba lpy, Amin tace Tana me kai kopin kunun bakinta, Juya kai Lami tayi gefe tana murmushin cin nasara kapin daga bisani tace mata xankoma gida Sadiya takusa dawowa daga makaranta.... Godiya sosae mama tayi mata.


Shigan ta gida tasamu Sadiya ta dawo daga makaranta tanata hura hanci don Sadiya a rayuwarta babu abunda ta tsana irin talaucin da suke fama dashi shiyasa Rayuwar ke garata, saboda Sadiya akwae Kwadayi.

Umma Badai kunu kike nupin xansha Amatsayin abincin Rana ba? Tambayar da tayiwa uwar knn kai tsaye batareda shayi ko ganin matsayi ba., Kiyi haquri kisha Sadiya karki damu burinmu yakusa cika Kin kusa kifara sa kaya irin wadanda kike so, kinkusa fara cin Abunda ranki yakeso, amma pa karki manta saikin bani hadin kai!

Jin Abunda mahaifiyarta ke fada yasata sakin fuska tareda fuskantar uwar dakyau snn tace Umma wlh kome kikeso inyi zanyi matuqar xamu samu kanmu cikin jin dadin rayuwa....

Sadiya 'yar shekara sha biyar da haihuwa Amma tapi mace 'yar shekara Hamsin iya duniyanci saboda tun tashinta ta farka akan halayyar uwar ta harma tafi uwar Buri ( Nace Dan nagada ai yafi Dan nakoya). Lami tazayyanewa Sadiya gaba daya Ra'ayinta akan Mal.Habu itakuwa tayi na'am tareda marawa uwar tata baya, snn tace wlh Umma kamar kinsan Abunda najima ina hararowa Saboda kullum nashiga tayata aiki kokuma takirani xata aikeni saina samu tanacin abun dadi, rannan Dana je bawa Almajiri sharanta ya xubar wlh Umma saikin ga takaddun Nama aciki (tahadiye wani jarababben yawu) hummm ki kwantar da hankalinki munkusa samun kanmu aciki,...... Yanxu matsalata bai wuce yanda zamu samu wadannan kudaden ba, sunyi yawa dubu Talatin pa MAYE yace inkai..

😳. Zare idanu Sadiya tayi tareda maimaitawa cikin dafe qirji tace Talatin Umma? To meye tafada mata da tsawa cikin gwasalewa snn tace mata, talle xaki fara na Goro amma pa kisani ba goron kadai xakina kaiwa tasha ba, inaso kiyi amfani da basirar da Allah yabaki kijanyo hankalin maza akanki, nafiso cikin qanqanin lokaci muhada kan wadannan kudaden mukai wa MAYE.

Umma iskanci kike nupin xanfara? Mtswwwww to sai me akanki aka fara kuma bawae ina nupin bude mishi qafafu bane shashshafaki kawae zaiyi nasan dabaran da xanmiki, yanxu dae kitashi kije gidan Baffanki a unguwar Kuka kice mishi bamuda Abunda xamuci yatai maka mana, inyaso Abunda yabamu musayi goron dashi, Sadiya tunzura baki tayi gaba kapin tafara qoqarin mikewa Sadiya menene kikeyi haka da fuska kamar kinci kashi , naga alama haka xakiymin da tallen to ubanwa xai saya kin hade fuska kamar Tunku, Wucemin da gani inji da Abunda yake damuna, qunquni tafara sannan tawuce a gidan tanupi gidan baffanta ..

Assalamu'alaikum! Wa'alaikissalam Asabe tafada matar Baffa Sunusi Yaya ga marigayi, ina wuni, lpy qalau Halima ya Umman taki? Lafiyarta qalau, baffa yananan ? Eh yananan yashiga kewaye kijirashi, Sadiya manya angirma ya kara2? Karatu Alhmdllh, Halimatussadiya kece tafe da ranar nan? Baffa anwuni lpy? Lafiya qalau ya wajennaku? Lafiya tayi shiru tana saqe saqe aranta can ta nisa tace, Baffa dama nazone kataimaka mana da abinci bamuda komai kuma gashi dama maganar kudin makaranta Umma ta ranta tayi agurin Umma Ayashe tabiyamin, kuma yanxu tana buqatar kudinta tayi shiru tana matsan kwalla harda sheshsheqa hahhahh gado ba karambani ba.
Ya isa yi shiru Sadiya daina kukannan haka, yafadi yana lalubar cikin aljihunsa, itako tanata wulli wulli da idanu taga nawa zai zaro,, Naira dubu hudu ya qirga snn yacewa Asabe ta auna mata Masara, shinkafa da kuma wake, godiya tamishi, ya Amsa mata tareda cewa kigaida Umman taki, kice mata indai nasamu sarari zanzo mugaisa abubuwanne sunyi yawa. Yamiqe yafita, Asabe ta tashi ta aiwatar da umarnin mijinta snn tace ta tashi takirawo almajiri yatayata, qofar gida taleqa tasamu almajiri, yadauka mata kayan tayi bankwana wa Asabe, ta rankaya xuwa gida.....



Bayan Fitar LAMI Mama hankalinta kwance take shan kunun ta, bayan tagama ne tadan kishingida nan da nan bacci yayi awon gaba da ita, bata samu ta farka ba, sai bayan la'asar sakaliya, tayi mamakin wnn bacci nata me tsawo, miqewa tayi ta dauro alwala ta Tattare tsakar gidan snn tashiga ciki ta tada Sallah...

Bayan ta idar tafito tafara kiciniyar hura wuta domin yin abincin dare, shinkafar Tuwo tadauko tafara gyarawa, jitayi kamar ana kiran Sunanta a hankali ta waiga bataga kowa ba, bata daina jiba, a qofar dakinta ta hango mage ta zura ma idanu, miqewa tayi danupin shigewa cikin madafi, amma damqan da mararta tayi mata ita tahanata, Wash Allah tafadi tareda durqushewa a gurin tagabanta wnn magen tazo snn ta karkada mata Bindi tawuce, jinin da ta gani yafara bin cinyoyinta ne yadaga mata hankali fiyeda ciwonda takeji,,, Anan gurin tafadi ta Sume.


Innalillahi wa inna ilaihirraju'un. Abunda ya iya fada kenan yaxubar da ledojin hanunsa yanufota a guje amma tsabar rudewa yarasa mexaiyi guda daya, can dabara tafado mishi yayi gidan Lami A qofar gida yahadu da Sadiya Wanda dawowarta kenan daga gidan Baffanta yace mata Sadiya yimin magana da mahaifiyarki yi sauri, ciki tayi aguje tana fadin UMMA UMMA fitowa tayi zani na faduwa a jikinta da kopin kunu n da takesha a hanunta bakinnan dumu dumu da kunu, tana menene Sadiya? Mal.Babu yana qofar gida yanai miki magana, fita takeda niyyar yi tsabar zumudi tama manta dawani Abu sunanshi mayafi 😉 Sadiya ce tai saurin shan gabanta tareda cewa Umma ga mayafinki, snn ta karba tayafa a kafada Rabi yanajan qasa tsabar zumudi kana ganinta kasan babu nutsuwa a tareda ita,....

Tana fitowa yace mata kitaimakamin don Allah Zainabu tana gida Babu alamar numfashi atare da ita farinciki ne marar misaltuwa ya wanzu tareda mamaye zuciyar Lami amma a fili saicewa tayi Inalillahi muje, suna Shiva ciki taganta male male cikin jin taji dadin haka don tagama sadakarwa Zainabu tabar duniya, lallai abunma yazomin dasauqi me kikace batasan a fili tafada ba amma dayake tasan kan duniya sai ta wayance tace, Cewa nayi tana numfashi abun yazo dasuqi, yanxu kayi sauri kasamo mota mukaita asibiti, To yafada tareda miqewa yatafi duk yabi yafita a hayyacinsa, ita ko LAMI sai yau taqare wa Mal.Habu kallo tabbas shine irin namijin da takeso ga kyau ga cikar zati, kana ganinshi kasan jarumine nagaxke, hummmm gaxkiya zata more tafada a ranta. (Lami badai jaraba ba😜)


Shiga cikin daki tayi domin daukowa zainab kayan da zata kintsata a ciki kapin yadawo amma hakan gagaranta yayi sakamakon shagaltuwa da kallon dakin datayi Sam dakinsu baida makusa komai a tsare yake, nan take kishi da kuma tsanar zainabun yaqara darsuwa a ranta, harta dau zani akan sallaya zata fito idonta yayi tozali da wani gasashshen nama akan filet nanfa ta durqusa tahau ci hanu haka hanu kwarya tamkat mayunwaciya, Sallamar da tajine yasata hadiye qaton lomar da yake bakinta jikake Muqut saida ta runtse idanu cikin firgicin Azaba, taiyo waje kamar anjehota....

Mal.Habu yace mata game motan Nazo, dashi to tace snn tagyarawa Zainab jiki nanma saida taji rabta yabaci don kua jikin xainab badai laushi ba harwani sulbi yakeyi, dakyar tagama shiryata zuciyarta namata quna da tuquqin bakin ciki, suka sungumeta suka sata a mota sai asibiti.


Da isarsu likitoci aka karbeta domin bata taimakon gaggawa san samu da taimakon Allah jinin yatsaya amma cikin jikinta babu shi ya bare, amma Abunda yake qara dagula mata lissafi baiwuce munanan mafarkan da takeyi da kuma razana datakeyi cikin bacci ba....
Kwanansu biyar a asibitin aka sallamesu suka dawo gida, Lami CE tabata Sadiya domin tadinga tayata ayyuka, Mama duk tadauka tsabar qaunace tahaduwar jini... Tun dawowarsu Mal.Habu yakasa gane kan Zainab saboda da rana tana walwala da kuma kwanciyar hankali amma dazaran sunxo kwanciya to paaa nanne tashin hankalin yake don kua tadinga ganin wnn magen tana mata kuka kala kala qarshe tanufota a guje tamkar zata hayo kanta watarana tasuma watarana kuma tafita da gudu yakamota......... Ya yanke shawaran xuwa yasanar da iyayensu halinda suke ciki...


Gidan Lami kuma a ranar suka sayo goro da kayan kwalliya aka hadawa Sadiya na zuwa talla, Umma to yanxu yaxanyi idan saurayin yace saiya taba jikina, Uhmmmmm yaro yarone inama ana Ciro zuciya, yau da naciro na dasa miki a qirjinki kinfita dashi Sadiya na. Idan namiji yatare ki yace kawo goro bafa tsayuwa zakimai akai qerere ba, kidan durqusa ki banqaro qirjinki tasigan Jan rai, kice ranka ya Dade na nawa kina fari da ido, idan Dan hannu ne xai gane, idan bai ganeba kice mishi na hutasheka da kudinka ga wannan kaci, kimiqa mishi idan yazo karbo kidan riqe yatsunshi na tsakon daqiqa biyu (duk abunnan dasukeyi tanafa gwada mata da kanta). Idan yanemi Ku kebe kice mishi da wuri haka, banshirya ba mubari sai gobe kai dai katanadi guri dakuma kudi, ta tashi tadauko tsumman data tanada tadauko manja tadan shafa mishi dakuma Jar qasan data kwaba, duka ta shafa snn tace sa ajikinki kapin kisa wando, snn taqara dace mata karki kuskura yafara shafaki batareda ya baki kudi kin damqe ba, kuma banason kina karban qasa da dubu biyar, idan yanemi shiganki kice mishi jini kikeyi, baxaiyiwu ba sai xuwa wani lokacin,amma pa ki bararraje dakyau maza saida dabara, karki kuskura ki sakankance saboda dadi,😜 (tasan Harkan ai itakam)


A qarshe race mata ta tashi ta gwada mata Abunda ta koya mata, hakan kuwa ta aikata tareda taimakon hudubar uwarta. Bayan sungama tagyara mata kwalliyarta tsab......


Suka fito waje tana baxa mata kirari da qarin hudubar tsiya... Ahaka tana karkada jiki tanupi tasha..........








(Baxan iya rantsewa ba amma inada tabbacin baxa'a rasa iyayenda suke bada kashi saba'in na gudumawar lalacewar yaransu, uwace take kwatantawa diyarta yanda zatai dabarun karban kudi ta hanyar saida darajarta a kkyauta, Allah ya DAFA mana aka. Tarbiyar yaranmu)..... amin




Muje xuwa mugani idan tusa zata hura wuta.



😍😍Anatare.......
(Mummyn Fadyl) CE



🎲🎲TUDUN DAFAWA🎲🎲



Rubutawa.......MUMMYN FADYL (Fatyma Muhammad Adamu)..


*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION*
*[onward together]*
*{we give the reader's of ours the best out of the bests,, our inks are melodious and dropping a kinda lights to reader's}*
```THE PEN OF LOVE😘 HEAT TORCHING❤ TEAR OF SORROWS😭 CURDLES😊 GIGGLES😁 AND MARRIEGE THINK💑```
*```JUST GIVE US FOLLOW..**


Tabbas Allah buwayi ne kuma gagara misali, mai kuma. zartar da hukunci ba tare da sauraron ra'ayoyi ko kuma shawarwarin bayinsa ba.......



Fitowa ta. 0⃣4⃣





!! Tafiya take tana rangaji tare da girgiza Nonuwanta balaifi Sadiya tanada halitta me kyau, bugu da qari tanada saurin girma idan kaganta baxaka bata shekaru kadan ba, ita kanta tagaji da tafiyar nan domin wahala yake bata, amma yazatayi kwadayin zuciyarta ya rinjayi duk wani wahala data fuskanta dakuma qalubalen da take shirin shiga, saboda gaxkiya itafa tana tsoron maza, baxata manta ba qawarta Maimuna tabata labarin abunda yafaru bayan takwana a dakin saurayin ta, saida tayi jinya, hummmmmm ta sauke wani nannauyan ajiyan zuciya, da irin wadannan tunane tunanen har ta isa bakin tasha, Tarasa ma ta ina zata fara...

Wasu samari ne suka fara hangota nanfa dayan ya zunguri dan uwansa tare da cewa kai Bello kaga wata Kaya a can kua, Wanda aka kira da Bello yajuyo ya zurawa Sadiya idanu ba tare da ko kiftawa ba, don shi yanason harka da yara,, Daga murya yayi tare da cewa 'Me goro' Sadiya tanajin ankirata tai banzà dasu saboda a hudubar uwarta akwae Jan Aji... Saida suka kirata sau kusan hudu snn ta juyo ba tare da tayi niyyar nufan wurinsu ba....

Saida suka yanke shawarar miqewa su isa gurinta duk da Sadiya tanata

Please Login or Register in order to submit comment