You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

saidai ta sirranta cewar gurin manemin mata aka kaita tadai nuna mishi cewar ita Ayashe takaita domin ayi iskanci da ita, Amma Allah ya kubutar da ita a sanadin Alhaji, domin wnn al'amarin sirrin su ne na cikin gida.


Hakan kuwa datayi baqaramin dadi yayiwa wannan ahalin ba, tare kuma daqara mata girma da daraja a idanunsu, harma dai Alhaji Wanda idanunshi kawai yatsareta dashi Wanda babu komai sai zallar qaunarta dakuma taisayinta a cikin su.


Mal.Habu yayi kuka tareda yin Allah ya isa wa Lami da Ayashe na ruguxa mishi xuri'a dasukayi, don acan qasan xuciyarshi bayajin xai iya yafemusu cutar dashi dasukayi, har abada kuwa.


Sunjima a falon suna jajanta abun tareda girmama izza ta ubangiji yanda ya qaddaro haduwar Nana da mahaifinta batare da ansha wahalar komai ba, lallai ba shakka Allah buwayi ne gagara misali.

Shikanshi Dan uwannasa yayi mamaki sosai sannan yakuma iwa Dan uwanshi murna nashigowa farin ciki kashi na daya.


Bbn Nana ne yaqara jawabinsa dacewa, Babu abunda xance daku abisa halaccin da kukai mini, domin kudin halaccinku a gareni fadinshi a fatar baki ba abune mai yiwuwa bane, fatana ubangiji yayi muku mafificin sakayya abisa riqemin yarinya dakukayi da Amana, badon sanadinku ba dabansan wani hali yanxu diyata take ciki ba, yaqarashe maganarsa acikin karyewan murya.


Babu komai ai yiwa Kaine, mai aikinsu ce tashigo dauke da muhsin takaishi ga mahaifiyarshi, itakuwa miqashi tayi gurin mahaifinta snn tace Baba ga yarona cikin jin kunya, Masha Allah shine abunda yayita nanatawa yana kallon Dan yakuma dafa kanshi tareda yimishi addu'oi.


Can Alhaji yacemishi ya shirya gobe da sassafe karyaci komai xa'aje asibiti, godiya yayi har babu iyakanta, ahaka taron ya watse Nana itada mahaifinta jisukeyi tamkar acikin mafarkin irin wannan ranar ta iskosu.



Zarah CE xaune a falo itada IBBY said hiransu sukeyi, tamkar yau ne suka fara sanin junansu, magana suke tayi akan shirye shiryen bikinsu, dhidai biye mata kawai yakeyi tareda nuna mata duk tsarinda yayi mata shima yayi mishi.


Mummy ce takatse musu hiran ta hangar cewa to Romeo and Juliet dare yayi a tashi aje akwanta, sai kuma gobe a Dora daga inda aka tsaya, IBBY ne yafara miqewa cikin Sosa qeya yayi hanyar waje, zarah ce tafara binshi mummy tace xaki bishi Ku kwana tare ne? Dariya tayi tadawo da gudu tayi dakinta.
Kakkashe wutan falon mummy tayi snn taje takwanta.



&&&&&&&&&&&&&&
Ayashe ce kwance da daddare tana kwance akan makeken gadonta, baccin ta take shararawa hankalinta kwance, amma can tafara juye juye kamar wacce ake qoqarin shaqewa.


Zainabu ce take tsugune a gabanta tana kuka tana roqonta ta taimaka mata, tasan xata iya fiddata acikin quncin da take ciki, amma tajuya baya tanuna baxata taimaka mata ba, hakan yasa zainabun fusata ta fincikota cikin hauka, tareda shaqe mata wuya tana cewa xaki taimakeni ne inkoma gurin 'ya'yana da mijina kokuma saina kasheki?


Aiko nan tafara kakari tana cewa xan taimakeki, xan taimakeki karki kasheni na tuba, batasan a fili take maganar ba, jin ana tabata ne yasata farkawa a firgice ta qanqamo 'yar dakinnata Wanda ihunta ne a tasota daga nata dakin.


Ruwa, ruwa ruwa taketa ambata aiko 'yar budurwan cikin Sauri tanufi Fridge dinda ke dakin, tamiqo mata goran ruwa, bata jira ta karbi cup din bama ta balle murfin Goran ta Dora abakinta, sai Goran ta yasar.


Kasa maida baccinta tayi maimakon tayi addu'a kokuma tamiqe tayi nafila? Ah ah tashi tayi tahau zarya acikin dakin tasaqa wannan ta war ware wancan.


Gari yana fara haske ta afka bayan gida ta watso ruwa tafito ta shirya a gurguje, batareda ta jira direbanta ba tafigi mota sai cikin daji gurin bokanta, tafiyarda ya kwasheta tsawon Awanni.


A gajiye ta isa cikin dajin, amma dai tayi farin ciki don tasamu ganinsa, nan ta xayyane masa abunda taji na game da mafarkin da tayi a Daren jiya.


Dariya yayi me isarsa snn can ya tsuke fuskarsa yace mata wnn aikin maye ne, shiyayi shi damacan yataba batamin aikina to faduwa yaxo dai dai da xama, yanxu xan fanshe abunda yayi min shekara da shekaru hhhahahahahhahahahahahha nan ya barke da mahaukacin dariya snn.................



😍😍🤝🏼Anatare
Mummyn Fadyl CE




🎲🎲TUDUN DAFAWA🎲🎲


Rubutawa....MUMMYN FADYL (Fatyma Muhammad Adamu)

Wattpad @ *fatimamuhammadadamu*


INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION*
*[onward together]*
*{we give the reader's of ours the best out of the bests,, our inks are melodious and dropping a kinda lights to reader's}*
```THE PEN OF LOVE😘 HEAT TORCHING❤ TEAR OF SORROWS😭 CURDLES😊 GIGGLES😁 AND MARRIEGE THINK💑```
*```JUST GIVE US FOLLOW..**

*OH ni madoyana ina xan saku inji dadi ne? Gaba daya qaunarku gareni har nakan rasa yanda xan misalta muku yanda nakejin dadin sa, da ace zan samu ganinku daya bayan daya, to bashakka xanmuku kyautar koda pure water daddaya ne* 😜😜 _kuymin afua I luv u Lodi Lodi_



Fitowa ta. 5⃣5⃣


Nan ya barke da mahaukacin dariya snn a take yafara surkullen sa, aiko saigashi Maye ya bayyana a gabansa, cikin qarfin shaidancin tsafinsa. Yana wuwwulla jiki, shiko bai tsagaita ba yacigaba da surkullensa.


Abunda xai baka mamaki shine Ayashe tsabar ta shahara a shedanci tana zaune a gurin komai yake wakana amma ko gexau batayi ba, balle kaga alamar tsoro a gareta. Itadai burinta baiwuce taga Yaya xasu qarke abun nasu ba.


Bokan Ayashe yadauki tsawon Samada kimanin Rabin awa yana ganawa Maye azaba iri daban daban a qarshe ya kwantar dashi a qasa tareda bashi umarnin gaggawa akan yakwance duk wani aiki dayasan yayi shi tundaga fara bokantakar sa har ixuwa yanxu.


Maye ko kamar ruwa ta cishi a gurin haka yakoma, atake cikin magagin azaba, yafara kwance duk wani sihirin dayasan haqaullashi, yana gamawa Yakuma sanar dashi cewa yakarya duk wani qarfi nashi, a halin da ake ciki yanxu dashi da banxa duk dayane, daga qarshe ya sallameshi tareda bushewa da dariya yakalli Ayashe.


Kikoma gida xata barki haka, tunda kinnema mata lpy, amma kisani a binciken danayi yanunamin cewa a dliilin matar nan xakiga hukunci kala kala, dakuma musgunawar rayuwa koba yanxu ba.


A razane ta dago ta kalleshi tareda cemishi cikin firgici, Yanxu wani taimako xaka iya yimini akan wannan al'amarin, kawar da kamshi gefe yayi yace mata babu abunda xanfada miki bayan Wanda na Sanar dake, domin iyakan abunda Nagano knn, ankuma jaddada min idan nacigaba da bincike xai iya zamowa Matsala a gareni dakuma aikina, kinsan dai akanki baxanso komai nawa ya lalace ba ko?


Don haka kitashi kikai kudin aikin ki inda kika saba ajiyewa kibar gurinnan domin inada baqin gaggawa inason ganawa dasu, aiko cikin sauri ta ciro 'yan kudaden taje gaban wani tulu taxubasu ciki snn tafita, kamar ana hankadata haka taita tafiya harta isa gurin motar ta.


Acikin motar haka ta xauna tareda kifa kanta akan sitiyari tanata faman tunani, lallai zama bai kamani ba dole xantafi nijar domin nafahimci wnn baigama Sanin kan sihirin ba, dama har akwai abunda xai gagareshi, mtswww ta danna wata tsuka can kuma ta hade rai tareda cewa lallai zainabu nixaki nemi ki wulaqanta?


Bayan taimakon da naimiki na fitar dake daga hauka, to xanyi maganinki ai idanna rabaki da duniyar gabaki dayanta kowa ma yahuta ko? Nan tasaki murmushin mugunta, tai wa motar ta key tafara tafiya tareda ji ajikinta cewar itadin mai nasara CE.


Tafiyarta takeyi tana juya irin mutuwar wulaqancin da xatasa aiwa zainabu, ai komai kudi ne kuma ta Tara, kamar an tsikareta tace Nana, kai ina yarinyar nan take? Yakamata in bincikota domin nayi mata alqawarin idan nasamu biyan buqata xan aurar da ita. Da wnn tunanin ta cigaba da tuqi harta isa gida.



Innalillahi wa'inna ilaihirraju'un shine abunda taketa maimaitawa tareda kallon jikinta dakuma inda take, qarshe tamiqe tsaye tana qara duba jikinnata dakyau..

Ganin qofa tayi aiko hakan yasata bin hanyar datagani Wanda take da tabbacin xai sadata da waje, mutane tagani adakunan kallo daya xakai musu kasan ba mutane ne masu hankali ke xaune acikin wannan yanayin ba.


Nurse's ne suka nufota cikin saurin su domin kamota, itako tsabar mamakin dake cinta yahanata qoqarin hanasu abunda take ganin sunada alamar aiwatarwan.


Maidata dakin data fiton sukayi, ganin sun kwantar da itane, suka dauko allura domin yimata, amma xuciyoyin su cike yakeda matuqar mamakin yanda akai, suke aiwatar da komai akanta cikin sauqi Wanda a baya komai xa'ayi sai antaru akanta samada mutane biyar, amma a yau mutane biyu suka shigo da ita daki.


Ganin da gaxke sukeyi allura xasuy mata Wanda batasak na menene ba, hakan yasata fashewa da kuma tareda riqe hannun nurse din tareda cemata, baiwar Allah wacece ke? Menakeyi anan, ina xuri'ata meyasa naganku atare dani bayan nidin ban sankuba?


Tambayoyi taimusu Wanda a qalla yakai kala goma, suko tsaiwa sukayi suna kallonta aqarshe suka yanke shawaran kiran ogansu, cikin Sauri ya iso dakin domin ganin abunda aka Sanar dashi yana faruwa.


Samunta yayi tana kukanta shabe shabe, kamar ranta xaibar gangan jikinta, lallasjinta yafarayi tareda yimata tambayoyi masu ma'ana, takuwa bashi amsa yanda ta dace batare da kwaba ko alamar matsalar kwakwalwa atareda ita ba.


Murmushin jin dadi yayi snn yace da nurse's din su matsa mata ta sauqo, matsawa sukayi yabata umarnin tasauqo tabiyoshi, haka tasauko a gadon tama kuma tareda waiwaye har sukabar cikin dakin.


Bai tsaya a ko ina ba sai cikin office dinsa, zama yayi tareda nuna mata kujera domin tazauna, zama tayi batare da tace mishi komai ba, saibin gurin kawai takeyi da kallo.


Miqewa yayi yanufi wani guri inda wasu tarin files suke, bincike yayi yadamo wani file snn yadawo yazauna, Wayarshi yaciro a aljihunsa snn yafara Neman Layin da yadauka acikin file din.



Assalamu'Alaikum, likita bokan turai, Algaji manyan qasa dariya sukayi dukansu snn likitan yafara cemishi yanason ganinshi yanxu a asibitin idan babu damuwa, inafatan dai lpy? Lpy qalau Alhmdllh ka kwantar da hankalinka kataho a hankali.


Ai kawai miqewa yayi yabar office din yayiwa direvan shi magana akan yawuce da shi asibitin, cikin qanqanin dakiku suka iso, office din likitan yanufa kai tsaye.


A zaune yasameta tareda likitan abinci aka kawota amma takasa ci, shigowa yayi xuciyar shi na kisima abubuwa dayawa, a mamakance yaqaraso tareda miqa mishi hannu sukayi musabiha da juna.


Alhmdllh godiya ta tabbata ga ubangijinmu wanda shike da ikon rayawa da kashewa, saka cuta domin jarabatar bawansa dakuma warkar dashi a lokacinda yaga dama, ba ikonmu bane ba dabaran mu bane, Lokacinda mukeson Abu ba lallai bane ubangiji yabamu shi awnn lokacin, munjima muna fafutukan lafiyar baiwar Allan nan, gashi batare da dabaran mu ba, cikin hikimar ubangiji yabata lpy a lokacin da yaga dama.


Kallon juna sukayi dasuri, Alhaji yana mamakin samun lafiyar natan, a fanninta kua tana mamamin da tu'ajjibin menene yake faruwa da ita, da har make murnan samun lafiyarta, badai hauka nakeyi ba? Ta tambayi kanta tareda due ban Alhajin tace, meke faruwa don Allah kuymin bayani yanda xan gane ban fahimci kudin suwaye bane, kutaimaka min kufitar dani a wnn duhun kan da nake ciki.


Ganin a birkice take yasa Alhajin roqonta akan ta kwantar da hankalinta, ta tashi sutafi xai kaita inda xa'a warware mata komai, badon tanada xabi bane kawai shiyasa tamiqe jiki babu lakka, shiko saida yatsaya yayi duk wani abunda yakamata ace xaiyi, bayan ya kammala suka tafi gida............




😍😍🤝🏼Anatare
Mummyn Fadyl CE



🎲🎲TUDUN DAFAWA🎲🎲


Rubutawa....MUMMYN FADYL (Fatyma Muhammad Adamu)

Wattpad @ *fatimamuhammadadamu*


INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION*
*[onward together]*
*{we give the reader's of ours the best out of the bests,, our inks are melodious and dropping a kinda lights to reader's}*
```THE PEN OF LOVE😘 HEAT TORCHING❤ TEAR OF SORROWS😭 CURDLES😊 GIGGLES😁 AND MARRIEGE THINK💑```
*```JUST GIVE US FOLLOW..**



Fitowa ta. 5⃣6⃣



Gaxkiya baxan boye miki ba, Maman larai abunnaki yanxu yafara isata tun banaganin kinada hannu acikin lamarin har nafara xarginki domin a halinda ake ciki yanxu abunnawa yawuce xargi xuciyata tagama ayyanomin gaxkiyan halinda ake ciki.


Hawaye ne yacika mata ido qoqari takeyi domin ganin bata basu daman fitowa ba, duk maganganun da yakeyi idanunta nakanshi har yakai aya snn tace dashi cikin muryan dakanaji kasan xuciyar meshi a karye take.



Haba Bbn larai shekarana nawa ina tare nidake? Baka taba kamani da laifin sa hannu indauka maka komai ba sai yanxu da girma yakamani, kamanta tun bansan darajar rayuwata ba nake tare dakai wannan toxarcin dame yayi kama? Tafashe da kuka mecin rai.


Shiko maimakon yaji xuciyarshi ta karye, a'a sai shedanne yaqara buga mishi ganga akan ai borin kunya kawai takeyi irinna mata masu halin beraye, inba ta raina mishi hankali ba tayaya dagashi sai ita xa'ai tamishi sata babu qaqqautawa?


Ada yayi tsammanin ko Lami ce amma har lami tabar gidan babu abunda yasauya hakanne ya tabbatar mishi me dakin tashi ne dai ta koyo halin berayen, Wanda shikuwa baxai dauka ba xaiyi maganinta.


Abunda bai saniba shine Lami tayi iyabakacin iyawarta ta kirsa rashin mutunci, toxarta matar baffan sadiyan ,amma hakan baiyi tasiri ba, daga qarshe ma daya fahimci halin da matar tashi take ciki na tsangwaman mai dakin nashi saiya canxa tunani akan yayi saurin nema mata matsuguni duk budirin da akeyi batasani ba.


Sai watarana kawai saiga Isah yaxo, bayan yashigo gari ansanar dashi abunda yafaru shine yanemeta, bayan sungama gaisawa ne yamiqa mata kayayyakin da yataho mata dashi daga birni, suna cikin hirarrakinsu na da da uwa yake sanar da ita cewa ai yasamu matar aure
, tayi farinciki domin ita hankalinta ma baya gurinshi, hankalinta nakan abun duniyar dataga dannata yatara



Suna zaunen saiga baffan nashi yashigo aiko Isah yatashi yabishi don damage yanason magana dashi, a xaure suka xauna, bayan sungaisa ne Isah ya koro mishi bayani daidai da yanda akai mishi bayani akan mahaifiyarshi dangane da barin gidan mijinta datayi, yaqarshe maganar nashi cikin qunar rai.


Baffan yasha mamakin jin wannan batun, sann yatausayawa Isah na rashin dacen mahaifiya dayayi, gashi bata karban shawaran kowa, nan shima yakoro mishi matsalar data haddasa dakuma Wanda take qoqarin haddasawa a nashi gidan shima.


Isah ya jinjina al'amarin suna cikin maganar ne taji shirun Isah yayi yawa shine tamiqe tabiyoshi, aiko taimusu lampo tana saurarensu, domin duk a tunanin tabaffan nasu roqon isan xaiyi wani abu,.


_kujimin Lami qaya nutumin da yayi miki karamci, amma bakya fatan a kyautata mishi?_


Nan isah yace da baffanshi yataho da kudade yanason a nema mata matsuguni tabar nan din koda daki dayane ,baffan nashi kuwa dama kamar akanshi take xaune a take ya amince Yakuma nuna mishi maqocinsa na dab da dab, yaqaura kuma dama haya xaisa a gidan don haka kawai sukama.


Isah yayi na'am don haka suka ajiye maganar a haka, Lami taji takaicin hakan, don haka tai kwafa a hankali tare da cewa inkunsan wata ai bakusan wata ba, don haka takoma tai zaman ta kamar dama can batabar gurin ba.


Basu wuce kwana Biyar da yin maganar ba aka sanar da'ita sunyi mamakin yanda bata nuna damuwa ko Kadan ba, matar baffan sadiyan kuwa kamar antsoma ta a aljanna, haka taita tayata harhada kayanta, xuciyarta fal da farin ciki, itakuwa Lami fada takeyi a ranta xakici ubanki ne.


Tana komawa gidan kua dayake tagama fahimtar gidan takuma karanci duk wani saqo da lungun gidan, shiyasa bai bata wahalan shigo domin yimusu sata ba yanda ranta yakeso tasan babu yanda xa'ayi a zargeta, tunda ba gida daya suke zaune ba.


Yan xumma dasuke xaune a dakin, taga shigowarshi ne kuma tasan jiya tayi musu barna Wanda bata taba yimusu irinshi ba, shiyasa tabari bayan yashigo da kamar minti biyar tabiyo bayanshi, isowanta taji yana maganar kumacikin daga murya, hakan baqaramin dadi yayi mata ba, takoma gidanta.


Zama tayi tafara tsara yanda xatayi tunda yanxukam a qalla ta Tara kudin da Maye xai iya yimata aiki, kai yanxu kanma ta yanke hukuncin baxataje gurinshi ba domin ta fahimci kudinta kawai yakeci, yakasa yimata komai, tahana kanta cin me dadi kokuma ta kwanta a guri me kyau, domin kuwa duk abubuwan da Isah yayi mata na gyaran daki kapin tafiyarshi kapin yabar garin saida ya tabbatar ya gyarata snn yatafi bata barshi da komai ba sai kudin mota, amma washegarin tafiyar tashin ta sayar da komai.



Yanxu banda tabarma babu komai acikin dakinta, Sai Dan wata tsohuwar gana mazgo Wanda tsummokin ta yake ciki. A waje kuwa daga randa sai 'yan tsirarun kwanukan abinci, komai idan xatayi amfani dashi gidan baffan sadiyan take shiga ta karbo.


&&&&&&&&&&&&&&


Isowarshi gida yaga motar IBBY hakan ya tabbatar mishi dacewa yana tare da zarah kuma yasan gabadayansu ana falon shiyasa yabi da ita taqofar baya, dakin baqi yanuna mata, akan xaije yakira mata matar gidan.


Cikin Dari Dari dakuma fargaba mai hade da bugun xuciya tashiga dakin, a qasa taxauna, tafara kalle kalle babbaj burinta Allah yakwo mata me sanar da ita halinda take ciki, domin itakam takasa tantance a wace duniyar take yanxu.
Duniyar matattu ne koko ta rayayyu?


Shiga falo yayi aiko yanda yayi tsammanin hakanne ta kasance domin kuwa zarah tana zaune suna hira da IBBY mummy kuma itada khadija dataxo musu wuni, da tsohon cikinta.


Mummy CE tafara ganinshi tamiqe tareda cemishi daddynsu yaukuma Kaine da shigowa taqofar baya? Dariya yayi mata snn yabata amsa, Mutum da gidansa baida ikon shigowa ta duk inda yayi niyya? Itanma dariya tayi tace ahh na is a kota sama kaga damar shigowa kashigo kawai nabaka izini domin gida dai nawane, gaba dayansu ne sukai dariya wannan karon, India kana wannan gidan topa koda kapi kashi tsumewa saikayi dariya😜

Gaidashi sukayi gaba dayansu, banda zarah Wanda saida ta task ta iso gareshi takama hannayenshi snn tagaidashi amsawa yayi snn taimishi wani magana ahankali Wanda shikadai yasan meta gaya mishi, dariya yayi mata snn yace to naji sauna fito, yanufi hanyar dakinshi mummy ma Tamara mishi baya.


Saida suka isa dakin bayan ta tayashi garage kayak jikinshi ne ya dakatar da ita snn yace, nataho miki da baquwa tana dakin baqi, inason kuma kibi komai a hankali.


Itakuwa tsabar gandokin ganin wayene yakeda wannan matsayin da har xai biyo ta gurin mijinta, yataho tareda shi harma kuma yayi mishi masauqi dakanshi, marmarin hakan yahanata tambayarshi kawai takama hanya direct saidakin baqi.


Isarta da sallama ta shiga, amsawa tayi gamida kallon qofar domin ganin wanda yashigo, aiko miqewa tayi tareda nunata, itama mummy zaro idanu tayi tareda rufe qofar ta qaraso gareta, rungumeta tayi tareda farinciki.


Itama Mama rungumarta tayi, domin tanada tabbacin komenene yake faruwa da ita bamai muni bane, don tasan baiwar Allahn nan bamai cutar da ita bane.



Zama sukayi suna hawaye Mummy CE taketa nanata Allah mungode maka, lallai ubangijinmu madaukakin sarki ne, me warkarwa Aduk lokacinda yaso, mai isa da buwaya, Allah muna qara godemaka take ta fada cikin kuka.


Mama kuwa sai binta takeyi da kallo snn tace inason don qaunarki da mahaliccinki inason kiy gaggawar sanar dani abunda yake faruwa dani.


Ki kwantar da hankalinki..............



😍😍🤝🏼Anatare
Mummyn Fadyl CE





🎲🎲TUDUN DAFAWA🎲🎲


Rubutawa....MUMMYN FADYL (Fatyma Muhammad Adamu)

Wattpad @ *fatimamuhammadadamu*


INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION*
*[onward together]*
*{we give the reader's of ours the best out of the bests,, our inks are melodious and dropping a kinda lights to reader's}*
```THE PEN OF LOVE😘 HEAT TORCHING❤ TEAR OF SORROWS😭 CURDLES😊 GIGGLES😁 AND MARRIEGE THINK💑```
*```JUST GIVE US FOLLOW..**



Fitowa ta. 5⃣7⃣



Ki kwantar da hankalinki kikuma godewa Allah akan dukkan ni'imomin da yayi miki, xan Sanar dake abunda yake faruwa amma bayanxu ba sai kin Dan huta namiki alqawarin xua dare insha Allah xan sanar dake komai ina fatan kin fahimceni? Taqarasa da qaqalo murmushin qarfin hali.


Itama murmushin tamayar mata Wanda baikai maqoqoranta ba, iyakan labban bakinta ya tsaya, da hakan sukai bankwana bayan ta nuna mata bayan gida da yanda xatai amfani da komai dake ciki, itakuma tafita domin kawo mata kayan da xata sauya.


Dawowa tayi tasamu daddy a xaune yana waya, jira tayi bayan ya kammala, matsowa tayi kusa dashi snn takama hannayenshi tace ranka ya Dade ya akayi haka tafaru? farinciki kwance akan fuskarta.


Dubanta yayi snn yace kedai mu godewa Allah kawai nan yasanar mata yanda sukayi da likitan, gabadayan su sun jinjina al'amarin qarshe suka ajiye akan bayan sallan isha'i xasu kira meeting din gaggawa.


Assalamu'alaikum da sallamarta tashiga dakin mahaifin nata a zaune bisa darduma ta sameshi da alama shine ya idar da sallan walha, Baba yau banga ka fito ba shine nace gara dai inxo indubaka kodai qafanne?


Murmushin
yayi snn yace Nana ba qafan bane, qafa kam Alhmdllh domin tun dawowarmu daga asibitin kano naji sauqin sa, snn kinga sikarin ma yanxu dayake ana samun kiyayewa akan harkan abinci snn kuma ga magunguna toshima Alhmdllh yadaina tabani.

To masha Allah tafada, xama tayi suka Dan taba hirarraki tana kuma qara tabbatar mishi Alhaji yaqara tsananta bincike akan Neman mahaifiyarta, yaji dadi sosai duk dama jikinshi a sanyaye yake matuqa, domin akoda yaushe idan yatuna wucewarta ta gabanshi tsikar jikinsa baya daina tashi.


A halinda ake ciki daga Bbn Nana har Dan uwannashi basa harkan gadi, don tuni ansamo musu Sabon mai gadi, amma dayake al'amarin tsofi tobasuda gurin wuni sai can bakin gate din.


Tun Alhaji yana yimusu magana haryagaji yayi shiru ya kyalesu, zama sukeyi na mutuntu juna, duk da madai Bbn Nana yanuna mishi shikam baxai iya zama gida guda da diyarsa ba, domin wnn ba al'adan mal.bahaushe bane, musamman suda suke katsinawa Wanda aka sansu da kara.

_yaukam na yabaku katsinawa, amma xan Dan taboku a gaba_ 😜 lol



Bayan sallan isha'i ne daddy yashigo cikin gidan nashi tareda Bbn IBBY, suna tafiya suna dan tattaunawa akan maganar bikin su Xarah, kagane inji daddy.


Nipa nafison hada bikinnan dana Aliey amma shikuma bayan na tuntubeshi nunamin yayi wacce yakeso bafa bahaushiya bace ma, kai wace qabilace inji Abba.


Wlh wai Igala ce 'yar jihar kogi state ce, a makaranta suka hadu, ikon Allah to Allah yasa Diyar arxiki ce, amma pa taron nan banson musako yara cikinshi, meyasa kace haka?


Koda xamu sako yaran to karya wuce Aliey da Ibby, inyaso sai daga baya sauran yaran xasu sani. Ah ah wannan ba hujja bace duk dama baka fadi hujjar kaba, amma inada tabbacin batada fa'ida inason asanar da kowa kuma kowa yasan matsayinta, ciki kuwa harda diyarta, hakan xai rage mata wasu radadin dayake cin xuciyarta, though bamusan tarihin rayuwarta ba.


To shknn tunda haka kace, yanxu ni bari inkoma naiwa nawa iyalan magana, ahadu a babban falon side dinka, OK sai kun shigo,yakoma gidanshi shikuma daddy yashigo gida, dakin mummy yanufa yasanar da ita yanda sukayi da Bbn ibby nan itama tamiqe tayi dakin zarah tasanar da ita buqatar daddyn ta, snn tayi dakin Aliey kai tsaye.


Samunshi tayi yana zaune akan _sofa_ jallabiya ce a jikinsa kalar ruwan madara, hakan yaxame mishi al'adar shi ce indai yana gida to da magrib shigensa knn, waya yakeyi yana ganinta yakatse kiran tareda cewa mummy kece?

Bakai tunanin ganina a wnn lokacin bako? Murmushi yayi mata, zama tayi a gefenshi tace Son saiyaushe ne xaka gabatar da taka matar? Yatsina fuska yayi shikandhi baisan dalili ba tun bayan dawowarshi yaji buqatan auren Siyaman yafice mishi a rai, bayan dayana can kuma har qosawa yayi yadawo gida ya gabatar da ita, ai musu aure sabida yanda yakejinta a ranshi.



Itakanta Siyaman harta gaji dayimishi magiya akan maganar ta haqura, domin yanxu Indai tanason su samu sabani tofa tadago mishi maganar aure, yanxu sai yay mata ba dadi.


Mummy nifa maganar auren nan a barshi kawai baya,xu ba, subhanallah anya ba ruqiyya xansa ai maka ba? Dariya yafara yimata harda kyakyatawa yana kallonta, mummy aljanu ne gareni ko me? To nasani tunda gashi bakason aure? Tabashi amsa snn taqara da cewa kai ko sha'awan IBBY da zarah bakayi? Duk familyn nan waye baisan da xaman soyayyar su ba?


Ai nan ya gimtse dariyarsa kamar ba shine yagama yinta yanxu ba, itako mummy batama kula da fuskartashi ba, domin ita yanxu al'amarin nashi haushi yake bata, kawai tamiqe tasanar dashi saqon daddynsu tai wucewarta.


Jiki ba lakka yamiqe ya shirya yafito xua falon, itakua Xarah gabadaya tsammaninta maganar aurenta xa'ayi itada IBBY, hakan yasata said a ta tsara kwalliyarta tafito Ras da ita, tafito riqe da wayarta maqale a kunnenta da alama waya takeyi domin yanda ta wanxar da annashuwa akan fuskarta, hakan xai tabbatar maka komai dawaye takeyin wayar to tanajin dadin shi.


Tafiyarta takeyi tana yauqi son ranta, hango Aliey tayi shima wayan yakeyi, saitayi tsammanin ko ibbyn ta ne, hakan yasata qara yanga da sauri taqaraso tareda cewa yauwa my paramour kainaketa kira mushiga tare, baxan iya shiga nikadai batare dakai ba, banson kowa yariga ka kallon kwalliya ta, tafada cin muryan shagwaba.


Baisan ya akayi ba yaji wani Abu ya tsirgo mishi tundaga tafin qafarshi had tsakar kansa, amma ya aro dakiya yace mata ke dallah can kimaida hankalinki saiwani rawan kai kikeyi kamar ballagaxa mamakin jin zagin da yake

Please Login or Register in order to submit comment