You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gida, yayi daidai da dawowan IBBY shima yakai qannensa, donshi rayuwarshi babu tsanani indai yana gari, topa yanayiwa qannensa iya bakin iyawarsa, tsayawa yayi suka gaisa, snn yatamanbayeshi saga ina yake? Mtswww barni kawau wlh nakai fitsararriyar 'yar nanne makaranta.


Dariya IBBY yayi Sanin da yayi wa Aliey yasa baice komai ba yayi shigewarsa side dinsu, shima Aliey gidansu yashiga yasamu daddy yafita don haka direct dakin mummy yawuce yasameta tana waya, a kan dadduma yazauna ya tankwashe qafansa.

Bayan taagama wayarne tafuskanceshi dakyau. Snn tacemishi yayadai Mazan fama? Shiru yayi sai can yacemata ni mummy sonake kigayamin gaxkiya Inda kikasamo wnn yarinyar takin marar kunya.

Dariya mummy tayi race mishi 'yata ba marar kunya bace, a qarshe dai cikin nitsuwa ta labarta mishi abunda yafaru tun farkon al'amarin har xua yau, abun ya shigeshi bana kadanba Yakuma tausayawa mmn Zahra, nan yatambayeta yaushe xataje? Eh to yanxu bama xuwa kamar da, domin ciwon nata yayi tsanani amma xuwa gobe xataje insha Allah.

To Allah yakaimu xamuje tare, daganan sukaita hiransu ta da da uwa.


**†*†***********

Yauma sunjima tsaye abakin gate din dakyar da bincike aka barsu suka Shiva akai musu iso xuwa falon, sunjima harsun fidda rai akan xai fito can saigashi yafito sanye da jallabiya kamar mutumin arxiki.

Ayashe ce tagaisheshi ya amsa kamar bada bil'adama yake gaisawa ba, tasanar mishi da abunda take tafe dasu, tareda Nina mishi wa'adinda ya diba musu ne yacika.


Saida yagama Jan ajinsa snn yace mata.......


😍😍🤝🏼 Anatare

Mummyn Fadyl CE




🎲🎲TUDUN DAFAWA🎲🎲


Rubutawa....MUMMYN FADYL (Fatyma Muhammad Adamu)

Wattpad @ *fatimamuhammadadamu*


INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION*
*[onward together]*
*{we give the reader's of ours the best out of the bests,, our inks are melodious and dropping a kinda lights to reader's}*
```THE PEN OF LOVE😘 HEAT TORCHING❤ TEAR OF SORROWS😭 CURDLES😊 GIGGLES😁 AND MARRIEGE THINK💑```
*```JUST GIVE US FOLLOW..**

_Aduk inda masoyi yake abun alfahari ne, ina alfahari daku masoyana, qaunarku nima acikin jinina take_

Fitowa ta. 3⃣6⃣


Saida yagama Jan ajinsa snn yacemata naji kujirani ina xuwa, yatashi yashiga ciki, itajuwa Nana inbanda addu'oi babu abunda take nanatawa a cikin xuciyarta, qirjinta sai lugude yakeyi kamar xai fado qasa, itadai yau taga tashin hankali ganin idonta.


Baiwuce minti shabiyar ba saigashi yafito da wata 'yar qaramar jaka a hannunsa, xuge zip din jakar yayi😳😳😳 gabadayansu sai da idanuwansu yaiwo waje har gara Ayashe ma don Nana jitake kanta na juyawa don tunda uwarta takawo ta duniya bata taba yin arba da kudi makamancin rabin wnn ba a rayuwarta.

Rafa ce ta dubu dubu Wanda baxaka taba cewa sune a sheqe a cikin wnn jakar ba, kallonsu yayi a wulaqance yakuma ga zalamar kudin atattare dasu qarara, don haka yayi gyaran murya yace, xan sallameki yanxu, Allah yaqara girma da arxiki, tafada jiki na bari kamar maxari, dauko kudin yayi dauri uku, dubu Dari uku kenan yamiqa mata, kamar me shirin kifewa ta qarasa gabanshi harda durquso kamar mahaifinta takarba tana godiya harda addu'a.


Shiko budan bakinsa yace shknn jeki kibarta kawai, batareda 2nanin komai ba tamiqe tayi hanyar waje, harta isa bakin qofa, tadawo gaban Nana tadan sunkuyo don kar yaji abunda take fada, tacemata kiyi haquri Nana amma indai nine wlh akan kudi babu abunda baxan iyaba, daga yau ba lallae bane muqara haduwa, shawaran da xanbaki shine Iya ruwa fiddakai, idan kin iya takunki xaki kwaci kanki, idanko kika kasa kindaisan yanda qarshen Sadiya yayi ko? Tosaikin fita wulaqanta.

Sam Nana takasa fahimtar inda duk bayanan na Ayashe ya dosa, saboda gaba daya kanta a juye take, Kalmar innalillahi taita banatawa bata dawo cikin hayyacinta ba, sai xuwa can kalle kalle taita yi taga babu kowa a falon sai ita kadai.


Agurin ta durqushe, taita rusa kuka kamar babu gobe, yau itakuma tanan rayywar ta bullo mata? Ya Allah ka iyammini naroqeka badon niba don darajar fiyayyen halitta.

Ayashe ko tafiyarta take hankalinta kwance tasan shirinda tayi, waxai tambayeta lbrn Nana duk saida tasa aka qara rufemusu baki, domin tun lokacin xamansu a gidan rasuwan tafahimci kamar hankalinsu yafara Dan dawowa jikinsu, aikuwa baxata lamunci wnn iskancin ba.

Da wannan tunanin ta iso gida amma can qasan xuciyarta taji tausayin Nana, saboda a xamanta da yarinyan bata taba quntata mata kokuma tayi yunqurin yimata musu akan wani Abu ba

Kai indai har Nana tafahimci tana son abuma kapin tasata xata aiwatar yarinyar ladabinta da biyayya ajininta yake, gashidai kobaka tambaya ba kasan a quntace rayuwarta take, saidai baxaka taba gani akan fuskarta ba, domin tana iya qoqarinta gurin boye damuwarta.

Sauda dama takan jiyota tana kuka koa bandaki kokuma a daki, amma idan taji alaman xata shigo to xatai saurin daidaita nitsuwarta bata taba bari ta sameta a wani yanayi.

Allah sarki haquri xakiyi Nana amma ni indai akan kudi ne babu abunda baxan iyayi ba, duk rintsi dai inkudi ya xauna min zance innemo duk inda kike nabaki haquri dakuma jindadi, saidai kawai naimiki fatan Allah yabaki ikon da xaki kwaci kanki don bana fatan ki wulaqanta.

Duk wannan maganar da xuciyarta takeyi amma afili taketa batun kamar wata xautacciya.


****************
*WASHE GARI*

Da yamma bayan sungama shirinsu gaba daya ne Zahra ketambayan Mummyn ta , ina xamuje mummy? Asibiti xamuje aiko kamar daga sama mummy tajiyota tahau ihu kamar wacce aka dosanawa wuta babu sassauci, mummy tayi lallamin duniya amma zarah taqiyin shiru ihunta kawai kakeji yana tashi a gurin.


Isowan Aliey kenan bayan yagama kintsawa cikin shigarsa ta alfarma he luks so takeaway, Qarar da zarah keyi ne yafara isanshi abun takaici anrasa wanda xai maketa acikinsu daga mummy har daddyn sun biyemata sai akin lallashinta sukeyi.

Aiko yana qarasowa ya buga mata mahaukacin tsawa tareda daga hannu xai kai mata mari, mummy CE tariqe mishi hannu tareda cemishi haba Aliey qanwarka cefa, qaramar yarinya haka ai wnn hukuncin yamata tsauri, itako zarah ganin an hanashi yasata qara daga volume dinta taita ihu, daddy ne yakamota yajata gefe yafara gaya mata wani magana a kunnenta, dakyar ya rarrasheta sai ganinta sukayi tashare hawayenta tana dariya. Nan suka dunguma gaba daya suka Shiga mota Aliey ne yajasu, kamar kullum saida suka tsaya sukayi sayayyan da suka saba snn yawuce dasu asibitin.


Kallo daya Aliey yayi mata yakauda kai, donshi mutum ne mai matuqar tausayi da jinqai, Itakuwa zahra kokusa da dakin kasa qarasawa tayi don tsoron kar akuma abunda akayi a baya, mummy CE da daddy ke tsaye ta window, hawaye ne yake taruwa a idanun daddy inda mummy kamma tagama yin sharkaf da nata hawayen domin kallo daya xakaiwa Mama kasan mahaukaciya ce tagaxke.


Ana gab da fara kiraye kirayen sallan magrib suka bar cikin asibitin, bawanda yakewa Dan uwansa magana don har uwar surutun ma a nutse take, zuciyar kowa da abunda yake raya masa, ko parking baiyi dakyau ba yatsaya suka fita, shida Abba suka nufi masallaci, mummy da Zarah sukai cikin gida.

Dawowanshi daga sallah ne yasamu IBBY a dakinsa kai mutumina naxo maka da sabon labari amma wlh saikamin alqawarin xaka rakani gurin Meenah ta yau, dariya yayi kapin yace baxaka gane bane, nipa bawai banason rakaka xance bane, wlh Aminan naka ce ni kwata kwata bataimin ba, banason mace me yawan. Surutu, kuma wlh nasan itace tabawa qawarta contact dina, mtswww nadai daga mata qafa ne don kai, gashi yarinya mai Dan uban naci wlh haushi safeena take bani, kira kamar don ita nasai wayan.

Dariya IBBY yayi mai isarsa snn yafara magana cikin dariya yace, kafadi yawan magana kaida kakeda qanwa parrot? Mtswww yaja wani dogon tsaki na tuno mai da zarah dayayi , har cikin ransa yanajin haushin yarinyan.

Kai Mallam idan xaka fadamin mega kawoka kafadi, idan kuma bahaka ba, ni infita yafada yana hade ransa, IBBY kuwa ko ajikinsa, saida yaqara cemishi xanso ganin ramda xaka xauna da mace daki daya, shinxaka ajiye Jan ajinnan ne kokuma ahakan xaka tunkareta, Aliey kuwa dayaga abunnashi bana qare bane niyyar ficewa daga dakin yayi.

Ibby ne yadaga murya yace inka gama kumburin kaxo ga admission din masters dinmu Abba yakawo, aiko bashiri yajuyo fuska asake.


*************

Tunda yashige yabar Nana agurin baiqara bi takanta ba, donshi daman Nana bata cikin tsarin matanda yake mu'amala dasu, shiyafi harka da tsofi wadanda suka manyanta acewarsa sumfi dadi😜.

Don haka tana xaune agurin har xaman ya gundureta ahaka har mangariba yacinmata. Dube dube tafarayi tanason tayi sallah babu ta Inda xatayi alwala, gawata baqar yunwa dayake ciciyarta kamar xai rabata da gidan duniya.

Tana zaune taga yafito da jallabiya a jikinsa kuma ba irinna daxunba, batai tsammanin samun kallo daga gareshi ba , hakanne kuna yakasance, wuceta ta yayi, tabishi da kallo da alama alwala yayi xaifita sallah.


Ikon Allah Ashe mugaye ma suna ibada? Tafada aranta, leqenshi tayi ta tabbatar yafita don haka..............


😍😍🤝Anatare
Mummyn Fadyl CE



🎲🎲TUDUN DAFAWA🎲🎲


Rubutawa....MUMMYN FADYL (Fatyma Muhammad Adamu)

Wattpad @ *fatimamuhammadadamu*


INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION*
*[onward together]*
*{we give the reader's of ours the best out of the bests,, our inks are melodious and dropping a kinda lights to reader's}*
```THE PEN OF LOVE😘 HEAT TORCHING❤ TEAR OF SORROWS😭 CURDLES😊 GIGGLES😁 AND MARRIEGE THINK💑```
*```JUST GIVE US FOLLOW..**

_Comments dinku a 36 yayi low dayawa, shiyasa nima xan Dan tafi Hutu yawan comments yanayin sambado shafi😜_......



Fitowa ta. 3⃣7⃣.


Leqenshi tayi ta tabbatar ya fita don haka tabi bayanshi baqaramin dadi tajiba ganin yafita batare da yayi yunqurin rufe qofan ba, cikin sanda take tafiya harta isa bakin gate din, maigadin tasamu yana zaune baida alaman tashi, komawa baya tayi ta buya yanda baxai ganta ba.


Tajima a wannan gurin tadai lura bashida alaman barin gurin, takaici ne ya turniqe ta, ganin Alhajin tayi yadawo, saiji tayi yace Daniel kaduba cikin mota akwai kaya kashigo dashi ciki.


Tsaki taja a gurin tanufi ciki batareda tabari ya ganta ba, a ranta tana fadin ashema kafuri ne? Ya Allah ka kawo sanadiyyar barina gidannan batareda na illatu ba, falon takoma taxauna agurinda ta tashi.

Yana shigowa kai tsaye yanufi dakin sa, amma wnn karon baijima ba yafito, xama yayi a kujeranda ke fuskantarta, Nana yakira sunanta.

Yanda tai saurin amsawa ne xai tabbatar maka a firgice take a gurin, ki saurareni dakyau, bani nakeda buqatar ki ba, abokina ne yakeson kasancewa da irinki, nakuma yimishi alqawarin xan kawomishi ke, amma yanxu baya gari donshi badan Katsina bane, Dan Kaduna ne.


Inason kisaki jikinki babu abunda xai tabaki, baxai jimaba nanda sati biyu masu xua xai dawo xankai ki gareshi, karki takura kanki domin baxai amfana miki komai ba, kisani ko wacce takawoki gidannan batada ikon fitar dake a yanxu, idan kikai yunqurin guduwa xakisha matuqar mamaki.


Kinga wancan dakin? Yanuna mata wani daki, bin hannunshi tayi da ido batareda tace komai ba, acan xaki xauna kapinnan akwai komai na buqata aciki, yanxu xa'a kawomiki kaya, yana kaiwa nan a qarshen maganar sa yatashi yawuce.


Bata tashiba a gurin saboda tunanin sabuwar rayuwarda ta tsinci kanta kuma tafarayi, jin qarar shigowar mutum falon ne yasata dagowa, wata mata tagani kallon farko taimata tasan tajiqu da nera, kuma baqarama bace don kana ganinta kasan anjima ana damawa da ita cikin rayuwar nan, ba abunda xai baka dariya gameda ita kamar yanda take yauqi da karairaya ala dole tanason ai mata kallon yarinya, fuskarnan an fante shi da kwalliya harda na hauka, duk quncin da Nana take ciki baihanata yin dariya ba.

Itakuwa batamasan tanayi ba, kai tsaye tai shigewarta dakin da taga Alhajin yashiga dawowarshi, kallon bayan matar tayi ta kwashe da dariya sosai hartana riqe ciki, lallai duniya cike take da qalubale harda fadi tashi.


Can data tuno halinda take ciki nandanan fuskanta yasauya ta tashi tanupi dakin da ya nuna mata, sake baki tayi gurin kallon dakin, don kuwa falon ba komai bane idan aka misaltashi da qayatuwan dakin. Sosai ta shagalta da kallon gurin, Naso ace nashigo gidannan ta niyya me kyau, kokuwa tareda mahaifiyata, da yau xan yi baccin farin ciki, amma saigashi na shigo gidan alfarma cikin mummunar niyya hannun fasiqi marar tsoron Allah.

A qarshe dai taga yawan tunanin babu Inda xai kaita, tashi tayi tashiga bandaki, nanma lalacewa tayi da kallon gurin, dakyar tasamu dabaran samawa kanta ruwa tayi alwala tafito, batasha wahalan Neman dadduma ba, domin komai a tsare yake a dakin.

&&&&&&&&&&&&&&
*Bayan kwana uku*

Lami ce zaune a gindin murhu tanata fama da aikin hura wuta hayaqi duk yacikamata ido, idanunnan sunyi jazur hanci kuwa sai yoyon majina yakeyi, itace dalbejiya ce wacce bata gama bushewa ba, taroqi almajiri yakawo mata tabashi naira talatin, duk faman nan kuwa datakeyi sotake tadafa wani guntun qanzon ta Wanda shikadai ne yarage mata ciki da waje.

Ahalin da take ciki yanxu tamadaina sawa a ranta tanada aure, don kuwa itada marar miji duk daya suke, iskancinma tanemeshi ido rufe tarasa meyi da ita.

Dama mutum daya ce mai iya taimakonta a wnn fannin itace Ayashe. To yanxu kuwa tafi qarfinta dob rabonta da ganinta ma harta manta, gashi batada komai, Dan abubuwanda baffan Sadiya ke kawo mata duk ta tarkata tasayar takaiwa Maye yacinye kuma babu biyam buqata, banda gurxanta dayakeyi, Wanda duk yawaancin bayan dawowanta a gurin shi saitayi jinyar kanta. Xuwa yanxu kanma harta gaji da xua ta kyaleshi don ta fahimci baxai tsinana mata komai ba.


Har jitayi abincin yagama fita mata a ranta, dakyar tasamu ya dahu tajuye a roba takoma gefe taxauna domin ci, miqewa tayi don ta debo ruwa ta ajiye a ganganta, sallaman da aketayi ne yasata tsagaitawa tareda danna dogon tsaki, tana fadin wnn anyi jarababbe kome yake nema oho.

Fita tayi tasamu wasu mutane tasandai dayan, amma bata gane fuskan dayan ba dagani dai ba Dan unguwan nasu bane, don kuwa me kudi ne.


Washe baki tayi kamar gonan auduga, jitake anata 2nanin wani abun suka kawo mata, Dan liti ne yafara mata bayanin abunda yake tafe dasu.

Lami wnn da kike gani shine Alhaji Sabo, kuma shine Wanda yasayi wnn gida dakike ciki, anmiki zuru xua yanxu yalura bakisan ana daga miki qafa ba, shine yaxo domin kifita yanada buqatan gidan.

Dan liti kayi batan kai tafada kanta tsaye, domin ni bansaidawa kowa gidana ba, nice dai mamallakiyar gidan kuma ban saidaba inaga ka bata a kwatance ne, nabarku lpy tafadi tana barin gurin.


Alhajinne ya fusata yace mata da qarfi ke Lami kike kowa banason iya shege wlh, Yaya na mallaki gida watanni Bihar dasuka wuce, ankuma bani tabbacin xaki tashi kapin lokacin buqatata ta tashi, kuma yanxu kina sanar mini xancen wofi, to wlh nafiki rashin Hankali, nabaki nanda minti biyar ki tattaro komatsan ki kifita kibarmin gida.

Itakuwa Lami yunwar cikinta ke damunta shiyasa batasamu lokacin fadi infada dasuba tai shigewarta ciki tajawo roban qanxonta tafara ci.


Loma daya tayi xatakai nabiyu kenan saiga Ayashe akanta babu sallama kamar tsohuwar arniya, binta tayi da idanu gabanta na fadi don batasan dame taxoba.


Lami tayaya xan aiko acemiki kifita me gida yana da buqatan gidansa kuma kitsaya kuna sa'insa dashi, duk maganar nan datakeyi tanayinshi ne cikin gadara dakuma ixxa.


Ayashe bangane me like nufi ba , batajira ta qarasa maganar ba ta tari numfashinta da cewa au yi haquri ai nayi tunanin da me kwakwalwar mutane nake magana, Ashe damai kwakwalwar kifaye nakeyi, to bari inyi miki gwari gwari.

Gidanki dai nasayar saboda inada buqatar kudi kuma nagurina baxai isheniba, karki dauka ke kadai CE a cikin quncin a'a hard a mijinki domin shima nasayar da gidan dayake ciki.

Idan baxaki manta ba, damacan namiki alqawarin mijinki bawai xan rayu dashi rayuwa me tsayi bane, Aro ne nadan wani lokaci idannagama abunda nakeyi xanbaki abunki, to yau dai rana tayi nabarki da mijinki Mal.Babu kapinnan kuma meshi taxi takarbi kayanta.

A qarshe abunda xangaya miki shine, kisan dabaran da xakiy muku na gurin da xaku tsuguna kuxauna, tunda yanxukam bakudashi, Abu naqarshe kuma shine alqawari nayi saina warkarda Zainabu ta dawo ga mijinta tanan ne kadai xan gama hucewa kan wulaqancin da kikai mini, xaki iya kaini qara duk India kikeso, amma babu abunda xai tsinana miki, domin kallinan , takardu ta Nuna mata.

Takaddu ne nagidan mal.habu da kuma naki, king a kenan gidan mallakin Alhaji sabo ne, tana kaiwa nan a zancen ta, ta tsirtar da miyau a gabanta tayi waje.

Lami kuwa ........


😍😍🤝Anatare
Mummyn Fadyl CE




🎲🎲TUDUN DAFAWA🎲🎲


Rubutawa....MUMMYN FADYL (Fatyma Muhammad Adamu)

Wattpad @ *fatimamuhammadadamu*


INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION*
*[onward together]*
*{we give the reader's of ours the best out of the bests,, our inks are melodious and dropping a kinda lights to reader's}*
```THE PEN OF LOVE😘 HEAT TORCHING❤ TEAR OF SORROWS😭 CURDLES😊 GIGGLES😁 AND MARRIEGE THINK💑```
*```JUST GIVE US FOLLOW..**


~Soyayyar gaxkiya abune dayakeda matuqar wahalan samu a wnn rayuwa tamu, banda tabbacin irin sonda kukemin amma inaji ajikina qaunarku agareni babu algus kokuma surki acikinta~ *Nayaba da soyayyar Ku masoyana* ❤


Fitowa ta. 3⃣8⃣

Lami kuwa kamar mutum mutumi haka take tsaye a gurin takasa tsinana komai wa kanta, a take tanemi wannan fitinanniyar yunwan dake addaban nata tarasa, tarasa meke mata dadi bata lokacinda tasa hannu aka ta fara kurma ihu babu qaqqautawa ba, qofar gidan tafito ko takalmi babu a qafaqunta, tana fitowa kua tasamu garaden maxa a qofar gidannata daman yanxu suka gama shawaran afka mata.

Ganinta dasukayi tafito hakan baisasu dakatawa da abunda sukai niyya ba, tanaji tana gani kuwa akadinga wurgo mata kayayyakin ta waje, dama can bawani kayan arxiki bane.


Cillo kayan sukeyi bana wasa ba, haka take ta bi tana kwasan abunda ya sawwaka kamar zautacciya haka takoma tana ihu tana tashiga uku.

Babu Wanda ya saurareta, anacikin haka saiga Mal.Habu ya iso, ganin da yayi gurin ya kacame da al'umma anata hayaniya ne, yasashi jin faduwar gaba, domin duk a tunaninsa mutuwa akayi.

Qarasowa tayi had qafafunshi suna sarqewa da juna, haka ya isowa gurin dakyar, yanata gifta mutane har ya iso tsakiyar taron ganin Lami CE ke hauka yasashi rabawa ta gefe xai shige gidansa.

A bakin gidan yasamu Ayashe cemata yayi, yayadai kike tsaye a qofar gida haka? Bata amsamishi ba, tafara yimishi bayani.


Mal.Habu inason ka saurareni a gurguje xanmaka bayanin halinda ake ciki domin inada uxiri, rashin isowarka da wuri gidannan shiya haifar min da bata lokacina.


Gaxkiya baxan boyemaka ba, aurena dakai aurene na wucin gadi, aurene na huce takaici, Wanda kai kanka baxaka iya tuno garin Yaya hakan tafaru ba, to duk aikina na ne, tanuna kanta batare da shakkun komai ba, don tanada tabbacin babu abunda xai iya yimata.

(Tunda tagama shiri ma xuwan wannan ranar tacewa bokanta tanason idan ta tafi da kwana biyu ya karya asirinda yayi mata na auren Mal.habu , don tagama samun ribanda taxo gidanshi domin shi, batada sauran buri akansa.)

Idan baxaka manta ba, nakarbi maqudan kudi a gurinka dasunan xan habbaka maka kasuwancin ka, to magana ta gaxkiya anan shine babu wani kasuwanci nice nai amfanin kaina domin cin riban gobena, karka damu kai namiji ne, kana iya fita kanemi wasu kudaden walau da dabaran ka walau da qarfinka.

Haka bata dakata ba taimishi bayanin gida, kamar yanda Taiwa Lami amma anashi ta dora da cewa baxan bari a wulaqanta maka kayanka ba shiyasa naimaka adalci daya tun fitanka na tarkata maka abubuwanka, duk abun buqatarka yanacin wancan akwatin tanuna mishi da yatsanta.

Mal.Habu kanshi ne yayi mishi nauyi kamar andora mishi babban goran dutse, yamakasa magana, can yadago da jajayen idanunsa ya kalleta, baisan lokacinda yadaga hannu da nufin xai kai mata mari ba, ai cikin zafin nama Alhaji sabo yariqe hannunsa.

Ayashe ce ta kwashe da mahaukacin dariya snn tace Aida kabarshi ko marinnawa xaisa yaji sauqin abunda yakeji a qirjinsa, saikuma ta tsuke fuska kamar ba ita bace tagama sheqe dariya, tanunashi da yatsa tace.


Saura qiris ka tafka kuskurenda xai abkaka cikin baka'in da yafi Wanda kake ciki yanxu, da ace hannunka yayi kuskuren hawa kan fuskata da sunan mari wlh da saina maidaka abun kwatance, sonake ka sakeni yanxu basai anjima ba tafada tana wurga mishi harara.

Tamkar kansa xaibar gangan jikinsa haka yakeji, tsawan da ta daka mishi ne yasashi dawowa cikin 'yar qaramar nitsuwar da yarage mishi, yafara magana cikin karyewan murya.


Tabbas Ayashe kin cika azzaluma baxance miki komai ba amma kisani nabarki da fitowan rana da faduwarta insha Allahu ubangiji xai mini sakayya na xaluncin da kikai mini kije nasakeki saki daya, bana fatan qara rayuwa dake koda a gabane , yajuya yafara tafiya, shan gabanshi tayi cikin sauri tareda cemishi.


Gaxkiya Mal.habu ka burgeni matuqa dabaka wahalar da kanka, kabarni da Shiga duniya ina yawo da igiyar aure akaina ba, domin INA mutunta aure duk yanda yake, abuna qarshe shine inason ka aiwatar dashi kasaki Lami itama tahuta tafada tana kallon lami tareda yimta dariyar mugunta.

Kallonta yayi yace wnn kuma ba huruminki bane, kedai na sauwake miki, saikiyi tafiyarki, ahh to abu yy kyau Allah yaqara danqon soyayya tsakanin Ku, badamuwa Mal.Habu Allah yasada fuskokinmu da alheri, yimin afuwa namanta kudinka na gado inafatan shima kayafe mini, domin nakarbi kasonka da sunan xanje maka sari, wlh ina tabbatar maka da cewa ni bata wasa bace..


Wucewarta tayi tamiqawa Alhajin sabo takaddun hannunta dakuma 'yan makullan gidajen tashige motar da take gefe tana jiranta, a take aka jaaa tareda bula musu qura aka bar gurin.

Lami ce tabisu da gudu tana ihu tana faduwa aiko cikin rashin sa'a taci tuntube da wani qaton dutse Wanda yayi sanadiyyar faduwarta ta fasa baki harda guxirin faduwan haqora guda biyu na gaba.


Ihun Azaba ta kurma tahau birgima a gurin, abun mamakin babu Wanda ya nufo ta, tagaji ta tashi tanufi gindin bishiyanda ta hango Mal.habu xaune, durqusawa tayi a gabansa ta rushe da kuka


Cemishi tayi yanxu yaxamuyi a ina zamu zauna, wlh baxamu yafewa Ayashe ba ta ha'incemu tarabamu dates jin dadinda muke ciki, bana fidda ran itace tai sanadiyyar tafiyan Nana kai harma da uwar ta, itace sanadiyyan mutuwan Sadiya na, duk maganganun nan da takeyi tanayinshi ne cikin kuka kamar ranta xaibar gangan Jikinta.


Baiko dago kanshi ya kalleta ba, miqewa tayi yace mata, tun wuri kinemi India dare yayi miki nasakeki saki biyu, ni idan xa'a shaqeni bansan tayaya na aureku ba, yawuce yabarta a gurin tana sake rushewa da wani Sabon kukan, bakinta jini ne kawai yake xuba da wani yawu me dan uban yauqi
(masoyan Lami kuxo Ku lashe mata 😜).

Haka Lami tamiqe tatattare 'yan komatsanta inaxata nufa? Tunanin da taitayi kenan inama da Allah xai koro mata Isah, yau shine rana ta farko data fara yin danasanin halayenta na baya, yau da ace bataqi gaxkiya ba, da sadiyanta tana raye, yau da bata gujewa gaxkiya ba, da Isah bai gujetaba, tabiyewa son xuciya yau rana daya tal dukkan alhaki yafara binta kuma taji abun yafita a ranta.

A qarshe dai tayanke shawaran xuwa gidan Baffan Sadiya, don ko Karen haukane yacijeta baxata nupi sauran 'yan uwanta ba, saboda bata manta rashin mutuncin da taimusu lokacinda duniya take hannunta tace dasu karsu qara takowa inda take, don itama har abada baxata taka qafarta xua garesu ba, yau kua anwayi gari tun abyn baiyi nisa ba, rayuwa tajuyata baibai ,batada komai.


A hakan kuwa ta taka har gidan da qafafunta batada zabinda yawuce hakan bata maganin ko sule a hannunta, don tanada tabbacin kirkin baffan Sadiya yanada yawa kodon darajan yaranta xaibata matsuguni, baxai barta ta wulaqanta ba.

Isarta da sallama tashiga gidan kamar mumina, bata samu matarshi a gidan ba, shikadai ta iske shidinma yana alwala xaifita sallah, da ganinta kua yamiqe bayan ya kammala alwalan shi, Ah ah Lami lpy kuwa da tsakan ranar nan?


Dakyar tasamu ta shimfida mishi qarya da gaxkiya, domin tasan fadin asalin gaxkiyar baxai amfaneta ba, saidai ma yajawo mata tsana kyara, shima kuwa yaji takaicin wulaqancin da akai mata dakuma sakin da Mal.Babu yayi mata.

Nan yafara banbami yana fadin Amma bantaba tunanin haka Mal.Babu xaiyi ba, ace da girmansa yayi irin wnn abun , nan yasamu ya rarrasheta tayi shiru tareda cemata tashigar a kayanta dakin matarshi , yanxunnan idan ya dawo daga sallah xaisa a gyara mata dayan dakin nacan gefen.

(Niko nace anya abun xai dore?🤔 humm)

&&&&&&&&&&&&&


Mal.Habu kuwa yana Barin gurin, gurin yaga Aida kunya yanufi 'yan uwanshi yasanar dasu bashida muhalli, 'yan uwan ma kuma mata Wanda sukansu Allo ne saida wasu suke jingina, tayaya xai dunfaresu da Neman taimako?

Wani tunanin yayi yamiqe zumbur yabar gurin.


😍😍🤝🏼Anatare
Mummyn Fadyl CE



🎲🎲TUDUN DAFAWA🎲🎲


Rubutawa....MUMMYN FADYL (Fatyma Muhammad Adamu)

Wattpad @ *fatimamuhammadadamu*


INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION*
*[onward together]*
*{we give the reader's of ours the best out of the bests,, our inks are melodious and dropping a kinda lights to reader's}*
```THE PEN OF LOVE😘 HEAT TORCHING❤ TEAR OF SORROWS😭 CURDLES😊 GIGGLES😁 AND MARRIEGE THINK💑```
*```JUST GIVE US FOLLOW..**

_Sadaukarwar shafi sukutum xuwa ga 'yan mate_ *ZODOZEN CANDIDATE QAC* _Idannace banyi

Please Login or Register in order to submit comment