You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tafada hadi da miqewa taimusu sallama bawanda yakulata tayi waje, tsugunawa tayi a gurin tafashe da kuka...



😍😍🤝🏼Anatare
Mummyn Fadyl CE



🎲🎲TUDUN DAFAWA🎲🎲


Rubutawa....MUMMYN FADYL (Fatyma Muhammad Adamu)

Wattpad @ *fatimamuhammadadamu*


INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION*
*[onward together]*
*{we give the reader's of ours the best out of the bests,, our inks are melodious and dropping a kinda lights to reader's}*
```THE PEN OF LOVE😘 HEAT TORCHING❤ TEAR OF SORROWS😭 CURDLES😊 GIGGLES😁 AND MARRIEGE THINK💑```
*```JUST GIVE US FOLLOW..**



Fitowa ta. 2⃣3⃣



A hanyarta ta dawowa gidansu ne tatuna batamayi sallar asuba ba, cikin Sauri taqara gidan, batabi takan kowa ba, tanufi bayan gida tayi alwala tashiga daki, bayan ta idar da sallan ne tajima axaune tana addu'oi cikin kuka, tana roqon Allah ya bayyanar mata da mahaifiyarta cikin qanqanin lokaci, domin batasan yanda xata cigaba da rayuwa a cikin gidan Babu Mamanta ba. Itace taxanma *TUDUN DAFAWA* nta.


*BAYAN WATA HUDU*

Haka dai rayuwartasu taci gaba da tafiya kowa a gidan quncinda yake fama dashi na dabanne, Nana tana fama da maraicin rashin uwa, uwa uba kuma duk wani haushin Lami akan ta take sauqeshi, Dan makarantan ma datake xuwa yana rage mata qunci anhanata xuwa wuni takeyi tana aiki, da daddarene kawai take samun sukunin yin kukanta a makwancinsu.

A fannin Lami kuwa duk yanda kake zaton abun yawuce tunaninka, don ynxu Mal.Habu ma yadaina kwana guri daya da ita, kuma bayajin maganarta banda kallon kyama babu abunda take samu agurinsa, don idan yamazaune intaxo gurin a take yake barin gurin, shiyasa take quntatawa NANA tanan kadai takesamun sauqin yanda qunci ke cinta a ranta.


Taje gurin Ayashe, tasanar da ita matsalar da take fuskanta, itako Ayashe, haka tayita karban kudadenta dasunan tana karbo mata magani, haka zataita zana mata yanda zatayi amfani dashi amma duk a banxa, a qarshe ma xuwa yanxu batada kudi a hannunta Dan kadarorinta ne daya ragemata, taketa dauka daya bayan daya tana saidawa.

Sadiya kuwa ahalinda ake ciki ba kasafai take zaman gidan ba, bin maxa takeyi na fitar hankali Wanda ita kanta mamakin abun takeyi takanji takaicin yanda tamaida kanta kariya, jakar gayu, har kuka takanyi wani lokacin idan maxa suka wulaqantata, da kudinta take bin wasu daga cikinsu amma suqi kulata..


Wata mata nahango a tsugune tanata kelaya Amai tamkar xata amayar da kayan cikinta, saida naleqa na hango fuskarta Zainabu nagani tagama fita a hayyacinta, tayi wujiga wujiga da ita, fuskarnan fayau kamar batada jini a jikinta, datti kuwa kamar xa'a kankara a jikinta, kannan babu dankwali gashin da kallonsa kaga alamar kwarkwata sunsamu gidan zamansu.


Tagama galabaita matuqa, komawa tayi taxauna tana dafe cikinta, fashewa tayi da kuka meqarfi a qarshe tamiqe dagudu tabar gurin tana gudu tana fadin Menai maka da qarfin gaxke.

Wnn sunan yariga yabi ta idan yara suka ganta binta sukeyi da gudu suna ihu sunacewa da ita Menai maka, itama tana nanatawa. Suko suita dariya...


*Bayan kwana Biyar*


Kamar yanda yasaba nufo gidan haka yauma abun baicanxa zaniba, fuskar nan babu annuri yashigo tare dayin sallama murya can ciki, bakowa a tsakar gidan sai NANA da take ta aikace aikacenta, amsawa tayi tareda qarasawa gurinshi cikin Sauri domin takarbi kayan dake hannunsa.

Daga mata hannu yayi alamar karma tafara qarasowa gurinsa, turus tayi ta tsaya, shikuma yanufi dakin Lami kai tsaye, A kwance yasameta tayi dai~daya akwance tanata baccin asaran data saba..

Qafarta yadan zungura tamiqe a firgice ganin shine yasata saita nitsuwarta don tana mugun tsoron abunda xai hadata dashi, don da dukkan alamu qiris yake jira ya saketa, itakuwa bata fatan hakan, baxataso abunda xaimaidata rayuwarta ta baya ba, itakadai tasan wahalan da tasha, yanxu kuwa ko banxa tanasamu taci sau uku. A rana.


Kallon wulaqanci yay mata kapin daga baya yafara mata magana cikin salon umarni.

Lami Aure zanqara bangayamiki domin jin shawarar ki ba, nagayamiki ne donki tattara ki koma dakin Sadiya da kwana dagake har Nana kuhadu a can.

😳🙉 Nashiga uku tafada da qarfi Aure kuma? Meya faru, menai maka, waxaka aura, duka tambayoyinnan taita jero masa su, shidai baiko bi takanta ba yayi waje tareda tabbatar mata karya dawo yasameta a wnn dakin.


Bashiri bakinnan duk miyon bacci tafito da gyale a hannu tanupi gidan Ayashe hajaran majaran.

Samun Ayashe tayi taci uban kwalliya harda qunshi a qafarta abunda tajima bata gani ba ajikin Ayashe, amma ba wannan bane a gabanta, damuwarta asamo mata mafita.

Ko gaisawa bata jira sunyiba tahau arattako mata abunda yake tafe da ita, cikin ran Ayashe fari tas, amma fuskarta a murtuqe tace abunda yay miki knn? Eyyi wlh tabata amsa

Lallai mal Habu ya tsokalo tsuliyar Dodo, kinsan mexamuyi? Inajinki tace mata, kikoma gidanki kiyi zamanki a dakin Jibi insha Allah xan xo miki da wani maganin..

Haka xa'ayi Ayashe? Mexai hana muje yanxu gurin sabon malamin da kikace min kinyi? To kikawo dubu Ashirin yanxu mutafi, dubu ashirin? Tafada tareda dafe qirjinta, wlh Rabona da samun irin wnn kudaden harna manta, ni yanxu kudina ciki da waje dubu uku ne.

Ayashe tace to kinga dole kiyi haquri ki saurarre ni, jibi xan kwashi Adashena inyaso sai inmiki amfani dashi, nasan idan lamuran suka daidaita kya dawomin dasu.

Washe haqoranta gaba daya tayi snn tace wlh harma da qari xanmiki Aminiya ta, kinmin komai arayuwa kece silar shigana jin dadi, Niko mexan miki in biyaki alheran da kikamin na rayuwa?

Kibari sai Jibi innaxo xan gayamiki, abinci Ayashe tamiqo mata, qinci tayi saboda tsabar murnan da take ciki, taimata bankwana tadawo gidanta.


Dawowanta gida hankalinta kwance tadauko dubu ukun da yarage mata adakin, takira Nana ta aiketa taiyo mata cefanen kayan dadi, tunda yanxu tanada tabbacin nanda jibi duk al'amarin nata xai daidaita kudi xaidawo hannunta yanda takeso.

Washe gari da safe tafito domin baiwa Sadiya kayan abinci don haryanxu saita gwada mata takeyi, ganin qartin maza tayi suna shigowa kai tsaye Aqarshe kuma maigidan yabiyo bayansu.

Cemusu kushiga wnn dakin kufito da duk kayan ciki kushigar wnn yanuna dakin Sadiya da hannunsa.


Ashar lami tafariyi shiko baiko kalleta ba, nan ta ari hauka ta dorawa kanta taita surutai da zage zage, harta isa gabanshi da niyyar cakumo Wuyan rigarsa, wani kallo dayai matane yasata tsayawa cak, batai gaba ba batai bayaba, nanyabada umarnin a wullo mata da dukkayanta waje, intai niyya ta shigar inbatai niyya bakuma tabarshi a gurin..

Snn yacewa Nana takwaso kayan dakinta tashigar dashi dakin Sadiya, sauran na mamanta kuma tabarshi yarato da dillali xa'ai gwanjonsu, dasauri tamiqe tashiga dakin tahau tattara kayanta inda a can qasan akwatin mamanta tacikaro da kudade masu yawa a qalla xasukai dubu shabiyar, dube dube tayi taga bawanda hankalinsa yake kan dakinnasu, cikin Sauri taninkeshi a bakin zaninta dakyau, snn tafara daukan kayan taiyo waje dashi..


Sukuma maxan basuy wata wataba suka fara kwasomata kayayyakinta suna watsowa waje ganinda tayi dagaxke nepa, yasata Shiga ciki dasauri tafara tattare kayayyakinta na sirri Wanda baxataso kowa ya ganiba, dayake majiya qarfine cikin mintuna qalilan suka kammala snn suka fara shirin gyare gyarenda yakawosu.


Mal.Habu bayan yagama nunamusu aikinne da yanda yakeson fasalin gurin yakasance, dakin Lami ne yakeson ahade mishi itada dakinsu Nana suxama ansamu ciki da falo, akuma yi rumfa ahado shi ta cikin gurinnata.
Nan yafita yy wucewarshi kasuwa.

(Sukuwa su Lami damacan dakin sadiyan gurin ajiyace batada girman zuwan Lamine yasa aka mayar dashi daki., zamuga yanda zaman dakin xai kasance)

itakuma lami juyowa tayi taga Nana tana shirin shigarda sauran kayanta ciki, firgitaccen tsawa tadaka mata tareda cewa karki kuskura kikai kayanki cikinmu kidauki tsummokaranki kikai cikin Madafi, kidawo nikuma kishigarmin dakin Sadiya kishirya mini, nabaki minti Ashirin ki kammala kidawo kicigaba da girki.

Haka Nana tacigaba a aiki baji babu gani, Lami duk da ranta babu dadi, amma tabar komi a hannun gobe, jiran Ayashe kawai takeyi ta iso mata da maganinta.

Har dab da mangariba masu aikin suka kammala snn suka tafi, Nana bata jira aka gayamata abunda yakamaceta ba, tafita tahau kintsa guraren cikin qanqanin lokaci tagama bayan ta kamar sara mata shi akeyi tasan al'adar ta ne yake shirin xuwa, bayan tagama tadebi ruwan zafi tashiga bayan gida domin wanka.

Amma amaimakon wankan saita buge da kuka, kullum rashin mamanta sabo yake agareta, takasa sabawa da rashinta, tasan inda Mamanta tananan duk wuya aikin baxai kai hakaba, snn xataje makaranta, amma yanxu bata leqa koda qofar gida Lami tahana.

_WASHE GARI_ da safe wasu mutane sukaxo akaita jeren kayan Amarya lokacin Lami bata gidan tashiga maqotansu anyi haihuwa kapin tadawo harsun gama sun kulle gurin, fitowanta daga maqotan sukuma sunshiga adaidaita bata samuganin ko daya daga cikinsu ba, Sauri tafarayi ta iso cikin gidan, nan ta Taras da abunda sukayi Yakuma bata amsar tambyarda Zuciyarta keyi, don ta tabbatar Jere akayi.


Haka taxauna aranar ko abinci takasa ci, tagama qaguwa daga shigowan Ayashe amma har yamma shiru, haka ta haqura akan gobe da sassafe xatai mata Asubanci.


Guraren qarfe takwas tafarjin hayaniyar mutane batai yunqurin leqa wa ba, don tafison sai an watse ta iskota har dakinta tacimata zarafi kapin tacigaba fuskantar baraxana tunda tahada kishi da ita.

Jin hayaniyan ya lafa ne yasata miqewa tayi dakin Amaryan.............



😍😍🤝Anatare
Mummyn Fadyl CE




🎲🎲TUDUN DAFAWA🎲🎲


Rubutawa....MUMMYN FADYL (Fatyma Muhammad Adamu)

Wattpad @ *fatimamuhammadadamu*


INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION*
*[onward together]*
*{we give the reader's of ours the best out of the bests,, our inks are melodious and dropping a kinda lights to reader's}*
```THE PEN OF LOVE😘 HEAT TORCHING❤ TEAR OF SORROWS😭 CURDLES😊 GIGGLES😁 AND MARRIEGE THINK💑```
*```JUST GIVE US FOLLOW..**

_Kuimin Afuwa fans dina, nayi muku alqawarin daily post amma jiya kunjini shiru, hakan yafaru ne sakamakon yanda nakejin raina babu dadi, saboda rashin lafiyar MAHAIFIYATA, amma Alhmdllh jikin dasauqi duk da haka ina buqatar addu'arku domin dorewar lafiyarta kunsan lafiyar mahaifiya shine komai_

*WNN SHAFIN NAKUNE MASOYAN LAMI QAYA SOKI UBAN KOWA😜*



Fitowa ta. 2⃣4⃣


Sai da ta isa gab da dakin kuma taji faduwan gaban xuciyarta ya tsananta, amma haka tadaure saidai batasan meyasa ba taxo daniyyar hankadowa dakin batare da Neman izini ba, saikuma taji dakin yamata wani mugun kwarjinin da baxata iya aikata hakan ba.

Sai gata ta bige dayimata sallama cikin qasqantar da murya, A'ah Lami dadina dake rashin haquri taji muryan Ayashe ya doki kunnenta.

Wanakeji kamar Ayashe? Bata tsaya bata amsa daga ciki ba, taiyo waje.

Ayashe kedai naita jiranki tun safe bangankiba snn yanxu kishigo gidan baki isoni ba kishiga dakinta, tafada da alamun bacin rai a fuskanta,

Itako bata tsaya bata amsa ba tadai kafeta da idanuwa kawai hakan yabata damar cigaba da magana.


Haba Ayashe banyi tunanin xakiymin hakaba, keda xamu hada kai mu yaqi matar kuma Sai in sameki a dakinta mekikeyi to? Tafada murya qasa qasa.


Saida tajira takai Aya snn tace mata ai ba tayata nakeyi ba, asalima nice nakewa kaina yaqin aiba kowa a dakin nikadai ce.

Lami kuwa bata dauki maganar da wata manufa ba, saice mata tayi, to ina Amaryan taje? Kodai maganin kika sa mata? kai bangane nupinki ba.

Ayashe kuwa saida ta qanqantar da idanunta snn tace mata,
kedai Lami bansan daqiqiyar ina bace Akwai wata Amaryan da tawuce nine? Kibude kunnenki dakyau kisaurareni nice sabuwar Matar Habu Baban Nana ba wata ba, yanxu shawara daya xanbaki tunda mutunci da arxiki kinemi takaddan sakinki a hannunsa tun dare bai miki ba, don da shirina naxo.

Lami kuwa Sai cewa tayi Ayashe yaufa ba ranar wasa bace, kinsan yanda xuciyata take min kuwa, kirasa ranar da xakimin wasa Sai yau?

Ayashe bata tsaya wata wataba ta tsinketa da wani gigitaccen mari Wanda yasa kwakwalwarta tafiya aiki na wucin gadi, idanunta kuwa duhu tagani tareda wasu taurari Wanda hakskensu yafi na Zara tauraruwa..


( maqiyan Lami nasan kunji dadi to wlh xan rama mata ne ehen 😜)


Muryan Ayashen ne yadawo da ita daga wnn duniyar inda takece mata wnn shine somin tabin uqubar Dana tanadar miki a wnn gidan, ina fatan kin farfado daga suman da kikayi...


Lami kuwa mamaki ne yake Neman halakata a gurin tamkar mutum mutumi haka ta tsaya, takasa fadin komai tsabar mamaki, Tsawa Ayashe ta daka mata Wanda yasata kusan kifewa batareda tashirya ba, itakuwa Ayashe ganin haryanxu lami bata dawo daidai ba yasata komawa cikin dakin inda tadauko ruwanta me sanyi data Adana don xubawa mal.Habu magani aciki.


Taiyo waje dashi, Lami tananan tsaye a
Gurin, Sai sauqan ruwa me shegen sanyi tayi a jikinta, firgigit tayi nan tasamu tadawo hayyacinta snn gaba daya maganganun suka tarayo xua cikin kwakwalwarta tareda sarrafa mata manufarsu...


Aiko nan itama jarabar masifarta ta motsa tafara xuba mata manya manyan Ashar, snn tace ke harkin isa ki munafurceni in kyaleki? Ki auremin miji, kina tunanin xan barki ne Ayashe, to kinyi qarya wlh baxai yiwuba dole kibarmin gidana.


Sheqewa Ayashe tayi da dariya kapin tace wai miji hahahhaah idan Ana maganar miji aikema baxakisa bakiba tunda a hannun wata kika kwaceshi, nikuwa kinsan karban goruba a hannun kuturu abune mai matuqar sauqi ko kin manta ni shugabanki CE a hatsabibanci?

Dakike maganar munafurci kuwa kisaurareni kikuma bani kwanaki kadan wlh xaki tantance tsakanin Aya da tsakuwa domin Wanda yarigaka bacci dolene yarigaka tashi, kinsan Allah Lami matuqar bakibar gidannan tun ana iya gane kamanninki ba to xansa kibarshi lokacinda kika xama abun kwatance taqarashe maganar nata tareda hankadeta snn tayi cikin dakinta takuma banko qofa.

Lami kantane taji yana juyamata , da kyar tasamu takai kanta dakin Sadiya inda tasamu Nana a kwance a tsakar dakin tana baccinta amma mafarkin kuka takeyi.

Aiko kamar Allah ya aiko Lami haka tarufeta da duka, baji bagani tun Nana tana iya ihu har abun ya gagareta, shiru tayi tacigaba da karban saqonnin dukan aduk kusurwan jikinta.

Don kanta tagaji tadaina takoma gefe taxauna tana maida numfashin azaba, rasa mexatayi tayi a wnn lokacin hakan yasata cewa Nana baxata kwana tareda ita a dakin ba, don haka takoreta waje gashi lokacin sanyi ne...

Haka tafito qofar dakin ta shimfida fallen zaninta takwanta tareda duqunqunewa guri daya, amma kamar qara kado sanyin akeyi gurinta, kamar tagudu tabar gidan takeji.


Itako Lami kwanciya gagararta yayi nan tahau safa da marwa acikin dakin data gaji da hakan ne taleqo da kanta ta taga, aiko idonta yy muguwar gani, don hango Mal.Habu tayi xai wuce hannunsa dauke da ledoji niqi niqi kowanne a sheqe da kaya, kamar tabishi ta kwace haka takeji amma inaa wani masifaffen tsoronsa da jarabarsa ce ta dirar mata lokaci daya.

Shikuwa ta gaban Nana ya wuce amma baiko luraba balle yagane mutum be a kwance, dakin Ayashe yayi wa tsinke, inda takuma ta tabude mishi qofar daga ita saiwata shedaniyar Riga, dake jikinta Wanda tsayinsa baiwuce guiwarta ba, A lalace yake kallonta duk ya shagalta, cikin kissa takarbi ledojin hannunsa, tareda jawoshi ta rungume shiko tsintan kansa yayi da biyemata saboda dokinta dayake ji.

Sunjima ahaka kapin tafara zare jikinta, fita waje tayi tahada mishi ruwan wanka, snn tasanar miqews yayi xainufi bayin tariqo hannunsa tabaya tsayawa yayi itakuma tajuyo snn tace mishi, ina xanbarka kaje kayi wanka batareda na taimaka maka ba saikace badan gata ba?

Yanda kikace hakan xa'ayi yafada ciki washe bakinsa, bata jira cewarsa ba taja hannunsa xuwa bayan gidan, bayan yacire kayansa ne ta shagala da kallon qasansa, a ranta tace ahhh lallai Lami dole kikasa barin Habu da wata macen, hummm aiko kinyi bankwana dashi har Abada.

Aibatasan lokacinda takai musu cafka ba cikin marmari da zumudi nantake yaji yafara kawo wuta don cikin salo take murza mishi su.

Cikin Axama yariqota bata mata mishi lokaci ba, donkuwa itama ta mugun yabawa da kayan aikinnasa, nan suka fara aika ma junansu saqon da yake azalzalan xuciyarsu saboda sungama zaquwa sujisu a matakin qarshe baisan lokacinda ya sabota domin yiwowa daki da itaba, yayo daidao da fitowan Lami domin sauqe sauran haushinta akan Nana acewarta ta isheta da sheshsheqar kuka.


Mutuwar tsaye tayi xata gansu, ai bata San lokacinda ta ari hauka tai Kansu ba amma kapin ta cimmusu sun shigo dakin, itako Ayashe taganta don haka suna Shiga ta diro tabanko qofar tareda sako sakata. Takoma gurin mijinta suka baje a gado, bantsaya ganin me xasuy ba don 'yan _Intelligent writers group_ sun hanani fadin komai.

Buga qofar tayi har hannunta yafara zafi, gashi banda nishinsu babu abunda take jiyowa hakan yaqara tunxurata ga kishinda take cin xuciyarta, yanda takeji matuqar tacigaba dajin wnn abubuwan to wlh tanada tabbacin xata iya rasa rayuwarta don ba shakka xuciyarta fashewa xatayi.

Dataga babu me saurarontane yasata juyowa kotakan Nana batabi ba tai shigewarta daki, itakuma Nana hakan baqaramin dadi yai mataba, takoma ta qudundune jikinta takoma bacci.

Lami yanda taga rana haka taga dare inda a fannin su Ayashe kuma suka more wnn daren (kunsan Ayashe 'yar bariki ce tasan kan harka)

Washe gari da sassafe Lami tafara kicinyar karya gadonta da sauran tarkacenta domin kaiwa gidan dillalai saboda tanada buqatar kudi sosai, akan Sadiya takeda tabbacin samun kudi a yanxu, amma rabonda tahada ido da ita yau kwana goma sha biyu knn, gashi al'amura sun cakude mata. .

Tana cikin aikinne taji cikinta ya isheta da qugin yunwa, bashiri taiyo waje domin ganin me Nana takeyi har xuwa yanxu bata kawo mata abun kari ba.

Samun NANA tayi a tsakar gida da Allon karatunta a hannun ta, ke Nana menake gani haka ina zakije, waya baki umarnin shiryawa xuwa makarnta?

Nana tana shirin yin magana Ayashe tafito cikin shiga mekyau taci uban kwalliya cikin dinkin Riga da zani, fuskarnan tasha fente fente irinnasu na 'yan bariki, tana taunar cingam kawai qas~qas kakeji.


Cikin yauqi tafara magana, Ke Nana wuce kitafi makaranta, snn inkintaso dakina xakishigo akwai aikinda xan saki, Itako kamar jira takeyi tayi waje kamar ana hankada ta.

Juyowa gurin Lami tayi tace mata dama nasan xaki fito kodon cikinki ma, to bari kiji daga rana irinta yau bakida abinci a gidannan kalli can tanuna mata gefen dakin Sadiya, kwanukan ta tagani axube kaca kaca.

Tamaido dubanta gurin Ayashen to wadannan kwanukan baxasu shiga min madafi ba, to banda abinki ma Lami mexakiyi da kwanuka tunda ba girki xakiyi ba? Aikeda girki a gidannan saidai idan nice nacemiki kifito ki karba, don haka yanxu tamkar zaman kanki kikeyi daga haka tabarta agurin.

A take xuciya ta kwasheta tai cikin dakinta mayafi kawai tadauka tayi waje...


Zainabu ce a Zaune akan Bola tadauko rubabben buredi tanaci tana kuka tana fadin menai maka? Kwari ne sukebin jikinta Wanda yasata taketa qaiqaya jikinta babu sassauci banda datti babu abunda take kartowa, faracunta sunyi zaro zaro kamar na tsoffin arna.

Wata hadaddiyar babbar motane tai _parking_ gefen bolan dayake yamma yayi sosai harma anshiga sallan mangariba, nacikinne yacewa direban itace wancan yanuna Zainabu A hankali xakai mata don xata iya fallawa aguje.

To Ranka ya Dade, nan yafita yanufeta a hankali amma.............


*plx idan kanada shawara kokuma kaga abunda baidace ba kuma kanada buqatan gyara drop it here, banda cin mutunci plx*


😍😍🤝🏼Anatare
Mummyn Fadyl CE




🎲🎲TUDUN DAFAWA🎲🎲


Rubutawa....MUMMYN FADYL (Fatyma Muhammad Adamu)

Wattpad @ *fatimamuhammadadamu*


INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION*
*[onward together]*
*{we give the reader's of ours the best out of the bests,, our inks are melodious and dropping a kinda lights to reader's}*
```THE PEN OF LOVE😘 HEAT TORCHING❤ TEAR OF SORROWS😭 CURDLES😊 GIGGLES😁 AND MARRIEGE THINK💑```
*```JUST GIVE US FOLLOW..**


*Yawan comments dinku shixaisa nidaku musamu yanda mukeso baxan boyemuku ba yanda kuke nunamin qauna yanamin dadi harna rasa ta yanda xannuna muku inajin dadin hakan matuqa* _masoya na kune silan yin murmushi na👯🏽‍♀_

~Jiya nasanar daku mahaifiyata babu lpy, ajiyan naga texts dinku via SMS dakuma social media nakuma ga kiranku nagode sosae Allah yabar qauna, she's getting much better~


Fitowa ta. 2⃣5⃣


Yana isowa gareta itakuma aka bata umarnin guduwa daga gurin don haka tai wurgi da guntun rubabben burodin nata, sauri yayi ya isa gurin tareda taliyeta da qafansa nan taxube tafadi...

Kallonshi tafarayi tareda furta masa Menai maka? Baikulata ba yafara qoqarin janta amma taqi binshi ganinda yayi zata bata masa lokacine don gashi wasu masallatan har sun idar, yasan yanxu xa'afara fitowa, aiko cikin sauri ya sungumeta inda wani qarni da hamamin datti ya ziyarci hancinsa, dakyar ya qarasa da ita gurin motar.

Mai gidan nasa yana ganin ya iso da ita ya fito yakoma gaba, shikuma yasata agidan baya, kalle kalle takeyi tana kuka, saida yarufe snn yadawo gaba yaxauna, sannu idi yafada shikuma yace bakomai megida ka cancanci haka, amma megida gani nakeyi kamar pa wnn tanada ciki, haba dai? Yafada cikin jindadi.

Allah kuwa tanada ciki don kuwa harya dago ma, haskata yayi nan yahango tumbinta daya fara tasowa saman riganta, farinciki ne ya dabaibayeshi. Yasan xaisha garabasa, ga hauka ga ciki, dadi kan dadi.

Iskan motane yasata bacci batareda tasani ba tana riqe da kanta data dorashi jikin glass, kalar tausayi da ita.


Alhaji Ado dai mutumin garin Kaduna ne, kuma shahararren Dan siyasa, Wanda yayi amanna da tsafi, yagama yarda cewa da tsafinsa dukkan sa'a take cimmishi.

Acikin wnn halinne siyasarshi takusa rawa, nankuwa Bokansa yabashi tabbacin duk bayan sati biyu yana kwanciya da mahaukaciya sai uku akwana uku, inko bahaka ba, yana gab da rasa kujerarsa harma da rugujewar duk wani abunda ya mallaka.

Shiko gogannaka tunda yataba yaji ai gabadaya mahaukatan ma sunpi masu hankalin dandano.

Kamar yanxu ma dawowarshi daga Maradi kenan cikin nijar, yakaiwa BOKANSA xiyara sakamakon kiran gaggawan da yamishi, shine yabiyo ta katsina domin gaisawa da abokinsa, yahadu da Zainabu a bakin kasuwa yara sunabinta.

Tundaga wnn ranar yake bibiyarta, daga sun Dana mata tarko xata wargaxa, don saika gama sakankancewa xaka kamata xata xura a guje, kapin qiftawar ido kuwa baxakaga inda tabi ba.

Hakanne yasa yau suka shirya yimata dabara, aiko sunci sa'a sun sameta.
_WNN KNN_


Lami xuwa tayi tasamu dillaliya domin ayi gwanjon kayanta, inda tabiyota har gidan taduba kayayyakin, tunawa datayi da kashedin Ayashe yasata tattarowa harda kwanukan a tunaninta in burinta yacika tasai sababbi daman tagaji da wadannan.

Bayan tagama dubawa tacewa Lami gabadaya kayan tamusu kudi naira dubu talatin, Talatin Lami ta fada cikin daga murya, Haba Indo bafa kayan sata bane, yaushe mai nai kayan, basu ji jiki ba kece shaida.

Ni inma badon inada buqatar kudiba a yanxu babu abunda xai sani sayarda kayayyakina don inason abuna matuqa.

Kinsan kinaso kika nemani Indo ta katseta, nan Lami ta sassauta murya tafara roqonta akan taqara tunda kayan da mutuncinsu, amma Indo qirmisisi taqi qarawa, daga qarshe ma cewa tayi Lami bata shirya sayarda kayan ba taga tafiyarta.

Saurin shan gabanta Lami tayi don tafi buqatan kudin snn tace mata kitaimaka min koba yanxuba kimin alqawarin qaramin wani Abu akai, a'ah wlh Lami baxan qara komai akan talatin dinnan ba, kinga inafa da aiki agidana kika daukoni inason komawa, tafadi tareda nufar qofar fita

Kawo kudin to Lami tafada cikin halin narasa yanda xanyi, nan Indo dillaliya ta irgo kudin tamiqa mata tareda cewa anjima xata aiko a kwashe mata kayayyakin.

A cikin kudin Lami taxari Dari biyar tasamo almajiri yasayo mata kayan shayi a gurin masu teburin shayi tasamu takarya snn tajita dai dai.

Wanka tafito yi amma wlh haka tanaji tana gani ya gagareta saboda Ayashe cemata tayi ai tagama yin wanka a bayin tun kapin xuwanta, saidai tajira da dare tafito tayi a tsakar gida. Inko ba hakaba ta dauwama cikin tsami babu abunda yadameta tayi wucewarta.

Itako yanda tasan wulaqanci da rashin mutuncin Ayashen ne bashiri ta wanke qafafunta tashafa musu Mai snn tadauki dubu Ashirin a hannun ta ta adana sauran canxunan nata snn tanufi gidan Maye.

Ayashe ko tasan Lami tasaida kayanta gaba daya domin tafiya gidan bokane ( kunsan ance mugu shiyasan makwancin mugu) kuma tanada tabbacin baxata Debi dukkan kudin takai mishi ba. Shiyasa tana ganin fitarta tayi cikin dakin batasha wani wahala ba ta tattare canxunan gaba daya tayi gaba dasu tana shu'umin dariya, badon tarasa kudin bane yasata kwashewa lami nata, itadai burinta yanxu taga Lami a wulaqance.


Lami tana isa gurin maye tasanar mishi gaba daya abubuwanda suka faru bata boye masa komai ba, nan yahau surkullensa shikanshi yana mamakin meyasa yanxu indai yatashi aiki to baya ganin komai, haka yanxu ma al'amarin Lami gaba daya a kulle yake baiga komai ba. Amma haka yake dikake yake basu magunguna duk da yanada tabbacin baxasuy musu amfani ba, yaxaiyi shima tahakan yake samun abincinsa.

Saida yagama abubuwan tsafinsa snn yamiqo mata garin maganin akan ta barbada abakin qofar dakin Ayashe da rana xata barbada kuma karta kuskura a ganta. Da tsorata xa sharadinda ya gindaya mata amma tunda Neman biyan buqata takeyi saitaji ai xata iyayin komai.

Tafiya sukeyi gaba jeji baya jeji motar tayi tsit bacci Mama takeyi inka kalli fuskarta Bacin datti xakai tsammanin hankalinta daya don bacci takeyi cikin nutsuwa.

Jifa

Please Login or Register in order to submit comment