You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Ranar wanka ba'a boyan cibi, baxan Boye miki ba Nakamu da qaunarki dakuma qudirin son Tallafawa marayunki, bansan Yaya xaki dauki batun nawa ba, amma nidai gaxkiya inada burin inga na aureki, aganina dake kadai xan iya hadawa da matana batare da fargaba ba kodon Amincewa da juna dakukayi.



Amina kuwa machine ta hau don aganinta adaidaita baxatai mata saurin isa ba, tana isa kasuwa taiwa shagon Mal.habu dirar mikiya, saida ta isa gab da shagon talura a rufe, gurin maqocinsa tanufa bayan sungaisa ne take gayamishi taxo gurin Mal.Habu ne, anan yake sanar mata suma yanxu suke ta'ajjibin tafiyarsa cikin tashin hankali batareda yasanar da su ko kuma yaron shagonsa inda xashi ba. Tunaninta yagama karkata kancewa yatafi asibiti don haka tafito takoma asibiti, isanta ta tarar nanma baizoba, Dora hannu tayi aka! 🙉. Jitake kamar takurma ihu don tashin hankali, taduba gabas taduba yamma bata samu makama ba, candai tayanke shawarar xuwa gida takuma dubawa.


Kallon yaudara tabi Mal.Habu dashi snn tace Haba Mal. Meyasa kayi wannan tunanin wannan ma ai cin Amanace jama'a xasu kalleni a matsayin wacce batasan halacci ba, bugu da qari ma baxan iya aurenka intare inkuma bar 'ya'yana ba,nanfa tafashe da kuka, tana fadin Allah yajiqanka baban Isah harda fyace majina na munafurci.

Dakyar Mal.Habu yashawo kan Lami ta amince inda atake yaji kamar ansauqe mishi nauyi ne akansa, gyara tsayuwarta tayi snn tace to Mal.Habu aiya kamata mushiga daga ciki koruwa kasha, washe baki yayi yana cewa oh to badamuwa muje, haka yabita kamar raqumi da Akala, itako tana gabansa tana juya jiki ~dafuska kamar angoya kare ya waigo~


Amina ta iso gida nanma bata sameshi ba, don haka tawuce can gidansu domin sanar da iyayensu.


A asibiti kuwa ganinda sukayi Zainabu tana Neman rasa rayuwarta ne, gashi kuma Babu wani nata dayazo, yasasu yanke shawaran shiga da ita.


Angama shirya ta saura aturata dakin tiyata kawai akaji tafara qoqarin _Pushing_ nanadanan aka maidata _labour room_ ta matuqar shan wahala inda a qarshe ta sunbulo yarinyarta mace kyakykyawa fara Sol.

Isan Amina gida tasamu iyayen su tasanar dasu halinda ake ciki, cikin gaggawa suka shirya suka nupi asibitin, isarsu suka taras ta haihu murna a gurin wadannan zuri'a biyun ma bata lokaci ne, wannan yadau yarinya wannan yadauka..... Mal.Jafaru ne yafara tambayarta ina Habu rasa amsarda xata bashine yasata kawar da kanta gefe, hakan datayi yanada nasaba da kunyar da takedashi shiyasa baidaukeshi amatsayin komai ba....

Anriqe Zainabu a asibitin saboda tana buqatar kulawar likitoci domin jinyatuwa, Zuwa Yamma suka watse akabar Amina tareda ita, amma kowa hankalinsa atashe saboda tunanin inda Mal.Habu yake, saboda ba qaramin Abu bane xai hanashi xuwa asibitin saboda kowa yana sane da soyayyar dake tsakaninsu.


Mal. Dahiru da Mal.jafaru ne suma sukaje kasuwa, abunda aka sanarda Amina shi aka sanar dasu, gidansa suka nufo isowarsu yayi daidai da fitowarsa daga gidan Lami atare da ita fuskarsa kana kallo kasan akwae farinciki me girma atareda shi....

Junansu suke kallo kapin suka maida allonsu kansa, inda shikuma yayi kamar baigansu ba, Mahaifinsa ne yakirashi cikin tsawa juyowa yayi ya kalleshi yace...........





🎲🎲TUDUN DAFAWA🎲🎲


Rubutawa....MUMMYN FADYL (Fatyma Muhammad Adamu).

Wattpad@ _fatimamuhammadadamu_



*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION*
*[onward together]*
*{we give the reader's of ours the best out of the bests,, our inks are melodious and dropping a kinda lights to reader's}*
```THE PEN OF LOVE😘 HEAT TORCHING❤ TEAR OF SORROWS😭 CURDLES😊 GIGGLES😁 AND MARRIEGE THINK💑```
*```JUST GIVE US FOLLOW..**


*Masoya na inajin dadin comments dinku daga na watxapp har na wattpad ba abunda xan iya cewa daku sai dai ince Allah yabar qauna.*


Fitowa ta.1⃣1⃣


Joyowa yayi ya kalleshi yakuma kalli mahaifin Zainabu snn yace dasu sannunku da zuwa, baiqara bi takansu ba yayi shigewarsa cikin gida.

Cikin fusata Mal.Dahiru yayi yunqurin binshi cikin amma Mal.Jafaru yace dashi haba menene haka kake shirin yi? Mujirashi muji uzirinsa a iya sanina Habu baitaba aikata mana makamancin irin hakan ba.

Haba Jafaru har Habu yanada uzirinda xai hanashi sauraronmu dayi mana duba ta arxiki yafadi hakan da kunfan baki, saboda ranshi yayi matuqar baci, duk abunnan dasukeyi akan Idon Lami ne, ta tabbatar yanxukam aikinta yagama ci tunda hatta iyayensa yana daidai dasu.


Fitowa yayi yana qoqarin rufe gidan batareda niyyar sauraronsu bane yasa Mal.Jafaru isa gareshi da sassarfa tareda fusgo bayan riganshi, tareda cemishi Habu kana cikin hayyacinka kuwa kagane dawa kake tsaye?

Can qasan ransa yarasa menene yake damunsa yau mahaifasa yake yiwa wnn wulaqancin amma a saman zuciyarsa jiyakeyi yana daidai da kowa, don kuwa Lami kadai yakejin Abu gameda ita, bayajin xai sararawa kowa.

Inakaje har Amina taxo gidanka aka kai Zainabu asibiti baka saniba snn bamu ganka ba harmuka baro asibitin kai qarshema menene hadinka da matarcan mexubin 'yan bariki da har kafito daga gidanta?

Da wani irin fuska yajuyo yadubi mahaifinnasa, snn yace Baba bana buqatar rashin da'a ya gifta tsakanina dakai amma matsawar xaka zagi Lami kokuma ka kusheta to gaxkiya xa'a jimu daga hakan yayi wucewarsa inda shikuma Mal.Dahiru kanma ko kallon arxiki baisamu daga gareshi ba.


Kasa magana sukayi,sunkuma kasa matsawa daga gurin, daga qarshe Mal.Dahiru ne yasamu qarfin guiwar bawa Mal.Dahiru baki kapin suka bar gidan..

Bayan Lami tagama leqensu ne takoma cikin gidanta tadauki kudinda Mal.Habu yabata tanufi gidan Maye akan yarufewa kowa baki acikin xuri'ar Habu batason kowa yakawo mata cikas snn kuma sucire hannunsu acikin al'amarin zainabu.... Bayan yagama mata aikinne tadawo abunta gida.


A hanya bawanda yake iya yiwa wani magana harsuka isa gida ganin Mal.Jafaru baiyi mishi maganar komawa asibitin ba, yasa shima bai tanka masa ba ahakan suka rabu.


Bayan ya isa gida yasamu zuwaira tana tankade yasanar da ita halinda ake ciki, budan bakinta sai cemishi tayi, aiko tayo gadon wahala tunda uwarta ma haka tayi mtswwww wannan yarinya dai tana wahalarda mijinta ace tunda akai auren nan baihuta ba?


Allah yakyauta yafadi yasamu guri yaxauna, candai yagama tunaninsa, anbar asibitin babu kayan buqatan jaririya balle name jego, zumbur yamiqe yayi waje da harara Zuwaira tarakashi.


Shagon kusa dasu yanufa, duk da bawani qarfi ne dashiba, saya musu kayan sawa yayi na yarinyar kala hudu na daidai talaka, sannan yasayi kayan shayi, yaje gurin me nama yasama mata gasashshen nama har yana turiri yawuce asibitin. (Allah sarki iyaye)


Koda ya isa asibitin Zainabu itakadai ce yasamu a dakin tana zaune riqe da jaririyar tana kuka, itama yarinyar tana kuka, cikin sauri yaqara so garesu tareda cewa Zainabu meya faru ina aminan?

Ta tafi tacemin baxata iya hidimana ba, saboda ba qaramin Abu xanyiwa Habu yafita harkata ba, don Haka innemi meyimin jinya baxata iyaba, ta tafi abunta, tsayawa yayi yama rasa mexai ce mata. Can dai yasaki murmushin qarfin hali snn yace mata Zainabu kiyi haquri komai zaiwuce.


Menene yake faruwa tsakaninki da mijinki? Bata boye mishi komai ba tsanar dashi iya abunda tasani, haquri yacigaba da bata yana kuma riqeda jaririyar yana jijjigata harya samu tayi bacci aka kwantar da ita.

Miqo mata ledan da yashigo dashi yayi budewa tayi tana murmushi gakuma hawaye yana gangaro mata lokaci daya, nagode Babana bansan dawani kalma xanyi amfani dashi gurin nuna jin dadina ba, nasan A yanxu kai kadai karagemin _TUDUN DAFAWA_ kul Zainabu kar inqara jin haka daga bakinki taimaka miki tilashi nane, duk abunda nai miki ai maida ruwa rijiya ne.


Tisata yayi agaba tanadan cin naman ahankali dukda ba dadinsa takeji ba, saboda ciwonda ke bakinta, dare yayi yarasa dawa xaibarta ta kwana baxai iya tafiya gida yabarta ita kadai ba, can ya yanke shawaran kwana a masallacin da yake cikin haraban asibitin, bankwana yamata tareda cemata takula da yarinyar asuban fari xaishigo.

Wacce take gefen gadon tane takece mata kekuwa baiwar Allah kirasa maiyi miki jinya sai namiji wnn wace iriyar rayuwace saikace dabi'ar maguzawa🤔. Itadai batace mata komai ba asalima ko kallo bata isheta ba. Cikin dare tafarka da wata matsananciyar yunwa gadai kayan tea kam, amma kuma batada ruwan zafi balle Kofi da cokali, harwani jiri tafara ji yana Neman dibanta ya yasar a qasa.

Makwafciyarta ta roqa akan ta taimaka mata da ruwan zafi dakofi dakuma cokali amma fafur taqi, sai can tace mata xan iya sanmiki ruwan zafi amma baxan iya baki kofina ba don baxan iya hada baki dake ba...Duddubawa tayi taga batada komai daxa'a saka mata ruwan zafin kawai ta rarumo buta, tamiqo ko a jikinta haka ta tsiyaya mata aciki, itakuma tazuba kayan _tea_ din aciki ta karkada ta shanye Tass, snn tadawo cikin hayyacinta a take bacci me nauyi yayi awun gaba da ita.


Cikin dare kukan 'yarta ya tasheta, inda taketa tsala ihu ba qaqqautawa, haka tamiqe idonta na liqewa tsabar baccin wahala gakuma ciwon ciki, jijjigata tafarayi ga tarin da jaririyar takeyi dagani murane me qarfi ajikinta, saikusan asuba tayi bacci itama tasamu tadawo kan gadonta ta dorata akan qirjinta sukai baccin ahaka.


Yana idar da sallah yanufo cikin asibitin , lokacin shigowarshi suna bacci don haka zama yayi yadauki jaririyar ya rataya a wuyansa taci gaba da baccinnta, har gari yayi haske snn tafarka murmushi tasakar mishi inda shikuma tausayinta da qaunar diyarsa daya tilo yaqara dirar masa, ya tabbatar Zainabu nacikin jarabawa dakuma gararin rayuwa yanafatan Allah yabata ikon ci.

Likitoci ne sukaxo _round_ inda suka duba jaririyar suka kuma sanar dasu yarinyar tana dauke da _pneumonia_anason akiyaye mata amfani da ruwa me sanyi dakuma kwanciya a guri mesanyi, koda kuwa uwar ne saboda xata iya kwasan sanyin yarinyar kuma tasha a Nono.

A qarshe aka basu Bill dinsu gaba daya, dubu goma sha biyar ne ajikin takardan saida gaban MalDahiru yafadi saboda baida wadannan kudaden amma zaije gurin MalJafaru tunda bai isa tunkaran Habu ba, saboda hoton abunda yai musu rannan baifita a idanunsa ba, shi yasan bashi dashi amma kuma bayason raini da wulaqanci.

Gurin qarfe goma ya isa qofar gidan shi, baishiga ba yayi gidan Mal. jafaru sallama Yayi atare suka fito shida Habu, abun yabashi mamaki saidai kuma yaji dadin hakan don yasan dole nema Habu yanemi sasanci da mahaifinsa duba da irin nitsuwarsa.

Miqa mishi hannu yayi domin suyi musabaha amma mal.Jafaru yanoqe inda shikuma Habu yakauda kansa kamar baisan anti tsiron surukinnasa agurinba, lfy daiko tambayarda ya jefi Mal.Dahiru dashi kenan.


Uhum Takardan maganin yaciro a aljihunsa yamiqa mishi tareda yimishi bayanin komai gyara tsayuwarsa yayi snn yace dashi a gaxkiya nipa nadaina takurawa Habu akan Zainabu tunda shiya rigada yace gaxkiya bayajin dadin zama da Ita, bata kyautata mishi ga danbanxan qazanta, yanxu haka maganar da nake maka ya yanke hukuncin qara aure, ayau ba'a gobe ba. Kodayake ance waqa abakin meshi yafi dadi Habu yimishi bayani.


Juyowa yayi yace to ai Baba babu maganar bayani aikagama yimishi , saidai inqaramishi haske akai, maganar asibiti dai ga wannan yamiqo mishi kudi snn yaqara da cewa ba yau aka saba cimin kudi na ba ana fakewa da jinya to Agaxkiya nagaji da zama da Ita nakuma gama yanke hukunci abunda xan sanar dakai daya shine 😭😭😭






😍😍🤝🏼Anatare
Mummyn fadyl Ce



🎲🎲TUDUN DAFAWA🎲🎲


Rubutawa....MUMMYN FADYL (Fatyma Muhammad Adamu)

Wattpad @ *fatimamuhammadadamu*


INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION*
*[onward together]*
*{we give the reader's of ours the best out of the bests,, our inks are melodious and dropping a kinda lights to reader's}*
```THE PEN OF LOVE😘 HEAT TORCHING❤ TEAR OF SORROWS😭 CURDLES😊 GIGGLES😁 AND MARRIEGE THINK💑```
*```JUST GIVE US FOLLOW..**


_Kaso Asoka shine So, yanda kuke ji dani har cikin raina nima hakan nakeji a tare daku._
*much luv to yhew Dearie's*


Fitowa ta.1⃣2⃣


Bansan dai yanda zaka daukaba amma idan kaga xaka iya barin 'yarka tacigaba da zama a qarqashin inuwar aurena falillahil hamdu, idan kuma baxaka iyaba xaka iya xuwa ka karbi takardanta iyakan batuna dakai kenan.

Dattako mutunci dakuma karamci shiya hana Mal.Dahiru daukan mataki akan Habu Kai harma da mahaifinshi, saidai maida martani banashi bane.

Tafiya yafarayi batareda ya karbi kudinba, sobada lafiyar 'yarshi yafiye masa, koda xai rasa komai nashi xai nema mata lpy, kuma yayi alqawarin baxai karbi Sisin Habu ba.

Yajuya ga mahaifinshi yace BABA muwuce lokaci na qurewa, Mal.Jafaru ne yafara daga murya yanacewa daurin aure qarfe hudu da Rabi a babban masallaci, xaka iya zuwa. Ahaka sukayi gaba suna tattauna lamarin auren.

Gidansa yawuce Kai tsaye damasu aiki, yasa aka fito mishi da kayan Zainabu Tass aka share kitchen a shigar mata dasu ciki, dakinnata kuma akayi mishi sabon fenti domin zuwan Amarya😜


Shikuma _store_ dinsu aka qara budashi Yakoma dakin sadiya acikin gefen dakin Lami kuma akai mata _kitchen_ na zamani, itakuwa Zainabu batada kitchen dakinnatan ma ataure yake, asalima kayanta akan juna aka daurasu guri dai ba dadi atattakure haka.


Mal.Dahiru gidansa ya ratse inda ya tarar da bala'in Zuwaira kan cewa ina yaje ya kwana? Saboda bayason tashin hankali ne yasanar da ita halinda ake ciki bai boye mata komai azatonshi xata tausaya wa Zainabu amma saboda kafurcin zuciya irinna Zuwaira Hannu yasa Aka🙉 tafara kurma ihu nanda nan ta Tara mishi jama'a.


Bai fahimci me take nupi da hakan ba, saida kunnuwanshi suka fara jiyomishi abunda take sanarda mutane cewa, Mal.Dahiru yafara kwana da 'yarshi na cikinshi harta haihu mijinta ya gujeta, cikin gigita yafara nunata da 'yatsa baisan lokacinda jiri yakwasheshi yazube agurin sumamme ba.


Kanshi tayi a guje sauran mutane suka rufa mata baya, gangami akayi gurin kaishi asibiti, cikin qanqanin lokaci likitoci suka fahimci yasamu shanyewar barin jiki tagefen dama.

(Zainabu ta kade har ganyenta, masoyanta kuymin haquri balaipi na bane labarinne yaxo da haka)


********
Andaura aure lpy, inda Mal.Habu yakejin baitaba sa'a a rayuwarshi irinta yauba, saboda yamallaki abunda yake ganin babu abunda yakaishi tsada a fadin duniyar nan.

Ansa tarewa bayan kwana hudu, saboda bata gama shiri ba acewarta saita tatseshi tayi kayan daki masu kyau zata tare a gidansa.

Haka Zainabu ta wuni bataga kowa ba, mamakinta akan Bbn ta yatsaya saboda shikadai ne takeda tabbacin yanada kwakwkwaran dalilin da ya hanashi zuwa, tayi kukan taji kewar mijinta kamar tayi yaya.


Ga yunwa dayake cinta ga kukan yarinyarta daya addabeta, kuma sunce baxasu qara bitakansu ba harsai sunyi _Settling bills_ dinsu.

Batasan yanda xatayi ba, tana cikin wnn halinne kamar daga sama taji muryan maqociyarta , tana tambayarta meke damunta itakuwa a rayuwa, koda yaushe tana kuka?

Tsintan kanta tayi baxata iya Sanar da ita halinda take ciki ba, babu komai tace mata tana share hawayenta, kinga baiwar Allah kiyafemin abubuwanda nai miki Abaya, wlh nayi nadama haka Allah ya halicceni inada zafi.

Amma ina roqon alfarmar ki, kisanar dani komai nikuma zan taimaka miki, kinga sunana khadija nima haihuwan nayi, yarona ne Yake fama da matsanancin ciwon kai, Wanda bantaba tsammanin xa'asamu yaro dashiba Wanda gado ne yayi a gurina, Sunanshi *ALIYU* banason daurawa kaina damuwa saboda da xaran raina ya sosu to ciwon kannawa tashi yakeyi..


Zainabu ta tausaya mata, inda a take taji ta Aminta da ita, a wannan lokacin tasanar da ita komai, hawaye ne yawanke fuskar Khadija a take tamiqe tadebo mata abinci me rai da lafiya, takuma hado mata tea me kauri tamiqo mata.

Hannu baka hannu kwarya haka tayita cin abincin harta kammala Hamdala tayi snn tacewa khadija Nagode, Allah yabiyaki Amin inaso kidauke ni amatsayin 'yar uwa insha Allahu idan aka sallamemu koda har xuwa wnn lokacin baban naki baixoba xan rakaki har gidanku muje muji ko lpy...


*BAYAN KWANA HUDU*

Wadannan tsawon kwanakin sun kasance kwanaki mafi muni agurin Zainabu duk dama tanasamun taimako gurin Khadija sosae don bata barinta da yunwa, saidai takasa sanar da ita kudinda Asibitin ke binsu, bata kumasan yanda zatayi dasu ba, lokacin kwanta Biyar da haihuwa, dakanta tayiwa 'yarta Huduba da Suna Hafsat takuma yanke hikuncin kiranta da NANA..

Yayi daidai da ranar tarewan Lami, ta tare da yamma, fadin Rawar kai da Zumudin da Mal.Habu yakeciki ma shirmene dakuma bata lokaci, domin yamanta da Zaman Zainabu cikin kundin babin rayuwarsa,

Lami kadai yarage da Ayashe acikin quryan daki, kitabbatar a darennan kin shafemishi dukkan jikinshi dashi indai kikai hakan to wlh Yakoma tamkar Yaro qarami agareki yanda kikeso hakan xa'ayi.

Lami zankuma yimiki gargadin qarshe wlh axaman da xakiyi da Mal.Habu kika kuskura kika wulaqanta ni kokuma hanani wani abun daina ruguxa miki gaba daya shirinki snn intona miki asiri kowa ma yarasa.

Haba Ayashe ai baxa'ayi hakan ba, insha Allahu baxan tabayin abunda xai sosa ranki ba, tabe baki tayi tace yadai rage naki,snn taimata sallama ta tafi.

A asibiti kuwa adaren yau Zainabu tayanke hukuncin guduwa, saboda tagama sanin batada Wanda takeda shi daxai iya biyamata wadannan kudaden, saboda haka anayin sallan isha tagoya diyarta a baya, dama batada komai a asibitin sai kayan shayi da rigunan 'yarta, harda Wanda Khadija tabayar da sallahu aka sayo musu.


Kintsa kayan tayi takai waje can snn tadawo, khadija taleqa taga tayi nisa abacci, da hawaye a fuskarta ta lallaba tayi waje ahankali harta fita waje.


Tsugunawa tayi a gurin kayanta ta fashe da kuka tana fadin kuyafemin hakkinku dayake kaina balaipi na bane banida gata ne, banikuma da hanyar daxan biyaku dashi.

Ganin kukan baxai kaita ko inaba tamiqe tafara tafiya a hankali saboda batada kudin hawa adaidaita, tanason tafara xuwa gidanta amma kuma tana tunanin cewa idan taje bada sanin mijinta bafa tanada zunubi, da wnn tunanin ta karya akalar ta xuwa gidan Aurenta....

🙉🙉🙉 Hummm Bakisan mexaki tarar ba.



😍😍🤝🏼Anatare
Mummyn Fadyl CE





🎲🎲TUDUN DAFAWA🎲🎲


Rubutawa....MUMMYN FADYL (Fatyma Muhammad Adamu)

Wattpad @ *fatimamuhammadadamu*


INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION*
*[onward together]*
*{we give the reader's of ours the best out of the bests,, our inks are melodious and dropping a kinda lights to reader's}*
```THE PEN OF LOVE😘 HEAT TORCHING❤ TEAR OF SORROWS😭 CURDLES😊 GIGGLES😁 AND MARRIEGE THINK💑```
*```JUST GIVE US FOLLOW..**


_Allah sarki rayuwa dubu su soka, dubu suqi ka, bantaba zaton novel dina zaitaka xuwa inda yataka yanxuba, Alhmdllh Masoyana kune silar yin murmushi na_...💃🏼💃🏼💃🏼


Fitowa ta..1⃣3⃣

Tasha matuqar wahala kapin ta isa Hutu kuwa tayishi yafi sau goma dakyar ta iso qofar gidan, ganin gidan a bude ne yatabbatar mata Mal.Habu yana ciki, kasa daga qafafunta tayi domin shiga don haka taxauna a qofar gidan domin tahuta.


Aciki kuwa Mal.Habu ne da Amaryansa a zaune yabude mata Gasashshiyar naman da yasayo mata, inda itakuma yawu yagama wanke mata cikin bakinta gaba daya miyonta yagama tsinkewa, Allah Allah take yagama budewa, aiko bata jiraba ta fusgi ledan hadi da cemishi kawo megida na hutasheka.

Tafara tauna kamar Wanda bata taba cinnama a rayuwarta ba (Wlh ciwo Daya Lami xatai maka sai anyi maka alluran Tetanus😜).

Har lumshe idanu takeyi don dadi fadi take a ranta yaushe gamo? Kafin ai haka ai haka ta kammala da naman, mamaki ne yacika zuciyar Mal.Habu saboda baiyi tsammanin xata iya cinyewa ita kadai ba koda wasa, snn bata damu dashi mexai ci ba, maimakon yaji haushinta saima qara burgeshi yaji tayi.


Bayan tagama hutawa ne, tamiqe tayi cikin gidan Hango dakinta tayi da haske saida xuciyarta tabada wani sauti daramdaram, saida ta dafe qirjinta qirjinta snn tasamu kuzarin matsawa kusa da dakin kapin tayi magana kukan diyarta yarigata miqa sallaman..

Waye ne abunda yafito knn abakin Mal.Habu, nice Zainabu tafada cikin siririyar muryanta, tsintan kanshi yayi da kasa koda motsa bakinsa balle yayi tunanin zai iya tashi ya leqa ta. Ganin ba'a ansa mata bane yasata qarayin sallaman a karo na biyu, Lami ce tamiqe tadaga labule nan sukayi tozali da juna, Zainabu bakinta yana rawa tafurta L...A...M...I 😳 kece tanuna ta da Dan yatsa, nicepa yadason ranki? Mekikeyi a gidana, dakina kuma atareda mijina?
Mtswww miji hahhahahhaha miji pa.


Habu tafada kanta tsaye shiko jiki na kyarma yamiqe ya iso garesu, Zainabu ne ta mitstsini jikinta domin tabbatarwa kanta ba mafarki takeyi ba, tabbas a zahiri ne, tsinkayan muryan Lami tayi tanacewa Habu nabaka minti biyu kacal kayiwa matarka bayanin matsayi na kadawo cikin daki..


Kallon Zainabu yayi rai Abace yace, dama bakida hankali? Xaki nufo dakin mata batareda sallama ba? Megida nayi sallama tafadi hakan tana girgiza NANA datake bayanta, to kibude kunnuwanki dakyau ki saurareni Lami yanxu Matata ce snn wnn dakin dakika samemu a ciki dakinta ne Ayanxu, kinga can? Yanuna mata _kitchen_ bin hannuwansa tayi da kallo tafahimci inda yanuna mata, daga mishi kai tayi alamar tafahimta, to shine dakinki zabi yarage naki inkinga zaki zauna to idan baxaki iyaba ga hanya, yadaga mata kafada irin baruwanshin nan🤷🏻‍♂.


Tinda yafara maganganun nasa take addu'oi acikin zuciyarta shiyasa cikin qarfin guiwa tanupi cikin dakin batare da tanajin qunan zuciya ba, cikin dakin taleqa batasan inda haskenta yakeba, kuma tanatsoron xuwa taroqesu batasan dawani fuska xasu kalleta ba, shiyasa ta lalubi gurin harta yi sa'a taji hanunta akan gado, kwantar da NANA tayi snn tafito waje domin tayi alwala.


Tajima bayan ta idar da sallah, xama tayi tana addu'oi sai a wnn lokacin taji kuka ya kwace mata, tayi kuka tayi kuka hartaji kanta yana amsawa tayi kukan maraici tarasa kafadan da xata kwanta ajiki domin taji sanyi.


A dakin Lami kuwa bayan tagama cin namanta tashare hannunta ajikin zanin gadon Snn tacewa Mal.Habu taso ka hauro mukwanta tafadi tana hawa kan gadon bayan ta tube kayan jikinta yabarta daga ita sai fallan zani, binta yayi da idanu aqasan ransa yarasa menene abun burgewa a jikin Lami, amma kuma bayajin xai iya kusheta kokuma wulaqanta ta.


Lami kikai min ruwa in watsa tukunna bana iya bacci batareda nayi wanka, ba, Zaburowa tayi a gadon tareda tsareshi da idanuwa inda atake yaji yayi la'asar, itakuma tace mishi Mal.Habu dama ka aureni don inbautu maka a gidanka ne? A'ah yafada cikin rawar baki.

To bari ingaya maka daga gobe Zainabu ce zatana yimana girki da duk wani abunda takeyi maka a da, Amma kasani bakai ba kwana a dakinta domin batada kwana.kaji? Dasauri yace mata Naji, yamiqe yanufi waje domin ya hada ruwa yayi wanka.

Fitarsa keda wuya itakuma tadauko man shafawanta data zuba maganin aciki snn tadansa mishi turare domin kore mishi warin maganin. Bai wani Dade ba yadawo nan ta taso cikin kirsa, ta tarbeshi Dauko zaninta tayi acikin akwati Badon a gaban idonsa ta ciro ba to bashakka xaice yashekara ajikinta baiga ruwa ba, haka yanaji yana gani togoge mishi jiki tsab da wnn zanin, baigama dawowa hayyacinsa daga duniyar wari ba tafara mulkeshi da wnn man.


Ainan yakusa shidewa yaji wani jaraba Wanda tunda ya balaga baitaba jin irinsa ba, ganin yafara binta da wani mayataccen kallo ne, yasata fadawa jikinsa rijib nantake labari tacanxa,inda nafara jiyo gurnanai kala kala, kamar wadanda suke sauke nauyin shekara Dari.

_Aguje nafito daga dakin har ina tuntube saboda tsoron irin abubuwanda sukeyi yasha qarfin ganin idanuna, Nasan kunason insanar daku to naqi😜)_


Anan bacci ya kwasheta tsakan dare wani firgitaccen kukan NANA ne yatada ta nan ta lalubo ta domin saka mata nono abaki, amma taqi karba tasha, lallashinta tafara, amma taqiyin shiru, miqewa tayi tagoya ta, nanma abun baisauya zaniba, saima qara sautin kukanta tayi, kuncota tayi abayan, duk abunda tasan xatai mata domin yin shiru tayi, amma Sam NANA batasan tanayi ba, aqarshe itama fashewa tayi da kukan ta durqushe a qasa, tana Kiran sunan Allah domin yakawo mata agaji.


Tun Mal.Habu yana fitoda ruwa har abun ya gagareshi bakin mazaqutarsa sai zogi takemishi, qarfinshi yaqare daga yayi yunqurin sauka akanta xata kuma rarumosa,saida suka shafe lokaci me tsawo ta kyaleshi badon tagaji ba saidon taga yana Neman shidewa, gefe Yakoma yanata numfarfashin azaba, itakuma na dadi, sai a wnn lokacin suka fara jiyo kukan Zainabu da 'yarta, Lami tagaji tanason bacci dalilin hakan ranta tabaci tacewa Mal.Habu yaje yasan yanda xaiyi dasu tanason tayi bacci.


Shikuwa miqewa yayi yanufi dakin Zainabu, duk a zatonta taumakonta yaxoyi hakan yasata rungumo 'yarta suka fito aguje, qiqam taganshi a tsaye duk da akwae duhuwa hasken farin wata yanuna mata yanda yahade fuskarsa, hakan yasa tasha jinin jikinta.

Cikin tsawa yake mata magana, ke yanxu Zainabu keda wnn abunnaki yanuna Sadiya, baxaku bar mutane su huta bako? Wlh Zainabu naqarajin duriyar tashin kukanku acikin gidan nan domin hana matata samun isashshen bacci xanyi maganinki xankuma dauki hukuncinda baki taba tsammanin xan iya dauka akanki ba, fuuu Yakoma dakin matarsa.


Tsayuwar ne yafara gagaranta, donhaka tarungumi diyarta dakyau taje tabude qofa a hankali tayi waje, a gindin bishayar qofar gidan tasamu dutse me fadi taxauna cikin ikon Allah NANA tayi bacci, dadi taji yakamata ganin 'yar tata tasamu bacci, bata San lokacinda bacci me qarfi yayi gaba da itaba


Batasan iya lokacinda tayi wnn baccinba harsanda haske yafara dallare mata idanuwa a firgice tafarka da Ambaton sunan Allah abakinta, tamiqe tayi cikin gidan, batasamu kowa a tsakar gidanba don

Please Login or Register in order to submit comment