You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

rawan kan nan, nasan baxai barmin 'yata da yanayinta dai2 ba.


Dariya taimishi tajuya tana fadin bari inje gurin wannan dannaka mai sheqen ra'ayin riqau inga koxai miqa musu abincin nan, domin babu Wanda yasan gidan acikin 'yan aikin mu, shikadai yasani don haka shixaije.


Samunshi tayi xaune yanata tilawarsa, qarasowa tayi taxauna akan kujeran dake cikin dakin, saida yakai ayah snn ya kalleta da murmushi a kwance akan fuskarsa.


Alaramma barka dai Allah yabada lada, Amin yace Yakuma qara da cewa Mummnyn Aliey kintashi lpy? Natashi lpyr dai ba sosai ba.


Dasauri ya qaraso ga durqusa a gabanta tareda dafa guiwowinta da hannuwansa duka biyu, ya kalleta yace meke faruwa dake mummy? Numfasawa tayi snn tace wlh son jikinane gaba daya babu kwari banajin qarfi, gakuma faduwar gaba danake ji.



Gabanshi ne yafadi, snn yatafi tunanin menene yake shirin tunkarosu a wannan lokacin, dagashi har mahaifiyarsh? Amma a fili yayi murmusa yace babu komai da ixinin Allah mummy.



To Allah yasa, yanxu dai tashi plx kuma banason musu ka kai abincin nan gidan qanwarka, baisan dalili saiya kasa yi mata musu domin babu qarfin yin hakan a jikinsa, snn kuma yaji shikanshi yana buqatan xuwan To bari inshirya.



OK saika fito tajuya tanufi falo, bai bata lokaci ba, saigashi yafito mummy saina dawo, kadai dage kaima kayi auren inbahakaba wlh kai xaka dinga kai abinci gidan Xarah, dariya yayimata kawai yacigaba da tafiyarshi.



Isarshi yasamu humairah a qofar gidan IBBY sai faman buga qofar gidan takeyi, nan ya qaraso gurinta tare da tambayarta meke faruwa, saida ta gaisheshi snn tasanar dashi abunda ke faruwa


Ciro wayarsa yayi a aljihu, yafara trying layin amma ba'ai responding ba, mummy yakira yace ta turo mishi numban Xarah, acikin sakan biyar numban tashigo wayarsa.



Nan ya kira amma still ba'ai picking ba, yakirasu a qalla yakai sau ashirin amma duka a banxa, nan yahau buga qofar cikin jin takaicinsu, yagama ayyana irin rashin mutuncin da xai musu idan duka fito.


Hatta humairah itama tagama cika, ta tsaya sai surutu takeyi acan gefe, fadi takeyi saikace akansu aka fara aure, ita dama tasani yanda suka jarabtu da junansun nan wlh tasan xasu iyayin abunda yafi haka ma.



Kiran mummy yayi a take a daidai wnn lokacin humairah ma, takira Ummy tasanar da ita tana tare da yayamsu Aliey amma sunqi budewa, shikuma cewa mummy yayi cikin xafin rai yace mummy gashinan kinsa naxo ba irin kira da kuma bugun qofar da banyiba amma basuy responding dinmu ba, ga humairah nanma da alama abinci aka bata daga gidansu.



No Haidar kasan ko IBBY xai maka haka Xarah baxatai maka ba domin kuwa tana tsoronka, snn ibbyn ma wasan baxai kai matakin haka ba, plx karka bar gurin ka bincika bana tunanin sunjika Kodai ma bacci sukeyi.



Mummy saikace masu baccin mutuwa nidai gida xandawo I'm tired nakira nema domin karkice nadawo batareda kinsani ba.



A'ah karka dawo wannan umarnina ne, karka kuskura kabar gurin saika miqa musu abincin nan, tana kaiwa nan takatse kiran, ohhh dafe kanshi yayi tsabar takaici yama rasa mexaiyi next.



A qarshe dabara tafado mishi jallabiyarsa ya nannade yahaye tasama, yabyde gate din wa humairah tashigo itama, luckily yana taba qofar falon tabudu, aranshi yace tsabar xalama ko qofar basu samu daman rufewa ba.


A falon nanma sallama yayi ta kwadawa amma shiru a qarshe yacewa humairah kishiga kidubosu domin yanxu kam jikinshi yafara sanyi.



Hakane itama gareta tafara taraddadin abunda xata tarar, a qofar ta tsaya kamar karta shiga candai tayi shahada tashige abunta kai tsaye, abunda tagani ne yaraxanata, domin IBBY ne kwance akan gadon Xarah kuma a sheme aqasa dagani dai kasan balafiya ba.



Kwalla qara tayi Wanda yasan Aliey cikin takun da baifi Biyar ba ya cimmata a dakin, abunda yagani shima ya matuqar raxani shi, gurin Xarah yafara xuwa, nan yaga bata cikin hayyacinta, yanufi gurin ibby a matsayinshi na likita bai sha wahala ba gurin fahimtar babu rai a jikin ibby.


Dakyar kamar xai fadi ya jingina da kujera humairah kuwa tuni ta barke da kuka, ganin halinda Aliey yashiga shiya qara gigitata, hannu tasa a ka tanata kurma ihu domin Tarasa mexatayi guda daya.



Binsu kawai yakeyi da kallo wata hadaddiyar ciwon kai ne yabugeshi Wanda ya tabbatar mishi B.p dinshi ne yahau a take, wayarshi datake vibrating ne yajawota a hankali domin babu kuxari a tare dashi.


Mummy CE yana dagawa yace mummy kuxo gaba dayanku harda su Abba, kawai ya kashe wayar ma gaba daya, mummy batasan lokacin da tai dakin daddy a gigice ba, nan tasanar dashi abunda Aliey yagaya mata a waya bata saurari mexaice ba tayi gidansu IBBY da Ummy tafaracin karo, tin kapin tasanar da ita abunda ke tafe da ita, ta fashe da kuka domin tasamu amsar abunda ke damunta kenan bamai dadi bane.




Mummy kuwa batama kula da kukan da Ummy keyi ba, tsanar da ita saqon Aliey akan tasanar da Abba, bata saurareta ba tajuya kamar mai shirin kifewa a qasa, a waje suka hadu gaba dayansu suka nufi gidan Ibrahim.



Suna isa suka fita gabadayansu Abba ne kawai yadan fisu dauriya, humairah ce tajiyo shigowarsu, nan tafito tana kuka basu saurari kukan taba suka wuceta xuwa dakin, ganin Aliey sukayi kamar gunki sai hawaye ne sirara kebin kuncinsa.


Mummy CE taqarasa kan Xarah dagudu harda fadi a qasa, daddy ma haka haryafi mummy rudewa domin shi dago Xarah yayi cikin gigita, Abba da Ummy sukayi kan IBBY a wannan lokacin ne Aliey yasamu kuka ta kufce mishi.



Abba ne yafara dagowa idanuns taff da kwalla, yace saidai muyi haquri domin ibrahemm yarigamu gidan gaxkiya dai dai lokacin Ummy fadi a gurin sumammiya.



Iyakan rudani ahalin wannan xuri'ar sun shigeta a wannan ranar, nan aka dungumesu sai asibi gaba dayansu sunkasa tuqa motar, direbansu suka kira daga gida sukaxo suka kaisu asibitin, banda daddy Wanda dashine aka wuce da IBBY gida.



A daki guda aka kwantar dasu, Aliey jininshine yahau shida Abba yayinda Ummy kuma doguwar suma ne, banda Xarah Wanda akace tahadu da abunda yafi qarfin tunaninta ne Wanda yayi sanadiyyar bugawan xuciyarta a take, ....




Sundauki awanni biyar kapin suna farfado da taimakon ruwan da aka daura musu wanda yasha allurai acikinsa, Lahaula wala quwwata illah billah, innalillahi wa inna ilaihirraju'un shine abunda Abba yaketa nanatawa.



Bayan farfadowansu Abba yanemi a sallamesu domin sunada uxiri a gida, banda Xarah wacce aka barta itada mummynta a asibiti, haka jiki babu qarfi aka kwashesu a mota, isansu guda suka samu gida yacika maqil da al'umma.



Ba'a bata lokaciba gurin suturtashi aka fitar dashi domin yimishi sallah, Ai Aliey kasa tsayuwa yayi a cikin sahun sallan domin sumewa yayi a gurin, jiyakeyi kalaman IBBY na jiya dadare dakuma text dinda yai mishi suna mishi amsa kuwwa a cikin kunnuwansa.


Shigar dashi cikin gida akayi, snn aka tafi dashi gidanshi na gaxkiya, anguwarce tayi tsit kamar babu halitta acikinta.
*Allahu Akbar ,Allahu Akbar* saidai muce Allah yasa kyawawan aikinshi suy mishi jagora gurin dacewa agurin ubangijinsa.



Bayan dawowansu ne Aliey yasan shknn IBBY yatafi yabarshi kuka yakeyi kaman qaramin yaro abokanshi sunata bashi bako amma a banxa domin bayajinsu ko kadan yakasa gaxgata yarasa abokinshi Dan uwansa.



Ummy kuwa ko magana ma kasayinshi takeyi sai girgixa kanta kawai take, Labari ya iske su Nanah suna isowa gidan bayan tagaisa da mutane ta sanar da mamanta xata tafi gurin Xarah a asibiti, domin Maman tace basai tajeba tunda mummy tanacan.........



😍😍🤝🏼Anatare
Mummyn Fadyl CE



🎲🎲TUDUN DAFAWA🎲🎲


Rubutawa....MUMMYN FADYL (Fatyma Muhammad Adamu)

Wattpad @ *fatimamuhammadadamu*


INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION*
*[onward together]*
*{we give the reader's of ours the best out of the bests,, our inks are melodious and dropping a kinda lights to reader's}*
```THE PEN OF LOVE😘 HEAT TORCHING❤ TEAR OF SORROWS😭 CURDLES😊 GIGGLES😁 AND MARRIEGE THINK💑```
*```JUST GIVE US FOLLOW..**


*Ina miqa saqon ta'axiyata ga team IBBY inakuma qara Baku haquri akan rashinda akai muku, Allah yajiqanmu baki daya*
_Nikaina banso ibbyn nan yamutu ba, amma yaxanyi labarinne yaxo a haka_ lol nikaina nayi kuka shame~shame.


Fitowa ta. 6⃣9⃣



Lokacinda ta isa asibitin itakanta ba acikin hankalinta take taka qafafunta ba, domin iya firgici tagani dajin mutuwar mutumin da jiya aka rabu dashi lpy batare da yana fama da wata lalura ba, gashi kuma alokacinda yafi kowani lokaci muhimmanci acikin rayuwarsa.


Batasha wahalan Neman dakinba domin itada Bbn ta dakuma direban gidansu Xarah nsuke tafe, isarsu dakin tasamu mummy yana xaune hannunta dauke da carbi, tanaja tanakuma addu'oi, ganinsu yasa xuciyarta qara karyewa.


Nana CE ta taho da gudu tafada jikinta, dagota tayi itanma tana hawaye tace ankai Ibrahim gidansa ko? Dakyar maganar yake fitowa a bakinta domin yanda tasha kuka, Ankaishi mummy ya jikin Xarah? Girgixa mata kai kawai take faman yi, sai Bbn Nanah ne yamatso yafara basu baki kapin sukadam tsagaita da kukan.


Mummy tasanar dashi abunda likitoci suka fada gameda ciwon dake damun Xarah. Nana qara kecewa da kuka tayi ta matsa gurin gadon ta riqe dayan hannun xaran Wanda babu ruwa a jiki ta manna shi a jikinta, tana fadin sannu 'yar uwa ba shakka mukam munga jarabawa a rayuwarmu.


Ke kadaice a tsakaninmu kikai rayuwa mai sauqi tun haihuwarki, kika taso cikin gata, amma saigashi kinga jarabawarda take baraxana da rayuwarki, mutuwar miji babu dadi, mijinma na kwana daya, Wanda kuka gama tsara yanayin rayuwar da xakuyi tare.



Ya Allah idan wani laipi muka aikata kake hukuntamu akansa Allah muntuba, Allah ga qanwata Allah ka tausaya mata kabata lpy, badon halinmu da aiyukan mu ba, Ya Allah Xarah tayi qanqanta.


Kulll taji muryan Bbn ta abayanta, Nanah Yaya kike shirin kauce hanya kuma? Kinmanta Allah shiyake tsarawa bawansa rayuwar da ta dace dashi? Kidaina fadin haka godiya xamuyi ga mahaliccin mu domin yana kawo mana mafita aduk lokacin da muka rasa *TUDUN DAFAWA* juyawa yayi yabar dakin sakamakon xuciyar shi data gama karyewa baya kuma buqatar Nanan taga hakan, idan shi yayi kuka dawani baki xai rarrasheta.



Komawa qasa tayi ta xube tana kuka mai tsuma xuciya tare kuma dayin duk addu'an dayaxo bakinta, mummy ma haka kukan takeyi kashi biyu, tana tausayin halinda su Ummy xasu shiga dajin wannan mutuwar data afko musu lokaci guda, A dayan bangaren kuma tana tausayin diyarta domin ita shaidace akan qaunar da take yiwa ibby, bata hadashi da kowa acikin xuciyarta ba.



Tana cikin wannan tunanin, xuciyarta ta tunano mata Aliey, cikin Azama ta xaro wayarta layinshi takira, yana cikin kuka abokinshi yamiqo mishi wayar, ganin _my pride_ a fuskar wayar yasashi jin faduwar gaba, domin bai San mexata sanar dashi ba, yana dagawa yace mummy Xarah ma tamutu ko?



Cikin kuka tace mishi ka kwantar da hankalinka Xarah tananan da ranta, mummy narasa IBBY antafi dashi mummy yaxanyi dawa xanyi wasa da dariya a gidannan waye xai tunkareni ya bugi qirjina yasanar dani gaxkiya koda banaso, mummy meyasa IBBY yatafi? Wayyo mummy Ibrahim yatafi ya fashe da kuka kamar qaramin yaro.


Kalamanshi qara jikkata ta sukayi, tarasa mexatace mishi, tarasa yanda xata lallasheshi, kawai saita kashe wayar domin baxata iya cewa komai ba, kuka takeyi kamar ranta xai bar gangan jikinta.



Ana xaune gurin karban xuciya, Abba ne yataso yacewa daddy, yakamata adubo matar marigayi kawai tadawo gida, inyaso ayita dubata a gida, inaga hankalinmu xaifi xama guri daya ko?



Daddy ne yadago jajayen idanunsa, domin shima kuka yayi bana kadanba, Abba yafishi dauriya nesa na kusa ba, wasu sabbin hawayen ne ke neman gangaro mishi, Abba yayi qoqarin maida nashi snn yadafashi yace haba Yallaboi meyasa kake hakane saikace yaro please kukan nan ya isa haka, ibraheem addu'arka yake buqata a yanxu shine kadai gatan da xaka nuna mishi Yakuma isa gareshi.


Miqewa yagi yana share hawayenshi da handkerchief din dake hannunsa, domin bayajin xai iyayin dogon magana, matuqar yace xai takura kanshi akan saiyayi kuwa ba shakka kuka ne xai kwace mishi me qarfi Wanda xai janyo hankalin mutane kanshi.



A mota Abba yacigaba da bashi baki, tsananin dauriya da tawakkali irinna Abba kowa saida ya jinjina masa, tafiyarsu asibitin ma dakanshi yajasu dashi da daddy dakuma wasu abokansu guda biyu.


Sun tarar da mummy da Nanah babu mai rarrashin Dan uwansa, Abba yafara qoqarin basu haquri, daddy ya katseshi cikin kuka yace mishi, kabarsu suyi kuka domin anyi rashin nagartaccen namiji, mai tausayi haquri kawaici dakuma jinqan iyaye, dole suyi kuka rashin mutum irin Ibrahim abun ayi kuka ne.


Hummm kawai Abba yake fadi, domin shikansji kukan yakeso yayi koxaiji sauqin yanda xuciyarshi dakuma qirjinsa kemishi xafi kamar xasu hudo Riga sufito waje haka yakeji, sun sanar da mummy akan xa'a tafi da Xarah gida, batace komai ba, nan suka karbo sallama daddy ne yasa hannu ya ciccibeta kamar qaramar yarinya yasakata a mota, suka shiga sukayi gida da ita.



Dakin mummy aka ajiyeta snn kowa yawuce maxauninsa, Nanah ce ke xaune a gefenta, mummy taje dubo su Ummy dakuma Aliey.



Kuka sukayi sosai itada ummy, tareda yiwa junansu ta'axiya nan take tambayarta labarin Xarah,nan tasanar da ita komai nagameda halinda ake ciki. Ikon Allah kawai tace.



Bayan mummy tadan gaggaisa da mutane, ta isa gurin Maman Nana tasanar da ita halinda ake ciki, snn tace mata Xarah tana dakinta ta gashi suje taganta, bata musa ba ta bita a baya, suka nugi dakin Mummyn.


&&&&&&&&&&&&&&



A wahalce Ayashe tayi tafiya mai nisa Wanda wahalanshi da nisanshi ya haddasa mata masifaffen qishin ruwa, ga ciwon qafafu Wanda dakyar take dagasu tsantsan axaba, itakanta tanajin warin jikinta tadai rasa yanda xatayi da yanayin ne itakanta.


Batasan ya akai ba taganta a cikin tasha, xama tayi a wani gindin mota tana maida numfashin wahala, ruwa ta hango a buta aiko a guje tanufeshi ta dauka ta kwankwada bata gama shaba saiga wani mutum ya hangota, Sam baxakai mata kallon mai hankali ba, domin gaba daya kamanninta sun sauya, koda wasa baxakace Ayashe bace tun tana xaman qauye balle dataje burni, acikin 'yan watanni tasauya gaba daya, shiyasa yana xuwa da sandansa baiyi wata wataba ya xula mata a bayanta tasake butar daqarfi.


Aiko yafara korarta irin koranda akewa mahaukata, fadi yakeyi wadannan sabbin mahaukatan narasa mesuke nema da wannan rumfan nawa, basuda gurin shan ruwa sai nan.



Mamakine yakamata domin kuwa tasanshi maqocinta ne, nan tahau kalle kalle bashakka garinsu taxo, bataji wani dadi acikin ranta ba, domin baxata iya tinkaran kowa a garinba, don kuwa batai wa kowa abun arxiki ba, tsakaninta da bayin Allah wulaqanci cin Amana dakuma rashin mutunci.



Cikin sauri tabar mishi rumfar tanajan qafanta tana kuka, tana kuma danasanin rayuwarta, tana tunanin tayaya xata gyara laifukan da ta aikata, a ina xataga al'ummar data xalunta tanemi yafiyarsu koxata samu sauqin axaban datake fuskanta, gashi a kullum kamar ninka axaban da ake yi mata akeyi.



Xuwa tayi can gurin da aka tanada domin mabarata, taxauna domin tadan huta kapin ta fita tadanyi bara koxata samu abunda xatasamu abunda xatasa abakin salati, Mabaratan dasuke gurinne sukaiyo kanta domin wani warin dayake tasowa a jikinta kamar danyen mushe..........




😍😍🤝🏼Anatare
Mummyn Fadyl CE





🎲🎲.🎲🎲TUDUN DAFAWA🎲🎲


Rubutawa....MUMMYN FADYL (Fatyma Muhammad Adamu)

Wattpad @ *fatimamuhammadadamu*


INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION*
*[onward together]*
*{we give the reader's of ours the best out of the bests,, our inks are melodious and dropping a kinda lights to reader's}*
```THE PEN OF LOVE😘 HEAT TORCHING❤ TEAR OF SORROWS😭 CURDLES😊 GIGGLES😁 AND MARRIEGE THINK💑```
*```JUST GIVE US FOLLOW..**


*TEAM ALIEY INA tare daku irin sosai dinnan* 😜


Fitowa ta. 7⃣0⃣



Isowarsu Altinece tafara matsowa domin kuwa itace masifaffiyar cikinsu, indai irin hakan ta taso to itace kan shige gaba, batada dadi ko kadan yanxu saitaima kaca kaca, koko taima zagi na diban albarka.



Ke baiwar Allah mahaukaciya kike kokuwa 'yar uwarta? dagowa Ayashe tayi da fuskarta shame shame da hawaye, tace niba mahaukaciya bace qaddarace tamaidani haka, Altine bata kulata da bayanan ta ba tacigaba da maganarta, to indai da hankalinki kinsan na ba gurin jinya bane kuma kinsan yanayin yanda jikinki ke fitar da wani doyi kamar danyen kashin asuba, dawanne xamuji da nakasan jikinmu kokuma da wannan lalura taki? Gaxkiya saidai kicanxa sheqa domin wlh kinji na rantse baxai yiwu mucigaba da xama dake da wannan lalura taki anan ba, kindaiji nagaya miki, kisan inda dare yayi kapin mudawo da yamma.



Ayashe tana kuka tacigaba da Sosa jikinta tana roqon Altine, tareda roqon sauran mabaratan akan sutayata roqon Altine, amma qus babu Wanda ya iya cewa komai don kua sun San halinta ba mutunci ne da ita ba.



Haka tana kallo suka watse suka barta a gurin, jikinta yana fidda jini da wani ruwa mai danbanxan doyi, kuka takeyi kamar ranta xaifita, bata tabayin danasani irinna yau a rayuwarta ba, a yau take tuno hudubar yayanta Wanda agabanshi ta taso, sanadiyyar fitsararta tabar gabanshi tafara xaman kanta tunkapin tayi aurenta na fari.


Wlh Maimuna sunanta na Asali kenan domin a yawon duniya tasamu Ayashe, indai baki maida hankalinki ba, duniya itace xata koya miki darasi, domin kuwa ita duniya makaranta ne, bakida gashin wance karkice xakiyyi kitson wance, kitsaida kanki inda Allah ya ajiyeki, kibi duniya a sannu, a wancan lokacin daukan maganarshi takeyi a matsayin farfaganda dakuma baraxana akan holewarta, yana takurawa rayuwarta, akan halayyarta ya koreta, batayi yunqurin Neman afuwar sa ba domin kua itakanta hakan takeda buqata.


Nan tafito duniya tafara jin dadin rayuwarta, har tafada gurin qawaye inda suka budemata ido da xua gurin bokaye,, da hakan itama harta samu 'ya'yan daki masu yimata fadanci a bariki, gashi yau cikin qanqanin lokaci duniya tayi mata atishawan tsaki, tarasa *TUDUN DAFAWA* babu mai taimakonta batada inda xata dosa domin Neman taimako, lafiyarta shine mafi girma dayake gabanta gashi kuma batada tabbacin xata sameshi a halin yanxu, don dama Bokanta ya sanar da ita matuqar ta matsa akan al'amarin xainabu tobaxata ga mai kyau ba, to kenan xainabun ma ba'a xaune takeba kenan? Kaii xainabu baiwar Allah ce dakanta tabawa kanta amsa.



Tun tana bin sassan jikinta da qaiqayi tanajin xafi kadan kadan, har yakai minzalin daga ta qaiqaya tanajin wani axaba mai radadi tamkar anyanka fatar jikinta an watsa mata ruwan barkono haka takejin ta.



Komawa Inuwa tayi koxataji sauqin radadin datakeji amma ina kamar ma qarawa akeyi, kwanciya tayi aqasan gurin tana burgima kamar wata qaramar yarinya, maimakon addu'a a'ah ihu taketa xabgawa acikin wannan layin, duk Wanda yaxo wucewa baya mata kallon mai hankali balle ayi tunanin kawo mata agaji.

&&&&&&&&&&&&


Mummy ce xaune agefen Xarah hawaye takeyi tana kuma tofa mata addu'oi domin babu kowa a dakin suna falo ana sauqan alkur'ani addu'a takemata iyakan gwargwadon iyawarta.



Kamar acikin mafarki taga Xarah tana motsa qafafunta dariya ne dakuma kuka ya hadu mata a lokaci daya, nan kuma taqara matsowa dab da fuskarta tana qara qaimi gurin addu'arda take mata, ahankali tafara bude idanunta.


Adai dai lokacinda Aliey yashigo dakin domin mummy tasanar dashi andawo da Xarah gida, snn takuma sanar dashi halinda xarahn take ciki dakuma lalurar da ta afku da ita dalilin rasuwan IBBY.



Idanuwanta tagama budewa ahankali tasaukesu akan mummy nan ta runtse su cikin sauri, bayan 'yan sakanni taqara budesu snn tabudi bakinta ahankali tace mummy ina mijina, ki kiramin yayah ibby kuma mummy kihanashi yimin irin wannan wasan wlh tsoro yake bani, kokuma in hadashi da daddy nasan inya hanashi xai daina.


Kukan da ya kufcewa mummy ne yasa Xarah miqewa dasauri tariqota nan Aliey ya iso garesu domin dafarko yarasa waxai fara rarrashi acikinsu, kallonsu takeyi daya bayan daya kapin tace mummy ina yake? Tajuyo gurin Aliey nan taganshi a hargitse.



Sakesu tayi tafara ja dabaya akan gadon tace mummy xantafi gidana, tasauqa a gadon tafara Neman mayafi, Aliey ne yakamota cikin xafin rai harta fado jikinshi batareda ya ankaro ba, runtse idanunsa yayi snn yajanye jikinsa, Yakuma fice a dakin cikin sauri.



Mummy ce cikin kuka ta riqota tareda mannata da jikinta tana shafa bayanta tace, kiyi haquri dotah ke musulma ce kuka Alhmdllh kinada ilimin addini kinsan duk mai rai mamaci ne, kinkuma San menene qaddarah kiyi haquri Xarah IBBY yatafi yabarmu , tafiya ta bar abada.



Sam a wannan lokaci batasan wani Abu waishi kuka ba, domin shi kuka ma guri yake samu snn shi kukan rahama take xamowa ga duk Wanda take cikin tashin hankali yakuma samu xarafin yi.



Kallon mummy daketa kuka takeyi, takoma ta jingina da gadon, can bada jimawa ba ta miqe kawai tafara tafiya mummy itama cikin hanxari tabiyo bayanta, a falo taja tayi turus, tanabinsu da kallo daya bayan daya, juyowa sukayi gaba data suka kalleta nan take aka fashe da kukan tausaya mata.



Kallonsu kawai takeyi can kawai akaga tafara tari, mai kamada aman jini, rudewa gurin yayi da koke koke, Mummy CE tayi sama da gudu tayiwa daddy magana gameda halinda Xarah take ciki.



Yana sauqowa said a yabiya dakin Aliey yayi mishi magana aiko kamar hankadosu akeyi domin atare suke sauqowa daga kan steps din, qaran takalminsu kawai kakeji.



Aliey yana isowa bai saurari kowa ba ya dagata yasa a kafadarsa yayi mota da ita, daddy yashiga yayiwa Abba magana nan suma suka rufa mishi baya, suna isa asibtin emergency direct, shigar da ita aka yi ciki da ita likitoci suka fara aiki akanta.



Basu jima ba babban likitan ya fito yakuma umarci su daddy su biyoshi office dinshi, bayani yayi musu akan Cewar kamar yanda ya sanar dasu a baya cewa xuciyar Xarah ta samu Matsala, to yakamata abita a hankali domin tana cikin yanayi mai hatsari a halinda ake ciki yanxu.


Jikinsu da sanyi haka suka fito suka tarar da mummy, Ummy dakuma Nanah, domin kasa xama tayi agidan harsaida ta biyosu asibitin, basuce dasu komai ba dangane da abunda likitan yace musu, kawai suncemusu yakamata abar mummy ta kwana dakuma Aliey tunda shine namiji in case koda akwai buqatan wani abun cikin dare, dahakan suka watse, ummy da Nanah suka tafi gida badon ransu nasoba....



Aliey da mummy kuma suka nufi dakinda aka kwantar da Xarah, kallo daya xakai mata kasan tanajin jiki.



Xama sukayi a kujerun dake cikin dakin da aka kwantar da itan, dukansu sun xura mata idanu sana kallona, tabbas hakan dole ya faru da ita idan kayi la'akari da irin shaquwa dakuma qaunar dake tsakaninta da IBBY, bai taba jin qaunar kojuma tausayin Xarah irin wannan lokacin ba acikin rayuwarsa, abun a tausaya mata ne a kuka rarrasheta.


Har gurin misalin qarfe dayan dare mummy tanabin Aliey akan yatafi masallaci yasamu ya Dan runtsa, amma yaqi tafiya shinema dai ya matsa mata ta kwanta akan darduma shikam yananan a xaune.


Gurin qarfe biyu saura ne suka fara jiyo sheshsheqan kukan Xarah alaman dashi tafarka, a tare sika iso gareta, wannan karon kuka takeyi sosai mai tsuma xuciya mummy xata tabata Aliey ya dakatar da ita ta hanyar cemata, ki kyaleta mummy wannan kukan da takeyi shixai rage mata xogin dayake cin xuciyarta.


Suna tsaye a jikin gadon itakuma tanata kuka, saida tayi me isarta sannan ta tsagaita don kanta juyowa tayi ta kallesu, tace Yayah yanxu shikenan narasa mijinah? Baxan qara ganin IBBY nah ba? Waxai soni ya qaunace ni kamar Yaya IBBY?



Waxai kirani tauraruwarsa? Yakima nunani a duniya a matsayin matar da tafi kowace mace agurinshi? Yayah Aliey daqaye xanyi rayuwa cikin jin dadi batare da nafuskanci muxantawa daga gareshi ba? Nan kuka ya kufce mata me qarfin gaxke.

Mijinah baxan qara ganinka ba sai a photo, baxan qarajin muryarka ba sai a mafarki, dama Kazan tafiya xakayi kabarni jiya kayitamin maganganu mai kamada kalaman bankwana? Xanyi yanda kace mijina sonda nake maka xaimin jagora gurin cika maka umarninka, nadaina kuka mijina nadau qaddara kamar yanda kafada, haka tadinga surutai marasa amfani, can kuma saikaga tayi dariya, takuma fashewa da kuka tafara birgima akan gadon kamar mai shirin fadowa.

Tagama karyar musu da xuciya Wanda mummy saida tagaxa yin haquri itama ta kece da kukan, harya rasa Wanda xai rarrasa acikinsu, kallonsu kawai yakeyi.



A qarshe yace Xarah!!.......



😍😍🤝🏼Anatare
Mummyn Fadyl CE




🎲🎲TUDUN DAFAWA🎲🎲


Rubutawa....MUMMYN FADYL (Fatyma Muhammad Adamu)

Wattpad @ *fatimamuhammadadamu*


INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION*
*[onward together]*
*{we give the reader's of ours the best out of the bests,, our inks are melodious and dropping a kinda lights to reader's}*
```THE PEN OF LOVE😘 HEAT TORCHING❤ TEAR OF SORROWS😭 CURDLES😊 GIGGLES😁 AND MARRIEGE THINK💑```
*```JUST GIVE US FOLLOW..**


*Tafaru ta qare wai anwa mai dami daya sata, komai yayi farko yanada qarshe, kai dai kayi qoqari karka cutar*


Fitowa ta. 7⃣1⃣




A qarshe Aliey yace da Xarah cikin raunananniyar Murya wacce tagama dishewa yace xaki amince namaye miki gurbin Ibby?


Gabadayansu ne suka dago suka dubeshi fuskarsu dauke da mugun mamaki Xarah bata iya bashi amsa ba saima fashewa da kuka dataqarayi mai tsuma xuciyar duk Wanda yake saurarenta, mummy kua mamaki ne yakasheta a gurinda take xaune tama kasa yin wani kwakwkwaran

Please Login or Register in order to submit comment