You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

haka tayi cikin dakinta, alokacinne tasamu damar kallon gurin da kyau, bakin gadonta taje zata zauna idonta yasauqa akan wata qatuwar kunama, miqewa tayi, amma datai tunanin babu mai taimakonta koda tafita asalima saidai kunamar tagudu tashiga wani gurin yasata, Aro qarfin xuciya ta dasa Aranta cikin dabara ta nannade zanin gadon tasauko dashi qasa snn tasamo sanda takashe shi tana kuka


Sauko da 'yarta tayi daga baya ta tube mata Riga kukanta ne ya tsananta a lokacinda tayi arba da kumburarren bayan NANA bayan nata yayi jaa, kana gani kasan tanashan Azaba, cikin kukan tafara tofa mata duk addu'arda tazo bakinta.

Zainabu fitonan daqarfi tayi maganar taji muryan Lami a qofar dakinta, gyara zamanta tayi a dakin don bata tunanin itama xata sarara mata, dukda haryanxu tarasa amsoshin tambayoyin daya addabin zuciyarta, ganin tana bata mata lokacin ne, yasata fadawa dakin...*****



😍😍🤝🏼
Mummyn Fadyl CE .





🎲🎲TUDUN DAFAWA🎲🎲


Rubutawa....MUMMYN FADYL (Fatyma Muhammad Adamu)

Wattpad @ *fatimamuhammadadamu*


INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION*
*[onward together]*
*{we give the reader's of ours the best out of the bests,, our inks are melodious and dropping a kinda lights to reader's}*
```THE PEN OF LOVE😘 HEAT TORCHING❤ TEAR OF SORROWS😭 CURDLES😊 GIGGLES😁 AND MARRIEGE THINK💑```
*```JUST GIVE US FOLLOW..**


*Ciwon cikin barewa a daji waxai bata kanwa, Allah daya ya halicci barewa a daji shixai bata magani,
Haqiqa Allah shike iyammini*


Fitowa ta..1⃣4⃣

Fadawa dakin tayi cikin fushi, tsayawa tayi a gabanta snn tanunata da 'yatsa Lallai Zainabu wuyanki yayi kauri ya isa yanka, kinsan dawa kikeyi kuwa? Hummm zanbaki mamaki wlh saina maidake abun kwatance acikin unguwarnan, kiran da Sadiya tai mata ne yasata fitowa batareda ta kammala maganganunta ba..

Menene Sadiya? Umma yunwa nakeji, tuntuni nake jiranki kifito amma kin qule can dakin, snn kinsan munyi maganar komawa gidan Umma Ayashe akan Alhajin nan amma bakicemin komai ba.

Kiyi haquri Sadiya yanxu xa'a fito ayi abun kari, snn maganar Alhajin kuma kibarshi yanxu pa ba kamar Da bane damuke cikin buqata, dukkan abunda kike so kiymin magana nikuma zanmiki shi.
To shknn Umma tajuya takoma dakinta.


Lami CE takoma dakinta, samun Mal.Habu tayi yanajin labarai, nanfa tazauna ta shiryamishi qarya da gaxkiya gameda abunda yashiga tsakaninta da Zainabu, shikuma hawa yafarayi kamar farashi, yamiqe a harziqe yayi dakin Zainabun, inda yasameta tana bawa 'yarta nono. Kapin taimata wanka gawani Azababben yunwa dayake addabarta.

Gaxkiya Zainabu baxan lamunci kiraina min mata tah ba, saboda Lami macece da bata qaunar tashin hankali, tana farkawa a gadonta da sunanki ta tashi kan cewa zataxo taduba lafiyarku snn taimiki maganar abun kari, amma kuma kirasa maganar daxaki gaya mata saina rashin mutunci?

To wlh baxan lamunci hakan ba, tunda na fahimci kedai ba Diyar arziqi bace, kuma Lami batada isashshen lpy, daga yau kece zaki nayin girki a gidannan, kuma yanxu basai anjima ba kifito kihura wuta...

Har yagama babatunsa, bata daga ido takalleshi ba harsanda taji maganarshi na qarshe, kuma kisani Aurenki yana lanqaye ne a wuyan Lami wlh duk ranar da kika nemi uzzira wa matata to kisani A ranar zamanki atare dani yaqare, A razane tadago jiqaqqun idanunta ta kalleshi shikuma yayi waje abunsa


(Karfa kumanta Mal.Habu har yau baisan kamannin 'yarsa kwaya daya tilo a duniya ba.😭)

Baqin cikinta da yake cinta ne, yasata miqewa cikin hanzari ta wanki 'yarta snn ta kwantar da ita, don kuwa tadauka wa kanta alqawarin Mal.Habu baxai taba Ganin 'yarta ba, tunda bainemi hakan ba, xata cigaba da killaceta tareda yimata addu'oin tsari, domin yanxuka abun tafara tabbatarwa kanta akwae surkullen qulli a tattare da al'amarin.

Fitowa tayi tanupi _kitchen_ domin tahura wuta, amma me Lami ce tai mata tsaye tana zuba mata ruwan bala'i saboda tashiga mata madafi, kifita kihura wuta a qofar dakinki, badon Lami din tafito ba, saidon darajar aurenta, murmushin takaici tayi tafito tanufi qofar dakinta tahura wuta, tsayawa tayi domin tarasa mexata daura.

Sadiya ce takece mata gashi, dagowa tayi taganta a tsaye akanta tana miqa mata taliya, karba tayi, cikin qanqanin lokaci ta kammala, tana qoqarin saukewa Lami tafito ta iso gareta, karban tukunyar tayi a hannunta, tai wucewarta dashi _kitchen_ .

Miqewa tayi batareda tanuna tafahimci abunda Lami take nupi da abunda ta aikata gareta ba, ruwa ta deba, taje ta watso ruwa tadawo tashirya, snn tagoya diyarta, kikkiintsa cikin dakinnata tayi, acikin kwalemar da takeyi ne tayi Arba da kudaden da Mal.Habu yake bata a da, kudin yakai kimanin dubu shida, lokacin batasan amfaninsu xai risketa a Dan qanqanin likaci haka, ba, hawaye taji yana gangaro mata sakamakon tunowa datayi da ranar daya miqa mata kudin naqarshe.

"Ki karba nidai koda baxakiy amfani dashi ba, ai baxaki rasa baqi masu xuwa miki ba saiki sallamesu dashi, cemishi tayi to ai wadanda kabani mapa sunanan banyi amfani dasu ba, acinyarta ya ajiye mata, snn yayi waje" Allah sarki rayuwa.

A take kuma ta tuno da Babanta, tanason xuwa taduba halinda yake ciki, donkuwa tanada tabbacin indai yana halin lpy to babu abinda xai hanashi xuwa, hakannema yake qara daga mata hankali, gashi batada Wanda takedashi daxai taimaketa yaje yadubo mata shi, da wnn tunanin tanemi yunwar dake Addaban nata tarasa shi.


Tunaninta yaqare akan taje ta tambayi Mal.Habu izini koxai barta tasamu taje tadubo mahaifinta, amma kuma batajin zata iya shiga wnn dakin saboda zai daga mata hankali, miqin da tasamu ta liqeshi ne xai balle mata.


Fitowa tsakar gida tayi tasamu Sadiya, roqonta tayi akan tayiwa Bbn magana, fitowar Sadiya tasanar da ita Ummanta tace tashiga, Shahada tayi tashiga cikin dakin da sallama.

Da gayya Lami takwanta ajikin Mal.Habu sai shafa shi takeyi, abun babu kyan gabi, shiko saiwani lumshe idanu yakeyi yana tande baki kamar tsohon baki, kawar dakai gefe tayi snn tagaidashi duk da tasan ba amsata xaiyi ba.

Sanar mishi tayi da buqatarta amma yayi tambar ba'ayi ruwan tsiranta a gurinba, tashafe kimanin Rabin awa, harta cire rai akan zaimata magana tana shirin miqewa taji muryan Lami da kece mata kitashi kije Amma kitabbatar baki wuce Rabin Awa ba, saboda xakiyi abincin rana.

Bata jira taji sauran bayanan nataba tayi dakinta tashirya kanta takuma shirya diyarta, sauda dama takan manta cewar jikinta danye ne, jikin jego, saiyanxu tagane Gata ne yakesa mace rasa qarfin jikinta bayan tahaihu, don kuwa ita yanxu yanda duniya tabugeta kallo daya xakai mata kayi 2nanin haihuwarta goma.

'Yan kudadenta ta kwasa, tafita tanupi hanyar gidansu, mai adaidaita ta tara, saida taratse shagon dake bakin layinsu tasaya musu kayan buqata itada NANA snn suka qarasa gidan.

Da sallama tashiga inda tasamu Zuwaira tana yiwa Diyar maqotansu kitso maimakon ta amsa gaisuwarda take mata saima haurata da baqaqen maganganu tayi, fadi take, Kedai wnn yarinyar anyi asararriya kuma tambadaddiya, ubanki ya kwanta jinya kwana dayawa ba'aga qafarki ba bayan duk a dalilin son xuciyarku keda shi yatsinci kansa awnn halin.


Kedai Zainabu nama rasa da wani suna xan alaqantaki dashi saidai ince miki KARIYA, kirasa dawa zaki kwana saida ubanki, asirinku ya tonu Mutan gari kowa yasan abunda kuka aikata, ace har asibiti Ubanki yabiki kuka kwana.


Tsananin mamaki ne yasa Zainabu kasa koda motsa 'yan yatsunta ne, ayaune tasan kuka ma rahama ne, don kuwa nemanshi tayi tarasa, saiki miqe kishiga kisameshi yana daki.....

A guje tashige cikin dakin Bbn nata tasameshi baya koda motsawa banda bakinsa datake kallon alamar yana son magana, da sassarfa ta isa gurinshi takai bakinta saitin kunnensa, ahankali yakece mata, Zainabu na kiyi haquri da duk wulaqancin rayuwa, komai yanada qarshe, kiriqe ibada, Ruwa Ruwa xansha kikawo min ruwa to tace tamiqe hartana tuntube, ruwan tadebo tashigo dashi dakin amma.....



*Vote,likes share, comments*

😍😍🤝🏼Anatare
Mummyn Fadyl CE





🎲🎲TUDUN DAFAWA🎲🎲


Rubutawa....MUMMYN FADYL (Fatyma Muhammad Adamu)

Wattpad @ *fatimamuhammadadamu*


INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION*
*[onward together]*
*{we give the reader's of ours the best out of the bests,, our inks are melodious and dropping a kinda lights to reader's}*
```THE PEN OF LOVE😘 HEAT TORCHING❤ TEAR OF SORROWS😭 CURDLES😊 GIGGLES😁 AND MARRIEGE THINK💑```
*```JUST GIVE US FOLLOW..**

_Al'ajabi yana gurin kanuwa wacce take tsiro akan kogi, kaidai nemi dacewar ubangiji kaga ni._



Fitowa tah.1⃣5⃣



Ruwan tadebo tashigo dashi dakin amma qarasowanta tasamu yana salati, riqe hannayensa tayi qam a jikinta candai taji jikinsa yasake, duk da batasan meye mutuwa kuma Yaya yakeba, to tabbas xata iya cewa mahaifinta mutuwa yayi, jijjigashi tafarayi amma babu shi. Wani qara tasaki me qarfi Wanda daganan bata sake sanin inda kanta yakeba.


((kullu nafsin xa'ikatul maut))

Qarar ne yafirgito da Zuwairah taiyo cikin dakin bashiri, ganinda tayi hannunsu sarqe Dana junane yasata saurin nufarsu cire hannunshi tayi daga cikin na zainabu snn tafara kiran sunanshi tajijjigashi itama amma shiru nanfa tahau kurma ihu.


Kan kace kobo gida yashika maqil Zuwaira kuwa banda ihu dafadin nashiga uku na lalace ba babu abunda takeyi, ana nunamata fadin sunan Allah a wnn lokacin shixai taimaketa amma inaa bata fahimtar abund aka gayamata. Ita tasan tafi kowa yin rashi don Mal.Dahiru tsayayye ne akan gidansa, bugu da qari baida tashin hankali, tanada tabbacin bamai iyawa halinta saishi, daga ta tuno irin wadannan abubuwan atake take qara daga hannayenta taxuba akanta tahau ihu tana burgima a qasa 'yan uwa suna dagata.


A cikin qanqanin lokaci jama'a suka taru inda kowa mutuwar Mal.Dahiru yatabashi saboda shina kowa ne, baida abokin tashin hankali bare gaba.

Maqocinsa Mal.Jafaru shikansa yasan yayi rashin Amini saida yamutu nema yaji lbrn Ashe yayi jinya saboda shi rabonda su hadu tun ranarda suka sanar dashi auren Lami.

Babu abunda yafi tsayawa mishi a rai kamar murmushinda yayi musu bayan yaqi karban kudinda Habu yamiqa mishi na maganar jinyar Zainabu Sam abun yaqi barin idanunsa, wasu siraran hawaye ne suke zirarowa daga idonsa ....

Miqewa yayi yatafi gidan Habu domin sanar da Habu rasuwar Sirikin nasa, yashafe a qalla minti Arba'in a qofar gida amma Habu baisamu fitowa ba gakuma lokacin jana'ixar takusa.

Shikuwa Acikin gida yana daki a kwance suna hira da Lami akan Jarin da xaibata, akaiyo aikan Kiran da mahaifinnasa ke mishi, harcikin ransa yanason xuwa amma kuma yakasa tashi saboda ba'a bashi umarnin hakan ba.

Can dai Lami tace mishi nasan yanxu haka kudi yaxo kabashi, nikuma baxan lamunci suyi ta tatseka bayan baka wani Tara yaraba, baxai yiwu inxuba musu ido kana basu kudi yanda sukeso daga baya gida qara yimaka nauyi xaiyi, yasuke so muyi, haka nekam abunda ta iya fada kenan. Bani kudaden da ke aljihinka kafita mishi haka, inyaso kace mishi kwanannan kasuwar ba ciniki kuma bana buqatar kawuce minti ashirin kadawo gida, don Nima inada buqatarka.

Kalmar da tadaga mishi hankali knn wai Buqata,shidai baisan wnn wace iriya bace, bata gajiya shiyanxu haka kunkuminshi ciwo yakemishi, amma ya lura ita ko ajikinta, itadai burinta a kwanta da ita, ai Buttt yamiqe yayi waje don daman yagaji da zaman Sam hirar ba dadi take mishi ba kamar akan qaya haka yakejinshi amma babu damar nuna hakan.


A qofar gida ya iske Bbn nan suka gaisa yake sanar dashi abunda yafaru, baisan dalili ba amma Sam baiji mutuwar tawani ratsashi ba baikuma yi jimamin taba, To saikaxo mutafi aje ayi jana'ixar dakai ko? Saboda lokacin yakusa yi don najima a qofar gidan naka.


Tsintar kansa yayi dacewa mahaifinnashi bari inshiga gida insanar da Lami idan ta Amince sai inzo muje, maimakon mahaifin nashi yaji haushi saima qara mishi qarfin guiwa yayi dacewa, eh wnn gaxkiya ne, mace ta gari irin Lami saida lallabi ae,yana washe baki, shikuma cikin jin dadi yakoma cikin gidan..

Sanar mata dayanda sukayi da mahaifinnashi yayi, itakua sai cewa tayi zauna anan nizanje inbashi amsar dakaina, komawa yayi cikin jin haushi bawai don xata hanashi xua gurin jana'iza ba, a'a saidon baxai samu yaleqa koda qofar gida ba.


Itako qerere ta tsayawa Mal.Jafaru Aka, shiyafara gaisheta batareda ta amsa ba tafara arattako mishi bayanai kamar haka, Gaxkiya Baba habu baxai samu binka ba, saboda baxaiyiwu ko sati banyi da Tarewa ba, afara dauke min miji ba, katafi kawae alabashshi kapin ayi sadakar bakwai yazo yayi muku gaisuwa, ai gaisuwa bata qarewa..


Maimakon yaji haushinta saima jiyayi a ransa tafishi gaxkiya ai bai kyautaba, yakuma fahimci shine mai laipi dayazo daukan mijin nata, nanfa yafara bata haquri, akan babu damuwa idan yasamu lokaci yazo yy gaisuwar, bata tsaya sauraran Shiba tayi ciki tareda banko qofar haryadan samu goshinsa. Ko ajikinta.


Acikin Gidan Mal.Dahiru kuwa bayan angama mishi wanka yayi daidai da farfadowar zainabu, ganinta tayi a kwance ga jama'a sai kuka sukeyi kowa idan ya kalleta sai hawaye tareda tausayinta. Ahankali ta isa gurin Goggonta a wnn lokacin babu alamar kuka atareda ita.


Goggo kisanar dani meke faruwa kicemin ba Bbn bane yarasu, kisanar dani mafarki nakeyi, duk tana maganar ne hannayenta a dunqule da juna, kukan goggon nata ne yatsananta, can tai qarfin halin cemata, kiyi haquri kidauki dangana Allahn da yabamu shi yakarbi kayansa, Qarfin hali tayi tace, Goggo ankai Bbn? A'a goggo kirakani inganshi, miqewa tayi, tareda yimata jagora har cikin dakin.


Gashinan cikin suturarsa, amma ba'a rufe fuskarsa ba durqusawa tayi da guiwowinta a gabansa, kallonshi takeyi tarasa metakeji a ranta, saboda batajinta a mutum a wnn lokacin, balle tace tanada damar yin tunani.

Gaf da fuskarshi tamatsa takaranta mishi fatiha, yanda taga fuskarshi da murmushine, yasata sakin murmushin tausayin kanta snn tafara magana. Inafatan kyawawan halayyarka subika mahaifina, Nagode da tarbiyarda kaimin Allah ya kyautata makwancinka, tabbas xanyi maraici, xanyi rayuwar qunci kai kadae dakedashi *TUDUN DAFAWA* yaukuma anwayi gari babu kai

Meyasa xaka tafi kabarni a lokacinda nakeda buqatarka, alokacinda banida kowa saikai,? Meyasa rayuwata batada dadi kamar na kowa? Meyasa aduk lokacinda na samu Abu saiya tafiBanida kowa saikai Baba naxo sanar dakai rayuwata takoma a hagunce, mijina yajuya min baya, waxan gayawa sirrin xuciyata, Bb kai kadai ne kake saurarena kuma katausaya min Baba narasa ka banida *TUDUN DAFAWA* Banida kowa Banida kowa Baba katashi maraicin zaimin yawa nida 'yata Baba katashi tafara kuka tana jijjigashi, nan mutane sukayo kanta aka dagata tana fusgewa akayi waje da ita.


Can dakin Zuwaira aka shigar da ita, kowa yadawo da kukanshi kanta, saboda kapin kowa yasan dadinshi to ita tafara sani, snn kuma batada kowa saishi din.


Hango mutane tayi anfito dashi a cikin Makara (motar kowa) a gigice tamiqe tayi Kansu tana Ku ajiyeshi kutausayamin karku fitar dashi daga gidannan acikinku waxai mayemin gurbinsa, waxai saurare ni, fitardashi waje sukayi inda itakuma tafadi agurin sumammiya😭😭😭. Kanta aka yiwo aka daga ta aka kaita cikin daki...



_Masu qorafi akan shafina baya yawa plx kuymin uxiri kunsan ni sabon shigane a system din, kunga kuwa sai ahankali, ina iyakacin qoqarina don ganin nafaranta ran fans dina, insha Allah xan gyara, Masoyana u mean alot to me_


😍😍🤝🏼 Anatare.
Mummyn Fadyl CE






🎲🎲TUDUN DAFAWA🎲🎲


Rubutawa....MUMMYN FADYL (Fatyma Muhammad Adamu)

Wattpad @ *fatimamuhammadadamu*


INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION*
*[onward together]*
*{we give the reader's of ours the best out of the bests,, our inks are melodious and dropping a kinda lights to reader's}*
```THE PEN OF LOVE😘 HEAT TORCHING❤ TEAR OF SORROWS😭 CURDLES😊 GIGGLES😁 AND MARRIEGE THINK💑```
*```JUST GIVE US FOLLOW..**

~Idan kanajin kankaa kafi wani, kasani kapin kaifa dubbannanka sunyi tashensu a qarshe kuma sunshude!! Allah ne meyi~


Fitowa ta. 1⃣6⃣

Xainab saida tashare kwana uku batare da tasan inda kanta yakeba, a wadannan kwanakin yarinyarta madara goggonta take bata takesha, A ranar da tadawo hayyacinta abub yadawo mata sabo, intana zaune saidai kaga ruwan hawaye yanabin kuncinta, babu magana a gurinta kam, intambaya ce saidai tabada amsa tareda gyada kanta, sama ko qasa.

A waje gurin maza kowa yayi matuqar mamakin rashin ganin Mal.Habu koda a gurin makoki ne, to hakaxalika acikin gida ma, inda akaita tambayarta ina yake? Basu amsa takeyi da cewar yayi tafiya.

****************

Randa akayi sadakar bakwai mutane duk sun watse, Zainabu tana daki tunanin duniya duk ya damu rayuwarta, diyarta take qarewa kallo yarinyar takoma tamkar qashi da rai, sakamakon rashin wadataccen ruwan Nono, ita kanta tanajin canji ajikinta koda tafiya takeyi, don yanda iska yake kadata ma tasan rashin qarfi ne ke dawainiya da ita.


Tun tana tunanin xataga mijinta, to xua yanxu tagama cire ran xaixo, ahalinda take ciki yanxu a rashin madafa ne, zata tattara takoma gidansa, kobanxa a gidansa xata samu gurin kwana batareda an tsangwameta ba.

Zuwairah ce tashigo itada yarta, yayar tata ce tafara magana, ke Zainabu yaukam ai anyi bakwai saiki tattara ki koma gidan mijinki, kin Riga kingama yin kashi a gurin xamanki, kedai Zainabu bantaba ganin asararriya diya marar Albarka irinki ba, kece sanadiyyar mutuwar mahaifinki, snn ga yarinya Wanda ba'ada tabbacin 'yar Habu ce, tunda kowa yashaida dalilin haihuwarta ce mijinki yaqara aure, yakuma cire hannunsa a gabadayan al'amarinki, tabbas qarshenki baxaiyi kyauba.


Zuwaira takarba tace kitashi ana miki magana kin tsaremu da shegen idanun naki irinna Uwarki, kinyi gadon wahala ae, yanda uwarki ta mulki ubanki kinyi tsammanin kema xaki samu wnn gurin a gidan Habu ne?

Yanxu gidannan nawane da 'yan uwana kijira randa nayi niyya a raba gado, inyaso idan aka Raba kyazo kixauna a fegin ki. Amma yanxu bakida gurin zama, koda kin zauna baxan ciyar dakeba, kisani ubanki bai bar komaiba sai wnn shegen dan qaramin shagon, Wanda yanxu Yahuza qanina ne xaifara zama aciki.

Banda mugun hali irinnaki ace ubanki yarasu a rasa mutum daya a dangin mijinki daxaixo gaisuwa daga mata har maza, gaxkiya mugun halinki yawuce a misalta.

Duk maganganun dasukeyi dinnan kanta na qasa bata daga ido takallesu ba balle su sa ran xata tanka musu, bahaka sukeso ba, sunso tayi magana, inyaso sutara mata jama'a suymata tofin alatsine.... A qarshe saima durqusawa tayi a gabansu tace.

Kuyi haquri nasan kuma bakwajin dadin zama dani, Umma kisani Wanda ya hadamu zama tare baya raye kuma kobabu aure tsakaninki da Baba xaki iya share hawayena, insha Allahu xanyi nisa daku baxaku qara shaqan baqin ciki ko kadanne a dalilina ba.

Daga haka ta tattara kayanta Dana 'yarta tayi waje tabarsu a gurin sororo, taxo fitane dab da dakin Babanta kuka me qarfi dakuma tsuma zuciya ya kufce mata batare da ta shirya wa zuwanshi ba.

Nantake taji al'amari da dama yana dawo mata tamkar a wnn lokacin ake yinsu, tayi kuka me isarta snn tafita, tadanyi tafiya kapin tajuyo taiwa gidan Nasu bankwana tagama cire ran zata qara samun farinciki a wnn gidan, Babu uwa babu uba babu kuma *TUDUN DAFAWA* me adaidaita tasamu tabiyashi yakaita har qofar gidan ta, wani mummunar faduwar gaba ne yaziyarceta, batasan yanxu kuma wace rayuwar zasu cigaba dayiba, saidae kawai tasawa zuciyarta indai bai furta mata sakiba to har gaban Abada baxata daga qafarta tabar gidan ba.

Tanashiga bata kalli qofar dakin Lami ba, tayi shigewarta dakinta, saidae kuma abubda tagani yabata mamaki, buhunan abinci ne reras acikin dakin, dakuma sauran kayayyakin abinci.

Kenan nanne yaxama ma'adanin kayan abinci? Tamvayar zuciyarta tayi, ganin batada amsar tambayan yasata kame bakinta gumm.

Fitowarta alwalar sallan mangariba ne yayi daidai da shigowar Mal.Habu gida. Tsayuwa yayi yana kallonta yarasa me yakeji akanta, yanason yaga farin cikinta yana kuma jin al'amari mai girma akanta, amma kuma sashin data tsaneta acikin zuciyarta tafi qarfin rinjaye.

Sunjima suna kallon juna, yarame bana kadanba, inda anashi fannin kuma yake kallon takoma tamkar tsinken sakace saboda rama, tafiya yafarayi ahankali kamar antuno mishi da wani Abu a take yaji yatsaneta a rayuwarsa bayason kallonta da duk wani abunda yashafeta.
( karku manta aduk lokacinda yataka wnn layar da Lami ta bunne to komai kwance mishi yakeyi). Lami bata damu da sallah ba amma duk rintsi bata mantawa da yayyafa ruwa a inda layarta yake... Domin sharadinsa kar gurin yabushe.


Lami tana daki tajiyo sallamar Mal.Habu amma shiru bataji yaqaraso ciki ba, maza tamiqe don ganin meya tsayayi, Tarar da Zainabu tayi a tsakar gidan nanfa ta tsuke mummunar fuskarta tanupe su, Bbn Sadiya meka tsayayi haka na ganka da wnn matar? ( kuji wai Bbn Sadiya😜) kame kame yafarayi itakuwa data fahimceshi nan tahau surfawa Zainabu bala'i ta inda takeshiga batanan take fitaba, itakuwa wucewa tayi tai alwalarta tanupi cikin daki....


Yakasance tun daga wnn ranar Zainabu tayi bankwana da ganin Mal.Habu saidai taji muryarsa watarana kuma taleqashi snn itace maiyin girkin takuma kaiwa Lami domin taraba, intai niyya tabata inbatai niyya ba kuma acemata tajira nagaba, bata taba tanka mataba, tasa aranta baxata bawa Lami damar ganin Lagonta ba...

Abun Mamaki shine Sam Allah yamantar da Lami cewar Zainabu pa tanada yarinya ita duk atunaninta yarinyar tamutu, tunda bata ganinta, ita yanxu damuwarta tasamu ciki...



!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!
Bayan shekaru biyu

Kapin xuwan wadannan shekarun abubuwa da dama sunfaru a wnn zaman babu abunda Zainabu ta tsinta na farinciki, saidai ixuwa yanxu tamasamun abinci balaipi takanyi dabara kapin tagama tadeba musu itada 'yarta suci adaki, Nana taqara girma har anyayeta, ta taso cikin gatan mahaifiyarta takuma yi sabo da zaman daki don Mamanta bata taba fita da ita, kullum tana daki abunta, har uwar tagama uzirinta tadawo ciki, dakinsu kuwa yagama zama dandalin ajiye abinci, inda hakan ya haddasa musu alaqa da beraye babu dare babu rana,.

A bangaren Lami kuwa tasamu yanda takeso kudi kan tana samu yanda ta tsara haka rayuwar take tafiya mata, tsakanin Mal.Habu dakowa nashi baqar magana snn Lami bata sararwa kowa amma kuma sunkasa jin haushinta saima qara qaunarta dasukeyi.

Abu daya yake damunta,shine yanda Sadiya take nema tamaida kanta Kariya, bin maza takeyi kamar Yaya, Sam bata zaman gida, dazaran uwar tafice itama zata fice su watse subar gidan.

Hakanne yasa Zainabu tafara sakewa a gidan itada NANA yarinyar tafara sabawa da wasan tsakar gidan.

Suna tsakar gida Nana tana kan cinyar mamanta itakuma tana mata kitso, yarinyar kyakykyawa ce ajin qarshe ga gashinta Harkan wuyanta tanada wushirya, fara ce amma rashin jin dadi yaboye hakan.


Lami ce da Ayashe sukai mantuwar kudin Zannuwan da xasu aika dashi gurin wata dillaliyar dasuke sayar mata da kaya don haka suka dawo dauka afujajan.

Babu sallama suka fado cikin gidan sukuma lokacin anfama yiwa Sadiya kitso mahaifiyarta tana tsokanarta itakuma tana tsalle tareda kyalkyala dariya, Lami ce ta waro idanu waje tana nunawa Ayashe NAnan.............



😍😍🤝🏼Anatare
Mummyn Fadyl Ce




🎲🎲TUDUN DAFAWA🎲🎲


Rubutawa....MUMMYN FADYL (Fatyma Muhammad Adamu)

Wattpad @ *fatimamuhammadadamu*


INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION*
*[onward together]*
*{we give the reader's of ours the best out of the bests,, our inks are melodious and dropping a kinda lights to reader's}*
```THE PEN OF LOVE😘 HEAT TORCHING❤ TEAR OF SORROWS😭 CURDLES😊 GIGGLES😁 AND MARRIEGE THINK💑```
*```JUST GIVE US FOLLOW..**


_WNN SHAFIN NAKINE QAWATA, AMINIYATAH_ *ZAINAB YUSUF*


Futowa ta.1⃣7⃣


Itama Ayashen a firgice take kallon inda ake nuna Matan, Wacece wnn din? Tambayarda taiwa Lami kenan 'yarta CE Lami tafada ahankali kamar meyin rada, hakan yayi dai dai da juyowar Zainabu takalli bakin qofa, saida gabanta yafadi sanadiyyar ganinsu, amma tayi tamkar bataji komai ba, kuma bata nuna musu tafirgitan da tayiba, asalima yitayi kamar bata gansu ba, cigaba tayi dayiwa diyarta wasa sunata dariyarsu a qarshe kuma sukayi cikin daki...

Ayashe ce tayi qarfin halin Jan Lami cikin daki, xaunar da ita tayi don talura bata cikin hayyacinta ko kadan, Ke Lami ki kwantar da hankalinki indai kina tare dani kisa a ranki ba'ayi damuwarda xata xota gabanki baki kawardashi ba.


Kudi ake buqatan kinsan hakan, maza tattaro abunda kikedashi a dakinnan mutafi gurinda xa'ai mana maganin 'yan iska yanxunnan. Ni kincemin 'yar tamutu shiyasa bantaba kawo lamarinta a gaba na ba, Batun Ayashe ne yasata sakin ajiyar zuciya me qarfi cikin kuzari ta miqe ta tattaro kudadenta da Wanda take tatsa agurin Mal.Habu dakuma wanda take sata, don bai isa yacire wando adakin ba, saita yasheshi. Haka xaisamu babu komai a aljihunsa kuma babu damar yin magana.

......................................................
Tun bayan dawowarsu daga samo maganin da xasu sawa Nana ne, ta fara Jan Zainabu a jiki, Itakuwa bataji aranta alkhairi ne hakan ba, shiyasa ko kadan takasa sakewa da ita, tsakaninta da ita gaisuwar nan dai dasuka saba. Itakuwa tarinqa janta da hira kenan

A halinda suke ciki yanxu Lami takan basu isashshen abinci, snn ta fara qowarin taga yarinyar tasaba da ita,yanda xata aiwatar da qudirinta batare da Zainabu tazargi komaiba, amma Nana Sam taqi sabawa da ita, da zaran tanufota take fara ihu baxata taba bari tadauketa ba.

Lami abun yana matuqar qona mata rai, tarasa yanda xata bawa yarinyar maganin, amma ayau tadauki aniyar saita cimma burinta, don tafijin haushin yarinyar fiyeda yanda takejin haushin uwar.

Alala ta aika almajiri yasayo mata, yaqara gyarashi, ne tanupi dakinsu, sallama tayi kamar mumina snn tace Zainabu kuna cikine? Eh munanan, shigowa tayi taxauna

Please Login or Register in order to submit comment