You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

missing dinkuba wlh nikaina nasan nafadi ba daidai ba, aduk Inda kuke inafatan wnn shafin xai iskeku I missed u gals_😭


Fitowa ta. 3⃣9⃣


Sai yamma liss matar baffan Sadiya tadawo gidan aiko tayi muguwar gani, Wanda saida yasata jin faduwar gaba, ganin da taiwa Lami a gidan ta, dakiya tayi taqaraso suka gaggaisa cikin mutunci snn tace, kece dayamma haka, Allah daiyasa lpy?


Aiko cikin kukan kirsa Lami ta juye mata abunda yafaru takuma qara mata qarairayi Wanda batama gayawa baffan sadiyan duk dai wai don atausaya mata.

Hummm Allah yakyauta tafada, don maganar bawai yashigeta bane balle ya girgizata, yau dinnan a gidan Taro tagama jiyo mugayen halayyar Lami da kuma rashin mutuncin da Ayashe taimata.


Bata dora komai akai ba ta tashi tayi shigewarta daki, tana tunanin yanda wnn zaman nasu xai kasance, har cikin qasan xuciyarta tana roqon ubangiji ya takaita musu xamansu tare, xaiyi wuya ta iya jure xama da Lami.


Lami ganin haka tabe baki tayi snn tace a fili, mutum dai dole yayi haqurin xama dani, tunda Wanda yakeda mallakin gidan ya aminta dani aikua dole kowa ya xuramin ido, idan kua mutum yace xaija dani xannuna mishi ni jigida CE dai dai nake da qugun uban kowa ta danna tsuka a qarshen maganarta.

Itadai bata cemata komai ba, tajira dawowan mijinta, shikanshi yaji kunyar matarsa akan hukuncinda ya yanke batareda Neman shawaranta ba, domin itace xata xauna da ita, don yasan halin Lami ba dadi ne da ita ba kokadan.

Haquri yayi ta bata tareda nuna mata taimakonta xasuyi taxauna na Dan lokacin qalilan kapin yayi tunanin abunda yakamata yayi akan al'amarin, dayake macece mai sauqin kai ta amince mishi tareda fatan Allah yaxaunar dasu lpy, da Amin ya amsa mata yana murmushi.

A wnn yammacin aka kintsawa Lami dakinda xata xauna, itadai matar baffan Sadiya kaffa kaffa takeyi da duk abunda xai hadasu, tana bata girmanta, amma ita Lami ganin hakan yasata jin ai takai ne, tanakuma da babban matsayi yakuma samata danyen tunanin ko mijin ne yasata dole saitayi mata.

_mai hali baya fasa halinsa_

Har washe gari Nana bata qarasa kowa nacikin gidan a idanunta ba tun tanajin tsoro harta sake, idan lokacin abinci yayi ana kwankwada mata kofa amma idan tafito baxataga kowa ba, saidai ledan abinci xata gani, itakan hakanma yafi mata dadi, don batason Hulda dasu.

*WASHE GARI*

Mal.habu ne nahango a rumfar kasuwa shida wani abokinsa me shayi suna hira inda yake qara roqonsa akan yabashi rancen kudi amma yaqiya, domin yasan ahalin da ake ciki Mal.Habu baida kudin da xai iya biyansa.

Mal.Habu dayaga abokin nasa baida niyyan bashi yasashi cemishi to Salihu xan baka jinginar gonata Wanda itakadai taragemin a rayuwa ta, xanbarmaka ita kabani wadannan kudaden koda bayan tafiyata ne saika sayar ka ajiyemin canjin, domin a halin yanxu wlh bana sha'awan garinnan ko kadan.

Salihu ne yanumfasa snn yace to shknn Allah yashigemana gaba, saigobe dasafe xan baka, Amma dai yaukam ba'a kasuwa xaka kwanaba ko? Murmushin takaici yayi batare da yabashi amsa ba, hakanne ya tabbatar wa salihu xarginsa.

Kayi haquri Habu kaxo muje gidana akwai daki a aljihun xaure, yaron danane kapin yayi aure anan yake da zama.

Kanaga bandaura maka nauyi ba? cewar mal.Habu, ah ah ah wani nauyi babu komai ai yiwa Kaine.

Sai guraren qarfe goma da Rabi snn suka nupi gidan salihu, jagora yayi mishi har Dakin yatabbatar akwai komai na buqata daidai na talaka, snn yafito yasa matarshi tasamusu abinci, yakawo suka ci snn sukayi bankwana salihu yashiga cikin gida ya kwanta.

Shima kwanciya yayi yafara tunanin rayuwa a haka har bacci barawo ya saceshi batareda ya Ankara ba.

Cikin baccinsa kuwa yafara tariyo rayuwar baya, acikin mafarki amma tamkar faifayin bidiyo haka yake kallo, babu abunda aka ragemishi har xuwa ranarda yarabu da Ayashe.

Idan kaga yanda yake baccin ajiqe sharkaf, kallo daya xaka mishi kasan baccin wahala ne, shikanshi badadinsa yakeji ba,

A firgice yafarka yana salati abunne yafara dawomishi ai nan hankalinshi ya tashi yatuna da Zainabu, hankalinshi yakai qololuwa gurin tashi ina Zainabu ina 'yarshi Nana? Haka yayi ta tunanin yanda xaiyi yagansu amma yarasa mafita.


Yama manta da yanda dare ya tsala ba yamiqe a firgice yabude qofa da xummar barin gidan, amma asalin qofan a rufe take da kwado, kuma yaga babu dacewar yabugawa Salihu qofa a wnn Daren yanatare da iyalansa, haka yadawo Dakin badon yaso ba.

Ganin zaman ya gagareshi yamiqe yafito yadaura alwala yakoma Dakin yafara salloli yana roqon Allah ubangiji yasa al'amarin yaxo mishi cikin Sauqi, bayan ya idar ne yadinga roqon Allah ya yimishi kyakykyawar sakayya akan cutar dashi da Lami da Ayashe sukai musu domin sun cutar dashi matuqa.

Yananan baisan lokacin da yafashe da kuka wiwi kamar qaramin yaro sakamakon tuna yanda rayuwarshi a baya ya kasance lallai ya musgunawa Zainabu daAhalinta cikin rashin sani.

&&&&&&&&&&&&

Zaune suke gabadayansu a falon sunata hira, qarfinshi hiran dai Mummy ce da IBBY domin Aliey kam a cike yake ya hade fuskar nan, musamman ganin yanda Zarah keta xuba shagwaba mummy da IBBY nata biyemata.

Musamman ma yanda IBBY ketayi kamar wata qanwarshi ta jini, yarasa menene yake burge ibby akan wnn shegiyar yarinyar kamar gwai~gwai, shikansa yasan Zarah ba mummuna bace amma baisan dalili ba haushi take bashi.

Mummy na'am ibby, nikam yanxu 'yarki shekaranta nawa? Murmushi mummy tayi snn tace, IBBY nalura fa take taken ka akan 'yata to tunwuri kasani, baxan bada 'yata wa tuxuru ba..

Baruwana mummy bahaka nake nupi bama, to shknn shekarar 'yata Tara, xata Shiga na goma insha Allah, uhmmm yafada snn yace yana Sosa kanshi um um umum.

Mummy CE ta katseshi da cewa IBBY 'yata tayi maka qarama snn wlh inason kapin 'yata tai aure yaxamana munsamu waraka akan wnn matsalar kagane menake nupi aiko?

Jinjina kai yayi snn yace nagane mummy wlh da matar nan nake kwana nake tashi narasa tayanda xan bullo wa al'amarin ne.

To maganar da xan fada shine gaxkiya duk Wanda yayi sanadiyyar warkewar matarnan insha Allahu xanbashi auren 'yata, nabaka satar ansa, tafadi tana kallonshi tana dariya..


Sai a lokacin yakai kallonshi kan zarah dataketa kallon cartoon batamasan mesukeyi ba, mummy ce takirata tacemata, Zara kinason Yayanki IBBY?

Tahowa da gudu tayi taxi gabanshi yafara kallonshi dakyau, can kua saitace mummy yayah IBBY yanada kyau inasonshi amma nafison in auri Yayah Aliey yafishi kyau.

Ai zaburowa yayi.......


😍😍🤝🏼Anatare
Mummyn Fadyl CE




🎲🎲TUDUN DAFAWA🎲🎲


Rubutawa....MUMMYN FADYL (Fatyma Muhammad Adamu)

Wattpad @ *fatimamuhammadadamu*


INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION*
*[onward together]*
*{we give the reader's of ours the best out of the bests,, our inks are melodious and dropping a kinda lights to reader's}*
```THE PEN OF LOVE😘 HEAT TORCHING❤ TEAR OF SORROWS😭 CURDLES😊 GIGGLES😁 AND MARRIEGE THINK💑```
*```JUST GIVE US FOLLOW..**


Fitowa ta. 4⃣0⃣.


Ai zaburowa yayi danufi yin kanta, a guje ta haye kan kujera taboye ta bayan mummy tanacewa, to qarya nayi maka bakada kyau? Kuma wlh saina aureka , koxaka yi kuka saina aureka, mummy da IBBY mexasuy inba dariya ba,

Shiko gogan yana tsaye yanata cin magani, ai dayaga abunnata bana wasa bane matsowa yayi xai cafkota a bayan Mummyn, ai sai cemishi tayi meye haka Aliey nalura fa bakasan Zuru da idanu ba? Yanxu meye abun duka ajikin baby?

To banaso tafada tana hade fuskanta, tasan muddin ba hakan tayimishi ba, tofa baxa'a wanye dashi lpy ba, ganin yanda tayi da fuskane yasashi dan ja dabaya yana cewa wlh mummy kindaurewa zarah gindi shiyasa take abunda ranta yakeso, kekuma xamu hadu ne,wlh zarah kapin intapi sainai miki dukan da zaki dinga tunawa dani...


Gwalo taketa mishi shiko saiqara cika yakeyi, inda yakeji a ransa inama yaganta a gabansa wlh shikadai yasan mexai mata.

Mummy tace amma yanxu idan kuka tapi kuna gama masters din xaku dawo gida ko? Aliey ne yayi saurin cemata ni wlh saina gama P.H.D na xan dawo gidannan yanayin maganar nashi ne zai tabbatar maka a cike yake.

Ibby ko cewa yayi mummy nidai insha Allahu xan dawo nanda shekara uku kapin lokacin nasan 'yarki taqara girma, ikon Allah IBBY babu ko kunya? Tafada cikin barkwanci bahaka bane mummy, to nidai 'yata baxata xauna da kishiya ba kaji policy na.

Nakuwa amince mummy, tsaki Aliey yayi yabar musu parlon, da dariya suka bishi, IBBY yacewa mummy nidai mummy kimin alqawarin xaki bani zarah idan nadawo.


Tabdi abakani inkoma gidanku da xama, yanda kuke da uban yawannan, sukaji muryan Xarah karaf a cikin maganar tasu, mummy ce tajuyo tace to uwar sanabe bake xaran ake nupi ba, zarah babba ake nupi matar Ibby.


Mummy toba yace yanason xai aureni ba, yafasa nidin kenan? Mummy wlh nima xan girma xankai kamarsu aunty khadija fa, tafada murya a shagwabe, shidai IBBY shagala yayi da kallonta, komai zarah takeyi burgeshi takeyi, yanason yarinyar duk da dai babu wani alamun girma daya bayyana a jikinta balle ace sha'awar wani abu nata yakeyi.

Haka dai sukaita tattauna yanda tafiyar nasu xai kasance xua wani sati, a qarshe yayi wa mummy sallama tareda cewa zarah ta rubuta mishi tsaraban da takeso idan yatashi dawowa yataho mata dashi, aiko nan tahau tsallen murna.


&&&&&&&&&&&&&

Kiran sallan farko akunnensa akayi shi, ji yakeyi kamar salihu xai makara sallah, gashi yanajin kunya xua yimishi magana amma harga Allah ya gama qaguwa yafito suje masallaci domin yabada uxiri mai matuqara muhimmanci a gabanshi.


Ankoyi sa'a domin Salihu ma mutum ne dayake matuqar daraja sallah a cikin jam'i, Mal.Habu na xaune yaji ana kwankwasa qofa, bugawa na daya, nabiyu saigashi ya fito.


A'ah yaya kamar jira kakeyi, uhmmm kawai yace mishi snn yace kayi alwala mutafi masallaci, da alwala ta ajikina, salihu xai qara magana, mal.Habu yafara tafiya don haka shima yarufa mishi baya.


Ana fitowa daga masallaci suka gaisa Mal.Habu yayi mishi godiya sosai a bisa karamci da yayi mishi, snn yacemishi yanason shiga gari.


Ah to muje mana inbaka kudin ka karya kumallo tukunna, yau wani irin uxiri ne haka, don Allah kayi haquri sai gari yadan washe, Mal.Habu yayi matuqar qoqari gurin danne xuciyarsa yabi salihu gidansa kudin kawai ya karba, bayan sunyiwa maqocinsa guda biyu bayani domin xamtowa shaidu, amma baya tunanin xai iya saka komai a cikin cikinsa, don haka yayi masa sallama..


Kai tsaye gidansu Zainabu ya nufa, sallama yayi, yajima a qofar gidan harma ya fidda tsammanin xa'a fito, saiga wani mutum yafito, hannu yabashi sukayi musabiha, snn yanemi ixinin ayi mishi magana da Umma Zuwaira.

Mutumin cemishi yayi lpy dai bawan Allah? Nine mijinta duk saqonda xaka bayar ta hannuna yakamata kabadashi, gaban Mal.Habu ne yafadi, wato dai tabbas abunda yagani amafarki yafaru dagaxke kenan? Inko hakane tabbas sauran baya tunanin xuciyarsa xata iya dauka.


Dakyar yashawo kansa yakiramishi Zuwaira, tana fitowa kua taganeshi da mamaki ta tarbeshi, domin bata taba kawowa a ranta xai qara kallon gidan ba balle tasa ran ganin kwayar idanunsa.

Bayan 'yan gaishe gaishe ne yafara da bata haquri akan abubuwan da yakeda Dan masaniya na gameda wulaqancin da yayiwa Zainab, snn yaqara da cewa yanxu ma haka yaxo tafiya da itane dakuma 'yarsa.

Dagowa tayi tareda zuba mishi idanu na Dan wani lokaci, snn tacemishi bata fahimci komai na gameda abun da yasanar mata ba.

Aiko nan yabayyane mata duk abunda yafaru, aibatasan lokacinda tasa hannu akai tafara kuka ba kamar ranta xai bar gangan jikinta, batare da taboye mishi komai ba tasanar dashi iyakan abunda tasani tun kapin rasuwan Bbn Zainabu har xua ranar qarshe na zuwan Nana gidan.


Tashin hankali Wanda ba'a samata rana, to itace ta xiyarci kwakwalwar mal.Habu banda salati babu abunda yakeyi, damuwarshi ina suke ta ina xaifara nemansu?


Itama cikin dana Sanin abunda ta aikata musu tafara Neman yafiyanshi tareda tsinewa Lami harma da Ayashe, nan taqara da cemishi ai itama Gadon Zainabu da taci baiqare ta da komai ba, domin yanxu mijinta ya kwace komai dagashi sai matarshi da 'ya'yansa sukecin kayansu, itada babu duk dayane a gurinsa, duk wannan maganar cikin kuka take sanar mishi.


Bayan yagama jin tabakinta ne yayi mata sallama, yafara tafiya yana tunanin ta ina xai fara? Babu shakka Zainabu da 'yarta sunyi rayuwa marar 'yanci a yanxu baida burin yaga daya wuce yaga yasamu haduwa dasu yaroqi yafiyarsu koxai samu sassauci, a iya abunda ya fahimta batare aka nemesu aka rasa ba.


A qofar gidan Iyayenshi ya xauna yana tunanin wani guri yakamata yafara xuwa nemanta, can yayi tunanin tafiya yanemi aiki mekyau yanda xai dogara da kansa, yakuma samu makamin yaqin neman iyalansa, domin a wnn zamanin idan bakada kudi kai da babu duk tafiyarku daya...

&&&&&&&&&&&&&&

*Bayan sati*

Alhaji ne xaune a falon sa, yanashan lemu me sanyi, a gefenshi wata dattijuwa ce sai yauqi takeyi ita a dole ana soyewa😜. Wayarshi ce tayi qara miqewa tayi tadauko mishi.


Sallamar ya amsa snn yace kadawo? To shknn ranka ya Dade insha Allah da yamma xamu taho, OK to shknn oga saina iso, ahuta lpy.


Yakatse wayar tareda kallon karuwar tashi yacemata mushiga cikin daki in sallameki don xua anjima xanbar garin.

Miqewa tayi sukai ciki jiki na kyarma, kuluwa knn jarababbiya ga kudi amma jarabarta baya barinta, tashahara gurin bin maxa, gata dai babba Wanda a shekare xata girmewa Alhaji nesa ba kusa ba, amma zalamarta bata barinta.


Bayan sun kammala badalan sune, sukai bankwana da juna akan saiyaqara dawowa domin shidama irin hakan ke kawoshi garin.

Domin iyalansa yabarsu akan yaje meeting ne Abuja meeting alhalin yananan yana kotsewarsa a garin katsina.

Fitowa yayi tareda bawa kuluwa umarnin tayiwa Nana magana tafito, kamar 'yar cikinsa haka yake bata umarni duk da tanajin haushin abun amma bata taba nuna mishi don sanin halinsa. _Niko nace tsare gida mutuncin dandi_


........


😍😍🤝🏼 Anatare
Mummyn Fadyl CE





🎲🎲TUDUN DAFAWA🎲🎲


Rubutawa....MUMMYN FADYL (Fatyma Muhammad Adamu)

Wattpad @ *fatimamuhammadadamu*


INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION*
*[onward together]*
*{we give the reader's of ours the best out of the bests,, our inks are melodious and dropping a kinda lights to reader's}*
```THE PEN OF LOVE😘 HEAT TORCHING❤ TEAR OF SORROWS😭 CURDLES😊 GIGGLES😁 AND MARRIEGE THINK💑```
*```JUST GIVE US FOLLOW..**


_JINJINAN BAN GIRAMA GAREKU_

*MUM SAFWAN*
*ZAINAB GWANI*
*TAKWARA TAH*
*HAFSAT*
*MMN SADIQ*
*MMN ARIFA*
*MMN IRFAN*
*MMN ARIF*
*SADIYA*
*MMN HUSNA*
*UMMY*
_kunada yawa idannace xan lissafoku duka wlh page din baxa'ai komi a cikinsa ba, inaqaunar masu qaunata aduk inda kuke._

*Masoyan Nana yaukam kusakemin Mara inyi fitsari*


Fitowa ta. 4⃣1⃣



Samun Nana tayi a xaune akan darduma domin shina
ta idar da sallah tana xaune tana laxumi, duk da hankalinta ba'a kwance yakeba amma wnn sati dayan datayi bata xua ko ina kallo daya xakai mata kasan hutun yafara ratsa fatan jikinta.


Sanar Mata da saqon Alhajin tayi tanawani yayyamutsa fuska kamar taga kashi, itadai tanajin haushin yarinyarnan tun ranar da tafara ganinta, duk da tanada tabbacin batacikin tsarinda mutumin nata yakeso.


Itakua Nana jin abunda tasanar mata yasata qara zuzuta addu'oi nda takeyi taqara qaimi gurin yiwa Allah subhanahu wa ta'ala kirari tareda roqonsa tana cewa Ya Allah don girman zatinka, ya Allah don buwayarka, don girman Al'arshinka, ya Ubangijin dukkan halittu, Allah karka bari in wulaqanta, ya Allah kana ganina gashi xasu fitar dani domin kaini gurinda nakeda tabbacin cutar dani xa'ayi akuma wulaqanta imanina.

Ina tawassali da ayyukana kyawawa Wanda nikaina bansan nayisu ba, Allah kasa fitar dani da xasuyi yaxomo mini silar samun farinciki a rayuwata, kasa rayuwata ta haskaka a sakamakon fitar dani daxasuyi, jin ana kwala mata kirane yasata saurin tsagaita addu'an ta ta taso ta fito.



Mal.Habu a qarshe tasha ya yanke shawaran tafiya yagama yanke hukuncin tafiya garin Kaduna don yanada wani Dan baffanshi Wanda xumuncin nasu yayi rawa, shiyana can sana'ar gadi yakeyi a wani gida, xaije gurinshi tunda xua yanxu yasan shikam yasan kan gari, baxai rasa yanda xai taimaka masa ba.


Yana isa tasha yasamu mutum dayane yarage motar tacika, don haka yana xua bada jimawa mota ta tashi akahau hanya, kallon garin yaketayi bayajin xai yi kewarta domin babu komai acikinta Wanda yaxama xai iya nunawa akan nashine, baida kowa sai yayyunshi mata guda biyu Wanda babbar tasu daya take yanxu da babu, domin batada lpy, sai yanda akai da ita.


Tafiya sukeyi sun hau titi sambal, direba kejansu, Alhaji na gaba Nana kua itakadai CE a baya, kalle kalle takeyi idan ka kalleta xakai tunanin kallon hanya takeyi amma a zahiri idan xa'a titsiyeta tafadi abunda take kalla baxata bada amsaba, domin xuciyarta yanacan yana aikin tunane tunane.


Suna gab da shiga garin Kaduna ne direban ya kalli Alhaji yacemishi ranka ya dade xamu shiga gidan mai domin man namu tayi qasa dayawa, badamua kawai yace.


Yayi dai dai dai da lokacinda motar su Mal.Habu ma takarya kwana domin shan mai, motar Alhaji ne a gaba nasu yana baya, amma saisuka je dayan gefen dayake fuskantar na Alhajin.


Mal.Habu ne yake bakin window itama Nana ajikin windon take, saidai bagurinda take kallon yake kallo ba, angama samusu man xasu fita agidan man kamar walqiya tajuyo waxata gani? Mutum tagani kamar Babanta kapin taitunanin koshine koba shibane direbansu yafinciki motar kamar mai shirin tashi sama.


Kuka tafashe dashi iyakan qarfinta, Tsawan da Alhajin ya daka matane yasata rufe bakinta da tafin hannunta batareda tasan lokacinba, sheshsheqa tacigaba dayi tana waiwayen baya.


Haka sukaita tafiya hankalin ta gabadaya yana baya, tana kallo wannan motar taxo da gudu tawuce nasu batasamu xarafin qara samun ganin abunda takeson ba, hakan ne yaqara dagula mata rai.



Gab da sallar isha suka iso garin, baikirashi a waya ba domin yasan Inda suke haduwa idan irin hakan ta taso, shiyasa kai tsaye yabawa direban umarnin awuce dasu can.


Sun iso tasha, kowa yanata sauka yana kama gabansa, mal.Habu kuwa yama rasa ta Ina xai fara, domin shi rabonshi da xuwa tun Zainabu tana Amarya shikuma matar mutumin tarasu sukuma sukaxo mishi ta'axiyya yasan anguwan dakuma gudan dayake amma baida tabbacin haryanxu ko yananan.


Xuciya daya Yakama hanya yatari mai adaidaita yakaishi gidan snn ya sallameshi.


Kai tsaye yanufi falon itakuma Nana kamar wata rakumi da akala haka take binshi a baya, sallama yayi yashiga, Alhajinne yadago a raxane domin yagama mantawa sunyi waya dashi xaikawo mishj yarinya guest house dinshi, gashi kamar matarshi tana zarginshi yanacemata yau xaidawo ta taho gidan.


Alhaji yana qarada shigewa Falon NANA ma Tamara mishi baya, ganin matarshi a xaune a falon ta hakimce said a yasa gabansu duka faduwa banda Nana da batasan halinda me ake ciki ba, itadai fargabanta daban.


Alhajinne cikin iya bariki dasanin halin duniyanci yayi saurin cewa Gaxkiya kacika alqawari kaga faduwa yaxo daidai da xama tunda kaga itama Maryam din tananan saira duba idan tayimata saisu tafi tare.

Duk da ba gaba dayan xuciyarta bane ya yarda da abunda yafadaba, amma taji sanyi ganin komai ya wakana akan idonta, ko banxa wnn qofar kam ta kulle.


Yaqara dacemata Maryam ga yarinyar da kika isheni da qorafin kinason 'yar aiki amma naqi, to yaudai nacika miki burinki, shknn ko yafada yana jefan Nana dawani shu'umin kallo.


Murmushin takaici ta jefeshi dashi domin alamun rashin gaxkiya ya bayyana a fuskokinsu gaba daya, banda Nana datake dofane kamar jira take ace ishh ta xura da gudu.

Basai gobe bama nagode sosai yarinta tashi mutafi, Alhaji zaika iso, bawan Allah saida safe, abunda ta iya fadi knn tashige daki tadauko mayafinta da Dan qaramin Jakarta ta umarci Nana akan ta tashi sutafi.

Ta gabansu suka wuce bawanda ya iya cewa komai, saidafe kai Alhaji yayi cikin takaici, candai yadago ya kalleshi cikin takaici yace meyasa Baka nemeni ba dakuka shigo garin?

Cikin tsoro yafara bashi haquri, tashi kabani guri kawai yafada, shiko dasauri yatashi yafita, shikanshi yaji takaicin rashin kiran nashin da baiyi ba, domin yanada tabbacin Nana itace irin kalan matan da Ubangidansa yakeso, yasan da yau xaisamu babban kaso, tsaki yabuga yashiga mota direbanshi yajashi suka tafi.


Tafiya sukeyi babu mai magana acikin motar, ahaka bar suka isa gidan, wani dani ta nuna mata tareda ce mata kije kiyi sallah kiyi wanka kifito kijirani a falon nan Ina son magana dake, haka kawai tafada tai shigewarta dakinta.

Sumu sumu Nana tashige dakin da tanuna matan.

&&&&&&&&

Lami ce Zaune a tsakar gida tana karkada qafafunta taci kwalliyarta, Matar Baffan Sadiya CE taxo giftawa ta gefenta amma saboda wulaqanci irinna Lami miyau ta tsitta mata aiko sai ajikin hannunta, bata kulata ba tanufi bandaki.


Itakuwa ba hakaan tasoba domin ason samu ta kulata suyi tunda mijin nata bayanan, tana xaune agurin ganin shigowarshi yasata saurin miqewa........😜



😍😍🤝🏼Anatare
Mummyn Fadyl CE




🎲🎲TUDUN DAFAWA🎲🎲

Rubutawa...... MUMMYN FADYL
(Fatyma Muhammad Adamu)


Wattpad @ *fatimamuhammadadamu*


INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION*
*[onward together]*
*{we give the reader's of ours the best out of the bests,, our inks are melodious and dropping a kinda lights to reader's}*
```THE PEN OF LOVE😘 HEAT TORCHING❤ TEAR OF SORROWS😭 CURDLES😊 GIGGLES😁 AND MARRIEGE THINK💑```
*```JUST GIVE US FOLLOW..**


Fitowa ta. 4⃣2⃣



Tana ganin shigowarshi tamiqe ta isa gareshi cikin sigar ganin mutunci ta tarbeshi tareda miqa hannu ta karbi ledan hannunsa tsabar makirci dakin matansa ta nufa da ledan.

Lokacin itakuma tana xaune a daki don yanxu batacika xaman tsakar gidan ba, tafi gane tai zamanta a dakinta don idan zaman zatayi Lami tayita jifanta da baqaqen maganganu knn, tasan aje aje watarana xuciyarta xata tunxurata tasata amsawa, a qarshe kuma laipinta xa'a gani, amma ace kai da gidanka xaman tsakar gida ya gagareka?


Dakin tashigo da sallama, bata shiga kai tsaye ba, sai,a tajira an amsa sallamar snn tabude labulen, tana shiga tabude ledan saida taga abubuwanda suke ciki snn tace, naga komai saura amin makirci. Daga haka taiyo waje abunta.


Tana fitowa dakin shima ya shiga, ganin matarshi a xaune babu kuxari atare da ita, yasashi saurin qarasawa gurinta, kafadarta ya dafa yatambayeta menene matsalarta gaba daya yaga a 'yan kwanakin nan tasauya, baya ganin walwalarta ko Kadan, gashi kullum idan yadawo a daki yake cimmata baya samumta tsakar gida, yadai disa ayar tambaya akan LAMI.


Shikanshi xaman Lami a gidan ya matuqar tsaya mishi a wuya, don dai babu yanda ya iya ne, amma yana bakin qoqarinsa ganin yasama mata matsuguni koda na haya ne.

Amsa mishi kawai tayi da sannu da dawowa ya kasuwa? Alhmdllh kawai ya iya cemata, snn yace natambayeki baki bani amsa ba, babu komai karka damu tafadi hakan tarefa qaqalo murmushin yaqe.


Bayan yayi wanka yadawo daga sallah dayake yanayin Zafi ne, tabarma ta shimfida mishi a qofar dakin yafito ya xauna domin cin abinci, Lami kuwa dama tagama dasa iyakan abunda takeson yi a wnn ranar don haka butt taiyo waje.


Ah ah ah Baffa abinci kakeci ne tafadi tana yanshare baki, eh Abinci xanci yabata amsa batareda ya dago ya kalleta ba, shidai rashin kunyar Lami tana bashi takaici, ba shakka yayanshi yayi matuqar qoqari don kuwa ya quntata.

Batako kalleshi ba balle tasan yanayin da yake ciki, Baffan Isah don Allah idan kagama cin abincin akwai maganar da nakeson muyi, to shknn kawai yace mata, saida gaban matarsa yafadi jin abunda Lami din tafada, amma ta dake, tai kamar bata jitaba.


Itakuma maimakon taje tajira daki tajirashi, a'ah saima Neman guru tayi taxauna yanda zama ta fuskanceshi dakyau😜.
_Takaici_

Bayan tagama duk uxurorinta tafito kamar yanda aka umarceta, aiko a falon tasameta a xaune, Barka da hutawa tafada cikin sanyin murya. yauwa barka samu guri kixauna.


Zama tayi a qasa yagefenta cikinta duk yacika da tsoro takasa tantance wani hali take ciki yanxu, bata tsakanin ta da wadannan bayin Allan ba, snn batasan dalilin da yasa Matar nan ta taho da ita nan gidan ba.


Ya sunanki? taji matar takatse mata tunaninta ai a firgice cikin tsoro tace Sunana Nana, Nana meye hadinki da Mijina? Taji wani tambayar kuma.

Bansan shiba nima haka naga ankawoni gurinshi, dakyau me aka kawoki kiyi mishi, a daburce tace wlh bansani ba nima, nibanma San inane nan ba, bansan a wani gari nakeba yanxu taqarashe maganar tareda fashewa da kuka.

Xuciyarta ce keneman karyewa ganin yanda yarinyar take kuka bilhaqqi, amma ta daure domin hakanne kadai xaisa ta tabbatar da xarginta gaxkiya ne kokuma akasanin hakanne.


Bakuka na saki kiymin ba, shi Wanda yakawokin meye alaqarki dashi, Kodak kune irin yarannan da ake kawalci daku, ai wnn karon a raxane tadago tana girgixa kanta domin baxata iya magana yanda kuka yaci qarfinta.

Dakyar tasamu tabudi bakinta tace wlh shidinma bansanshiba banida alaqa dashi kaini gurinshi akayi, saida nayi sati biyu a gurinshi snn yakawoni nan gurin.


Sati biyu tafada tareda zaro idanu waje gamida dafe qirjinta, nashiga uku ni Maryam tsawon satikan nan mekukeyi?


Babu abunda mukeyi domin ya tabbatar wa Ummana cewa Nana cikin tsarin matar da yake harka dasu, kitaimakamin kidubi girman Allah kixama sanadiyyar kubutata daga hannunsu, wlh banida kowa, tafashe da kuka mecin xuciya.


Ummanki? Kinason kicemin mahaifiyarki ce takawoki gurinshi? A'a ba mahaifiyata bane, matar Baba nane, nikam mahaifiyata ta bata bansan inda takeba, tana kaiwa nan axancenta taji kamar an fame mata mikin da yake cikin xuciyarta

Please Login or Register in order to submit comment