You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya kaucemin.


Fuskantarshi tayi dakyau snn tace tunanin da nakeyi Wanda a ganina shine mafita na qarshe shine mukai cikiyar mahaifin Nana tukunna, idan muka sameshi cikin hukuncin Allah abun xaixo mana dasauqi.


Snn batun mahaifiyarta kua addu'a xamu dage dashi snn kuma mu raba qafa gurin Neman taimako, a qarshe kuma maganar aurenku bana tunanin xai samu tangarda domin Allah yaga nufinmu bamuyi domin cin zarafinta kokuma toxarci a gareta ba.


Ina kyautata tsammanin duk lokacinda iyayenta suka bayyana zasuy alfaharin ganinta da hijabin aure sanye a jikinta.


Matuqar shagaltuwa yayi da saurarenta, lallai ne Ubangiji yayi gaxkiya da tace sai Wanda yakeso yake azurtawa da mace tagari, babu abunda xaiyi sai qarin godiya gamida miqa wuya a gurin Allah.

Murmushi kawai yayi mata Wanda itakanta tasan ma"anarshi murmushi ne dayake mata nuni da cewa maganarta takarbu ankuma ji dadinsa Dari bisa Dari , juyowa tayi gurin Nana tace da ita, Nanan mu mekika gani, kinada abun cewa? Domin har abada bana fatan mu tauyeki kokuma yin zalunci a gareki.


Cikin kukanta tace musu duk yanda suka zartar akanta daidai ne, tana kuma qara godemusu bisa halaccin da sukai mata, fatan ta suriqe ta Amana itakuma tayi alqawarin faranta musu, roqonta na qarshe tace musu tana son asata a makaranta domin qarin ilimi.


Sunji dadin maganarta snn sunyi na'am da buqatarta da wnn Alhaji yaja motarsa suka hau kan titi, xuciyarsa cike fal da farinciki.


&&&&&&&&&&&&...

*Bayan wata takwas*


Zarah ce kwance tana baccinta wurin misalin qarfe Tara na rana, juyi tayi tajita jikinta babu dadi, tana jinta wani yame yame, qasanta kamar a jiqe, aiko farkawa tayi tamiqe zumbur mexata gani?


Gani tayi tabata gadon da jini, ai batasan lokacinda ta duro akan gadon tanufi dakin mummynta da gudu ba.


Mummy Mummy mummy kina ina? Nashiga uku mummy zo kigani, mummy ko tana bandaki tana alwalar sallan walha, jin kiran bana kwanciyar hankali bane yasata fitowa a rude.

Ganin zarah tayi ta bata wandon nyt gown dinta da jini, Zarah!!! tafada cikin kallonta, yaya xaki fito a haka idan wani ya ganki pa?


Mummy wlh farkawa nayi pa naganni cikin jini, kuma ni banji ciwo ba kapin inkwanta, kallo daya xakai mata Kasan a razane take taqarsa maganarta cikin kuka.


Mummy ce ta kalleta tace mata Doter ba abun kuka bane girma ne yaxo miki, qara zaro idanu waje tayi tace mummy yanxu shknn na balaga? Shknn yanxu wannan ne jinin Al'ada? Nashiga uku mummy wlh a duk class dinmu babu mai yi sai mutum daya kuma duk ta girmemu pa, tafaashe da kuka.


Mummy ko gani tayi idan pa tabiyewa shirmen Zarah harsai tayi staining inda take tsayen ma, hakan yasata lallashinta ta Shiva bayan gida tanuna mata yanda xata gyara kanta, duk dahaka saida tabata lokaci sosae a bayan gidan, don komai kwalawa Mummyn kira takeyi ta sanar mata abunda tagani, tun mummy na bata amsa har tagaji, tace mata idan kina fadin duk abunda kika gani tobaxai taba daukewa ba, saikinyi sbekara yana xuba miki.


Aiko daga nan aka samu salama tagyara jikinta tsaf, adakin Mummyn nata ta kintsa, snn taxauna kusa da mummy tace, mummy baxan gayawa kowa nafara ba? Eh karki fada.

Mummy amma ai xan iya gayawa Yaya Ibby idan yakira a waya ko? Kull karki gaya mishi ko 'yan ajinku karki sanar dasu, kiy shiru kawai da bakinki kinji ko?

Amma wlh daddy na kam sai nagaya mishi ta xumburo bakinta gaba, bata kulata ba, hankalinta Yakoma kan wayar ta, can kuma taqara cewa.


Amma mummy kekam nasan xaki gayawa Yaya Aliey ai, tunda shikam komai ma gayamishi akeyi na gidannan, a'a shima baxa'a gaya mishi ba, tabata amsa kawai.


Mummy ce tajuyo dasauri tunowa datayi da halin 'yar tata, yauwa dota kisaurareni dakyau, daga yau babu ke babu wasa da Maza koda kuwa wayene shi? Kallonta takeyi amma bata fahimci metake fadi ba, data gane ba fahimtar ta tayi ba yasata nitsuwa ta fuakanceta dakyau tareda yimata bayani takuma Dora da nasiha dakuma gargadi mekyau.


A yanda ta lura batutuwan ta sunyi tasiri a xuciyar Xahra sosai, domin wani sabon nitsuwa ne ta wuni dashi wunin wnn ranar gaba daya, _Niko nace ba girin girin badai ta fidda mai_

Zaune suke a falo suna tattauna tsare tsaren da xa'ayi a bikin duk dama bawani hidima xa'ayi ba, tunda mijin ba yaro bane, utadai Nana saurarenta kawai takeyi bata iyacewa komai don kunya.


Wayar Haj Maryam ce ke ringing hakan yasata nufoshi, ganin 'yar uwarta yasata saurin dagawa cikin farin ciki, 'yar uwa haba don Allah yaushe xaki dawo qasan ne, daga xua follow up shknn ki daskare a wani qasa? Gani da tulin magana data addabi xuciyata narasa dawaye xanyi shearing damuwata.


To uwar magana kiymin haquri nadawo jiya da dare nima inason muhadu wlh, ahhh maraba da dawowa bari inkira Alhaji intambayeshi yanxu xantaho insha Allah.


Ai suna gama wayar tai dialing numabanshi yana dauka suka qara gaisawa snn tasanar dashi uxirinta, ya amince mata sukai bankwana tai hanging call din.


Cikin sauri sauri ta kammala shirinta tafito waje, a falon ta Tarar da Nanan a inda ta barta, sanar mata tayi xataje gidan sister nta, taimata a dawo lpy snn tawuce.


Direba takira yaxo yadauko mota snn tashiga suka wuce gidan, tana Shiga da Humaira tafara cin karo.............



😍😍🤝🏼Anatare
Mummyn Fadyl CE



🎲🎲TUDUN DAFAWA🎲🎲


Rubutawa....MUMMYN FADYL (Fatyma Muhammad Adamu)

Wattpad @ *fatimamuhammadadamu*


INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION*
*[onward together]*
*{we give the reader's of ours the best out of the bests,, our inks are melodious and dropping a kinda lights to reader's}*
```THE PEN OF LOVE😘 HEAT TORCHING❤ TEAR OF SORROWS😭 CURDLES😊 GIGGLES😁 AND MARRIEGE THINK💑```
*```JUST GIVE US FOLLOW..**



Fitowa ta. 4⃣7⃣


Da humaira tafara cin karo cikin shigarta ta fita xuwa islamiya, tana ganinta ta saki murmushi tareda karban jakar hannunta tana gaisheta, amsawa tayi suka nufi cikin gidan, Zarah ce takwala mata kira tareda cewa humairah kiyi sauri munkusa yin latti pa, a tare suka juyo Gaban Maryam ne yafadi, don wani mugun kama dataga yarinyar yau tayi mata da Nana.


Ta ina ma suka hada hidi bandama sharrin xuciya tafadi hakan a ranta, cikin gidan suka nufa sai da humairah ta dangana ta da dakin ummin ta snn tawuce islamiya..


Cikata akayi da abun motsa baki, bayan sunqara gaisawa ne, Haj.Maryam tafara sanar da 'yar uwarta halinda take ciki tun daga ranar da tafara haduwa da Nana har xuwa yanxu saidai ta sirranta rayuwar Nanan, tadai nuna mata cewa marainiya ce.


Tajima tana juya abun a ranta, a qarshe tace gaxkiya Maryam kinyi tunani snn kinyi ceton rai da kuma mutunci.


Saboda da ace kin kori yarinyar nan to pa akwai yiwuwan mijinnaki ya bita su hadu acan wani gurin ya rinjayeta har ya lalata mata rayuwarta, idan kuma basu hadu abai xata iya fadawa cikin wani hali marar kyau, Wanda kinada hakki akai domin kinga alamar kintsuwa a tartare da ida amma kika kasa taimaka mata.


Munadai fatan Allah ubangiji yasa hakan da kikayi Allah yadubeki yaxamo sanadiyyar shiryuwar mijinki domin a bayanin da kikamin na gameda zumudin da yakeyi akanta ba qaramin so yake mata ba.


Maganar kishi kuma Dole nepa saikin danne xuciyarki, da zafi kam, ace kinfaro rayuwarki da mijinki tun bakusan rayuwar auren ba daga ke har shi Ku biyun Ku, amma rana tsaka kiga kinfara rayuwa da wata dukanku a qarqashin ni'imarsa, shawara ta gareki shine kiriqe addu'a, cikin riqo da addininki dakuma gaxkiya komai xaixo miki dasauqi, karki cutar da ita, domin a rayuwa da ace kai ka cuta gara acuceka, idan ita ta cutar dake ubangiji xai dubi taimakon da kikai mata da kyakykyawar niyyar ki akanta yabi miki hakkinki.


Amma idan ke ce kika cutar da ita, to ina tabbatar miki duk abunnan dakikayi yatashi a banxa, don kua kin sako ha'inci a cikin zaman naku,ubangiji kua baya xalunci bai bimata itama.


Haka taita mata nasihu masu ratda jiki, saida ta tabbatar tagama yin sanyi snn tafara janta da Hiran wasa, tace mata kuma wlh saura ranar first nyt dinsu ki kasa bacci, dariya tayi sosae harda riqe cikin ta snn tace mata.


Haba dai Allah ya sauwaqe saikace wata qaramar yarinya, ke wlh a xancen kishi babu yaro babu babba kawai haquri ke determining mutum, kedai kidaure kawai karki cika Baki domin sassafen washegarin tariyar xan shigo gidanki induba halin da kika kwana.


To Allah yakaimu Da Amin ta amasa ta, hiransu sukai tayi daga baya sukai bankwana da juna akan sai sun shigo a bikin kawai.



_Bayan wata biyu_


Cikin hikima da ixxar ubangiji andaura auren Nana da Alhaji Abbakar akan sadaki naira dubu Dari biyu, aurenda da yatara manyan mutane qusoshin gwamnati dakuma shahararrun 'yan kasuwa kowa yayi matuqar mamakin yanda yadago xancen aure lokaci guda Wanda a da can kowa yasanshi ba mutum bane me sha'awan ajiye mata biyu.

A gurin daurin aure kuwa Mal.Habu ne ya kalli Dan uwansa yace dashi kaji ikon Allah sunan Amaryan daya da 'yata, yafadi hakan cikin karyewar murya, dafashi yayi yacigaba da bashi baki har yasamu yadan sake.



Acikin gida kuwa 'yan uwan Hajiya Maryam sunyiwa NANA kara Nana Kadan ba, domin kuwa sun nuna mata gata sosai sun maye mata gurbin 'yan uwanta. _Abu daya ne basuy mata ba, domin kuwa basu shiryata yanda yadace ba I mean babu kayan harka lolx_😜 itakam batama San anayi ba, tunda batasan wace rayuwar xata Shiga ba.



Mummy ce taiyowa Ummy rakiya Inda aka barta a dakin Amarya tana yimata kwalliya, kwalliyar take mata amma hankalinta yanakan yanda take hango kamannin dayake tsakinta da zarah nta.


Humairah kirakani gurin mummy nidai wlh ban cikason taron mutane dayawa ba, shiyasa pa kikaga yanxu bancika xua gidanku ba, domin kullum gidanku cike yake a mutane.


Kedai kika sani, mutum ai rahama ne, naji muje dai kirakani, ahakan sukaita gota cicirindon mutane har suka shiga side din Amaryan.


Mummy abunda tafara fadi ne, sauran maganar da ke bakinnata ne yamaqale sakamakon toxali datayi da fuskar Nana, faduwar gaba taji wani Rass batareda tasan dalilin saba,.

Menene dota? Kasa qarasa maganar tayi sai matsowa kusa da Mummyn datayi, daidai lokacin da itama Nanan ta dago ido domin kallob wacce aka kira da dota donkuwa muryanta babu maraba Dana Mamanta.


Itakuwa Zarah shagaltuwa tayi da kallon Nana don kuwa tayi matuqar yimata kyau tareda shiga ranta lokaci qanqani, Nana ce tadaga musu gaisuwa badon komai ba saidon tanason qarajin muryan zaran.


Humairah ce kadai ta amsa domin zarah kam kafeta tayi da idanu kawai, mummy ce tace dota baxaki amsa bane? Shagwabe fuska kawai tayi batareda ta amsa ba, sunjima a hakan, har Nana ta fidda ran zarah data qara yin magan acikin dakin, a qarshe zarah tace Mummy har shi yaushe xamu tafi gida?


Dota anjima kadan xamu tafi, harkin gama kallon Amaryan? Duk xumudinki akan amarya anan xai tsaya? Murmushi kawai tayi tace mummy inason xanyi waya da Yaya Ibby ne, yacemin xaki kirani after magrib.


To muje muy sallama da mutanen gidan mutafi, haka suka fita, xarah kasa haquri tayi saida ta waiwayo suka hada idanu da juna aiko suka sakarma junasu murmushi kapin sukai waje.



Nana ce takwanta akan bayanta tana tunanin muryan da taji na Xarah, a take taji tunanin mahaifiyarta yadawo sabo a ranta, dakuma tunanin yanda auren ta yaxo mata, kuma be me qarfi ya kufce mata, Wanda yasa tama manta da wata kwalliya da akai mata, yitayi me isarta batai shiru ba, saida taji kanta yafara amsawa, _Niko nace ki Adana kukanki xakiy me dalili_


😍😍🤝🏼 Anatare
Mummyn Fadyl CE



🎲🎲TUDUN DAFAWA🎲🎲


Rubutawa....MUMMYN FADYL (Fatyma Muhammad Adamu)

Wattpad @ *fatimamuhammadadamu*


INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION*
*[onward together]*
*{we give the reader's of ours the best out of the bests,, our inks are melodious and dropping a kinda lights to reader's}*
```THE PEN OF LOVE😘 HEAT TORCHING❤ TEAR OF SORROWS😭 CURDLES😊 GIGGLES😁 AND MARRIEGE THINK💑```
*```JUST GIVE US FOLLOW..**



Fitowa ta. 4⃣8⃣



Haka akaita hidima babu kama hannun yaro, Haj.Maryam yawanci al'umma sai binta da idanu kawai sukeyi inda wasu ko suke ganin wautar ta, domin acewar su basuga abun barin miki akan lamarin kishiya ba, wasu daga cikin qawayenta tun da sukaji labarin biki suke kawomata gurbatattun shawarwari amma haka kowa ke tafiya da kayanta domin maganganun nasu basu samu muhalli agunta ba.

_yakamata a jinjina mata_


Zame jikinta tayi a cikin jama'a dakyar saboda yanda gidan yacika maqil babu masaka tsinke, dakin Nana tanufa kai tsaye, komai na dakin daya tasa suka saya da nata banbancin su kawai kala, nata komai peach ne sabanin na Nana komai purple ne.


A qasa tasameta atsugene, kanta a kan gado tanata dirzan kuka, cikin sassarfa Haj.Maryam tanufeta, dagota tayi gani tai fuskannan tayi jazur tsabar kuka gashi tayi caba~caba, domin tagama bata fuskar da powder.


Zamatayu ta Dora kanta akan cinyarta snn tafara tambayarta meke damunta kodai wani abun akai mata? Da kanta tabata amsa domin baxata iya magana ba.


Dakyar tasanar da ita abunda yake damunta, haquri tashiga bata dakuma bata baki hartasamu ta tsagaita kukan, sata tayi tashiga bathroom da wanko fuskanta ta gyarashi snn tace mata bari takoma mutane sunata jiranta amma xata aiko mata dawata sister nta taxi suxauna tare, ai batasan ita kadaice a dakin ba, don batasan tafiyar Mummyn zarah ba.


Ummyn IBBY Ashe Mummyn zarah ta tafi bansaniba tabarmin 'ya sai kuka takeyi ita Kadai a daki? Ummy ce tace wlh kua zarah ce ta takura mata akan saisun tafi gida, wash daga cikin qawayenta ne adakin tai tsaki domin ita abunna Maryam yamxu yafara bata takaici, batabi takansu ba, taci gaba da harkokinsu.


Horn akeyi babu qaqqautawa dagaji kasan meshi a matse yake mal.Habu da Dan uwanshi ne a zaune, cikin hanzari mal habu yamiqe yabude gate din, Jada baya yayi domin kamar me motar zai bangajeshi, tinted glass ne hiyasa Sam baiga nacikij motar ba, komaws yayi yana mamakin nacikin rufe gate din yayi yadauki but a yashiga bayi.


Ko parking maishi baiyi dakyau ba, _nikaina zura idanu nayi domin ganin me fitowa daga cikin motar, aiko waxan yi tozali dashi macece nagani kuma bakowa bace face AYASHE_ lallai tabbas kudi na gyara Dan Adam, cikin shigarta ta alfarma, fuskarnan tasha kwailin an kwaile ta, tayi radau da ita.


Swiss lace ne ajikinta kalar sky blue, anmata dinkin Riga da zani, kyau kanfa tayi kyau akin qarshe barikinta yaqara fitowa dodar ajikinta, itada wata 'yar akinta ne take riqe mata da wata 'yar qaramar troley dinta, kaitsaye sukai tambaya aka kaisu sashen uwar gida.


A kitchen akaiyo kiran Haj.Maryam domin tanacan tana bada odan irin girge girgen datake shiryawa mijinta domin yasanar mata yananan shigowa gidan by 4pm.


Kai niyau yaxanyi da mutane🤦🏽‍♀ ina xua tabada amsa, saida taqarasa bada umarnin aikin snn tafita tayi dakinnata, ganin masu Neman Nata tai baqin fuska ne batasansu ba, amma hakan baihanata fadada fuskanta ta qawatashi da murmushi ba. Taqaraso garesu aka gaisa a mutunce.


Nan Ayashe tasa 'yar dakin nata tabude qaramin jakar nasu, nan sukaga wasu tulin ledoji ne a qulle kala kala, Ayashe tasauqo qasa tahau warwarewa tana fadin sunayensu dakuma amfaninsu, dagalo sukai da bakinsu suna kallonta yanda taketa bayani kallo daya xakai mata basai kaqara ba, xaka fahimci batada ruwa a idonta, a taqaice dai batada kunya.


Saida tagama bayananta gaba daya Haj Maryam tayi murmushi tace da ita, nagode da karamcin da kika nuna tunda kika taso gari ya gari kikazo domin taimakona kamar yanda kika fada, amma kiyi haquri nibana irin wannan harkan Nana cikin irinsu, daga fadin hakan taja bakinta ta tsuke.


Kowa agurin yayi yo mata caaaa kamar xasu cinyeta, itakua ko ajikinta tananan akan bakanta domin akan kishiya baxatai abunda bata saba yiba, abunda batasan ya qarshen shi xaixo mata ba.


Aiko nan mutane suka matso gareta sukaita kwasa ana cika mata jaka da kudade, saida ta kammala kwashe kudadensu tai haramar tafiya, itakam Haj.Maryam batama dakin domin tajima da fita.


Ayashe tana fita taqara Neman akaota side din Amarya, shiga sukayi suka zauna a falo, sunjima sunajiran fitowan Amaryan, amma shiru, a qarshe gajiya sukai dazaman, watace tafito tabasu haquri akan cewa baxasu samu ganin Amarya ba, domin yanxu haka tana sallah baya. ta idar kua xa'a shiryata ne domin miqata gurin dangin mijinta, Ayashe ce tafara miqewa cikin takaici , a ranta tace saikace wata 'year gwal? Mtswww bahaka tasoba sukai tafiyarsu.


Bayan angama shiryata ne Haj.Maryam ma tafito da ita suka jera har can side dinda aka sauke 'yan uwan Alhaji, sun yaba sosae da dabi'un Nana Wanda wasu daga cikin su kyanta kedaukan idanunsu.

Sunyimusu nasiha gabadayansu tareda yabawa gwaxon dakuma jarumtar Haj.Maryam, aqarshe tariqo hannun Nana suka dawo.


Misalin qarfe Tara na dare jama'an gidan bikin suka watse bakajin qaran komai banda qira'an Ahmad Sulaiman na suratul baqarah Wanda Haj maryam ce akunnashi ganin qafa yadauke.


Shigowa yayi da leda guda biyu a hannunsa saida ya tako tsakiyan falon, snn yafara tunanin meya kamata yafarayi jin qara kamar xa'a bude dakin yara ne yasadhi saurin shigewa dakinsa haryana tuntube, baxai iya hada idanu da yaranshi ba, duk dama baida jaa akan tarbiyarsu, dakuma ilimin da uwarsu ta dorasu akai, yanada tabbacin baxai samu matsala irin Wanda ake samu a wasu gidajen ba.



Zama yayi yadafe kansa, yau rana daya amma ya tsinci kansa cikin matsanancin kunyar matarshi, baisan dawani ido xai kalleta ba, yashafe kusan rabin Awa a zaune yana tubka da warwara, qarshe dai yayi tamaza yamiqe yanufi dakinta.


A kan darduma yasameta, isa gareta yayi, itakuma ganinsa yasata tsagaitawa da karatunta bayan takai Ayah, gaisheshi tayi cikin girmamawa, tareda tambayarsa ya fama da jama'a? Aike xan tambaya, ya fama da mutane? To Alhmdllh.


Yakasa furta komai itama agareta hakan abun yake, qarshe dao itacce tafara cewa Yaya kuma kaxo gurina kaida xakaje dakin Nana? Tafadi hakan tanajin wani Abu yatsaya mata a maqoshinta, in ina yafarayi Wanda kanaji kasan yarasa mai xai fada ne.


Fahimtar hakan datayi a tattare dashi yasata miqewa tsaye takama hannunsa, shiko binta yacigaba dayi kamar qaramin yaro, saida takaici qofar dakinnata snn takoma bayanshi shikuma yaxama yana gabanta.


Magana tafarayi tace nasan xakace kanason kahadamu guri dayane, Nayi maka Alqawari mijina baxaka samu matsala daniba matuqar inacikin hayyacina, xanyi qoqarin gurin ganin daidaituwar gidanka, kaidai ka kasance me adalci tsakaninmu, ina roqon Alalh yasa wnn auren shixai kawo silan kawo farinciki madauwamiya a gidanmu Amin, inai maka fatan Alheri, Rama kaiwa nan a zancen ta tai saurin rufe qofan dakinnata tareda sa mishi key.


Yajima tsaye yama rasa mexaiyi guda daya domin Maryam tagama daureshi da jijiyoyin jikinsa, a qarshe kama hanya yai sai dakin gimbiya Nana.


A zaune yasameta itama akan darduma tana karatun qur'ani, gabanta yaje yaxauna ya tsura mata idanu har muryanta yafara sarqewa domin ganin dirkeken namiji a kusa da ita dab da dab.


Kaiwa qarshen aya tayi an tagaisheshi cikin rawan murya, amsawa yayi cikin sakewar fuska, miqewa yayi yashiga bathroom yadauro alwala ya umarceta tamiqe suy sallah.


Jansu yayi sallah bayan sun idar nikaina nayi mamakin yanda Alhaji yaketa kwararo addu'oi banyi tsammanin yayi sani haka ba, bayan sun kammala yajuyo yafara yimata tambayoyi gameda addininta tabashi amsa yanda yadace cikin taimakon sabon malamin Islamiyar da aka samo mata.


Yaji dadin yanda tabashi amsoshi, hannu yasa a saman kanta yayi mata addu'oi kamar yanda musulinci ya tanadar.


_Tsoho dashi kun zuzzura idanu kunason jin abunda xai aikata ko? Hahahahhahahhahah wlh baruwana kujira na yara, kedai Nana fatan Alheri_

😜😜



😍😍🤝🏼Anatare
Mummyn Fadyl CE




🎲🎲TUDUN DAFAWA🎲🎲


Rubutawa....MUMMYN FADYL (Fatyma Muhammad Adamu)

Wattpad @ *fatimamuhammadadamu*


INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION*
*[onward together]*
*{we give the reader's of ours the best out of the bests,, our inks are melodious and dropping a kinda lights to reader's}*
```THE PEN OF LOVE😘 HEAT TORCHING❤ TEAR OF SORROWS😭 CURDLES😊 GIGGLES😁 AND MARRIEGE THINK💑```
*```JUST GIVE US FOLLOW..**


*Yau dai ayimin uxiri idan anhadu da typin errors don bada wayata nai ba, kuma wayar danai amfani da Itan tana buqatar ganin likita, itakadai tana sending emoji's hahahahha*



Fitowa ta. 4⃣9⃣



Dawowarshi daga sallan asuba dakin Nana yawuce direct don yasan xata buqaceshi a irin wnn lokacin, amma ga mamakin sa samunta yayi da alama harta kintsa jikinta don kuwa gyaran gado ya Tarar da ita tanayi.


Ganin shigowanshi yasata jin kamar qasa ta tsage tashige ciki haka atakejin ta, shikua harde hannayenshi a qirjinshi yayi yanabinta dawani mayataccen kallo, baxaice ga iyakan yanda yakejin Nana a ranshi ba, domin qaunarta yagama mamaye mishi kowani kusurwa na jikinshi, yanda yaji Nana gaxkiya baxai misaltu ba, xai dai iya cewa Itan ta dabance.


A kunyace kanta kuma a qasa ta qaraso gabanshi durqusawa tayi akan guiwowinta snn tafara gaisheshi, tayi hakanne badon batajin zafin jikinta ba, a'ah idan gaxkiya xata fadi takuma nunashi a aikace to ko yatsan hannunta saiya zame mata aiki gurin dagashi tayi amfani dashi, amma tana tuna hudubar mahaifiyarta, a duk lokacinda tace mata tagaji da aiki kaza, to takance mata Nuna jarumta a aikin lada yana qarawa mutum kima


_Bance karki langabe wa miji ba, no akwai inda yakamata kibaxa baiwarki ta shagwaba son ranki, akwai kuma inda idan kika nuna jarumtan koda kadanne kima xaki qara a idanunsa._


Maimakon ya amsata said dagota yayi yamannata a qirjinsa, tareda Dora kanshi akan nata, yana shaqan qamshin kalolin mayukan gyaran gashin da kanta yasha.


Zama yayi a bakin gado itakuma yadaura ta akan cinyarsa, snn ya amsa gausuwarta tareda tambayarta ya jikin, kasa cemishi komai tayi domin batada amsar da xata bashin.


Nana inason insanar dake wani abu, wanda nasan kinsanshi bakomai bane illa muhimmancin matana Maryam............yajima yana bata labarin wasu daga cikin fadi tashinda Maryam din tayi akansa tun farkon aurensu, har xua ranar da Nanan tashigo rayuwarsu.


Tayi jimami sosai takuma jinjinawa Maryam din sosai da sosai, abunda nakeso dake shine kibita baxata taba ha'intar ki kokuma ta cutar dakeba, kisaki jikinki da ita, ina tabbatar miki xaki ji dadin rayuwa da ita insha Allah.


Cikin sanyin murya tace insha Allahu baxaka samu matsala daga gurina ba nidinma, murmushi yayi mata, snn yafara tsokanarta duk da takasa sakin jiki dashi yanda yakeso.


Alhaji mutum ne shima mai barkwanci, nan yazage yayi ta bata labarai na ban dariya, itakua jinta akan cinyar nasa ne yahanata sakewa gakuma tsoro.


Amma cikin dabara yai ta janta hira a qarshe naga yagaya mata wani magana akunnenta gani nayi ta sake da dariya me sauti kadan takuma boye kanta a qirjinshi.
_kunsan tsofi da iya luv_😜


Itakua Haj.Maryam tunda ta idar da sallah tai karatun qur'ani kamar dai yanda tasaba, muqewa tayi tashiga kitchen ta hada musu breakfast me rai da lpy. Chips ta soya snn tasoya wainar kwai takuma Dama musu kunun gyada, saman kunun kadai Idan ka kalla xaisaka jin sha'awar shanshi koda kua bakada niyyar hakan, maiqo ne kwance bisan kunun gashi fari tass.


Jereshi tayi a dinning duk abunnan datakeyi tasbihi taketa nanatawa a cikin xyciyarta, domin batason shaidan yayi galaba akanta gurin sauya mata tunaninta.


Yayi daidai da lokacin farkawan Nana daga baccin da suka koma itada Alhajinta, itace tafara farkawa jinta a maqale dashi yasa tama rasa yanda xata cirekanta daga jikinshi gashi gari yayi haske, tanason miqewa ta sake wanka taje kitchen domin batason haj. Tarigata xua kitchen din.


Shikua tun farkawanta na farko ma idonshi biyu yanason yaga yaxatayi ne, ganin sai yamutsa fuskanta takeyi yasashi qara rungumota yace mata banason raba jikina da nakine, domin nikadai nasan dadin hakan, hummm kawai ta iya cewa snn can kuma tace inason inje nai mana abincin kari ne banson tafito tasamu ba ai komai ba baxataji dadi ba.


Saida yazaro idanunsa shima don wlh dayajishi a jikinta komai nashi sukurkucewa yayi, yama manta akwai wacce baison tabawa xuciya, aiko nan yasaketa itako kamar jira takeyi tashige bayi.


Shima saukowa yayi, yafito daga dakin kayan baccinsa ne ajikinsa yama manta baisa jallabiya ba, fitowarshi yayi dai dai da itakuma xata shiga kitchen shiyafara hangota aiko kamar walqaiya yashige dakinsa harda maida ajiyan zuciya kamar Wanda yayi sata.


_ki kasance mai kawaici xa'aji tsoron quntata miki koyaya abun yake_

Nana bata tsaya cewar xatai kwalliya ba, tunda damacan ba gwanar yin kwalliyar bane, haj.maryam cema ke satayin kwalliyar don itakam bai dameta ba, doguwar Riga ta zura tasanyo hijab dinta tafito, a kitchen tasameta tana maida kayan datai amfani dasu mazauninsu, dasauri ta qarasa gareta tsugunawa tayi zata gaisar da ita, tai saurin dagota tayi tareda cewa Maraba da Nanata, kintashi lpy? Lpy qalau, meyasa bakiy kwalliya ba? Kinason mijinmu yaje yana kallon na 'yanmatan zamani a waje ne? Murmushi kawai taimata batareda ta iya cewa komai ba don kunya, to muje falo abincinmu nacan nagama shirya mana.


Yana Shiga ya fada bayi ya watsa ruwa cikin sauri ya kintsa jikinsa snn yafito a zaune a dinning din yasamesu gwanin sha'awa dasu, Gaisheshi haj.maryam tayi cikin fadada fuskarta

Please Login or Register in order to submit comment