You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

jifa Alhajin yakanyi waya da abokanan harkansa inda shikuma direban yamaida hankalinsa gurin tuqi kadai.

Gab da shiga garin Kaduna ne Zainabu ta farka kalle kalle tafarayi tako ina bata ganin kanta tayi acikin mota nanfa fa firgita tahau buge bugen glass tanason fita hakanne ya farkar dasu halinda take ciki gani sukai harda fasa glass din hannun ta kuwa sai jini yakeyi, nan direban yatsaida motar a gefen hanya, sukai saurin fitowa bude motar keda wuya tafito ta ruga aguje kapin suyi yunqurin kamota harta yi kan titi a guje, inda atake wata mota qirar _RANGE ROVER_ tai kanta.....

Ganin haka yasa Alhaji gaggawan cewa direbansa kai yisauri kashiga mota mubar nan gurin aiko nan suka figi motarsu suka bar gurin a gaje kamar xasu tashi sama.

Cikin Sauri naga wani mutum mai cikar kamala yafiyo cikin tashin Hankali yanufo gareta, mutanene suka fara cicirindo a gurin a take yace sutaimaka masa asata acikin mota, baisha wahala ba atake isarsu asibitin aka karbeta saninshi da akayi babban mutum mai muqami..

Likitocin sun duqufa akanta sunsamu ta farfado amma sunyi bincike akanta sungano cewa mahaukaciya CE, don basuy duba da yanayin jikinta. Ba, saboda mutane da Dama masu hankali suka tsinci Kansu cikin hali na datti da musgunawar rayuwa fiye da nata dalilin hakanne yasa saida suka binciketa sosai da sosai.

Likitanne yayi kiran Alhajin xuwa _office_ dinsa bayan sun xaunane yake sanar dashi cewar kawai buguwa tayi amma yanxu Alhmdllh komai yaxo cikin sauqi saidai fa mahaukaciya ce, Mahaukaciya kuma yatambaya, gyada mishi kai yayi alaman tabbatarwa.

Amma _doctor_ kanada tabbacin ba'a hatsarinnan tasamu matsalan nan ba, eh gaxkiya a iya bincikena tajima da haukannan snn abunda nakeson sanar maka shine dalilin hatsarinda tayi abunda yake cikinta idan ba'a luraba xai iya samun matsala.

Ciki kuma? yaqara mishi tambaya a karo na biyu, tareda nanata Kalmar innalillahi wa inna ilaihirraju'uj a xuciyarsa yana girmama wnn al'amarin ace mahaukaciya ma bata tsiraba, nanma likitan ya tabbatar mishi da abunda yafadi.

Shknn karubuta magungunan daya dace da irim masu lalurarta insha Allah xan taimaketa, haka likiyan yagama duk wani abunda ya dace snn ya sallamesu, dakyar da taimakon alluran baccinda akai mata yasamu aka samishi ita cikin mota yai gidansa da ita......

Wanene wnn mutumin?

Alhaji Abdullahi Maitama Dan Asalin garin Kaduna ne cikin garin Zaria amma yana zama a cikin kadunan, mutum ne me karamci idan akadawo fannin arziki kuwa daganinshi kasan baya kukan Naira, saidai kace Nairan CE xatai kuka saboda tasan indai tadhigo hannun to fa saita kasu.

Dalilin dawowarshi Kaduna yasamu asaline ta sanadiyyar Abokinshi, Amininshi kuma Dan uwansa, Alhaji Mukhtar Sabo.

Alhaji Mukhtar sabo unguwarsu daya da Alhaji Abdullahi Maitama iyayensu maqota ne, tun suka yara suka taso da abotansu , babu abunda ke rabasu sai gurin xuwa makaranta, don iyayen Abdullahi basuda halo sabanin iyayen Mukhtar.

Amma a qarshe saida mukhtar yasa baban shi yadauki nauyin karatun Abdullahin har suka gama matakin sakandiri, duk da matar shi wato maman mukhtar bataso hakam ba amma bayanda ta iya don tana tsoron mijinta.

Bayan sun gama sakandiri ne Allah yayiwa mahaifin mukhtar rasuwa, dalilin hakan yasa karatun Abdullahi yatsaya don babu yanda iyayenshi xasuyi ya cigaba, mukhtar kuwa yayi yayi da mamnshi tayarda sucigaba tare tunda akwai kudin amma qirmisisi taqi, haka ta turashi karatu qasar waje.

Haka sunaji suka gani suka rabu, randa xasuyi bankwana da juna ne Mukhtar yame tabbatar wa Abdullahi cewa insha Allahu abotarsu baxata yankeba yakuma yimishi alqawarin indai yadawo xaitaimaka mishi.

Haka rayuwar tacigaba inda Abdullahi yacigaba da xuwa kasuwa shagon dinki yana Neman kudinsa acan yana tallafawa iyayenshi shikuma mukhtar yanacan qasar waje yana karantar _law_.

Bayan shekaru bakwai Mukhtar yadawo da takardar kammala karatunshi inda yazamo cikakken _barrister_ baqaramin murna sukayiba na ganin junansu tun mahaifiyar mukhtar tanaqi harta gaji ta xuba musu idanu.

Abotansu bata tsaya anan ba har aure ma tare sukayi inda mukhtar ne yagina musu gidan da suke xaune da matayensu, snn a wnn lokacin mukhtar ya ware kudade masu yawa yabawa Abdullahi shikuma yaha jarin kansa.

Mukhtar yana xaune da matarsa me suna khadija, dansu daya aduniya *Aliyu* wanda yanxu shekararsa ashirin a duniya tundaga Kansa basu qara samun haihuwa ba hakan yasa son duniya suka Dora akansa.

Shikuma Abdyllahi Matarsa sunanta Hajara yaransu uku, babban shine sa'an Aliyu Wanda wata daya ne tsakaninsu wato Ibrahim, sai khadija takwaran maman Aliyu, sai qaramarsu habiba, yanxu haka tanada ciki.
Matannasu ma aminta ce sosae tsakininsu da mutunta juna....

Masubin novel dina da gaxke ne xasu iya tuna *KHADIJA DA DANTA ALIYU*....

_don't 4get to_
_vote_
_share_
_comment_
_likes_


😍😍🤝🏼Anatare
Mummyn Fadyl CE




.🎲🎲TUDUN DAFAWA🎲🎲


Rubutawa....MUMMYN FADYL (Fatyma Muhammad Adamu)

Wattpad @ *fatimamuhammadadamu*


INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION*
*[onward together]*
*{we give the reader's of ours the best out of the bests,, our inks are melodious and dropping a kinda lights to reader's}*
```THE PEN OF LOVE😘 HEAT TORCHING❤ TEAR OF SORROWS😭 CURDLES😊 GIGGLES😁 AND MARRIEGE THINK💑```
*```JUST GIVE US FOLLOW..**


Fitowa ta.2⃣6⃣


A halinda ake ciki yanxu Aliyu Wanda yaran suka laqaba mishi suna Yaya Aliy da ibrahim Wanda shima sukece mishi Yaya IBBY sungama karatun su na _secondary_ a _Turkish_ yanxu kuma suna karatu a jami'ar qasar _Uganda_ ajinsu biyu inda Aliy yake karantar likitanci a fannin mata wato _gynecology_ haka IBBY shima likitancin yakeyi amma fannin yara wato _pediatric_.


*Aliy* kyakykyawa ne Wanda karon farkon haduwarka dashi xaka fahimci hakan, yakasance me cikar halitta irinta maza, ba fari bane can snn baxamu kirashi baqi kai tsaye ba, xadai mu iya kiran shi da _chocolate colour_ fuskarsa tanada tsayi dai dan gwargwado, yanada saje kwantance a fuskarsa baqi sidik datake haska fuskarsa, yanada dogon hanci, hummm mai karatu nabarka ka qarasa siffantashi amma inason ka ajiyeshi a sahun kyawawa kawai.


Misskili ne sosae da sosae, indai kaganshi yana wasa da dariya to yana cikin ahalinsa ne,bashida jijji dakai shidai maganace bata dameshi ba, shiyasa mutane da dama suke tsoron fuskantarsa don atunanisu daganinsa xaiyi wulaqanci, halinsa yanada wuyar fahimta, amma muddin ka fagimceshi kuma ka xauna tare dashi yanada sauqin mu'amala.


Sabanin Ibby Wanda shi mutum ne wara~wara faram faram da jama"a gwani a fagen barkwanci don xaiyi matuqar wuya kaxauna da IBBY na mintuna qalilan batare da kayi dariya kamar cikinka zai qulle ba, snn shima yanada kyau daidai halittarsa...

*WNN KNN*

Yana isowa maigadi ya wangale mishi _gate_ na matuqar tsorata da tsarin gidan nasu wannan shine aljannar duniya nafadi hakan a raina, _parking space_ yanufa don yau shikadai yafita juyowa yayi ya kalleta haryanxu baccinta takeyi, don haka yafito a hankali don karya tasheta yanufi cikin gidan.


A falo ya isketa zaune habiba tana kwance a kan qafafunta suna hira da khadija tana bata labarin Kayanda mummy (Mmn Aliy knn, mamansu kuma Ummi) xata saya mata idan tadawo daga umrah kai kedai khadija bakya rabuwa da yawan magana, abunda ke hadani da ke....bata qarasa maganar nata ba sallamar Abbu ya katseta Amsa sallamar sukayi nan yaran sukahau yimishi barka da dawowa shikuma cikin sakewar fuska yayi musu Barka da gida.


Sama yanufa kai tsaye a take Ummy tarufa mishi baya suka nufi saman a tare suna hira jefi jefi.


Suna isa dakinshi yakamo hannun ta bayan yaxauna a kan Sofa hankalinta ta tattaro gaba daya tamiqa xuwa gareshi ganin hakanne yasa shi fara magana, Ummynsu da baquwa nake tafe fa, baquwa kuma? amma kai kadai naga kashigo ai, bani kadai bane yabata amsa...


Nan yagaya mata duk abunda yake faruwa, dayake macece mai ilimi nan take tagamsu, snn suka fara shawarwarin yanda xasu shigo da ita ciki, shine yafara magana inda yacemata kinsan mexa'ayi? Saika fada tafadi tareda zama akusa dashi, bari insanar da Mukhtar baxai rasa mafita ba, yafadi hakan yana zaro wayarsa daga aljihunsa.


Ringing daya xuwa biyu yayi aka daga wayar bayan sungaisa ne tareda wasansu na barkwanci don mukhtar mutum ne me wasa da dariya, don har cewa sukeyi kowa ya haifi me halin dayan.

Kar barni kai idan aka biyemaka baxa'ai komai ba, kasan meyake faruwane, saika fada mijin me ciki,mtsww Abdullahi yy tsaki snn ya Sanar dashi komai.

Saida yayi jimm na 'yan daqiqu snn yace mishi kajirani bari inqaraso OK to shknn saikaxo.

Alhaji mukhtar fitowa yayi yasamu Mummy a falo yace mata Matar gidannan, juyowa tayi tareda cemishi Megidannan cikin salon tsokana, cemata yayi tadauko mayafi su shiga gidansu Ibby,batare da ta tambayeshi mexasuy ba, tafito tareda shiga dakinta Hijabinta tadauko har qasa suka fito tare.


Bayan sun iso gidanne akayi gaishe gaishe nan kowa yafara fadin Albarkacin bakinsa inda a qarshe mummy ta roqi abar mata ita kodon cikinda akace akwai a jikinta tunda itace batada qaramin yaro, insha Allah xata riqeta Amana har xuwa lokacinda xata samu sauqi...

Sun tattauna sosae akan maganar inda a qarshe akayi amanna da batun mummy aka dunguma domin xua gurinta bude motar Abba yayi aiko mummy na had a idanu da ita tasake wani salati me qara tareda dafe kanta tareda fadin wlh nasanta tareda fashewa da kuka me ban tausayi, mamakinsu bai tsawaita ba domin kukan mummy yatasar da Mama daga bacci tahau zazzare idanu cikin qanqanin lokaci tafara qoqarin fita ta window cikin azama.

Abunka da mahaukaci kiciniya takeyi iya qarfinta don ganin tafita, cikin hanzari batare da tunanin komai ba Mummy tayi cikin motar tana kuka, Saidai kafin ta isa gareta hartayi nasaran fasa glass din motar hannun ta yaji rauni, qaramin glass dinda ya maqale mata a hannun tane ganin mummy na nufota yasata qoqarin tureta cikin rashin sa'a tacaki mummy a fuskarta gab da idanunta.


Wani qara me hade da ihu na azaba mummy tasake tareda rude gurin da tafin hannun ta a take kuwa jini ya wanke mata hannun, cikin axama daddy yayi cikin motar yafito da ita, Ummy CE tafara matsowa snn Abba, nan daddy yace kawai awuce asibiti don shi gabadaya ya tsorata kardai ace idanun khadija ya tabu, Abba kuma jikinshi yy sanyi don yasan duk shine sila..

Mai gadi suka kira tareda mai bawa fulayi ruwa, suka CE suriqe ta don karta qara jima kanta ciwo direba ya tuqasu, snn sukuma suka shige wata motar , aka dunguma sai asibiti.....

********** Haka tanufo hangar gida bata tsaya jiran mai adaidaita ba don ganitake bata mata lokaci xaiyi kanaganin fuskarta xata ga annashuwan da yake kwance akai.


Ranta wasai tasan yaukam xatai maganin matsalarta, har ita Ayashe xata munafurta? Humm lokaci qanqani gidanta na Neman gagararta? Ko a mafarki vata gaba tunanin Ayashe xatai mata hakaba, wlh kuma shikanshi Mal.Habun idan yadawo hannun ta saiya dandana kudarsa duk da tasan bawai yana cikin haiyacinsa bane.

Baxai yiwuba tafadi hakan a fili tareda yin kwafa,

Sam bataji gajiya a tare da ita ba, duk da kuwa Nisan tafiyar, gab da layin da xai sadata da gidannata ne, taxo wucewa taji wasu samari dayan nacewa kamar pa wnn ce Maman sadiya, karaf sai a kunnenta, juyowa tayi tareda kafesu da idanu.

Suko ganin haka yasasu saurin fara tafiya, kamar tabisu amma domin yaji mesuke tattaunawa akai Wanda har sunanta Dana 'yarta ya gifta, amma sai taga ai abunda ke gabanta yafi qarfin matsalar su, don haka kawai tayi wucewarta, tabarsu.

A Dan gefe da gidannasu Kadan taga cicirindon mutane kamar xasu Cin kasuwa, tayi mamakin abun harxata wuce xata shiga gidan sai wata xuciyar ta kwabeta akan ta leqa mana,aiko wnn xuciyar CE ta rinjayeta, cikin Sauri tajuya takoma gurin.

Haka taita gifta al'umma da kyar tasamu ta isa 😳😳😳 mexata gani🙉🙉🙉.............



😍😍🤝🏼Anatare
Mummyn Fadyl CE




🎲🎲TUDUN DAFAWA🎲🎲


Rubutawa....MUMMYN FADYL (Fatyma Muhammad Adamu)

Wattpad @ *fatimamuhammadadamu*


INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION*
*[onward together]*
*{we give the reader's of ours the best out of the bests,, our inks are melodious and dropping a kinda lights to reader's}*
```THE PEN OF LOVE😘 HEAT TORCHING❤ TEAR OF SORROWS😭 CURDLES😊 GIGGLES😁 AND MARRIEGE THINK💑```
*```JUST GIVE US FOLLOW..**

_Naga messages dinku kuna tambayar alaqar mummy da Mama, banyi niyyar gaya muku ba, tunda a 2nanina indai kanabin karatun daki daki, to u don't have to ask 4 d past, amma yaxanyi Ku masoyanane na haqiqa_ *Mummy itace khadija dasuka hadu da Mama Zainab a asibiti lokacin haihuwan Nana* dafatan na 2no muku.

~Readers muje xua ina qaunarku acikin qalbina burina karku taba bani kunya gurin comments plx~


Fitowa ta.2⃣7⃣


Sadiya tagani babu kayan arziki a jikinta, kaca kaca da jini ai batasan lokacinda ta kurma ihu ba tafadi a gurin sumammiya..


Nan kallo yadawo kanta akai saurin dagata aka shigar da ita gida tareda ciccibo Sadiya itama akaiyo ciki da ita.

Duk abunnan da akeyi a tsakar gidan Ayashe tana daki, tadai leqo ta window tunda taga meke faruwa takoma kan gadonta tai kwanciyarta, kamar batasan acikin gidan ake sha'ani ba, duk kuwa da irin doka sallamar da aka dinga kwadawa qarshe suka tabbatar da bakowa a gidan..


Ruwa aka debo aka yayyafawa lami nan tasauke numfashi maikama Dana tsabar wahala, babu salati abakinta illa wani ihun data qara kurmawa tareda miqewa har zani na faduwa a jikinta, yabarta dawani baqin siket dinta bata kulaba tayi kan Sadiya da gudu.

Jama'a kuwa ganin rashin hankalinda takeyi ne yasasu barin cikin gidan daya bayan daya.

Gurin sadiyan tanufa tadurqusa tana jijjigata amma babu motsin jijiya balle bugawar qirji a tattare da ita, haka taita ihu babu qaqqautawa tamaida gidan tamkar gidan mahaukata, don kuwa duk Wanda yaganta baxai taba yimata kallon me cikakken hankali ba.


Jin kururuwan da takeyine yafara damun kunnuwan Ayashe cikin yamutsa fuska tafito daga dakinta, dama tayi zargin hakan zaifaru, qullin magani tagane a gurin zaninda yafadi ajikin Lami Wanda tama manta da kashinsa.

Bata tsaya ga komai ba, tsugunawa tayi tadau maganin kunceshi tayi snn tazo gurin Lami din, bata damu da halin da take ciki na mutuwar diyarta ba, tana tsaye ta kunce qullin maganin ta zaxzageshi akan Lami tsaf, nan Lami ta Ankaro amma Sam batada wnn lokacin.

Yanda bata dago ta kalleta ba, haka itama bata fasa surfa mata buhun bala'i ba, a qarshe kuma tace tasan yanda zatai da gawan 'yarta don yanxu xai iya fara damunsu da wari....

Wani tunanin ne yafado mata tamiqe zumbur harta nufi qofar fita ta taka qusa, wani azaba ne ya ziyarceta har tsakar kanta, ta durqusa domin cire qusan ne a lokacin talura babu zani a jikinta juyowa tayi taganshi can jefe, tana dingisa qafa ta qarasa tadauka, wani iri haka tadaurashi tayi waje tanajan qafafunta saboda zogin da yake mata, gakuma jini.

Tsaki Ayashe tayi, duk da harga Allah a ranta bahaka taso qarshen Sadiya ba, aiko banxa taci ajikin ta, kuma snn itace duk silar lalacewarta, duk uwarkice tafada tareda nuna gawar da hannunta, da mugun baqin halinta ta jawo muku, kekam kintafi kinbarta itaxata cigaba da dandana kudarta a hannuna kapin Dan nata yadawo shima ya jonata.


Can kuma dai taji a ranta tanason sanin meya faru, ai antake tadauki niyyar xuwa gurin Alhaji Nuhu domin jin menene silar mutuwan Sadiya.

****************
Taimakon Allah ne kawai ya kaisu asibiti, duk da su biyu ke riqe da ita, amma hakan baihanata qoqarin fusgewa ba, kapin su isa asibitin duk sungama yin laushi, itako sai wani gurnani takeyi, idan abun yayi kaman ya lafa, to sai tafara fusgan gashin kanta tana jijjiga jikinta can kuma saikaga ta fashe da kuka tana fadin menai maka?

Suna isowa daddy yai saurin kama dayan hannun mummyn yashiga da ita A&E nan aka tarbesu tareda shiga da ita dressing room,saida yabari anshiga da ita snn yafito waje nan yasamu anata artabu da Mama don kuwa ankasa fitowa da ita daga cikin motan.


Can dai dabara yafado musu Abba yayi saurin dauko wani snacks dinshi daya manta a mota yanufo ta dashi, ganin da tayi abuncine ya hannunsa yasata qoqarin xuwa gurin shi, shikuma ahakan da taimakon wnn snacks dinne har ya fara janta, duk da anatafiya tana tuburewa amma ahakan dai har suka isa psychiatric, tabbas idan kaje wnn gurin sai ka rasa me yake maka dadi, likitoci suka xo anan Abba yamiqa mata snacks din amma taqi karba saima fashewa da kuka datayi tareda kafeshi da idanuwanta tana kuma nanata menai maka?


Kallon juna suka farayi da Daddy itakuwa Ummy bata iya qarasowa gurin nasu ba, don tamugun karaya tunda tahango mahaukata burjik a gurin kukanta taketa risga.

Wani doctor ne yafito acikin dabara irin tasu yasamu yajata snn yanunawa su daddy hanyar da xasubi su sami office dinshi su jirashi anan..

Gaba dayansu sunyi mamakin yanda tabishi batare da amsamu matsala ko tangarda ba, wnn shi ake kira dabara kashin kwance Wanda bai iyaba ya bata jikinsa Abba yafada yana kallon daddy muje ko yafada, kai wani muje banje naqara dubo matata ba? Kazo dai mukoma mudubo lafiyarta inyaso idan angama mudawo.

To shknn tafada suka qara juyawa suka koma A&E din, sun samu ancire glass din harkuma angama mata dressing din, abunka da tsautsayi kusa da ido, nandanan har kamanninta ya sauya, fuskarnan ta kunbura, sannu sukai mata Inda daddy kuma ya matso gurinta tareda kama duka hannayenta.


Daddyn Aliy ina take? Tanacan psychiatric, meyasa xaku kaita can? Wlh nasanta itace matar da nake baka labarinta Wanda naso ka taimaka mata, itace wacce nake baka labarin an wayi gari a asibiti ta gudu, itace wacce nasaka kabiya duka bills dinta lokacinda ake cikiyar Wanda yasan daga inda take, taqara maganar nata da kuka.

Jinjina kai yayi irin tasu ta manya, Abba ne yadafa kafadarsa tareda cewa yakamata Ku fahimtar damu abunda yake faruwa don kuwa kanmu acikin duhu yake.

Daddy ne yafara yimusu bayanin iyakan abunda yasani gameda matar , don Mummy kam kuka yaci qarfinta, bayan yagama ne yajuya gurin mummy yatambayeta ya sunan matar? Tsagaita kukanta tayi snn tace wlh baxan iya tunawa ba, don Allah mijina kataimakeni karka barta a gidan mahaukata ni na amince xan rayu da ita har xua lokacinda xata samu waraka. Ina da tabbacin labarinta bamai dadi bane abun tausayi ce ita.


Shidai daddy dagalo yayi yana kallon mummy yanda taketa arattako bayanai cikin salon magiya da Neman taimako, can ya nisa snn yace.

Khadija yanxu hukuncin nan ba a hanuna yakeba, baxan iya barinta a gidana tareda iyalai na, tana cikin wnn halinba, don xata iya aikata komai ciki kuwa harda kisan kai, tunda mahaukaciya ce, sai abunda likitoci sukace indai har akwai taimakon da xasu iya bamu mu rayu tare da ita to shknn, alqawari daya xan iya miki shine xan tsaya tsayin Daka akan lafiyarta.


Bahaka mummy tasoba,amma hakanma yamata dadi nan tafara qoqarin share hawayenta murmushi yayi mata tareda cewa kinga yanda kikayi kuwa wlh kincanxa harwani qaton baki kikayi, inbaki sabeba dawuri aure xan qara, dariya sukasa gaba dayansu don sanin Halin Daddy duk abunda akeyi baya hanashi taba halin nan nasa na barkwanci.


Haka suka fito suka qara nufan Psychiatric din atare , ta hanyar da likitan yanuna musu, tanan sukabi suka shiga har cikin office dinnashi........



😍😍🤝🏼Anatare
Mummyn Fadyl CE




🎲🎲TUDUN DAFAWA🎲🎲


Rubutawa....MUMMYN FADYL (Fatyma Muhammad Adamu)

Wattpad @ *fatimamuhammadadamu*


INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION*
*[onward together]*
*{we give the reader's of ours the best out of the bests,, our inks are melodious and dropping a kinda lights to reader's}*
```THE PEN OF LOVE😘 HEAT TORCHING❤ TEAR OF SORROWS😭 CURDLES😊 GIGGLES😁 AND MARRIEGE THINK💑```
*```JUST GIVE US FOLLOW..**


Fitowa ta.2⃣8⃣

Lami tafiya takeyi hajaran majaran kai tsaye tayi gidan Baffan Sadiyah Wanda baxata iya tuno rabonta da wnn gidanba, kai rabonta da ganinsu ma tun wani lokaci dayaxo mata fada akan halinda Sadiya takeyi, aiko batai qasa a guiwa gurin baxa mishi rashin mutunci kala kala ba, har ta Tara mishi mutane, kunya ta addabeshi a qarshe yabar gurin.

Sallama tayi matar baffan Sadiya mamaki ne yahanata fadin komai tun bayan amsa sallamar tata, haka tamiqe jiki ba kwari tadauko mata kujera don tasan ba lafiya ne xaisa kaga Lami cikin wnn halin ba.

Xama tayi nan itama tadauko wata kujerar ta ajiye kusa da natan, gaisar da Lami tafarayi amma bata iya amsawa ba saima kukan da tasake.

Meke faruwane Lami kisanar dani mana, amma sai kuka kikeyi, Ganin da tayi batada niyyar magana ne yasata miqewa tayi cikin dakinta da hanxari, can saigata ta fito tareda mijinta..

Cikin sassarfa ya iso gurin Lami yafara tambayanta meke faruwa, cikin kuka tafara labarta mishi abunda ke tafe da ita, baitsaya jin qarashen xancen nata ba yakoma daki yaxanxo kayan jikinsa yafito tareda cemata tashi muje.

A kan Babur dinsa suka taho basu Tarar da kowa a gidanba, gashi yanda tabar Sadiya a tsakar gidan haka tadawo ta sameta, rige rige sukayi gurin isa gareta, shine yafara tattaba jikinta can yaa dago tareda furta kalman Innalillahi wa inna'ilaihirraju'un, kalman ce taqara dagawa Lami hankali, inda batai qasa a guiwa ba tahau kururuwa tareda birgima a qasa kamar qaramar yarinya.

Baibi takanta ba, don yasan idan yace xai tsaya bata haquri ne topa tabbas baxai je suyi abunda ya dace ba, yana fitowa qofar gidan nasu yahadu da Isah Wanda shine shigowarshi garin.

Ganin baffan nashi ya matuqar bashi al'ajabi cikin Sauri yaqarasa ya durqusa da nufin gaidashi, dagoshi yayi cikin sanyin jiki, don kuwa ganin da yayi mishi yasan baisan abunda yake faruwa ba, hannu yamiqa mishi sukai musabaha da juna.

Baffan ne yafara magana, saidai yayi mishi nasiha sosae kapin daga qarshe yasanar dashi halin da ake ciki, duk qoqarin da yayi don ganin yanuna jarumtarsa saida abun ya gagareshi, baisan lokacin da ya kece da kuka ba, bakukan komai yakeyi ba, sai kukan halinda Sadiya tamutu akai don yanada masaniya akan komai, sau da dama yakanyi qoqarin nusar da ita abunda fa takeyi dinnan baida fa'ida, ita kanta takanyi kuka snn tace mishi itama tanajin takaicin rayuwarda ta tsinci kanta aciki, snn takasa dainawa koda tayi yunqurin hakan saitaji baxata iyaba.

Dakyar yasamu ya rarasheshi inda yasanar dashi cewar xaije gidane domin neman sutura, snn xai turo matarsa axo maganan wanka, xaikuma sanar da duk Wanda yadace, haka sukai sallama tareda ajiye lokacin jana'ixa.


Gidansu yawuce don shi koda yaxo baya sauqa gidan mmn nashi, saidai idan gari yawaye yaxo ya gaisheta, duk dama duk xuwanshi basa wanyewa lpy, tunda bayabin abunda take shimfida masa, donshi gaxkiya yake gaya mata, itakuma bataso.


Ayashe kuwa gidanda ta tabbatar xata samu Alhaji nuhu tanufa. Takuma ci sa'a tasameshi yana ganinta yahau xuba mata kirari kamar kullum itako ta tsume kunsan ance Tsare gida mutuncin dandi😜.

Dakatar dashi tayi dacewa da Allah ya isheni rufemin baki mayaudarin Banxa, harni xaka yaudara kagama mantawa da uban kudaden da nake binka, kamanta halaccin da nai maka nakawo ma qananun yara kana moruwa dasu, duk da nasan sauran wa wasu kake kaiwa su mora, amma ai ba banxa kake kaimusu ba, tunda suna biyanka, xaka iya tuna yaushe rabonka daka sallameni?

Sanin da yayi mata na idan tana magana ba'a katseta, zunzurutun bala'in ta da iya tijara yasa baiyi yunqurin tsaidata ba harsanda yabari takai Aya, snn yafara bata haquri cikin dadin baki yafara cemata wlh inada niyyar cikin satinnan in hada miki kudaden ki in aika miki, tunda kinyi aure kinga haduwarmu baxai yiwu yanda mukeso ba, najima wai mijin Lami kika aura ko? Gaxkiya mutumiyata vakida kirki.


Jin labarin kudi ya gifta ne yasata sakin fuska tareda fuskantarsa dakyau tace mishi cikin murya qasa qasa, duka dai ba wnn ne kefe dani ba, amma shidinma dama inada niyyar zuwan maka, amma yanxu abunda yakawo ni shine Sadiya fa tamutu.

Tamutu😳??? Yafada bangane tamutu ba, meya faru subhanallah, xakacemin bakasan da hakan ba? Ta katseshi, wlh bansaniba rabona da Sadiya yau sati daya knn tunda narakata Kano gurin wani Alhaji kinga mani kintuna min domin bai biyani kudina ba amma bari innemeshi inji.



Kiran wayarsa yayi baijima ba yadauka, gaisawa sukayi sama sama snn ya tambayeshi lbrn Sadiya kamar baisan abunda yake faruwa ba, aiko nan yacemishi Sadiya tamutu saboda na'ajiyeta a gidana muna hutawa tare don kawai natafi Abuja meeting da niyyar kwana amma kwanan bai yiwuba nadawo kawai na tarar da Sadiya da maigadin gidana!


Abun ya girgizani snn yabani takaici, saboda meye xata hadani da maigadi na kuma a shimfidana? Jaraban Sadiya yajima daman yana qonamin rai don bantaba haduwa da macenda na kwanta da ita batai kuka ba sai Sadiya, ina haquri da itane don tasan kan harka. don inada tabbacin yana dauke da cuta.


Shiyasa nasa yarana sukai musu Dan banxan duka, cikin rashin sa'a yaran nawa sukaita amfani da ita Wanda yakai munzalin bata iya motsi, nasasu sukaita asibiti Ashe basukaita ba washe gari suka sanar dani tamutu amma tabasu lbrn gidansu akan sukaita gurin mamanta, yaqarasa maganar da Alamun rashin damuwa a tare dashi tamkar kiyashi ne yamutu a hannunsa ba Dan Adam ba.

Bayan yagama fadar hakan ne a qarshe yacemishi xan 2ro maka kudin

Please Login or Register in order to submit comment