You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

reader's}*
```THE PEN OF LOVE😘 HEAT TORCHING❤ TEAR OF SORROWS😭 CURDLES😊 GIGGLES😁 AND MARRIEGE THINK💑```
*```JUST GIVE US FOLLOW..**

*idannayi badai daiba agyaramin plx Kunsan tunani kowa da irinnashi*


~qorafi akan pages dina basa yawa kuymin haquri plx kunsanpa ni sabon shigane, 😉 yau pages biyu nayi don kuji dadi my fans~


Futowa ta. 0⃣7⃣.


Da sallamarta tashiga gidan Ayashe tasameta a tsakar gida da daurin qirji, tanadan busa sigarin ta, sai da takammala snn taimata iso har cikin uwar daki, a qasa Sadiya tazauna snn tagaisheta, lpy qalau Sadiya ya karatu?
Mungode Allah .


kapinnan Ayashe ta Dora da to Sadiya kinsan menake so dake? A'a tafada da ladabi don tana matuqar tsoron Ayashe, saboda tasanta ba mutunci ne da ita ba yanxu saita tsigale ta, Ayashe tace kudi zaki sama muku anan gidannawa domin cikar burinku keda uwarki, abunda zakiyi daya ne kidaure kibawa Alhaji hadin kai, bawani zafi idan kika sake jikinki amma pa idan kika takure wlh kaca kaca zai miki har jama'ar gari su fahimci halinda ake ciki, ko kinpison Asani?


A'a tafada da sauri hade kuma da girgiza kanta, to shknn zanje inturoshi yanxu, amma kapinnan tashi ki canza wadannan kayan jikinnaki shegun tsummokara banda tsami ba abunda ke tashi ajikinsu, jikin Sadiya yayi sanyi da wnn wulaqancin Ayashen, Amma haka tamiqe itakuma tawatso mata wasu shegun kaya matsatstsu Wanda daman takan ajiyesu ne idan irin hakan tafaru.

Waje tayi tana qara jaddada mata akan tashirya pa dawuri, Sadiya cikin zumudi tamike tafara gwada kayan, hummm Allah yasa Alhajinnan yabani kudi dayawa wlh saina sayi irin wadannan kayan, tsab Sadiya tayi kyau surarta taqara fitowa acikin kayan,
Zama tayi tana yatsina fuska alamar yanga... ( ansamu guri)



Lami kuwa asibiti tayi, saidae abunda ta taras yamatuqar daga mata hankali, don ko ansanar da ita suntapi tun jiya da rana.


Zama tayi a gindin wata bishiya tafara tufka da warwara, gakuma tunanin Sadiya daya addabeta jitakeyi kamar taje tacewa Ayashe tafasa amma kuma shine kadai damarta na qarshe akan Mal.Habu, can dai taga batada mafita ta tashi tayi gida, zuciyarta cike da takaicin Zainabu don tanada tabbacin idan takoma gida zatayi lpy, hummm lallai Zainabu kinawasa dani LAmi Qaya.

Wlh yanxu zan taho miki gadan gadan, kenan duk aikinda nashirya akanki saikin wargaza min? Haka taketa sambatu kamar mahaukaciya ita kadai a Titi. Harta isa gida tazuba tagumi tana jiran dawowar Sadiya..


Tana ciki ne? Taji muryan Alhajin yana fadi? Eh kashiga amma Alhaji baka sallameni bafa, haba Ayashe kin cika gaggawa kibari in Dana mana kapinnan ko? A"ah Alhaji dinyar makaho tanuna a hanunsa bani kawai inji dumus tamiqo mishi hannu, dubu Ashirin yadanqa mata, washe baki tayi snn tace afito lpy. Amma kadubi girman Allah kabita ahankali wlh yarinyace shakaf, snn bata taba yiba, bakida Matsala da wannan, yayi shigewarsa cikin. Dakin.....


Tunda yahango Sadiya yafara hadiye miyau gamida lasar lebunan sa, 'yan mata yakika takure kanki, ah matso mana kamo hannunta yayi snn yace mata kisaki jikinki dani Sadiya kinji? Daga mishi kai tayi, amma zuciyarta bugawa takeyi ganin Girman jikinsa don tulin tumbinsa ba abun kallo ne fuskarsa ko faranti guda wayyo Allah na tafada a ranta.

Shikuwa Alhajin Allah shafa jikin Sadiya yashigayi jikinsa na mazari bai bata lokaci gurin kaiwa nonuwanta cafka ba azaba yasata sakin qaramar qara, dazafi ne? Yafada murya can ciki, eh tafada da sauri, sannu yace snn yacigaba ganin da yayi tafara lumshe ido tareda banqaro mishi qirjinnata, nan yarabata da gabadayan kayan jikinta.

Batareda ta Ankara ba, nishi tafarayi sama sama, Alhaji yamiqa hannunsa cikin harabarta jin dayayi gurin yafara bulbulo da ruwa yasashi rudewa, sandar girmansa taqara girma da tsayi kamar zata hudo wando, saida Sadiya taji ana goga mata abune tadawo hayyacinta amma nauyin da Alhaji yasake akanta yahanata aikata komai amma tafara roqonsa akan yayi haquri, baima fahimci yarenda takeyi ba, itakuwa azaba takeji Wanda bata taba jin irinsa ba a rayuwarta.


Alhaji kuwa dayaga abun na bata mishi lokaci da qarfinsa yamiqa mata saqonsa, batasan lokacin da tayi wani wawan qara ba,jikinta yasake amma hakan baisa Alhaji yasassauta mata ba har saida yasamu nitsuwa ya gungura gefe yana maida numfarfashi, Azaba yahana Sadiya koda daga yatsunta ne banda tsinuwa babu abunda takeyiwa Alhaji da Ayashe kai harma da Umman nata..

Shikuwa bayan yagama komawa cikin hayyacinsa ne, yatashi ya kimtsa jikinsa tareda cemata kigyara jikinki, ga wannan ya ajiye mata dubu arba'in agefenta yayi waje.

Duk kwadayin Sadiya haka tana kallon kudin takasa bi takansa savoda halinda take ciki, takasa yin farinciki don wahala, koda ta yunqura zata tashi jitakeyi kamar ana tsaga mata qasanta da reza.

A wannan halin Ayashe tazo tasameta, a'ah Sadiya Yaya haka, sai yanxu Sadiya tasamu tafashe da kuka, sannu Sadiya daure kitashi kigyara kapin insamo me adai da ita sahu ya kaiki gida, wlh Umma baxan iya tashiba,yau naji sakarcin banxa wani irin kuma baxaki iya tashiba Sadiya? Tafada ta sigar hantara, UMMA qasana zafi yakemin, kowa dahaka yagirma don hakama gara ki tashi ki kimtsa atoh.

Cikin abunda bai wuce minti goma ba Ayashe tadawo tareda me adai daita, haka tashigo tasamu Sadiya a kwance kamar yanda tavarta taimaka mata tayi tamiqe tanata yimata sababi, .


Tsayuwar adaidaita ne ya fargar da Lami tamiqe har tana tubtube tafito waje, Sadiya na ganinta ta qara langabewa, sannu Sadiya fito umma qasana, sannu Sadiya wnn rusheshen mutumin nasan xa'a Rina hakan, Kudin tamiqawa uwar itakuwa ta qumsheshi a bakin zaninta kapinnan tajuyo gurin Ayashe, to Ayashe angode, bakomai ai yiwa Kaine.

***Bayan kwana bakwai**


Alhmdllh sauqi daga Allah yake, domin kuwa zainabu tasamu sauqi sai dan abunda baxa'a rasaba, tafara magana saidae kawae rashin kuzari dakuma rashin walwala tana yawan tunanin dalilin irin rayuwar data tsinci kanta aciki murna gurin Mal.habu baxai misaltuba, sun yanke shawarar komawa gidansu washe gari.

Lami tana zaune Sadiya na gefenta, Umma to yanxu kibani dubu ukun mana, tunda nagaya miki maganar anko din Hafsatun gidan Yakumbon kumapa jibi xa'aje cikin gari kawowa, sallamar da sukaji ke yahana Lami amsa mata, cikin qunan rai don kamar anxuba mata ruwan dalma a qirjinta haka takeji. Tamiqe tsaye cikin razana tace.....



😍😍🤝🏼Anatare
Mummyn Fadyl CE .

Wattpad@ fatumamuhammadadamu


🎲🎲TUDUN DAFAWA🎲🎲

Rubutawa...MUMMYN FADYL (Fatyma Muhammad Adamu).


Wattpad@ fatimamuhammadadamu.

*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION*
*[onward together]*
*{we give the reader's of ours the best out of the bests,, our inks are melodious and dropping a kinda lights to reader's}*
```THE PEN OF LOVE😘 HEAT TORCHING❤ TEAR OF SORROWS😭 CURDLES😊 GIGGLES😁 AND MARRIEGE THINK💑```
*```JUST GIVE US FOLLOW..**

~'yan hannun damana Intelligent writers association! Idannace zan lissofo sunayen to tabbas zan manta wasu daga cikinmu, inadai mana fatan Alkhairi, Allah yabarmu tare Yakima qara daga qungiyarmu Up Up Our Group.. Luv u All~


_Kunga ba'a Ado da yana, shinge shike kare gida, Koba yanka kifi ana iya kamawa Aci!!!_


Fitowa ta..0⃣8⃣.


**Da sanyayyiyar murmushi zainabu ke kallon Lami, itakuwa Lami din zuciyarta ce cunkushe da baqincikin ganin zainabun akan qafafun ta, amma haka tadaure ta qaqalo murmushi cikin makirci tace wayyo Zainabu kece haka? Allah me iko, harna rasa inda xansa kaina don dadi, ga guri kizauna, Zainabu tace mata kawai nashigo ne mugaisa yanxunnan isowar my,banko shiga gidana bama.

Ayya nagode idan kinhuta xanshigo muqara gaisawa ai wlh naso zuwa saidae bansan gidannaku ba kuma gashi niba waya ba, amma yanxu kam ai xannemi gidannaku insha Allahu kodon gaba ma, bakomai wlh jiki kam Alhmdllh nayi sauqi, to shkn Lami saikin zo.

Duniyar tunani ta Lula itakuwa wace iriyar macece haka kome akai mata bayanisa? Sadiya kece mata Umma kibani kudin.. Yayubo ashar tayi ta watsa mata, cikin bacin rai Sadiya tace Umma wnn kudinpa nawane Yaya kuma zance kibani kidinga zagina? to wlh gaba kokin turani baxani ba, ta turo baki tatashi tana buga qafafu tayi waje, itako Lami Sadiya bata isheta kallo ba, saboda damuwarda take ciki tagirmi matsalar sadiyan.

Haka rayuwar taci gaba da tafiya, inda Lami taci gaba da shigewa jikin Zainabu, duk dama dai akullum tadawo daga gidan baka safai take samu tayi bacci me dadi a ranar ba, saboda abubuwan cigaban da take gani dakuma qaunar da take qara wanxuwa a zuqatan su. A wnn halin ta fahimci Zainabun tana dauke da sabuwar shigan ciki. Hakan yamatuqar daure mata kai, saboda tayi tsammanin Maye yagama Lalata mahaifar tata, gashi tanason komawa gurinshi akan cikin amma tana tuno jarabar Maye, Sam baxai sarara mataba.

Daga qarshe dai tayanke hukunci zuwan kawai, tabashi kanta, yakuwa turmusheta snn yace xataga wiki dacikawa, dukda yaqara jaddada mata batun kudaden, akan takawo amata mai gaba daya, itakuwa Lami tun isowar kudi maqo yahanata su amfana da kudin, inbanda dubu biyu data cire aciki Taiwa sadiya jinyaba to ko sule basu qara tabawa ba..

Saidae a wnn karon Zainabu bata sakaci da addu'a don Mallam na dutsan Ma. Yabata,tasha gargadi sosae da sosai akan maganin, gaba daya addu'o inda yabata bata wasa dasu hakanne ya tserar da ita dakuma abunda yake cikinta...

Domin wnn kyenwar a gidan ta tare saidae kuma babu damar nufan gurin Zainabu, ko bacci Zainabu xatayi tofa xatayi addu'oi ta tofe Mal.Habu don talura haryanxu bai farka daga mummunan baccinda ake fama dashi a wnn zamaninba sau da dama idan ta ankarar dashi to yakanyi qoqarin yi na 'yan kwanaki daga nankuma ya watsar.

(jama'a yakamata mufarka daga wnn baccin muriqe addu'oi don kuwa addu'a shine tokobin mumini bakasanin maqiyinka, baka damu da rayuwar mutum ba, amma akullum burinshi yaga ka wulaqanta, Allah yayi mana tsari)

A zaman da tayi da Zainabu ta fahimci cewar Mal.Habu yana matuqar son Zogale shiyasa tayanke shawarar amfani da wnn damar domin cika burinta, tunda baxaiyiwu ta fitar da Zainabu a yanxu ba, gara tashiga gidan kawai inyaso xatasan yanda xatayi daga baya.

Da wannan tunanin hankalinta yakwanta takawa MAYE kudaden sa shikuma yabata maganin daya ta bunne a cikin gidan inda tasan tabbas baya bushewa ruwa yana jiqashi kullum dayan kuma ta tabbatar Mal.Habu yaci wannan abincin.

Gab da mangariba ta shiga gidan basu jima da fara hira ba aka fara kiran sallan Mangariba, cikin. Hanzari Zainabu tamiqe tafara shirin alwala, itama Lami din cewa tayi kiyi Nima inyi, cemata tayi haba Lami har sai kin jirani? Gawani buta kidauka mana, hummm kekam kainane yakemin ciwo kiyi kapinnan naqara hutawa sai inyi, ayya to Allah yabaki lpy ciwon kai babu dadi, tayi alwalar ta tashige daki tabar Lami, saida ta tabbatar Lami ta Tayar da sallah itakuma tamiqe tanufi inda zainabu take alwala, ta dauko qaramin qarfe ta tona tabunne Layar snn tarufe gurin ta tattaka baxaka taba 2nanin akawae wani Abu agurinba, tagama tayi alwalar snn tadauki sallayar ta fara sallah Wanda Zainabun ma bata rigata idarwa ba, don batai minti daya mekyau ba.

Zaunabu bayan ta idar tayi addu'o inta tafito tasamu Lami tayi gidanta, jinjina ibadar lami, saboda Sam bata nitsuwa tayishi tayi mata maganar harta gaji amma bataga alamar xata canza ba, Allah yakyauta tafada tareda nade tabarmar tashiga dashi cikin daki.


Ran Lami yayi fari Tass saboda tafara aiwatar da ayyukanta yanda takeso, Washe gari kuma ta tashi da qarfin guiwarta ta aika Sadiya tasamo mata zogale dafaffe don tasamu tahada tun kapin Mal.Habu yawuce kasuwa, kiy sauri don Allah karki bata mana shirinmu don wnn shine damar mu taqarshe.

Bayan dawowar Sadiya ne tagyara zogalan ta Wanda yasha kayan hadi😋 taxuba garin maganin tayi gidan zainabu ranta fess, da sallama tashiga batasamu kowa a tsakar gidan ba, hakan yatabbatar mata da suna cikin daki, abunda yaqara turnuqa zuciyarta knn, yaqara xuxuta wutar qiyayyar Zainabu a zuciyarya, sallama taqarayi a karo na biyu, jin Anata sallama ne yasa Zainabu fitowa ganin Lami ce yasata fadada murmushinta, 'Akwana a hantse sai kyakykyawa Lami tafada, kayya ba bacci nakeyi bama wlh Inadan kintsa guraren ne, Ayya wlh kwadan zogala nayi shine nace bari inshigo miki dashi, abunka da masu sarauta nasan zaki buqaceshi..

Kai Amma naji dadi saidae ni Zogala bata dameni ba, amma nasan Malam zaiyi farinciki sosae wlh don kuwa baida abunso kamar Zogala, nagode Allah yabar zumunci, Ahhh bakomai wlh ai yiwa kai ne, sai anjima.

Lami ta tafi gida tazauna tanajiran sakamako harta fara zartar da ranar tarewarta.
Cikin daki takoma tasamu Mal.Habu yanajin labarai, Ranka ya dade ga zogala, miqewa yayi snn yace wlh yanxu ina rayawa a raina idanna fita yau zan aiko miki dashi kogyara min akai kasuwa. Aiko gashinan Lami ta hutar dani, tashi tayi da niyyar fita takawo mishi ruwa, shiko cikin zumudi har yakai loma daya baki yana lumshe idanu, riqe hannun nasa tayi tareda cewa Mal. Haryaushe xaka dinga tuna kiran sunan Allah a gabannin cin abincinka? To Bismillah insha Allahu zanna tunawa...


Anya aikin gama bai gamaba?🤔



😍😍🤝🏼Anatare
*Mummyn fadayl CE*




🎲🎲TUDUN DAFAWA🎲🎲


Rubutawa...... MUMMYN FADYL (Fatyma Muhammad Adamu).

_wattpad@ fatimamuhammadadamu_


*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION*
*[onward together]*
*{we give the reader's of ours the best out of the bests,, our inks are melodious and dropping a kinda lights to reader's}*
```THE PEN OF LOVE😘 HEAT TORCHING❤ TEAR OF SORROWS😭 CURDLES😊 GIGGLES😁 AND MARRIEGE THINK💑```
*```JUST GIVE US FOLLOW..**


*De battle is about to start*


Fitowa ta. 0⃣9⃣


Tunda yacigaba da cin abincin baisake tanka mata ba, saboda shikadai yasan halinda yake ciki ganin hakan yasata miqewa taje tahada mishi ruwan wanka snn tadawo.

Ranka ya Dade tunda ka kammala ai sai aje ayi wanka asamu afita kasuwa ko? Bai mata magana ba snn bai juyo ya kallaeta ba balle tasa ran zan amsa mata, Yaukam Yallaboi na sarautar ce ta motsa? Tafadi hakan ta sigan barkwanci ke! Xainabu dakata🖐🏼 Yaya nekam xaki sakani agaba kamar danki? Tsoro firgici dakuma tashin hankali ne ya dirar mata lokaci daya, kalmar Innalillahi wa inna ilaihirraju'un! , bata samu tadawo daga tunanin ba taji yana cewa, kince kin hada ruwan wanka ai naji tunda ba kurma bane ni, kuma saiki tisani a gaba, to wnn abubuwan dakikemin ya isheni, nakuma kusa kawo qarshen iskancin nan naki Mtswww yamiqe yafita.

Sororo tabishi da idanu meye haka? Menene yake shirin tinkaromin gidana, tananan azaune harya fito daga wanka.tashi tayi domin taimaka masa, nanma dakatar da ita yayi tareda cemata, Zainabu nikam lafiyarki duk pa abubuwanda kikemin ina sane dashi nabarki ne kawai. Shawarar da xanbaki daya ce kifita harkata tunkapin nasaba miki.

Hawaye ne ya gangaro mata, meye faru, mijina menayi maka? Don Allah idan laipi nai maka kasanar dani innemi yafiyarka, baxan jurewa fushinka da irin wadannan abubuwan su dinga faruwa tsakanin mu ba. Duk maganar da takeyi dinnan tana riqe da bakin rigarsa ne itakuma tana durqushe a qasa.

Fusge rigarsa yayi tareda hankada ta yayi waje abunsa, fashewa tayi da kuka, tajima tana kuka ganinda tayi kukan baxai fishsheta bane, tamiqe tayi waje tadauro alwala taxo ta Tayar da sallah, hawaye yana kwaranya a idanunta tadaga hannuwanta sama tana miqa kukanta gurin mahaliccinta, bata gusheba har sanda
taji xuciyarta tayi mata wasaii, tadainajin komai saima sabon qaunar mijinta dakuma abunda yake cikinta.


Mal.Habu tun isar shi kasuwa yakasa sukuni yakuma kasa tantance me yakeji acikin zuciyarsa! Meya sameshi? Meyake ji? Meye zainabu tamishi, anya kuwa yayi mata adalci? Meya shigesa kai yakamata yakoma gida yabata haquri pa, Zumbur yamiqe yaron dake zama mishi a shago yakira tareda jaddada yana dawowa bada jimawa ba.


Tsayawa yayi yasamata gwaiba saboda tun shigan ciki yalura aduk abunda yake sayo mata tafi qaunar gwaiban gidan yanufo da niyyar rarrashinta, amma yana shiga gidan yamanta darajarta da kimarta yadaina yimata kallon matarsa, tamkar baiwar da yasayo haka yake kallonta.

(Idan baku manta ba ata bakin qofa gurin alwalar yake, saikabi tagurin xaka Shiga gidan kaga kuwa dole ataka Layar LAMI QAYA SOKI UBAN KOWA) 😜



Jin qarar taku a tsakar gidan ne yasata fitowa domin ganin wayene, shikuma a daidai wnn lokacin yagama yanke hukuncin komawa don haka basu hada idanu ba, qeyarsa tagani yafita, cikin sauri tarufa mishi baya, amma kapin tafita, harya hau Babur dinsa yayi gaba, dawowa tayi taxauna. Atsakar gidan , idanunta ne yasauka akan ledan tamiqa hannu ta jawo tabude, gwaiban da taganine yasata sakin murmushin da batasan tayishi ba, Allah sarki mijina nikaina nasan kana qaunata tafadi hakan wasu siraran hawaye na zubowa daga idanunta.....


Matar gidannan tananan kuwa? LAMI inanan inaxanje da sassafennan? Qaraso mana kintsaya a bakin qofa, shigowa tayi taxauna snn tace mata Nazo karban kwanon dazune Sadiya tasani a gaba wai ita xata mayar dashi gidan Ayashe, kinsan nata ne, ta aikomin da Alalan gwangwani shekaran jiya, Ayya to bari inmiqo miki, Allah daiya biyaki don mal. Yaji dadin sa wlh, shikadai ma yaci yatafi kasuwa.

Farin cikine yaxiyarci xuciyar Lami,cikin dakiya tace Ayya. Sun fara hira lami tace xata tafi abunta, Haba Lami yau baxakimin hantsi ba? Wlh nasaba muyta hira habadai, Hummm xakiyi Dana sanin wnn hirannema don kuwa kinkusa samunsa kusa dake bada jimawa ba Lami tafadi hakan aranta, Amma A fili tace wlh ina sauri ne xanje dubiya matar Matar baffansu Sadiya ta haihu suna asibiti.
To Allah yaraya saikin dawo. Nikam ya labarin Isa? Uhum isah munyi waya dashi tawayar Ayashe yacemin Wata mai kamawa zaizo. To Allah yakwoshi lpy Amin tafada snn tayi waje.


Itakuma Zainabu ciki takoma tadaura abincin Rana...

Lami bayan ta'ajiye kwanon agidane tayanke hukuncin xuwa shagon Mal.Habu a kasuwa don haqurinta yagaza gani takeyi kamar maganin nata baiciba, tunda harya iya wucewa kasuwa batareda ya tunkareta da maganar ba,kudi tadauka tareda ficewa tayi kasuwa.


Bayan komawarshi shago yakasa sukuni yakuma kasa fahimtar halinda yake ciki, haka yaxauna acikiin shagon amma yaron shagonsa ne mesayar da atampopin. Sallamar da aka kwada ne yashiga harcikin kwakwalwarsa tareda aika masa sakwanni nantake yagane cewar abunda yake buqata ne ya iso gareshi.... Dagowa yayi nan take idanunsu yayi sarqiya...........


Yi tayi kamar bata Ganshi ba, snn tacewa yaron Atampa nakeso na qaramin kudi, kamar na nawa? Dubu uku, a'ah Wace nake gani kamar Lami, itace dama nanne shagonka? Eh nanne mekike so? Fari tayi da idanunta snn tagyara tsayuwa tace mishi na dubu uku nakeso, cikin rawar jiki yadauko zani na dubu biyar yasa a Leda snn yamiqa mata.

Uhumm cikin makirci tace wnn atampar ai tafi qarfin kudina washe baki yayi, yacemata bakomai Lami kyauta na baki, kibar kudin kawai. Juya idanuwa tayi ta sigar yaudara, tace to nagode Allah yasa afi haka, Amin..

Tajima a tsaye tana qaremishi kallo yayinda shima yakeji xuciyarsa na Azalzalarsa akanta, Wanda ko matarsa ta sunna bayajin hakan akanta, inama yanada ikon rungumarta?


Sai can tace xankoma sai anjima, am ummm nace ba, maganar ce tamaqake mishi a fatar bakinsa shikuma yakasa furtawa, to agaida gida, cikin kufula tabar gurin batareda taqara tanka masa ba.

Taso ace yasanar da ita halinda yake ciki, xanjira ka harxuwa lokacinda zaka kawo kanka gareni, da wnn tunanin ta isa gidanta.


Gab da mangariba yasamu ya iso gidanshi parking din Babur dinsa yayi, amma yakasa shiga gidansa domin babu abunda yakeda muradin gani kamar fuskan Lami, ganin tsayuwar na Neman gagararsa ne, ya yankewa kansa hukuncin shiga gidan Lami din.


Lami tana bandaki taji Sallama muryar mal.habu ne yashiga kunnenta, bashiri ta fusgo zaninta a jikin Katanga, jiki duk kumpa tayi waje, harzata fita ta tunada mayafi aguje harda tuntube ta gobje qafarta amma bata lura takuma ji azaban ba tayi waje abunta..

Umm Mal.Habu Kaine dakanka rasa ta inda zai fara yayi, candai yayi ta maxa yace..................





🎲🎲TUDUN DAFAWA🎲🎲


Rubutawa....MUMMYN FADYL (Fatyma Muhammad Adamu).


~wattpad @ fatimamuhammadadamu~



*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION*
*[onward together]*
*{we give the reader's of ours the best out of the bests,, our inks are melodious and dropping a kinda lights to reader's}*
```THE PEN OF LOVE😘 HEAT TORCHING❤ TEAR OF SORROWS😭 CURDLES😊 GIGGLES😁 AND MARRIEGE THINK💑```
*```JUST GIVE US FOLLOW..**


*Ga bikin zuwa babu zanin daurawa, tafiyarce tazo da haka*


Fitowa ta.1⃣0⃣


Candai yayi ta Maza yace mata daman nadawo ne naga yadace inshigo mugaisa ga wannan😊 bada sunanta yakawo ledan ba, amma ganin yarasa yanda zaiyi ne yasashi yin kyautar dole, hannu tamiqa takarbi ledan hannunsa a daqile tamishi godiya batajira cewarsa ba tai shigewar ta ciki, tsintan kansa yayi da leqenta kamar yabita ciki hakan yakeji, amma yaxaiyi 🤦🏽‍♀ haka yakoma cikin gidansa.....


_BAYAN WATA BAKWAI_

abubuwa da dama yafaru rayuwar gidan Mal.habu ya tabarbare yagama gaxkata cewar qaunar Lami yakeyi haiqan, wulaqanci kuma bawanda Zainabu bata gani agurinsa, yadaina cin abincinta yadaina kusantarta asalima ba abunda yake shiga tsakaninsu baya amsa gaisuwarta.


Duka wadannan abubuwan sunada nasaba da Sharrin Lami din, saboda tariga tagama dashi duk dama haryanxu yakasa Sanar da ita abunda yakeji gameda ita.

Hakan baya hanata aikatamishi duk abunda yasan hakkinta ne, bata fasa yimishi komai akan abunda takeyi mishi da ba, duk dama baya yabawa kokuma taga alamar jindadi atare dashi.


Tun cikin dare tafara jin ciwon Mara kadan kadan, tana juyi akan gado yayinda shima Mal.Habu yakejin duk duniya bawanda yake cikin damuwa irinsa, don kuwa wata masifaffiyar qaunar Lami ce ke addabarsa, wani sashin na zuciyarsa kuma na azalzalarsa akan Zainabu saboda bayajin digon komai atare da ita, yakuma kasa rabuwa da ita.

Ke Zainabu tashi yafada cikin halin ko inkula, miqewa tayi tazauna tana ciza lebunanta saboda azaban da takeji, kinsan menakeso dake? A'a saika fada, inason kisaurareni da kunnen basira Aure nakeson inqara, Tamkar saukan Araduwa haka taji!

saboda baxan boye miki ba gaxkiya banajin dadin zama dake, nagaji da halayyarki kwata kwata don haka inason kicire komai a ranki idan kuwa kikace zakisa damuwa a ranki to wlh zuciyarki ce zata fashe, kinsan kuwa bawanda zaiyi asara tunda ba uwace gareki ba, mahaifinki kuma baqarfi ne dashiba balle kiyi tunanin zaisa hannu a jinyarki.


Tunda yafara maganar take kuka babu sassauci bata taba kawowa a ranta akwae ranar da xataji maraici irinna yauba tun haduwarta da mijinta yake debe mata kewar mahaifiyarta, amma yau anwayi gari shida kansa yake ruguza mata tunani baya hango halinda take ciki, wannan bala'in dame tayi kama? Inazata sa kanta taji sanyi...


Komawa yayi yakwanta, yaji kukan nata yana Neman takurashi, miqewa yayi yadaka mata tsawa tareda cewa, idannine bakyason gani zanfita inbar miki dakin, yamiqe yayi waje yana sababi, mace sai shegen tarin damuwa? Mtswww yayi waje abunsa, itako damuwarce taqara tado mata da naquda gashi shine nafari batasan yanda xata taimaki kanta ba, Allah ka kawomin dauki haka tayita maimaitawa ciwo kuma sai gaba yakeyi.


A Qofar gida yazauna wata zuciyar nagaya mishi yadubo halinda Zainabu take ciki, amma dayar zuciyar tayi rinjaye inda shikuma yaga dolena yabi umarninta don haka yayi zamansa, baidawo gidan ba harsaida gari yafara haske kuma koda yashigo baiji ajikinsa yaje yadubata ba.


Zainabu ciwo ya tsananta bata iya komi tarasa makama tarasa wazata kira yataimaka mata.

shikuwa Mal.babu wanka yayi bayan hantsi ta hudo kai yatafi abunshi kasuwa.

tanacikin wannan halinne yayar Mallam Habu Amina tayi tsinkaye wa gidan, saboda Zainabun ta kwana biyu bataje mata ba, tace yakamata tadubo yanayin jikinnata tunda tayi nauyi, sallama tayi sau kusan biyar ba'a amsa ba kuma taga gidan akwai alamar masu gidan sunanan, Nishin wahalar da takeji ne, yasata kutsawa dakin cikin tashin hankali.

Mexan gani nashiga uku ni Amina, Zainabu tagani a kwance tanata taunar harshenta Wanda yayi kaca kaca da jini, rasa abunda zatayi kokuma yakamata tayi, nan tai waje tadawo ciki, gaba daya jikinta rawa yakeyi, dakyar tunanin xuwa asibiti yazo mata, nanfa tayi bakin layin dagudu tanemo me mota.


Sakata sukayi a ciki sai asibiti, taimakon gaggawa aka bata inda akagano b.p dinta ne yahau sosae har yahaifar mata da taune taune, bayan ansa mata magani a qarqashin harshenta ne, da ikon Allah kuma yadakata, saidai kuma labour ya kwanta, babyn kuma tagaji saboda hakan sukace ana Neman mijinta yasa hannu xa'a shiga da ita tiyata domin ceto rayuwarta dakuma abun cikinta.


A kasuwa kuwa Mal.Habu yakasa aiwatar da komai ko makwafcinsa da yaron shagonn nasa baiyiwa sallama ba yawuce gida, domin yaukam ya yanke hukuncin tunkarar Lami da buqatarsa, duk da baisan yanda xata dauki abun ba, don haka yana xuwa ya aika akai mata sallama, fitowa tayi qirjinta na dukan uku uku, zuciyarta na ayyana mata irin rashin mutuncinda ta tanada masa matsawar bai Sanar da ita abunda takeson ji ba.


Bayan sun gaisane ya numfasa, tareda cewa, agaxkiya Lami Hausawa dai sunce

Please Login or Register in order to submit comment