You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

motsi balle ta iya furta wani kalma.



Ganin batada amsar da xata bashi yasashi fita waje domin yanajin kukan nata yana ratsa duk wani sassa na jikinta, can ta dago kamar an mintsineta tace mummy ina wayata? Dakyar tabata amsa wayarki tana gidanki ba'a taho da ita ba.



Mummy kice a daukomin akwai abunda xan duba, snn banason komai dayake cikin gidan, tafadi muryanta yagama dishewa dakyar maganar ta yake fitowa.


A take mummy takira Humairah akan tayiwa qaninta magana da asuba ya rakata gidan Zarah a dauko mata wayarta yana daki, juyowa tayi domin cigaba da bawa xarah baki, amma tace mummy don girman Allah karkice indaina kuka, mummy kece shaidan qaunar dake tsakanina da IBBY, mummy kinsan yanda nasaba dashi, mummy tayaya xan iya mantashi dakuma halaccinsa a gareni lokaci daya?


Tacigaba da magana tana girgixa kanta, mummy baxan manta da IBBY ba, da ace mutuwa tasan halinda xan shiga bayan daukeshi datayi data daukemu a tare, da ace tasan qaunar da mukewa junanmu data tafi damu a tare, mummy baxan iya rayuwa babu.....


Rufe mata baki mummy tayi tareda cewa haba Zarah Yaya kike Neman ja da hukuncin ubangiji, kinmanta yafiki son IBBY? Kinmanta shine ya hada xuciyoyinku guri guda? Xarah bakikai iyayenshi qaunarshi ba, sunyi haquri sunmiqa kamuransu ga Allah, kiyi haquri dotah nasan mantashi lokaci guda abune mai wahala, amma kidaure kisawa xuciyarki salama kodon lafiyarki ma.



Daga wannan lokacin kowa yayi shiru acikinsu kowacce da tunanin daya haddasa mata yin shirun, a bangaren Xarah tunanin Daren jiya takeyi yanda suka kwana da IBBY gado daya amma batasan ya akayi yatafi yabarta ba, batasan lokacinda rai ya fita a gangan jikinsa ba, yadaina motsi, abunda xata iya tunawa cikin dare tayi juyi taganta manne ajikinshi da wayarta a hannunsa alamar Abu yakeyi da ita, taso gani amma saiya qara maidata qirjinsa tareda cemata a kunnensa my star kiyi baccinki kodai jarabar tahanaki bacci ne, inkashe miki ita, kunya yasata yin dariya takoma ta rufe idonta tacigaba da baccinta.


Tabbas Allah buwayi be me kashewa da rayawa, Wanda baiyi imani da Xatin Allah ba yashiga uku, takwana gado daya da gawa bata saniba, masoyinta abun qaunarta mijinta yatafi yabarta a lokacinda suke neman xama daya dashi da ita.



Kuka banata bane gatan da xataiwa mijinta a yanxu daya shine addu'a, shikadai ne xatai mishi takuma dauki dangana ta dorawa xuciyarta, da wannan tunanin tayi shiru tana naxari.


A bangaren mummy kuwa kalaman Aliey ne ketayi mata yawo a cikin kwanyarta, me hakan yake nufi? Dacan yanason xarahn ne kokuma yaune 2nanin hakan yaxo Mishi? To Allah ya xabar da mafi alheri.


Da asuba Xarah da kanta tamiqe lokacin mummy bacci yadauketa, tashinta tayi tasanar da ita Asuba yayi, snn tawuce bathroom ta dauro alwala ta dawo ta tada sallah, bayan ta idar tajima tana addu'a ga mijinta Wanda a qarshen addu'an kukane yaci qarfinta agurin datai sallahn a gurin ta kwanta tana kallon sama, ahaka bacci barawo ya saceta.


Har isowan su humairah bata saniba, mummy takarbi wayan taboyeshi domin karta gani balle wani abub yaqara damunta, gari yanayin haske asibitin yafara cika da'yan dubiya, anan ne tafarka, ganin mutane dayawa yasa xuciyarta qara karyewa amma tunawa datayi da alqawarin da taiwa kanta na cewar xatayi juriya kamar yandai taiwa mijinta alqawari yasata shanye kukan da ke shirin kwace mata.


Kowacce dama kapin xuwansu saida daddy yayi gargadin cewa dukpa Wanda yasan xaiyi kuka a gurin Xarah to karma yaje, domin yanxu kwanciyar hankalinta akeso dakuma walwalanta kodon lafiyarta dake baraxana da rayuwarta.


Kowa burinshi ya faranta mata, ganin hakan yasata Dan fara sakin jiki dasu, hartanayin magana jefi jefi a cikin hiransu, Dago ido tayi ganin shigowan daddy nan ta shagwabe fuska tace daddy.


Qarasowa gurinta yayi cikin sauri domin jin mexata gaya mishi, yana xuwa tace daddy xanci abinci dariya 'yan dakin sukai mata mummy tace lallai munga wariya dukanmu nan bamukai mubaki abinci ba saida daddynki yaxo? Ko kallonsu daddy baiyi ba yasa humairah dake xaune gefen xarahn taxuba Mishi abinci a plate, snn yasa ta hada tea dakanshi yake bata itakuma tana karba tanaci ahankali kamar bataso, dariya aketa musu, abundai gwanin sha'awah.


Tanacin abincin tace daddy nikam nagaji da asibitinnan mukoma gida, xamu koma gida amma saikinyi min alqawarin xaki kwantar da hankalinki ki rage damuwa snn kifara walwala, murmushin takaici tayi snn tace xanyi qoqari insha Allah, yauwa dotah albushirinki goro tace tana kallon 'yan dakin tanai musu dariya da gwalo.


Nabiya miki hajji insha Allah hajjin wannan shekaran dake xa'ayi, batasan lokacinda ta miqe tsaye kamar wacce takeda isashshen lafiya, tama mantada yawan mutanen dake cikin dakin, ta Dane jikin daddynta don tsantsan farin ciki.



Dariya akaitayi a dakin daga qarshe Abba yace mudai yau muna kallo, muryan Abba dataji yasata sakin daddy takoma jikin mummy tarufe fuskarta, futa sukayi suka karbi sallama snn suka dunguma xua gida.


Haka dai ranakun suka cigaba da tafiya inda kowa da hanyar dayake fuskantar tasji qalubalen rayuwan, a fannin Xarah shirye shiryen tafiyarsu aketayi ita da mummy da dakuma Aliey Wanda shine yace yanason ayi tafiyar dashi.

Anmaida auren Bbn Nqnah da mamanta, Inda daddy yabasu gida, daga daya dagacikin gidajenshi Wanda take cikin wannan unguwar, kowa yayi farinciki da irin karamcin daddy.



A bangaren gidansu Nanah kuma Isah ya roqi alfarman xaije garinsu domin dubo mahaifiyashi, inda shima Baban nanah ya shirya musu tafiya garin jibia domin suje ga danginsa ya roqi abashi Xarah suje tare kapin tafiyarta makka yatashi,


Haka suka shirya tafiyarsu gaba daya a washe garin ranar.



&&&&&&&&&&&&&&


Haka taketa rayuwa acikin kasuwan tana kuma gujewa duk wata hanya datasan xai hadata da Altine domin bata manta da irin mugun kashedi dakuma sharuddan data gindaya mata ba.


Amma dayake hausawa sunce tsautsayi bata wuce ranarta, tana zaune tanashan hantsi da safiyar ranar a gindin wata bishiya, wanine yabata wani busashshen buredi a can bakin tasha, shine taxauna tanaci, sai qulle mata yakeyi a maqoshinta domin babu ruwa atare da ita.



Tafiya sukeyi inda Altine keta sababi akan wata ladiyo Wanda aka basu kudi su raba amma taboye naira hamsin, aiko haka altine tace wlh baxa'a raba da ita ba.


Kamar annuno mata Ayashe aiko kamar ta kife, haka tahau cangala qafarta harta iso tasameta, dunguran kayinta tayi, Ayashe tadago da fuskarta dayake cabe da quraje aiko fuskarta bai sauqa akanna kowa ba sai Lami datake tsaye gefen Altine dukta kode ta jeme.



Duk halinda Ayashe tashiga da yanayin yanda jikinta ya sauya bai hanata gane taba, Aiko nan suka hau nuna junansu, wlh dama na rantse sainayi ajalinki duk randa nayi ido hudu dake, domin kece silar fadawata duk wata halaka.



Ayashe batada qarfin aiwatar da komai, don haka tafara bawa Lami haquri, kowa agurin saiya tsaya yana kallonsu domin babu wanda yasan alaqarsu da juna, nan lami taita waige waige, can ta hango wani fasashshen kwalba da gudu ta daukoshi taiyo kan Ayashe dashi.



Yunqurin kamata sukeyi domin sunga alamar barnar data tasanma yi, amma inaa kapin sukamata ta kai wannan fasashshen kwalban akan Ayashe aiko atake kanta yafashe kwalaben suka huhhuda jikinta snn jini yafara wanke jikinta nan take.


Abunda ya raxana mutanen gurin kenan sukaiyo kan Ayashe domin taimaka mata, kapin sukai gareta tayi luu taxube agurin, nan take akahau ihu acikin kasuwan wanine acikin mazan dasukaxo ganin abunda ke faruwa, yayi shahada yadaga Ayashe yasaba akafadarshi yayi bakin hanya da ita domin Neman taimako, asamu me motar daxai kaita asibiti.



Suna isa bakin hanya Ayadhe tafara shaquwa mai qarfi a qarshe tayi wani wawan miqa nan take rai yayi halinsa, ajiyeta yayi tareda duban mutanen dasuke gurin yace dasu, saidai muyi haquri domin rai yayi halinsa.


Salati aka dauka gaba dayansu snn mabaratan dasuka San ainihin abunda ya faru suka maida subansu ga Lami Wanda tamatsa gurin gawan tana kuka tareda fadin abubuwan dasuka aikata tare batareda kowa ya tambayeta ba, gurinne yacika maqil, Wanda dandaxon mutanen ya haddasa wani gow slow, yahana mutane masu motoci wucewa yanda sukeso.



Wannan lokacin ne su Nanah suka iso gurin, ganin babu hanya a gurinne yasadu tsayuwar dole, tsaki sukeyi daya bayan daya, Isah ne yafita domin dubo abunda yake faruwa.


Haka yayita kutsa cikin al'umma harya samu ya hango abunda ya firgitashi yakuma daga mishi hankali a lokaci guda, dasauri yaqarasa gurin mahaifiyartashi ya durqusa a gurin, cikin kidima yake tambayarta meya faru?



Dagowa tayi cikin gunjin kuka tace dashi kisa nayi, nina kasheta wlh Nina kasheta, xaro idanunsa waje yayi jin abunda yafito a bakin mahaifiyar tashi.




Gajiya sukayi dajiran Isah suka fito domin dubawa, mamah CE tafara gane Lami saikuma nanah, mamah ce tace dasu ga Lami, mamakin bai gama sakin jikinsu ba sukaga 'yan tasha sunfara jifan Lami babu qaqqautawa, ruwam duwatsu kawai akeyi acikin tashan.



Isah ne yafara tarewa cikin xafin nama, amma akasamu wasu daga cikim matasan suka rirriqeshi, dakyar aka dakatar dasu a wannan lokacin sungama yimata kaca kaca, tahowa yayi gaban Alhaji yana cemishi ataimaka mishi mahaifiyarshi karta mutu.



Sata akayi acikin mita aka nufi asibiti da ita, karon farko akace batada jini, snn tana dauke da cutar HIV basuyi mamakiba jin ance tana dauke da wannan cutar.


Isah ne yabata jini akasamata snn akai mata dressing aka kaita daki inda aka kwantar da ita, shiga dakin sukayi gaba daya, kallonsu takeyi daya bayan daya, bata gane kowa acikinsu ba, amma mutane biyun da tagani na qarshe sune suka hargutsa mata tunani, Mal.Habu da zainabu idanuwanta ne sukaiyo waje tafara nunasu da yatsa tana wani irin gunji, kanagani kasan magana ne abakinta, amma baxai fito ba domin an nannade fuskar da bandeji, nan tafara daddaga qirjinta tanata gunji can takoma rigib akan gadon...........



😍😍🤝🏼Anatare
Mummyn Fadyl CE



🎲🎲TUDUN DAFAWA🎲🎲


Rubutawa....MUMMYN FADYL (Fatyma Muhammad Adamu)

Wattpad @ *fatimamuhammadadamu*


INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION*
*[onward together]*
*{we give the reader's of ours the best out of the bests,, our inks are melodious and dropping a kinda lights to reader's}*
```THE PEN OF LOVE😘 HEAT TORCHING❤ TEAR OF SORROWS😭 CURDLES😊 GIGGLES😁 AND MARRIEGE THINK💑```
*```JUST GIVE
US FOLLOW..**

*Sannu sannu bata hana xuwa saidai a Dade ba'ajeba, insha Allah munkusa kaiwa gaci.*

Fitowa ta. 7⃣2⃣



Mmn Nanah ce da isa sukai rige rigen isa gareta hannun ta mmn Nanah takama atake taji hannun yasake, innalillahi wa inna ilaihirraju'un shine abunda mmn Nanah ta furta.


Shikua Isah a hankali ya jingina da jikim bango yana karonto duk wani addu'an dayaxo bakinshi, tabbas yasan mahaifiyarshi batayi dace da rayuwa ba, Allah sarki rayuwa bayanda baiyi da itaba domin ganin yacanxa mata rayuwarta amma taqi fahimtarshi, ubangijinmu yayi gaxkiya dayace damu, shine mai shiryarwa sannan da ace duniya xasu taru suna sonka to baxasu qareka dakomai ba, sai abunda yanufeka da samu, sannan da ace duniyar data taru domin ganin ta cutar dakai tobaxasu iya yimaka komai ba sai abunda yanufeka daxai sameka.



Jikinsu ne yayi matuqar sanyi musamman Xarah Wanda komai yadawo mata sabo, gani takeyi kamar yaune IBBY yarasu yabarta, kuka takeyi Wanda yasa hankalin kowa dawowa kanta, nan aka dawo rarrashinta.



Haka aka tattare ta akayi gidan baffan Sadiya da ita, wanka akaimata akayi mata sutura aka kaita, bayan dawowansu Isah ya tsuguna a gaban Bbn Nanah yafara roqawa mahaifiyarshj yafiya domin yasan ta cutar dasu ba kadan ba.


Bbn Nanah ne yace a madadin nida iyalai na na ari bakinsu na cimana albasa, mun yafe mata dukkan abunda yashiga tsakaninmu da Wanda muka sani harma da Wanda bamu saniba, Allah ya jiqanta, haka yayita bin duk Wanda yasan yanada alaqa da mahaifiyarshi yanema mata yafiya.


Bayan sundanyi gaisuwa ne suka nufi gurin 'yan uwan Mal.habu babu abunda ya sauya acikin rayuwarsu, daddy dakuma Bbn Yasmin baqaramin Alheri sukayi a garesu ba, harma da gurin xama mai kyau, sunkuma nemi yafiyar mmn Nanah, damacan batada riqo macece ita mai haquri da kawaici, da wannan alheran suka dawo gida.



Bbn Yasmin ne yabiyawa Nanah da mamanta harma da Kuma Bbn ta aikin hajji, tabbas rayuwa kam dai tayiwa wannan xuri'ar dadi.


Shirye shiryen tafiyarsu aketayi domin yanxu suna xua bita ne, Xarah tafara dan komawa hayyacinta babu abunda ke takurata yanxu kamar wani sabon kulawa datake samu daga gurin Aliey, abun har mamaki yake bata, domin ita damacan tsakaninta dashi 'yar tsamane, babu sabo ko kadan tsakaninsu.


Shikanshi kamar a takure yake komai, gani yakeyi kamar duk abunda yakeyi IBBY na ganinshi shiyasa yake qoqarin kyautata mata kodon nauyin alqawarin daya daukawa Dan uwansa.



Samunta yayi xaune a dakinta tana jera kayanta a wardrobe, xama yayi shikanshi abun kunya take bashi domin baitaba yin qasa da muryanshi a gurin mace kamar yamda yakeyi a gurin Xarah ba.



Xarah mekikeyi? Dago idanunta tayi takalleshi murmushi ta sakar mishi snn tace kayan da aka gogemin ne nake jerawa a wardrobe, shima murmushin ne yasubuce Mishi da baisan dalilin yinta ba, yarasa meyasa a kullum yaxo gurin ta yakan tsinci kanshi cikin nishadi, saiyake ga farincikin dayake samu yafi Wanda shi yake qoqarin batan.



Rasa mexasuce sukayi dukansu biyu, sai itace dayake gwanace gurin iya magana snn tayi rayuwa da Wanda yasan yanda ake sarrafa harshe, cemishi tayi yayah kaci abinci naci yace mata.


Shagwabe fuska tayi snn tace yayah niyanxu babu Wanda yake sani agaba kamar yanda yayanah yakemin, Yaya IBBY bayacin abinci sainaci, ko ruwa sainasha yakesha, tamaida fuskarta kalan tausayi.


Kapin yace komai mamakine yafara kamashi yanda akayi Xarah ta iya shagwaba da kuma magana, ada kullum kallon marar nitsuwa da kamala yake mata,snn kuka wacce bata waye ba, amma gashi acikin 'yan watanni yafara Sanin ainihin Xarah.



A daburce yace mata to bar kayan kibiyoni dakina muci tare, xaro idanu tayi waje tacemishi dagaxke kake? I mean it, haka tamiqe tabar kayan fa biyoshi suka jera sai hira takemishi amma baya cewa komai saidai tayi dariya domin bai saba da yawan magana ba, a ranshi yace lallai IBBY yayi qoqari da wannan yarinyar.




Qarasawa dakinshi sukayi xama tayi a qasa, amma yace mata ta tashi dakanshi ya shimfida mata darduma taxauna, xuba mata abincin yayi a plate yace taci, fara cin abincin tayi can tadago ta dubeshi tace yayah, amsa mata yayi da Xarah.



Murmushi tayi mishi snn tace kabani labarin yayah ibby, lokacinda kuke makaranta, suwaye 'yan matanshi kallonta yayi dakyau snn yace IBBY baitaba son wata 'ya mace a rayuwarsa kamar keba, baya kula kowa a dalilinki, shifa cewa yayi baya yiwa matan kallon mata saboda ke Kadai yake yima kallon isashshiyar mace.



Dariya tayi mekyau kapin daga baya idanunta ya sauya Yakuma tara hawaye tace shknn yanxu kam! Narasa masoyin gaxkiya waxai soni? Waye xansamu daxai kwatanta min irin soyayyar da ya IBBY yakemin? Allah sarki mijina Allah yakai haske kabarinka, ya inganta makwancin ka, jiya nayi mafarkinshi yacemin indaina kuka



Shikanshi xuciyarsa a karye take, amma ya daure yace Xarah wannan rashin bake Kadai akayiwa ba, IBBY Dan uwane a gareni aboki nagari snn kuma Amini ne agareni Ibrahim kamar yasan xai bar duniya yayita yimin magana mai kama da wasiyya, xaro idanu waje tayi snn tace kaima yayita yimaka surutai na bankwana ko?



Kwashe irin labarai daaganganun da yayita yimata tayi tasanar da Aliey, haka shima yasanar da ita dukkan yanda sukayi harma da text dinda yaturo mishi, sai a wannan lokacin ta tuno da wayarta Wanda tun bayan dawowarta daga asibiti take roqon abata amma mummy taqi.



Yayah ka karbamin wayata a gurin mummy, nima akwai saqon da Yaya IBBY ya barmin inason dubawa kuma taqi bani, yace mata nima nagoyi bayan karta baki domin babu abunda hakan xai haifar face wani sabon tashin hankalin , bayan Alhmdllh ansamu kin warware. Saqon inaji ajikina kusan iri dayane shidai burinshi a samu mai riqe xarahn shi.



Kuma yabarmin amanarki amma bansan tayaya xan iya taimakonshi ta wannan fannin ba, yahadani da nauyi, duk abunda yake fadi idanuwanta na kanshi, bakadan ba yake bata mamaki da irin sauyin datake gani a taredashi.



Narasa yaxanyi da wannan nauyin kinaga xaki iya taimakona gurin ganin nasauke nauyin masoyinki? Bangane mekake nufi ba yayah, ina nufin xaki amince ki aure ni?



Gabanta ne ya yanke yafadi, xuciyarta tahau yin sama da qasa a take, takasa kallonshi dakyar tabudi bakinta tace tayaya xan auri mutuminda baya sonah, tayaya xan kwatanta iya rayuwar aure dashi? Ko kanasona?



Kasa bata amsa yayi domin gani yake hakan xai iya xamowa raini agareshi, bayason taji a ranta cewar itadin watace, yayah kabani amsa kansona? Kai tsaye batare da tunanin komai ba yace banasonki Xarah amma inaga xan iya taimakonki in aureki domin cika alqawarin mijinki.



Jitayi ranta yabaci wato batakai matsayinda shixai sota ba saidai taimako? To wlh baxata tabayin auren taimako ba.



Atake itama taxare duk wata kunya da girman shi datake gani, ta dago ta kalleshi tace kayi haquri yayah wlh baxan tabayin auren taimako ba, domin xuciyata da soyayya ta rayu takuma ginu, tayay kake ganin xata iya karban soyayyar alfarma? Xan aureka xuwa duk lokacinda kaga xaka iya aurena a matakin qauna, tana gama fadin haka tamiqe batareda ta saurareshi ba tabar mishi dakin, ganata kiranta amma taqi sauraronshi, dafe kanshi yayi tareda jin takacin abunda ya aikata.



Tana USA dakinta tafada kan gado tafashe da kuka, kukan takaicin abunda Aliey yayi mata, kukan rashin ibby, Wanda da ace yananan atake xata Samar mishi yakuma kwantar mata da hankali, inma bata amince ba yarama mata a take.



Miqewa tayi kamar ana hankada ta tanufi dakin mummy, sanunta tayi shine fiyowarta daga bathroom aiko nan ta fashe mata da kuka said a tayi me isarta mummy tanata aikin rarrashinta, dakyar ta sassauta kukanta snn tasanar da ita abunda Aliey yayi mata.



Murmushi mummy tayi tace mata kikwantar da hankalinki dotah kuma naji dadin amsar da kika bashi, wlh kinfi qarfin auren alfarma inason kifita harkanshi ninan nagane manufarshi babu kuma mai taimaka mishi harsai yasauqo daga wannan dokin daya hau, yafadi gaxkiyar xuciyarshi, kici gaba da addu'a inkinje Makkah kiyta roqon Allah yaxaba mini abunda yafi alheri kinji?



Tahi dadin kalaman mummy haryasata jin xuciyarta tayi wasai hiransy suka cigaba dayi har mummy tace mata tashirya xasuje sugaida mamanta domin tun bayan dawowansu daga jibiya batajeba.



Takuma fahimci iyayen xarahn suna buqatarta a kusa dasu amma iya dayake bata saba dasuba bata sha'awan xuwa.



Haka sukaita shirinsu Inda Xarah tafara wasan buya da Aliey, duk hanyar datasan xai sadata dashi ta tosheshi, bata yarda taxauna a dakinta matsawar tadan yana gudan domin xai iya rutsata acan, inkuma sun hadu a dakin mummy bayanda ya isa yayi mata wani magana, saidai kallo, yagama qudirawa aransa yasan ta inda xai kamata.



A yaune jirginsu ya daga xua gari mai tsarki......


_Allah yabada sa'a, ayi ibada lpy_




😍😍🤝Anatare
Mummyn Fadyl CE




🎲🎲TUDUN DAFAWA🎲🎲


Rubutawa....MUMMYN FADYL (Fatyma Muhammad Adamu)

Wattpad @ *fatimamuhammadadamu*


INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION*
*[onward together]*
*{we give the reader's of ours the best out of the bests,, our inks are melodious and dropping a kinda lights to reader's}*
```THE PEN OF LOVE😘 HEAT TORCHING❤ TEAR OF SORROWS😭 CURDLES😊 GIGGLES😁 AND MARRIEGE THINK💑```
*```JUST GIVE US FOLLOW..**



Fitowa ta. *QARSHE* (7⃣3⃣)

~Bayan Shekara biyu~


kuka takeyi a kan gadon kamar ranta xaifita bawai ranar ce batasoba ko ko dokin sa ba, abubuwa ne suke yawo suka kuma cukurkude mata acikin xuciyarta Wanda takejin tarasa yanda xatayi dasu.



Bayan shigowarsa yarufe ko ina snn yanufi cikin dakinda yakeda tabbacin tana cikinsa, sheshsheqar kukanta sune suka amsa mishi sallamar daya shigo da ita a bakinsa, dasauri ya ajiye ledar daya shigo da ita a hannunsa yaqaraso an yahau kan gadon, mayafin data rufa dashine ya janye ganin yanda take kuka bilhaqqi ne yasashi rudewa a take ya janyota jikinsa, rarrashinta ya farayi kamar jaririyar da uwarta tahanata nono amma kukan yaqi sakinta, ita kanta sotake ta tsayar da kukan, amma damar yin hakan ya gagareta.


Ganin kukan nata bamai tsayawa bane, ann shikuma xyciyarsa baxata iya daukaba, domin jiyake kamar ana xuba mishi ruwan dalma acikin xuciyarsa a duk lokacin sauqan digon hawayenta.


Harcensa ya tura acikin bakinta yafara sarrafashi yanda kukan nata yatsaya cak batareda tasan lokacin faruwan hakan ba, bai tsaya anan ba yacigaba da lailaya ta, gaba dayansu suka fara Neman ficewa a hayyacinsu itane tafara kwatan kanta dasauri, tareda lumshe idanuwanta, takoma gefe, binta yayi yakuma jawota cikin sexy voice yake tambayarta meya sata kuka haka a wannan ranar farinciki haka a garesu?



Xaman danayi akan gadonnan a matsayin matarka shine yasani tunowa da ranar da nake xaune akan gadon Yaya IBBY, ina qaoqarin mantawa da wannan ranar amma samun hakan ya faskara a gareni.



Rana tafarko daya farajin kishin IBBY akan Xarah, tayaya ma xa'ayi yana tare da ita tadinga tunowa da wani akan gadonshi tana kuma matsayin mallakinsa, lallai yaxama dole yayiwa tufkar hanci.


Juya mata baya yayi cikin bacin rai snn yafara magana, Xarah yafada cikin kakkausan murya Wanda ya raxana ta, domin kuwa Yakoma mata asalin Aliey nshi.


Matuqar kinason muyi xama dake cikin faranta ran juna toyaxama dole kicire IBBY a cikin xuciyarki, kinsan dai mutuwa dayace idan antafi ba'a dawowa kuma IBBY dai yatafi, nine yanxu mijinki, yafada batareda ya juyo ba.


Mamakine yakamata domin ko a mafarki batayi tsammanin Aliey xaiyi kishi da IBBY ba, Wanda yake matsayin gawa a qarqashin qasa, ba shakka akwai aiki a gabanta, share guntun hawayen da yaxubo mata tayi ta rarrafa ta rungumo shi tabaya tace.



Mijina kayimin afuwa insha Allah baxan qara kawo maka makamancin magana irin wannan ba, a yanxu banida burin daya wuce murayu tare nidakai, ka sassauta fushinka a gareni xuciyata marainiya ce kataimaketa ka rarrasheta nima nayi alqawarin tallafan xuciyarka da hannu bibbiyu.



Baisan lokacinda ya juya ya rungumota ba shima, kissing dinta yayi a goshinta snn yace, zarah karkiyi tunanin komai akan qaunar da nake miki, INA kishinki fiye da tunaninki, shiyasa nakeson in kasance a cikin xuciyarki ni kadai, banadon kihadani da kowa gurin tunaninki, bansan tayaya xan sanar dake wnn sirrin xuciyar nawa ba, amma zarah nafara qaunarki tun lokacin dawowar mu daga makaranta, ganin baxan sameki ba, domin kuwa baxan tana shiga cikin soyayyar da aka ginata shekaru dayawa ba, inada tabbacin idan na nuna ina qaunarki ba shakka Ibrahim xai iya sadaukarmin ke, amma nakasa saboda halaccin dake tsakaninmu.



Amma kinga dayake ke Tawace Allah yadauki kayanshi nikuma nasameki, murmushi sukayi dukansu biyu, Wanda ita acikin ranta haryanxu tanajin IBBY bana wasa ba, amma xata daure tacireshi don kua gaxkiyar Aliey ba xai dawoba har abada.



Saida suka gabatar da komai na Addinance harma Dana al'adance, snn suka kwanta, janyota yayi jikinshi, yace mata Xarah kisanar dani iyakan gaxkiyarki akwai abunda yashiga tsakaninki da IBBY a first night dinku? Muryanta na rawa tace mishi babu komai.



Jindadi yayi domin yasamu damar mllakan xuciyarta cikin sauqi, wani salo yafara gwada mata mai wuyar fassarawa tun ba'aje ko inaba ta tabbatar cewa Aliey jarumin namiji ne ba malalaci bane.



Labarinne ya canxa, bashiri nafita nabar musu dakin domin abunnasu ya girmewa tunanina balle nai tunanin dauko muku rahoto, don haka najawo musu qofa na rufe.

_Asha luv dakyau, Team Aliey Ku gargadeshi yabi 'yar mutane a hankali_ atohh



Kamar a mafarki da asussuban fari domin shine anfara kiran salla nafarko a masallatai, farkawa tayi tafara laluban Aliey, bata jishi akan gadon ba, bashiri ta washe idanunta, wayarta ta haska can tabhangoshi akan darduma yana ta sallolinsa, sauqowq tayi a hankali domin gaba daya mijinta ciwo yake mata, xama tayi kusa dashi harya sallame.


Juyowa yayi ya kalleta yace priceless kin tashi? Yamutsa fuska tayi snn tafara magana kamar mai shirin kecewa da kuka, yayah mafarki nayi wai kaima ina farkawa xan samu kaima rasu, murmushi yayi snn yace karki damu sharrin mafarkine, mijinki yananan xaki rayu Ku hayayyafa tare.


Dariya tai mishi yace tashi muje intaimaka miki kiyi wanka kiyi sallah, maqe kafada tayi tace a'ah nikam xan iya, saida yabari tafara tafiya snn yace badai kunya kikeji ba? Kodai intuna miki irin ihun dadi dakuma cakumoni dakikai tayi jiyane? Wlh banaso tafadi tare da shigewa bayin dasauri.



Qarfe Tara nasafe kamar rige rigen kai musu abinci akeyi domin kuwa lokaci daya ka aiko da abincin gidan mummy da Ummy, domin kusan kwanan fargaba sukayi.



*Bayan Shekara Daya*



Mijina wata alfarma nake nema agareka kokuma ince inason katayani ne gurin sauqe nauyin abunda yake kaina, Kallonta yayi da sha'awa domin gani yake kullum kamar kullum qara gyarata akeyi haihuwa tayi amma babu abunda ya sauya na halittar ta, inajinki yace da ita.



Marigayi yacemin naimishi alqawarin haihuwana na fari, idanna samu da namiji xanyi Mishi takwara, nakuma amsa domin bantaba kawowa a raina xanyi rayuwa da wani bayanshiba, shiyasa nake Neman alfarmanka, ta kai qarshen xancenta da kashe Mishi ido daya, Wanda yajishi harcikin kowani kusurwa na gashin jikinsa, Yakuma haddasar mishi da kasala atake.




Cikin sanyin Jikk domin

Please Login or Register in order to submit comment