You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da fara'a, bai amsaba sai cemata yayi yanaga yau kuma kinyi min yarinya danya shakaf kamar yau aka kawomin ke?


Dariya sukayi gabadayan su, itakuma tace mishi nima saikai min kamada randa kafara xua qofar gidanmu xance, haka sukaita tsokanar juna har suka kammala cin abincinsu.


Haka rayuwar gidannasu taci gaba da wakana cikin farantawa juna rai, mijin su tanabakim qoqarin yin adalci a tsakaninsu, inda haj.maryam ma tana iya bakin qoqarinta a matsayinta na babba don ganin gidan ya dai daita.


A bangaren Nana ita harta rasa Wanda xata fara ambata a farko gurin nuna kyautatawa agareta, inda ace tana cikin iyayenta tahadu da wnn gatan topa xata iya cewa itakam tagama yin dace da duniya, to amma a kullum idan ta tuno da iyayenta jinta takeyi ta manta da duk wani jin dadin rayuwa datake ciki.


Zarah CE kwance akan cinyar mummy tanai mata kalaba snn tana kuma bata labarin wayar da sukai da IBBY jiya da dare, domin akwai shaquwa me qarfi tsakaninsu, snn ta sake mata yanda tashiga jikinta yanda bata iya boye mata komai na rayuwar ta, bana Kadan ba mummy tanajin dadin hakan, domin tanan takesamun yi mata gyara gameda al'amuranta.


Wlh mummy jiya hiranmu yayi dadi, mummy baxaki gane bane Yaya IBBY na sona, ikon Allah nikam damacan bance miki inason ganewa ba, dariya tai mata tace hummm mummy inason Yaya IBBY, don Allah mummy kiyarda in aureshi riqe baki tayi tareda daka mata dukan wasa snn tace lallai IBBY can kirashi xai gamu dani, tunda yafara rarraba mini tunani.


Ai dasauri tamiqe tareda Cuban Maman nata tace, wayyo mummy karki yimishi fada wlh banason ranshi ya baci, kuma kinga yana karatu, korata daki tayi tace tashi kibani guri inyi jimamin rashin kunyar ki kapin anjima insane mexanyi akanki kedashi..

Dariya zarah tayi tadauki dankwalinta tayi dakin daddyn ta.


*BAYAN SHEKARA UKU*


IBBY zaune suna hira saiga wani abokinsu sabon xua ne domin shi harya fara hada PHD dinshi, amma dai guru data suke xaune gabadayan su, hira sukeyi sosai sunashan dariya,banda Aliey dayake can gefe yanafama da wayarshi Inda yake chrtn da budurwarshi siyama, 'yar class dinsu ce Tun farkon shigowarshi makarantar sukafara soyayya domin yanayinta yayi daidai da zabin Aliey.


Hiran su na duniya sukeyi har dai suka sauko kan labarin masu matsalar kwakwalwa aiko kamar an tsikari Ibby yafara tambayar Sudais shin yanada masaniya akan matsalar ne?

Amsa yabashi da.............




😍😍🤝🏼Anatare
Mummyn Fadyl CE





🎲🎲TUDUN DAFAWA🎲🎲


Rubutawa....MUMMYN FADYL (Fatyma Muhammad Adamu)

Wattpad @ *fatimamuhammadadamu*


INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION*
*[onward together]*
*{we give the reader's of ours the best out of the bests,, our inks are melodious and dropping a kinda lights to reader's}*
```THE PEN OF LOVE😘 HEAT TORCHING❤ TEAR OF SORROWS😭 CURDLES😊 GIGGLES😁 AND MARRIEGE THINK💑```
*```JUST GIVE US FOLLOW..**


_Masu qorafo akan warkewar xainab kuymin haquri saura qiris in faranta muku Rai kamar yanda kuke qoqarin faranta min nawa ran, andai kusa akai gaci insha Allah, addu'arku gareni shine linxamina_

Fitowa ta. 5⃣0⃣



Amsa yabashi da cewa Niko nasan hakan tunda mahaifina malamine ta fannin addini snn kuma babban psychiatric Doctor ne, aiko kamar an tsikare shi yataso daga maxauninsa yamatso kusa da sudais, har abokansa sunayi mishi dariya, bai bi takansu ba.


Shikua Aliey duk abunda sukeyi yanajinsu ganin yanda IBBY yazabura yasan dama abunda yake jira kenan, shiko abun haushima yabashi yadanna tsuka kamar mace yatashi yanar gurin, gabadayansu binshi sukayi da idanu banda IBBY Wanda shiyasan dalilin Alieyn yin hakan, baitsaya bata lokacinsa gurin bitakanshi ba yamaida hankalinsa kacokan akan sudais.


Kagane Sudais wlh inada patient wlh tabaiwa shekara goma baya tana fama da wnn cutar tun ana maganin a 9ja har baban asibitin mahaukata dake Egypt ankaita, amma wlh abun kamar ma gaba yakeyi.


Ikon Allah shine abunda yafara fitowa daga bakin sudais snn yacigaba da cewa amma kuntaba gwada maganin mu na gida? Eh to gaxkiya dai wnn ne bansaniba amma xan tambaya.

Karka damu mubi komai a hankali Yanxu haka Baban nawa baya gida amma next month insha Allah zai dawo yana dawowa sai musan yanda xa'ayi,

Ibby ne yace yauwa kaga kua yayi dai~dai da lokacin da xanje gida, kasan Allah jina nakeyi kamar akan qaya nake, naqosa inga zarah na, murmushi sudais yayi mishi snn yace mishi na zarah bada kanka a sare kaje gida kace yafadi, dariya yayi mishi snn yace nabaka sarkin makka koda nayanxu baiyi murabus ba.

Haka sukaita tattaunawa akan matsalar har magriba ya cimmusu agurin, suka miqe suka nufi masallaci domin gabatar da sallah.


Bayan sun idar ne yadawo dakinsu yasamu Aliey a kwance yana hira da siyama idan ka kalleshi baxaka tantance yanayin da yake ciki kai tsaye ba, shidai yarasa Aliey wace iriyar dabi'a yakedashi, *Siyaman* ma dayake qauna kenan , bakullum take samunshi yanda ranta yakeso ba.

Don yawancin lokuta da dama takan kawo kukanta gurin IBBY akan wulaqancin dayake gurza mata, shidai nashi yabata haquri. Qafar Alieyn ya shure da nashi qafar, shikuma yawani juyo kamar xai cinyeshi danye yace menene?

Inason tabbatar maka da cewa insha Allah nakusa mallakar rising star dina, domin kua ina gab da nemo mafita akan al'amarin mahaifiyarta, tsaki yayi snn yace mishi matsalarka, yajuya yaci gaba da wayarsa.


Wanka yashiga yasakar ma kansa ruwa, cikin farin ciki yake wankan jiyakeyi kamar harma ansamu mafitan wankan yakeyi yana bin waqar zarah na Nura m.inuwa yanayi ne kuma domin yabawa Aliey takaici , tunowa dayayi da star dinsa cikin Sauri yakammala wankan yafito daure da towel, gani yayi dakin wayam Alamar Alieyn yafita, yasan takaicinsa ne yasashi ficewa daga dakin.


Aiko cikin jin dadi yamiqa hannu yadau wayansa yadanna mata kira ta wayan mummy shidai wnn abun yana bashi takaici ace yarinya tana SS2 amma anhanata riqe waya, wai dole saita kammala?


Haka watarana xaigama kwaso labbari mai zafin da xai bata, amma saiya kira yasamu ba ita bace, gashi ita mummy tahanata bude duk wani kafafen sada xumunta a yanar gixo balle yadinga ganin picx dinta, haka suke haquri suyta exchanging ta E-mail.


Kiran har yakusan tsinkewa snn mai aikin tai saurin miqa wa mummy datake kitchen, ganin me kiran yasata yin murmushi snn ta daga, batai magana ba hakan yasashi tinanin ko zaran nashine, aiko sai yace _Rising star_ cikin wani salon murya jin hakan aiko dasuri mummy tace wannan Maman tauraruwar ce! Ai kyatt yakashe wayar cikin kunya, dariya tayi snn tanufi dakin Zara.


Tana shiga tasameta a gaban mirror anata fente fenten fuska, Rising star juyowa tayi dasauri jin an ambaceta da sunanda mutum dayane ke kiranta dashi, mummy ai kin yankar min da zuciya tafada a shagwabe, ai saikiy hanzarin tattaro shi ki dinke, tafadi hakan tareda ajiye mata wayar a gefenta...


Mummy gidan Aunty Amarya fa xamuje nida humairah, nidai ina mamakin wannan shaquwa dakikai da Amaryan nan, bakida labari sai nata Dana danta, wlh mummy matar tanada kirki ne, bugu da qari kuma jinina yahadu da nata, baxaki taba xua gidannasu kitafi batareda kindau darasi azamantakewar datakeyi itada Haj.qarama ba.


To Indai kinje karki jima, kinsan daddyn Ku baicika son yawan fitan nan nakiba, insha Allah tafadawa Maman nata cikin dariya domin wayar data fara ringing a hannunta itadai mummy dariya tayi tai ficewarta a dakin ma gabaki daya.


Zama tayi akan gadon nata ta janyo pillow guda daya tadaura shi akan cinyarta, takuma jingina jikinta da saman gadon snn ta Amsa wayar

_Hello my paramour_ shine abunda tafara fadi mishi Inda a dayan bangaren ya Amsa mata da _hyy my star_ dariya sukai dukansu biyun snn suka fara gaisawa cikij so da qaunar juna can dai yace mata Albishirinki my star! Goro inafatan abunda xaka sanar dani yanada babban alaqa da tarayyar mu, shikadai ne nakeda yaqinin xai iya zamowa Albishir mafi girman da nakeson ji akowani lokaci.


To gaxkiya bashi bane, tsuke fuska tayi don sanin halinsa datayi bayanda xa'ai yasanar da it a labari kai tsaye batare da yaja mata rai ta hanyar tsokanar ta ba.


Yakuma naji kinyi shiru kodai inkatse kiranne yau bakyason jin muryata? Nidai bance ba tafada mishi cikin muryar shagwaba, to indai kinason jin muryata saikin min dariya Wanda xan iya jinshi yanabin duk wata jijiya dake cikin sassan jikina, shiru yayi yana sauraronta, itanma shiru taimishi, hakan yasashi cemata xan kashe wayata...


To ai Kaine baka bani dariyan ba, bari inbaki labarin wata budurwan abokinmu dataxo dakinmu kawo mishi ziyara, kinsan meya faru? A'ah tace mishi.


Ina irin dinkinku nayanxu dakuke sawa Wai breast cup ko? Qin amsa mishi tayi, baikula dahakan ba domin damacan yasan bataxa iya amsa wnn ba, don haka yacigaba da bayaninsa.

To ingaya miki tashawo matsunta ko brexia bata saba, rufe idonta tayi kamar yana gabanta, tsabar kunyan maganar da yafada dakuma Wanda take hasashen xai iya fada a gaba.

Tazo tsakiyar dakin sai wayarta yafadi qasa, gashi babu mayafi ajikinta, aiko tana duqawa domin daukan wayarta kinsan meya faru? Nanma batace mishi komai ba, INA gayamiki my star, tsugunawar da xatai domin dago wayarta aiko nan nonuwanta suka fito daga cikin Rigan dukansu biyu, wayyo tafada daqarfi kamar yana kallonta, tai cilli dawayarta ga tausayin matar gakuma dariya dayaci qarfinta.


Dariyanta takeyi bilhaqqi shima yana tayata, sunshare tsawon mintuna suka ta dariyarsu, can dai ta tsuke fuska sakamokon..............



😍😍🤝🏼Anatare
Mummyn Fadyl CE



🎲🎲TUDUN DAFAWA🎲🎲


Rubutawa....MUMMYN FADYL (Fatyma Muhammad Adamu)

Wattpad @ *fatimamuhammadadamu*


INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION*
*[onward together]*
*{we give the reader's of ours the best out of the bests,, our inks are melodious and dropping a kinda lights to reader's}*
```THE PEN OF LOVE😘 HEAT TORCHING❤ TEAR OF SORROWS😭 CURDLES😊 GIGGLES😁 AND MARRIEGE THINK💑```
*```JUST GIVE US FOLLOW..**


_ADDU'OIN KU GARENI YANA QARAMIN QARSASHI YANA SANI FARINCIKI HARMA YANA INGIZANI HAR NAKEJIN KAMAR IN KYAUTAR MUKU DA WAYATA_😉😉😜




Fitowa ta. 5⃣1⃣


Can dai ta tsuke fuskarta sakamakon wani kifiyar kishi data soketa harma tarasa yanda xatai dashi, shiko jinta daina dariyan ne yasashi saurin tambayar ta, _star_ menene? _My star are you dere_ yaduba wayar tashi batai hanging call din ba snn bata amsa mishi ba.


Kamar daga sama yaji ta fashe mishi da kuka, nanko IBBY ya rude yayi ta aikin rarrashi dakyar yasamu yashawo kanta tai shiru snn yatambayeta meya faru?


Cikin muryan shagwaba tafara ce mishi bakaine ka kalli jikin budurwan abokinka ba, ai baisan lokacinda dariya ta subuce mishi ba, ammai yayi saurin guntsewa saboda yasan xai qara ballo ma kanshi wani liqin.


Cikin maqale murya kamar maiyin rada yace da ita _my star_ ummm kawai tace dashi, yanda nakejin kishinki a raina haka nake tayaki kishin kaina, baxan iya kallon jikin wata ba bayan naki, ke kadai ce a cikin raina, jikinki kadai nake ji da kuma gani amatsayin jiki, idanna tuna da jikinki nakan ji inkuma kalli jikin kowacce mace bayan naki a matsayin jikin Dan uwa na namiji.


Kisa a ranki jikinki kadai nake mararin kallo zarah inamiki so Wanda nikaina bansan adadin yawansa ba, sonda Nike miki zarah _is beyond expectation_ , banida burinda yawuce inganni a tare dake, badon iyayena ba zarah Dana ajiye wnn bokon naxo gareki, duk da hausawa sunce Aski inyaxo gaban gosji yafi zafi, wata dayan nan daya ragemin jinake kamar yau naxo qasar my star.


Da irin wadannan dadadan kalaman yayi ta amfani haryaga tasaki ranta, itakua a nata bangaren tunda yafara zubamata narkakkun kalamai zaman ya gagareta nan tazame takwanta tareda janyo dayan pillown tai matashi dashi.


Bayan yagama rikitata da labarai masu narkar da xuciyar masoyi ne, snn tabuqaci yabata labarin albishir dinda xai gaya matan.


Sanar mata yayi da cewa yakusan samo mafita akan matar da mummy tace duk Wanda ya warkar da ita xata bashi auren zarah, cikin zumudi ta tambayeshi ya akayi?


Bai boye mata komai ba, yasanar da ita yanda sukayi da abokinshi snn ya tabbatar mata da cewa next month xasu dawo insha Allah, aiko nan tabuga tsallenta akan gadon snn tahau xubamishi labarin irin tarban da xata tanadar mishi, nan shikuma yagaya mata irin abunda yakeso tai mishi a ranar ciki kua harda kalan kayanda yakeda buqatan tasa a ranar.


Sun share zamani guda suna wayar daga qarshe sukai sallama badon sungaji ba, xuciyarta fal da Annashuwa tamiqe ta qarasa shirinta ta fito, samun mummy tayi zaune a falo tana kallo sallama tai mata itakuma taimata a dawo lpy tareda gargadin kar awuce 4pm.


Gidansu humairah tashiga, ta tarar da Ummy batanan tashiga makwafta, hakan itama takeso domin tunda Ummy tafahimci akwai soyayya tsakaninta da IBBY gaba daya tadaina sakewa da ita, duk yawan surutun ta tana tsintan Kanta da nutsuwa indai a gabanta ne.


Dakin humairah tawuce tasameta tana waya da saurayinta, don itama har ta kammala shirinta ganin zarahn baisa ta tsagaita da wayar ba, saima qara narkar da muryanta tayi tanata zuba mishi shagwaba, shiko sai aikin biye mata yakeyi.


Aqarshe Xarah ce tagaji da jiranta ta fizge wayar a hannunta ta kara akunnenta tace dashi plx kayi haquri xamuje anguwa ne later, takatse kiran.

Humairah ce tabita da harara tareda yin tsaki tamiqe daga kan gadon tareda cemata banxa kinyiwa kanki wlh anjima xai fita damu shopping, amma tunda kikai mishi iskanci wlh baxaki ba, dariya zarah tayi tamatso gurin humairah ta dafa kafadar ta snn tace yarinya kin kusa kidaina min rowan da gorin saurayi, ninawa me kankat nema daura wata daya yadawo gareni, snn ina tabbatar miki idan yadawo baxan wuce watanni biyu a gaba batareda igiyarsa a kaina ba.


Da sakakken baki humaira ke binta da kallo domin bata gane manufarta ba, ganin tanayi mata kallon rashin fahimta yasata janyota suka xauna abakin gado ta fayyace mata komai dasuke ciki itada IBBY.


Humairah tayi farinciki harma tarasa yanda xata misaltashi, Xarah tamiqe tana taku daya bayan daya tana girgixa duk wani sashe na jikinta tajuya gaba da baya snn tace, kifara biyayya don wlh mijina yana dawowa bani babu wasa dake, don kuwa naxama yayarki, kekuma kinxama qanwata humairah na tausaya miki xakisha aiki a gidannan, humairah ce takawo mata duka itakuma ta goce suka hau dariya.


Direban gidansu humairah ne yakaisu har gidan Nana, shigansu suka samu Mal.Habu xaune yanata fama da ciwon qafafu sakamakon ciwon hawan Jini dakuma ciwon sugar data kamashi.


Hakan yasa bakowani lokaci yake iya fitowa waje yaxauna ba,yanxun ma Dan uwan nasa yatafi aika wa Haj.Amarya ce data aiko me aikinta a bashi saqon aikan.

Sunyi horn yafi say biyar, dakyar yasamu yaja qafafun nashi duk da kua tarin xogin dayake azabtua dashi ta dalilin ciwon, Xarah ko a cikin Mota tagama cika tayj famm da ita saura qiris ta fashe, jira kawai takeyi abude Taiwa mai gadon kaca kaca.


Amma me yana budewa taga tsohon a gefe yana dingisa qafansa, Wanda dagani kasan qarfin hali kawai yakeyi, jitayi baxata iya yin masifar data fito da niyyar yimishin ba, saima jin wani tausayinshi tayi ya shigeta farat daya.


Humaira nayi mata magana Sam bata kulaba, domin tayi gaba isa gurinshi tayi alokacinda idanunsu ya sarqu Dana juna, gaba dayansu biyun saida tsikar jikinsu yatashi batareda sun shiryawa hakan ba.


Sannu Baba shine abunda yafito daga bakinta cikin raunananniyar murya, yauwa sannu 'Yata yafada yaname kallonta kallon da ake kirada kallon qurilla.


Tama rasa meya kawota mekuma takeson sanar dashi, hakan yasata fakaicewa da ce mishi Baba qafarka ne yake ciwo? 'Yata qafata ke ciwo yafada yanayi mata murmushi tareda jin wani Abu ya sokeshi dabai San daga ina abun yakeba.


Tsintar kanshi yayi da kallonta sosai idanunshi kemishi qaryan yana hango kamanninta da Nanan shi, saurin kauda tunanin yayi a ransa tareda lallashin xuciyashi.


Hankalinsu ne yadawo jikinsu itace tafara kame~kame a qarshe tace Allah yabaka lpy, shikuma ya amsa mata da Amin, tai shigewarta cikin gidan, tana tafiya tana waiwaye kuma duk juyowanda xatayi xata samu shidinma ita yake kallo.


Side din Haj.maryam suka fara Shiga kamar kullum, sun sameta itada yasmeen axaune suna hira Yasmeen tana riqe da Muhsin tana mishi wasa.

Suna Shiga Xarah tanufi Yasmin takarbi muhsin itadai yanxu inkaga taxo gidannan to saboda mutane biyu take xua daga muhsin sai mahaifiyarshi, gaisawa tayi dasu sama sama tanufi sashen Nana da muhsin a hannunta Tanata yimishi wasa shikuma yana aikin bangare mata baki.


Samun Nana tayi a zaune a falon ta tanayiwa kanta qunshin Jan lalle, suna ganin juna suka saki murmushi tareda gaisar da junansu cikin mutunta juna.


Hira sukeyi sosai da sosai inda Xarah kebawa Nana labarin ciwon qafan megadinsu, ikon Allah kumapa ko jiyama na aikeshi banga alaman qafanshi na ciwo ba, kuma daxunnan mafa na aika larai da saqona gurinshi bata gayamin baida lpy ba, to gaxkiya kuywa Baban su Yasmin magana Asama mishi magani yaban tausayi dagani ba tambaya kasan yanashan azaba, shknn insha Allah xan sanar dashi.


Sun idar da sallan la'asar sukai haraman tafiya gida, taso tasake ganinshi amma kuma bashi tasamu a bakin aikin ba, don haka suka wuce gida kawai.


Idanta gida ta labartawa mummy labarin albishir dinda IBBY yayi mata, duk da kua ya kwabeta akan karta Dada harsai ya dawo xai yiwa mummy baxata, ai mummy kamar xatasha ruwa a qasa tasha haka takeji, itakanta tajima tana zargin akwai qullin a cikin jinyar Zainab.

Aiko yau xan sanar da daddyn Ku, mummy nikam wacece wannan matar, meye alaqar mu da ita dakowa yasamu da samun warakar ta, harkuma ake alaqanta ta da aurena?????..........



😍😍🤝Anatare
Mummyn Fadyl CE




🎲🎲TUDUN DAFAWA🎲🎲


Rubutawa....MUMMYN FADYL (Fatyma Muhammad Adamu)

Wattpad @ *fatimamuhammadadamu*


INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION*
*[onward together]*
*{we give the reader's of ours the best out of the bests,, our inks are melodious and dropping a kinda lights to reader's}*
```THE PEN OF LOVE😘 HEAT TORCHING❤ TEAR OF SORROWS😭 CURDLES😊 GIGGLES😁 AND MARRIEGE THINK💑```
*```JUST GIVE US FOLLOW..**



Fitowa ta. 5⃣2⃣




Har kuma ake alaqanta ta da aurena? Shiru mummy tayi tana kallonta nadan tsayin wasu mintuna a ranta bakomai take aiyanawa ba kamar irin ranar da xa'ace Xarah tabar hannunta, tagama jarabtuwa dason yarinyar bugu da qari gakuma shaquwa dake tsakaninsu.


Mummy xara tafada da Dan qarfi, na'am itama tafada ta kalleta da murmushi akan fuskarta, zarah mekike so insanar dake bayan abunda nake sanar dake kullum idan kin yimin irin tambayar nan.


Nagaya miki matar nan tanada matuqar muhimmacin a rayuwarmu musamman ma ke, mummy to ai kullum maganar a dunqule kike sanar min da ita, bakya fayyacemin, bana gane manufarki, dariya taimata tareda dafata tajuyar da kanta gefe saboda jin da tayi idanunta na qoqarin kawo ruwa.


Snn tadan buga kafadarta tace very soon dota insha Allah lokaci yakusa isowa da xakiji komai karki damu kinji? Nikanma mummy abun bai taba damuna ba, tafadi hakan tana miqewa tanufi dakinta, da kallon tausayawq mummy tabita har tabule tadaina ganinta, snn tasauqar da ajiyar xuciya kapin tacigaba da abunda takeyi.


A bangaren Nana kuwa dawowan mijinta sashenta hakan yabata daman yimishi maganan da zarah taimata na gameda rashin lafiyar mai gadinsu, yajinjina maganar sosai a ransa tareda cemata insha Allah xaisan yanda xa'ayi akan matsalar, da hakan sukabar xancen.


_Washe garin ranar sunfita xai kai Nana makaranta ne yayiwa maigadin magana, isowa yayi gareshi cikin ladabi yagaisa dashi, Alhajin yace mishi akace dani qafarka na ciwo?


Nisawa yayi snn yace bani bane Dan uwana ne, tare muke aikin dashi, OK ina yake? Yafada yana waige waige don ganin koxaiga Dan uwan nasa.


Alhaji ai bayanan yafita cikin unguwa domin miqe qafafunsa, Ayya yayi kyau Allah yabashi lpy, insha Allahu idan nadawo xan yi magana dashi, baxai gagara ba xa'san yanda xa'ayi, mungode Alhaji Allah yaqara girma da Arxiki, Allah yasa kafi haka, Da Amin ya amsa mishi suka wuce.


A hanya take ce mishi kasan meye Bbn Yasmin? Juyowa yayi kacokan yana kallonta dariya tayimishi snn tace a'ah tuqi fa kakeyi, shidinma dariya yamayar mata tareda kanne mata ido guda daya yace, kome nakeyi baxai hanani sauraron maganar da duk kikeda muradin sanar daniba.


Hafsat baxan iya cewa kece rayuwata ba, amma ba shakka kinacikin ta, kuma kin yamki kaso mafi girma acikinta, kinsauya ta alokacin da banyi tsammani ba, banyi tunanin hankalina xai dawo cikin gidana gabadaya lokaci qanqani ba, ke kadai kike iyawa dani, baki gajiyawa Allah yabiyaki yafada yana murxa mata yatsunta da hannun da badashi yake tuqi ba.

( _namiji Dan duniya kace maryam itace komai dinka and now Nana taxama komai naka_ 😏😏😉

Tabbas kalamansa sun ratsata fiyeda tuananin me tunani, taji dadin batunsa, cikin lankwasar da kanta tace mishi baxan iya furta komai akan alherin da kayi agareni ba, domin kamin komai bansan kalamanda xanyi amfani dashi gurin nuna godiyata agareka ba, fatana Allah yabarmu a qarqashin inuwa daya, Yakuma baka ikon kulawa dani da kuma nemamini mafita akan damuwata.

Allah yanani iko, yafada ita kuma ta amsa mishi da Amin, wlh Bbn muhsin a kwanakin nan yanda nake ji ajikina da kuma irin mafarke mafarken da nakeyi, insha Allah nakusa haduwa da ahalina, katayini da addu'an samun nasara kai dai. Addu'a a kullum knayimiki ta alheri.


Da hirarrakinsu dasukeyi cikin dadin rai harsuka isa makarantan, ajiyeta tayi tareda cemata idan Antashi xaixo, ohh baka gajiya baxaka bari direba yaxo ya maidani ba.


Xaro idanu yayi waje snn yace mata waneni? Sokike inmutu idan naganki da direba xaune Ku biyu a cikin mota? Xariyama maganar yabata hakan yasata sakankancewa tanata zuba dariyarta shikuwa ya shagala yana kallonta, can yace mata Hafsat komai naki dabanne ina qaunarki 'yar qaramar matata, dariya tai mishi ta balle murfin motar tawuce domin idan tabiye mishi baxai barta ta tafi ba, saida yadaina kallonta snn yajuya kan motar shi yatafi.


*BAYAN WATA DAYA*


Zarah ce giji giji acikin kitchen anata aiki baji babu gani harwani xufa tahada na wahala domin tahana kowa samata hannu a cikin girkinta, acewarta baxataso yadan dani komai Wanda ba hannunta ne ya sarrafashi ba.


Sai gab da azahar ta kammala komai taraba gida biyu, dayan tajereshi a falonsu domin Yaya Aliey badon halinshi tai mishi ba, saidon mummy alfarman da mummy ta roqa mishi, nacewar tasan baqaramin girki xaran ta iyaba, domin har makarantan koyan girki aka sata Wanda yaxamo tana xua Saturday da Sunday, takuma San yau rana ce ta musamman don tun ana saura sati aka fara shirye shiryen domin xuwan wnn ranan.


Shirya komai nasu itada IBBY tayi a falon daddyn su, can take so suxauna batareda an takura musu ba, kowa dayake cikin wnn family saida suka shaida xarah tana zumudi a yau dinnan.


Wanka tashiga tayi, Wanda tashafe sama da minti talatin tana wanke duk wani saqo na jikinta da sabulai masu inganci, kanta dama can yasha gyara, faduwa yaxo mata daidai da xama kua domin bata sallah hakan yabata daman yiwa kanta gyara da gel, inka Ganshi sai sheqi yake tayi.


Bayan fitowarta a wanka towel dinta tadauka na share jiki ta tsane dukkan ruwanda ke jikinta snn taiwa kanta mazauni akan stool dinda ke gaban mirror nta.


Mai ta shafa snn taxauna zaman kwalliya Wanda shima yadauki zamani guda kapin ta kammala dashi, Waldrop dinta tabude naga taciro wani hadadden swiss lace kalan maroon, dinkin Riga da sket, pattern dinshi ne akai kwalliya dashi ajikin Rigan.


Matsowa tayi gaban mirror domin daura dankwali, wayarta taji yayi ringing alaman alarm dinda ta saita ne yabuga, aiko cikin sauri sauri na zumudi harma takasa daura daura dankwalin akan ta dakyau.


Ai dataga takasa mayafinta kawai taxara fari qal dashi, snn tasaka takalmin ta shima fari mai tsini, kamar xata dungura haka take sauqowa daga steps din, jikake tas tas tas, qarar takalminta ne kawai ke amsa kuwwa a cikin falon.


Mummy lokacin dauko su Yaya yayi pa ki tashi muwuce taqarasa maganar nata tana haki kamar Wanda tai gudun fanfalaqi.


Kallonta kawai mummy takeyi harma tarasa mexata ce da ita, mummy kinyi shiru kuma? Tafada tana bubbuga qafafunta a qasa, Doter wani irin zumudi ne haka kikeyi? Bakisan idan rawan kan yayi yawa xai rainaki ba? Kidan nitsu kikuma saka Jan aji koda kadan ne kinji?


Kallon Maman nata tasakeyi snn tace to naji mummy mutafi to!! Allah Nagode maka ni khadija janyo hannun zaran tayi taxaunar da ita, dakyar yasamu tasahawo kanta, bata bari sunpita xua Airport dinba, saida ta tabbatar ta nitsar da ita snn sukaiwa direba magana yayi Airport dasu, motarsu a Jere Dana gidansu IBBY.



Isarsu lokacin saura minti biyar jirgin nasu yasauqa, basu wahalar da Kansu Neman gurin zama ba suka tsaya suna hirarrakinsu, Zarah da humairah labari humaira kebata amma can ta fahimci hankalinta fa sam baya gurinta, domin idanunta wuwwurgasu kawai takeyi.


Aiko can taga sunfara sauqowa daga kan step din jirgin..............




😍😍🤝Anatare
Mummyn Fadyl CE




🎲🎲TUDUN DAFAWA🎲🎲


Rubutawa....MUMMYN FADYL (Fatyma Muhammad Adamu)

Wattpad @ *fatimamuhammadadamu*


INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION*
*[onward together]*
*{we give the reader's of ours the best out of the bests,, our inks are melodious and dropping a kinda lights to reader's}*
```THE PEN OF LOVE😘

Please Login or Register in order to submit comment