You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sumamme, domin ya matuqar raxana, daganin matarshi dakuma 'yarshi Wanda shinema Yafi komai bashi mamaki, saida yaxubar da hawayen farin ciki.



Nan akaita tayasu farin ciki, daddy ne yahangi IBBY yanata duba lokaci, can ya nisa yace Ibrahim kana Cuba lokaci domin tafiya dinner ko? Sosa kai yayi yana murmushi.


Nan akai musu nasiha sosai Wanda yagama karyar da xuciyar Xarah harta fashe da kuka mai ban tausayi, IBBY ne yayi godiya ga iyayenshi, yakuma matsa gurin Bbn Nana yataya shi murnan haduwa dayayi da iyalansa lpy, Yakama qafan mahaifinshi snn yace nagode Abba. Ina roqon Ku gafara akan dukkannin laifin danai muku Wanda nasani da Wanda bansani ba, inakuma roqon kutaya ni addu'a Allah yabani ikon riqe xarah da amana.


Addu'a sukayi musu da fatan alheri daddy ne yace musu Atafi da Xarah gidanta daga can su tafi gurin dinner domin bidi'ar ta isheshi haka...........




😍😍🤝🏼Anatare
Mummyn Fadyl CE



🎲🎲TUDUN DAFAWA🎲🎲


Rubutawa....MUMMYN FADYL (Fatyma Muhammad Adamu)

Wattpad @ *fatimamuhammadadamu*


INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION*
*[onward together]*
*{we give the reader's of ours the best out of the bests,, our inks are melodious and dropping a kinda lights to reader's}*
```THE PEN OF LOVE😘 HEAT TORCHING❤ TEAR OF SORROWS😭 CURDLES😊 GIGGLES😁 AND MARRIEGE THINK💑```
*```JUST GIVE US FOLLOW..**


Fitowa ta. 6⃣6⃣


Bbn Nana yayi musu godiya sosai da irin xumunci dakuma jajircewan dasukayi akan rayuwar matarshi harma da 'yarshi, haka yayita godiya har da hawaye, a qarshe dai akaita hira inda kowa a cikin xuri'ar yakejinshi kamar a sabuwar duniya. A qarshe daddy yace xa'a gyara musu aurensu da xaran taron ya watse sai su xauna inuwa daya, kowa yaji dadin wannan hukuncin nashi. Farinciki agurin su baxai misaltu ba, Bbn Nana da mama sai satar kallonsu junan su sukeyi. _tsohuwar tsumi ta motsa_


Duk irin miskilanci irinna Aliey saida ya tsinci kanshi cikin farin ciki, amma Abu qalilan yake tunawa yaji ransa ya baci, ba'a kammala taron dashiba yamiqe tayi ficewarsa.


Da haka taron ya watse mummy ce tariqe Xarah xasu fita daddy ne yakira mummy akan ta miqo mishi diyarshi akwai maganar da xai gaya mata, dawowa baya sukayi suka nufoshi, nan ya kamo hannunta yayi yaxaunar da ita a kusa dashi, hannunta yakamo ya damqa mata key.


Waro idanunta tayi waje duk da kukan da takeyi bai hanata yin mamaki tare da yin murmushi a take ba. Yanxu kam xanga murmushin ki ko? Yafada yana kallonta, godiya xata fara xuba mata amma yakatseta tahanyar cemata shhhhhhsh. Ta hanyar da xaki godemin dayane, zarah kiyiwa mijinki biyayya banida haufi akanku dukanku biyu, amma kisani Ibrahim mutunne me kawaici da haquri, inada tabbacin xakiji dadin xama dashi, kinji.


Amsa mishi tayi yace mata, Allah yayi miki Albarka 'yata Amin tace mishi janta yafarayi da labari harsaida mummy ta leqo tace kayi haquri akan garin pa xata xauna, ai xakuga juna, dariya yayi yace mata naji dai, inbadon rawan kan danaga Ibrahim nayi ba ai da sai ince abarta sai gobe, dariya sukayi ganadayan su banda Xarah data fara kukan shagwaba domin harga Allah itakam tagaji da kukan nan, sotake akaita gun mijinta yanxu kam...


Lokacin da akaxo fitowa da Xarah daga guda baqaramin turjiya tayi ba, ganin dagaxke tafiya xa'ayi da ita nan yaji tagama karaya gaba daya takuma Nuna babu inda xataje.


Dakyar aka shigar da ita tana kukan kamar wacce ranta xai bar gangan jikinta, aka kaita gidanta da qawaye kawai aka barta domin xasu shirya su wuce gurin dinner.


Shiryata akayi sosai aka fitar mata da ainihin kyanta, tayi kyau sosai idannace xan misalta muku yanayin kayanta dakuma kwalliayarta to shafinne xai qare gaba daya akanshi batare da munyi komai a cikin ta ba, kawai dai Xarah tayi kyau matuqa.


Motoci ne a fake a qofar gidan ibbyn a qalla sunkai guda Ashirin gaba daya su baqaqen, gurin mota ta shida aka nufa domin shine aka tanadar domin Amarya, kwalliyar jikin motar ma kadai abun kallo ne.


Suna isa gurin motar ta budu, hango Ibby tayi xaune a cikin motar, hannu yasa yariqo nata hannun yashigo da ita, tana shigowa kuwa motar ta koma ta rufu.


Jawota yayi jikinsa ya rungume, tasaki ajiyar xuciya ahankali ya rada mata a kunnenta, my star yanxu fa ke matata ce ko? Dariya tayi tace mishi tabbas kamar yanda kake miji a gareni.


Kallin juna sukayi, suka saki murmushi haka motacin suka fara tafiya ajere cikin tsari har aka isa hall din da aka tanadar domin yin dinner n, qara jawota yayi jikinsa dakyau tare da riqo kunkuminta, Wanda yasata jin wani shock a jikinta tadago da Sauri ta kalleshi, murmushi ya sakar mata, nan tafara qoqarin had a bakinshi da nata, xaro idanuwanta tayi waje tace mishi xaka bata kwalliyar pa.


Qara kallonta yayi snn yatuno karsu qara kwatanta abunda sukayi lokacin kamu akaita jiransu, nan tafara qoqarin akan su fito, aiko suna fitowa suka samu kowa ya fito su ake jira domin shiga dakin taron kamar yanda aka tsara.



A gurin dinner nma babu abunda IBBY yakeyi banda rawan kai domin yaqosa atashi dutafi gidansu jiyakeyi a ransa kamar yaune yafara ganinta, gakuma wata masifaffiyar sha'awsrta dayake Faman fixgarsa kamar xaiyi Yaya.


Dakyar ya lallaba yasamu har aka gama baijira suka yi tsarinsu kamar yanda suka faro taba, domin kuwa amafata yin rawa yaja Xarah suka koma mota dakanshi yaja suka nufi gidansu magana take mishi akan sujira sauran mutane mana amma baiko saurareta ba, dukaiyo gida.


Suna shigowa yarufe ko ina afalo yasauqe wani nauyayyen ajiyar xuciya domin jiyayi kamar wandayayi gudun fanfalaqi yatsira snn yasamu ruwa ya kwankwada, kama hannunta yayi suka nufi dakinsu.



Mamakin bare barensa kawai takeyi domin babu nitsuqa a tare dashi ko kadan, nan taji tsoro ya shigeta har cikinta ya duri ruwa.


Wayarshi ce tafara ringing cirota yayi a aljihunsa ganin numban Aliey yasashi dakin murmushi snn yadauka, yacemishi kai mallam Yaya haka? Yakamata kasan lokacin daya kamata kana kuran mutum mai iyali pa.


Tsaki Aliey yaja snn yace kaidao kaji kunya da bare bare karasa nitsuwarka kan wata qaramar yarinya salon ta rainaka, dariya IBBY yayi mishi yace wlh kamar kasani kai ni rainin ma nakeso, in Xarah bata rainani ba, waxata raina?



Kaika sani nikam fito kasameni ga Abu nakawo muku, OK kadan jirani in nemi ixinin matata kasan yanxu bani kadai nakeda iko da kaina ba. Dan iska idan kaga dama karka fito.


Dariya yayi snn yacewa Xarah bari infita inkarbo saqo gurin Aliey, shagwabe fuska tayi harda bubbuga qafafu akan baxaije waje yabarta a dakin ita kadai ba.


Haka dayaga darun Nata bamai qarewa bane Yakama hannunta suka fito tare, hangoshi sukayi motar abude yaciro qafarshi guda daya a waje, waya takeyi amma tunda ya hangosu hannayensu sarqe da juna yaji ranshi ya baci, baisan lokacinda yayi hanging call dinba. Kiramshi aka sakeyi nan yayi rejecting.


Tsayawa tayi tareda riqe kunkuminta juyowa yayi yace muje manah my Star, a'ah ina jiranka anan kallonta yayi tare da kashe mata ido daya ya wuce.


Yana qarasowa yabude dayan side din yashiga, jin wayar tana ringing yasashi kallon Aliey, yadaidaita muryansa snn yace .


Dan uwa meyasa kake wulaqanta masoyanka? Meyasa Baka daukan soyayya da daraja? A yau daya inason inyi maka wani tambaya amatsayina na Dan uwanka Amininka don Allah kasaurareni.
Ina jinka kawai yafada batare da ya kalleshi ba.



Inason kasanar dani meye tsakaninka da matata, metai maka da baka sonta? Yakamata ace kodonni ka sararawa Xarah koma ace don sonda mahaifiyarka take mata, Alieyu yakamata ace Kaine mutum na farko daxaka fara gwadawa Xarah gata, nakanji ajikina kobayan raina xaka iya taimakon xarah, amma idan natuna qiyayyar da kake gwada mata jikinta yakamyi sanyi.



Yakamo hannuwansa yaqara da cewa Haidar kadubi girman Allah ka sassauta qiyayyar ka akan Xarah, xanxo qiyayyarta yadawo kaina, snn soyayyar dakakemin Yakoma kanta don girman Allah.


Kobayan raina xanyi alfahari xansan kanunamin gata, tunda kaso abunda nake matuqar qauna fiye da komai Dana mallaka. Alieyu inason Xarah sonda Kaine shaida, amma inaji ajikina baxamu Mori soyayyar mu yanda muka dayko tafiyar ba, banida tabbacin mexai faru, amma kawai daiiiiiiiii, kariqemin Xarah karka bari tayi kuka Indai Kanada ikon hanata, karka bari tayi maraici.



Juyowa yayi yace wani irin magana kakeyi ne haka? Dariya yayi sosai harda riqe cikin snn ya sassauta yace Dan iska Ashe kanasona bakason inmutu, babu inda xani insha Allah sauna mori Amarci muhaihu tareda my star, mu tsufa tare amma nudai nayi wannan roqon a karo na qarshe.


Murmushi yayi mishi Wanda yabawa IBBY mamaki, yace duk wannan magiyar akan waccar qaramar matar taka? Oho komadai jaririya ce yakaimishi duka.


To shiknn Ango xanfara Nuna mata soyayya a matsayinta na qanwata dakuma matar Dan uwana Aminina, tafawa sukayi snn Aliey yace kar matarmu tayi fushi ka kaxa na kawo muku da madara Asha Amarci lpy, amma plx wannan rawan kan Nana karage saboda kabita ahankali ko?



To shknn ja tsamin motarka xan rufe gidana matana ta gaji da jirana kaga tsayuwa tafara gagarar ta, haka yaja mitarshi yafice sunaiwa juna bye bye......,..........




😍😍🤝🏼Anatare
Mummyn Fadyl CE



🎲🎲TUDUN DAFAWA🎲🎲


Rubutawa....MUMMYN FADYL (Fatyma Muhammad Adamu)

Wattpad @ *fatimamuhammadadamu*


INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION*
*[onward together]*
*{we give the reader's of ours the best out of the bests,, our inks are melodious and dropping a kinda lights to reader's}*
```THE PEN OF LOVE😘 HEAT TORCHING❤ TEAR OF SORROWS😭 CURDLES😊 GIGGLES😁 AND MARRIEGE THINK💑```
*```JUST GIVE US FOLLOW..**


*My fans kutayani jaje wlh writers dayawa a bayansu nafara amma duk sungama harsun kusa kammala wani, amma ni inanan kamar anshuka dusa, to wlh ynxu nataso da haxaqa ta, 💪🏽 a kwanakin ga xan kammmala kowa ya huta*


Fitowa ta. 6⃣7⃣


Dawowa yayi kusa da ita ganin ranta a bace yasashi rungumota tareda manna mata kiss a kumatunta snn Yace, my star yaukam nayi iya bakin qoqarina na shirya tsakaninki da yayanki, saura ta gurinki a matsayina na mijinki wannan umarni ne inason kiyiwa Aliey biyayya matuqar kinason farinciki na.



Kallonshi tayi da mamaki domin baitaba yimata magana da wannan fuskar ba, he means wat he's saying don haka ta saurareshi dakyau.


Banason qara ganinku a yanayin da naganku tun farin ganinki a tare damu, Xarah Aliey matdayinshi a gurina basai na nanata miki ba domin ke maibawa wani labari ne, saboda sonda kikemin inason kibawa Aliey matsayi babba a rayuwarki kodon gaba?


Menene gaban xata haifar? ta tambayeshi
Babu komai sai alheri mata ta muje ciki yunwa nakeji king a yayanki ne yakawo mana abinci domin daukaka mana wannan ranar a garemu, Xarah inason Aliey kisoshi kinji my Star?


Murmushi tayi tace my paramour ur wish is always my command, insha Allah xanyi yanda kakeso, bai tsaya sauraron taba ya sureta hade dayi mata cakulki acikinta nan tahau kyalkyala dariya tana fadin xan fadi, wlh yayah xan fadi.



Bai direta ko ina ba sai falon su, nan ya umarceta akan tadauko musu plate dakuma cups, Shiva kitchen din tayi, tsaruwan kitchen dinne yasata jin farinciki ya malala acikin xuciyarta domin ba shakka su mummy sun taka rawar gani akan al'amarin rayuwarta, babu abunda xaka daga ido ka kalla na cikin gidanta ka kushe, ko maqiyi ne saidai yagani ya tabe baki, babu tacewa akan gidanta.


Dawowa falon tayi hannunta dauke da abunda mijinta yasata xuwa daukowa, xama tayi xata fara Cuba musu yace nooo my star aike yau hukumace saida rarrashi, sha xamanki ki huta gimbiya nixanyi komai, harsai randa nace kiyi.


Nan ya xuba musu komai dukai basmala suka fara ciyar da junansu, abundai gwanin sha'awa da burgewa, kallo daya xakai musu kasan asalin masoya ne Wanda cuciyarsu ke cike taff da begen junansu.


Bayan sun kammala cin abincinsu dakanshi ya tattara gurinda suka ci abincin, yadawo Yakama hannunta sukai dakin barcinsu, kamar yanda aka tsara a musulunce haka suka suka gabatar da sallahn su domin juna godiya ga mahaliccinsu, bayan sun idar ibby Yajima yana kwararo musu addu'oi Wanda har xarah tayi mamakin yanda saninshi acikin addini yayi nisa haka.


Bayan ya kammala ne yajuyo gareta yaga harta fara gyangyadawa yasan gajiya ne a tare da ita sosai, yanda yakejinshi tamkar baxai iya haquri ba, amma kuma baxai iya takurata taba.


Xarah ya ambaci sunanta cikin wani salo, da idanunta dasukai mata nauyi kawai ta amsashi, tashi ki canxa kaya muyi bacci ko? A shagwabe tace wlh baxan iyaba nagaji bacci nakeji tafadi kamar me shirin fashewa da kuka.


Sorry dear basai kinyi kuka ba, bari ni inshiryaki da kaina, haka ya dagata kamar wata matacciya domin gaba daya jikinta yagama sakewa, akan gado ya direta, yafara rage mata kayan jikinta, arba yayi da halittun qirjinta nan yaji komai yana Neman kwance mishi, dakyar ya saita kansa yasamu yacire mata kayan, snn yasa mata kayan bacci.


Gyara mata kwanciyarta yayi snn shima ya canxa nashi ya kashe musu wuta, ya haura kan gadon jawota yayi jikinshi sosai tare da matseta, harta saki Dan qara, washh yayah da xafi, shikuwa jiyayi muryan nata kamar qara mishi qaimi takeyi.


Nan kuwa ya xura hannunsa cikin rigan baccinta, aiko nan tsoro ya bayyana qarara afuskar Xarah tunowa datayi yanxu fa bakamar da bane, yanada iko da damar yin duk abunda yayi niyyar yi da ita.



Jikinta ne yafara rawa tace yayah kabari ina tsoro fa, murmushi yayi mata mai dan sauti snn yace my star baxan shiga hakkin kuba, plx kibarni inji dumin jikinki insarrafa albarkatun da ubangiji ya axurtani dasu, Xarah karki hanani kitayani namiki alqawarin baxan wuce gona da iri ba, amma inason kicire kunya ki tattaro duk wani kwaxo da haxaqar ki kinunamin soyayya a wannan Daren kinji?



Yaya nah ban fahimci abunda kace wai baxaka shiga hakkinmu ba, nida waye? Ohhh haka nafada I mean baxan Shiga miki inda bakyaso ba harsai randa kika amince min.



Xatai magana yarufe mata baki da nashi, kissing dinta yafara yi passionately cikin kwarewa, bata bata lokaciba itama jin sauyi a tattare da ita, nan tahau mayar masa da martani, shafa kowani lungu da saqo na jikin junansu sukeyi cikin burin faranta ran junansu.



Tagama sakewa dashi suna farantawa juna rai domin tanada tabbacin IBBY baxai taba wuce gona da iri ba, domin baya magana biyu, sun shafe a qalla minti talatin suna romancing junansu cikin xafi xafi, shine yafara xare jikinsa tare da yin magana cikin shaqeqqiyar muryansa yace ohhh my star haka kikeda jaraba saiwani rirriqeni kikeyi kamar xaki cinyeni? Kalli bakina wlh kinjimin ciwo.


Kunya ne ya lullubeta amma tayi borin kunya tace amma duk jarabata ai banice nafara taboka ba, kuma ni ai banyi nishi ba, dariya yayi yace to dani dake wayafi jaraba? Shagwabewa tayi sosai takai mishi dukan wasa a qirjinsa, shikuma yasaki Dan qara yace wayyo qirjina ya fashe kamar dagaxke.


Aiko nan Xarah ta rude ta lalubi wayarta ta haska shikuma sai muqursusun qarya yakeyi, tafara Dan qoqarin dagashi tana qoqarin fashewa da kuka, fadi takeyi kayi haquri Yaya IBBY wlh bansan xakaji ciwo ba.


Saida ya tabbatar Takai qarshe gurin rudewa snn yajuyo yana mata dariya, ganij haka yasata fadawa jikinshi tafashe da kuka tana fadin wlh saina rama.


Rarrashinta yafarayi yana cewa haba my star xaki iya ramawa? Ibbyn ki nefa, mijinki mai qaunarki, Xarah ina sonki bantaba son wata 'ya mace a duniya kamarki ba, tun bakisan kanki ba nake dakon qaunarki harkika girma kika amince dani, gashi yau Allah yakawo mu nidake muna kwance akan gadonmu na sunnah a matsayin ma'aurata.



Kinsan meye? A'ah saika fada yayanah mijina, gyara mata kwanciya yayi akan qirjinsa snn yace haihuwanki nafari inason kisa sunana, dagowa tayi ta dubeshi tace u mean sunanka xaka mayar wa danmu na fari? Bai amsata ba, yacigaba da maganarshi.



Xarah a duk halinda kika tsinci kanki inason kixama mai miqawa ubangiji al'amuranki, Xarah har abada karkiyi jayayya da hikuncin Allah akanki, kome yafaru dake a rayuwa kiss aranki cewa dama can Haka Allah ya tsarawa rayuwarki, baduk abunda mukeso Muke samu ba.



Xarah haquri, kawaici Ibadah, wadannan Abu ukun inason kiriqesu a ranki, suxame mini makami a Duk halinda kika tsinci kanki, a qarshe kuma inadon sanar dake wani Abu Wanda baki sani ba, dab da kunnenta yafara yimata magana Wanda nikaina banji meyace mata ba, kawai naji sun bushe da dariya, wannan karon itace tafara canxa musu yanayin....

&&&&&&&&&&&&


Kamar yanda yasaba haka yauma yana cikin tafiya acikin garin nijar cikin salasainin dare, motarshi sheqe take da mahaukata kamar yanda yasaba kowacce an fesa mata hoda ta bingire da bacci.


Kai kai dakata yacewa direbansa, dasauri yataka burki yafara waiwaye kashe motar yayi yafito, sakamakom hango abunda ogan nashi yake nufi gameda dakatar dashi dayayi.



Tsallaka titi yayi hankalinshi kwance domin babu hayaniya, yanayin yanda dare ya tsala, tun kapin ya isa gareta wani wawan wari ya xuyarshi hancinsa Wanda yajishi har maqogoronsa, bashiri yayi baya kamar xai fadi, komawa yayi gurin motarsu yasanar da ogan shi.



Fuskarnan a murtuqe yace mishi kasan dai dolene adadin mutanen nan yacika domin wannan umarnin boka ne, snn kana ganin Idan mukace baxamu tafi da ita ba, gari xai iya waye mana batareda adadin mahaukatam yacika ba, wannan kuwa daidai yake da tonuwan dukkan asiri na.


Cikin xafin nama yajuya gurin Ayashe yanufa yana toshe hanci, harya isa dab da ita baiga alamar xata gudu ba kamar yanda sauran mahaukatan sukeyi idan yaje garesu, saidai shine ya qarasa har gareta.



Itakuwa ganinshi datayi tadauka aljanine batayi motsi ba domi a halinda takeciki yanxu babu abunda tafi qauna fiye da mutuwa a rayuwarta, aganinta shuxaifi mata komai sauqi, dayaxo xai tanata kuwa jiyayi jikinta ya tamkar auduga, don yafi jikin tsoffin da sikai shekara Dari a duniya xagwanyewa, shikanshi ya tsorata matuqa domin yayi tunanin koba mutum bace, jiyayi kamar ya juya amma yatuna da kashedin da boka yayi musu a game da hakan.



Aiko nan yafara janta har gurin motar tasu yabude gurinda suka xuba, sauran mahaukatan, Yakoma cikin ya finciki motar suka cigaba da tafiya, suna cikin tafiya saida yafesawa motar turare bila adadin amma warin Ahashe daban qamshin turaren ma daban.



Suna shiga garin jibia kua barayi suka taresu, kapin ace yayi abunda yasaba yiwa barayi idan irin hakan tafaru, saiyaga wadannan sunfishi laqani domin nasu na musamman ne, ya murxa layarsa yayi surkullensa duk a banxa, gashi babu kudi a tattare dashi balle ya sallamesu suwuce damuwarshi kar gari yafara haske asirinsa ya tonu.


Basu saurara mishi ba suka fito dasu gaba dayansu, Wanda acikinsu yasan kan irin motar yanufi Inda aka Tara mahaukatan nan yabudesu nan aka gandu burjik kamar basuda rai a jikinsu.



Xaro idanu sukayi waje shikuwa Alhaji hankalinshi ne yakai qololuwa gurin tashi ganin anata fitowa dasu, Ayashe ce taqarshe wanda dakanta tafito duk dayanda takejin axaban naman jikinta, amma ganin barayin yasata jin dadi a ranta burinta akasheta tahuta...
_nace duk abunda ya koro bera daga rami ya afka wuta to abunda yakecikin Ramin yafi wutan xafi_



Babban cikinsu ne yamatso yace da Alhaji Bala haryanxu baka daina safaran mahaukata kana kaiwa bokanka kuna lalata suba? Jiki na kyarma jin an anbaci sirrinsa yasashi saurin bashi haquri akan kome yakeso xai iya bashi, amma yayi haquri yabarshi su wuce.


Ogan bai tsaya saurarenshi ba yasaita kan bindigarsa akan Alhaji Bala, yace bakada arxikin da xaka bani domin a yanxu natara iya abunda nakeso, saboda wani dalili nawa make fashi. Kawai yau kayi bankwana da duniya nan yafasa kanshi da alburushi sai jini kake gani yanayin sama.



Bai tsaya wata wataba yaqara Harbin direban a qirji dakuma qafafu nan shima yaxube matacce, motarsu suka shige dayansu yaja na Alhaji bala suka qarawa kansu iska sukabar dajin.



A gigice Ayashe take takawa tana tafiya batasan Inda takesa qafafunta ba, tsabar rudewa, domin yau taga iyayenta a tijara, tayi tafiya mai nisa kapin ta fahimci acikin garinta take...



&&&&&&&&&&


Koda asuba tayi Xarah ce tafara farkawa ganinta tayi a rungume ajikin ibby yanata baccinsa hankali kwance, wayarta ta xare a dayan hannunsa ta kunna gani tayi fuskar wayan akan hoton ta yake da alama ita yake ta aikin kalla, murmushi tayi kapin...........





😍😍🤝🏼Anatare
Mummyn Fadyl CE



🎲🎲TUDUN DAFAWA🎲🎲


Rubutawa....MUMMYN FADYL (Fatyma Muhammad Adamu)

Wattpad @ *fatimamuhammadadamu*


INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION*
*[onward together]*
*{we give the reader's of ours the best out of the bests,, our inks are melodious and dropping a kinda lights to reader's}*
```THE PEN OF LOVE😘 HEAT TORCHING❤ TEAR OF SORROWS😭 CURDLES😊 GIGGLES😁 AND MARRIEGE THINK💑```
*```JUST GIVE US FOLLOW..**


_NASAN YAU AKWAI MASU GANIN LAIFINA DAYAWA, amma ina Baku haquri tun kapin Ku kai ga karantawa, kuymin uxiri haka labarin yaxo_

*TEAM IBBY🤲🏼*


Fitowa ta. 6⃣8⃣



Da hanxarinta ta miqe tanufi bayi saida tadan watsa ruwa ajikinta kapin tadauro alwala ta fito sauri tayi akan tarigashi yin sallah domin tun suna gida yana yi mata gorin bata sallah dawuri.


Bayan ta idar ko addu'a bata tsaya yiba, taqarasa gurin gadon domin tadashi taimishi gorin tarigashi yin sallah yaukam...



Qarasawa tayi ta haye kan gadon tamatsa kusa dashi, rungumo hannunshi tayi a jikinta nan taji hannun nashi kamar a sake, hankalinta bai kai gurin ba tafara mishi magana a hankali ganin bai kulata ba yasata matsawa jikin kunnenshi, hura mishi cikin kunnuwansa tafarayi nanma taji shiru.


Tun tana lallabinshi har haqurinta ya gaxa ta fashe mishi da kukan shagwaba domin tasan lagonshi matsawar yafara yi mata wasa, to indai tafara kuka xai daina, fadi takeyi wlh Kuma kokatashi kamin magana baxan kulaka ba harsai munyi sati daya, babu ruwana dakai, niba zaran ka bane.


Haka taita sunbatu amma bai kulata ba, hayewa jikinshi tayi tafara jijjigashi amma babu alamun motsi a tare dashi, cikin firgici takai kunnenta kan qirjinshi, jin bataji alamar numfashi a tare dashi ba, yasata saurin dirowa daga kan gadon tayi falo ruwa ta dauko acikin gora ta yayyafa mishi domin tunaninta suma yayi.


Nanma babu alamar motsi baya baya tafara tafiya tana girgixa kai, kamar an hankadata taqara komawa jikinshi tafada tana fadin wlh ba gaxkiya bane, yayah nasan wasa kakemin katashi karkayi irin wannan baccin.


Tadauki a qalla minti arba'in tana kwance a jikinshi ta jijjigashi taimishi magana, tunaninta yafara xarewa kamar an mintsineta aka sanar da ita kodai mutuwa yayi.


Daqarfi tace wlh baxaka mutu ba, yayah karka tafi kabarni nima mutuwa xanyi, wayyo mijina yaxanyi, gani tayi kamar yana mata murmushi dasauri ta isa gabanshi nan taga zahiri ba murmushi yakeyi mata ba amma fuskarshi a sake take.


Hannayenshi ta daga dama tasake nan taga sun sake yaraf, gigitaccen qara tasaki taxube a gurin sumammiya, gashi babu kowa a gurin.


Tun bayan dawowan Aliey daga masallaci yaji gabanshi na fadi, wayarshi yajawo domin tsokanar Ibby, domin da tunaninsu ya kwana a Daren jiya, yasan baqaramin tsiya xai mishi ba, shiyasa yafasa kirannashi, ganin envelope a fuskar wayarshi alamar shigowar saqo yasashi budewa IBBY ne. Murmushi yayi yafara duba saqon.


_Dan uwa babu abunda yafi aure da masoyi dadi a rayuwa, bansan tayaya xan sanar dakai dadin aure ba, kaidai kadage ka fitar da mata ayi maka aure, plx Dan uwa don Allah ga Amanar Xarah, kaimin gata gurin nuna mata qauna ka tausayawa maraicinta, nasan Xarah xata jigata, Xarah tanada sauqin kai, katausaya mata karka manta da alqawarin da kaimin inason duk soyayyar da kakemin ka dunqula guri daya kamayar dashi kan Xarah, nabarka lpy gwauro_


Dariya yayi gameda yin qaramar tsaki yace a fili, saikace mai bayar da wasiyya, wannan yarinyar kamar ita kadai ya mallaka a rayuwarshi, bashida buri saina a riqe mishi ita, Xarah, xarah, Xarah komai Xarah his Star..


Komawa kan gadonshi yayi yafara karatun alqur'ani acikin wayarsa kamar kullum, al'adarshi ne wannan.


Mummy kuwa a dakinta, haka kawai ta tsinci kanta tanacikin wani yanayi harwani sanyi sanyi takeji yana ratsa qofofin gashin jikinta, haka yake a bangaren Ummy domin itakan harkasa haqura tayi taje ta sanar da Abba.


Murmushi dabai kai qasan ranshi ba, domin shima hakan take a gareshi, amma dakiya irinta maxa ya kwantar mata da hankalin ta hanyar cemata idan kika jiki a irin wannan yanayin addu'a akeyi kinji? Dakyar ta amsa mishi ta tashi tanufi kitchen.


Abincin breakfast tahada me rai da lpy tajere acikin basket snn tanufi dakin humairah, ke tashi ki kai wasu yayanki abincin kari, mutditstsike idanunta tayi snn tace Ummy wlh xakisa Xarah ta qara rainani ne, idan nakai musu nasan tsiya xatai ta min, kinsan Yayah kuma kome tayi biye mata yakeyi.


To kome xatamiki yanxukam ai dai2 ne domin wanki take aure, nikam tashi kikai musu, karkuma kiymata shirme kinsan da dayanxu ba daya bane, atoh, haka humairah tamiqe tana tura baki tashirya tadauki basket din..


Mummy ma haka ta shirya abincin nata, dakin daddy tanufa tana xolayarshi dukda babu qarfi jikknta ko kadan, tace Daddy ga abincin gidan diyarka ko xaka kai, dariya yayi mata yace yaukam baxai yiwuba domin baxanso ganinta a yanayin da take ciki yauba, yanda IBBY yake

Please Login or Register in order to submit comment