You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

daya 'yan matan dake dakin suka dauki tafii ana mata guda, itakuwa yanga tacigaba dayi musu, dakyar aka samu ta nitsu makeup artist dintasamu taci gaba dayi mata kwalliyar donma saida aka fitar da humairah domin itace gwanar dake tsokanarta gashi batada haquri daga humairah tayi magana xata zaburo domin bata amsa.


Wowww shine abunda qawayen Zarah suka fada gabadayansu domin kyanda tayi yawuce in misalta muku domin innace xan kwatanta muku kyan da tayi a rana me kama ta yau to ba shakka akwai yiwuwar wayata tai hanging tadaina amfani na tsawon satikai biyu.


Xanbarku Ku qiyasta kyanta da kanku, zarah dai kyakykyawa ce, takuma sa net dinta blue mai ratsim golden dinkin Buba, takalmin ta Ash ne haka head dinma Ash colour ne, purse din hannunta Ash, anyimata dressing shigen na yarbawa.


A bangaren angwaye kua Anko sukayi da Aliey Inda sukayi shige cikin danyar shadda coffee hularsu Zanna brown amma tanada rashin golden ajikinta kallo daya xakai musu kasan kayan Dake jikinsu naira tayi kuka kapin yasamu maxauni a jikinsu.


Gurin yasha kwalliya anqawata shi sosai da sosai, motar angwaye ne yafara isowa a bayansu motan Amare ne, Fitowa ibby yayi abokinshi sudais yana tsokanarshi baida kawaici ne? Dariya yayi yace musu indai akan Xarah ne baxai taba daga musu qafa ba.


Motar daya tabbatar acikinta take yanufa ya bude bayan, shagala yayi da kallonta yakasa aiwatar da komai, itakuwa murmushi kawai taketa xuba mishi sakamakon wani sihirtaccen kyau dataga yamata.


Gani tayi kallon nashi bamai dainawa bane yasata hura mishi ido, a firgice ya kalleta snn yasaki murmushi me hade da ajiyan xuciya, itama murmushin tamayar mishi tace kallon pa, cemata yayi My star I'm speechless narasa tayaya xan misalta kyanki, anya xan yarda ayi wannan program din? Kowa yayi ta kallenin ke?


Shagwabe fuska tayi tafara lallashinshi nan ya bingire da dariya, acan gurin taro kowa yagama halarta amma babu ango da amarya, Aliey ne axuciye yanufi gurin motar, xuwa yayi yasamu tuni Ibby kanma yashige cikin motar yakuma rufe tareda xuge glass sama................




😍😍🤝🏼Anatare
Mummyn Fadyl CE


🎲🎲TUDUN DAFAWA🎲🎲


Rubutawa....MUMMYN FADYL (Fatyma Muhammad Adamu)

Wattpad @ *fatimamuhammadadamu*


INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION*
*[onward together]*
*{we give the reader's of ours the best out of the bests,, our inks are melodious and dropping a kinda lights to reader's}*
```THE PEN OF LOVE😘 HEAT TORCHING❤ TEAR OF SORROWS😭 CURDLES😊 GIGGLES😁 AND MARRIEGE THINK💑```
*```JUST GIVE US FOLLOW..**



Fitowa ta. 6⃣3⃣



Isowar IBBY cikin takaici da xaquwa ya kwankwasa musu kamar zai fasa glass din, xuge glass din yayi itakua daidai lokacin da take xabga mishi shagwaba domin batama kula da xuwan Aliey gurin ba.


Shikuma ganin hakan yasashi yin tunanin ko ganinshi ne yasata narkewa tanata xuba shagwaba wa ibbyn, abunda yasashi jin takaicin ta knn.


Cikin jin haushi tareda watsawa zarah harara snn yace kaikuma wnn wani irin salon iskanci ne anacan anata jiranku kun shanya mutane, dama kunsan bayi xakuyi ba kuka gayyato al'umma? Yaqarashe maganar haryana kunfan baki tsabar haushin su dayaji ya turniqe shi Wanda baisan dalilin sa ba.



So sorry Dan uwa wlh ganinta ne ta shagaltar dani, plx kacewa qanwar nan taka tarage wnn salon nata domin wlh xata iya zautar dani batareda na Ankara ba. Itakuwa harwani lumshe idanu takeyi cikin salon qara narkar da xuciyar Ibbyn tah..


Baibi takansu domin jiyayi yagama isowa wuya, idan kunga dama karma kuje garesu, maimakon yakoma gurin taro sai shiga motarshi yayi ya figeta a guje yabar gurin, cikin Sauri ibby yafara binshi amma kapin ya iskeshi har yabar gurin.


Dafe goshinsa yayi yace hohh Aliey maxa sarkin fushi, baiso hakan tafaru tsakaninsu a irin wadannan kwanakin ba, domin yana buqatarsa a duk cikin hidimarsa.


Yasan kuma tunda yatafi babu mahaluqin daya isa yadawo dashi, shiyasa jiki a sanyaye ya nufi jikin motar, itakanta Xarah batason hakan yafaru ba, taso ace Aliey yana gurin kodon tacigaba da shaqar dashi. Yanda taga fuskar IBBY babu walwala tasan baxaiso tai wata shirme ba, duk da tasan xai biyemata amma bacikin dadin rai ba. Shiyasa kai tsaye tamiqo mishi hannu suka fara takawa cikin gurin taron, amma a xuciyarta tana jinjinawa irin qaunar da ibby yake yiwa Alieyn.


Qawayenta ne suka taso suka tareta tareda rakata har maxauninta, bada jimawa ba aka cigaba da gudanar da taron cikin yanda aka tsara, taron ya qayatar yanda akeso saidai kawai fuskar Angon ne bakamar yanda ake buqata ba, domin Rabin taron hankalinshi nakan wayarsa yana trying numban Aliey, shidai baisan wani irin tsana Aliey yayiwa Xarah ba, koda bawai don son da yakeyiwa Xarah ba, shibaiga aibinta ba.
Haka akaita gudanarwa har aka watse...



Lami haka takoma cikin tasha daxama duk da yanda take fama da wani mahaukacin xaxxafan xaxxabi, Wanda tarasa dalili da Dan mafarinsa, gashi yanxu kanma harda xawo, don idan bata Ankara da wuri ba yanxu saita bata jikinta, haka suke yawo cikin Ahalinsu na Mabarata, idan dare yayi sunemi rumfa acikin kasuwan su kwana.



A dalilin baran ne take samu taci takuma sha, snn idan yamma tayi sundawo daga baran ta biya chemist tasayi koda paracetamol ne tasha domin jin sauqin zazzabin dayake damunta.


Tana zaune a rumfan da suke kwana ne, bayan motsin yadan lafa ta xaro 'yan kudaden da tasamo na yau, farin ciki ne ya mamaye ta domin cinikinta nayau yafi na kullum, qidayasu taqara yi dubu Bihar ne ciff, nan tamaida shi cikin lalitar ta tarufe takoma can gefe inda makwancin ta yake, bata wuce minti biyar da kwanciya ba bacci me nauyi yayi awon gaba da ita.



Itakuwa Larabiyo tanacan akwance kamar me bacci, amma a xahiri hankalinta dakuma tunaninta gaba daya suntapi kan kudin da tagani Lami tana qidayawa.


Batun yau takeson yasheta ba, tajima da wnn burin saidai akwai wata acikinsu Wanda bata bacci wato Altine Kurma kwana takeyi sallah, baka isa kayi data wa wani a gurin ba, domin kua xata ganka, amma yau sunwayi gari 'yan uwanta sunxo sunnuna mata gata domin suma saida sukai musu kyaututtuka na ban mamaki.


Saida tabari guri yayi shiru snn tamiqe salon alin da dan tocilan ta marar haske sosai tanufi gurin kwanciyar Lami, aiko yanda tai xato hakannr ta auku domin kuwa ta baje tai dai~dai sai tashin minsharinta kakeji yana tashi a gurin.


A hankali tasa hannu ta xuge xip din lalitar takwashe kudaden cikin kaff batareda tayi tunanin halin da Lami din xata Shiga ba, tajuya abunta takoma makwancin ta kamar batai komai ba, hankalinta kwance.



Sanyin asuban daya fara bugata ne yasata miqewa dasauri damacan sallah bawai ya dameta bane, idan tafarka tanemi ruwa tawanke idonta akuma baxama cikin gari afara bara.


Da lalitar ta tafara cin karo ganinshi a wangale hannu tasa kamar wata marar rai, nan ta tarar wayam babu komai aciki, ai batasan lokacin da ta kurma wani gigitaccen ihu Wanda ya fargar da ilahirin mutanen da ke kewaye dasu.


Nan akaiyo kanta domin ba'asan meke faruwa da ita ba, tambayarta suka farayi amma bakinta yakasa furta komai inbanda lalitar ta datake nuna wa da hannunta, takasa aiwatar da komai , Larabiyo ce cikin kissa da munafurci ta taho gabanta take qara tambayarta bata bata amsa ba, amma ita tafahimci me take nupi.


Cikin siyasa tace mata kudinki aka dauke? Aiko nan tahau gyada kanta kamar kadangaruwa babu qaqqautawa gurin yadau salati wasu na tausaya mata, inda wasu kuma kemata Allah shiqara domin a cikin rumfan nasu babu Wanda baisan irin wawan baccinta ba.


A hankali aka fara watsewa akanta amma larabiyo tana wajenta tanata lallashinta, hardai tasamu ta nitsu kadan, nan suka tashi suka nufi cikin tasha domin Neman abincin kari.



Hidima akeyi sosai da sosai gida yacika maqil, sai kaiwa da kawowa akeyi a cikin gidan, daga bangaren Ango har bangaren Amarya babu Wanda yaxauna.


Nana ce a falon Haj.Maryam suna tattauna yanda xasu tsara yanda bikin xai wakana domin me aikin nasu Wanda xata aura mebawa fulayin gidan ruwa ne snn a halin yanxu yau kwananshi uku da xuwa qauyensu domin tahowa da danginsa amma annemi mahaifiyarshi anrasa sai baffansgi da aka taho dashi.


Haj.maryam ce tace to nidai kinga yanxu lokaci yafara qurewa qarfe takwas amma bamu wuce ba? Kekam ma naki abun ai yayi uku, ga Isah me aiki ga Ibby Wanda dole kiymin kara, uwa uba kuma ga 'yar dakin ki Xarah.


Murmushi Nana taimata snn tace habawa ai qafarki qafata amma insha Allah idan aka daura auren xan xo mucigaba da hidiman Isah, nifa haryau bansan shiba.


Habadai? Wlh kuwa bamu taba haduwa ba, kinsan dayake yana xuwa makaranta da asuba yakeyin aikinshi yatafi, sallaman dasukaji ne yadadu tsagaita hirannasu ta hanyar amsa sallaman.



Iso mana Isah Haj.maryam tabashi amsa, gaban Nana ne ya yanke yafadi sakamakon hada idanu da tayi da isahn lami, shima haka xaro idanu waje yayi duk da tasauya bana wasa ba, amma hakan baxai hanashi gano fuskarta ba.


Itace tafara magana tace Isah Kaine? Nine yabata amsa jiki a sanyaye, gaisawa sukayi snn tasanar da Haj.maryam matsayin Isah a gareta, baisan lokacin da yafashe da kuka yakuma ji kunyar ta fiye da tunanin mai tunani.


Sunyi mamakin al'amarin Sosai, gabatar musu da baffanshi yayi, Alhaji suka nemo dakuma Bbn Nana sukaita jimamin abun, Aphaji dayaji xafin abun sosai ranshi Yakuma baci atake yace yayi danasanin taimakawa tsatson Lami Wanda takasance mace mai ha'inci.


Yakuma qara dacewa xai sallami Isah a gidanshi, nan baffan Sadiya yafara magiya, Bbn nanah ne yasa baki a maganar inda yaroqawa Isah alfarma, yakuma sanar dasu cewa ba halin Isah daya da mahaifiyarshi ba.


Baffan Sadiya ma yaqara musu da bayanij halinda lami take ciki da abunda aka sanar dashi dangane da ita, salati suka dauka, banda Isah Wanda yaji tamkar qasa tatsage yashige yabar doron qasa domin wata masifaffiyar kunya data lullubeshi.



Bbn Nanah yace dama shi duniya yagaji haka Indai kai cuta to xaka hadu da daidai dakai, Allah yakyauta, Isah ne cikin kuka yafara nemawa mahaifiyarshi yafiya kapin Allah yayi haduwarsu.


Cemishi sukayi xasu yafemata duk ranar da suka hadu da zainab..............




😍😍🤝🏼Anatare.
Mummyn Fadyl CE




🎲🎲TUDUN DAFAWA🎲🎲


Rubutawa....MUMMYN FADYL (Fatyma Muhammad Adamu)

Wattpad @ *fatimamuhammadadamu*


INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION*
*[onward together]*
*{we give the reader's of ours the best out of the bests,, our inks are melodious and dropping a kinda lights to reader's}*
```THE PEN OF LOVE😘 HEAT TORCHING❤ TEAR OF SORROWS😭 CURDLES😊 GIGGLES😁 AND MARRIEGE THINK💑```
*```JUST GIVE US FOLLOW..**


Fitowa ta. 6⃣4⃣


Haka xaman Nasu ya watse amma kowa da abunda yake saqawa acikin ransa, Nanah da haj.maryam suka shirya domin tafiya gidan biki, iyayen Talatu mai aikinsu ne sukaxo gaidasu domin Alhaji ya ware musu dakuna domin gudanar da hidiman harsu gama, shine kuma yadau nauyin komai a cikin al'amarin auren.


Nana harsuka Isah gidan hankalinta baya jikinta, domin bacin rai dakuma tunanin baya ne yaketa bijiro mata a cikin ranta, side din Ummy suka yada xango inda hankalin Nana gaba daya yatafi kan taje taga Xarah, saidai ita tamada kawaici saita tsinci kanta dajin kunyar ratsawa cikin mutanen domin tafiya can gidansu xaran harma tanemo inda take.


Zarah ce a kwance a dakin tun safiyar yau takejin wani sanyi yanabin duk wani huji na gashin gangan jikinta, ga kuma faduwar gaba data farka dashi wayarta dake ringing ne yasata jin faduwar gaban nata ya tsananta, xaro wayan tayi a qarqashin pillow nta, ganin my paramour a fuskan wayar ne yasata yin murmushi bawanda yasan tanayi domin hayaniyar da aketayi a cikin dakin...



Daga wayar tayi ta kara a kunnenta my star ya hidima yau tun sape baki kirani ba, nikadai naketa aikin kiranki, murmushi taimishi maidan sauti, idan xata iya tunawa Kiran da yayi mata a tsakanin Daren jiya dakuma safiyar yau bashakka xata iya cewa xaifi hamsin a qiyasin ta, don wani lokacin baida abin cewa saidai yayita kame Kame idan yakirata, ita kuwa idan tagane hakan saitayi qoqarin kashewa amma saiya hanata ta hanyar cemata tacigaba da hidimarta amma ta tabbatar yanajin muryanta, haka xatabar wayar tayita hira da qawayenta hardai yagaji ya kashe.


A wannan karon cemata yayi yana son ganinta, shagwabe mishi tayi snn tafara magana kamar yana gabanta, haba Yaya nah ta ina xan ratso cikin dubban nan jama'ar nan intafi gidan Ku, Kasan dai xa'a gane gurinka xanje ko?


To saime? Yabata amsa, akwai Wanda xai hanaki xuwa amsa kiranda nai miki ne? Babu amma nidai inajin kunya babu damuwa Xarah tah baifi saura 'yan awanni bane mu mallaki juna inganki a dakina a
akan gadona a....... Wayyo nikam kadaina banaso tafada tana dariya, shima dariyan yayi yace karki ji komai xarah na I will be gentle to you kinji? Naji kawai ta iya fada, sunjima suna hira kapin daga baya sukai bankwana akan saiya kirata.


Tana ajiye wayar kiran Nana yashigo cikin wayar Nata, nan suka gaisa har Nanah na tsokanarta, itakuma Xarah sai cemata tayi yanxu bakixo ba? Lallai nayi fushi dake kuma baxan qara xuwa gidanki ba.


Kiy haquri kimaida wuqan ina gidansu Ango kinsan bantaba xuwa gidannaku ba, gashi jama'a suncika narasa tayamda xanfara kutsowa cikin gidan, haba dai to shknn bari insa a taho dake, to shiknn, nan suka katse kiran.


Humairah ce tashigo aiko Nanah tasanar da ita uxirinta, hararar ta tayi snn tace wlh Xarah kin rainani kodai kina mantawa nice babba akanki ne? Kiyi haquri ta langabar da kai, domin ita yau vatajin masifa nan ta lallabeta tasamu taje mata, Dan qaramin tsaki tayi tace himairah matsala.


Tahowa sukayi a tare har cikin dakin da Xarah take tareda qawayenta, nan sukahau hiran su, humairah ce tace Xarah wlh kuna kama da Autyn su Yasmin pa, dariya sukayi itakuma taqara da cewa kinsan Allah dagaxke kuna kama abar batun wasa.


Sauran qawayensu taiwa magana nan suka mammatso kowa kuwa yabada shaidar suna kama, saidai Xarah tafi Nana haske, Xarah bata gama amincewa ba tace dasu a dakata, wayarta taxaro tadaukesu photo ta turawa ibbyn ta a watxapp snn takirashi tace yahau watxapp ta tura mishi wani Abu.



Mtswwwwww tsaki qawayenta sukayi sukace mata kedai wlh Xarah anyi jarababbiya ace komai saikin sanar dashi? Banxa taimusu tafara waqa tana fadin soyayya da dadi nayarda dakai masoyina duk don taqara basu takaici, aikuwa hakan yafaru domin himairah kasa haquri tayi ta haye kan gadon, nan suka hau damben wasa kamar dai yanda suka saba matuqar suna guri daya, dariya akai ta musu domin inda sabo sun saba da halin Xarah da humairah.



Nanah ce taita kallonsu da sha'awa tana ayyanawa a cikin ranta inama ace itama tana cikin farinciki, kuma tana cikin Ahalinta ahaknma tana godiya da Allah domin tafara tunkaran jin dadin rayuwa tunda tasamu miji takuma hadu da mahaifinta suna cikin wadata da kwanciyar hankali, amma rashin mahaifiya babban gurbi ne.



*Gurin daurin Aure*


Masallacin dake qofar gidan cike yakeda mutane maqil, babu masaka tsinke manyan masu kudi daga kasuwa har qusoshin gwamnati, motoci kuwa har titin layin saida suka kashe domin yin parking.



Angwayen ne nahango suna qoqarin Shiga cikin masallacin gaba dayansu Anko din fararen kaya ne a jinkinsu sunsha babban Riga, takalminsu baqaqe ne, hularsu iri daya buhariyya, amma kalar na ango ya banbanta da nasu, domin cewa yayi baxaisa komai irinnasu ba don baxa'a tantance ba.



Sun matuqar yin kyau cikin shigarsu ta alfarma, idan ka kalli ibby farinciki da annashuwan dake kwance akan fuskarshi ne xai tabbatar maka dacewa shine Angon domin bakinshi yakasa rufuwa, inda shikuma Aliey kyanda yayi dakuma kwarjinin dayayi ne xai sa ka kasa tantance kodai shima auren xa'a daura masa ne. Yayi kyau harya gaji da haduwa, kowa sai binshi da idanu yakeyi duk Inda ya ratsa.


Anyi addu'oi angabatar da siga andaura aure tsakanin ibraheem da fatimatul~xarah akan sadaki naira dubu Dari lakadan ba ajalan ba.



Fitowa sukayi aka fara gaggaisawa da 'yan uwa da abokan arxiki, inda akaita daya ibby murnan aure, inda wani abokinsu mai suna mujahid yace mishi to saika dage nanda awanji Biyar ka jefa kwallonka cikin Raga, mudan cewa ka auri Xarah tauraruwa kamar yanda kake fadi.


Dariya yayi yakai mishi dukan wasa shikuma ya goce, yace mishi kallo daya xakai min Kasan ni jarumi ne ba malalaci ba, suka Dan taba barkwanci snn suka shige motocin su domin wucewa gurinda aka tanada domin gudanar da reception.



Suna Shiva cikin mota yakira xarah, daga wayar tayi yasanar da it a cewar yanxu taxama nashi domin andaura auren su, godiya taiwa mahalliccinta snn tace Allah yabani ikon yimaka biyayya mijina, nan tafashe da kuka Wanda takasa tantance na menene farinciki ne kokuma jimami domin ba shakka itama tana tunanin ahalinta.


Nanah tamatso ta dafata domin a yanxu sukadai ne a cikin dakin, wawaye gaba daya suntapi wani daki domin shiryawa, kiyi haquri kinji kikuma godewa Allah domin anmiki auren gata,nan itama kuka ya kwace mata me qarfi.



Mummy ce ta tsame jikinta dakyar tanufi dakin mama, samunta tayi tana karatun qur'ani domin tanemi alfarman mummy tabarta ta kebe gurinda babu hayaniya sosai, tanason ta kebance domin Shiga hayaniyar xai iya sata jin komai yadawo mata sabo.


Ah ah karatu kikeyi ne? Saida Takai qarshen Aya snn ta juyo da murmushi akan fuskarta ta amsa ta, xama tayi a gefenta snn tadafa kafadarta tasanar da ita aure ya dauru, tanuna jin dadinta sosai tafara godewa Allah Wanda daga qarshen godiyan kecewa tayi dakuka mai cike da tunani daban daban.



Dakyar mummy tashawo kanta ta tsagaita da kukan, dago jajayen idanunta tayi ta kalli mummy snn tace mata inason inga Xarah, mummy ce tayi murmushi tace yanxu kua, tashi inkaiki gurin diyata Amarya............



😍😍🤝🏼 Anatare
Mummyn Fadyl CE



🎲🎲TUDUN DAFAWA🎲🎲


Rubutawa....MUMMYN FADYL (Fatyma Muhammad Adamu)

Wattpad @ *fatimamuhammadadamu*


INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION*
*[onward together]*
*{we give the reader's of ours the best out of the bests,, our inks are melodious and dropping a kinda lights to reader's}*
```THE PEN OF LOVE😘 HEAT TORCHING❤ TEAR OF SORROWS😭 CURDLES😊 GIGGLES😁 AND MARRIEGE THINK💑```
*```JUST GIVE US FOLLOW..**



Fitowa ta. 6⃣5⃣



Gaba taiyo itakuma tana biye da ita a baya, taron jama'ar daketa zarya a cikin gidan yasa mummy biyowa dasu ta qofar baya, qawayen Xarah ne suka fara gaisawa dasu, inda himairah take cewa mummy, Xarah pa mummy haryanxu batai kukan an daura mata aure ba.


Mummy ce tai dariya snn tace ai dadina da zarah itace maganin irinku 'yan sa ido, indai zarah ce sai xuciyarku tayi bindiqa da takaicinta, dariya sukayi dukansu snn suka nupi cikin dakin.


Nana ce xaune a bakin gadon, sai zarah dake hakimce a tsakiyar gadon tana waya da ibbynta, Nana ce ta amsa sallamar ganin matar dake bayan mummy yasata miqewa zumbur tareda fara goge idanunta.


Itakuwa mama kasa motsi tayi banda hannunta datake ta nunawa, Nana kuwa murxa idanunta taketayi alamar tagaxa gaxkata abunda take gani.


Xarah da mummy kuwa sai rambayarsu sukeyi cikin tashin hankali amma sungaxa samun amsa daga gurinsu duka biyun.


Abubuwa ne suka fara yawo acikin kwakwalwar Mama batasan sanda tayanke jiki tafadi ba, kanta sukaiyo gaba dayansu Nana ce tafara magana tana fadin nashiga uku naga samu naga rashi yaxanyi da rayuwata, sai yaushe rayuwa xataimin dadi?


Bawanda yakula da abunda take fadi acikinsu domin bawanda yake cikin hayyacinsa, Mummy ce tadauko ruwa tafara yayyafa mata, tadayki tsawon minti biyar kapin tasaki wani wahalallen ajiyar xuciya.


Mummy ce tace mata sannu, nan tabude idanunta tace shin abunda nagani a dakinnan gaxkiya ne kuna gani kokuwa gixo ne kamar yanda yasaba yimin akullum a farke dakuma cikin mafarki?


Subhanallah menene kika gani? Suka tambayeta a tare amma banda Nana wacce tana durqushe takasa dagowa domin jitake kamar xata rasata akaro na biyu.



'Yata nagani a dakinnan, 'yarki? Suka tambayeta a tare miqewa tayi batare da ta amsa suba, hango Nana tayi a durqushe cikin xafin nama takai hannunta kan Nana, itama Nanan dagowa tayi ta kalleta wlh itace suka juyo suna kallonsu.


Nanah ce tamiqe daga durqushen da take Nana tasaki dariya mai kama da kuka domin atare takeyinsu lokaci guda.


Rungume juna sukayi, saketa Mama tayi tajuyo tadubi mummy da zarah Wanda jikinsu yagama sakewa domin suna cikin rudu da xulumin wannan abunda yake faruwa.


Sauqowa mama tayi tai sujjada kapin tadago takallesu tace tabbas babu abun bautawa dagaxkiya sai Allah, ubangijinmu yayi gaxkiya dayasanar damu cewa dukkan tsanani tana tare da sauqi, bansan tayaya xan gode mishi ba, ubangiji yamin komai koyau na koma ga mahaliccina xan tafi inamai farincikin domin burina yacika.


Nabarku cikin mamaki, kutayani godiya ga Allah, domin yau yahadani da Ahalina, wannan itace Nana 'yata, kullum ina mafarkin inda xan ganta, Allah yaji tausayina yakawomin ita har gida, nan suka juyo suna kallonta!


Xarah ce tai saurin sauqowa ta isa gurin nanah, rungumeta tayi suka kalli juna suka sakarwa juna murmushi hawaye kwance akan fuskokinsu, Xarah ce tafara magana Ashe ke 'yar uwata ce yanda nakejinki a daina jini ne yake yawo a jikina.


Narasa yanda xan misalta tun randa nafara ganinki nake jin akwai wani Abu tsakaninmu, amma nayi tunanin tayaya haka xai kasance? Nanan ce take kallonta da mamaki akan fuskarta snn tace bangane me kike nufi ba? Tayaya naxama jininki bayan nasan nikadai mahaifiyata tahaifa?


Kallon tane Yakoma kan mummy da mama, nan mama tai mata murmushi snn tasauqo ta dafata, tace Nana labarin dayawa snn yanada tsayi dafarko kifara godewa ubangiji akan ni'imomin da yayi mana, snn inason kisa a ranki zarah qanwarkice jininku daya kamar yanda kikaji tafada miki.


Idan taro yadan tsagaita xanmiki bayani, murmushi tayi itama tacewa Maman nata, nima inada albishir dinda xanmiki amma sai taron ya tsagaita kamar yanda kika buqata, mama nah wlh nayi kewarki a rayuwa ta.



Itakuwa gwanar rahoto jiyowata sukai a bathroom tana Sanar da mijinta wani abun dadin daya samesu, Myrna tayi mata sosai tare da cemata goron albishir dinta saisun hadu a gurin dinner. Dariya tayi tareda tabbatar mishi itama tanada surprise dinda ta adana mishi.



Fitowa tayi tasamesu suna maganar ta, nan kunya ya kamata, mamah ce tace Xarah bakida kunya ko? Harkin sanar dashi baki sanar da yayanki Aliey dakuma daddyn ki ba? Dariya tayi tace wlh namanta dasu ne, mummy ce takai mata dukan wasa itakuma ta goce snn tanufi bathroom din kuma da gudu.



Nan suka xauna suketa hiran yaushe gamo, mummy ko kiranta akaitayi a waya jama'a sunata nemanta, ta fitaa tabarsu, itakuma Nana kiran Haj.maryam tayi a waya akan taxo tanada albishir dinda xatai mata.


Bata bata lokaci ba ta iso dakin aiko ta taras da abun arxiki takuma yi murna tamakar itama mahaifiyarta ce dasuka rabu Allah yayi haduwarsu, itace nasanar da Nanah cewa ita xata yiwa Alhaji albishir, batace da ita komai ba domin tana matuqar kunyar ta akan al'amarin da ya shafi Alhaji, ko maganace Indai ta shafeshi bata iyayi a gabanta.



Amma tace mata a kunnenta cewar tacemishi karya sanar da Bbn ta domin tana buqatar yimusu baxata amma sai xuwa dare, dariya tayi mama tace musu to tunda abun na wariya ne ai saiku cemin infita ko?


Dariya sukayi Nana ce takamo hannun Hajiya maryam tanunawa Mamanta, tace Mama duk sauyin da kika gani atare dani wannan baiwar Allahn itace sila, har Abada halaccinsu a garemu ba abune da xa'a misalta Shiba kokuma amanta, tamin komai a rayuwa ta. Bani kadai aba a cikin Ahalina.



Mama ce takalli Haj.maryam idanunta taf da hawaye tace bansanki ba amma kinmin taimakon da balallai ne Wanda yakeda hakkin hakan yayi ba, banida bakin da xan furta godiya ta a gareki saidai inai miki Fatan gamawa da duniya lpy, Allah ya albarkaci xu'arki yasa kuma kema yaranki su ji qanki, dariya tayi domin taji dadin addu'ar a qarshe tace Amin.


Hidima aka cigaba da gabatarwa cikin kwanciyar hankali, Inda aka gama shirya kai Amarya bayan sallar isha'i domin xa'aje dinner da qarfe Tara na dare.


Bayan An idar da sallan magrib ne mummy taxo domin tafiya da Xarah sashen daddy, mama taso taqi xuwa amma mummy tanuna mata daddy ne ya buqaci hakan. Domin ta Sanar dashi komai snn shima yasanar da amininshi.


A bangaren Nana kua da yamma tasanar da Bbn ta cewa akwai inda xasuje kuma harda shi, don haka ana sallar magrib suka nufi gidan su Xarah gabadaynsu.


Kowa tana xaune a falon harsu Xarah amma ba'a fara cewa komai ba, daddy ne yaga IBBY sai kallonsu Xarah yakeyi, dariya yayi yacewa Xarah babynah tashi kidawo kuwa da mijinki ko?


Dariya sukayi a falon itakuma ta maqe kafadarta alamar baxata iya tashi tajeba, mummy ce taimata magana akunnenta tamiqe dakyar domin ba qaramin cika akayi a falon ba. Xama tayi shikuma tasaki ajiyar xuciya yacemata kokefa my star, itakadai tajishi batace mishi komai ba.

Minti biyu bayan hakan saiga sallamar su Nanah, Alhaji ne tafara sallama saikuma Bbn Nanah, abayanshi Haj.maryam ne da Nanah.



Badon dauriya dakuma taurin xuciya irinna da namiji ba, babu abunda xai hana Bbn Nanah xubewa aqasa

Please Login or Register in order to submit comment