You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

matsayin ranar da xai kaita gurin Alhajin.


*WASHE GARI*

Washe gari dasafe suka shirya suka dau hanyar katsina ana tafiya Mama tanata kallon hanya har suka isa, da kwatance har suka isa gidan, gani tayi komai ya canxa mata a cikin garin harma da unguwar.


Kamar yanda xuwansu Nana yakasance to wannan karon xuwansu Mama abun bai canxa zani ba, domin kuwa Alhajin dayake xaune a gidan bai boye musu komai ba, nadaga abunda yasani, domin shi yanxu yafara qosawa da irin binciken da ake mishi akan wannan gidan, saikace Wanda yasayi gidan gwamnati. Yayi Neman Ayashe Neman duniya baisamu ganinta ba, koxai Dan huce takaicin abunda taimishi.


Haka suka bari garin amma xuciyam mama tagama karyewa gani takeyi tarasa mijinta dakuma tilon diyarta, a qarshe ma kukane ya kufce mata, akai ta lallashinta har aka samu aka Dan kwantar mata da hankalinta.......

😍😍🤝🏼Anatare
Mummyn Fadyl CE




🎲🎲TUDUN DAFAWA🎲🎲


Rubutawa....MUMMYN FADYL (Fatyma Muhammad Adamu)

Wattpad @ *fatimamuhammadadamu*


INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION*
*[onward together]*
*{we give the reader's of ours the best out of the bests,, our inks are melodious and dropping a kinda lights to reader's}*
```THE PEN OF LOVE😘 HEAT TORCHING❤ TEAR OF SORROWS😭 CURDLES😊 GIGGLES😁 AND MARRIEGE THINK💑```
*```JUST GIVE US FOLLOW..**


Fitowa ta. 6⃣0⃣



Kamar wadanda aka raba Kansu haka suna shiga yawuce side din Haj.maryam, itakuma kamar kullum side din Nana ta wuce a falo ta isketa tana bitan karatunta.


Amarya yau kece a gidan namu, saura qiris nai fushi nace baxani ba, domin naji labarin kunfara rabon kati amma banga nawa ba, dariya tayi tace mata kiyi haquri kina raina wlh shiyasa yau muna fitowa nace takanki xan fara biyowa.


Ina muhsin ta tambaya, muhsin yanacan hannun talatu, Allah sarki mai aikinku nnan tanada qoqari wlh, ah balaipi gata dagaxkiya da riqon Amana, gashi ranar aurenku daya, amna saidai mai bawa fulayin gidannan ruwa xata aura, kinga baxamuy nisa ba.



Ayya amma dai baxai hanaku xuwa nawa ba ko? Murmushi taimata bata gajiya da kallon zarah domin tanajinta har cikin ranta, ai ana bikin magaji ake na magajiya, insha Allah babu abunda xai hanani xuwa aurenki.


Sunjima suna hira har kuwa Nana ke sanar da ita mahaifinta yana gidan yaxo, domin bata taba Sanar da ita tarihin rayuwarta ba, wannan sirrinta ne, duk da wasu lokacin takanji buqatar hakan yana taso mata.


Har ibby yagaji da jiranta yai kiranta a waya, fitowa sukayi tare da Nanan falon Haj.Maryam suka shiga cikin jin kunya Xarah ta gaidata amsawa tayi cikin sakin fuska tare da cewa Nana nikam sauda dama nakan hango kamanni tsakaninki da 'yar dakin kinnan.

Dariya sukayi gabadayansu ibby yace wlh nima nagani, Nana ce tabasu amsa da cewa shaquwarce tai yawa ina fatan baxakai min rowanta bayan karaba mu da ita ba, Insha Allah yafada yana miqewa sukai musu rakiya suka wuce.


A hanya yakecewa da ita My star ya akayi ne nikam kika saba da matar nan? Dariya taimishi snn tabashi labarin yanda suka saba da Nana, ya sunanta yajefe ta dawani tambayan, Tabdi ni wlh bansan asalin sunanta ba, Aunty amarya kawai nake ce mata. Da wannan makamantan hirarrakinsu sukaita yawo a gari, qarshe suka zarto gida.




🎲🎲TUDUN DAFAWA🎲🎲


Rubutawa....MUMMYN FADYL (Fatyma Muhammad Adamu)

Wattpad @ *fatimamuhammadadamu*


INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION*
*[onward together]*
*{we give the reader's of ours the best out of the bests,, our inks are melodious and dropping a kinda lights to reader's}*
```THE PEN OF LOVE😘 HEAT TORCHING❤ TEAR OF SORROWS😭 CURDLES😊 GIGGLES😁 AND MARRIEGE THINK💑```
*```JUST GIVE US FOLLOW..**


Fitowa ta. 6⃣0⃣



Kamar wadanda aka raba Kansu haka suna shiga yawuce side din Haj.maryam, itakuma kamar kullum side din Nana ta wuce a falo ta isketa tana bitan karatunta.


Amarya yau kece a gidan namu, saura qiris nai fushi nace baxani ba, domin naji labarin kunfara rabon kati amma banga nawa ba, dariya tayi tace mata kiyi haquri kina raina wlh shiyasa yau muna fitowa nace takanki xan fara biyowa.


Ina muhsin ta tambaya, muhsin yanacan hannun talatu, Allah sarki mai aikinku nnan tanada qoqari wlh, ah balaipi gata dagaxkiya da riqon Amana, gashi ranar aurenku daya, amna saidai mai bawa fulayin gidannan ruwa xata aura, kinga baxamuy nisa ba.



Ayya amma dai baxai hanaku xuwa nawa ba ko? Murmushi taimata bata gajiya da kallon zarah domin tanajinta har cikin ranta, ai ana bikin magaji ake na magajiya, insha Allah babu abunda xai hanani xuwa aurenki.


Sunjima suna hira har kuwa Nana ke sanar da ita mahaifinta yana gidan yaxo, domin bata taba Sanar da ita tarihin rayuwarta ba, wannan sirrinta ne, duk da wasu lokacin takanji buqatar hakan yana taso mata.


Har ibby yagaji da jiranta yai kiranta a waya, fitowa sukayi tare da Nanan falon Haj.Maryam suka shiga cikin jin kunya Xarah ta gaidata amsawa tayi cikin sakin fuska tare da cewa Nana nikam sauda dama nakan hango kamanni tsakaninki da 'yar dakin kinnan.

Dariya sukayi gabadayansu ibby yace wlh nima nagani, Nana ce tabasu amsa da cewa shaquwarce tai yawa ina fatan baxakai min rowanta bayan karaba mu da ita ba, Insha Allah yafada yana miqewa sukai musu rakiya suka wuce.


A hanya yakecewa da ita My star ya akayi ne nikam kika saba da matar nan? Dariya taimishi snn tabashi labarin yanda suka saba da Nana, ya sunanta yajefe ta dawani tambayan, Tabdi ni wlh bansan asalin sunanta ba, Aunty amarya kawai nake ce mata. Da wannan makamantan hirarrakinsu sukaita yawo a gari, qarshe suka zarto gida.




Lami ce kwance akan Dan yadin tabarman ta, duniya taimata qullin goro, tarasa yaxatayi da rayuwarta domin ko daga yatsanta ta motsa shi ya zame mata aiki, babu mai taimaka ma, intana jin fitsari haka take Jan jikinta tayi a gefe,koko kashi dakinta kam Sam baxa'a iya shiganshi ba domin ko ina wari yagama dashi.



Tarasa meyake damunta domin bata iya dukan nan bane yaja mata wannan bala'in amma shine sanadin komai datake ji a gangan jikinta.



Yau nema tadanji dama dama, harta fito bakin qofan dakinta, jan jikinta tayi tadebi ruwa tasha aiko nan cikinta yanemi qullewa domin babu komai acikin sa, yunwa yagama cinyeta inka kalleta xakai tunanin shekara goma tayi tana fama da cuta.



Amma dayake macece marar tunani tanacin qanxo tadan ji qarfin jikinta aiko ta tattari kudaden tayi gidan sabuwar uwar dakinta datayi hatsabibiya wacce tasan kan bibiyar bokaye, agurin Maye suka hadu da ita.



Anace da ita Mama Attu taje ta tsigale Maye ciki da waje tareda yimishi alqawarin itace ajalinsa, domin taje bokannta yasanar da ita ankarya mishi laqaninsa amma bai daina rudan mutane yana karban kudi a hannun su ba.



Hakan da Lami tagani shiyasa ta qoqarin shiga jikin Mama Attu, dakyar ta amince amma saida taiduba da irin rashin wayon Lami tasan xataci ajikinta.



A qofar gida tasameta cikin shiganta na fita anguwa domin harda jaka a hannunta, ganin Lami yasata sassauta fuskanta Wanda da yake a tamke kamar hadari.


Gaisawa sukayi tareda tambayar Lami din hatsari kikayi ne naganki bakyan gani? Dayake ita bawai ta iya duniyar bane nan ta kwashe komai tasanar da Attu, a xuciyar attu tace faduwa yaxo daidai da xama, xan ribantu dake.



A zahiri saita sako fuskar tausayi da jimami ta sanyawa fuskarta, ayya sannu amma yanxu kam anxo wajen don yanxu haka Nima ganina dakikayi gurin malami na xani akan wata matsala data kunnomini, kinga saiki miqo naki aikan in hada duka ingabatar mishi dasu.



Lami har cikin xuciyarta bata gama aminta da shawaran Attu ba, hakan yasa cikin jimami ta tambayeta baxai yiwu muje tare bane?


Ahh baxai yiwu domin ni kaina bawai ina samun ganinsa bane, Yaya tah nake baiwa saqon ta Isar gareshi nidai nawa amfani da magani ne, inkuma kinaga baki amince ba saikiyi gaba domin ni sauri nakeyi, koda taji haka tai saurin xaro kudaden.


Ganin kudin yasa Attu sakin ajiyar xuciya ahankali, Lami ta qirga kudi cass dubu saba'in da bakwai ta baiwa Attu, itakuma tasa hannu takarba sukayi bankwana akan jibi xata kawo mata magunguna.



Har ta bule Lami bata daina waiwayenta ba, haka taji a ranta kamar Attu batada gaxkiya amma saita daure tasawa xuciyarta amincewa da Attun.


Itakuwa Attu tana isa Tasha tashige motar garinsu wato yola, saida tafiya tafara nisa snn tadauko kudin taimusu kyakykyawar ma'ajiya snn, ta bushe da dariya a xuciyarta tace lallai kinyi ragon Axanci.


Har akai kwana uku Lami batani labarin Attu ba, haka yasa jiki babu qarfi ta shirya tafita domin xuwa gidanta, tana fita yayi daidai da fitowar Baffan sadiya, aiko cikin faduwar gaba haryana tuntube takoma ta labe tabayan qofa, domin bata manta kashedin dayay mata ba.


Saida ta tabbatar ya fita snn itama tarufa mishi baya, tana tafiya tana tufka da warwara, har ta is a gidan Attu, ganin cicirindon mutane yasata jin faduwar gananta ya tsananta, da sanyin jiki ta qarasa gurin mutanen.


Samun daya saga cikin mutanen dake gurin tayi ta tambayeta meke faruwa, tana haki cikin fushi take bata labarin abunda yake faruwa akan, kudin Adashe ne suke Tarawa a hannun Attu a matsayinta na uwar Adashe, Ashe macuciya ce domin ta tattara kudin al'umma sama da dubu Dari tayi gaba, takuma tattara komai nata annemeta an rasa.


Ai lami bats qarasa jin sauran bayanan ba sakamakon jirin daya kwasheta yazubata da qasa aiko nan mutane sukaiyo kanta , ruwa aka kwaso aka fara yayyafa mata, amma tana farfadowa idan ta kallesu sai kaji tace Attu Attu, saita qara sumewa...


Wata daga cikin gidan hayan da Attu taxauna, taimata alfarma akan ashigo da ita ciki domin tadan huta ko hankalinta xai dawo jikinta, haka akai tangare gare da Lami aka shigar da ita ciki.

_WNN KNN_


Yaune Alhaji yagama shiryawa Ayashe gadar xare shiyasa ya amince domin yakaita gidan Alhaji, badon tasamu wani Abu ba, saidon a rufta da ita. Domin yaji komai dangane da yarinyar da tabashi yakaiwa Alhajin a bakinta.



Bayan sun isa ne, taga ai tasan gidan ma, domin ta taba xua gidan lokacin ana biki, amma saita boye mamakin ta cikin salon iya bariki tace, wato Alhajin nan ma yasan harka knn?


Dariya yayi mata snn yace yanxu kuma wa aka bari a baya? Dukansu dukai dariya, ce mata tayi tashiga yayiwa Alhajin bayaninta tace kawai tana Neman Amarya, domin agurinta yarinyar take..

Jin haka kanta tsaye ta wuce cikin gidan bata nemi akaita ba domin tasan side din Amaryan, sabida haka da sallama tashiga.




😍😍🤝🏼Anatare
Mummyn Fadyl CE





🎲🎲TUDUN DAFAWA🎲🎲


Rubutawa....MUMMYN FADYL (Fatyma Muhammad Adamu)

Wattpad @ *fatimamuhammadadamu*


INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION*
*[onward together]*
*{we give the reader's of ours the best out of the bests,, our inks are melodious and dropping a kinda lights to reader's}*
```THE PEN OF LOVE😘 HEAT TORCHING❤ TEAR OF SORROWS😭 CURDLES😊 GIGGLES😁 AND MARRIEGE THINK💑```
*```JUST GIVE US FOLLOW..**



Fitowa ta. 6⃣1⃣


Da sallama Ayashe tashiga, itakuwa Nana tanacan dakinta jin sallama yasata amsawa tare da fadin inaxua, jin an amsa yasa lami yiwa kanta mazauni a daya daga cikin kujerun dake malale a cikin falon.


Baquwa mukayi........... Maganarta ne yamaqale a fatar bakunta domin arba datayi da fuskar Ayashe, a bangaren Ayashe kuwa motsi ma gagaranta yayi a gurinda take xaune.


A fusge tace meya kawoki nan gurin Nana, dakewa Nana tayi cikin qarfin xuciya tace keya kamata intambaya mekike min a gida, tayaya xaki sameni a cikin gidan shi kitambayeshi meya keyi?



Mutuwa ce tagifta tsakaninsu domin ko bakinsu nauyi yayi musu, sungaxa tabuka komai qarshe sai Ayashen ne tayi ta maza tamiqe xata fita, cikin xafin Nama Nana ta hanxarta ta isa ta kulle qofar falon tare da ce mata harkin isa kishigo har inda nake amma kitafi cikin sauqi.



Bansan da guxirin sharrin da kikaxo ba amma ina tabbatar miki wlh yanxu nafi qarfin jahilcin ki, idan Ada kin cutar damu kin share to kisani Allah yana juya al'amarinsa yanda yaso akuma duk lokacinda yaso.


Kallo daya xakiymin kisan nawuceki nesa ba kusa ba, kin kaini inda kike da nufin saidamin mutunci na inda xa'a keta haddina a wulaqanta ni, tana kuka tacigaba da fadin, amma dayake ban zaluntar dakeba saigashi addu'ar danayi alokacin da kika kaini gidan mala'iku suntayani miqawa gurin ubangijin rahama shikuma ya amsa min, nazamo 'yan tacciya maimakon wulaqan tarciya.


Hannu tasa akan dining tadauko wayarta numban Haj.maryam tafara dialing cikin daqiqan da bai wuce buyu ba tadauka, kit saurin kixo sashena don Allah, abunda ta iya fadi knn ta katse kiran.


Nan take hanjin cikin Ayashe ya kada, tsoro qarara ya bayyana akan fuskarta itama wayarta ta jawo tafara dialing numban Alhaji aiko switch off taji, nan hankalinta yatashi har tarasa inda xatasa kanta taji dadi.


Bbn Yasmin takiran shidinma kiran gaggawan tai mishi inda bashiri yabaro gurin aikinshi hankalinsa a tashe domin bata taba yimishi irin wannan kiran ba, komenene yafaru sukansan dabaran da xasuyi amma basa tasoshi daga gurin aikinsa.

Haj.maryam cikin Sauri kamar meshirin tashi sama tanufo cikin side din Nanan tana xuwa tafara buga qofa babu qaqqautawa domin tajishi a rufe.


Nana ce taqarasa bakin qofan tace ki rufe qofan falon, Haj.maryam dasauri ta rufe shi snn NANA tabude mata qofan shigowa tayi, nan kuwa tayi arba da fuskan Ayashe sharkaf da xufa sai wuwwulla udany takeyi.


Meke faruwa? Haj maryam ta fadi cikin zaquwa taji abunda yafaru, nuna Ayashe tafarayi da hannunta snn tafara yimata bayani cikin kuka.


Zaro idanu Haj.maryam tayi waje tare da fadin yanxu baiwar Allah duk uquban da kikasa bayin Allahn nan ciki bai isheki ba, harsai kin biyota gidan aurenta? Tome kikaxo yi? Ayashe jin ance gidan auren Nana hakan yaqara hargitsa lissafinta, itakuwa Haj.maryam cewa Nana tayi mekike jira kin kira Bbn Yasmin?



Nakirashi tafada cikin sheshsgeqar kuka, suna cikin haka sukaji ana knocking Haj.maryam ce taje bude qofan, hanya tabashi yawuce itakuma tamaida qofan tarufe.


Yanda akaiwa Haj.bayanin Ayashe haka sukaiwa Alhaji, yasha matuqar mamakin qoqarin Ayashe da har ta iya qara kawo kanta gidan, nan shima yakirawo Bbn Nanan akaxo aka taru a falon.


Bbn Nana yana shigowa yaci karo da fuskarta baisan lokacinda bakinahi tafara bari dakyar ya iya furta Ayashe....itama qara shiga rudu tayi dalilin ganin mal.habu a wannan gidan, ga mamaki qarara akan fuskarta dakuma train tambayoyi, amma tsoron dayake cinta yadanne komai.



Ayashe meya kawoki inda muke kpdai kinxo qara tarwatsa sauran fadin cikin danake lallabawa ne? Menai miki Ayashe meyasa saini kadai, shin babu wani namiji ne a duniyar nan saini? Xuciya ce tadibeshi yayiwo kanta gadan gadan babu Wanda yayi yunqurib hanashi, domin sunbarshi kodan yarage xogin da yake cikibshi akan ta.


Saida yayi mata lilis ganin xaiyi barna yasa Alhaji yamiqe yariqeshi yafara bashi haquri kunyar Alhaji dayakeji dakuma nauyinsa da yake gani ne kawai ya ceci Ayashe a hannunsa yakoma gefe yana maida numfashi, itakuwa ko motsin kirki ba ba iyashi takeyi ba.


Alhaji ne yadaka mata wani gigitaccen tsawa yatambayeta meya kawo ta, tare da jaddada mata matuqar tai mishi qarya acikin maganar da xata gayamishi yanada hanyar da xaigano gaxkiya, matuqar yagano gaxkiya dakansa kua tasa a ranta xaisa a wulaqanta ta, kuma xata dauwama a gidan yari.


Jin an ambaci gidan yari yasata qara gigicewa nan ta xayyane mishi komai, dariyan da yasaka ne yasa kowa maida kallonshi kan Alhaji, saida yayi dariya son ransa snn yace.


Lallai kin tabka babban kuskure Wanda yaxo daidai da laipinki, Wanda ya kawokin ma ai yabar qasar, domin bayan kiran da kukaimin ina gurin aiki yakirani yasanar min yabar qasan, wayyo Ayashe tafada da qarfi tamiqe tana fadin nashiga uku yagudu da kudina.


Kowa a gurin kallonta yayi anai mata kallon wawuya, itakuwa haukan ta taken yi tamkar wanda ta zauce, duk kudinda ba'a tarashi ta hanyar arxiki ba to wlh baxa'a cishi da kwanciyar hankali ba.



Alhaji ne yatambayi Bbn Nana akan wani hukunci yakeso ayi mata? Bbn Nana yace baya buqatan ai mata komai, yabarta da fitowan rana da faduwarshi yasan duk rintsi Allah baxai barta ba, xaijira har lokacin da ubangiji xai kwatar musu hakkinsu akanta, domin ganinsu cikin kwanciyar hankalinta da wadata datayi ma kadai ya isheta rashin kwanciyar hankali.


An yaba mishi sosai da irin tawakkali dakuma tsananin tausayinshi, dahaka aka sallameta, tafiya takeyi kamar xata xube qasa, mai adaidaita ta tara yakaita qofar gidanta, amma tana xuwa tasamu babu komai acikin gidan domin kuwa ansanar mata ai tun shekaran jiya aka kwashe komai na gidan ankuma saida gidan, domin yanxu me asalin gidan ne, yaturo ai mishi Dan wasu gyare gyare.



Bata San lokacinda ta tsuguna agurinba, domin kuka ma Ashe rahama ne, domin a yau nemandhi tayi tarasa, batada komai sai Dan kudaden da yake cikin jakanta saikuma gwal dinda ke jikinta na dankunne, sarqa dakuma zobe.....



A lokacin tadauki damaran bin hanyar nijar, ba ita ta isa garin maradi ba, sai misalin qarfe biyu ba dare, maimakon takwana a koda tasha ne, a'ah mummunan nufinta bai barta tarufawa kanta a siri tabari gari ya waye ba.


Haka taiwa masu mota bayanin inda takeso akaita, amma sukaqi domin daji ne meban tsoro, dakyar wani mai mota mai kwadayin tsiya ya amince sukadau hanya.



Tafiya sukayi mai tsayi kamar na yada dan shege, saida sukaxo gab da shiga qauyen, barayi suka tare su, cikin tsoro Ayashe tai aniyan neman inda xata boye gwala gwalanta, amma haqanta bai cimma ruwa ba, domin da duka suka fito dasu, cajesu sukayi sosai suka kwashe komai a hannunta, suka kora me Motan domin suna amfani da mata.


Basu jira komai ba suka haiqewa Ayashe su kusan biyar saida sukayi amfani da ita, na qarshen yace dasu matar nan oga xaiso irinta, haka suka wurga ta a mota babu alamar sassauci ko tausayi a tare dasu.


Har xasu tada motar ogansu yace karfa mukaita tunda kunga yau bamuyi ciniki dayawa ba, kawai muraba Dan abunda mukasamun inyaso muce mishi 'yan sanda ne suka biyo mu, dakyar mukasha, dariya sukayi gabadayansu suka kumayi amanna da shawaransa.



Bude motar sukayi sukaiyo wurgi da ita waje, suka bar gurin a sittin, dai sanyin asuba ne yataimaketa gurin qaramata kuxari ajikinta.


Jikinta duk jini ga masifaffen yunwa da yake cinta,tunowa datayi da halinda take ciki ne yasata kurma uban ihu, takuma manta da halin da takeciki, da gudu tayi cikin dajin taita ratsa ciyawu har ta isa gurinshi.


Xata shiga taji an wuntsulota waje, haka taji, aiko nan taji murya kamar daga sama, ansanar dani bakyajin magana, kinje gurin mai buxu yace mikinkarki tsananta akan matunen nan, shine kikaxo ko? To kamar yanda yasanar dake baxakici nasara ba, augurin nawa ma haka abun yake, nan taji an wurgo mata wani abun kamar tumbin sa, wari ne tafara qoqarin gugitata kapin wani masifaffen qaiqayi yafara bin duk wani sassan jikinta.

Ihu tafara yi can taji hankalinta naneman gushewa, batasan ya akayi ba utadai ta tsinci kanta a bakin titi, qaiqayin ne yake qara tsananta snn a duk inda ta qaiqaya quraje ne masu ruwa tamkar bororon wuta haka yake mata, ihu takeyi tana qaiqayi kamar xautacciya.......

😍😍🤝🏼Ana tare
Mummyn Fadyl CE


🎲🎲TUDUN DAFAWA🎲🎲


Rubutawa....MUMMYN FADYL (Fatyma Muhammad Adamu)

Wattpad @ *fatimamuhammadadamu*


INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION*
*[onward together]*
*{we give the reader's of ours the best out of the bests,, our inks are melodious and dropping a kinda lights to reader's}*
```THE PEN OF LOVE😘 HEAT TORCHING❤ TEAR OF SORROWS😭 CURDLES😊 GIGGLES😁 AND MARRIEGE THINK💑```
*```JUST GIVE US FOLLOW..**



Fitowa ta. 6⃣2⃣



Haka taita fama da uquban wahala gata a qasan da banata ba, batada hanyar da xata koma qasarta mahaifarta, babu mahaluqin dayake mata kallon hankali balle tai tunanin xata samu mai tausaya mata, ko ina taje sai kyara da hantara saboda warin da jikinta keyi.



Lami ce kwance a kwananta na hudu a gidan Attu, matar ce ta iso gareta tace da ita, gaxkiya Lami nagaji da wannan jinyar naki Abu kamar cin kwan makauniya yaqici yaqi cinyewa? Babu dangin iya babu na Baba baxan iyaba maganar gaxkiya ki tattara kisan inda dare yayi miki.


Da kodaddun idanunta tadago ta kalleta, itakadai dakuma ubangijinta sukasan axaban da takeji a gangan jikinta, amma wannan matar batabi takan yanayinta ba taci gaba da surfa mata ruwan bala'i harsai da tasata ta dingusa dakyar tabar mata gidanta.



Dubawa tayi gabas da yamma bataga inda xata nufa domin Neman taimako ba, haka tadinga Jan jiki tanabin inuwa har tasamu dakyar ta isa matsugunin ta.



Bata samu xarafin shiga cikin gidannata ba sakamakon mai gidan data taras yaxo karban 'yan kudadensa domin shekara taxagayo samunta yayi a duqun qune a gindin bishiyar qofar gidan.


Matsowa yayi suka gaisa da dasashshiyar muryarta ta marasa lpy, nan yake sanar da ita cewa yaxo yafi sau goma baya samunta akan kudinsa, yayiwa maqpcinta magana tunda shiyayi jagora gurin kama gidan, amma meshi yace mishi yajirata duk lokacinda suka hadu suyi magana, domin shibaida hadi da ita.


A zabure tadago ta dubeshi duk da rashin jindadin da takeji a duk gabobinta hakan baihana damuwar da tashiga ta nuna ba, cemata yaqarayi Yaya kuma ina miki maganar kudi xaki tsareni da idanu?


Hawayene yafara zirarowa akan fuskarta tasjiga yimishi magiya akan danta daxai biya mata kudin bayanan snn ita batada komai domin yau sati daya kenan da aka damfare ta.



Dayake bawai yanada kirki bane, ko gexau baiji ba, yayi mata rashin mutunci tareda shiga cikin gidan dakan shi har uwar dakinta yafara watso 'yan kayayyakin ta waje babu tausayi bare kawaici, a qarshe ya wullo mata 'yar yadin tabarman ta.


Tana kuka ta tattara abubuwan nata guri daya, nadama ne yafara shiganta Wanda bata taba yin irinshi ba a rayuwarta, A yaune tayi Allah wadai da xuciyarta Wanda babu komai a cikin ta face tsantsan son kai, ta tsani mayaudariyar xuciyarta, ayaune tafara tunani dakuma Dana sanin abubuwan da ta aikata munana a baya, yau gashi an wayi gari taxama wulaqan tacciya, batada mai qaunarta babu mai tausayinta yau gashi inda xata xauna ya gagareta.


Tana durqushe a gurin tana kuka kamar ranta xai fita, a sarari take magana tana fadin " Inama ban cutar dakeba zainabu nasan duk hakkin kine dana 'yarki suke bibiyar rayuwata, da ban dagaki a Kansu ba da haryanxu ina tare dake dakuma mijinki cikin Aminci, Ayashe har inkoma ga Allah baxan yafe miki ba kin cuceni gashi yanxu nice a cikin wahala ke kinacan cikin daula, Allah kasaka min.


_Bakisan itama Ayashen halinda take ciki bane, dabaxakiy magana ba, kina maganar sakayya ai sakayyar kuke gani keda ita._

*Allah muna roqonka ka tsarkake mana xuqatan mu, kahanemu cutar da bayinka takowace siga, ya Allah karka bari a cutar damu ka tsaremu katsare mana imanin mu, Allahumma Amin* 🤲🏼



Batasan iya awannin da tadauka a wannan gurin ba, tun tanajin rana yana tafarfasa ta hartaji ranan yayi sanyi, dagowa tayi taga yamma tayi daidai dakuma dawowar baffan Sadiya, tun shigowansa Layin ya ganta amma yadauke kai gefe kamar baisan dawata halitta a gurin ba.


Ganin dagaxke yayi kamar bai ganta bane yasata miqewa dasauri kamar xata kife a gurin sakamakon jirin da yake dibanta, qarasawa gurinshi tayi tareda kiran sunanshi.


Kamar baxai amsata ba amma haka ya juyo, fuskarnan a tamke babu alamar rahama ko sassauci a tare dashi, hakanne yasata shan ruwan jikinta guri daya, tadan tattaro nitsuwa ta axawa kanta, snn tafara sanar dashi abunda yake faruwa.


Shikuwa tamkar baitaba saninta ba yace mata to ai babu abunda xan iya yimiki akai domin kuwa ni banida kudin da xanbashi yabarki ki xauna, snn baxan qara gangancin saki ki xauna a gida ba, domin Wanda nayi a baya ma tsautsayi ne na rashin San in ainihin ke wacece kuma gashi alhakin taimaka miki danayi kika xauna a gidana haryamxu baidaina bibiyata ba.



A don haka inamai baki shawaram kisan Inda xakisa kanki, kamar yanda nagaya miki a baya yanxuma xan nanata miki wlh xan wulaqantaki idan kika qara gigin nuna kinsanni, daga fadin haka yashige cikin gudansa yabarta dagalo da baki.


Har dare yafara yimata nan ta yanke hukuncin tafiya tasha koxata samu gurin kwana ga yunwa dayake damunta domin duk wani hanji na cikinta kokuwa da juna sukeyi suna son asaka musu wani Abu domin su warware.


&&&&&&&&&&&&


Shirye shiryen biki akeyi sosai da sosai babu kama hannun yaro, yau saura kwana biyu daurin aure kuma yaune suka fara programs dinsu sakamakon daddy dayace Sudan tsagaita programs din bayason bidi'ar tai yawa.



Da yammacin ranar aka fara halarta a gurin taro, Amarya tana cikin gida itada qawayenta sai rawankai taketa yimusu, duk bayan Minti biyar saitayi waya da ibby domin tasanar mishi yanxu angama kaxa ta bangaren kwalliyarta shima kuma haka.


Qawayenta sai tsiya suke mata musamman humairah Wanda cemata takeyi sai
kace akanta xa'a fara aure, koba akaina xa'a fara aure ba inada tabbacin nice mace tafarko da xata fara dacen nagartaccen miji a duniya, mai kyau kwarjini dakuma tarin ilimi, uwa uba sakin fuska barkwanci da sanin darajan Dan Adam.


Kwashewa dakin sukayi gaba

Please Login or Register in order to submit comment