You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

aikinka snn xan 2ro maka kudin da xakabawa uwar dakinnata yana kai nan a maganar nashi yayi diff yakashe wayarsa.


Dayake a hands free yasa wayar shiyasa babu amfanin tsayuw yimata bayani tunda taji komai da kunnenta, Tabdi jam Abu baiyi dadi ba wlh bari intafi gida, nasan jama'a xasu taru bawuya amin sata, amma ka tabbatar anayin uku katahomin da duk kudadena karka bari inqara xuwa gidanka haduwarmu baxatayi kyau ba. Tana gama fadin haka tajuya ta tafi abynta.


Shikuwa baffn Sadiya 'yan uwanshi yasanarwa gaba daya, kan kace kobo gida yacika, nan aka samu masu ilimin cikin sukaiwa Sadiya wanka, lokacinda akaxo yimata wanka sun dauraye mata gabanta yafi sau a qirga, amma baidaina fitarda wani ruwa Mae yauqi hade da wari atattare dashi, suna tottoshe hanci haka dai aqarshe suka barta da katanta suka suturtata, aka fitar da ita.


Xanso Ku qiyastawa kanku irin haukan da Lami tayi, dakyar aka daddanneta abunka da jahila, babu ilimin da xataiwa 'yar tata tilo addu'a, idan sukaga kamar ta haqura akadan saketa saita deba aguje tayi qofar gida, Abunda yay ta qona ran Isah knn.

Anyiwa Sadiya sallah snn aka miqata gidanta na gaxkiya kuma madauwamiya...

_Allah ya kyautata mana qarshenmu Amin_

*********
Zugum sukayi a office din sundan jima kadan can sai gashi ya shigo........


😍😍🤝🏼Anatare
Mummyn Fadyl CE




🎲🎲TUDUN DAFAWA🎲🎲


Rubutawa....MUMMYN FADYL (Fatyma Muhammad Adamu)

Wattpad @ *fatimamuhammadadamu*


INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION*
*[onward together]*
*{we give the reader's of ours the best out of the bests,, our inks are melodious and dropping a kinda lights to reader's}*
```THE PEN OF LOVE😘 HEAT TORCHING❤ TEAR OF SORROWS😭 CURDLES😊 GIGGLES😁 AND MARRIEGE THINK💑```
*```JUST GIVE US FOLLOW..**


*DEDICATED TO*

_Real mom Afra_
_Tawan_
_My water😜 (Sainah)_
_swt hrt (Aufana)_
_Beebah cute_
_Haleemah_
_Mummyn Afrah_
_Mummy Zill_
_Mmn khausar_
_Sistur naja'at_
_Meenah Abba_
_Janat_
Sorry idannayi mantuwa, ina begenku har cikin Raina.

Fitowa ta.2⃣9⃣


Sallama yayi musu snn yamiqawa daddy da Abba hannu suakai musabiha, suka kuma gaisa dasu ummy snn ya Samu kujerar sa yayi yakame yafara koro musu jawabinsa cikin nitsuwa kallo daya xakai mishi kasan Hutu dakuma ilimi yasamu maxauni a tattare dashi.

Amm abun da nakeson sanar daku shine a gaxkiya a halin yanxu baxan iya cewa komai akan cutar taba, don kaina ya matuqar daurewa akan ciwon natan, tunda nayi iya binciken da xanyi, bance muku shine qarshen bincike ba, domin duk wayewan gari ilimi buduwa takeyi, amma a halin yanxu gaxkiya baxance komai akan ta ba, don banga matsala a tattare da kwakwalwarta ba.


Babu matsalar komai acikin kanta, amma kuma tana hauka tuquru,Wanda yana qaruwane akan ta duk kwanan duniya, xanso kubarta anan kodon cikinda yake jikinta, insha Allah xamu bata kulawa matuqa gurin ganin abunda ke cikinta bai illatu ba, saboda idan mu kace xamu daurata akan magungunan su ne to tabbas xai shafi lafiyar abunda ke cikinta, snn bayan ta haihu xamusan wani mataki xa'a dauka akai.

Sun gamsu sun kuma yi na'am da shawarwarinsa, duk da hakan baiyiwa mummy dadi ba, tanada burin taimakon zainab don jininsu ya hadu, tajima tana fatan haduwarsu sai gashi sun hadu bacikin dadi ba, Allah yabaki lpy tafada a fili, duka gurin aka amsa mata da Amin.

Sun nemi su ganta, shiya jagorancesu har dakinda take, samunta sukayi ta kamo qafafunta sama tana son cixan tafin qafanta, tagagara amma tanace sai tayi a qarshe kallon gefenta tayi takurma ihu tana fadin menai maka, taxube agurin jikake gibbb tafadi kannan yabugu da simintin dakin, kasa daurewa mummy tayi tafashe da kuka gami da barin gurin da gudu tanufi wajen asibitin.

Ummy ma da guntun hawayenta suka rufa mata baya, mota suka shiga suka nufi gida, tunda suka shiga cikin motar babu Wanda yasamu qarfin guiwar yin magana, sheahsheqan kukan mummy kawai kakeji, har suka isa gida kowa yanufi sashensa.


*****************
Har akayi ukun rasuwan Sadiya Mal.Habu baiyiwa Lami ta'aziyya ba abun yana damunta duk dama rabonta da ganisa tun ranar da akayi rasuwan da yamma tafito xata xaga bayan gida, don Ayashe bata tanka tana tasan kuma don tana ganin idanun jama'a ne shiyasa.

Tafito shikuma zaishiga dakin Ayashe ko kallon tsiya baiyi mata ba, balle kallon arziki, haka ta wuce bandakin, ita kanta yanxu baxata iya cewa ga halinda take ciki ba.

A bangaren Nana kuwa tayi kukan Rashin Sadiya hartaji babu dadi, don Sadiya ce kadai ke taimakonta dakuma sonta tsakani da Allah, don xuwa yanxu tafara gano manufar soyayyar da Ayashen take nunawa a gareta ammadai bata gama tabbatarwa ba.

_To ko menene_


Tunda aka watse kuwa rayuwar tagama qulleta, don kuwa Ayashe taharass tabbatar mata batada girki, bata kuma bata abinci kamar yanda tayi alqawari, abunda yataimaketa daya taci darajan 'yan canjunan da danta yabar mata bai qareba dashi take samu takecin abinci, ganinda tayi kudin xaiqare dawuri yasata yanke shawaran saro kayan miya tafara kasawa.
_Duniya juyi juyi wai kwado yafada ruwan zafi_



Ayashe tunda ta kyallara idanunta taga kayan miyan Lami tace mata saidai taxabi daya, kodai tadaina sana'ar saboda masu saya suna damunta da sallama kuma lokacin yawanci lokacin baccinta ne, don haka kota daina kokuma takoma gidanta tacigaba da sana'ar.

Lami abun yaqona mata rai, taso nuna cewar baxatabi umarninta ba wnn karon amma ganin tana Neman kore mata kasuwa yasata ji aranta gara ta tafin hummmm amma ita tasan meta qulla mata.

Haka tanaji tana gani tadan tarkata Dan Abunda yarage mata tafara kaiwa gidanta, saida tayi shara don gaba daya gurin yakoma kufayi, har gurin Yamma tilis snn tagama aikace aikacenta taxo deban kayan sawanta, amma me xata gani, kayanta tasamu. Abakin dakin koda taleqa dakin kaji tagani masu yawa aqalla xasukai guda Dari biyu da alama shine ankawosu don basu gama sakewa da gurin ba.


Wani munduqun baqin ciki ne da qunci yataru ya maqale mata a wuya, shibai fito ba, kuma shibai koma ciki ba, gashinan dai ya tokare mata qirji Ni Lami wann rayuwar quncin da nake ciki dame tai kama batasan a sarari tai maganan ba saida taji Ayashe A bayanta tana magana.


Ai Lami tunda kika wulaqantani kika kuma nemi ki toxartani, to Kadan ma kika gani daga sharrina dakuma kaidina, munyi zama dake bana wasa ba, amma har muka watse zaman mu baki gama Sanina ba, in Ayashe tanuna kanta, xanxo gidanki don kinacin Abu kidaure fuska, innemi alfarmar ki ta kudi kigayamin baqar magana, a qarshe ma kicimin mutunci kinmanta nice silar shiganki duk wata duniyar dadi.


Xan qara nanata miki ni shugabanki ne a hatsabibanci, namiki nisanda baxaki kamoni ba, kinadai gani tun tafiyar batai nisa ba, ci dasha kai harma da mijin ya gagareki ko?

Kibini a sannu karkiyi kuskuren shiga gonata don haduwarmu gaba da gaba baxaiyi ma'ana ba inkunne yaji gangan jiki ya tsira.

Daga wnn maganar bata qara da komai ba tabarta agurin da sakekken baki, xuciyarta na tunxurata amma bakinta baida ikon da xai iya furta mata magana makamanciyar na ramuwa agareta, haka tabita da kallo a qarshe kuma ta tsuguna a gurin ta kwashe komatsanta ta fita dashi, gashidai babu fada balle saki amma gidan mijinta ya gagareta.

_BAYAN WATA HUDU_

Haka rayuwar taita tafiya wasu agaresu Zuma, wasuko a garesa madaci ma yafishi dandano don xuwa yanxu Lami tagama tabbatarwa tarasa *TUDUN DAFAWA* gashi jigon rayuwar nata wato Isah yayi fushi da ita, tunda aka watse a makoki baiqara waiwayenta ba, tamkar abun asiri fitanannen jarababben son Mal.Babu ne yake azalzalan zuciyarta harbatasan yanda xatayi dashiba.


Sau da dama takan leqa qofar gida kawai don taga wucewarsa, don kwatakwata Ayashe tama hanata cigaba da shiga gidanne, don tun watarana dataje domin Neman alfarman Mijinta don batada abincin ci.

HHaka Ayashe tafito ta tsigaleta tatas tanajin duriyarshi a ciki amma dagashi har ita bamai ikon tankawa Dan uwansa, a qarshe kuma tace mata karta qara tako mata gidanta, ita xataxo kuma ta tabbatar randa ta ganta a gidanta to takaddan sakinta takawo mata tana gama fadar hakan ta hankada ta daga qofar dakin. Daga ranar bata qara yunqurin shigaba saidai leqe..


*****************
A bangaren su mummy kuwa iya kulawa suna bawa Mama don kullum Mummy saitaje itada Ummy, amma yanxu itakadai takexua don Ummy tayi nauyi sosae, dasafe direba yaje yadubota dayamma kuma mummy taje, saboda yanxu tayi nauyi sosae.

Haka kullum intaje da kuka take dawowa , saboda wani lokacin idan abun yamotsa tayita burgima qasa kokuma taita dukan cikinta, abundai babu dadin kallo.

Amma yanxu ankaita bangaren masu tsofin ciki don samun cikakken kulawa.

Allah dai auke fatan yaraba ta wnn cikin lpy.


*WATA SAFIYA*

Suntashi lpy amma banda Ummy domin wnn ranar tatashi da naquda kuma yaxoda gardama har yakaita ga matakin sai an cire mata abunda yake cikinnata.

Alhmdllh anshiga da ita lpy Ankuma fito lpy India aka Ciro mata Sambalelen yaronta mai kamada IBBY sak, amma mahaifinta ya stage har sanda akai mata dinki, tasamu matsalar da mahaifanta baxai qara samun qarfin daukan wani cikin ba..

Ansallameta da kwana biyu mummy tayanke shawaram xua duba Mama domin kwananta uku batajeba, haka tashirya ta nufi asibitin amma tanaxuwa ta samu...............



😍😍🤝🏼Anatare
Mummyn Fadyl CE




🎲🎲TUDUN DAFAWA🎲🎲


Rubutawa....MUMMYN FADYL (Fatyma Muhammad Adamu)

Wattpad @ *fatimamuhammadadamu*


INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION*
*[onward together]*
*{we give the reader's of ours the best out of the bests,, our inks are melodious and dropping a kinda lights to reader's}*
```THE PEN OF LOVE😘 HEAT TORCHING❤ TEAR OF SORROWS😭 CURDLES😊 GIGGLES😁 AND MARRIEGE THINK💑```
*```JUST GIVE US FOLLOW..**


_Idan ban bata shafin nan ba baxata barni insha iska ba, na sadaukar miki_ *Asma'u Abdullahi chinex*


Fitowa ta. 3⃣0⃣


Mummy tana xuwa asibitin ta iske Mama acikin halin naquda, ankuma tabbatar mata tun jiya tafara, sai naqudar ta taso gadan gadan sai bakin mahaifar yarufu jin bayanansu ne yasata saurin xuwa office din likitan domin jin menene mafitan al'amarin.

Tashiga office dinshi tasamu yana ganawa da wasu aciki don dole tasauna a parlour domin jiransu, mijinta taiwa waya tasanar dashi halinda ake ciki, yace mata yana tafe bada jimawa ba.


Tajima agurin axaune har ranta yafara sosuwa, can saiga Alhaji mukhtdin, isowarshi yayi dai2 da fitowar mutanen da suke cikin office din don batareda jiran komai ba yayi mata alama da hannunsa akan tabiyoshi kamar xataci da qasa tamiqe suka shiga ciki.

Bayan yagama rubuce rubucen takaddun dayake gabansa ne yadago yadubesu, suka amsa cikin sakin fuska, saboda xua yanxu sun gama sabawa.

Wato gaxkiya mungama iya yinmu, to kunsan lamarin masu irin wnn larurar sai ahankali, dama inajiran isowarku ne, nidai anawa da'barta ta haihu dakanta gara kawai acire mata, tahuta abun cikin nata ma yasamu hutu, kar asamu matsala gurin haihuwan, don idan baxaku manta ba a baya namuku bayanin irin cutan nata kamar gaba yakeyi.


Sun gamsu sun kuma yi na'am da bayanansa, atake aka bawa daddy takaddu yasaka hannu akai, snn yaje yagama biyan duk abunda yadace ace anyi, ba qaramin gwagwarmaya akasha ba kapin akai mata alluran bacci, nanma tadauki Rabin Awa tana birgima, inda duk Wanda yaganta, indai akwai digon imani a xuciyarka saika tausaya mata, can dai aka samu baccin yaci qarfinta, aka Shiga da ita theatre room.


*Bayan Awa Daya*


Safa da marwa take tayi agurin tanata addu'oi daddy tun yana ce mata taxauna har yagaji ya zuba mata idanu, juyowan da xatayi taga anbude dakin, cikin azama tayi gurinsu da sassarfa, Nurse ce tamiqo mata baby wacce take nannade cikin kyakykyawan towel.

Cikin hanxari takarba a hannunta, Nurse din cikin murmushi tace mata Alhmdllh munsamu baby girl, Mummy Sam bakinta yaqi rufuwa.

Sai nanatawa takeyi _FATABARAKALLAHU AHSANAL KHALIQIN_ tana juya yarinyan, shikuwa daddy sai binta yakeyi da murmushi can dai yakasa jurewa yace mata, habawa mmn Yarinya aiya kamata kiymin kawaici kibani inganta ko?

Da kunya a kan fuskanta tanufi gurinshi tamiqa mishi yarinyan tareda bude mishi fuskanta, Kai Tabarakallah! Yafada tareda fadada fara'anshi, jaririya CE amma kallo daya xakai mata, kai tsaye zaka kirata da kyakykyawa, haka sukaita kallonta batareda gajiyawa ba.

Rufeta kar iska ya shigeta tafada mishi tareda Jan towel din tarufe mata fuska, tooo tundaga yau anfara min rowanta? Bahaka bane tafada gamida karban yarinyar a hannunsa tanamai dariya ciki ciki.

Suna zaune a gurin aka gingurota aka kaita Side room nacan ward dinsu, binta sukayi har sanda sukaga an kwantar da ita, Mummy ce tamatsa kusa da ita tareda yimata addu'oi ta tofa mata snn suka nufi office da yarinyan.


Sun sameshi da batun yaxa'a barma uwar yarinyan, ta hanyarda baxata illata ta, saida ya gyara glass din fuskarsa snn yafara magana.

A bincikena abunda nalura dashi shine shayarda ita xai iya zama illa ga yarinyan, tunda kunga halin da take ciki, though madai kunsan ko mahaukaci yanason dansa, amma ta shayarwa ana iya shan Abu da dama, ciki kuwa harda hauka, koda batayi haukan wani abun xai iya samunta wanda baxamuy fatan faruwan hakan ba, duk da haryanxu bamusan yanayin haukan nata ba.


Yajima yana musu bayanai akan matsalan aqarshe dai suka sanar mishi sunada Wanda xata shayarmusu da ita, kapin tawarke afara nema mata magani, da wnn sukai sallama dajuna, suka fito suka Shiga mota sukaiyo gida.


Sashin su Ummy suka fara Shiva, sunci sa'a kuwa Alhajinma yana gida, gaisawa sukai da juna tareda sanar dasu qaruwan da aka samu, sunyi matuqar farin ciki nan sukaita karban yarinyan suna yaba kyanta, said a surutunsu ya lafa ne snn daddy yaroqi Abba alfarman da sukaxo Nema agurinsu.

Ran Abba yabaci indai yayi magana cikin qunan xuciya, haba Mukhtar meyasa xakace kaxo Neman alfarma agurina? Atunaninka bakaji cewar kafi qarfin alfarma ba? Bakaji kamar tsakanina dakai babu alfarma ba? Banji dadin wnn abun ba kwata kwata.

Daddy ne yabashi haquri tareda jaddada mishi cewa Hakkine a roqi Ummy domin itace xatai aikin tunda shayarwa ba Abu bane me sauqi ba, don haka wajibi ne aroqeta,.

Ummy ko qasa tai dakanta snn race wlh babu damuwa Insha Allah xata riqeta da Amana, tana fatan sutayata da addu'a Allah yataya ta. Suka Amsa da Amin gaba dayansu.


Daddy ne yakatsesu da cewa inada magana, hankalinsu suka tattaro gaba data suka miqa gareshi saida yayi gyaran murya wnn yace, Ummy banason Iran kina shayar da yarinyar nan kina kallon kwayar idonta, saboda banason tashaqu da kowa sama da matata yafada cikin barkwanci.

Gabadayansu sukasa dariya bawanda kuma ya tanka mishi don Sanin halinsa, miqewa su mummy sukayi da Ummy duka Shiga daki, Abakin gado Ummy taxauna riqe da Babyn itakuma Mummy tanufi gadon da jaririyar Ummy take kwance.


Ummy yanaga 'yar taki saiqara qiba da kyau takeyi? Kedai nononki yanada kyau wlh murmushi kawai Ummy taimata tafara gwadawa yarinyan nono. Allah yasa nima tawa hartafi takin ma qiban, to shknn Amin tunda abun son kai ne.


Ta gwada mata nono karo nabiyar kenan duka biyun, amma fafur taqi karba, tayi mamakin abun a qarshe dai ta ankarar da mummy, aiko taku daya tayi na biyu ta isosu tana zaro idanu waje.

Qara gwada mata ingani, Ummy ce tasake kaimata nonon baki a karo na shida nanma bata karba ba, kuma kallo daya xakai mata kasan tanajin yunwa don yanda taketa qoqarin kai hannunta bakinta, a qarshe ma sai kuka data sake.

Mummy cikin hanzari ta karbi yarinyar tareda cewa, Ummy taso muje musanar da su halinda ake ciki, fitowa falon sujayi jiki duk a sanyaye suka sanar dasu abunda yake faruwa, shiru sukayi gabadaya, sai xuwa can Abba yace, badamua xa'a koma asibiti asanar da likita, domin yagaya musu irin madaran da yakamata abata.


To tashi mutafi mummy tafada cikin zaquwa don har cikin zuciyarta takejin kukan diyartata. Bai bata lokaci ba yamiqe harda Abban suka fita domin xua asibitin.


*****************
Mal Habu ne zaune agaban shagonsa gaba daya abun duniya tadameshi, takuma yimishi atishawar tsaki, don yanxu shagonnasa tamkar kufayi haka takoma, kaya qalilan ne aciki.

Banda uban basussukan da mutane ke binshi, don xuwa yanxu Ayashe ce ke tsara komai na gidan, bashida tacewa haka xataita tsara komai shidai nashi idanu kawai.


Gashi ko acikin xuciyarshi baxai iya musanta mata ba, balle fatar bakinshi tayi garajen furtawa, tadai Sanar dashi cewar duk kudaden da take karba a gurinshi tana yimishi tanadin wasu kayayyaki ne Wanda takeson yafara Sabin kasuwanci dasu, shidai baice komai ba, tunda ba shawaranshi ta nema ba.


Girki kuwa dama tun xuwanta gidan sau biyu tayi tareda shi, kuma takafa dokan Indai xai koma gida da dare daga kasuwa tofa xai tafi musu da abunda xasuci da dare.


A halinda yake ciki harya sallami yaron shagonsa, saboda bashida zarafin sallamarsa kullum kamar yanda akewa kowani yaron shago.

*****
Nana ce Zaune a qofar daki tanaqara mamakin rayuwar Ayashe, dukda takasa yarda da irin son da take matan ba, ammaa duk dahaka tana halacci, tunda bata barinta da yunwa snn tana barinta taje makaranta, duk dama watarana idan tafita xataje makaranta Lami takan kiranyeta ta daura mata kayan kolin da take saidawa, tareda jaddada mata karta kuskura tabari Ayashe tasani.

Kamar kullum yauma saida takirata takarbi Allonta ta ajiye a gefe, snn tadora mata tareda cewa Wlh karki kuskura kiymin ciniki kadan, kika dawomin da kaya dayawa na lahira saiyafiki jin dadi, shegiya ta dungure mata kai kamar xata kife, tafito tana hawaye, fitowarta yayi dai dai da........



😍😍🤝🏼Anatare
Mummyn Fadyl CE




🎲🎲TUDUN DAFAWA🎲🎲


Rubutawa....MUMMYN FADYL (Fatyma Muhammad Adamu)

Wattpad @ *fatimamuhammadadamu*


INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION*
*[onward together]*
*{we give the reader's of ours the best out of the bests,, our inks are melodious and dropping a kinda lights to reader's}*
```THE PEN OF LOVE😘 HEAT TORCHING❤ TEAR OF SORROWS😭 CURDLES😊 GIGGLES😁 AND MARRIEGE THINK💑```
*```JUST GIVE US FOLLOW..**


Dedicated to
*Me Dambu*
*Mamuh gee*
*Rahama na lele*
*Sadnaf*
*Dada naseer*
*Mmn Husna*
*Khairaty*
*Mmn khalifa*
*Mrs Muhammad ×2*
*Ummu Khalil*
*Mmn Arifa*
*Mmn Abdul~rahaman*
*Mmn Sadeeq*
Ayimin afuwa wadanda babu sunansu I heart u all.

_A rayuwa babu abunda yafi masoya dadi,inajin dadin soyayyarku gareni, baxan fasa nanata muku ba, masoyana kune silan yin murmushi nah._


Fitowa ta. 3⃣1⃣


Fitowar Nana yayi dai dai da sauqan Ayashe daga cikin adaidaita dawowarta knn daga yawon gantalinta, Xaro idanu tayi ganin Nana tafito daga gidan Lami kuma dauke da tiren kayan talla a kanta.

Itako Nana daburcewa tayi ganin Ayashe ta ganta, tama rasa yaxatayi takoma cikin gidan ba itaba, ta tsaya ba itaba kawai sai ta daskare a gurin.

Ayashen ne tasallami me adaidaita ta qaraso gareta, tareda ce Mata nasan me hakan yake nufi amma baxai hanani tambayarki ba, ina nabarki xaki tafi, Tallan waye, snn tun yaushe kikeyi?

Har idanunta yaciko da hawaye bakinta yana rawa tace, Makaranta kika barni xan tafi daga haka ta fashe da kuka takasa qarasawa hakanne ya qara tunxura Ayashe, ta Hankada ta suka koma cikin gidan Lami din.

Samunta sukayi a zaune tana gyaran ganyen miya, jitayi mutum ya fado kanta dago idanu tayi taga Ayashe ce ta hankado Nana kanta, cikin zafin nama itama ta hankade Nana saida ta FASA bakinta a qasa ihun azaba ta kurma.

Ayashe kuwa cikin kururuwa da azalzala tafara yiwa Lami magana, Ashe bakida hankali Lami, saboda ke jahilace bakisan dadin ilimi ba shine xaki hana 'yar mutane jin dadinsa? To wlh baki isaba, yanda na haramtamiki shiga tsabgar mijini to wlh haka 'yarsa ba kar inkuma ji ko gani.


Daga haka tajuya tafara tafiya harta kai qofa tajuyo tai mata kallon wulaqanci snn tace nasan kina magana a xuciyarki, xaki kuma so kiga kin amayar dashi hahahahaha tayi dariyan qeta, ,saida tayi me isarta snn ta tsagaita tace Lami kinyi kuskuren karawa dani amma kiyi haquri kiqaramin lokaci xanbaki mijinki alokacin da nagama tabbatar da bashida mamora a tare dashi ko kadan. Daga haka tayi waje abunta.

Kamar wucewar walqiya haka Nana tafita a gidan, tarufawa Ayashe baya, don tasani da wani baqiqqirin din aigara baqi baqi, kobanxa Ayashe bata dukanta.


Lami kuwa Kamar tabita ta shaqeta haka takeji, tarasa meke mata dadi a rayuwar ta, gaxkiya wulaqancin yayi yawa tafada a fili, miqewa tayi da nufin xuwa takawo qarshen wnn cin mutuncin da Ayashen take mata, tana fitowa kuwa tasamu isowar Mal.Habu kenan gidan, ai batasan lokacinda ta shagala da kallonsa ba, tamkar yau tafara ganinsa, wata xuciyar kuma tana raya mata Kamar takamo hannunsa tashigar dashi gidanta amma babu dama.

Tana tsaye a gurin tana saqa da warwara, jitayi muryan Ayashe yadoki dodon kunnenta takuma tabbatar da cewa fitowa waje takeda niyyar yi, ai batasan lokacinda ta antaya cikin gidan ta hartana cin tuntube😜gaba da gabanta raqumi wan doki.


***************
Bayan kwana uku Mummy tana xaune da diyarta a cinyarta daddy yashigo, dagowa tayi ta kalleshi da murmushi akan fuskarta, shi abun har mamaki yake bashi, kullum cikin fara'a take tun samuwar yarinyan nan.


Zama yayi a gefenta tareda cewa kinsan meye sunan babynki? Dasauri tadago ta kalleshi tace bansaniba nayi iya kawaici tun lokacinda na tabbatar kamata huduba amma nadaure ban tambayeka ba jnajiran kasanar dani, duk dama yaukam haquri na ya gaxa inasa ran xan sameka intambayeka.

Dariya yayi mata snn yace baxan Sanar dake kai tsaye ba, xanbaki dai satar amsa akai idan kinci shknn idan bakici ba kuma saiki jira ranar suna in sanar dake yafada da zolaya.


Bata kulashi ba tadaiyi shiru tana sauraronshi, xuwa can yafara magana.


Sunan 'yarki sunane da babu kamarsa, sunan 'yarki babu acikin sunaye Wanda yakaishi yawan inkiya, sunan 'yarki Haske ne Wanda kowa yasan yana haskawa yayi shiru yace nabarki haka don nasan idanna cigaba da koro miki yanayin sunan babu wuya xaki ganoshi cikin sauqi, xuwa yamma inason kifadamin sunan 'yarki. Yana kaiwa nan a zabcen yatashi yamatsa kusa da ita yabude yarinyan yafara binta da idanu kamar dai yanda yasaba kullum kyanta sai qara fitowa yakeyi yafada a fili.

Murmushi mummy tayi tareda cewa daddy yakamata kafin kawuce gurin aiki mu Shiga asibiti muduba jikin Baiwar Allah nnan, Gaxkiyarta kam kitashi Ku shirya Donni a shirye nake, inajiranku a falo.



Tashi tayi xuciyarta cunkushe da tunani kala kala to meye sunan yarinyar nan? Kai subhanallah wnn miji nawa halinsa baxai sauya ba wlh, haka tayita sukur sukur basu tashi sun shirya ba, saida taji ya kwala mata kira snn tafara shirinta cikin sauri, tashirya diyarta tsaf ta nadota cikin towel me shegen kyau suka fito cikin Shiga ta alfarma dukansu suka nufi mota sai Asibiti.


Ranar suna a gidan Ummy yarinya taci suna A'isha anmata inkiya da *Humairah* agidan suna anata shagali kowa mummy tasamu acikin qawayensu saita Dan kebance dashi domin yimai tambayar sunan 'yarta cikin hikima amma bata samuba, Aqarshe tasamu kebancewa da qanwar mahaifiyar Ummy bayan ta koro mata bayani ne, itakuma tayi murmushi tace.


Kinbani mamaki khadija Saikace bakiy karatun addini ba sunan 'yarki ai yagama bayyana miki, sunan 'yarki..........

*BAXANYI NEXT PAGE BA HARSAI ANBANI SUNAN YARINYAR NAN*
inajiran amsoshinku da sunanta


_Duk wacce tafara sanar dani wnn sunan next page nata ne kyauta👌🏼_

😍😍🤝🁁natare
Mummyn Fadyl CE




🎲🎲TUDUN DAFAWA🎲🎲


Rubutawa....MUMMYN FADYL (Fatyma Muhammad Adamu)

Wattpad @ *fatimamuhammadadamu*


INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION*
*[onward together]*
*{we give the reader's of ours the best out of the bests,, our inks are melodious and dropping a kinda lights to reader's}*
```THE PEN OF LOVE😘 HEAT TORCHING❤ TEAR OF SORROWS😭 CURDLES😊 GIGGLES😁 AND MARRIEGE THINK💑```
*```JUST GIVE US FOLLOW..**

_Alqawari nadauka nacewa duk wacce tafara sanar dani sunan yarinyar daidai, xan saadaukar mata da shafin, baxan fasa ba wnn sahafin nakine_ *MMN ARIF* kece kika sanar dani sunan yarinya *Fadimatul~zahra* tareda hujjojinki masu qarfi. Nagode



Fitowa ta. 3⃣2⃣

Sunan 'yarki Fadimatul Zahra'u mummy dajin haka ta kalleta da farinciki marar misaltuwa, tareda cewa Zahra sunan diyata? Alhmdllh Allah baxan gushe ba ina qara gode maka, inaxuwa tafada gamida miqewa bata jira cewar hajiyarba tafito a gidan dauke da 'yarta tayi side dinta da sauri xuciyarta fal da farin ciki.


A falonta tasameshi yayi dai daya yana waya da dansa yana ganinta yacemishi to Son ga Mummyn taka ta shigo yafada yana miqa mata wayar, saida ta shimfidar da 'yarta snn takarbi wayar, tafara magana My son ykk? Magana yafara yimata cikin shagwaba.

Mummy tun lokacinda kikasanar min Kinsamu yarinya kika rage nunamin kulawa yanxu a rana baifi muyi waya dake sau biyar ba, yafada yana qara shigar da muryan nashi cikin sigar shagwaba kamar Wanda xai fashe da kuka.

Dariya tayi kapin tace Haba dearest bahaka bane kodayake duk yanda xanmaka bayanin reno baxaka fahimta ba, fatana kawai Allah yakawoka watarana kaga yanda dawainiyar yake da idanunka, baiyi magana ba hakan yabata damar cigaba da magananta, Son na2ra maka hoton baby na ta EMail dinka amma har yanxu baka nunamin alamar kabude ba, balle insa ran xakai commenting akai, kana tunanin ka kyauta kenan.


Dajin hakan yafara bata haquri don bayason abunda xai Sosa ranta ko Kadan a rayuwarsa, saida ya tabbatar ta huce snn Yakoma salonsa yace mata Mummy' amsawa tayi snn yacigaba wlh yunwa nakeji, cikin Sauri tace bakaci abinciba Haidar haryanxu meya faru, meye dalilin hakan? Mummy ni kawai girkinki nakeson ci, dariya tayi

Please Login or Register in order to submit comment