You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

don tagank yau rigimarce ta motsa.

Don haka ta shirya yimishi yanda tasaba yimishi, cikin lallabi tasashi yaje gurin cin Abinci nan yaqara kiranta tafara yimishi hira yanacin abincin yana dariya har ya kammala, aqarshe sukai bankwana,, bayan takashe wayar ne ta dafe kanta🤦🏽‍♀ oh haidar rigima, kukan 'yarta ne yadawo da ita aiko tamiqe dasauri ta qarasa gareta, tadauketa tanufi ma'ajiyar abincinta da ita.


*RANAR SUNA*
Fadin irin hidimomi da kuma barnan kudin da akayi a taron sunan _Zahra_ bata lokaci ne, baxaka taba cewa ba iyayenta bane saboda gata kam annuna mata, kuma baxaka taba fahimtar ba Nono takesha ba dalili kuwa yanda jikinta yy kyau baxaka ga rashin npnon yanuna ajikinta ba.

Idan kaganta xakai 2nanin tayi wata saboda yanda tai qiba kyanta yaqara fitowa a sarari, idan aka sanar dakai sunanta xaka tabbatar da ta cancanci wnn sunan *Zahra tauraruwa*.

**************

*Bayan shekara biyar*

Umma nagama shirin tafada tana rabe a gefen dakin, Ayashe ce tafito taganta tafa mata tafarayi snn tadora da cewa Gaxkiya Nana saiyau nasan kindaura damaran farantamin, shekara guda nawa ina fama dake saiyau kika amince, indai kikaimin yanda nake so wlh namiki alqawarin baxaki jimaba xanmiki auren gata kije gidanki ki huta ko?

Ke barima kiji ni nan nasan yanda xanyi mahaifiyarki ta dawo gareki muddin xaki kawomin kudi, kinadai ganin babanki ya tsiyace yanxu kam bashida komai abincima nike Sayan mana,
Hawayen da yake taruwa a idonta ne yasamu damar kwaranyowa kamar anbude fanfo, saboda ita Sam takasa amincewa har cikin xuciyarta xatayi abunda umman takeso, yanxun ma ta amsa mata ne sakamakon uquba da horon yunwar da take mata, gashi batada mafita.


Kai jimin sakarcin banxa Ayashe tafada cikin fada, babu dole fa yanxunma idan baki amince ba, xaki iya tafoya kiyi xamanki babu abunda yashamin kai tayi tsaki tareda qoqarin komawa cikin dakinta.

Cikin sauri da muryan kuka tace kiyi haquri Umma na Amince tafada muryanta na rawa, Komawa ciki Ayashe tayi tadauko mayafinta snn tace mata muje.

Fita sukayi suka nufi bakin hanya tamkar kurame don babu maiyiwa Dan uwansa magana har suka shiga adaidaita Nana addu'oi taketa nanatawa cikin Ranta fadi takeyi Ya Allah kaji qaina, Allah Kaine shaidana banason saba maka, Allah kaimin agaji, ka tausayamin ka kawomin dauki cikin gaggawa.

Inda itakuma Ayashe aranta tana ganin girman al'amarin da take fuskanta, kudi kamdai gashi tana samu tunda tagama tatse Mal.Habu tasaida gidansa baisani ba harma dana Lami duk batareda sunsani ba, rana kawai masushi suke jira suxo su koresu, shiyasa takeson tayi amfani da Nana tasamu kudin domin qarin dogara da kanta.

Tawan yau ko gone xa'a kori Mal.habu a shago don tajima da sayansa, ita yanxu Kano takeson tafiya acan takeson bude sabuwan rayuwarta, saidai batadan Yaya Alhajin xai karbi lamarin ba.

Haka har suka isa wani gida, a bakin gate suka tsaya don maigadi yanuna baxai barsu su Shiva batareda anbashi ixinin barinsu ba, saida yakira maigidansa yasanar dashi akabashi ixini snn yabude musu qofa suka shiga nan Ayashe tahau mishi sababi, saida tayi me isarta snn suka shige

*******
A kasuwa kuwa mutane ne cike abakin shagon Mal.Habu, anata hataniya, wani ne acikinsu yake magana da alama shi aka tabo, Wlh yau baxan yarda ba saiya fita yabar shagon nan tunda bana gado bane, shekara uku bai biya haya ba, ko abun shagon nashi nace xan kwashe duka ai baxan fanshe kudina ba.

Haquri ake ta bashi amma yaqi haqura shiko Mal.Habu yana gefe bashida katabus, a qarshe dai aka bashi shawaran yafita yabar mishi shagon kawai, haka yanaji yana gani yamiqa makullin shagon, don ko zarafin shiga ciki yadauki koda tsinkene aciki baisamu ba.


A falo suka zauna sunajiran fitowarshi, yabata lokaci sosae kapin can saigashi yafito donsu har sunqosa da zaman, a dakile yaxauna yafara kallon Nana sheqeqe kamar yaga kashi.

Can yafara magana cikin isa da mallaka, Ayashe kike kowa? Yatambaya cikin halin ko inkula eh Ayashe ne Yallaboi tafada cikin xumudi da kwadayi.


Yayi shiru kamar baxaiyi magana ba a can qasan maqoshinsa yafara musu bayani, To Ayashe yarinya tayimin xansan yanda xa'ayi amma yanxu kije sai nanda wata biyu kidawp don yanxu akwai abubuwa a gabana, dafatan kingane.

Jiki a sanayaye Ayashe tace bakomai Yallaboi, cikin xuciyarta kuwa tsinemishi take yi, don ba haka tasoba, baikobi takanta ba, yamiqe kudi yaxaro a aljihunsa ya wurga haryasamu idonta, maimakon taji haushi ma, a'a bugewa tayi da godiya da nuna farin ciki.

Bai amsata ba yayi shigewarsa, suko suka tashi suka nufo gida.

Kamar hadin baki atare suka iso gida tareda Mal.Habu, shima akan Babur din haya don harda Babur dinsa yabayar cikin kudin shagon.

Yayi mamakin ganinsu sundawo daga anguwa a wnn yammacin, amma bashida ikon tambayansu daga ina, basu yi magana da junaba sakamakon wani dam Anguwansu Mal.Habu dayaxo yana haki yana kwala mishi kira tun daga nesa.


Mal. Habu ne yanufeshi da sauri don yakasa qarasowa, dafashi yayi yana tambayarshi lpy? Shiko cikin in ina yace.........


😍😍🤝Anatare
Mummyn Fadyl ce



🎲🎲TUDUN DAFAWA🎲🎲


Rubutawa....MUMMYN FADYL (Fatyma Muhammad Adamu)

Wattpad @ *fatimamuhammadadamu*


INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION*
*[onward together]*
*{we give the reader's of ours the best out of the bests,, our inks are melodious and dropping a kinda lights to reader's}*
```THE PEN OF LOVE😘 HEAT TORCHING❤ TEAR OF SORROWS😭 CURDLES😊 GIGGLES😁 AND MARRIEGE THINK💑```
*```JUST GIVE US FOLLOW..**


Fitowa ta. 3⃣3⃣

Dafashi yayi yana tamabayarsa lpy? Shiko cikin in ina yace kayi Sauri ana nemanka a gidanku, ai baijira saura qarashen xancen ba yabi gefensa kotakan inda Ayashe suke tsaye bai kalla ba.

Itace tai saurin tare mai kawo saqon tafara tambayarsa meke faruwa, aiko nan yace mata iyayen Mal.Habu ne suka rasu sakamakon guban da sukaci acikin waken da yakasance da magani acikinsa.

Bataji komai a ranta ba, sabanin Nana da hankalinta yagama tashi harta rasa yanda xatayi don har tafara kuka babu shiri tajuya da nufin bin mahaifin nata.

Ayashe ce tai saurin katseta tareda cemata kekuma ina xakije? Xance gidan kaka nane tafada tana kuka gwanin ban tausayi hakanne yasa jikin Ayashen yin sanyi matuqa, tace mata muje.

Haka suka nufi gidan tundaga gefen gidan Mal.Jafaru kake hango cunkoson jama'a babu masaka tsinke ko ina al'ummar annabi ne cike maqil.

Haka sukaita rabawa har suka isa gidan, nafa suka fara cin karo da mata anata koke koke, dakin Mmnshi suka shiga suka tarar da ita kwance sambal don har ammata sutura, Nanace tai saurin qarasawa gurinta ta duqa tafara magana cikin sigar tashin hankali.

Magana tafarayi cikin kuka, tana cewa Shknn nikam naxama banida kowa yaxanyi da rayuwa ta, babu uwa babu kakanni bansan dadin kowa ba saina Mamana gashi anwayi gari anyi satittika har anfara irga shekaru duk da Inada tabbacin babu mai irgawa saini.


Nayi rashin mahaifiya tah, inaji a jikina baki mutuba, inaxan ganki, bawanda yataba yimini jajen rashinki, wanda yakamata yatausayamin yaxame mini *Tudun dafawa* baidamu da rayuwata ba, dani da babu duk daya ne agurinsa, bansan dadin rarrashi ba.

Naso ace haka naga mahaifiyata daya fiyemin kwanciyar hankali a rayuwata, rabona da bacci me dadi tun Daren da kika bar gida, kowa bayayi dani Mama kitausayamin kidawo gareni konima xansamu gata, Kakatah kin huta Allah yajiqanki.

Tafashe da matsanancin kuka gurin kowa yayi shiru ita kadai ake sauraro inda xuciyoyin mutane da dama na gurin ya karye, tasa mutane da dama kuka duk da basuda abunda xasu gaya mata.

Yayar Mal.habu ne tasamu qarfin guiwar matsawa gurinta domin ta rarrasheta amma tana xuwa Nana taqi yarda a dagata a wajen. Haka taita kuka agurin babu qaqqautawa, har aqarshe aka fitar da ita domin asamu damar fitar da ita.

Fadar tashin hankalinda Mal.Habu yashiga ma bata lokaci ne, abunda yafi tsaya mishi arai shine rabonshi dayasa iyayen nasa a idonsa harya manta, gara ma mahaifinsa wata takwas dasuka shude yaje har shago yagaisheshi, duk da baya amsawa cikin dadin rai amma hakan baya hanashi xuwa akai akai, don rabonshi da gidan harya manta.

Mahaifiyarshi kuwa baxai taba iya tuna rabonshi da ita ba, sai yau dayaganta cikin sutura, ganinda baxai amfaneshi ba, haryamxu baxaice ga dalili kwaya daya daya gifta tsakanin sonda yake musu na iyaye ba.

Yayi kukan zuci haryadawo yanayin na fili, idan yaxauna yakanji a ransa yana buqatar yin tunani nashi na kanshi amma baya iyawa, yaxaiyi haka kanshi xaiyita ciwo, aqarshe yadau dangana.


Nana acikin kwana bakwai dinda tayi a wnn gidan taga banbanci sosae domin tasamu kulawa kwarai dagaxke bana wasa ba, saidai baida amfani a gareta domin ba'ai mata a lokacinda takeda buqatar hakan ba, abunda yake daure mata kai baiwuce yanda duk yanda taso aimata maganar mamanta hakan yagagara ba.

Koda ita tadauko maganar to sai ansamu anjanye maganar ansako wani maganar na daban, saboda irin hakan taja bakinta tai shiru tabarwa xuciyarta, tacigaba da roqon ubangiji ya bayyana mata mahaifiyarta, snn tana qara roqon Allah yadora ta akan Ayashe dakuma Alhajin nan.

**********
Mummy! Mummy!! mummy!!! Na'am taji muryanta a kitchen, ciki tashiga tasameta, tabayanta ta riqe ta snn tafara magana cikin shagwaba mummy kinga Humairah ansaya mata wnn kayan da kikace xaki sayamana musa idan Yaya xasu dawo ko? Taqarashe maganar kamar xatayi kuka.


Hohh _zahrah_ nah to nice nasai muku ankawo lokacinda khadija tana nan ne shiyasa nabata nata ta tafi mata dashi, badai bakyason zama guri daya ba? Kinzabi kiyta zirga zirga tsakanin parts dinnan? Sai cikin dare ki isheni da kukan ciwon gabobi.

Mummy to muje daki inga nawa kayan, kidaiyi haquri in kammala abincin xuwa asibitin saimutafi tare dagacan mushirya yaukam xaki Bini ko?

Um Umm ta maqale kafada alaman baxata jeba, nidai Mummy tsoro take bani, kai mummy ta dafe, abunnan yana matuqar damunta, Sam _zahrah_ batason xuwa gurin mahaaifiyarta, wataran da kuka da qarfi take turata a mota suje tare.

Itakuma tanayin hakanne domin tasan cewar Matar tanada muhimmanci a garesu yanda ko watarana duk Daren dadewa idan Gaxkiya tafito xasuy saurin shaquwa.

Amma itakuma taqi yarda, hade rai mummy tayi snn tace, Baby na idanpa baki Bini ba babu ruwana dake, snn next week badake xa'aje Airport ba, kai inshort ma keba qanwar Yy Aliey bane, tana gama fadin hakan tai kamar xata raba ta gefenta tawuce.

Aiko dasauri tariqota tace sorry mummy ni qanwarshi ne, xanje to tafada tana murna, datx my dotah, to kijira ingama girkin muje dakin tare don banason kije ke kadai badadi ne dake ba, yanxu xaki hargitsamin guri.


Da wannan surutun nata taita yimata harta samu ta kammala girkin duka nufi dakin, bathroom suka shiga saida mummy taimata wanka, suka fito ta shirya ta tsaf, cikin wata dakekkiyar shadda, dinkin doguwar Riga,wanda takarbi jikinta bana wasa ba.

To maxa kije kijirani a gurin himairah, kapin ingama shiryawa nasan daddyn ki yadawo sai in aika talatu ta kiraki ko?

Eh tafada tareda fita da gudu daga dakin, banda gudu Mummy tafada mata, amma inaa ai tayi nisa, ikon Allah, Allah yashiryar min dake tafada tareda shigewa bathroom domin itama tasamu tashirya.

Saida suka gama shirinsu snn ta aika aka kirata, tafito tanayiwa humaira gwalo, mummy nipa a gaba xan xauna, daddy ne yace shigo dota na, duk inda kikeso anan xaki xauna babyna, dariya tafara yiwa Mummynnata tashige suka nufi asibiti.

Isarsu asibitin suka nufi sashinda take kamar kullum, saida suka kai abubuwan da suka taho mata dashi gurin me kula da ita, itakuwa taimusu jagora har dakinda take, kamar kullum sun sameta a xaune tasa kanta a tsakankanin cinyoyinta, kuka takeyi kamar ranta xai fita, tsayuwa sukayi ta window suna leqenta don yanxu bata bari suje inda take, abunnata yana matuqar daure musu kai, duk wayewan gari salon haukan nata canxawa yakeyi.


Magani kuwa anayinsa kamar ba'ayi watarana idan abun yatashi ba sauqi, tofa ko ma'aikatan ma sai sunyi ahankali da ita, don wuni takeyi tana buge buge.

Tajima ahakan can a qarshe dago idanunta daxatayi tasauke akan _zahrah_...........



😍😍🤝🏼Anatare
Mummyn Fadyl CE




🎲🎲TUDUN DAFAWA🎲🎲


Rubutawa....MUMMYN FADYL (Fatyma Muhammad Adamu)

Wattpad @ *fatimamuhammadadamu*


INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION*
*[onward together]*
*{we give the reader's of ours the best out of the bests,, our inks are melodious and dropping a kinda lights to reader's}*
```THE PEN OF LOVE😘 HEAT TORCHING❤ TEAR OF SORROWS😭 CURDLES😊 GIGGLES😁 AND MARRIEGE THINK💑```
*```JUST GIVE US FOLLOW..**

🗣🗣🗣 *WNN SHAFIN NA MASOYA NANE NA WATTPAD KADAI, I SO MUCH LUV YOU*

Fitowa ta. 3⃣4⃣

Hada idanunda xasuyi tamiqe kamar an tsikareta da allura, tanupi windon a guje da niyyar kamota, aiko ganin haka daddy ya tajanye ta mummy tamatuqar tsorata jikinta sai kyarma takeyi.


Ganin hakan yasata yin kururuwa tafara buge buge tanata kurma ihu likitocine sukaiyo tsinkaye wa dakin, kamata suka fara qoqarin yi, amma hakan yaci tura don qoqorinta daya taga takamo Zahra, likitan kodaya fahimci abunda takeso knn saiya umarci su mummy akan sumiqo mishi yarinyan.

Daddy ne yayi qarfin halin cewa anya kuwa Doctor baxatai mata illa ba? Karku damu ai muna gurin insha Allahu babu abunda xatai mata, tunda tanuna hakan takeso Ku miqo ta, bamusan hakan mexai haifar ba.


Itakuwa Zahra ganin anashirin miqata gurin mahaukaciya ne yasata saka uban qara danufin baxata jeba, itakuma a can gefen sai ihu takeyi tana banqaro jikin tanason isowa takama yarinyar.

A qarshe dakyar likitan ya lallabota yamatso da ita gurin ta, aiko tariqeta tana kuka tana kallonta tanata shafa jikinta, kuka takeyi me cinrai tana shafa jikin Zahra, mummy ko banda sheshsheqar kukan ta babu abunda kakeji a gurin.

Guri yayi tsit sai kallonta akeyi, abun mamaki itama Zahra saita tsinci kanta da daina qoqarin kwatan kanta a gurin mahaukaciyar tai shiru tana kallonta itama.


Mama kuwa daga baya shiru tayi tana murmushi ganin Zahra tadaina kwatan kanta, abunda yabawa kowa mamaki knn don 2nda taxo gidan cikin kuka take, inkaji tayi magana kuma saidai cewa takeyi Menai maka" shknn iyakan maganarta.

Sunjima a haka, mummy da daddy Neman gurin zama sukayi suka zauna suna hango ikon Allah, amma duk da haka mummy taji dadin hakan, don dama tanason shaquwa ya gifta tsakaninsu yanda daga baya baxa'asha wahala ba, burinta knn.


Har yamma suna gurin, saida sukai shirin tafiya gidane sukaiwa likita magana, akan ya karba mmusu Zahra a hannunta xasu tafi gida, yafito yaxo dakin.

Dan dan dan dan dandan...Aikuwa yana qarasowa Mama tana ganinsa kamar tagane da nufinda yazo, aiko ta qanqame 'yarta tana ihu tana gurnani akan baxata bayar ba, shiko bai saduda ba yanufota.

Ganinda tayi dagaxke yakeyi, tajuya ta hango wani qarfe, hannunta na cikin na 'yarta ta yunqara tadauko wani qarfe da niyyar buga mishi, shikuma lokacin yayi nasaran fisxo Zahra, aiko cikin rashin sa'a ta wurgo qarfen sai goshin Zahra.

Wani wawan ihu tasake taxube a hannun likitan, cikin hanxari yayiwo waje tareda bada umarni wa nurse akan tarufeta acikin dakin yana xuwa.

Mummy suna hango shi sukaga yana tahowa da xahra jini yagama bata kayan jikinta, ai dasauri tanufoshi tana tambayarshi meya faru? Bai bata amsa ba, yadai miqa mata Zahra tareda cemusu sunufi emergency da ita.

Daddy ne yasa hannu akarbeta daga hannun ta, itakuma tarufa mishi baya suka nufi can, daxuwansu aka karbeta, gaxkiya tabugu bana wasa ba, don dakyar aka samu jinin ya tsaya, takuma farfado amma anbata gado.


Shikuma yana komawa yasamu tayi kaca kaca da dakin, dama yasan hakan xaifaru, glass din window Dana qofa duk ta fashe, ta yayyanka jikinta, kururuwanta da gunjin kukan ta kawai ake jiwowa.


Saida yakira wani abokij aikinsa, snn suka shiga, gurinta, dakyar sukai nasaran yimata allura, albarkacin kwarewan dayan abokin aikin nasa, a take aka canxa mata daki.


*Bayan kwana biyu*


Mummy ce xaune a gefen Zahra tana bata tea abakinta, takauda kai snn tace mummy naqoshi, to ai kinyi qoqari ma babyna, mummy yaushe xamu tafi gida?

Yau insha Allah xamu tafi ai kinji sauqi, mummy amma baxaki qara kaini gurin matar can bako? Kinga tajimin ciwo bata sona tafada cikin sigar tausayi.


Karki qara fadin hakan tana sonki, saikin girma xaki gane hakan, kuma ai bake takeda niyyar kwadawa qarfen ba, wannan likitan ne, amma baxan qara kaiki gurinta taba, tunda bakyaso.

Mummy toshi meyayi mata daxata kwada mishi wannan qaton qarfen, ai tsokananta yakeyi kullum kullum shine tarama, kinga kullum ina hanaki tsokana to yaukam kinga illar shi ai.

Mummy nadaina yi, dama humaira ne takeyi amma nikam ai kince nagirma ko mummy na? Kingirma babyna daganan tayi dariya, sukaita hiransu.....


*********†***

Saukowa sukeyi daga jirgin cikin tafiyarsu mai daukan ido, Ibby ne a gaba sai Aliey a baya, 😳Idanuna ne sukaiyo waje sakamakon wata sabuhar halitta danayi, hummm Tsarki ya tabbata ga ubangijin da ya qagi wnn halitta mai cikar haiba.


Kyakykyawa na hango, ya ajiye sajensa dayaqara qawata kyawun fudkarsa, bakinsa Dan tsurut dashi, gwanin burgewa yanada fadi....... Me karatu inshort Aliey kyakykyawa ne ajin farko.

( _kugane mana star din novel_ 😜 hahahha)


Yana isowa mummy tanufeshi yarungumeta tareda dakar mata kiss a tsakar kanta, snn ya furta i realy miss you mum, miss u too my son.


Mummy ki dagani nima yamini abunda yamiki, sukaji muryan Zahra daga bayansu, dariya mummy atayi aiko cadak tadagota tamiqo mishi ita.

Shiko fuskewa yayi kamar bai fahimci abunda ake nufi ba, Kallon juna sukayi, inda tawashe baki tana dariya shikuma ya hade fuska kamar bashine yagama dariya yanxu ba.


Mummy jindatayi kamar baida niyyar yimata ne yasata saurin juyowa da ita, tasauketa qasa, tareda nuna mishi Zahra da hannunta, Son wnn itace dota na, plx inason kaxame mata babban Yaya, idannace maka haka, u know wat I mean right?


Kawai murmushi yayi batareda yanata amsa ba, sakamakon su Ibrahim dasuka qaraso gurin anata tsokanar mummy.

Dafa kafadar IBBY tayi tareda cewa kai mekuke cine, naga duk kunqara girma lokaci daya, kufadamin meye sirrin? Duka suka kwashe da dariya tareda nufan gurin motocinsu.


*†***************

Nana ce a tsakar gidan xaune tana wanke wanke, kallo daya xakai mata kasan a rame take, saboda tun xuwansu gidan Alhajin nan batada sukuni, har xuwa yau, tanada haquri da kawaici, bayan takammala tashiga tayi wanka domin tashirta da wuri, fitowanta daga wanka tadauro alwala snn tashiga daki.

Saboda yau Ummanta Ayashe tasanar mata yau xasu koma gidan Alhajin don wa'adin da yabasu yacika, shiri takeyi tana kuka, duk a daburce take.

Bayan tagama shirinta ne, tahau kan darduma tayi raka'anta biyu, bayan ta idar tajima axaune a gurin tana addu'oi cikin kuka na Neman agajin ubangiji.

Fitowa tayi jikinta a sanyaye, tayiwa umman nata magana akan tagama, saida tagama uxirinta tsaf snn tafito, kallonta tayi sama xuwa qasa snn tace mata koma kicanxa dayan kayan jiyan ba wann xakisa na xuwa gidan Alhajin ba........





🎲🎲TUDUN DAFAWA🎲🎲


Rubutawa....MUMMYN FADYL (Fatyma Muhammad Adamu)

Wattpad @ *fatimamuhammadadamu*


INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION*
*[onward together]*
*{we give the reader's of ours the best out of the bests,, our inks are melodious and dropping a kinda lights to reader's}*
```THE PEN OF LOVE😘 HEAT TORCHING❤ TEAR OF SORROWS😭 CURDLES😊 GIGGLES😁 AND MARRIEGE THINK💑```
*```JUST GIVE US FOLLOW..**


_Shafinnan na sadaukar muku dashi 2Dun dafawa fans, nabakushi kyauta Ku yagalgalashi son ranku nakune😄_

*Masu qaunata nakysa Dana nesa masu fadin ina burgesu masu turomin messages harma da masu kira, nima qaunarku tanq qara yaduwa a qalbina much luv* 💋💋


Fitowa ta. 3⃣5⃣


Haka tanaji tana gani badon ranta yasoba takoma ciki tasako dayan kayan da tasa aka dinko mata domin son xuciyarta,
Kwata kwata kayan basuda tsari, Nana bataji xata iya fita da wnn kayan, don haka bayan tagama sakawa tayi zamanta tafara 2nane 2nane, itayau yaxatayi da rayuwarta.


Ayashe ko gani tayi jimawar tayi yawa don haka tanufi dakin kai tsaye, samunta tayi a zaune dirshan hakanne yamatuqar bata mata rai, don haka ta daka mata wani uban tsawa Wanda saida azarar dakin yayi motsi.


A firgice Nana ta tashi cikin kidima harma tarasa mexatayi daki, Ayashe tafara magana amma dai Nana kingama ganin makwancina raini yashiga tsakaninmu wato don kinga ina binki ta lallama ko? To wlh kishiga taitayinki tun kapin infito miki ta dayan suffan nawa, dallah malama tashi kiwuce mutafi.


Sum sum sum Nana tamiqe suka kama hanya, adaidaita suka hau kamar kullum, yakaisu har gidan.


***************
Yah Aliey ne xaune akan dining yana jiran fitowan mummy da daddy suxo su karya, donshi yayi sabo da haka tun tashinsa baya karyawa har sai sunfito gaba dayansu , yanda xai xamana yanaci yana zuba shagwaba son ransa ana biye mishi.


Daddy ne yafara fitowa, yaxauna a kujeran da ke gefen Na Aliey, daddy gud mwnin, mwnin my son how wax ur night, cool dat, Alhmdllh daddy yafada, maganarshi ce ta tsaya sakamakon ganin mummy dayayi tafito riqe da skul back a hannunta, tanata surutu.


Zahra yaukam wlh baxakisha kayan sanyi da sassafen nan ba, kibari lokacin break dinku idan yayi xan aika miki dashi, fashewa tayi da kuka tareda bubbuga qafanta, nidai to baxanci abincin ba.


Sanin halinta da mummy tayi yasata jawota ajikinta suka qaraso dining mummy xaunar da ita tayi a kujeran gefen na Aliey itakuma as usual taje xata xauna a wanda yake fuskantar na Aliey.

Aiko karaf Xahra tanufi gurin kamar xata buge mummy, cikin mamaki mummy take binta da kallo amma bata cemata komai ba, tacanxa gurin xama.

Duk abynnan dasukeyi akan idon Aliey amma baiko dago ido yakallesu ba, shifa kallon farko dayayi was yarinyar tabashi haushi, bugu da qari ma yanda mummy take biyemata.

Ada dayake shikadai mummy batada wani uxiri sai nashi, amma wnn karon yaga bambanci idan yayi qorafi kuma tacemishi aishi yagirma yakai akirashi magidanci, gashi har yanxu bata gayamishi inda tasamo yarinyar ba.


Tanuna mishi 'yarta ce while khadija kuma ta tabbatar mishi ba 'yarta bace amma dai itama batasan 'yar waye bane.


Yanacikin tunani, mummy kuma tagama serving dinsu tasawa kowa nashi, baiyi aune ba tsulum yaga Xahra tasa spoon dinta cikin abincinsa, wani kallon haushi yabita dashi amma yaga ko ajikinta, daddy kuwa dariya yayi ya kalli mummy yace mata madam 'yarki akwai neman rigima.


Sai a lokacin mummy tasan mesuke ciki, shi Aliey sai aikin harara yake itakuma Xahra saicin abincinta take hankalinta kwance batama San yanayi ba.


Haka suka cigaba dacin abincinsu gurin yayi shiru sai qaran cokula kakeji kas kas kas suna karo da juna, Zahra ce tasaki dariya iyakan qarfinta aiko gabadayan su suka dago suna kallonta, mummy keta tambayarta meya faru, bata tsagaita ba saida tayi me isarta snn tafara magana cikin dariya, mummy kinsan meyene?

Saikin fada Xarah wlh mummy yah Aliey ya iya harara kamar yanda wata qawata takeyi class dinmu waidon kar inci abincinshi kuma nagane amma naqi dainawa saida naqoshi taqara fashewa da dariya.

Daga daddy har mummy bawanda baiyi dariya acikinsu ba, ganinta sukayi tamiqe tareda cewa mummy a sch dinmu kowa yayanta ne yake kaita amma nikuma kullum direba ne yake kaini wlh yau baxan yarda ba tunda yaya na yadawo taqarasa maganarta ta kimtsa fuskarta kamar xatai kuka.

🤦🏽‍♀ Allah nagode maka mummy tafada snn tadubi Aliey daya hade fuskarsa babu alamar wasa a tartare dashi, hakanne yasa mummy tarasa ta ina xata fara, snn kuma tasan halin zahra wlh baqaramin aikinta bane ta Tara mata jama'a da ihu tunda tunkapin yaxo take jaddadawa uwar itafa idan yayanta yadawo shixai na kaita sch, snn kuma mummy n tayi kuskuren amsa mata, gashi yanxu abun yana nema yaxame mata damuwa don bataga sassauci a fuskar yayan ba.


Daddy ne yasamu qarfin guiwar cewa Aliey, my Son kadaiji qorafin qanwarka hope ka karbi uxirinta, bata fuska yayi dakyar daddy ya lallameshi yatashi badon yanaso ba, sai don tun tashinsa baya yimusu musu.


Itako ganin ya tashi yadau key dagudu taxo taiwa mummy da daddy kiss, tace daddy yau a hannu xanmaka, hannunshi yamiqo mata ta sumbace shi, taqaraso gurin mummy tace mummy a baki xanmiki😳 idanu suka waro waje tareda cemata dota ai yarinya bata yiwa iyayenta a baki, shagwabe fuska tayi tace towaye xaimiki a baki ai bakida kowa saini, eh bakyau ne, to xo inmiki a goshinki yauwa haka ta qarasa itakuma mummy ta tsuguno taimata snn tafita a guje.


Murmushi sukayi, daddy yace watarana sai labari, ina tuna miki ranar rabuwa da zahra, bata fuska tayi tacemishi mubar maganan nan, Aliey ne yafito mummy taimishi bayanin makaranta, bai amsa ba yayi ficewarsa, itama batasa batasa ran xai amsa ba tunda kaje dai duk dasauki mummy tafada.


A mota kuwa bai kulata ba, sai labari taketa bashi, shikuma ko kallonta baiyi ba, don shi yaro kallo daya yakemishi yashiga taitayinsa, amma ita gashi idonsa kamar xai fado qasa amma ko ajikinta.

Isarsu makarantan ya ajiye ta, tadauki box dinta, tace mishi yayah idan munyi break ka kawo min ice cream dina, bai kulata ba,taqara cemishi yaya a ina xanmaka kiss kai kam ba iyayena bane, xan iya yimaka a baki ai ko? Takaici ne ya isheshi ya hankadeta ajikin motar taje taga taga xata fadi Allah yataimaketa, wani ya tareta, shiko ko ajikinsa yay tafiyarsa xuciyarsa cike da haushinta.

Dawowarshi

Please Login or Register in order to submit comment