You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tashi kibamu gurin munafuka Ayashe tafadawa Nana cikin kidima tayi dakinsu.

Ayashe kuwa cikin iya tsara magana tasanar da Lami abunda yakawota tareda kitsa mata alheran da xasu samu, cikin tsuke fuska Lami tace gaxkiya Ayashe baxamu shirya dakeba matuqar kina kawomin irin wadannan maganganun yaushe ma sadiyar ta warke? Kuma shknn takoma kamar shaddar kasuwa?

To baxiyiwu ba, inma kudinsa kika karba kimayar mishi ni 'yata aure nakeso tayi yanxukam nima ina burin ganin zuri'ata, keda yakamata kitaimakeni mu cetota cikin halinda take ciki kuma, kece ke qara ingixa abin?
.
Sororo Ayashe tayi amma tayi qoqarin danne xuciyarta snn tahau bawa Lami haquri, dayake abokan cin mushe ne a take suka shirya amma Ayashe a qarshe xaman gagaranta yayi sukai sallama tafita.

Isarta gida a tsakar gida tayi wurgi da gyalenta cikin fushi tafara magana lallai Lami kintaboni yau tunda kika hanani samun nawa tokema kina gab da rasa duk wani jindadinki, dani kikeyi tafigi gyalen ta taiwaje kamar meshirin tashi sama.......


Anzo wajen😳


😍😍🤝🏼Anatare
Mummyn Fadyl CE




🎲🎲TUDUN DAFAWA🎲🎲


Rubutawa....MUMMYN FADYL (Fatyma Muhammad Adamu)

Wattpad @ *fatimamuhammadadamu*


INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION*
*[onward together]*
*{we give the reader's of ours the best out of the bests,, our inks are melodious and dropping a kinda lights to reader's}*
```THE PEN OF LOVE😘 HEAT TORCHING❤ TEAR OF SORROWS😭 CURDLES😊 GIGGLES😁 AND MARRIEGE THINK💑```
*```JUST GIVE US FOLLOW..**


*I'm Addicted to you my fans*

Fitowa ta.2⃣0⃣


Harta fito waje ta tuno da kudadenta dawowa tayi dasauri tadauka snn tanupi waje, adaidaita ta tara wani qauye taimishi kwatance can bayan gari baxaka taba tunanin akwai wani halittan da xai iya zama acikin wnn kungurmin dajin ba,

Tsaidashi tayi snn taciro dubu uku tamiqa mishi takuma jaddada masa akan yajirata xata fito sutafi yanxunnan.


Kutsawa take tayi yayinda qayoyi keta sokinta amma tsabar tijara batamaji burinta daya ta qarasa inda takeso don yanda takejin ranta xata iya komai akan qudirinta ciki kuwa harda yawo tsirara.

( *SUBHANALLAH*)

Dakyar ta isa hango layi tayi kamar anacin kasuwa hakan baisa taji takaraya ba domin tasan tana isa xata samu shiga.

Hakanne kuwa yakasance domin tana isa naji wata murya data raxanani harsaida wayar tafadi aqasa, sai fadil ne yamiqo mini ita😜

Murya ce me matuqar firgitarwa qara neda muryar cikin kururuwa akace da Ayashe kumatsa gaba daya tashigo, haka aka daddare a layin ita kuwa cikin kwanciyar hankali tanupi ciki.


Agabanshi ta durqusa tayi sujjada snn tamiqe tahau xuba kirari harsanda yadaga mata hannu alamar dakatarwa, dafa kanta yayi na 'yan daqiqu snn yace mata kije dakinki a qarqashin filo xakisamu magani shixaki bata tayi amfani dashi xaku kori Zainabu a gidan amma bayanxu xaki bata ba, sai kudinda take gadara dashi yafara qarewa.

Snn xuwa yanxu nagama bata duk aikinda Maye xaiyi mata a gaba, duk
maganinda xaibata na banxa ne, baxai amfaneta da komai ba, kuma xai cigaba da moreta tana karban kudadenta.

Shaaradin aikinki shine daga yau xaki farayin sallah batareda alwala ba,

(Aigwara kahanata sallar gaba daya, 😏 sallar da babu alwala gara bakayishi ba ae.)


Bayan kinbata maganin xakixo Aljani xai kwana dake na tsawon kwana biyar, bayan kinkoma Habu xaikawo kansa gurinki.

Cikin jin dadi tafara mishi godiya tareda miqewa taciro gaba kudin da yake jikinta gaba daya taxuba a wani kwarya, Aikinki yana kyau Ayashe duk mutanen da kike 2rowa suna xuwa Aljani yace kiqara qoqari, washe baki tayi snn tanupi waje domin ba'ayin magana bayan yayi saidai kapin yayi, don haka tun kapin tasaba umarnin tai waje tabarshi yana surkullensa.


Tundaga wnn ranar tadauke qafarta a gidan Lami tafita harkanta kwata kwata takuma kwantar da hankalinta saboda lokaci kawai take jira yayi takafa nata gwamnatin.

A gida kuwa Lami abunna Sadiya yafara damunta don a 'yan kwanakin nan tama fara kwanan wani guri ba'a gidaba, snn gashi Mal.Habu yacigaba da satar hanyan xuwa dakin Zainabu duk da Maye yana tabbatar mata cewa babu abunda xasu iya aikatawa koyaya xasuyi amma duk da haka hankalinta baya kwanciya.

Kamar kullum yauma cikin dare ya sidade yatafi dakin Zainabu don tun jinyar Sadiya Nana tafara tayata kwana to haryanxu acan take kwana shiyasa kanshi tsaye yake nufarta.

Duk da yanxu tafara Nuna mishi su haqura sudage da addu'a babu abunda yafi qarfin Allah,amma yaqi, Bacci yasameta tanayi cikin nitsuwa kan gadon ya haye ya kwanta ta bayanta, shafa jikinta yafarayi, bude ido tayi, batayi mamaki ba don tasan xa'a Rina hakan...

Bbn Nana mexai hana baxakabi shawarata bane, munemi Agajin mahaliccinmu shifa masanin komai ne, mudage da addu'oi insha Allahu xa'a dace bai kulata ba domin wani jaraba datake ciciyarsa, don haka yafara aiwatar da abunda yakawoshi cikin tsoron abunda xai biyo baya.

Gashinan dai yaukam bata kwanta ba tananan sambal da ita, cikin farinciki yafara qoqarin shigar da ita jikinta amma me? Saiyaji kamar ruwa yana gangaro masa, gabansa ne yafadi ruwan kuma tanayimishi kamar qaiqayi tareda mutstsinin cikin jikinsa bashiri yamiqe itama miqewa tayi a raxane tareda tambayarsa menene kuma? Ina Haske yafada cikin raunananniyar murya, lalubo tocilan ta tayi ta haska gani yayi wani ruwa me yauqi hade kuma dawasu qananun tsutsotsi sunata yawa a cikin ruwan abun babu kyan gani.

Saurin runtse idonta tayi, inda shikuma yakasa komai sakamakon yanda zuciyarsa dakuma kwakwalwarsa ta tafi hutun wucin gadi, Candai yadawo hayyacinsa , haquri yafara bawa zainabu tayi saurin toshe mishi baki da tafin hannunta.


Bbn Nana kadage da addu'a lamarinmu yana buqatar hana idanuwan mu bacci mu raba dare muna roqonshi yakawo mana sauqi cikin al'amarin mu.

Jiki a sanyaye yace mata Magode yasakai yafice, itakuma kasa kuka tayi, yau kam, idanunta bushewa sukayi, tashi tayi ta kimtsa jikinta, tareda qudirtawa a xuciyarta xata daina yarda dashi matsawar bazai tsaya kan ibadarsa ba, don tagaji tanakuma cutuwa, tunda xa'afara abu rimi rimi amma daxarar ankai matakin zama Abu daya labarin xai sauya, saikuma yabarta da matsan cinya da ciwon Mara, tunda shi yanada inda xai sauqe nauyinsa.


Shikuma shigarshi Lami tana kallonsa damuwa fal a fuskarsa, hakan yasata jin dadi harta kasa danne farincikin ta, tafashe da dariya me qarfi, juyowa yayi ya kalleta itakuma tamiqe ta qaraso gareta da uban tsamin jikinta, lavarin ne yasha banban hakan yasani barmusu dakin.

Haka rayuwar tacigaba da tafiya inda Lami tafara ganin sauyi a gurin Habu don har wasa da tsokanar Nana yakeyi duk da baya kula Zainabu ko kadan, taje gurin Maye yabata magunguna tabasu sunci sunsha amma duk a banxa, don haka tayanke shawarar xuwa gurin Ayashe...

Samun Ayashe tai kamar kullum gidanta kamar dandalin karuwai kowa na abunda yakeso, wasuna shan taba, wasu na Caca, wasu xaune anata hira, itakuma uwar gayyar tana gefe tana busa sigarinta.


Daganinta tafadada murmushinta ta tarbi qawartata da farinciki suka gaisa tareda wasan barkwanci kamar yanda suka saba, can Lami ta nisa taiwa Ayashe bayanin abunda ke tafe da ita.


Wanin wawan dadi ne ya ziyarci xuciyar Ayashe aranta tace Anzo gurin amma ta danne tareda saka fuskar damuwa a fiskarta, tai shiru kamar me tunani karki damu indai kina tare dani kije gida Gobe zanzo ina Layar kwankin bayan nan? Eh yananan ai kinsan ba'asamu mahadinsa bane.

To ki kwantar da hankalinki ki koma gida gobe xantaho miki da maganin damuwarki, xan samo miki mahadinsa ayita taqare kawai yanxukam, a yasar da kwallon mangwaro ahuta da quda.

To nawa xan bayar na karbo maganin? Ah habadai karki damu aini Lami kinfi qarfin haka a gurina kece bakidau keni da muhimmanci ba, akwai isashshen kudi xankarbo miki karki damu, bahaka bane Ayashe wlh kudinne yanxu sun yankemin, wlh ingaya miki Mal.habu yanxu baya dawowa da kudi gida, danai mishi magana wlh abun tsoro kai tsaye yacemin Babu kudinne.

Tafadi hakan tareda tagumi don tana cikin tashin hankali matuqar tayi sake asirinta yagama tonuwa, Nace miki ki kwantar da hankalinki kekam me gabadaya xa'ayi kowa yahuta.


Lami Kuwa dadi taji ya mamaye ranta, taiwa Ayashe bankwana tareda fatan ganinta washegari kamar yanda Maganin........

Fitarta keda wuya Ayashe takwashe da kafurin dariya me rage imani, saida tayi me isarta snn tayi shiru tace Lami dani kikeyi yanxu ne xakisan kintabo Ayashe hahhahahahhahaha kindauka ke kadai ce xaki dauwama a cikin dadin?

Har xakiymin wulaqanci akan kudi, kicimin mutunci akan 'yarki? To muxuba mugani, 'yartakin ma kinja mata baxatai auren ba kuma xata dauwama a iskanci, snn kekuma xan kwace Habun daranki saikin zama 'yar kallo kintaro ruwa bakida Leman karewa takece da dariya snn tacigaba da xuqar sigarinta..


*WASHE GARI*

Shiryawa tayi tsab tanupi gidan Lami da qullin Maganin.

WNN SHINE ABUNDA YAFARU A FARKON LAVARIN IDAN XAKU TUNA MUJE XUWA. (Ayashe takawo magani itakuma Lami ta aika kiran. Mal.Habu akasuwa).

_CIGABAN LABARIN_



😍😍🤝🏼Anatare
Mummyn Fadyl CE




🎲🎲TUDUN DAFAWA🎲🎲


Rubutawa....MUMMYN FADYL (Fatyma Muhammad Adamu)

Wattpad @ *fatimamuhammadadamu*


INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION*
*[onward together]*
*{we give the reader's of ours the best out of the bests,, our inks are melodious and dropping a kinda lights to reader's}*
```THE PEN OF LOVE😘 HEAT TORCHING❤ TEAR OF SORROWS😭 CURDLES😊 GIGGLES😁 AND MARRIEGE THINK💑```
*```JUST GIVE US FOLLOW..**



Fitowa ta.2⃣1⃣


Sai da ta isa gab da layinda xai sadata da shagon Baban natan snn tai qoqarin saita nitsuwarta, taqarasa cikin shagon.

Yaron shagon nasane tasamu yanata hada hadar sayarda kayan, gaisheshi tayi snn tace mishi tana Neman Bbn tane, to kijirani bari nai mishi magana yanacan cikine.

Nana lpy daiko? Taji muryan Bbn ta, murmushi tai mishi kapinnan tabashi amsa da cewa Umma ce take inkiraka, saida gabansa ya yanke ya fadi, dakyar ya iya cemata kije ina xuwa....

Komawa cikin shagon yayi yaxauna, baida alamar tashi, haka kawai yaji yaukuma baxai iya bin umarninta ba, wnn shine karo na barkatai tana yimishi irin hakan, wataran ma shine yafito Amma haka xata danno mishi kira, shikuma yakoma gida, kuma bb abunda xata mishi.


Haka yacigaba da zamansa batareda yaje garetan kamar yanda tabuqatan ba..
Haka kawai kuma yaji buqatar matarshi yana qara qaruwa acikin ransa, duk da yana tsoron tinkararshi bashida tabbacin yanda xata karbi abun, snn bugu da qari baisan mexai faru ba kuma..


Itakuwa Lami a gida tacika tagama yin fam axuciyarta kuwa tsoro ne yake qara kamata, tana Allah Allah dare yayi tasamu tasamishi maganin a ruwan wankan.

*DA DADDARE*

Bayan dawowan Mal.Habu daga qofar gida bai kobi takan dakin Lami ba, dakin zainabu yawuce kai tsyaye ledan hannunsa ya ajiye cikin Mamaki takebinshi da kallo fa ido taiwa Nana magana, a take tamiqe tabar dakin.

Menene wnn Bbn Nana? Nakune keda Nana yabata amsa a taqaice, takasa boye mamakinta hannu tasa ta matso da ledan gabanta tareda budewa, Nama tagani dakuma kifi soyayye hade da lemun gwangwani, bai saurareta ba yai fitarshi.

Miqewa tayi takira Nana, miqa mata tayi tace mata Nana nah zauna kici kiqoshi, duk da yawunta ya tsinke babban burinta tajishi acikin bakinta, hakan bai hanata tambayar mahaifiyarta ba.

Mama yau kuma Baba ne yashigo gurinmu harda tsaraba irinna Umma? Dariya tayi snn tace mata Nana knn aina gayamiki komai idan kikai haquri yanada qarshe, kullum ina tunatar dake muhimmancin haquri, kiriqeshi xakici riba, murmushin jin dadi ta sakarwa mahaifiyarta snn tafara cin naman cikin jin dadin sauyin rayuwar da suka samu.


Dare ya tsala, gari yayi duhu, guri yayi tsit, babu abunda kakeji sai kukan tsuntsaye, saukowa yayi a gadon kamar kullum cikin hikima yafito daga dakin, Lami kuwa a ankare take don haka yana fita taiyo waje cikin Sauri, maganinta tadauka takuma lalubo boyayyiyar layarta..


Cikin hanxarinta ta fito waje, qofar dakin Zainabu taje, cikin sanda inda ta tsuguna ta toni guri kadan ta bunne layar snn taxuba ruwa a gurin, ruwa takoma da deba bokiti, ta raba maganin kashi biyu, ta xuba Rabin acikin Nata, kai tsaye tashige bayi ta watso ruwan, wani qaiqayi takeji a jikinta ta ko ina tareda wani wari marar dadin ji, a haka taketa daurewa, itadai indai burinta xai biya tofa xata juri abunda yafi warima.


Cikin Hikima Mal.Habu ya lallashi Mama itako Sam bata iya yimishi musu, Don haka baisha wuyan shawo kantaba, yafara sarrafa duk wani sassa na jikinta cikin xaquwa da rawan jiki, abunda ya bashi mamaki bai wuce rashin samun matsalar da akayi yau ba, Don kuwa yau yaji abunda baitaba jiba, gaxkiya yayi kewar matarshi, inda itama a fanninta take farincikin hakan, yau taji mijinta ajikinta abunda tai rashinshi tsawon shekaru masu dinbin yawa.


Sunshare Awanni suna Abu daya batare da qosawa ko gajiyawa da juna ba, wnn Daren yashiga cikin darenda yakasance me tsayawa a rayukansu, jinta yayi ayau kamar sabuwar budurwa baxai taba cewa ta haihu ba ayanda yajita, (Yo ba doleba shekara nawa ba service😜, Donna ba ai gyara ba tun haihuwa)


Dokinta yacigaba daji, xai barta ne badon gajiyaba sai don tausaya mata. Yau ne yatuno da wani Abu waishi nitsuwa a kwanciyar aure.

saidaga baya suka samu nitsuwa, shine yafara magana cikin not tsuwa, tareda mannata da jikinsa yafara ce mata, kiy haquri da duk abubuwanda suka faru a shekarun nan Zainabu idan xance miki baxan iya tuna komai ba wlh kiyarda dani, banida tunani nawa nikadai, bansan menake ciki ba inabuqatar addu'arki ina muradin mudawo cikin rayuwarmu na da..

Itako tsabar dadine yamantar da ita komai, jitakeyi a ranta kamar yau tafara jin dadin kasancewa dashi, itako mexai hanata karban uxirinsa, dama can tasan balaipinsa bane, kodama laipinsane tasan dole xasu sulhunta junansu tunda a iya saninta bata bata masa ba. Ashe xataga wnn ranar a 'yan kwanakin nan? Haka yayita gaya mata maganganu masu tsayawa a rai itakuwa binsa kawai takeyi da murmushi dakuma godiya, har sukakai matsayinda kowa ya gamsu da batuttukan dan Uwansa.

Bai gusheba yaci gaba da bata labarai Amma me? gani gani yayi tajima da bacci duk a tunaninsa baccin gajiya ne, yajima a haka yana kallonta, sai can yamiqe da niyyar fita amma jiyayi baigaji da kallonta ba, shafa fiskarta yayi yace baxan taba mantawa da karamcinki a gareni ba, tabbas ke 'yar halak ce, Allah yaqara miki haquri, yakuma fiddani acikin qangin da nake ciki, da hakan yasamu yafita yana waiwayenta.

Lami a dakinta tayi mamakin jimawarsa na yau, kasa haquri tayi tafito tsakar gidan, jitakeyi kamar tashiga dakin taga mesukeyi kokuma tashiga tarufesu da duka koxataji sauqin yanda xuciyarta ke tsalle kamar xai fado qasa, saida tahango alamar fitowarsa snn tashige dakinta da gudu tai likimo akan gadon kamar me baccin gaxke.

Yana dawowa kuwa ta turmusheshi kamar kullum duk da nayau buqatar ta dabance, burinta sugama yayi wanka a Daren, shikanshi yayi mamakin yanda ta gyaleshi da wuri haka, duk da yaji dadin hakan don kuwa a matuqar gajiye yake da ita.

Ba'anan mamakin nasa ya tsayaba, ganinda yayi dakanta, tafita tahada mishi ruwan wanka, harda cemishi rayi muje intaimaka maka kayi wankan, baki bude yake kallonta cikin duniyar mamaki, tareda cemata a'a barshi kawai yamiqe yafita yayi bayangidan.


Fadi tayi a gadon cikin farinciki, yaukam xan huta da damuwarki Zainabu saura kuma 'yarki, fita tayi dasauri ta leqa dakin Zainabu ta tabbatar tanakan baccin dadi ne yaqara cikata tadawo dakinta taxauna dirshan tana jiran sakamako.


Shikuwa Mal.Habu a bayi yana watsa ruwan ajikinshi yaji kamar anjuya mishi kwakwalwarsa gaba daya, kamar mutum mutumi haka yakejin kansa, tamkar anxare komai axuciyarsa yakeji saikuma wani baqon al'amari dayake shigarsa Wanda baida tabbacin daga inda yake.

Jiyayi gaba daya ankwashe tunaninsa na baya anshigar mishi da sababbi, a wnn yanayin yake harya kammala wankan yafito.

Baiyi yunqurin shiga kowani dakiba, a qofar dakin Sadiya yasamu wani dutse, akanshi yaxauna tareda dafe kansa.. Lami ce taleqo bahaka taso ba, batason abunda xaifaru, yafaru akan idonsa, don batason yashiga wani halin baqinciki ko kadan don tanason mijinta.

A bangaren Mama kuwa Gab da asuba ne baccin nata yacanxa akalarsa xuwa marar dadi, inda takeyin wani mafarki mai ban tsoro, wani halitta take gani razanar da ita yake kuma sanarda ita abunda xatayi daga zarar tafarka, cikin murya me firgitarwa a qarshe yabuga mata wani qarfe a tsakar kanta, farkawa tayi amma cikin dakin gaba daya juya mata yakeyi snn gashi sai hankada ta akeyi waje...

Tana tako qofar dakin ta taji wani qara acikin kanta, batasan lokacinda tafita a gidan da gudu ba.............


Also, don't 4get to

_Share_
_Vote_
_Like_
_Comment_


😍😍🤝Anatare
Mummyn Fadyl CE




🎲🎲TUDUN DAFAWA🎲🎲


Rubutawa....MUMMYN FADYL (Fatyma Muhammad Adamu)

Wattpad @ *fatimamuhammadadamu*


INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION*
*[onward together]*
*{we give the reader's of ours the best out of the bests,, our inks are melodious and dropping a kinda lights to reader's}*
```THE PEN OF LOVE😘 HEAT TORCHING❤ TEAR OF SORROWS😭 CURDLES😊 GIGGLES😁 AND MARRIEGE THINK💑```
*```JUST GIVE US FOLLOW..**

*Masu qorafin akan novel duk akan Zainabu karfa kumance asirinnan baitashi kamata ba, harsai lokacinda yakasance babu tsarki ajikinta, plx koya kuka tsinci labarin ina tabbatar muku inada dalili, kuyi haquri insha Allah xaku fahimci abunda nike nufi a gaba* _10Q SO MUCH_


Fitowa tata. 2⃣2⃣

Tagabanshi ta wuce amma Sam bai luraba baikuma ganta ba, saboda duniyar da kwakwalwarsa ta Lula duniyace me matuqar nisa, Wanda yataba xiyartar ta shixai gane halinda yashiga.

Ganin shirunne yasa Lami fitowa domin ganin ko lpy, duk da yanda gabanta yake tsananta faduwa Wanda tarasa dalilin hakan, cikin rashin kwarin guiwa ta tinkareshi magana tafarayi amma ko kadan hankalinsa baya gurin balle yasan taxo.

Ganinda tayi baya cikin hayyacinsa ne, yasata taboshi firgigit ya miqe kamar Wanda aka tsikarawa allura, Lpy dai Bbn Sadiya?

Runtse idanunsa yayi sakamakon wani dafi daya soki xuciyarsa a dalilin tabashin da tayi, lpy qalau yabata amsa batare daya kalli inda take tsaye ba yayi wucewarsa masallaci domin yaji amfara kiraye kirayen sallan Asuba.

Sororo ta tsaya agurin kamar an dasata sai bin qofar gidan tayi da idanu, meye hakan tafada bahaka tayi tsammani ba, don a yanda maganin yake indai tayi yanda akace to xai manta da Zainabu har abada baxai kuma tambayarta ba, xai koma qarqashin ikonta sai yanda takeso xai nayi, to Yaya haka kuma acikin qanqanin lokaci kodai abun baigama shiga jikinsa bane, da wnn tunanin tasaki murmushi.

Tunawa datayi da lbrn Zainabu ne yasata nufar cikin dakinnata, wayam ta taras bakowa hakan yasata jin matuqar dadi tareda fadin Angama da wnn, tayi dakinta cikin farinciki marar misaltuwa.

NANA ce tafarka kamar kullum domin ita Sadiya dama can Sallah bai dameta ba, sai randa taga damane takeyi kuma nanma sai Rana tafito takan dauki tsawon watanni kapin tayi, ahakan kuma Asuba tafiyi domin sauran kam a gurin gantalin ta yake isketa.

Fitowarta ganin dakin mahaifiyar tata babu haskene yasata fadin Lallai Mama yau tayi bacci me nauyi haryanxu bata farka ba? Don tasaba itake tadata daga bacci tayi alwala, suy sallarsu a tare, hakan yasata nufar dakin domin tadata.

Mama na nima yau narigaki tashi kinacewa ina bacci inmanta jikina, yau nima naxo tashinki, jitayi ba'a ansata ba hakan yasata lallabawa ta isa gurin da suke ajiya tocilan su kunnawa tayi amma bataga Maman akan gadon ba, tayi tunanin tazaga bayan gidane, hakan yasata fitowa bakin bayan gidan tana jiran fitowarta itama tasamu tashiga.

Lami ce ta fito tasameta a tsugune don tagaji da tsayuwar sosai qafafunta sunfara tsami, Nana mekikeyi a hanyar bayi kamar wata aljana, Mama nake jira haryanxu kuma bata fitoba.

Dariyace ya kwacewa Lami Wanda Nana tarasa ta mecece dariyar tunda itadai bata fadin maganar da xaisa mutum dariya ba a gurin.

Saida tagama dariyar muguntarta snn tai shiru kana tadubeta tace, ai da dauko kujera kikayi kika zauna don anjima kadan tsugunon ma gagarar ki xatayi,
Nana kuwa bata fahimci maganar nata ba, asalima ita bata dauki maganar nata da muhimmanci ba, don sau da dama Lami takanyi mata maganar da bata ganewa intajewa mahaifiyarta da maganar kuma saita cemata bakomai hakan ke nupi ba, duk da tasan ba gaxkiya maman nata ke gaya mata ba, amma takan bar abun a haka.


Wasa wasa tana gurin har gari yafara haske, hakan yasata matsawa dab da bayin snn tafara kiran Mmn nata ahankali bataji ta amsa ba snn bataji alamar akwai mutum a ciki bama kwata kwata, hakan yasata saurin leqawa, Aiko bakowa.


Fitsari takeji amma a take tanemishi tarasa a gurin, dawowa dakin tayi nanma dai batanan da gudu tanufi qofar gida duk da tasan Mmn ta bataxuwa ko ina, ballema da asuba haka amma bata daddara ba, saida ta fito wajen layinsu tana dubawa, nanma shiru hankalinta ne yaqara tashi taiyo gida cikin Sauri kamar xata kife a qasa.


Sallama tafaryi a qofar Lami, itakuwa tana daki tanashan shayinta hankali kwance saice mata tayi kiriqe sallamar taki xai iya yimiki amfani wataran amma yanxu bashida muhalli anan kedai fadi damuwarki, cikin rawan murya tace Umma Banga Mamana ba, bata daki kuma bata bayangida, har waje naduba batanan.

Toooo Mamar taki jaririya ce daxakixo gurina cikiyarta? Kenake tamvaya kin tsareni da idanu kamar mayya, a'a tafada tareda fashewa da kuka tabar qofar dakin tayi waje.


Fitarta yayi daidai da shigowar Bbn nata, durqushewa tayi a gurin cikin kidima dakuma kuka take sanar mishi da halinda ake ciki, cikin fada yace mata karta qara tinkaranshi da wnn maganar duk inda taje ingaji xata dawo yayi shigewarsa cikin gidan yabarta a tsugune kamar maroqiya, kuka takeyi kamar ranta xaifita. Daga qarshe tadawo gidan tashiga dakinsu.

Sadiya tasamu tana yamutsa fuska alamar yanxune take tashi daga bacci, gaisheta tayi, snn tagaya mata, 😳 zaro idanu Sadiya tayi atake taji baccin ya watstsake mata, tanemi tarasa snn tace mata dagaxke kikeyi Nana?

Wlh dagaxke ne, Yaya kitaimakamin ke kadaice xaki iya taimakona, jawota tayi taxaunar da ita abakin gadon tareda cemata kidaina kukan kijirani ina xuwa karfa kifito, To tacemata tana goge idanu don tanada tabbacin Sadiya xata tayata nemo Mmn ta.


Dakin Ummanta tashiga kai tsaye inda tasamu tayi tagumi takasa shanye shayinda ke gabanta, zama tayi ta fuakance ta, snn tafara magana cikin qaramin murya.

Umma ina Mmn Nana take nasan kinada masaniya akan komai bana raba dayan biyu kece👉🏼 tanuna ta, Sauke hannayenta tayi tareda bata lbrn gaba daya abunda yafaru dakuma abunda yake faruwa na bayan shigowan Mal.Habu baiko kulata ba tana kuma yimishi magana yayi banxa da ita, yayi waje abunsa, abunda baitaba faruwa ba arayuwar aurensu tun farko sai yau.


Sadiya tai dagalo da baki gamida tafa hannayenta aqarshe tai salati snn tace Umma? meye hakan? Gaxkiya baki kyautaba wlh matarnan batai miki komai ba, kinhanata farin cikinta, mijinma bakulata yakeyi ba balle kisa ran xata samu wani abinsa, duk da cin mutunci da kikemata aikin gidannan gaba daya itada 'yarta sukeyinsa, amma ko sau daya bata taba nunamiki alamar gajiyawarta kokuma kiji muryanta ba, yanxu haka bakisan halinda takeciki ba dawanda xata fada a gaba ba.

Lami kuwa ba nadaman abunda ta aikata takeyiba ko kadan damuwarta dai sauyin da yake qoqarin tunkarota, can tacewa Sadiya kitashi kibani guri inji da damuwarda take damuna, ai ance ka kashe macucinka tun kapin ya cuceka, mexanyi da kishiya koban cutar da itaba a ranta nasan tanada aniyar cutata.

Bansan meke damunki ba Sadiya Sam yanxu bakya kishina kamar da, kinaga ko maganar rashin auren nan naki, babu hannun Zainabu ne aciki? Hummmm bakida wayo ne ke arayuwarki, snn kinaga nima yau shekara Biyar da komawar Isah Burni haryau babu lbrnsa Dan wayarda yake mananma yanxu yadaina tunda naimishi kaca kaca akan nuna Zalamarsa akan yarinyar nan NANA taqarsa maganar da hada wani tagumin.

Itadai Sadiya tabe bakinta tayi tace mata yanxukam dai yarage naki, Donni yanxu inagab da barin garinnan tai ficewarta tabarta azaune cikin Zulumi.


A Fannin Mama kuwa tun fitarta daga gidan takejin kamar ana qara hankada ta don haka taita tafiya babu takalmi babu dankwali cikin qanqanin lokaci tai tafiya me Nisa, haka intana cikin tafiyar xataji ambata umarnin fara gudu, nan xakaga tafara cilla qafafunta tana gudu.....


Nana kuwa ganin datayi babu maimata maganar mahaifiyarta ne, yasata fita tayi gidan marigayi Mal.Dahiru inda tasamu Zuwaira duniya ta saita mata don tasake sabon aure, kuma a wnn gidan suke zaune, harma da qannenta, sallama tai musu, suka amsa fuskarnan a gimtse kamar sunga mutuwa..

Dama...dama.....dama.... tafadi don gabadaya ta rude, sakamakon hararar da take karba ta kowani fanni daga cikin su, Dame me? Zuwaira ta daka mata tsawa, a daburce ta sanar da su halinda ake ciki, dariya zuwaira tayi kapin tafara magana.


Allah me mutantani wai jaba taga bakin surukarta, Lallai Zainabu wato likafar karuwancin nata ya tabbata knn? Harta San ta tsallake mijinta da 'yarta tashiga duniya, yanxu mekike so muyi miki, mukai shela gidan radio ko telebijin? Inxaki kwantar da hankalinki ki kwantar don kuwa Uwarki tashiga bariki.

Maganar ya matuqar yiwa NANA zafi amma haka ta dake tunda Neman agaji taxoyi tundaga haka bawanda yakulata, saican ne zuwaira tace daga gani ma yunwa ce kecinki gacan qanxo kidauko ki daka kisa gishiri kici, iyakan abunda xan iya miki knn!

Naqoshi

Please Login or Register in order to submit comment