You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gefen gadon tana yamutsa fiska, ranta namata xafi, bahaka taso ganin dakin ba, taso ace dakin yana nan kaca kaca ne, gwanin qazanta, amma ko ina Fes, duk da idan taxo deban kayan abinci saita xuxxubar a qasa, amma bataga alamar sunacikin qunci ba, itako mezatai wa Zainabu taji zuciyarta yamata sanyine? Bata qaunarta ko kadan.


Alala ne Ayashe ta aikowa Sadiya, itakuma batanan, idannace xan ajiye mata kuma kartazo taqici, shine nakawowa 'yarki niya sunanta ne? NANA sunanta tabata amsa, acikin ranta kuwa sunayen Allah taketa karantowa, Ayya Nana miqota taci Alalan, miqata tayi da zuciya daya, itakuwa Nana maqe kafadan ta tayi alamar baxata xoba.

Bayanda batayi ba amma NANA taqi xuwa a qarshe miqawa uwar Alalan tayi tace mata gashi kibata da kanki tasamu taci, karba tayi tafara qoqarin gyara Nana domin tabata, itakuma ganin uwar na dagata saitai tunanin miqata gurin Lami xatayi, don haka ta banqare jikinta tafara kuka harta bangaje kwanon Alalen yaxube gaba daya, gashi dakinnasu babu fulo balle akwashe taci.

Kan Uban can! Abunda Lami tafadi kenan cikin qaraji to wlh kisani kun zubar da abincin ranan ku kai harma dana dare, tunda har kina kallo 'yarki ta zubar zanyi maganinku gaba daya fuuuu tayi waje, Uhmmm murmushi Zainabu tayi snn ta tashi ta gyara gabadaya Inda ya baci...

Fitowarta tsakar gidan batasamu kowa ba, fita tayi tasamu yaro tabashi naira dari yasayo musu buredi domin suci itada 'yarta.


Itakuwa Lami gidan Ayashe tayi tasanar mata abunda yafaru, itakua Ayashe cemata tayi, ke madai Lami kincika zalunci dayawa tunda kinhana uban kulasu kifita harkarsu mana, dukfa a qarqashinki suke, kedai kawai karki kuskura kibari ta karkato da hankalinshi gareta, kenipa tsoro take bani, dakewa kawai nakeyi amma dazaran naganta gabana kefadi.

Snn Alhaji nuhu yanata damuna akan maganar Sadiya, meyasa kika hanata kulashi bayan kinsan irin kudadenda yake Baku, humm ni wlh yanxu damuwata dayace nafison Sadiya tadaina bin maxannan tunda pa kinga zamaninnan cututtuka sunyi yawa ina tsoro wlh


Hahhahhahha lallai Lami amma kinsan nima ta dalilin Sadiya Alhajin nan yana sakemin kudi snn karo daya kicemin xaki rabasu, nikuma Yaya kikeso inyi, rasa abunda xata gayamata ne yasata yin shiru.

Kedai kiyarda dani babu abunda xaifaru da ita kawai kiturota gobe snn karki manta da maganar xuwa bikin 'yar goggon nawa kinsan jibi nepa, kitanada mana kudi isashshe.
Jiki a sanyaye Lami ta baro gidan.

Tana shigowa tayi dakin Sadiya itama kuma isowarta kenan taciro kudi acikin Jakarta tana irgawa, Sadiya wadannan kudaden pa? Cikin gautsin baki tace Bello ne yabani, nashiga uku ni Lami, yanxu Sadiya baxaki daina bin maza ba, gaxkiya Umma kiyi haquri nipa yanxu badon kudi nake binsu ba, inabinsu ne saboda inji dadi.

😳Kiji dadi Sadiya nikike gayawa wnn maganar? Tashi tayi daga gurin uwar tayi waje tabarta a zaune baki bude, takuma kasa rufewa tsabar mamaki, gaxkiya yakamata innemo wa Sadiya taimako, da wnn tunanin tafito.

Itako Sadiya jininta ne yahadu da NANA har yarinyar kuma tasaba da ita, indai tafita yawon gantalinta to a hanyar dawowa saita sayo wa NANA tsaraba. Tun Zainabu tana dari~dari da hakan harta sake.

Lami tasanar da Sadiya maganar Ayashe, itakua cikin zumudi tafara shiryawa, Sadiya bakya tsoro? Lami ta tambayeta, tsoron me Umma? Wlh banajin tsoron komai kinsan yanda Alhajin nan yake kuwa hummm, Sadiya nikam inkinje karki amince kinji, lallai ma Umma ke akwae Wanda yataba hanaki yin abunda ranki yakeso da Bbn Nana ne? Wlh gaxkiya baxan boye mikiba banajin dadin abunda kikemin inkinga kinatsoron injamiki Abun kunya ne, to kiymin aure kawai, tanagama fadin hakan tai waje tayi tafiyarta.

Taje tasamu Alhaji yana jiranta don haka tana shiga basu bata lokaciba, suka dira akan gado, suka fara aiki ba kama hannun yaro, babu abunda kakeji sai nishinsu dakuma qaran gadon qarfen Ayashe.

Bayan tafiyar Alhajinne Ayashe tashigo tana washe baki, snn tacewa Sadiya, kinsan meye ne Sadiya? wlh kinada baiwa king a Alhajinnan? Gyada kanta tayi alamar ganewa, yacemin gaxkiya ya yaba da ni'imarki yakuma bawa uban dakinsa na cikin birni labarinki, don haka inason kibani hadin kai, nikuma zanshige miki gaba. Baqaramin kudi zamu samu daga gurinsu ba.

To ai Ummana baxata yarda ba, dariya tayi kapin tace karki damu nixan shawo kanta, dahaka takarbi 'yan kudaden hannun nata snn tace mata ta sanar da uwarta maganar tafiyar tasu da sassafe ne.
itakuma ta tafi gida babu ko sisi sai uban tsamin jiki.

_WASHE GARI_

Dasassafe Lami tashirya Mal.Habu ta tayar snn tacemishi yawuce yatafi kasuwa, da sassafennan? Ehto yayi sassafe kam amma katashi mufita tare inyaso kaje yaukam kagaida su Baba dagacan kuma kawuce kasuwan, miqewa yayi yaje yadebi ruwa yayi Wanka, kapin fitowarshi a wankan itakuma ta debo ruwa cikin bokiti ta jiqa gurin layar ta, shikuma yafito suka kama hanya, duk abunnan dasukeyi akan idanun Zainabu, tajima tana mamakin meyasa Lami ke yawan jiqa wnn gurin? Tabbas abune me muhimmanci saboda ta lura da ita bata taba mantawa da jiqa gurin, Allah ya kyauta tafadi tamaida kanta cikin daki.

Kapinnan sufita saida tashiga dakin Sadiya tarar tana baccinta harda minshari, daka mata duka tayi acinya itakuma afirgice ta miqe tana Sosa gurin, kisaurareni dakyau, karki kuskura kitapi gantalinki kimanta da jiqa gurin can, kinajina? Naji tafada da bacci a idanunta, itakuma tayi waje.

Rana akeyi katakau hakanne yasa basu zauna a tsakar gidaba , sunacikin dakinsu don basuda runfa, kasancewar gurin daman a mazaunin kitchen yake.

Sadiya kuwa tun bayan fitan ummanta bata jima cikin baccinba tafarka ta wanke fuskarta takuma wanke bakinta tadawo daki ta cancada kwalliya tawuce yawon gantalinta, bata tsaya ko inaba sai dakin Bello anan tayada zango, don ayanxu tagama gano dadin abun, kobai nemetaba tana iya kai kanta, wataran yaqiyi yi dakyar take lallabashi ya yarda, yau dinma hakance takasance.

Bayan isarta a qofar gida tasameshi, alama yayi mata data shiga ciki yanaxuwa, itakuwa taje tabaje akan gado tana jiransa, tashafe yafi tsawon awa guda snn yashigo fuskar nan atamke, can nesa da ita yatsaya snn yace waike Sadiya intambayeki bakya gajiya da abunnan ne? Ni wlh ina mamakin jaraba irintaki, Abu ba abinci ba amma kinkasa gundura dashi wace iriyar mace ceke? Babu Jan aji babu komai yafadi hakan yana tsareta da idanunsa na masu shaye shaye.

Kame kame tafarayi snn tace kayi haquri don Allah Bello nibama saikaban kudi ba nayarda wlh abunne dadi yakemin kuma baya isata, Tab gaxkiya duk Wanda ya aureki kasheshi xakiyi batareda lokacin mutuwarsa tayiba, itadai tananan tayi zugum tanajiransa yayi mata abunda taxo dominshi.

Haka yaxo yafara tumurmusan ta, shikanshi yanajin dadin Tarawa da Sadiya saboda tanada ni'ima amma matsalarsa daya ne da ita bata gajiya, tadinga cakumoka knn baxata gaji ba.


Bayan ya samu nitsuwa ne, yakwanta a gefenta yahau baccin wahala, itakuwa jitayi kamar basuy komaiba kuma tana tsoron yimai magana karya tsigaleta yace xai daina ma gaba daya, a ina tasan zata samo wani.


Bacci ne mai nauyi yadauketa, kamar a mafarki tafara tuno maganar Ummanta, afirgice ta miqe har yamma yayi, gabanta ne yafadi agurguje ta farara sa kayanta, gyalenma a hannu tariqe shi aguje taiyo waje tanupi gida........


😍😍🤝🏼Anatare
Mummyn Fadyl CE




🎲🎲TUDUN DAFAWA🎲🎲


Rubutawa....MUMMYN FADYL (Fatyma Muhammad Adamu)

Wattpad @ *fatimamuhammadadamu*


INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION*
*[onward together]*
*{we give the reader's of ours the best out of the bests,, our inks are melodious and dropping a kinda lights to reader's}*
```THE PEN OF LOVE😘 HEAT TORCHING❤ TEAR OF SORROWS😭 CURDLES😊 GIGGLES😁 AND MARRIEGE THINK💑```
*```JUST GIVE US FOLLOW..**


_ko a mafarki bantaba tunanin xansamu masoya masu bibiyata ba, amma gashi lokaci daya nasamu harda wadanda banyi tsammani ba, godiya me tarin yawa gareku masoyana nacikin Facebook, watxapp harma da wattpad, masu bani shawarwari ta private damasu kirana, bansan dawani baki xanyi godiya ba, NAGODE NAGODE I SINCERELY LUV U ALL_


Fitowa ta.1⃣8⃣


Kamar Anjehota haka tafado cikin gidan gurin ajiyar mahaifiyar tata, amma abushe tasamu gurin, cikin gigita ta antayo ruwa cikin bokiti ta kwaza agurin taqara taxuba sau uku tana zubawa, duka akan idon Zainabu, Sadiya na juyawa suka hada idanu, cikin borin kunya tafara magana.


Maman NANA ina qanwata take? Qanwarki tana bacci, murmushi tayi taqarasa gurinta kawo intayaki wanke wanken, Mama tace a'a Sadiya bari jeki huta abunki.

Tanaso ta tambayeta meyasa take zubawa gurincan ruwa kullum, saikuma xuciyarta ta kwabeta da cewar tafita daga abunda babu ruwanta, da wnn shawaran na zuciyarta takama bakinta tayi gum tareda bin Sadiya da idanuwa.

Itakuwa Sadiya tana Shiga daki ta sauke nannauyan ajiyar zuciya, tareda fadin Allah yasa kar Umma tagane,nan tacire kayanta tanupi waje domin yin wanka Duk da bawai wankan tsarki takeyi ba, itadai wankanta kawae takeyi na sabulu.


Sai bayan sallan isha ne Lami ta iso gidan, gurin ajiyarta tafara dubawa, ganinda tayi gurin a jiqe ne, yasata sakin murmushi taleqa dakin Sadiya ganinta tayi tana sharara baccinta sakin labuleb tayi tanupi nata dakin.

Bayan Mal.Habu yashigo cikin gidanne daidai gurin ajiyar Lami, jiyayi kamar yatuno dawani abunda yajima da mantawa amma yarasa gane menene, ganin zai takura kansa da tunani ne yasashi barin qoqarin tunawa.


Dakin Lami yashiga kamar kullum karban ledan hannunsa tayi batareda tambayarsa labarin kasuwa ba, dukda yanxu al'amura sungama kwabe masa, shagonsa ta koma baya bana wasa ba, amma kosau daya tun aurenshi da Lami bata taba tuntubarsa akan harkokin kasuwancin nasa ba, itadai yabata kudin kawai, Bashi yanason yai yawa akansa.


Saida tagama duba ledan snn tai murmushi tace Ashe baka manta da saqon kifinnawa ba, gaxkiya Idi duk fadin unguwarnan bawanda yakaishi iya suya, shiko binta kawai yakeyi da kallo qarshe yace mata bari yaje ya watsa ruwa yadawo. To shknn nima bari intashi inmiqawa Sadiya nata.


Dawowanshi daga wanka ne kamar kullum yauma saida ta mulkeshi da wnn man nata me uban qarni, Sam wnn man bayajin dadinsa amma kuma ko xa'asa mishi wuqa a wuyansa baxai taba yunqurin fada mata ba.


A wnn Daren bacci baiyi gigin daukan Habu ba, saboda yawan tunane tunanen daya addabeshi, kamar Wanda aka tsikara da allura haka yatashi, kallon Lami yayi, yaga tabude qaton bakinta tana ta sharara minshari, cikin sanda ya lallaba yafito waje baitsaya ko inaba sai qofar dakin Zainabu, tura qofan yayi a hankali, yatura kansa ciki, tanakan darduma ta idar da sallah tana addu'oi qaran kamar shigowan mutum ne yasata saurin lalubo tocilan ta, kamar daga Sama taga Habu, Rasa ta inda xaifara yayi, kawai Saiya durqusa a gabanta tareda kafeta da idanunsa masu kashe mata jiki aduk lokacinda tayi tozali dasu.

Mekake buqata, tayi tambaya cikin rawar murya, toshe mata baki yayi, snn yafara magana a hankali, Zainabu bansan meyake damuna ba, Sam banida tunani aduk lokacinda nace xanyi tunanin wani Abu atake nake tsintar kaina cikin mawuyacin hali, bansan Yaya zan misalta miki yanda nakeji ba, inama da inada iko, toda babu shakka xanbude miki zuciyata koxaki iyamini wani taimakona akai, rufe bakinta tayi da tafukan hannayenta sakamakon kukan da yake qoqarin kwace mata, miqewa yayi tareda karban tocilan hannunta, ya qarasa bakin gado haska NANA yayi yanata kallonta amma yakasa jin komai akanta, zama yayi tareda tallafe kansa, saboda wani azababban ciwo dayake barazanar raba mishi kai gida biyu.


Can kuma kamar walqiya yafita a dakin, hakanne yasa Zainabu kokonto kodai Mijinta yafara mata gizo ne, tabbas gixo ne don babu yanda ma xa'ayi yayi tunanin xuwa gurinta harya duba 'yarta.


Juyawa gurin NANA tayi tarungumeta tana kuka, fadi take aranta, 'yata kiyi haquri tamu kalar qaddaran kenan nataso bansan gatan kowa ba saina mahaifi, daga baya nasamu gatan miji, tun tafiyar batai nisa ba narasa kulawar mijina, snn narasa mahaifina rasawa ta har abada, yabar duniya bamuda *TUDUN DAFAWA* ina roqon Allah kobayan raina ya *DAFA* miki banson kiy rayuwar qunci irinnawa ke kadai kika ragemin da wadannan zancen zucin bacci yayi Awon gaba da ita.


~BAYAN SHEKARA GOMA SHA UKU~

Rayuwarsu haka tayita tafiya babu wani sauyi acikinta, Habu yacigaba da satar dare yana Shiga dakin Zainabu batareda Lami tasani ba, amma abunda yake bata mamaki shine baitaba yunqurin koda kama hannunta ba, Sadiya tasan shi a matsayin mahaifi amma babu shaquwa balle soyayya tsakaninsu, hakan sayo musu Abu ya turo musu ta _window_ da wadannan kudaden take samu Duke saida 'yan kayan miya take kuma biyawa NANA kudin makaranta, amma a tsakar gida tamkar baisan da zamansu ba, tun NANA tana bibiyarshi harta daina.

Nana tagirma yarinyar me kyau,kwarjini dakuma cikar haiba, ga ilimi, samari sunfara cicirindo akanta amma bata taba basu fuska ba, kyanta yanata qara fitowa batada shishshigi ko kadan, snn tana ajiye kanta inda Allah ya ajiyeta.

A Bangaren Lami kuwa duniya tagama saita mata, tagama samun yanda takeso a rayuwa kuma duk abunda Mal.Habu yakeyi tasani sarai don MAYE yagaya mata wnn ajiyar nata anbarshi ya bushe dole asirin xaiyi rawa, tasan komai amma taxuba musu ido ne don tanada tabbacin babu abunda xasuyi saboda qullin da taimusu ba qarami bane, saidai haryanxu burinta naganin taraba Zainabu da gidan haryanxu baicika ba.


Sadiya kuwa likafar iskanci yagama Jan gaba, saboda a yawon iskancinta tahadu da qawayen banxa inda suka bude mata idanu Wanda xuwa wnn lokacin harcikin gari takexuwa, tagirma sosae sa'anninta duk sunyi aure harda 'ya'ya, gashi bata ganin kowa da gashin ido,ciki kuwa harda uwarta, batajin maganar ta koda wasa, don inta matsa mata da magana topa watsewa sukeyi baram baram, harta gaji taxura mata idanu.



Da Safe Mama ce tafito hada kayan kumallo a qofar dakinta inda tahura wuta tanajiran dawowar NANA daga markaden qosan da xasuyi na karyawa, itakuma tadaura ruwan da xata Dana kunun tsamiya akan wuta.


Sadiya ce tafito a guje ko qarasowa bakin makwarari batayiba aqofar dakinta tafara kwarara amai ba qaqqautawa, idanun nan sunyiwo waje kai dagani kasan tanashan azaba, Mama ce taisaurin debo ruwa a buta, tanufo ta amma kapin ta qaraso Lami tayi saurin bangajeta Meye haka Zainabu, kindauka bansan abubuwanda kikeyi bane?


Kin asircemin yarinya batajin maganar kowa sainaki, kinshayar min da ita guba, tun farin rashin lpyrta nan dama nasan da hannuwanki a ciki, to wlh kifita a idona idan kika kuskura kika cigaba da shiga tsbgata wlh xanmiki abunda bakya tunani.

Sallamar Nana ce yahana Mama furta komai tayi gurinta tana tambayarta kindawo? Saboda tasan yanxu Nana tagirma takuma fara Ankara da irin zamanda sukeyi agidan, baxataso yarinyar ta taso da wadannan tunane tunanen ba don sungirmi shekarunta, ki ajiye qullin ki karbo kayan hadi gurin Ummanku kikawo.


Itakuwa Lami kama hannun Sadiya tayi suka nupi dakinta da ita, kwantar da ita tayi snn tafara tambayarta, Sadiya nipa ina lura da yanayinki a kwanakinnan meke damunki ne? Saida ta yamutsa fuska snn tace wlh Umma xazzabine saikuma kasala, Nashiga uku na doka lullubi ni Lami, yaushe rabonki da ganin Al'adarki? Yanxu wata na biyu kenan! Hannu tafara tafawa tana salati, kinga abunda naketa gujewa knn oh ni yanxu yaxanyi dake Sadiya? Kodayake ta inda aka hau tanan ake sauka, dare nayi idan qafa yafara daukewa a layinnan xamu nupi gidan Ayashe tasan yanda xatayi dake.


Fitowa tayi daga dakin snn tafara yabawa Mama baqaqen maganganu itakuwa kamar batasan da ita yakeyi ba, saida ta tabbatar takai aya snn tace mata kibamu kayan hadin qosan Rana tafarayi kuma ba'a fara suya ba, Baza'a bayarba tafada cikin hargagi wlh yau sakamakon baqantamin rai dakukayi saidai kuwuni da yunwa atoh, tawuce dakinta ta barsu baki bude.

Tana shigewa ciki Nana takalli magaifiyarta da hawayenda suka fara cika mata idanu tace, Mama Ke meyasa Baba baya baki kayan hadin ki ajiye, kuma adakin Umma babu kayan abinci? A gidansu hauwa'u ba suma Matan Babansu biyune amma kowa tanayin girki, meyasa Umma batayi?


Kai Nana kincika tambaya yanxu wanne kikeso in amsa miki? Banason kinasa damuwa a ranki, komai kikaga yafaru tofa yanada sila kuma xaiwuce babu abunda yazo domin zama, dadi ko baqinciki xai wuce kinji, kisaki ranki 'yata kinji? Murmushi tayi...

Kishiga daki. A qasan filo akwai naira goma kisayo mana gishiri mumaida qullin na Alale, kapin kidawo xan wanke mana gwangwani kinji? Umma babu manja da yaji pa, karki damu bakullum akecin abinci don dadi ba, kedai kiysauri kidawo kisamu kici kitapi makaranta ,yanxu xakiga Hauwa'u ta turo.


*DA DADDARE*
Bayan Lami ta tisa qeyar Sadiya suka nupi gidan Ayashe shikuma Mal.Habu dawowarshi yasamu babu Lami hakan yasa cikin sauri yanupi dakin Zainabu, yaci sa'a itakadai ce, don Lami tasaka Nana gyaran dakin Sadiya inda tabata shida Amai.

Cikin sassarfa yaqarasa gurinta kamar wani mayunwacin zaki, cikin mamaki takedubanshi da irin sauyinda yaukuma aka samu, bata bata mishi lokaci ba, don idan tace batai kewar mijintaba tayi qarya shekara nawa?
(Zainabu tsohon tsumi ya motsa😜)

Nan suka shige jikin juna batareda fargaban komai ba, cikin shauqi suka raba junansu da kayan jikinsu, suna gab da isarda saqonne pa, Mal.Habu yamiqe a firgice sakamakon............



😍😍🤝🏼Anatare
Mummyn Fadyl CE



🎲🎲TUDUN DAFAWA🎲🎲


Rubutawa....MUMMYN FADYL (Fatyma Muhammad Adamu)

Wattpad @ *fatimamuhammadadamu*


INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION*
*[onward together]*
*{we give the reader's of ours the best out of the bests,, our inks are melodious and dropping a kinda lights to reader's}*
```THE PEN OF LOVE😘 HEAT TORCHING❤ TEAR OF SORROWS😭 CURDLES😊 GIGGLES😁 AND MARRIEGE THINK💑```
*```JUST GIVE US FOLLOW..**


*Hannu daya a Sama, sama 🙋🏾‍♀ kai a qasa, qasa🙇🏻‍♂ fidda waya waya, 📞 kiramana haba haba haba💃🏼💃🏼💃🏼 Wnn shafin nakune Alhaji Hamma's family especially Matan much luv 'yan uwana*


Fitowa ta.1⃣9⃣

Miqewa yayi a firgice sakamakon jin Abunashi kwata kwata yakoma yakwanta luguf kamar lagwani, itama Zainabun miqewa tayi tana tambayarsa lpy? Kasa amsamata tambayar yayi snn yafara qara qoqarin ganin ya cimma burinsa.

Haka yaita fama gurin sau biyar, xata tashi tsab amma dazaran yayi yunqurin shigar da ita zatakoma takwanta, haryakai Zainabu tafahimci halinda ake ciki, kifewa a gurin tayi tafashe da kuka maiban tausayi, inda shikuma yadafe kansa cikin takaici dakuma al'ajabin wnn sabon al'amarin da yakuma dunfaro shi, to Kodai banida lpy ne? Tambayarda yayi wa kansa kenan amma kumapa jiyama yakwanta da Lami lafiya lau, pa.


To menene manufar hakan? Abubuwa sunmishi yawa a kwakwalwarsa yarasa dawanne xaifara, juyawa yayi da niyyar lallashin Mama amma alamun ana taba qofar gida da niyyar shigowane ya hanashi, cikin sauri yakintsa a hargitse ya fita haryana tuntube, yayi dakin Lami itakuma Nana lokacin xatayi dakin Mamanta ganin mahaifinnata cikin wnn halin yasata saurin shiga dakinnasu.

Mama daganinta taisaurin gyarawa snn tafara qoqarin qaqalo murmushi Wanda kana gani kasan iya fatar bakinta ya tsaya, Mama menene, meye Baba yayi miki? Babu abunda Yayi mini Nana kaina kemin ciwo kuma yakawo min magani ne nasha, to kuma naga yafita haryana tuntube yashiga dakin Umma?

Hoo ni Nana ban hanaki shiga abunda babu ruwanki ba? Kiyi haquri Mama baxan sake ba, shikenan maxa yiki kwanta karki makara sallan Asuba, kwanciya Nana tayi, itama kwanciya tayi amma bataga alamar bacci xai iya kusantota da garaje ba, hakan yasata miqewa tanupi bayi wanka tadauro alwala tadawo ciki.


Itakuma Lami can gidan Ayashe kwashe mata halinda Sadiya keciki gaba daya tayi snn taqara da cewa kinga pa Ayashe abunda naketa gujewa knn, niyanxu babu abunda nafi qauna kamar Sadiya tayi aure, harga Allah nagaji da zamanta haka kiduba pa kiga sa'anninta duk sunyi aure.

Ayashe kuwa acikin ranta cewa take ai aure kam bayanxu ba, don nalura ajikinta xanpi samu fiye dake, abunda Lami bata saniba Ayashe CE taiwa Sadiya karfa da auren snn kuma akasa mata jaraban maxa,

A fili kuwa cewa tayi Lami yanxu dai dukba wnn ba, kibari Alhaji inyazo insanar dashi gobe dasafe nasan xaisan yanda xa'ayi da cikin, Yo wani Alhaji kuma Ayashe?

Nida nakeson muxubar dashi, yabi rariya batareda kowa yaji me ake ciki ba, a'a karki sanar dashi muje dai chemist da ita kawai mubiya, ayita taqare a darennan, tunma kapin yacigaba da girma,yanxu ma bansan watannin sa ba, inagadai yayi wata biyu.

A'ah yanxu kam dare yayi sosae snn idan muka tafi da ita, aimunso tonon asirin kenan, kibari gobe dasafe xan biyo miki muje mu biyu mu amso maganin tasha agida kawae kinga bawanda yasan anyi koya kikagani? Eh hakanma yayi duban Sadiya tayi wacce tun isowarsu ta bingire a gurin taketa sharara baccinta, daka mata mari tayi tareda Daka mata uban tsawa tamiqe suka kama hanyar gida.

_WASHE GARI_

kamar yanda suka tsara haka Ayashe taxo, iso taimata har cikin daki, snn tamiqe xuwa gurin Mama karbo mata abun karyawa, tana fita Ayashe tacigaba da bin dakin da kallo kamar kullum tareda raya abubuwa da dama aranta, kwafa tayi a qarshe snn tagyara xamanta.

Shigowa Lami tayi bayan ta'ajiyemata takuma hada mata shayi snn tace mata bari taje tayi wanka, bayan fitarta nanma Ayashe miqewa tayi taduba cikin jakar Lami Wanda takeda tabbacin acikinsa take ajiya, don tana lura da ita kullum acikinsa take daukan kudi, 😳😳zaro tayi sabodan yawan kudadenda tagani a cikin jakar, lallai Lami shine idanna tambayeta kudi taita karantomin babu? Xanyi maganinki, saurin komawa mazauninta tayi. Saboda tajiyo qarar tahowan Lami, don ita tafiyarta baya buya yanda kasan doki haka take😜

Dakyar Ayashe ta daidaita nutsuwarta sabada ita kadai tasan yanda xuciyarta kemata suya, dakuma abunda take qudirtawa aranta, Lami tagama shirinta tsaf. Snn tabawa Ayashe baya tadauko jakar a fakaice kamar babu abun arziki a ciki, zaro kudi tayi kadan aciki snn tafara cewa, wlh Ayashe yanxu Sam babu ciniki a kasuwar kudi sunfara yankemin, Allah sarki kawai ta iya fadi tareda tabe bakinta. Tagama shirinta suka fito domin tafiya, Mama ko tana dakinta Nana ce a tsakar gidan taketa kaikawo a dakin Sadiya, tasakata taimata fate, gashi kuma ta malala Amai a tsakar dakin, Nana tanashan wahalar jinyar Sadiya, duk da haka tana mugun tausayinta don koba komai Sadiya tana qaunarta, sau da dama takan bita idan xata tafi makaranta tabita waje domin tadan bata na kashewa, itako bata saba kashe kashen kudiba haka take dawo dashi gida tabawa Mmn ta.


Ganinsu yasata ruaunawa tace Umma Ayashe ina kwana, bankwana ba don gidanku shegiyar yarinya wacce tai gadon kissa, kyaleta Ayashe mutafi abunda ke gabanmu yawuce mutsaya muna kula wnn me idanun magen,

Saida suka fara tafiya snn Lami tace Ayashe nipa da akwai yanda xa'ayi ma zanso amaida cikin nan jikin wnn yarinyar Nana, wlh tatsayamin a maqogoro yanda kikasan qashin kifi, wlh nafi tsanarta akan uwar, duk abunda nashirya akanta bayaci, kinaga badon Maye ya ankarar dani dawuri bafa da aikin gama yagama xuwa yanxu.

Ayashe bata iya cemata komai ba don xuciyarta acike yake da haushinsu gaba daya......

Mai shagon yagama yin sabo da Ayashe don takan kawo mishi _customers_ sosae don haka yana ganinta yasan tasamu, gaisawa sukayi snn sukai mishi bayani, tambayarsu yayi watannin cikin, bayan sun sanar mishi ne yabasu magunguna Lami tafito da kudi tabayar, miqo mata canji yayi rige rigen karba sukayi da Ayashe amma Lami ce tayi Nasarar karbewa abunda yaqara cin ran Ayashe knn takuma qara tamke fuska tareda qara jaddada qudirin zuciyarta....


Yanda sukaga Rana haka sukaga dare a bayan Sadiya tayi amfani da magungunan da suka kawo mata, ciwo harda fadowa a gado, har Mal.Habu a dakin Sadiya ya kwana, yanason ya tambayi cuwon menene amma yana tsoron Lami da amsar da xata bashi, suna tsaye cirko cirko, ihunta ne yatado Mama da Nana suka nufo dakin a guje, amma suna shiga Lami tafara jefansu da baqaqen maganganu tareda cewa duk itace silar ciwon 'yarta kuma a sannu xaikoma kanta.


Itakuwa Mama ganin cin xarafin yafara yawa ne yasata Jan Hannun 'yarta sukabar musu dakin sum sum da Harara tabisu, shikuma yatsaya yanda kasan hoto saibinsu da idanu kawai yakeyi.

Sai gab da Asuba snn Sadiya tasamu bacci me nauyi ya dauketa, ananne suma suka nupi dakinsu Mal.habu kuwa ganin asuba ya qarato shiyasa baikoma bacci ba, itakuwa Lami kan katifa tafada, acikin abunda baifi minti biyiba sai tashin minsharinta takeji, kamar wata kwado.



*BAYAN KWANA ASHIRIN DA BIYU*

Sadiya ta warke tsab takoma harkokinta harma yafi nada, tunda yanxu Alhaji yana hadata da ubannin dakinsa, kudi kam sai dai tabawa Ayashe don batada buqatarsu itadai taji dadinta😋..

Ayashe ce tazo gidan Lami saboda Alhajin yayi mata maganar wani uban gidansa, kuma kwana yakeson yayi da Sadiya, yabata maqudan kudade akan indai takawo mishi ita toxai ninka mata ninki baninkin wnn kudin, ai jiki na kyarma tazari gyale tayi gidan Lami ba shiri...


Lami tasamu tana tsakar gida, filet din dafaffen kwai ne aganta tanaci hankali a kwance, ta mimmiqe qafafu Nana tana daddana mata, harwani lumshe idanu takeyi.

Maraba da Ayashe tafada tana fadada fara'arta, kina hutawa qawata, kekuma

Please Login or Register in order to submit comment