You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ne yadawo sabo fill.


Subhanallah tafada tanason qara yimata wasu tambayoyin amma ganin kukan nata baxai barta tayi magana ba, yasa Haj. Maryam yin shiru Badon taso hakanba.


Kinsan menakedo dake? Da kai tabata amsa don baxata iyacewa qala ba, kitashi kitafi dakinki xan aiko miki da abinci kici kikwanta kihuta xamu hadu gobe a safe idan Allah yakaimu darai. Nagode tafada tareda miqewa tabar gurin.


&&&&&&&&&&&&&&

Tun tafiyarsu ba'a samu xarafin yin waya dasuba, yau Zarah tana xaune a falo taci kwalliyarta itada humairah suna hiran makaranta.


Zarah ce take cewa Humaira nifa wlh a A class naso asani domin naga sunfi kowa rawan kai acikin mate dinmu, humairah ko cewa tayi kedai kice can kikeso asaki kodon ma kuyta fada dasu, on kam Zarah bansan dadin da kikeji a fadace fadace ba.


Mtswww shiyasa kikebani haushi wlh humairah ke kullum ba'a tafiya dai dai dake, maganarta ne yatsaya a fatar bakinta sakamakon wayar mummy dataji yanata amsa kuwwa a cikin falon.


Aiko dagudu tadauko ganin sunan yasata dauka cikin sauri da zumudi ta kara visa kunnenta tareda cewa Hello Yayah Aliey ya karatu shine sai yau xaka kiramu ko? Kullum sai mummy tayi maganarka yaushe xaka dawo? Haka taita maganganunta shikua tunfarkon daya fahimci ita tadau wayan, kawai yasa wayar a hands free yacigaba da tsabgoginsa tayi duk abunda xatai intagama takai wa wacce yakira domin ta.


A qarshe dai dataga baida niyyar magan sai tsakinta ta danna tareda cewa inka yi magana ma, to wlh bakaci sunanka ba, taqarasa dakin Mummyn tana ta guna guninta cikin takaici tamiqa mata wayar taiyo waje abunta.


_Kuymin uxiri yau ina busy ne wlh, kunsan ance yau da gobe kayan Allah_



😍😍🤝🏼 Anatare
Mummyn Fadyl CE




🎲🎲TUDUN DAFAWA🎲🎲


Rubutawa....MUMMYN FADYL (Fatyma Muhammad Adamu)

Wattpad @ *fatimamuhammadadamu*


INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION*
*[onward together]*
*{we give the reader's of ours the best out of the bests,, our inks are melodious and dropping a kinda lights to reader's}*
```THE PEN OF LOVE😘 HEAT TORCHING❤ TEAR OF SORROWS😭 CURDLES😊 GIGGLES😁 AND MARRIEGE THINK💑```
*```JUST GIVE US FOLLOW..**


Fitowa ta. 4⃣3⃣



Mummy ko batareda da tadubi sunan Wanda yakira dinba takara wayar a kunnenta tareda yin sallama, yanajin maganar mummynsa yayi sauri amsata cikin farin cikin da nuna jin dadin magana da ita din.


Gaisawa sukayi sosai kamar yanda suka saba snn taimishi gorin meyasa tun tafiyarsu tsawon sati biyu bai nemesu ba dagashi har IBBY? Haquri yabata tareda nuna mata abubuwanne basu gama kammala shiba amma dai yanxu Alhmdllh sun gama komai kuma xasu fara karatu nan da satikai uku masu xua. Fatan alheri taimusu snn suka taba hirarrakinsu na da da uwa, inda a qarshe take bashi lbrn zarah tashiga js1 pa.


Batareda tunanin komai ba yacemata wnn kam ai IBBY xaki gayawa dariya tayi me isarta snn tace mishi dakai da ibbyn wayafi kusanci da ita, amsa yabata kai tsaye yace mata, mummy IBBY yanaban mamaki wlh Shifa dagaxke yanason yarinyar nan, kuma mummy tun zuwanmu baida magana saina matsalan mamanta, kullum maganarshi tayaya xa'a samu warakan cutar ta.


Tsam tayi tana sauraranshi a qarshe ta jinjina kai tace dashi wlh nima Son matsalar matannan yana damuna, yanxu dai daddyn ka yayi min maganar xa'a fita da ita Egypt kuma yana tunanin likitocin su nacan sunpi namu kwarewa ba shakka xa'a samu waraka, mudai bawa abun tym, komai xai xama tarihi, to Allah yasa mummy Amin ta amsa, sukai sallama bayan ya gama Cuba mata shagwaba da uban qorafe qorafe.


Bayan yagama cin abincinsa ne matarshi ta tartare gurin, bata sauraresu ba tai shigewarta daki, amma saita tsinci kanta da baxata iya xaman dakin batare da taji meye lami keson sanar da mijinta ba, don haka tamatso gab da labule tafara sauraronsu.


Uhmmmm ya gajiya tafada cikin langabar da kayinta, cikin qosawa da ita ya amsa, itakuwa batama kalli fuskarsa ba tafara magana cikin kirsa da kissina...


Wlh wata alfarma nakeson nema a gurinka inafatan xan samu, Allah yasa xan iya yabata amsa, Ita kuma ta Dora dacewa nace mexai hana ka aureni tunda Kanada daman yin hakan? A tunanina hakanne xaisa yaran marigayi su San baka bar musu uwarsu a wulaqance ba, snn nima kuma ka 'yantamin rayuwata, tafadi maganar kanta tsaye cikin sarrafa harshe....


Ba matarshi kadaiba, harshima sanda hanjin cikinsa suka kada, itakuwa matarshi a cikin dakin jitayi qafafunta sun kasa riqeta, aiko babu shiri ta sunkuya cikin faduwar gaba, shknn kwann aurena ya qare, nashiga uku ina zamana xaya jawomin bala'i ina zaman zamana.

Banji kace komai ba kayi shiru, yaji muryarta ne yafarkar dashi daga duniyar tunanin da ya Afka, firgigit yace mata kibani kwana biyu xanyi tinani, yatashi yabar gurin, India yabarta a xaune kamar an shukata, yana Shiva dakin yasamu matarshi a tsakar dakin, cemishi tayi matsawar kaxabi xama da Lami amatsayin matar aurenka da kake fatan ka hadamu inuwa daya to wlh kayi babban kuskure domin kuwa baxan xauna da ita ba, gurin akwatin ta tanufa ta fara kwashe kayanta na sawa, batare da ta kalleshi ba, shikuwa a raxane yanufi gurinta....


*Washe gari*

A tasha Mal.Habu ya kwana da sassafe kuwa ya shiga cikin anguwan saidai abunda ya daure mishi kai shine an sauya anguwan domin gidajen gaba daya kusan Kama sukeyi, yarasa Wanda xai fara nufa a cikinsu a qarshe yayi shahadar fara Shiga daya bayan dayan duk da yana tsoro yanakuma fatan kar Allah yasa ya hadu da marasa mutunci, sumai rashin mutuncin mutanen birni.


Da wannan tunanin nashi yafara nufan gida na farko ya kwankwasa yana addu'oi a cikin ransa, bude qofar akayi cikin sa'a kuwa yayi arba da Dan uwansa abunda baiyi tsammani ba samun sauqi batareda yasha wahala ba, ikon Allah kawai suketa fada gaba dayansu, cikin farin ciki yace mishi shigo shigo daga ciki habu yau Kaine a gurina?


Shiko murmushi kawai yaketayi yana qara godewa ubangijin sa na taqaita mishi wahala dayayi cikin qanqanin lokaci, dakinshi yashigar dashi shiko yafito da Sauri sakamakon horn din motar dayaji, Wanda ya tabbatar mishi uban dakinsa ne dawo.


Aiko dasauri yafita ya wangale mishi gate din shiko cikin mahaukacin gudu yashigo yayi matuqar ganinsa batareda da direban sa ba, ya tabbatar ba qaramin Abu bane yake faruwa Allah yasa lpy dai haka yafada a ranshi yarufe gate din snn yanufi dakinsa gurin Dan uwansa.


Alhaji inuwa knn, director na ministry of health dake jahar, mijin hajiya maryam, ga mutum har mutum a waje amma cikinsa Sam baida dadin tonawa, akwai kirki da iya mu'amala amma kash indai ta harkan mata ne, tofa yanada tawaya, baya iya kauda kai Indai akan powder ne.


Yana cikin wnn mahaukacin saurin ne, dayaga ya isa cikin palon babu shiri saurin nashi yayi matuqar sanyi tunawa da yayi da case dinda ke gabansa, yanada tabbacin baxata kulashi akan maganar ba, amma yana jin nauyin hada idanu da ita. Yasan ta shareshi ne domin daga idanuwanta ya fahimci maganganun da yayi mata bai shigeta ba.



Cikin sanyin guiwa ya murda qofan dakinta a xaune yasameta a gaban mirror da alama fitowanta knn daga wanka, ta mirror ta hangoshi taji haushinshi a ranta tumawa datayi da abunda yayi mata jiyan amma saitaga nuna bacin rai banata bane, sake fuskarta tayi tamiqe tareda cewa barka da safiya Bbn Ilham tariqo hannunsa tanufi bakin gado dashi, shiko kamar wani solobiyo haka yabita jikinshi duk a sanyaye yake.


Shidai wannan halin na Maryam yanasa shi cikin gashi ace kayiwa mace laipi amma takasa nunawa akan fuskarta balle kayi tunanin xata dauki mataki a kanka? Gaxkiya hakan yafiyimishi, saboda baisan metake qullawa ba, saidai watarana yakan ji ta yanko mishi magana dayakan kasa gane madosar su.


Saida ta danganashi da bakin gadon yaxauna snn tajawo stool din mirror taxauna a gabanshi tafara gaidashi cikin nuna biyayya, amsata yayi cikin farin ciki snn yafara magana cikin langwasar da kai yace, Maryam inason abunda yafaru jiya........ Shhhshhshh tadora mishi hannu akan bakinshi tahanashi qarasa abunda yakeson fadin, binta yayu da idanu yana sauraronta...


Haba mijina mexaisa mu attauna dakai akan abunda kace yafaru jiya? Kaida bakinka kace jiya idan mukace xamu cigaba da tuna abubuwanda suke faruwa a baya, topa bashakka baxamu samu farinciki da jin dadi ba, don haka jiya yawuce, muna yau inafatan xamu gyara aiyukan jiyanmu cikin yimishi gyara dakuma kwaskwarima da ayyukan yau, taqarasa maganarta cikin sakarmishi tattausan murmushi....


Duk dai bama wnn ba bari insa kayana muje dinning kaci abinci ka qoshi akwai maganar da nakeson my tattauna dakai......



😍😍🤝🏼 anatare
Mummyn Fadyl CE




🎲🎲TUDUN DAFAWA🎲🎲


Rubutawa....MUMMYN FADYL (Fatyma Muhammad Adamu)

Wattpad @ *fatimamuhammadadamu*


INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION*
*[onward together]*
*{we give the reader's of ours the best out of the bests,, our inks are melodious and dropping a kinda lights to reader's}*
```THE PEN OF LOVE😘 HEAT TORCHING❤ TEAR OF SORROWS😭 CURDLES😊 GIGGLES😁 AND MARRIEGE THINK💑```
*```JUST GIVE US FOLLOW..**


*My Fans badon kuba Dana ajiye rubuta wnn labarin, don kuwa ya tsayamin a wuya kamar qashin kifi a wuya, kutayani da addu'a Allah ya dafamin insamu ingama shi cikin satinnan wlh nagaji kunsan 'yar koyo ce ni* 😜



Fitowa ta. 4⃣4⃣


Tashi tayi bayan tagama kintsawa tafito falo shikuma yana biye da ita har dinning area, abinci ta xuba musu cikin nitsuwa shikuma sai binta yakeyi da kallo a xyciyarsa yana qara godewa Allah da ni'imar nagartacciyar mata daya mishi, harta kammala abunda takeyi, yaga tahada tea a wani cup takuma Debi abinci a plate snn yaga tanufi dakin yara dashi, yasan dai wa yarinyar xata kai.


Jiyayi inama yanada qarfin guiwar binta, Aida yaje yaganta, gaxkiya yarinyar ta hadu, gashi kua amma anruguxa mishi gaba dayan shirinsa.


Da sallama tashiga cikin dakin, samunta tayi a tsakiyar gadon tana kwance ta duqunqune kanta cikin bargo, ba bacci takeyi ba, amma xakai tsammanin baccin takeyi, domin motsin kirki bayinshi takeyi ba, Amsa sallamar tayi gamida tashi xaune data ganta da Abu a hannunta kuma tafara kiciniyar sauqowa ta karbeta.


Da murmushi Hajiya Maryam ta miqa mata plate din, itakuma ta ajiye ta durqusa a gabanta tagaisheta amsawa tayi cikin sakin fuska, snn tace da ita kiyi kumallo kapinnan nima ingama inaxua, nagode tafada itakuma tamiqe tabar dakin tareda jawo mata qofa.


Dawowa falon tayi tasameshi a xaune yagama shagaltuwa gurin tunani, isowarta ta hura mishi iskan bakinta, firgita yayi snn yasakar mata murmushi xama tayi a kujeranda ke fudkantar nashi, shuru gurin yayi suka fara cin abincin nasu a nutse sabanin shi, Wanda kawai turawa yakeyi domin xuciyarshi takasu kashi biyu, dayan yatafi tunananin yarinyar da ko sunanta bai saniba, dayan kuma yana tunanin maganar da Maryam tace xasuyi da ita.


A haka har suka gama cin abincin nasu, bayan tayi hamdala tadago ta kalleshi, shidinma ita yake kallo, atare sukai murmushi wa juna, shiya farayin magana cikin qarfin hali, inajinki na qagu ki sanar dani maganar da kika ce xamuyin.


Canxa fuska tayi cikin sigan rarrashi tafara magana, Alhaji inason kadubi girman ubangijinka katuna da mutuwa dakuma kwanciyar kabari kasanar dani alaqarka da yarinyar na Wanda ka haife wa wadanda suka girme mata?

Sosa kanshi yayi badon yana tsoronta bane yakasa bata amsa a'a yana matuqar jin nauyinta, saboda kawaicinta tajima tana kamashi da laipinda sukafi wannan muni indai ta harkan mata ne, banda labaran da ake bata, kuma bata taba nunamishi alamar daukan mataki ba kokuwa xafin abun ba.


Ganin alamun rashin gaxkiya ya bayyana akan fuskarsa qarara ne yasata murmushin takaici tace akullum burina inganka cikin farin ciki, inga na inganta maka rayuwarka ta hanyan haskaka rayuwar aurenmu, ina maka biyayya a iya tunanina bangaxa maka ba har akan shimfida, amma meyasa kakeson yin hakan? Bai bata amsa ba.


Hakan yasata sake ce mishi, shin kasan daga ina aka dauko maka ita? Kayi tunanin iyayenta? Akaso a dauki 'yarka akai ma wani? Idanunshi ne yakada yayi jawur a maganganunta babu qarya gaxkiya take gaya mishi, nadama ne tawanke xuciyarsa ganin hakan yasata jin dadi koba komai mijinta tana daykan nasiharta duk da batada tabbacin yana tasiri akansa.


Jitayi ya tambayeta kintambayeta a ina yasamota? A 'a bantambayeta ba, to tashi ki kirata.


&&&&&&&&&&&&--
Lami ce a tsaye akan matar Baffan Sadiya tanata surfa mata bala'i tamkar 'yar cikin, wai a dalilin menene xata samata naman miya guda biyu bayan akan idanunta aka aiko da cefanen kuma ta qidaya tasan kowa yanda xai samu, _kujimin qarfin hali adashen manga_ itakuwa tamkar da dutse akeyi, ko dago idanunta batayi ta kalleta ba balle tasa ran xata bata amsa.


Tashi tayima ta gicciye ta gefenta tai wucewarta kwafa lami tayi tacika tayi fammm kamar xata fashe don takaici, Tana tsaye a gurin taji sallamar baffan Sadiya, nanfa ta daidaita kanta ta duqa a gurin tana ixa itacen.


Ah ah ah Lami aiki akeyine? Eh wlh itacen nema yaukam bashida kyau gashinan inata fama da hayaqi, nayi mata magana akan koxa'a canxo itacen ma batace dani komai ba, dagowa tayi taga babu kowa a gurin, batasan shikam ma yajima da Barin gurin ba, tunda yaji xata fara soki burutsun qaryanta da kuma yawan maganganunta....


Tabdi jam gaxkiya wnn mutumin yagama rainani anya baxan biyo mishi ta bayan gida ba, gashi yakasa cewa komai akan maganar da taxo mishi da ita, snn kuma bataga fuskar tunkaranshi don jin amsar ta ba. Lallai kam wlh baxan taba barin wannan Damar ta wuce niba, dani kake xancen. Tayi kwafa tabar gurin.


&&&&&&&&&------

Nana ce tafito ahankali take takowa kamar wacce kwai ya fashewa a ciki, kanta a duqe a qasa, Haj.Maryam ce a gaba itakuma tana binta a baya, a haka har suka isa falon, da sallamarsu gaba daya suka Shiga ciki.


Amsawa yayi ya qurawa Nana idanu Wanda har Maryam ta fahimci hakan, suna hada idanu babu shiri yayi qasa da nashi don yasan ya barar😜 _lols_ gaisheshi tayi batareda ta dago ta kalleshi ba, amsawa yayi cikin nitsuwa domin saida ya tattarota gaba daya don gudun karya kwafsa.


Gurinne yadau shiru na Dan wani lokaci kapin cannn takatse shiru tareda cewa Nana inason kisanar samu tarihin rayuwarki a taqaice, dagowa tayi ta kalleta har idanunta ya fara canxa launi.

A hankali ta fara labarta musu tarihin rayuwarta batareda ta boye musu komai ba, har xuwa lokacin da Ayashe takaita gidan na qarshe, takuma barota xywa kawota gidannasu da akayi.


A qarshe tacemusu cikin kuka, inaji a jikina mahaifiya ta tana Raye, yawan mafarke mafarken da nakeyi da ita, yana tabbatar min tananan, tayaya xan ganta? Kutaimaka min kuyi sanadiyyar haduwata da mahaifiya ta, tafadi hakan cikin kuka tareda kamo qafar Haj.Maryam ta durqusa a gabanta, domin a ranta tanajin sauqi xaixo gareta.


Gabadayansu sun matuqar girgixa dajin labarinta, banda Haj.maryam kan ma data gama jiqa da hawayen tausayin Nana, wnn wace irin rayuwa ce haka?


sun matuqar tausaya mata tare da yin Alawadai hali irinna Lami da Ayashe.

Babban tashin hankalin ma shine rashin sanin inda mahaifiyar tata take, dakuma yanda xa'a fara nemanta, abune mai matuqar wahala duk da komai mai sauqi ne idan aka sako Allah aciki.


Alhaji ne yadago yace Maryam idan kin Amince inason muje garinsu yarinyar nan domin nema mata iyayenta dakuma karba mata 'yancin ta snn a qarshe ina qara Neman alfarmanki inaso........


😍😍🤝Anatare
Mummyn Fadyl CE






🎲🎲TUDUN DAFAWA🎲🎲


Rubutawa....MUMMYN FADYL (Fatyma Muhammad Adamu)

Wattpad @ *fatimamuhammadadamu*


INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION*
*[onward together]*
*{we give the reader's of ours the best out of the bests,, our inks are melodious and dropping a kinda lights to reader's}*
```THE PEN OF LOVE😘 HEAT TORCHING❤ TEAR OF SORROWS😭 CURDLES😊 GIGGLES😁 AND MARRIEGE THINK💑```
*```JUST GIVE US FOLLOW..**


Fitowa ta. 4⃣5⃣.


Yace mata inaqara Neman alfarmarki inason bayan na hadu da iyayenta inason innemi aurenta batareda tunanin komai ba yayi maganarsa.

Ba Haj.Maryam kadai ba hatta Nana saida ta dago ta kalleshi domin firgici mamaki dakuma tsoro ne qarara ya bayyana a idanunsu.

Cikin dakiya Maryam tace mishi bangane abunda kake nufi ba, Aure nake nupi idan hakan yayi miki, yabata amsa yana tsareta da idanunsa.

Cikin wani irin hali tace na Amince ranka ya dade ina fatan Allah ubangiji yasa hakan yaxama alheri, Yakuma sa aurenka yaxame mata *Tudun dafawa* .


Nana kindaiji abunda Alhaji yafada ko? Inafatan baxaki bani kunya ba, kisani bamuda niyyar cutar ki, kidaukeni kamar yayarki, xamu taimaka miki da ixinin Allah, amma baxamuy miki tilas ba saida amincewarki, kin Amince?


Bata dago ta kallesu ba, kanta a qasa cikin sheshsheqar kuka muryanta a sarqe tace duk yanda kuka zartar akaina daidai ne, nidai kuji tsoron Allah karku cutar dani.

Sunji dadin furucinta sunkuma tabbatar mata basuda niyyar cutar da ita, a qarshe suka sallameta ta Tashi tanufi dakinta, tana wucewa ta Shiva dakinta, itama Haj.Maryam tamiqe xata nufi dakinta, cikin azama ya riqo hannunta tareda cemata Yaya xakibarni nikadai kuma?


Bahaka kika saba minba batareda ta kalleshi ba tabashi amsa da inason Shiga dakinne na kwanta, domin a gajiye nake, qarya bai kamace ki ba, badai kishi kikeji ba, yatambayeta.


Juyowa tayi ta fuskanceshi tareda kallon kwayar idonshi tace mishi laifine donnayi kishinka? Shin ban cancanci inji zafin kishi bane? Shekarata nawa ina tare dakai amatsayin mallakinka batareda wata na, rana tsaka kacemin ka bijiro da maganar aure kuma kayi tsammanin baxanji komai ba?


Jawota yayi ya xaunar da ita kusa dashi snn yafara mata magana, Kiyi haquri Maryam amma idan baxaki manta ba, kullum fa kece mecemin inqara aure indai inada buqatan hakan, yanxu kuma wlh baxan boye miki ba, naji inason yarinyar nan tun ganinda nai mata nafarko, nasan matata bata daga cikin jahilai wadanda suke hana maxajensu aure saboda wasu dalilai mararsa asali da tushe.

Gaxkiyar kine dole kiji kishi, nakuma ji dadin nuna kishinki akaina, amma kiyi haquri ki danne xuciyarki kisa a ranki duk macenda xan yi tarayya da ita har gaban Abadan baxata kamo qafarki a cikin xuciyata ba.


Maryam ke haskece a rayuwata halaccinki a rayuwata ba abune daxan mance shi cikin sauqi ba, indai Aljannarki a qarqashin qafata take wlh Maryam wuce ki shige na dage mata yafada tareda nuna mata qafarshi guda daya Wanda ya dage, su dukansu saida sukayi dariya taji dadin furucinsa matuqa, daganan suka xubar da komai sukaci gaba da hirarrakinsu cikin farin ciki.


Itakua Nana tana shiga dakinta ta fada kan gado ta fashe da kuka mai ban tausayi, fadi takeyi nidai bansan rayuwata wace iriyar bahaguwan rayuwa bane, wayyo ni bahaka naso aure na yakasance ba, wayyo Mamana inakike a yau gani acikin gidan mutane masu karamci, suna Neman su 'yantamin rayuwata, gani Cikin jin dadi, dadin da banyi zato ba, amma bansan tayaya xan mori jindadin ba, don kuwa bakya tare dani, tunanina yana gareki, tafashe da kuka...


Xaune suke acukij dakin gadin, suna Dan taba hirarrakin su na yaushe gamo, tambayanshi yayi yace Niko Habu xua yanxu yaranka nawa? Nan danan yanayinsa ya canxa, Wanda haryasa yafahimci akwai Matsala, lpy dai naga daga tambayarka iyalanka naga kashiga wani yanayi?


Hummmm numfasawa yayi snn yace ba tambayar da kaimin bane yasakani cikin wannan halin saidai tambayar taka ta tunomin ko ince ta tonomin liqin dayake cikin xuciyata.


Qasake yayi yana sauraransa, nan shikuma ya labarta mishi abunda yasani na dangane da rayuwar shi Dana iyalansa a baya, iyakan wanda yakeda masaniya akai...

Ai kasa furta komai yayi tsabar tu'ajjibin al'amarin, sai xuru dayayi yana kallon Mal.Habu Wanda yake cikin tashin hankali, kallo daya xakai mishi ka fuskanci hakan.


Yanxu dai matakin farko da xamu dauka shine addu'a acikin abunda na fuskanta na halayyar rayuwarka akwai sakaci da ibada, a Dan kwanakin da kayin nan na fahimci addu'oi basu dameka ba, yanxu mudage da addu'oi kapin wani dab lokaci insha Allahu xamuga sauyi kuma komai xaixo mana da sauqi, Allah ya bayyana manasu, sukuma wadancan matan Allah ya shiryesu, yasa sugane da Amin ya Amsa mishi yakuma ji dadin shawarwarin Dan uwan nasa.



Saida sukai kwana uku suna tattauna yanda xasu tsara tafiyar nasu, sunkuma tsayar da jibi a matsayin ranar tafiyar nasu.

Haj.Maryam ta matuqar yabawa da kawaicin da mijinta ya nuna Akan Nana, domin bai nuna mata yana zumudi ba, duk da bai boyemata irin sonda yakeyiwa Nanan ba, itama Alhmdllh xafinda takeji akan nanan yamatuqar raguwa acikin kashi dari baifi kashi talatin takeji ba da taimakon addu'oi nda takeyiwa kanta.


Bayan sungama shirya wa ne, Haj.Maryam tayiwa Nana magana akan tafito su wuce, fitowarsu yayi daidai da shigan Mal.Habu bandaki don haka cikin sauri Idi yaxo yabude gate din, daudai xasu fita ne Alhaji yasauqar da glass din motar suka gaisa cikin mutunci, nan shima yagaida Alhaji, kapin yagaida Nana tarigashi daga mishi gaisuwa, gaba dayansu saida sukaji dadin abunda tayi, hakan yaqara sa musu qaunarta acikin xuqatansu.


Tafiya sukeyi cikin gudu Haj.Maryam sai fadi takeyi Alhaji mutafi a hankali don Allah saikace masu shirin tashi sama? Nidai banason yawan gudu wlh, dariya yayi yace mata kiyi haquri ranki yadade so nakeyi muje mu kammala abunda yakaimu in time mudawo, banason yin dare a hanya kinsani.


Da taimakon kwatancen da Nana keyi musu har suka isa gidannasu, cemata sukayi ita tafara shiga taiyo musu sallama da mahaifinta, sauqa tayi a hankali tafara tafiya qirjinta na luguden tashin hankalin abunda xata iya taras wa acikin, gida mai dadi ko akasin hakan.


Tayi mamakin yanda aka gyara gidan, don gaba daya ancanxa tsarin gidan ikon Allah tafadi hakan a ranta, da sallama tashiga cikin gidan yaranda ta gani a tsakar gidanne wadanda sukafi su goma qananu dasu, Kansu daya, kamar rana daya aka haifesu ne yabata mamaki, domin bata sansu a unguwarba, snn ita a iya saninta basuda qananun yaranda xasu jawo musu su, amma ta daure tace ina Baba ta tambayesu mai wayon cikinnasu ne yace mata bari inkirashi yamiqe yayi dakin Umma Ayashe.


Itadai tana tsaye kamar andasata tanajiran fitowansu, sai ganin yaron tayi yafito da wani sangamemen mutum Wanda ganinshi ma ba dadi ne dashiba, saida ta runtse idanunta data kalleshi, amma ta daure ta gaisheshi amsawa yayi yana binta da kallo daga sama har qasa.


Bata biyemishi ba ta tambayeshi race don Allah mai gidan nake nema, washe baki yayi snn yace mata 'yan mata ai nine mai gidan aikoki akayi ne? eh tafada mishi cikin rudewa domin takasa fahimtar abunda take ji take kuma gani.

To kice inaxuwa, aiko kamar qiftawar ido tabar cikin gidan, isa jikin motar tayi ta tsaya, dukansu biyu ne sukafito suna tambayarta ya ake ciki? Cikin kuka tace musu basu bane a gidan, kamar Yaya ?? Bata kaiga basu amsaba mutumin ya katsesu da sallamarsa, kallonshi sukayi, miqawa Alhaji hannu yayi sukayi musabiha tukunna snn yace ka aiko akirani gashi banganeka ba.


Eh to a xahirin gaxkiya nima bawai saninka nayiba, domin asalin me gidan naxo nema saikuma aka samu akasin mun hadu da wani bashiba.


Eh to asalin gidandai banawa bane a da, amma yanxu nine mallakinsa domin nasayeshi...........


😍😍🤝🏼 Anatare
Mummyn Fadyl CE





🎲🎲TUDUN DAFAWA🎲🎲


Rubutawa....MUMMYN FADYL (Fatyma Muhammad Adamu)

Wattpad @ *fatimamuhammadadamu*


INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION*
*[onward together]*
*{we give the reader's of ours the best out of the bests,, our inks are melodious and dropping a kinda lights to reader's}*
```THE PEN OF LOVE😘 HEAT TORCHING❤ TEAR OF SORROWS😭 CURDLES😊 GIGGLES😁 AND MARRIEGE THINK💑```
*```JUST GIVE US FOLLOW..**

_Masoyan Mummyn Fadyl adai cigaba dayimin uxiri, rayuwar haka take, ba abunda kake samu, yake zama kullum xaka sameshi ba, inada uxirin dasuke hanani typing dayawa, amma kusani ko banyi muku typing ba, wuni nakeyi cikin tunanin Ku I heart u oll💋_

Fitowa ta. 4⃣6⃣


Eh to asalin gidan dai banawa bane, amma a yanxu nine mallakinsa domin nasayeshi a hannun mai gidan.


Ikon Allah shine abunda suka fadi su biyun banda Nana, to yanxu ina me gidan? Gaxkiya a yanxu baxance ga inda takeba saboda munkwana biyu bama waya da ita, kuma dama ba maxauniya bace, tana kasuwanci a yawancin garuruwa.


Idan mun fahimci maganar ka kanason gayamana cewa me gidan macece? Kwarai da gaxke a hannun mace nasaya sunan ta Ayashe matar Mal.Habu.


Zaro idanu suka sakeyi cikin mamaki, Alhaji yayi qarfin halin cewa don Allah karka gaji damu Kasan inda xamu samu shi Mal.Habun a yanxu?


A zahirin gaxkiya bansani ba, domin........ Nan ya kwashe abunda ya faru a ranar da yakarbi gidan harma yaqara musu da labarin sayar mishi da gidan Lami xatayi.


Jinjina al'amarin sukayi da gaxken gaxke, banda Nana da kuka yakusan fidda ta daga haiyacinta, a qarshen sallama sukai dashi tareda cewa Nana tashiga Mota sutafi, taso tace musu sukaita gidan yayyin mahaifin nata, saidai tana tsoron tarban da xasuy mata, don bata yarda da soyayyar da suka Nuna mata a rasuwar kakannin ta ba, domin tadaukeshi na wucin gadi ne kawai.


Parking yayi a gefen hanya tareda kallon Maryam yace da ita, Hajiya me kike 2nani gameda wnn al'amarin? A Sanina dake kikan nemomin mafita a duk lokacinda tunani

Please Login or Register in order to submit comment