You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

daga inda nake zaune nake k'are musu kallo na ga sun sake yi mini tsayi ko dai don na kwana biyu ban gan su ba ne oho sun dai yi mini kyau k'warai Khalil na cikin shadda riga da wando da aiki a gaban rigar har da hula a kansa. Ita kuma tana cikin abaya baka mai jajayen dutsuna ta yafe mayafinta a wuyanta har da gilas baki a idonta da jar jaka da takalmi.

Na juyar da kaina cikin nutsuwa na amsa sallamar da ta yi suka 'karaso falon ita da yaran gabad'aya shi kuma ya haura sama ba tare da ya ce komai ba.

"Ta zauna kan kujerar da take fuskantata fuskarta a sake kamar ba itace Hauwa mai k'uncin rai ba. Ta zare gilashin idonta tana duba na sosai ta ce.""Amina ina yini mun same ku lafiya."""

Na amsa a tak'aice ina nazartarta.

Sukairaju ya shigo ya tsaya daga bakin kofa akwati biyu ya ajiye madaidaita don basu da girma kayansu ne a ciki daga nan ya juya ya fita da sauri.

"Hankalina ya d'auke wajan amsa gaisuwar da yaran suke jero mini Usai ta zo ta dafa cinyata tana ta kallona sai kuma ta dora kanta a saman cinyata. Na dora hannuna a kanta ina le'ken fuskarta. Hassana cikin narai-narai da ido ta ce.""Mama ki ka ce za ki dawo gobe."""

Ta fadi maganar muryarta tana rawa kamar za ta yi kuka lokacin na tuna da alkawarin bogi da na yi musu a lokacin ma tun ina maiduguri.

"Na ri'ke hannunta amma ban ce mata komai na kira Khalil da hannu Ina fad'in .""Zo mu sake gaisawa."""

"Ya kuwa taho da sauri yana dariya yake fad'in. Mama mun yi kewarki fa sosai kullum muna labarinki shiyasa da muka zo muka ce mu dai nan a wajenki za mu kwana."""

"Na ce."" Ni ma na yi kewar yarana sosai Khalil ina su Mairo baba Tabawa da Sultan."""

"Ya ce."" Duk suna nan lafiya sun ce a gaisheku Sultan ba shi da lafiya yana zazzabin hak'ori Baba ya ce a bar shi a gida kada a zo da shi."""

"Na gyada kaina ina dubanta lokacin da take yin magana cikin yar dariya ."" Aikam yara sun yi kewarki a gida Amina shi kansa ma gidan kewarki yake yi."""

"Murmushi na yi ina duban Minal da wayata a hannunta tana latsawa ko kusa da uwar ba ta je ba gefe guda kuma ina nazarin abinda yake so ya faru domin ga dukkanin alamu ba yaran ne kadai suka zo mini kwana ba har da ita tunda ga akwatin kayansu nan."""

"Na danne tare da furta."" Kun ci abiñci a gidan Hajja ko kuwa na kawo muku."""

littafin nan na kudi ne kada ki karanta ba tare da kin biya ni hakkina ba

"Ita ta ba ni amsa duk da ba ita na tambaya ba na ji tana cewa."" A alhmdullhi ai sai da muka ci abinci muka fito mun"

"gode sosai."""

Na yi shiru ban tanka mata ba ina ta sauraran labarin Mairo a bakin yaran da sa'kon gaisuwar da suka ce a gaya mini. Wajan goma daidai na tashi na hau saman domin tunda ya hau bai sauko ba ga yara suna so su kwanta. Yadda tsarin gidan yake dama can babban falo ne da dakuna manya biyu a cikinsa toilet da kicin wanda yake d'auke da store wadatattu.

Saman kuwa dama can d'akuna biyu ne amma daya ne a gyare wanda yake mu'amula a cikinsa tun farkon tarewarta a gidan zaman mace daya ne babu takurawa yanzu kuma Khalil ya zama d'an saurayi ya d'an fara girma babu buk'atar a had'a shi da mata a d'aki daya tunda tun can abujan aka raba musu d'aki.

"Yana zaune da jallabiya a jikinsa ya yi wanka yana waya shigowata bata hana shi cigaba da wayarsa ba amma kafatanin hankalinsa yana kaina har na zauna daga dan nesa da shi waya yake yi da Alhaji Sulaiman yana yi masa bayanin yadda al'amarin ya juya har aka d'aura auran da waninsa ya yi masa fatan alheri a yayin da yake ta amsawa da Amin Amin can kuma sai ya yi shiru yana sauraransa na ji yana fad'in."" Anya kuwa Alhaji ba dai yanzu ba tukkuna wad'annan ma fama nake da su amma za mu cigaba da neman zabin Allah."""

Daga haka suka yi sallama ya juyo yana kallona 'kuri! Na sake tamke fuskata tare da tariyo maganganun da ya gaya

"mini dazu amma bari mu ajiye wannan mas'alar a gefe kafin nan ina so na ji dalilin da ya sa ya kawo mini matarsa cikin gidana bayan da bakinsa na ji yana gaya mata babu waje a ina zai sauke ta. Ba ni buk'atar Hauwa gabad'aya a rayuwata bana tsammanin zan iya sake sakin jikina da ita domin bata daga cikin mutanan da Ubangiji ya ce idan sun tuba ku yafe musu Hauwa bana jin za ta yi taubatun nusu'a akan zamantakewa ta tsakani da Allah."""

"Ya dube ni yana fad'in."" Hajja ta ce ta zo cikinmu gabad'aya tunda yaran sun dage anan wajanki za su kwana can"

"kuma ita kadai za ta kasance, amma ni ma na fi buk'atar su zauna a can gidan Hajja saboda ba ni son fitina fa na gaji idan ba so kuke na mutu ba."""

"Na ce."" Ai ita kanta Hajjan ta san gidan ya yi mana kad'an ni wallahi tallahi na gaji da wannan rashin adalci da son zuciya ba ni son had'a numfashina da matar nan domin zahirin k'iyayya ta nuna mini na bar mata can gidan na zo nan na zauna domin zuciyata ta samu nutsuwa ta sake biyo ni ko sai ta yi wa rayuwata illah tukkuna za a gane abinda nake nufi."""

"Ya 'bata ransa ainun yana duba tsabar idona ya ce."" Rashin kunyar ta tashi daga kaina Amina ta yi tsalle ta tafi kan mahaifiyata kenan ko, gidan ki ko nawa da za ki yi mini iko da abinda nake da iko da shi, ki gaya mini gidanki ne ko nawa na ce?"""

Ya fad'a cikin 'karaji har yana dukan hannun kujerar da yake zaune.

"Duk da na tsorata daga ganin yadda ya burkice na dake sosai ban sarayar da mutuncina ba na ce."" Gidanka ne ai dama ban ce gidana ba ne amma dai ni ce yanzu a cikinsa kuma na ce ba ni buk'atar zama da wata a cikinsa. Idan lallai sai ka zauna dani a irin hukuncin da na yankewa kaina na rayu ni kadai da yarana a waje daya babu wata bagidajiya da za ta d'aga mini hankali ko ta nemi halakar da rayuwata. Kuma kada ka sake ka yi mini k'azafi akan maganar da na fad'a domin ni ban ga ta inda na kausasa harshe akan mahaifiyarka ba."""

"Ya sake hasalowa yana fad'in."" A ciki nake dake domin kin jima kina yi mini rashin kunya kala-kala saboda kin samu dama akaina ko kin lura ina sonki da yawa za ki samu damar taka ni yadda ranki yake so kin zo geji muddin ki ka ce za ki sanyo mahaifiyata cikin wannan rashin mutuncin naki wallahi ranki idan ya yi dubu sai ya 'baci."""

"Na sake aro jarumuta da jajurcewa domin dai duk wannan hargitsin da yake yi bai karya mini lagona ba ko na tsorata na furta ."" Kada fa ka yi mini sharri akan abinda ban yi ba babu cin mutunci balle rashin kunyar da kake magana a tsakanina da Hajja wannan alkawari ne na daukarwa kaina."""

"Ya ce."" Idan ba rashin kunya da rashin arziki ba mai yasa za ta bata da umarni ki ce ba daidai ba ne har kina fad'in ita kanta wannan ai wulakanci ne da nuna mutum bai isa ba."""

"Na girgiza kaina cikin ko'karin nuna masa ba haka nake nufi ba na ce."" Idan wannan maganar dana furta akan Hajja ta hasala maka zuciya Allah Ya baka ha'kuri amma zan fita yanzu tunda da sauran dare a gidanmu zan kwana nan gidan Hauwa ne da yaranta kamar yadda wancen ma ya zama nata."

Na yun'kura na tashi a hankali yaran dake cikina suna naushin marata duk da ciwon da nake ji na yi azamar kama hanyar fita.

Ya cimma ni dalili da kyar nake iya cire 'kafa.

"Ya tari gabana da b'acin rai a fuskarsa ya furta."" Ba za ki bari mu huta ba ko Amina, ba ki duba nauyin da ki ka yi, kin ki ki bari mu fahimci juna har mu raini yaran dake cikinki kin dusashe mini farinciki da annashuwata kina nema ki dasa mini b'akinciki me na yi miki ne?"""

"Na daga kaina na dube shi a hankali na ce."" Ka bar ni na huta ni ma?"""

Ya yi shiru bai ce komai ba da akwai alamar sasaauci a fuskarsa. Ya rike hannuna daya na fizge tare da ratse shi zan wuce ya san janyo ni da sauri tare da sanya ni a jikinsa. Na sake cirewa rik'on karfi ya yi wa hannuna. Yana jana ina turjewa so yake mu je mu zauna a gefan gado.

"Na ce."" Ai babu buk'atar wani zama na samun maslaha da daidaito a tsakaninmu tunda har yanzu baka fi karfin gidanka ba. Zaman sulhu da samun mafita ba za a yi shi da ni ba a yanzu zaman 'yanci zan yi da kare kaina."""

"Ya ce."" Na gaya miki tuntuni Hauwa ta gyara ta daina duk wasu abubuwa na rashin kyautawa kada ki manta da irin yadda na fifitaki a kanta na nuna miki kulawa da k'auna a kanta ki ka fitar da hannu ki ka tsinka mata mari a gabana. Na hana ta d'auka mataki ta kuma hanu. Wannan bai isheki ba Amina."""

"Na ce."" Ai baka burge ni ba daka sani ka bari ta rama marinta ko kai ka rama mata tunda ka ji mata haushi. Ka daure mata gindi tunda baka musanta abinda ta fad'a ba a kaina kawai ka mayar da abin wasa. Mataki ma ban gama d'auka a kanta ba wallahi muddin ba ta fita daga rayuwata ba."""

"Ya rungumo kafada jikinsa yana dan rawa har yana gyara mini sar'kar wuyana ya ce."" Ni ban d'auki maganganunta da muhimmanci ba saboda nasan wacece ke, nasan ta fadi haka ne domin ta 'bata miki rai da kishi irin naku na mata"

me yasa maganarta za ta dame ni tunda na fi kowa sanin da baiwar da Allah ya yi mini na rabauta dake giwar mata

shige mu zauna mu yi magana wadda za ta kawo mana sasanci

*GARKUWAR MATA.*

*BINTA UMAR ABBALE*

"[6/4, 3:03 PM] Hauwa Galadima: *PAID BOOK VIP 1K ON TALGRAM WHAT'S APP GRUOP KUMA #700. VIA"

0542382124 BINTA UMAR GTBANK*

*V-VIP AREWAPEN*

*07084653262*

*154*

Ganin yana neman wuce makad'i da rawa ya sanya na tankwa'be hannunsa ya sake mayarwa tare da tarairayoni jikinsa sosai na yi 'kokari wajan 'kin barin abinda yake yi mini ya yi tasiri a tare da ni muka zauna gefan gado a tare yana ta sauke wata irin ajiyar zuciya wadda na kasa tantance ko ta mecece. Raina a b'ace na zura masa ido domin sauraran abinda zai fad'a abinda na sake kud'irewa a raina shine ko sama da 'kasa za ta had'e ba zan zauna da Hauwa ba tunda ba tare a ka hallice mu ba. A wannan karon na shirya sosai koda Hajja za ta sanya bakinta ba ni tsammanin za ta sake samun wannan alfarmar.

"Sai da ya daidaita kansa sosai ya furta."" Za mu yi kwana biyu da Hauwa anan zuwa jibi zamu tafi tare da ita da yaran gabad'aya ba dai akan maganar raba gida kike magana."" Ya fad'a yana kallona."

"Na gyad'a kaina ba tare da na ce komai ba. Ya sake sauke ajiyar zuciya yana ce wa."" Za a yi yadda ki ke so amma ya zama dole kema ki bi umarnina tunda kin san bai zai yiwu ki zauna anan ba mu muna can"

"kuma duk wasu d'abiu da ki ke yi a yanzu ki ajiye a gefe ba zai yuwu ki dinga juya ni ba Amina kin san dai ba ki isa ki kafa mini doka na bi ba ko?"""

Ta'be bakina na yi tare da juyar da kaina gefe wai ban isa na kafa doka ya bi ba. Ita din yake bi ai a yanzu na tu'ke tunda bai san alheri ba. Dole ne aka ce na zauna da wata Allah Ya gama hore masa ta ko'ina idan ya'ki raba ma mazauni bai shirya kashe rikici ba.

"Ya juyo da fuskata yana fad'in."" Ki kalle ni mu yi magana domin fahimtar juna nake so mu yi ni dake saboda na gaji da wannan halin da ki ke yi mini ina ce akan an bani auran wannan yarinyar ne Hajara ki ka canza gabad'aya ni fa ba yaro ba ne giwa na baki shekaru sama da goma sha biyar duk yadda ki ka kai ga gogewa na fi ki kuma bai wai ina tsoronki ba ne."""

"Na dube shi sosai ina cewa."" Ni dama na ce ka ji tsorona ne? Wallahi ka ji tsoron Allah a cikin dukkanin lamarinka ka dinga gaskiya yanzu ba ka ji kunyar duban idona ka dinga fad'a mini irin haka ba me yasa ka ke da mance alheri ."""

"Ya ce."" Ni kin d'auke ni mak'aryaci kenan."""

"Can k'asa na ce."" Iyi."""

"Ya sake sanya hannunsa ya juyo da fuskata yana ta'ba le'bena kafin ya furta."" Ni ki ke yi wa Allah Ya isa Amina."""

"Na cire hannunsa ganin kamar yana so ya shagaltar da ni, na ce."" Don Allah ni ka rabu da ni babu fa wani kalami da za ka yi mini na ji dad'i tunda ka rasa Hajara sai ka nemi wata ba yanzu na ji kana waya da abokinka ba ya baka kanwar amaryarsa sai ku yi anko ina ruwana."""

"Ya girgiza kansa yana cewa."" Ko zan yi aure anan gaba sai da amincewarki ke za ki duba mini wadda ta dace."""

"Na kalle shi a sakarce wai shi dole sai ya yaudareni da kalaman bakinsa. Na ce."" Ya ake ciki ne za ka d'auki Hauwa ka mayar da ita can gidan Hajja ne domin fa hakan shine samun nutsuwarmu da ni da kai da ita gabad'aya."""

"Ya yi d'an shiru kafin ya matso ni sosai yana fad'in."" Dambatta fa aka ce Amina da tafiya sosai ki bar ta ta kwana na ce miki."""

"Ya fad'a yana d'ora fuskarsa tsakanin wuyana. Gabad'aya ya rikice kuma na gane abinda yake so. Na cire jikina ina fad'in."" Shikkenan ta kwana daya zan mata wannan alfarmar amma wallahi daga wannan kwanan ba za ta sake yi mini wani ba."""

"Can k'asa ya ce."" Na ji abinda ki ka ce."""

Ya sanya hannuwansa ya kewaye 'kuguna jikinsa na rawa.

"Tsaki na ja wanda ban san lokacin da ya fito ba. Ya dago yana kallona idonsa ya canza gabad'aya ya ce."" Kin san na tsani wannan dabi'ar ko. Kin ce a bi ra'ayinki an bi me yasa kike wulakantani ne Amina."""

Jikina ya d'an yi sanyi jin muryarsa har tana d'an rawa bai ba ni tausayi ba ko kad'an saboda nasan akan abinda ya sanya shi rawar murya din duk yanayi ne domin ya yaudare ni ya more ni kuma Hauwa ta ci ribar abinda ta shirya domin dai ban yarda da cewa Hajja ce ta turo ta mu kwana tare ba.

"Na ce."" Game da kudin sadakin Hajara nawa ka ba su?"""

Shiru ya yi mini yana girgiza kansa tabbacin ya kai 'kololuwa wajan Jin haushin tsakin da na yi masa wanda ni ma ban

"san lokacin da ya fita ba tsabar haushinsa da nake ji ne. Na sake maimaitawa ya ce."" Ban sani ba."""

"Na ce ."" Ya asalin baka sani ba, ka fad'a don Allah a baka hak'kinka ai ba lefi ba ne."""

"Ya ce."" Ba zan fad'a ba Amina ke kina jin kin yi k'arfin da za ki nuna mini wani abu ne.''"

"Na ce."" A a wace ni idan da irinku a wuri ban isa ba kawai dai ina so mu biya ka hakkinka ne saboda kada nan gaba a yi mini gori."""

"Ya yi shiru bai tanka mini ba can kuma ya ce."" Yanzu za ki ba ni ha'kkina ko kuwa?"" Na ce."" Wane hakki?"" don har ga Allah ban zanci hakkin kwanciya yake nufi ba ."""

"Ya d'ora duka hannuwansa biyu saman kirjina yana fad'in."" Wannan dai mallakina ne ke kan ki ba ki da karfin ikon da nake da shi a kansa. Idan na d'ora hannu a kai ki tankwa'be kina neman rahamar Allah kuwa?"""

Ya fad'a yana dam'kar d'aya da k'arfi cikin mugunta gasu tubarkallq sun sake kumburi dalilin abinda nake d'auke dashi sun cika sosai.

"Na sake tankwa'be hannun ina fad'in."" Allah Ya hallice ni da abina a jiki ka ce ka fi ni iko da shi abincin yarana ne masu zuwa."""

"Ya kuwa gigice yana fad'in."" Abincin mu dai, wallahi ba ki isa ba, abincinmu ne da ni da su."""

"Na juya da kaina gefe ya matso ni sosai yana yi mini magana. Na girgiza kaina tare da cewa."" Ba zai yiwu ba sai Hauwa ta tafi ka yi hakuri ni tunda cikin nan ma ya tsufa na daina jin wani abu"

"Ya ce."" Ni kuwa a cikinta nake koyaushe kin matse ni da yawa Amina ba kya gudun hakkina ya kama ki uhum! mu d'an yi soyayya kad'an kafin Hauwa ta shigo sai mu kwana tare kada ta ce ba a yi mata daidai ba."""

"Na ce."" To bari kawai idan ta shigo sai ku yi soyayyar gabad'aya."" Ya sake rikicewa yana cewa."" Ya ki ka tsara yanda zai kasance."""

Na rasa da wane mizani zan auna maganarsa. Ya na tsara yanda zai kasance me yake nufi. Na gane kawai a rikice yake maganarma ya fad'e ta ne cikin rashin hayyaci.

Ina sane na 'kyale shi ya dinga abinda yake so ba don komai ba sai don na nuna mata cewa kowace mace da irin tata kissar. Gidana kuma ta zo sai abinda ta gani.

Wajan sha biyu da wani abu muka sauko kasan ni da shi bayan ya samu gamsuwa da abinda ya buk'ata. Yaran sun yi bacci duka a saman kujera tana zaune zuru da tibi a kunne duk ta muzanta ganin sakkowarmu ta yi kasa da kanta fuskata a had'e kamar ma kuka ta yi.

"Na wuce d'akina ban tsaya a falon ba na ji yana cawa da ita."" Tashi yaran su je su kwanta. Amina bude musu daya d'akin, shi Khalil ya zo mu kwana tare a d'akina."""

"Dakinsu Baba Tabawa da Yusra kenan anan suke kwana na bud'e kamar yadda ya buk'ata. Ita da shi suka fara tashin yaran. Na yi shigewata d'aki a raina ina fad'in."" Ki zauna da ni a gida daya ki zama 'yar aikina Hauwa, zan kuma ga abinda gobe za ta haifar ni daku ne gabad'aya."

"Na rufe kofa tare da cire kayan jiki na sanya na bacci na yi kwanciyata ban sake sanin wainar da suka toya ba ba. Da asuba gari ya d'an fara haske ina saman dadduma ya shigo ya jira na kammala muka shafa addu'a a tare. Na gaishe shi babu sakewa na ce."" Zan je gidanmu idan an jima zan kuma tafi da yara."""

"Ya yi d'an jim kafin ya ce."" Babu damuwa amma ya za a yi da abin kari kada su tashi a bacci ko."""

"Na ce."" Za ka iya bayarwa a sayo abinda za su ci ba ni jin zan shiga kicin gaskiya wanka zan yi na shirya."""

"Ya ce."" Wace banzar magana ce wannan Amina ni zan sayi abinci bayan ina da shi a gidana, ban yi wannan lalacewar ba."""

"A takaice na ce."" To sai ka shiga kicin din ka yi da kanka kada dai ta shigar mini kicin."""

"Ya dinga kallona cike da takaici ya ce."" Jiya ba na gaya miki cewa zan raba muku gidan ba me yasa kike da neman fitina ne Amina. Ya kamata duk abinda ki ke ji a ranki ki ajiye a gefe mu fahimci juna gabad'aya mu gyara kuskuranmu Hauwa bakuwa ce anan gidan."""

"Na ce."" Bakuwarka dai ai ni ban gayyace ta ba."""

"Ya sake had'e rai yana fad'in."" Kina yin abubuwan da suke nema su wuce gona da iri fa. Ko babu"

Na kudi ne kada ki karanta ba tare da kin biya ni hakkina ba.

dangantaka ta aure a tsakanina da yarinyar akwai dangantaka ta jini sannan uwar yarana ce kiyayyar ki a kanta ta

"tsananta."""

"""Humm kawai na ce tare da tashi na bar shi zaune bandaki na shiga. Koda na fito baya d'akin na yi tsaki cikin raina na fara shirya jikina zuciyata cike da abubuwa ma su yawa."

Wajan takwas na fito falon yaran sun shirya ko ita ta yi musu wanka oho suna zaune a falo gabad'aya har da Baban

nasu ita tana kicin domin fitowata na ji kamshin k'wai na tashi raina ya baci sosai. amma sai na daure na cigaba da amsa gaisuwar da suke jero mini. Shi kuma ya zura mini ido da alamar na gaji da wannan abubuwan da suke faruwa. Kai tsaye kicin din na nufa na same ta tana soya dankali da k'wai ta d'ora ruwan tea yana ta k'amshi citta da kaninfari.

"Na cika da mamakin karfin halinta. Kai tsaye gas din na kashe ta yi sakato tana kallona. Na furta."" Ba ki da hurumin yi mini yadda ki ke so a gidana Hauwa ko ni na gayyato ki ne, me ya sa za ki shigo mini kicin har ki saki jiki kina soye- soye."""

"Ta d'an yi murmushi tana fad'in."" Amina manya ai kya bari mu gaisa ko?"""

"Na ce."" Dube ni nan Hauwa ba ni buk'atar gaisuwar na ce miki tambayarki nake dalilin da ya sanya ki shigo mini kicin."""

"Ta yi 'yar dariya cikin raini ta ce. "" To Hajiya masu gida ki goya ki kai gidanku."" Ta ajiye cokalin hannunta ta kama hanyar fita zalo-zalo na ce."" Sakarai kawai."" Ta juyo a fusace tana cewa."" Amina ai ba a sakarai d'aya sai dai sakarkaru biyu."" Na ce."" Hakane da ke da ta Bauchi ko?"""

Ta zura mini ido da matsanancin mamaki tasan dai inna Uwani nake nufi

"Sai ta rushe da kuka mai karfi."" Amina ni ke zagi, inna Uwani ce sakarai mahaifiyata."" Ta fadi maganar a daidai lokacin da ya shigo kicin din ta dinga wani irin kuka hawaye na kasa tsere a kumatunta."

"Yana tambayarta ta yi shiru ta kasa magana ta jingina jikin wardrobe. Can ya juyo kaina ganin yadda fuskata take ya sanya shi fad'in."" Me ya faru ke ba kya jin magana da rarrashi ko?"""

"Na ce."" Ni na ce Hauwa ta zo gidana?"" Na katse shi ta hanyar yi masa wannan tambayar. Ya ce."" Gidanki ne ko nawa?"""

"""Gidanka ne amma kaima na fi ka iko dashi wallahi duk zan iya da ku."""

Ya gyad'a kansa kamar zai rushe da ihu ya ja hannunta suka fita bata sake tanka mini ba tunda ya shigo sai ta yi shiru kawai tana kuka. Wai na goya gidan na kai shi gidanmu. Magana ta gaya mini a fakaice ashe babu dadi. Ita da uwarta duka sakarkaru ne na fad'in su yi yadda za su yi da ni.

Na same su gabad'aya har yaran sun tsuru-tsuru na wuce daki ban sake kallonsu ba.

Muna waya da Usaini ya shigo da wani irin b'acin rai a tare da shi ya cire wayar daga kunnena ya sanya a aljihunsa. Na

Please Login or Register in order to submit comment