You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

an ce goyaki ne kawai baya yi kuma ba ke"

"ki ke yi masa ladabi shine yake yi miki, har cewa aka yi kin mallaka shi da mahaifiyarsa sai abinda ki ka ce musu a gidan."""

Tana dariya ta kai k'arshen maganarta da zolaya.

"""Sahura duk wanda ya gaya miki haka ya zalince ni wallahi domin kuwa ni kadai nasan da wanda nake zaune, ba zan iya 'boye miki abinda yake faruwa ba sis, amma wallahi kallon kitse kuke yi rogo, da yawa mutane za su dinga ganin ai kakata ta yanke sa'ka saboda mafiakasari mutane sun amince da cewa kudi sune jin dad'i alhalin ba haka ba ne, na yarda da maganar nan da hausa ke fadi cewa ka auri mai zuciya ba mai dukiya ba, mutumin nan yana da tarin matsaloli wad'anda ya bi ya ninke abinsa ba wanda zai gansu sai wanda zama ya had'a mussaman ni dai da nake a matsayin matarsa. Akwai ci dasha kula da lafiya da biyan buk'ata ta aure duk akwai wannan to amma kin san wad'annan abubuwan da na zayyano miki idan babu kwanciyar hankali ba za su yi tasiri ba. Idan zan zaga kaf garin nan Ina sukar mutumin nan babu wanda zai yarda da maganata domin ya riga ya siye jama'a da alherinsa."""

"""Sis ki gaya mini abinda yake faruwa don wallahi ni gabad'aya kin kashe mini jiki, don Allah ki yi hakuri ki zauna a d'akinki."""

"Murmushi na yi Ina dubanta, itama magiya take yi mini na ha'kura na zauna ko bata fad'a ba na san dalilinta bai wuce irin na Anti Yagana ba."

"Na ce."" Sahura zaman bashi ne a wahala ba, abokin zaman shine matsala, ni idan ta ni ne wallahi ba ni da matsala dashi amma fa zan gaya miki abinda ba ki sani ba ya sake ni akan wani abu da yake hasashe kuma bashi da hujja akai."""

"Cikin kad'uwa da tashin hankali ta furta."" Saki kamar yaya k'awata, yanzu kina so ki gaya mini cewa babu aure a tsakaninku?"""

"""Ya sake ni shekaran jiya saboda yana zargina. Duk na kwashe abubuwan da suke faruwa na gaya mata. Jikinta ya yi bala'in mutuwa har da 'yar k'walla a kwarmin idonta ta ce."" Wato ita dai 'ya mace rayuwarta ta kan kasance cikin 'kalubale akoyaushe duk abinda ta yi ba zata tsira ba, sis na ga dai harkar social media nan da ki ka yi neman na kanki ki ka yi baki taba aikata wani abin assha ba wanda zai zama tambari na zubewar mutuncinki. Kuma mutumin nan ba yaro ba ne a ganina bai kamata ace yana yi miki munanan zargi irin wannan ba, wallahi a wannan zamanin sis da wasu 'yan matan har gwara zawarawa ban ce duka 'yan matan lalatattu ba ne, amma wasu mazan na yanzu sun gane gwara su auri bazawarar sun san ita suka aura akan su kashe kudi wurin auran budurwa daga baya su gane ba kamila ba ce, kuma mata nawa manzon Allah s.a.w ya aura a matsayin bazawara, ko wannan ya kamata a ce wasu mazan na d'agawa mata kafa. Amma abinda na fi fahimta ga mutumin nan yana da zafin kishi wanda dama haka aka ce na maza ya fi na mata, kuma idan ya yun'kuro masa yakan iya kasa sarrafa kansa, amma ai kishi ba hauka ba ne, zai lalata auransa ne kawai bai sani ba, a wannan ga'bar gaskiya ba na tare dashi."""

"Na ce."" To kin fahimce ni ashe, Sahura a shirye nake akan wannan dalilin wallahi na tsinke auran nan, ban yi abu tunda kuruciya ba akan me yanzu zan yi, har wanda yake aurena ya gaza fahimtata, koyaushe addu'a nake yi Allah ya"

"kare mu daga rudin zamani. Shekaran jiya ya yi sakin jiya da safe ya ce ya mayar da ni. Ai aure ba abin wasa ba ne,"

"ko 'yar tsana ba za a yi mata wannan wulakancin ba, Sahura dole ne na nuna masa nasan abinda nake yi."""

""" 'Kawata ina bayanki, amma don Allah kada ki zafafa da yawa nasan halinki, ki dubi shekaru da kuma matsayinsa da wad'anda suke k'asansa, dan fa kuskure ya yi kuskure gaskiya."""

"Na ce."" Shi me yasa bai duba shekaru da matsayinsa ba, ai gudun zubewar mutunci yake yi a gari to idan bai yi wasa ba sabuwar jarida zata fita a kansa."""

"""A a 'kawata kada ki yi abinda duniya zata san me kuke ciki, ki sakaya auranku don Allah, shi dai sannu a hankali ki hukuntashi amma kada ki fitar da sirrinku, ai dan Adam tara yake bai cika goma ba, bai kyauta miki ba amma ki dubi abubuwan alherinsa a gareki ki rangwanta masa."

"'Kwafa na yi tare da cewa."" Mu bar maganar nan Sahura ta ishe ni wallahi, yanzu ashe yawo ake yi da ni a gari ana cewa juya shi nake yi, mutane basa tsoron Allah."""

"'Yar dariya ta yi tana fad'in."" Wallahi cikin unguwarmu na ji maganar tana yawo, kuma daga gidanku ta fito Ummansu Hadiza ce take gayawa ma'kota ai kin shiga kin fita akansa da Mamansa sai yadda ki ka yi dasu, Hadiza da ta zauna a gidan ta ga irin zaman da ku ke yi."

"""Ita Ummansu Hadiza tana d'auka yadda take bin malamai kowa ma haka yake, kin san mai yin abu sai ya dinga"

"zaton wani ma yana yi, ai na gaya miki Sahura wallahi ban ta'ba tsugunawa agaban wani da zummar ya taimaka mini akan mutumin nan ba, kin fi kowa sanin halina. Anti Yagana ce ma da taga abin ya rincabe ta fara biye biye na ce mata ba na so, duk abinda ya tunkaro bawa kawai ya nemi sau'ki a wajan Allah."""

"""Wannan shine gaskiya 'kawata domin babu wani abu da wani mahaluki zai yi maka face ya kara jefaka a masifa, kuma na ji labarin ma an ce Hadizan bata kasar wai ta tafi dubai saro kaya."" Ta kare maganar tana dariya."

"Na ce."" Ni ma haka na ji Sahura na ce me Hadiza take so ta zama ne, ai mutumin nawa shi ta kira ya bata jarin kudi zaman da ta yi a wajena ta samu kofa a gabana ya ce mata duk lokacin da wata buk'ata ta tashi ta nemeshi. Wallahi Sahura ashe had'a baki suka yi da Ummansu suka shirya karya ciwo ga Fati wai tana da cancer za a yi mata aiki, duk suka daga mana hankali ni dashi a lokacin ya ba su miliyan shida ya kuma bata kofar tambayarsa duk abinda suke so shi ya d'auka da gaske ne sai da anti Yagana ta bincika ta tabbatar da cewa k'arya suke yi. Kuma maganar fa da nake yi miki lokacin da ya tura mata kudin zuwa Dubai din rikici muke yi don har ya yi sakin ma, bai gaya mini ba itama Hadizan ba ta gaya mini ba sai da Babanmu ya kira anti Yagana yana gaya mata."

"Girgiza kanta ta yi tare da cewa."" Amina Hadiza 'yar uwarki ce, duk inda aka je aka dawo babu wanda ya isa ya raba tsakaninku tunda uba daya ba wasa ba ne, amma wallahi ki yi hankali da ita dan ta gurgud'e miki auren nan ba wani abu ba ne a wurinta, nasan ta fi ni kusanci dake amma kin san wani abu da ban gaya miki ba tun lokacin da abin nan ya faru da aka dinga yawo da sunanki a social media cewa kin ce ke ma a baki hakkin yaranki da Yallabai ya take, na dinga bibiyar lamarin wallahi har acct din da ya fitar da magana na dinga bibiya na kwafo lambar da aka bude acct din na ajiye, wallahi Koda na tsananta bincike akai sai na gano lambar Hadiza ce amma ba kowa ya san tana da ita ba, kuma yanzu ki shiga fece book ki yi sarcin din acct din za ki ga babu shi ta goge, dama ta bud'e ne domin ta 'bata ki."""

Kada ki karanta mini littafi ba tare da kin biya ni hakkina ba. Littafin gudun aure na kudi ne.

"Da mamaki mai yawa a tare da ni na ce."" Anya kuwa Sahura Hadiza fa bata da wani boko akanta ina ganin"

"azancinta ba zai iya b'ata damar bude fece book ba har ta yi wannan rubutun."""

"""Itace fa na gaya miki, idan ba ta iya ba zata iya biyan kudi a bude mata ta yi amfani dashi a lokacin wanda ya bude mata ya goge shi gabad'aya."""

"Na ce."" To idan na fahimta ta yi amfani da boyayyiyar lambata ne don kada a gane ita ce, tunda ai ina da lambata ko a fece book din ma ina ganin gilmarwarta."""

"""Shine ai abinda na gaya miki da wata wayar ta yi amfani amma da an tabbatar mini da cewa layinta ne kuma tana amfani dashi sa'i da lokaci."""

"Dariya na yi na ce."" Lallai Hadiza abin har ya kai haka, to Allah Ya kyauta ke kuma Sahura sannuki da k'okari, na rantse miki da Allah ban ta'ba kawowa zuciyata ita ce ba."""

"Ta ce."" Ke dai Allah Ya kyauta a wannan zamanin duk mutumin da Allah Ya rufawa asiri ai yana ganin hassada da bita da kulli na mutane."""

"Wayata na d'auka na duba lokaci sha biyu saura na ce."" Sahura kinga sha biyu har ta kusa muna luguden lebe."" Na kwalawa Salima kira dake can tana aiki, ta shigo na ce."" Kawo mana shayin nasan kin gama dashi."""

"Ta ce."" E Mama abincin ma na kusa."""

"Na ce."" Sannunki diyar albarka ranar bikinki ban san wane shagali zamu sha ba."""

"Uwar ta fashe da dariya tana kallonta ta ce."" 'Kugu za ki daure da gyalenki ki shiga filin rawa kawai Hajiya."" Ina dariya na ce."" Sai kin fad'a ma, ai rawa zan yi hadda juyi."""

Gabad'aya muka fashe da dariya. Yarinyar ta yi saurin fita tana sinne kai.

"Ta dube ni tana cewa."" Kin san fa wani yaro dan gidan yayar babanta yana nan yana naci a kanta wai ya kama don Allah kada a bawa kowa shine fa uban ya zo yana gaya mini na ce to guda nawa Yusuran take da har za a fara wannan maganar shekara sha hud'u fa kawai don an ganta da tsayi shi yasa ake bata girma."""

"Na ce.'' Ai girman 'ya mace ba wahala Sahura Kuma ta isa fa, ai tana da san girma, amma dai da Idiris zai d'auki shawarata da na ce masa kada ya yi mata auran nan na gaggawa ya bari ta samu koda diploma ce."""

"Ta ce."" Ya bari kuwa, ai shi idan magana ta 'yan uwansa ce baya wasa da ita, ni ma nafiso ta dan yi karatu ko yaya ne zai taimaketa anan gaba."""

"Na ce."" Gaskiya hakan zai fi dacewa."" Wayata na d'auka na kira Hamusu yana d'agawa na ce."" Kana asibitin ne "

*GARKUWAR MATA.*

*BINTA UMAR ABBALE*

"[6/3, 8:38 PM] matar mijinta: *Wannan littafin na kudi ne vip 1k akan telegram. Normal What'sapp group kuma #700 hanyar da za a biya kudin ita ce wannan...0542382124...Binta Umar gtbank ko kuma 7084653262. Binta Umar"

Opey bank. 'Yan nijar dala dari katin airtel za ku tura mini bayan kun kankare hoton. A tura da sheda ta wannan lambobin iya What'sapp kawai.*

*07084653262*

*08089965176*

*V-VIP AREWA PEN *

"[12/29/2025, 10:50 AM] Aunty B: TEEMAH DATA SERVICES MTN 1GB @550"

2GB @950

3GB @1450

4GB @1550

5GB @1700

CHECK CODE *323*4# VALIDITY 30DAYS CHAT@08112392177 CALL @08037026306

8037026306 fatima musa ibrahim opay

https://chat.whatsapp.com/K944WIHnBaKHDrZS6snUky

*TALLAH!*

"*Albishirinku mata ´an ™walisa matan da suka amsa sunansu mata, waWanda suka san sirri da fa'idar gyaran jiki domin ta da komaWar sha'awarsu. To ku matso kusa kuji, wai kuna da labarin shahararren kamfaninnan na ™awa da ™awa Waya tamkar da dubu, sha ™undum, mai suna?*"

*DUNIYAR LAFIYA ISLAMIC NATURAL PRODUCT & WOMENS CONSULTATION*

*Daga aunty Fatima Buhari rijiyar lemo 7ano state*

*Cibiyace da tai fice wajen gyaran ma'aurata*

"*Wannan kamfanin basu fito ba saida suka shirya tsab domin taimakon mata ta hanyar samar musu da magunguna ingantattu nagartattu wanda aka haWa da natural kaya cikin tsabta da inganci, komai a kwali yake ´ar uwa cikin tsabta da nutsuwa aka shirya muku*"

"*ina masu son soma kasuwanci ku matso Anty Fatima tana bada kaya a sari akan farashin da zaki gode mata, tana raba kayanta ga manyan shagunan saida magunguna dake cikin kasuwar kurmi dake kano, tana tura kayanta izuwa gari_gari ™asa_™asa. Kayan sari kona miliyon nawa kike da bu™ata zasu iso hannunki a cikin kwana biyu da izinin Allah*"

"*Ni Badiat Ibrahim Mrs Bukhari ™awar Sabuwan maigogul, Aminiyar Iyabo, uwar Wakin Tani Shanono na gwada na san amfaninshi, kema ´ar uwa ki kwada zaki bani labari siyan nagari maida kuWi gida.*"

*Mun sani yanzu yana da kyau duk abinda zamu siya musan ingancinshi da nagartarshi bawai muita siyan magungunan mata kara zube ba.*

"*Wannan kamfanin kayansu babu algus ko almundahana a ciki, da tsoron Allah da ™warewa gami da gogewa ta"

"sanin* *yadda ake sarrafa magunguna suke aikinsu, cikin nagarta da gangariyar tsabta.*"

*Abu mafi sha'awa komai a cikin kwali yake a rufe kirib*

*ga kaWan daga cikin abubuwan da kamfanin yake samarwa*

*Tsumin dadi har Madiga tareda gunbarshi*

*Tsumin no excuse mela™abin bita zaizai*

"*Gumbar dare daya wanka goma, dana gari da zumarta da tsuminta duk muna dashi*"

*Zumar hana bacci gumbarta da garinta*

*Munada Arabian sabaya tare d Sudanese sabaya*

*Da zumarta*

"*Sabaya ce dake cuko da ´a mace duk ramarta, da ™anjamewarta*"

*Itama da zumarta*

*muna da mummuna da aiki*

*Akwai tsumi da gumbar ta da zaune tsaye*

*muna da kogin daWi*

*Abangaren sanyi sun samar ma mata maganin matsolilinsu*

*muna da fitattun maganin sanyin da yake fata_fata d sanyi yayi mishi korar kare*

*Khanzur Rahman herbal formular*

*Sanyi clear syrup*

*7 days for chronic infections flusher*

*Sannan kuma muna da* *Package amarya*

*Package Uwargida*

*Package irin na zawarawan da suke shirin sabon aure*

"*Bugu da ™ari wannan kamfani yana sarrafa magungunan maza ba a iya na mata ya tsaya ba, wannan kamfani magungunan da yake samarwa suna da yawa wannan tsakurene daga cikin kayansu*"

*Da sauransu da sauransu wanda bamu ambata ba.*

*Ba fa a iya haka muka tsaya ba muna d cancada cancadan zannuwan Gado da carpet*

*Domin neman ™arin bayani ku tuntuSeta a kan lambar wayarta kai tsaye*

+2348032089456

*42*

"Ya ce."" E, anti Amina jikin Gwaggon kam alhmdullhi."""

"Na ce."" To haka ake so, ko za ka zo ka d'aukar muku abinci gashi nan Yusura ta kusa kammalawa kafin mu zo din."""

"Ya ce."" Ai yanzu nan ma Baba Zulai kanwar Babanmu suka zo da abinci dama kullum tana zuwa sai dare take tafiya wani lokacin ma da safe kafin na je ta riga ni, tunda sun hana kwana."""

"Na ce."" To shikkenan Hamusu ka gaishe mini da Gwaggon da ita inna Zulai din kafin mu k'araso."" ""In sha Allahu rabbi anti."" Yafad'a cikin kulawa da girmamawa."

To sai wajejan biyar na yamma muka gama shiri nida Sahura muka fito da zummar tafiya asibitin. Yusura na gidan

anan muka barta dama tunda suka zo na cewa uwar ta bar mini ita ba jayayya ta ce dama ai taki ce. Hijabi nasa har kasa na rufe fuskata da nikab saboda ba na so jama'a su gane ni.

"Tare muka shiga shago da ita na gayawa yaran zan fita amma ba zan jima ba zan dawo, ita Kuma Yusura na ce mata ta rufe gidan daga ciki."

A daidaita sahu guda muka d'auka har asibitin Malam.

"Muna d'an ta'ba hira na ce."" Sahura duk abin nan da nake yi wallahi idan na tuna halin da Alhaji Muntari yake ciki sai na ji kasala ta kama ni, haka kawai nake tausayawa masa ki ba ni kwarin gwiwar taimakonsa tunda ke ki ka gaya mini yadda yanayin jikin nasa yake."""

"Ta ce."" Sis kina da raguwar zuciya gaskiya, na taimaka miki ta wace siga kenan?"""

"""Idan mun shiga sai mu binciki asibitin bangaran maza ko Allah zai sa mu samu d'akin da yake sai na dubo shi."""

"""Kina da tabbacin yana asibitin har yanzu watanni uku fa na ce miki da suka wuce, wata'kila ma an sallameshi yanzu."""

"Na ce."" Sai mu sanya rana ki raka ni na duba shi a gidansa, wallahi har yanzu ina tuna irin alherinsa akan Kamalu ya yi mini kokari sosai akan Yusi lokacin da ya aureni bai bambamta tsakaninsa da yaransa ba."""

"Ta ce."" Kina cikin wannan rikicin sis, kada ki rikitowa kanki wani don Allah ki bar maganar nan, idan ki ka yi masa"

"addu'a daga nan ma ya isa ai Allah ya ga zuciyarki."""

"""Babu abinda zai faru Sahura Ubangiji da zuciya yake amfani."" Shiru ta yi tana girgiza kanta kamar buk'atata bata damu karbuwa ba a wurinta."

To muna shiga asibitin muka fara cin karo da motocinsa tunda komai nasa baya 'buya duk motocinsa akwai alama mai d'auke da ayyukansa na yau da gobe

"Cikin faduwar gaba na ce."" Kada dai mutumin nan ya sauka."" Na d'auka a zuciyata nake maganar sai da na ji maganar Sahura tana fad'in."" Shine ma ai kin san komai nasa a bayyane yake duk inda yake sai an gane, kuma tunda naga wannan motacin na tabbatar yana cikin asibitin nan."""

"Na ce."" Sahura kin ga irin abinda nake gaya miki ko? Matar nan fa mahaifiyar tsohon mijina ce amma ya yi ruwa da tsaki akan lamarinta ni ya hana ni ma aiwatar da komai, don girman Allah ki gaya mini ta yaya za a yarda da abinda zan fada a kansa."""

"Muna cigaba da tafiya ta ce.'' Kin san kuma Yana da tausayi da zuciyar Imani fa, shiyasa ake ta yi masa sha'awar mulki domin ana yi masa kyakykyawan zato da wahala ya samu labari ko ya ga mai neman taimako bai taimaka masa ba, ya yi da jiki da aljihunsa wannan yana daya daga cikin kyawawan halayensa."

Shiru kawai na yi ban ce mata komai ba domin gabad'aya kaina ya kulle da al'amarin nan da yake faruwa.

"Kiran da ya shigo wayata ya katse nazarin da nake yi. Hamusu ne, cikin nutsuwa na daga wayar nasa a kunnena. Sai da ya fara gaishe ni tukkuna ya furta."" Kun shigo asibitin ne anti?"""

"A takaice na ce masa ."" Eh, na dora da fadin wai kai baka gajiya da gaisuwa ne Hamusu Ina ce da safe mun gaisa haka ma d'azu dana kira ka sai da ka gaishe ni gaisuwa nawa za mu yi ne a rana."""

"Dariya ya fara yi kafin ya ce."" Ai babu lefi anti girmamawa ce, kin cancanci hakan ne."" Humm kawai na ce Ina ko'karin kashe wayar ya ce.'' Yallabai ma bai jima da shigowa ba tare da su Yusi suka shigo."""

"Ban yi mamakin jin cewa suna tare ba domin akwai Sukairaju a tsakani. A takaice na furta."" To babu lefi muna daf da shigowa ni da Sahura.''"

Ban jira amsarsa ba na datse kiran.

Ni da Sahura babu wanda ya sake wata magana har muka isa d'akin da Gwaggo take kwance wanda 'yansanda biyu ke tsaye a bakin kofa.

Ko ba a fad'a ba nasan masu tsaronsa ne. Muka kàrasa wurin suka nemi su hana mu shiga wai sai ya fito tukkuna. Kawai na tsaya ina kallonsu dan ban iya furta komai ba Sahura ce take ko'karin nuna musu wani abu Hamusu ne ya fito tare da wani likita suna magana.

"Ganinmu da sauri ya ce."" Yallabai ya haka kuma iyalinsa ce fa, ita kuma wannan kawarta ce."""

"Da sauri wanda yake tsaye a bakin kofar ya gyara yana sunkuyar da kansa ya ce."" Madam sorry ban gane ki ba kasancewar kin rufe fuskarki, a yi hakuri."" A nutse na ce."" Babu komai."" Na juya ina sauraran tattaunawar da suka yi da likitan yana fad'in tunda jikin ya yi sau'ki za a iya sallamarta gobe ko jibi ya dube ni yana kara yi mini bayanin yanayin jikin nata, da kulawar da ya kamata a dinga bata da kuma canjin abinci da sauransu."

"Na ce."" In sha Allahu za a kiyaye. Ya yi mana sallama cikin girmamawa da kulawa ba don mun kai ba sai don alfarmar wani wanda duniya ta d'aukaka shi."

Hamusu shi ya shige gaba kafin mu bi bayan shi ni da Sahura haka kawai sai na fara jin faduwar gaba kamar wadda ta tunkari ajalinta.

Gwaggo na zaune sosai a gefan gado Yusi yana kusa da ita da lemon zaki a hannunsa yana bare mata. Yayin da shi kuma yake hakimce a wata kujera dake d'akin wadda take kallon gadon da Gwaggo take zaune. Da alama hira suke yi yanayin da muka riskesu gabad'aya fuskokinsu sun nuna farinciki da murmushi.

Sukairaju da abokin tagwaitakarshi 'Dahuru dama su biyu ne masu take masa baya escort d'insa kenan suna tsaye a kansa.

Mu kula da hakkin wani komai kankantarsa. Littafin gudun aure na kudi ne kada ki karanta ba tare da kin biya ba.

Sai gwiwata ta yi sanyi ganin yadda kaf hankalin Gwaggo yake kansa cikin kulawa suna magana shi ma ya bada

hankalinsa kacokan gareta.

"Muka yi sallama gabad'aya ina kallon Sahura ta nufi wurin da yake da azama. Ni kuwa da sauri na kawar da kaina na nufi Gwaggo da kulawa ina fad'in."" Alhamdulillahi Gwaggo jiki ya yi sau'ki ma sha Allah."""

Yadda na rungumeta itama haka ta rungume ni ta dora hannunta wanda yake da wadatar lafiya a bayana tana

"fad'in.'' Na ji sauki sosai Amina, na gode muku kwarai da gaske, yadda kuka yi mana Allah Ya sa ku ma yaranku su yi muku, Allah Ya yi albarka."""

"Na dan gyara na zauna gefanta har yanzu ina ri'ke da ita a jikina na ce.""Babu komai Gwaggwo, ai na yi wa Hamusu fad'a a lokacin da yake gaya mini, na ce daka yanzu kada ya kara bari sai abu ya yi nisa tukkuna zai gaya mini, ban ji dad'in abinda ya yi ba ko kad'an."""

Murmushi kawai ta yi bata ce komai ba.

"Yusi da tun shigowarmu yake ta satar kallona Ina kallonsa yaron kamar yana shakkata a tsorace ya ce."" Mama ina yini?"""

"Na dubi shi a tsanake na amsa da ""Lafiya lau ya kake?"" Da dan murmushi ya ce."" Ina nan lau Mama ."""

"Na harareshi da fad'in."" Ai na ji labarin shegantakar da ka yi, za mu had'u ne."""

"Dariya ya yi yana sunkuyar da kainsa. Jikina ne gabad'aya ya mutu sakamakon idonsa da ya zuba mini, a jikina na jiki hakan a nutse na dubi wurin da yake muka had'a ido fuskarsa babu yabo babu fallasa yake ta kallona. Sahura ta iso wurin da muke da wani irin yanayi a tare da ita, ba ita kadai ba ma na lura duk wanda yake d'akin bai ji dadin abinda na yi ba, shi ma Hamusu duk ya yi tsumu-tsumu sai ya'ke ya ke yi."

"Cikin nutsuwa na dube tare da cewa."" Yallabai barka da yamma."""

"Bai yi nauwar amsawa ba ya ce."" Barkanmu dai mun same ku lafiya."""

"Na amsa da ""Lafiya lau."" Da wahala dama ya nuna akwai 'baraka a tsakaninmu bai iya nunawa a bainar jama'a ba zan yi masa wannan shedar ya iya taku."

"Bayan amsawarsa ma sai ya biyo ni da kyataccen murmushi. Na yi saurin dauke kaina gabana na cigaba da bugawa. Ni kaina na san Allah Ya jarrabe ni shi, domin ko Yaya Aminu karyar so nake yi masa. wannan mutumin ya riga da ya gama sace zuciyata. Inda Allah Ya taimaka ni ban ta'ba nuna masa tsananin so ballantana ya rike hakan a matsayin makamin da zai ya'ke ni."

"Gyaran murya ya yi gabad'aya muka dubi wurin da yake. Ya tashi tsaye a nutse ya nufo inda muke hakan ya

Please Login or Register in order to submit comment