You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

irin sanyi na fili da boye wanda zaku hadu da maigidanki kuyi amfani tare. Akwai ingantattun supplement wad'anda basu da illa balle su cutar da GARKUWAR jiki. Sai dai su gyara su kuma tayar da komad'a ina nufin inda ya samu nakasu a jikinki. Muna sayar da sabulan gyaran jiki dilka da man gyaran gashi, muna kuma bayar da sari a fad'in najeria da nijar muna tura kayanmu kowane gari da ikon Allah.*"

*Muna garin kano duk inda kake za mu aika maka da kayanmu. Domin neman karin bayani sai a yi mana magana ta Whasap ga lambobin da za a same mu a kai.*

*07084653262 ko*

*08089965176*

*SIYAN NAGARI!!!!!!*

*A JARRABA A SAMU BIYAN BUKATA DA YARDAR ALLAH*

TEEMAH DATA SERVICES MTN

1GB @550

2GB @950

3GB @1450

4GB @1550

5GB @1700

CHECK CODE *323*4# VALIDITY 30DAYS CHAT@08112392177 CALL @08037026306

8037026306 fatima musa ibrahim opay

*22*

Dama tare muke da Hadiza a d'aki daya ina shiga d'akin na sameta tare da Yusi suna hira da yake yau asabar babu makaranta sai wajan sha daya tukkuna yake tafiya islamiyya sai yamma kuma ya dawo.

"muka gaisa gabad'aya a gurguje na shiga toilet domin watsa ruwa. Ina ciki na dinga jin magana kasa-kasa Hadiza ce take waya kuma na ji tana ambatar sunana. Ban kawo komai a raina ba domin dan zaman da na yi da ita na fahimci cewa dole akwai k'auna irin ta 'yan uwantaka a tsakaninmu ba zata cutar da ni ba. Ina fitowa take cewa da ni."" Fati ce babu lafiya, tana kwance a asibitin Malam Aminu an yi gwaji sakamakon ya fito tana d'auke da cancer mama. Hankali ya tashi ainun domin kuwa nasan ciwon yana da illah."

"Cikin damuwa na ce."" To yanzu ya ake ciki ya jikin nata."""

"Cike da alhini don har sai da hawaye suka zubo a kumatunta ta ce."" Kin san mijin nata ba wani kudi ne dashi ba akwai dai rufin asiri kuma tunda suka tara yara nauyi ya yi masa yawa da kyar ma yanzu suke samun ci abinci yanzu yaranta biyar."

"To shine yake gayawa Babanmu shi ya gaji ba zai iya cacar asibitin Malam ba domin bashi da iko a dawo da ita gida ayi mata na hausa kawai. Shine Ummanmu take gaya mini yanzu."" Tasa hannu goge hawayen da yake ta zarya a kumatunta."

"Na ce."" Ba za a yi haka ba Hadiza ni menene amfanin arzikin nawa ai saboda irin haka nake nema ba dare ba rana in"

"sha Allahu babu abinda zai gagara, ki kira mini Ummantaku a waya yanzu sai mu yi magana."" Da sauri ta d'auki wayarta dake ajiye ta kirata."

"Na kar'ba muka gaisa na ce."" Ashe Fati ce bata da lafiya Umma amma me yasa ba a gaya mana da wuri ba."""

"Da damuwa a tare da ita tace."" Yanzu ne tura ta kai bango shiyasa na ce Hadiza ta taho gida domin ta taya ni jinyarta ga yaranta a gabana uban yana nuna gazawarsa nema ma yake ya sakar mana dawainiya."""

"Na ce."" Yanzu nawa ake bukata a asibitin wajan yi mata aikin."""

"Ta ce."" Ai kin san jan kudi irin na asibitin Malam wai suna buk'atar miliyan shida domin yi mata aikin saboda kada d'ayan ma ya harbu.''"

"Na ce."" To ku kwantar da hankalinku in sha Allahu rabbi zan sanya Hamusu ya je asibitin ya biya kudi Kafin na"

"kàrasa ta ce."" Ki dai sanya shi ya tura a acct din ita Fati din kin san mijin nata da zargi kada ya juyawa mutane magana idan ya zo sai na yi masa bayani kece ki ka biya kudin aikin, zan yi wa babanku bayani ma."""

"Na ce."" To shikkenan zan kar'bi acct din a wajan Hadiza Ubangiji Allah Ya bata lafiya."" Ta amsa da ""Amin Ya Allah, mun gode sosai Amina Allah Ya yi miki albarka."""

"Na ce."" Babu godiya a tsakaninmu Umma Fati kanwatace don na yi mata abu ba komai ba ne."

Mukayi sallama na kashe wayar na mik'a mata wanda har zuwa lokacin kuka take kashir'ban tana share hawaye kamar wadda aka ce mata Fati din ta mutu.

"Na ce."" Hadiza ki yi shiru don Allah, a yanzu Fati babu abinda take buk'ata sai addua. Kuma in sha Allah idan kudi"

"suna magani, na yi alkawarin zan yi daidai gwargwadona sai kuma mu bi ta da addu'ar samun lafiya daga wurin Allah domin shine yake saukar da cuta, ya kuma bada sau'ki."""

Ta goge hawayen fuskarta tana sake yi mini godiya. Ban ce komai ba na nufi wardrobe dina domin sanya kayana a jikina.

Da tunanin rashin lafiyar Fati na yini a cikin raina. Gashi na yi ta kiran wayar Hamusu domin mu san yadda za a yi

"bata shiga ban san menene dalili ba. Amma na bari da daddare sai na kara trying na ji, Hamusu baya kashe wayarsa a duk lokacin da aka kira shi ana samunsa."

"Daddare ina d'akin maigidan Hamusu ya kira, ban yi mamaki ba domin lokacin dana kira shi ban same shi ba sai na kawai tura masa text wanda na san koda matsalar network ne idan ya saki zai gani."

"Lokacin maigidan yana bandaki don shima bai jima da shigowa ba, kuma baya zaman cin abinci sai ya yi wanka tukkuna."

"Na daga wayar da zuciya daya Ina fad'in. "" Hamusu lafiya ake ta kiran wayarka bata shiga."""

"Ya ce."" Wallahi anti Amina yini akayi ana ruwa anan duk network din layina ya sauka sai yanzu ya dawo. Na ce."" Ni ma na zargi hakan shiyasa na ce bari na yi maka text na san zaka ga ni."

"Daidai lokacin da yake ba ni amsa shi kuma ya fito daga band'akin... Na ce."" Wallahi kuwa d'azu muka yi waya da"

"Ummansu cewa jikin nata ya yi tsanani, asibiti sun bukaci kudi zan dai yi maka magana ta Whasap idan an jima sai muga yadda za a yi."""

"Ya ce."" To shikkenan anti ina sauraranki.''"

"Na kashe wayar tare da ajiyeta a gefena na dube shi yana zaune kan sofa yana dan mutsika cream a jikinsa. Amma canzawarsa ta ba ni mamaki fuskarsa babu annuri bai kuma kalle ni ba ya ce."" Wanene ma Hamusu ne?"""

"Ya fad'a babu annashuwa a tare dashi. Kallonsa nake da mamakin tambayarsa ai na d'auka a iya dad'ewarmu dashi ya fahimci wanene Hamusu tunda har tafiya mun had'a shi a lokacin da muka je duba Kamalu a makaranta wanda har alherin kudi ya yi masa, amma yanzu saboda tada zaune tsaye yana tuhumata."

Shiru na yi ban iya ce masa komai ba.

"Ya sake cewa."" Wanene Hamusu Amina?"""

"A nutse na ce."" Kanina ne shi, abokin kasuwancina kuma mahaifinsu Yusi ne tunda kanin Ubansu ne."" Ya zuba mini ido da ce wa."" Ni ban haifesu ba kenan shiyasa kike so ki nuna mini iyakata."""

"Na ce."" Ba haka nake nufi ba."""

"""Okey wace magana na ji kuna yi fitowata daga bandaki ki ka katse har kina cewa zaku hadu ta whasap."" Cikin ko'karin kama mutuncina na ce."" Ba wata magana ba ce ranka ya dad'e wani abu ne da shafe ni."""

"Ransa ya sake 'baci."" Okey shi Hamsun ne yake auranki da har ni ban isa ki gaya mini abinda ya shafe ki ba sai shi, ni"

"namijin hotiho ne ko, sai a shimfida nake namiji amma a zamantakewa ba ni da amfani ko."" Na ce."" Wai don Allah me yasa kake nema ka canza mini magana ne nifa ba hak..."

"Ya buga hannun kujerar da yake zauna yana kallona da kishi da b'acin rai ."" Ke ba ki ji kunyar yin magana da wani namiji a d'akina ba Amina, wai me yasa kike nema ki raina mini hankali ki mayar da ni shashasha, ni zaki ciwa fuska a gidana, a kuma d'akina ki dinga waya da wani dan iska, har kina kashe waya saboda kada na ji abinda zaku tattauna, ba ki d'auke ni mutum ba ko."""

"Cike da mamakin fusatarsa na ce."" To da kuma ka ce baka gane shi ba, Hamusu ne fa ba wani ba, a tunanina ko zaka zargeni da wani namajin ba zaka zargeni dashi ba tunda kanin uban yarana ne, kuma kasan dole a kowane lokaci alaka ta had'a ni dashi dalilin Kamalu da Yus ""Me yasa baki aure shi ba."" Ya katse maganata yana huci ya cigaba"

"da ce wa."" Idan zargi zan yi akanki shine mutum na farko da zan zarga domin alak'ar(ALAKAR ZUCCI) Littafin marubuciya (Maidamu) kada ku bari a baku labarinsa. domin alak'ar da take tsakaninki dashi ta yi muni, wane irin cin fuska ne wannan."""

"Shiru na yi ban ce masa komai ba, amma raina ya gama baci da irin abinda yake yi mini, wani lokacin yana kasancewa mai sanyi da sau'kakawa a cikin al'amuransa, amma a wasu lukutan idan yana masifa har mamaki yake ba ni, sai ya rufe idonsa kamar bashi da ilimin Arabi da boko."""

"""Ba za ki gaya mini akan abinda kuke magana ba ko?"" Ya fad'a yana tsatstsare ni da Idonsa. A nutse na ce."" Fati ce"

"bata da lafiya shine aka bukaci kudi a asibiti za a yi mata aiki, to dama akwai kudina a hannunsa shine na ce ya cire ya tura musu."""

"Ba tare da ya kalleni ba ya ce."" Wacece Fati?"""

""" 'Kanwata ce, itace take bin Hadiza a dakinsu."""

"""Shine ba za ki sanar da ni ba saboda kina so duniya ta zage ni ko?kin san dalilin da ya sanya suka kira ki a waya suka"

"gaya miki domin sun san kina aurena akwai hanyar da zasu samu mafita, sai ki ka za'bi kiran kanin tsohon mijinki, kina gaya masa ya basu kudin maganin ko?"""

Kaina na dafe da yake sarawa. Na dago na kalleshi Ina auna maganganunsa da basu da tushe balle makama. Na tsira masa Ido ina ayyanawa a raina cewa babu mamaki rikicin tsufa ne ya fara kama shi amma idan ba haka ba ya za a yi ya nemi ya canza mini manufa bayan ba haka ba ne a cikin zuciyata.

"Ya ce."" Kin yi shiru saboda kema kin san ba ki da gaskiya ko?"""

"Na dai yi shurun ban tanka masa ba, saboda ba mu jima da sasantawa ba, ba na so akan wannan 'karamin dalilin da yake nema ya mayar dashi babba mu koma 'yar gidan jiya."

"""Ba za ki ba ni ha'kuri ba kenan?"""

"Cikin dariyar da ban san lokacin da ta sub'ce mini ba na ce."" Ka yi hakuri Baba, ba zan sake ba."""

"Ya girgiza kansa tare da mikawa ya nufi wardrobe dinsa yana cewa."" Saboda kina waya da Hamusu ko kayana baki d'auko mini ba na gode miki Amina."""

Wallahi shaf na manta domin hankalina ya tafi wajan ganin na samu Hamsun a waya an gama komai.

"Daidai lokacin dana isa wajan da yake tsaye ya d'auko k'ananun kaya t-shart da short nicker na kar'ba daga hannunsa tare da cewa."" To mu je na shiryaka."""

Ya kuwa biyo ni zalo zalo! muka zauna a gefan gado yana ta kallon fuskata yayin da ni kuma na take ta danne dariyar da take yun'kuro mini.

"Bayan na taimaka masa ya shirya sai ya dube ni babu wasa a fuskarsa. Ya ce.'' Ki goge lambar Hamusu daga wayarki."""

"Da mamaki na ce."" Me yasa Baba?"" ""Ki goge dai kawai akwai dalilaina."""

"Ganin da gaske yake yi ya sanya ni ma na shiga nutsuwata sosai na ce."" Kai ma kasan hakan zai yi wuya, mu yi maganata gaskiya da gaskiya my love, ba na neman fitina domin ba za ta yi mana dad'i ba, Hamusu ba kowa ba ne a wurina face d'an'uwana abokin kasuwancina, sannan kuma kafi kowa sanin dangatakar da take tsakaninsu da mijina na fari uwa daya uba daya suke, bayan wannan ba ni da wata alaka dashi, Ina ganin baka da hujja mai karfi da zaka ce lallai sai na goge lambarsa daga wayata."

"Ya zuba mini ido da tsananin b'acin rai yake ce wa."" Ba ni da hujja mai karfi ko?"""

Juyar da kaina na yi daga barin kallonsa domin na lura maganata ta yi masa zafi.

"Ya d'auki wayata dake ajiya a gefena, na bishi da kallo amma ban yi yun'kurin kwacewa ba, ina kallo ya goge lambar Hamusun daga wayar ya dube ni."" Ban yafe miki ba idan ki ka sake magana dashi, na san goge lambar ba zai dame ki ba tunda zai kira ki wataran saboda yana da taki. Idan ki ka ci amanata Allah Ya yi mini sakayya."

"Hawayen da nake dannewa suka zubo. Na ce."" To sai ka gaya mini zargina kake yi ko me? Ka san ko zan yi neman maza ba zan yi da Hamusu ba, domin kuwa kafi kowa sanin halina."

"""Ni ba na zarginki, kawai na datse alakarku ne domin mutuncina da kike ko'karin ki zubar mini."" Na gyada kaina ban sake ce masa komai ba na tashi na bar masa d'akin."

"Da takaicin abin na kwana a cikin raina, amma hakan bai hana ni zuwa na gaishe shi ba yana zaune wajan da yake hutuwa, muka gaisa babu sukuni bai dube ni ba ya ce."" Ki dama mini kunun tsamiya dashi nake sha'awar karyawa."" Ban ce komai ba na tashi na fita. Minti talatin na gama tsaf na kai masa na ajiye tire din zan fita ya ce."" Sannu."" Kanzil ban ce ba na fita. Kicin din dai na koma na d'auko wanda na hadawa Hajja na kai mata har dakinta tunda lokacin bata fito ba. Kafin na shiga na ji maganarsu ita da 'yar'uwarta inna Uwani suna tattaunawa akan abinda ya shafi hidimar da take gabatosu. Muka gaisa ko da wasa ban nuna cewa na ji abinda suke cewa ba, kuma na yi kokarin ganin na boye bacin raina."

"Na fita na nufi d'akina. Hadiza tana ta had'a kayanta a cikin kwataki na ce."" Hadiza wai tafiyar ce ba zaki bari sai wani satin ba."""

"Ta ce."" Zan dawo ai Amina, gabad'aya hankalina ne ya yi gida ina so naje naga jikin Fatin.' Na ce.'' Ni ma in sha Allahu bada jimawa ba zan zo, Ubangiji Allah Ya bata lafiya"""

"Ta amsa da Amin."" Kayan jikina na cire ina shirin shiga wanka ya shigo d'akin."

Lamari mai girma ne yake kawo shi d'akina dalilin da ya sanya ma kenan dana ganshi gabana ya fad'i.

"Hadiza da sauri ta risina tana gaishe shi. Ya amsa fuskarsa a sake Yana dubanta da kulawa ya ce. "" Ashe Fati ce bata da lafiya."""

"Ta ce. Eh wallahi yanzu ma shirin tafiya nake yi domin zuwa dubanta."" Sai ya kalleni yana cewa."" Zata tafi amma ba ki gaya mini ba."""

"Shiru na yi. Ya kawar da kansa yana cewa da ita."" Nawa ne abinda aka buk'ata?"" Cikin inda-inda ta ce."" Miliyan shida ne?"""

"Ya ce."" Me yasa ke ba ki same ni kin gaya mini ba, tunda ita ban isa ta ta sanar da ni ba."""

"Ta yi shiru tana dan murmushi ya ce."" Ba ni lambar asusun da za a sanya kudin sannan zan sanya a kai ki gida don ba zan yarda ki bi motar haya ba."""

"Cikin sauri ta gaya masa lambar acct din Fati mai suna Salisu Fatima Fedlity bank. Ya ce."" Zan saka in sha Allahu idan kin je gidan ki gaishe mana dasu kafin mu zo."""

"Ta amsa da sauri tana cewa."" In sha Allahu kowa zai ji, Ubangiji Allah Ya saka da alheri ya kara arziki mai amfani ."" Bai amsa ba ya fita daka d'akin."

"Ta dube ni tana cewa."" Amina don Allah ki kara yi mana godiya, ke kam Allah ya kashe ya baki, shi so yake yi ma ki fad'a masa hidimar 'yan uwanki ya yi miki."""

"Na dubeta babu yabo babu fallasa na ce."" Hadiza ba wannan ba, ki nutsu dan Allah kada don kin ga ya ce haka ki"

"nemi zubar mana da mutunci don girman Allah duk abinda kuke buk'ata ku gaya mini ba zai gagareni ba, amma ba na so ku tambayeshi yin hakan sai ya rage mini kwarjini da martaba a idonsa."""

"Ta ce."" Eh kuma hakane to zan kiyaye in sha Allahu."""

Na tashi na shiga toilet din da tunaninka masu yawa a kwanyata.

"Hadiza kuwa kwafa ta yi cikin zuciyata tana ce wa'' Mutuncin banza da wofi ya dad'e b ai zube ba, saboda b'akinciki"

"mutum yana so ya yi alheri kina dakusar dashi, sai mun tambaye shi din ki yi duk abinda za ki yi "

*GARKUWAR MATA.*

*BINTA UMAR ABBALE*

"[6/3, 8:38 PM] matar mijinta: *Wannan littafin na kudi ne vip 1k akan telegram. Normal What'sapp group kuma #700 hanyar da za a biya kudin ita ce wannan...0542382124...Binta Umar gtbank ko kuma 7084653262. Binta Umar"

Opey bank. 'Yan nijar dala dari katin airtel za ku tura mini bayan kun kankare hoton. A tura da sheda ta wannan lambobin iya What'sapp kawai.*

*07084653262*

*08089965176*

*V-VIP AREWA PEN *

*TALLAH!*



*DA MAGANI A GONAR YARO!!*

*08089965176*

*07084653262*

"*Dayawa akwai matan da suke da matsala ta lalacewar nono yamushewa da kuma fad'uwarsa. Wasu ma 'yan mata ne basu kai ga matakin aure da shayarwa ba amma sai su samu matsalar faduwar nono. To gaskiya akwai magani sai dai kawai idan ba a yi dace ba. Wasu zasuyi ta faman kashe kudi amma buk'ata bata biya ba, wasu kuma zasuyi ta fargaba kada su je garin neman gira a rasa Ido, ma'ana su sayi abinda zai cutar dasu da kudinsu. Kuma yanzu dai tsakani da Allah rijalu sun riga sun gama nuna abinda suka fi karkata a kansa a jikin 'ya mace kirji da kuma baya. Wasu Allah ya hallice su dashi har ya yi musu yawa, wasu kuwa basu dashi kuma mai saurin zubewa ne. To mu dai duk wanda ya san maganinmu ya san ingantacce ne, kuma Yana aiki kwarai da gaske wurin dawo da daraja da martabar nono da izinin Ubangiji. Sahihin magani ne da ya samu sheda da lambar yabo, kuma Islamic ne da akayi masa hadi mai inganci domin gyara jikin mace ba ma iyakacin nono kawai ba. Babu nadama haka zalika babu dana sani da asarar dukiya wurin sayan maganinmu. In sha Allah matsalar ki zata gushe idan kin jarraba amfani dashi. Ba mu tsaya ina nan ba, muna da na gyaran hips sahihi dana k'iba idan kina fama da matsalar rama. Haka zalika muna dana tumbi, da kuma maganin sanyi mai mugun kyawun da yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye wanda zaku hadu da maigidanki kuyi amfani tare. Akwai ingantattun supplement wad'anda basu da illa balle su cutar da GARKUWAR jiki. Sai dai su gyara su kuma tayar da komad'a ina nufin inda ya samu nakasu a jikinki. Muna sayar da sabulan gyaran jiki dilka da man gyaran gashi, muna kuma bayar da sari a fad'in najeria da nijar muna tura kayanmu kowane gari da ikon Allah.*"

*Muna garin kano duk inda kake za mu aika maka da kayanmu. Domin neman karin bayani sai a yi mana magana ta Whasap ga lambobin da za a same mu a kai.*

*07084653262 ko*

*08089965176*

*SIYAN NAGARI!!!!!!*

*A JARRABA A SAMU BIYAN BUKATA DA YARDAR ALLAH*

TEEMAH DATA SERVICES MTN

1GB @550

2GB @950

3GB @1450

4GB @1550

5GB @1700

CHECK CODE *323*4#

VALIDITY 30DAYS

CHAT@08112392177 CALL @08037026306

8037026306 fatima musa ibrahim opay

*23*

Bayan tafiyar Hadiza da kwanaki uku sai na ce bari na kira na ji ya taje gida domin na yi mamaki sosai da bata kira ni ba wai bahaushe ya ce 'Idan ka ji shiru lafiya ce.'

Babanmu na fara kira domin mun kwana biyu ba mu gaisa ba. Bayan mun gaisa sosai na tambayashi gida ya ba ni amsa da komai lafiya sai na ji bai sako mini maganar rashin lafiyar Fati ba. Lokaci kan'kani na fara nazarin wani abu a zuciyata.

"Na ce."" Baba ya jikin Fatin ina fatan an yi mata aikin domin tun bayan barin Hadiza daga nan nake ta dakon kiran waya domin a sanar da ni halin da take ciki, wallahi hankalina ya tashi sosai da wannan ciwon da ya same ta."

"Ya ce."" Ai ta ji sauki tuntuni jiya ma ta koma gidanta, maganar aiki kuma ni ban san dashi ba, domin bayanin da mijinta ya yi mini cewa zazzabin typhoid da maleria ne yake damunta. Shine ya kawo ta gida domin a kwance take sosai a can din, k'arin ruwa kawai nasan anyi mata da allurai shikkenan kuma kwana biyu kacal ta warware mijinta ya zo ya d'auketa da yaran suka tafi."

"Cike da mamaki da mutuwar jiki na ce."" To ikon Allah, amma ni ba haka Hadiza da Ummansu suka gaya mini ba, amma shikkenan babu komai Ubangiji Allah Ya bata lafiya."""

"Ya amsa da Amin kafin ya d'ora da cewa."" Amina me yasa idan kin tashi yin alheri ne ba kya had'awa da Sakina tunda Hadiza ta dawo suke husuma a gidan sun hana ni shan ruwa Hadiza da uwarta sun had'ewa Sakina kai, kuma duk irin alheran da ki ka bata sun hana Umman Saminu, shin ko kema Murja ta lalataki ne."""

"Da sauri na ce."" Wallahi a a Baba, sharrin ba na kowa ba ne face na Hadiza domin kuwa ni duk abinda na bayar gabad'aya gidan na basu ban ware kowa ba, ai kaga ko da salla d'inki iri daya nake yi musu."""

"Ya sauke ajiyar zuciya yana cewa."" Ni ma na zargi Hadiza da d'aga mini hankali, domin kuwa tunda ta kaso auranta ta dawo gida ta zauna shikkenan gidan ya zama kamar sansani, itace fad'a da wannan itace fad'a da wannan."""

"Na ce."" Baba ka yi hakuri kayi mata addu'a Allah ya fito mata da mijin aure, amma ya zama dole na kira ta a waya"

"domin na ji dalilinta na yin hakan."""

"Ya ce."" To shikkenan hakan ya yi Allah ya yi mini albarka."""

"""Amin Baba zan sanya Hamusu ya tura maka kudi koda da akwai buk'atar da zakayi."" ""Na gode sosai Allah ya sanyawa dukiyarki albarka, ya kuma shirya miki zuriarki."""

Muna yin sallama na kira Anti Yagana raina a b'ace na shiga sanar da ita abinda Hadiza da Ummansu suka aikata.

"Yanzu na gane karyar ciwo suka shirya da Fati domin su samu kudi a hannunà ban ta'ba kawo hakan a cikin raina ba domin zaman watannin da ta yi a gidana ban ta'ba zargin zata cutar da ni ba, don Ina ganin yadda take shiga damuwa a duk lokacin data gan ni, a cikin matsala."

"Anti Yagana itama ranta ya 'baci sosai, ta dinga fad'a tana cewa dama tun farko sai da ta zargi hakan shiyasa a lokacin da ta tubure sai ta zauna mini ranta bai so ba, babbar damuwarta ma kofar da maigidan ya basu tunda da bakinsa yake cewa idan suna buk'atar wani abu su sanar dashi, wannan zai basu k'warin guiwar zubar mini da dan ragowar mutumcin da nake dashi a wajensa. Ta ce lallai zata kira Hadizan ta ja mata kunne akan abinda suka shirya ba daidai ba ne."

Ni ma a take a lokacin bayan na yi sallama da ita na lalubi lambar Hadizan na kira minti daya ta daga da fara'ata

"muka gaisa a takaice na ce."" Ba na neman wani 'karin bayani daga wajanki Hadiza na gode bisa abinda kuka yi mini, Babanmu ya gaya mini komai, yanzu Hadiza idan kudi kike so a wurina har sai kun shirya karya, me yasa ba zaki tambayeni ba."""

"Shiru ta yi ba tace komai ba. Na cigaba da cewa."" Sannan duk uban kayan nan dana hada da na ci, dana sha, dana sanyawa babu abinda kuka bawa Ummansu Saminu alhalin cewa na yi a rarraba har gidajensu Baba Sule shine kuka had'a gabad'aya babu wanda kuka bawa."""

"Ba ta ce mini komai ba ta dai yi shiru tana jina. Na ce.""Wannan zama na farko ya kuma zama na karshe wallahi tallahi kada ki sake yi mini haka domin ni na tsani na zauna da mutum da zuciya daya amma shi

Please Login or Register in order to submit comment