You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kashe wayarsa, ko jiya da yamma mun gaisa."" A sanyaye ya ce."" Ina tsammanin hakan."""

"""Neman me kake yi masa ne?'' Na fad'a idona a tsaye a kansa. Bai dube ni ba ya furta."" Ina son zuwa kano din ne na"

"kwana biyu a wurinsa"" Na ce."" To ka gayawa Baban?"" Ina nufin maigidan."

"Ya gyada kansa a nutse ya ce."" E jiya naso na sanar masa kuma sai na manta, kuma mun yi waya fa, amma dai zan gaya masa ina jin tsoron ya ce a a ne Mama."""

"""Ka dai gaya masa mu ji mai zai ce, itafa Momin taku?'' ajiyar zuciya ya sauke a hankali ya ce."" Mun yi maganar dazu"

"har ta fara had'a mini tsaraba."""

"Shiru na yi kawai ina kallonsa. Har yanzu yanayinsa bai canza ba. Na ce."" Kaga ka gaya mini dalilin da zai sanya ka zuwa kano ina tsammanin ai baku wani jima da zuwa ba ko ba haka ba ne?"""

"Shiru ya yi bai ce komai ba sai da na sake maimaita maganarta sannan ya ce."" Eh kafin tafiyarku legos ke da Baba muka je wata shida kenan yanzu. Mama ba na tsammanin zan cigaba da zama anan, can wurin Baba Hamusu zan koma?"""

"""Akan wane dalili?'' Na fad'a ina kallonsa. Wannan maganar za ta iya janyo rikici a gidan, ta kuma janyo mana b'acin"

"rai ni da shi, abinda maigidan ya tsana kenan. Ya dai yarda dai ya sanya akai su su yi kwana biyu gidan Gwaggo kwana biyu gidan Hajja a dawo dasu wajan matarsa. Ni kuma ba ni da damar magana ko da ta maslaha ce sai ya juyata ya yi ta neman rigima yana fad'in don ba shi ya haifesu ba zan nuna masa iyaka, zan nuna masa bai iya ba, duk yadda zan yi masa misali ba zai gane ni ba, karshe ma sai ya ce zai kira Baban Saude dole nake jan bakina na yi shiru na kyale shi."

Gudun aure paid book ne kada ki karanta mini littafi ba tare da kin biya ni hakkina ba

"""Mama ba zan rufe miki ba, tunda Salim ya dawo daga karatu yake yi mini wasu abubuwa na rashin kyautawa da"

"nuna k'yama. Ba zai ci abinci tare da ni ba, ba zai kwanta d'akin da nake ba, haka zalika a cikin kwana biyun nan baya bina jam'in sallah a massalaci, ina kallonsa ya ke tafiya wani massalacin na daban. Ban san menene dalili ba, Mama amma kuma baya nunawa Yusi k'yama, wannan dalilin ya sanya ni yanke shawarar barin gidan gabad'aya domin ba na so watarana na kasa jurewa muddin a haka zamu dinga tafiya dashi babu kyakykyawar ala'ka, babu musabaha da girmama juna sai k'yama, zuciyata ba zata iya jurewa ba, Ina jin tsoron mu yi fad'a hakan ya ta'ba zumuncinku da zamantakewarku. Kin ga Momi babu komai a tsakanina da ita sai alheri Ina sonta sosai wallahi irin yadda nake sonki Mama, amma ba na so mu yi abinda duka zai bata muku rai shine dalilana."""

Nasan dama ruwa baya tsami banza. Amma kuma sanin da na yi wa yaron a baya kafin ya tafi karatun ba haka yake

"ba. Yaro ne mai nutsuwa da son mutane irin d'an uwansa Adam ga barkwanci. Nusaiban dai ce mara fuska. Na daure ban nuna b'acin raina a fili ba na ce."" Kenan ba ku taba magana ba tunda ya dawo?"""

"Ya ce."" Idan na mik'a masa hannu domin musabaha baya kar'ba. D'azu da safe a gaban Momi ya y hakan ya 'bata mata rai sosai ta yi masa fad'a. Shine ya tashi ya fita bai dawo ba har na fito, wallahi mama kada ki so ki ga yadda hankalinta ya tashi, shine take cewa kada na gaya miki."""

"Shiru na yi ina nazarin al'amarin. Kamalu bai yi lefi ba domin kuwa anan ya yi aiki da hankali da kuma iliminsa. Na kuma ji dad'in abinda ya yi da har ya iya danne zuciyarsa bai biye masa ba. Shawarar da ya yanke itace mafita muddin kuwa ana son zaman lafiya. Idan har Salim bai gane abinda yake yi kuskure ba ne, to babu mamaki wataran gagarimar matsala ta faru tunda ni nasan wanene Kamalu a fagen zuciya."

"Amma yadda zan yi na sanar da maigidan halin da ake ciki shine matsalata. Na riga nasan rikice ne akwance domin kuwa baya d'aukar abinda ya shafi matarsa da wasa. Maganarsa daya amanarsa ce 'ya'yanta ma amana ne, a wannan ga'bar kuwa ya zame masa dole ya bincika domin tabbatar da gaskiyar abinda yake faruwa ya kuma gyara matsalar kafin ta yi nisa."

"Na ce."" Abinda za a yi yanzu shine ka d'an daure kad'an, ai ni ka burgeni sosai da har ka yi irin wannan tunanin"

wannan ya sake nuna mini cewa Kamaluna ya bambamta sosai da wanda na sani a baya. Ka cigaba da yi masa magana kada ka biye masa ni kuma zan yi magana da Baban nasan dai haka kawai ai ba zaka kirkiri karya don jin dadi ka gaya mini ba ko?''

"""Wallahi Mama babu karya cikin maganata gaskiyar abinda yake faruwa na gaya miki, menene ribata idan na yi k'aryar kuma me ya yi mini da zan 'bata shi."""

"Na ce."" To kada nunawa Momi damuwarka a fuska ka daure ka ji ko."""

"Ya ce."" In sha Allah Mama."

"Daga haka sai muka bar maganar muka shiga wata ina d'an jansa da wasa duk domin ganin ya manta abinda yake damunsa. Amma zahiri ni a can 'kasan zuciyata cike nake da fargabar yadda zan tunkari maigidan da maganar. Wala'ala ya fahimceni, wala'ala kuma ya juya mini manufa, amma dai tun yanzu ya kamata a ce ayi wa tufkar hanci kafin lamarin ya yi tsamari rayuka su zo suna 'baci."

Daf da magriba ya tashi ya fita da zummar shirin shiga massalaci.

Bayan kwana biyu ina cikin nazari domin har yanzu na kasa tsayar da abinda nake ganin shine daidai. Ba na so na yi

magana ne a ce na goyi da bayan yarona wata'kila shi kansa zai iya ganin haka shiyasa hankalina bai kwanta ba har yanzu sai dai na gaza daurewa na sanar da Baba Tabawa abinda yake faruwa domin kuwa macace mai tsinkaye da nisan tunani.

"Ta jima tana jimantawa kafin ta ce."" Ai shurun ba shine mafita ba, gwara ki gaya masa tunda shine jagoran kowa a gidan ya yi wa tufkar hanci kada lamari ya yi k'wari hatsaniya ta tashi ya ce mai yasa ba a gaya masa ba. Ina ganin duk wanda zai ce kin so kanki da zummar kawo gyara to ya zalinceki domin kuwa abinda ki ka yi shine daidai, ai ba ki za'bi Kamalu kin fifita akan Salim ba, duka naki ne kamar yadda itama Momin take nunawa, to ya kamata a ce wannan 'barakar da take ko'karin kunnowa an yi maganinta."

"Ajiyar zuciya na sauke bayan duk na gama sauraran maganganunta. Na ce."" Shikkenan Baba, in sha Allah zan sanar"

"da shi halin da ake ciki duk kuma yadda muka yi aki ji."" Ta ce."" To shikkenan, Allah Ya maganta."""

"To daddare ina d'aki a kwance misalin takwas da rabi ya shigo mini cikin tsananin b'acin rai. Na tashi zaune da sauri gabana na fad'uwa. Ya zauna samar kujerar madubi na ce."" Kai lafiya Kamalu."""

"""Mama barka da dare."" Da abinda ya fara kenan. Na amsa a takaice na ce."" Menene?"""

"Duk dauriyarsa sai da muryarsa ta yi rawa ya ce."" Mama ba zan iya ba, ba zan iya jurewa ba, zan tafi kano gobe domin kuwa Salim baya neman zaman lafiya da ni."""

"""Mai ya yi maka kuma?"" Na tambayeshi jikina sanyi kalau domin kuwa wani yanayi na shiga na tsananin tausayin yaron ba komai ne ya janyo masa hakan ba sai maraici da rashi domin kuwa duk abinda Salim yake yi yana yi ne domin ya ga a cikin rigar arziki su yake."

"""Salim tare da abokansa suke yi mini dariya har na ji daya daga cikinsu yana kirana da 'kolo, dayan kuma yana cewa"

"mini criminal."" Sai hawaye suka fara kasa tsare a kumatunansa....."

Chapter 29 Bata kai kalma 2k yanzu na cika she muku a wannan chapter din

*GARKUWAR MATA.*

*BINTA UMAR ABBALE*

"[6/3, 8:38 PM] matar mijinta: *Wannan littafin na kudi ne vip 1k akan telegram. Normal What'sapp group kuma #700 hanyar da za a biya kudin ita ce wannan...0542382124...Binta Umar gtbank ko kuma 7084653262. Binta Umar"

Opey bank. 'Yan nijar dala dari katin airtel za ku tura mini bayan kun kankare hoton. A tura da sheda ta wannan lambobin iya What'sapp kawai.*

*07084653262*

*08089965176*

*V-VIP AREWA PEN *

*81*

"Zuba masa ido na yi ina kallo a yayin da hawayen ke ta zarya a dakalin fuskarsa bai goge ba, ni ma kuma ban ce masa ya yi shiru ba sanin da na yi cewar kukan shine zai sassauta masa takaicin abinda aka yi masa. Lallai gagarimin abu ne ke sanya fitar hawaye a idon Kamalu tun yana yaronsa balle yanzu da shekarun samartaka suka fara kama shi dole an yi gwagwarmayar rayuwa a samu zuciya ta sake 'ke'kashewa."

"Idan an kira shi da 'kolo (almajiri) ai ba damuwa ba ne, ni na ji dad'i ma da ya zama 'kolon mahaddaci kuma marubucin al'kur'ani. Kalmar criminal din ce ta hargitsa dukkanin lissafina, Salim abin har ya kai haka. Abinda ya faru shekaru kusan shida zuwa bakwai yaro ya samu nutsuwa ya zama mutum shine yanzu za a tayar masa da hankali."

"Cikin jan ajiyar zuciya ya ce."" Mama Salim na b'akinciki da yadda Allah ya yi mini jama'a a area nan, sannan yana kishi sosai ya ga na bude massalaci manya mutane na bina sallah suna gaisawa da ni. Wannan na ji da kunnena yana"

"fad'in duk wanda ya bi b'arawo sallah shi ma bashi da maraba da 'barawo, kuma sannan bashi da sallah. Mama"

"yaushe wannan sunan zai goge a tarihin rayuwata"""

"Na ji kwalla ta ciko mini ido. Na daure ban yadda ta zuba ba, na ce."" To share hawayenka ka daina kuka ka ajiye abinda yake faruwa a matsayin cigaba, domin kuwa haka siddin ba zaka cimma wata nasara ba tare da kalubale ba. Ita hassadar ai itace matakin komai. Kada ma ka damu, kuma ina mai tabbatar maka da cewa watarana Salim zai bi ka salla, zai kuma nemi fatawa a wurinka, wannan ni ce na gaya maka, domin kuwa ina nan ina roka maka d'aukaka da shura ta fanninin addini anan gidan duniya, Kamalu idan Allah Ya yarda duniya da mutanan dake cikinta za su amfana da kai."""

"Hannu yasa ya goge hawayen dake zuba a kumatunsa. Na ce."" Ka kyale mini komai a hannuna, ka ji ko ka cigaba da hakuri, ni kaina a wannan ga'bar ba zan ha'kura ba dole a yi wani abu kai, amma kada ka nunawa Momi komai, ka bar abin a zuciyarka."""

"A sanyaye ya ce."" Shikkenan Mama, zan yi yadda ki ka ce din, amma ni ina so na koma can kano zan fi samu nutsuwa cigaba da gudanar da neman ilimina."""

"Na ce."" Idan har hakan shine alheri za ka koma Kamalu, ka cigaba da addu'a ka kuma bar maganar tsakanina da kai."" To a daran na nemi maigidan a waya duk da nasan ba sosai yake amsa waya da daddare ba amma yadda nake jin zuciyata ba zan iya bari sai gari ya waye ba. Wayar ta katse bai daga ba sai na yi masa text na cewa ina son magana dashi a duk lokacin da ya ga sakona."

Wajan goma da rabi kuwa ya kira ni da kansa. Na daga muka gaisa a nutse.

"Na ce."" Baba ina son magana da kai amma kada ka fahimce ni girman Allah da Annabi ka dubeta ta fuskar hankali da maslaha."""

"A nutse ya ce."" To ina jinki ai ni mai hankali ne ba mahaukaci ba, kada dai ki ce mini kin yi 'bari domin kwana biyun"

"nan mafarkai nake yi marasa kan gado, Ina ganin ma farkon watan nan za mu zo."""

"Na ce."" Ban yi 'bari ba, amma ka sani cewa ni da kai ba mu da ikon komai akan abinda Allah Ya zartar. Idan har kaddara ta gifta cikin ya samu matsala ba za ka d'auki kaddara ba kenan?"""

"Ya ce."" Zan d'auka mana, ai mafarkan da nake yi ne ya sanya ki ka ji na yi miki wannan maganar. Na tuba ga Allah duk yadda ya yi daidai ne."""

"Shiru na yi ina sauraransa har ya gama maganganunsa. Na ce dalili ne mai karfi ya sanya ni kiranka a daran nan,"

kuma ni kaina zan ji dadin zuwanka domin ka gyara abinda yake faruwa Kamalu ne da Salim Duk abinda yake

"faruwa na zayyane masa. Ya jima yana nanata maganar da mamaki mai yawa a tare dashi ya ce."" Yaushe Salim ya lalace haka, kuma abu ya faru tunda kuruciya saboda rashin hankali ka tara abokai kana gaya musu criminal?"" Ya sake maimaita kalmar tabbacin hakan ya bashi tsoro da mamaki."

"Na ce."" Kamalu ya ce zai koma kano da zama can wurin Hamusu."""

"Gyaran murya ya yi tare da cewa."" Wannan kuma abinda yake cikin ranki ne shekara da shekaru shine ki ka samu mafaka dalilin wannan matsalar. Na gaya miki Amina idan har Kamalu zamansa zai koma kano to Yusi ma zai bi shi. Nusaiba da Salim Adam amana ne a hannuna. Haka zalika tunda ina auranki yaranki ma amana ne a hannuna koda ubansu yana raye to balle kuma baya raye. Idan har kina ganin za ki yi iko da abinki ni ban iya ba sai na ce Allah Ya taimaka."""

"Na ce."" To yanzu ya kake so a yi? Kasan dai cigaba da zaman Kamalu a gidan Momi akwai matsala watarana za su iya yin abinda bai da ce ba."""

"""Babu abinda zai faru, ki kyaleni da yaran dukkaninsu tunda kin gaya mini kin gama aikinki."""

"Jiki babu karsashi na ce."" Shikkenan sai da safe."" Sai kawai na kashe wayar domin kuwa jikina yana ba ni kamar ba zai d'auki tsatstsauran mataki ba."

Da lamarin na kwana na kuma wayi gari dashi dalilin da sanya kenan na kasa barin abin iyakacinmu. Na kira anti Yagana na gaya mata halin da ake ciki. Sosai kuwa ranta ya 'baci ta dinga fad'a tana cewa babu lallai babu dole muddin da cin zarafi da cin mutuncin da kuma tozarci Kamalu dole ya bar gidan. Arziki ai ba hauka ba ne.

"Na ce."" Anti Yagana tun farko fa ni dama abinda na guda kenan, shiyasa da matar nan ta bukaci zaman Kamalu a wurinta na dinga gocewa. Karin abin kuma maigidan ya'ki ya fahimceni, wai muddin Kamalu zai bar gidan sai dai su tafi da Yusi wanda na tabbatar da cewar hakan matsala ce babba. Da ya zauna mun yi magana da fahimta tuntuni da tun farko wannan matsalar bata kunno kai ba. Abu na biyu kuma ga yanayin bayanin da Kamalu ya yi mini yadda na fahimta shine shi Salim yana adawa da yadda Allah ya d'aukaka Kamalu fiye dashi, ai nasan yaron yana da kirki tun kafin ya tafi karatu dawowarsa al'amura suka lalace kishi ne shi mai yasa Allah bai yi masa ba."""

"Ta ce."" Wannan kuma Ubangiji zai kalubalanta. Wace irin wahala da gwagwarmaya ce Kamalu bai sha ba. Yanzu"

"kuma Ubangiji Allah Ya d'aukaka darajarsa wannan duka ba dabararmu ba ce ikonsa ne, gaskiya a wannan ga'bar ni ma bana goyan bayan mijinki Amina Kamalu dole ya tafi ya bar musu gidansu idan sun ce ba haka ba sai ya dawo hannunki shine karshen magana."""

"Na ce."" Anti Yagana ni na fi so fa ya koma kanon ko ya dawo nan wurinku hankalina zai fi kwanciya gaskiya, domin ai"

"ko yana gidana ba a kashe matsalar ba tunda duk lokacin da ya fita zai iya yin karo da Salim da abokansa kin ga matsalar ai bata mutu ba."""

"""To ni da kaina zan kira Yallabai din a waya na bashi shawara yadda za a yi. Ta fad'a tana nishin 'bacin rai."""

"Jin haka ya sanya na ce."" Kada ki kira shi yanzu anti Yagana mu bari ya zo mu ga hukuncin da zai yanke idan babu adalci sai ki yi masa magana."""

"Ta ce."" Shikkenan haka za a yi in sha Allah, na manta ma ban gaya miki ba shekaran jiya amaryar Babandi matar da ya aura ta uku ta haihu."" A takaice na ce.'' A yi masa barka Allah Ya raya, domin ni yanzu ko lambarsa ma ba ni da ita yadda maigidan ya tsaneshi haka ya tsani mutuwarsa shiyasa na goge lambarsa daga wayata a gabad'aya duk domin a zauna lafiya."

**

Bayan sati biyu al'amura suna cigaba da tafiya da dad'i babu dad'i. Har zuwa lokacin Salim bai kyale Kamalu ba. Kusan kullum da b'acin rai yake shigo mini duk da yana ko'karin daurewa amma ina fahimta. Ha'kurina yana daf da k'arewa domin tun ranar da na kira maigidan a waya na gaya masa abinda yake faruwa bai sake nema na da maganarba duk kuwa da cewa kusan kullum sai mun yi bidiyon call. Ni ma ban sake tayar da maganar ba na bari ne kamar yadda ya ce mu jira zuwansa. Amma koyaushe idan na dubi Kamalu na ga yadda ya rage walwala da kuzari zuciyata takan yi zafi. Ina dalili haka kawai saboda gudun b'acin ran wani a 'kuntata zuciyar yaro. Babu lallai fa babu dole muddin ba zai d'auki mataki ba wallahi sai Kamalu ya tafi ya bar garin da gidan gabad'aya.

Gudun aure littafin kudi ne kada ki karanta ba tare da kin biya ni hakkina ba.

Ranar litinin da yamma suka sauka shi da Hauwa. Baiwar Allah ta kuma samo wani cikin domin yanayinta kadai ya

"tabbatar mini da cewa laulayi take yi ta yi mugun haske dama idan tana da ciki d'ashewa take yi. Macace mai kwainika Minal na da wata goma sha takwas. Allah Ya sa tana da san girma, tana yawo da kafafunta da yake abincin gwangwani take ci a can ta zama rusheshiya kataf-kataf haka take yawo uban yana tsokanarta da 'yar sukuta. ko ya kira ta da giwa wai na washeta har ta fi su Hassana girma jiki tunda su jikin irin nasa ne. Kwana biyu da zuwansu na fahimci rashin jituwa a tsakaninsu. Kamar ma basa magana da juna. Na yi dai shiru ina kallon ikon Allah. Ita yini ma take yi a d'aki sai yamma take fitowa falo shi kuma har ya yi kwana biyunsa a wajena bai ce mini komai ba."

Na cika da mamaki sosai. Lallai ma wannan mutumin wato maganar tabi shanun sarki kenan Salim ya yi daidai babu kuskure akan abinda yake yi.

Ba zan lamunta ba domin kuwa har yanzu a cikin matsalar ake sai abinda ma ya yi gaba. Kamalu bai rasa madogara ba hakama Yusi idan har ba zai gyara abinda yake faruwa ba to na yarda ya ba ni yarana su kuma can hannun Babansu Hamusu.

"Cikin wannan nazarin Hauwa ta shigo d'akina ta same ni. Ta zauna gefan gado tana fad'in."" Ko jikin ne?"" Na tashi zaune Ina fad'in."" A, a ni kam ai na warware na bar miki Hauwa."""

"Kwafa ta yi tare da cewa."" Ban ji dad'in shigar cikin nan ba wallahi.''"

"Na dubeta a tsanake tare da cewa."" Mai yasa Hauwa ki godewa Allah da fatan samun masu albarka."""

"""Humm!"" abinda ta ce kenan kafin ta ce."" Ban shigo domin na tunzuraki ko tayar da husuma ba. Idan kin lura da yanayin yadda muka zo da ni da maigidan babu dadi don wallahi mugun haushinsa nake ji fad'a muka casa tun a can."""

"Na ce."" Menene kuma ya kamata ki manta da matsalar matar nan Hauwa, ki yi ta kanki haihuwa ta uku za ki yi da mutumin nan duk abinda zai yi ya je ya yi haka ya ga zai iya."""

"""Wallahi Amina ko kaffara ba zan yi ba matar nan ba haka ta bar mutumin nan ba."""

"""Mai yasa ki ka ce haka Hauwa, zato zunubi ne fa koda ya kasance gaskiya ne?"""

"""Amina maganar gaskiya zan gaya miki na gaji da zaman nan da muke yi na rashin 'yanci da kaskanci wallahi tallahi ba zan jiya jure ba, wannan shine dalilin ma da ya sanya ki ka ji na ce ina b'akinciki da takaicin samuwar wannan cikin na jikina, in banda ina gudun sa'bawa Allah wallahi da sai na zubar da shi......."

*Rikicin gidan Alh Tajo sai dai na ce Allah ya yayyafawa abin ruwan sanyi bari mu ya ya zata kaya. *

*GARKUWAR MATA.*

*BINTA UMAR ABBALE*

"[6/3, 8:38 PM] matar mijinta: *Wannan littafin na kudi ne vip 1k akan telegram. Normal What'sapp group kuma #700 hanyar da za a biya kudin ita ce wannan...0542382124...Binta Umar gtbank ko kuma 7084653262. Binta Umar"

Opey bank. 'Yan nijar dala dari katin airtel za ku tura mini bayan kun kankare hoton. A tura da sheda ta wannan lambobin iya What'sapp kawai.*

*07084653262*

*08089965176*

*V-VIP AREWA PEN *

*83*

"Na ce."" Ai ba ta yi lefi ba gaskiya ta fad'a domin shine zama na amana. Kuma wallahi a yanzu ni Amina Hauwa ta fiye mini kai sau dubu tunda ka nuna mini zahirinka na gani, ni duk wanda za a had'a kai dashi a k'yamaci abina, ba na daukarsa a matsayin masoyi babban ma'kiyi nake kallonsa."""

"Da wani irin yanayi a tare da shi ya furta."" Idan na fahimce ki kenan kina kallona a matsayin ma'kiyinki wanda ya"

"za'bi Maryam da 'ya'yanta ko Amina."""

"Na ce."" K'warai kuwa wallahi tallahi ba ka cikin jerin masoyana tunda har ka iya yadda da cewa Kamalu zai aikata wannan mummunan lamarin. Ba na yi maka kallon masoyi."""

"Ya jima yana kallona kafin ya gyad'a kansa ya nufo ni, na kuwa zabura domin kallon dodo nake yi masa na ce."" Kada ka zo inda nake na rantse da Allah zan illataka."""

"Bai daina tafiya ba har sai da ya cimmani zai ri'ke hannuna na fizge da sauri na wancakal da nasa hannun cikin zafin nama na yi wajan madubina na zari wata doguwar kwalba ta turare na ri'ke a hannuna. Ya sake nufo ni yana fad'in."" To illatani kin ji, na ce ki illatani tunda kin 'ki tsayawa mu fahimci juna. Da k'araji na ce."" Har abada na sake aminta da maganar munafiki."""

"Ya 'bata fuska ainun yana fad'in."" Kada kuma ki wuce gona da iri, kin naushe ni a ma'karfafata d'azu na kyale ki yanzu kuma kina kira na da munafiki ranki zai b'aci fa ba ni son rashin hankali."""

"Na ce."" Ya 'baci ma ai ba tsoro nake yi ba, menene karshen hukuncin shine saki ko to ka sake ni kaga yadda ake liyafa ai ni kassara mini rayuwata ka yi zama dakai bai amfanar da ni komai ba."""

"Ya kuwa 'kadu da wannan furucin ya ce."" Har yaran da muka haifa ba su da amfani?"" Na ce."" E, ai ba nawa ba ne tunda ka d'aukesu ka bawa bushshiyar matarka nata ne taje na bar mata."""

Ya dinga kallona da mamaki mai yawa kafin ya sake tunkaro ni a karo na biyu na daga abinda yake hannuna zan buga masa ya yi saurin ri'ke hannun tare da k'wacewa. Muka yi cirko cirko a tsaye shima nishin yake yi kamar yadda nake yi kamar wanda ya yi tsere. Mun jima haka ya ri'ke ni katamau na ja tsaki tare da yun'kurin bangaje shi ya riko kafadata jikinsa duk ya yi la'asar. Na ce ka cika ni na gaya maka

na rantse da girman Allah da Annabi sai yaran nan sun bar hannunka tunda ka gaza ri'ke su tsakani da Allah ko da hakan zai yi sanadiyar rabuwarmu

"""Ba ki da hankali har yanzu ko Amina?"""

"Na ce."" E, ba ni dashi tunda kai din

Please Login or Register in order to submit comment