You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya sanya ni zubewa gabanta na furta."" Baba Tabawa Momi ce ta rasu fa?"""

"""Innalillahi wa'ina ilaihi raji'un! Kalmar da ta fara furtawa kenan kafin ta tallafe ha'barta cikin alhini da tace."" Baiwar Allah nan ashe ciwo ba na tashi ba ne."" Hanci na ja tare da furta "" Baba tunda ranar da muka je dubata farkon ciwon Awallahi hankalina ya kasa kwanciya haka kawai daga ta fad'o mini sai gabana ya yanke ya fad'i wallahi ciwon nan nata ya tsaya mini a rai na sosai."""

"Ta girgiza kai cike da kasala ta ce."" To a Amina abin ne da ban tsoro ga yanayin yadda hallittunta suka jirkice ba ke kad'ai ba ni kaina da ita nake kwana da ita nake tashi a rana wallahi Ubangiji Allah Ya gafarta mata ya yafe mata, halinta nagari ya bita don arzikin Annabi."""

"Da ""Amin na amsa tare da cigaba da nanata Innalillahi wa'ina ilaihi raji'un domin samun nutsuwa da k'adaita Allah da kuma tabbatar da cewa gare shi muke kuma gare shi za mu koma."

Wannan littafin na kudi kada ki karanta ba tare da kin biya ni hakkina ba.

Mun jima muna alhini tare da tariyo kyawawan halinta ( mu kula anan kun san dai a al'ada koda mutum ya ninke

(boye ) abinda ya shuka na sharri da rashin kyautawa a duniya babu yadda za a yi a ce rud'ani da razani na mutuwa ya bari mutane su iya furtawa. Ku sani ko kafiri ne ya mutu a matsayinka na musulmi kaga gawarsa sai ka shiga hankalinka lokacin ne za ka tuna lallai fa ni ma akwai wannan ranar za ta zo mini ba tare da na yi shiri ba. Zan mutu za kuma a haka rami a binne ni. Amma ita mutuwa ai mai tonan asiri ce idan an shuka kairan za ta nuna idan sharrin ma aka shuka duka zata nuna. Mu bi a sannu a hankali a daina yanke hukunci don Allah kuma a fahimci sa'kon da ake so a isar a wannan littafin ta kowace siga zai fita yadda kuke so)

"Sahura na kira a waya na gaya mata. Itama dai kamar yadda yake faruwa a al'ada a kidema take fad'in."" Da gaske ta"

"rasu Amina?"""

"Na ce."" An ta'ba wasa da mutuwa dama, wallahi ta rasu da gaske. "" Ta dinga nanata kiran sunan Allah tana istigifari da fad'in Allah ka yafe mana."

"Na ce."" Mutuwar matar nan ta dake ni wallahi"

Sahura ba ki ji yadda nake ji ba a raina na tsorata da wannan duniyar gabad'ayanta. Ita kanta Hauwa tana can cike

"da gigita domin kasa magana ta yi da na kira ta a waya na sanar da ita sai kashe wayata na yi domin bakinta ya mutu murus ta kasa magana."""

"""Ai Amina mutuwa wa'azi ci ga duk wanda Allah Ya sa zai hankalta, duk d'aukaka da sharafin mutum a duniya ba iya"

"tsallaketa. Mu 'yan adam ai muna da mantuwa shiyasa muke ganin kamar ba za ta zo kanmu ba, a yadda dai kike ba ni labarin irin abinda Hauwa take yi wa matar nan wallahi ita ya fi kamata mutuwar ta dake ta, ta kuma ji tsoron Allah har ta mutu bata nemi afuwarta ba Allah baya yafe hakkin wani akan wani har sai wanda aka zalinta ya ce ya ya yafe, aikin banza ai kishi ba hauka ba ne, ni kaina Hauwa ta ba ni mamaki kuma na raina wayo da iliminta domin jalihi ne kadai ba zai fahimci cewa ba hassada take yi wa baiwar Allah nan ba, misali dani daku duka hasashe muke akanta domin ba mu da tabbas a duniya muke ji ana fad'in mashirika ce amma ai ba mu ta'ba ganinta tana yi ba. Idan ma tana yi din wannan ita da mahallicinta ne, ni yanzu tsoron duniyar nan nake yi wallahi Amina kowa ya kashe wutar gabansa."""

Shiru na yi ina ta auna maganganun da take yi. Ni kaina na kan zauna na yi ta nazari akan mai yasa Hauwa ta

"zafafawa matar nan da yawa. Kishi ne ko hassada mai yasa komai sai ta mayar da shi rigima da sa'insa lefi ni aka yi wa amma ban yi irin abubuwan da take yi ba, tabbas dole a dora ayar tambaya a kanta koda kuwa ba hakan ba ne a zuciyarta ni kaina ba zan fita daga zargi ba tunda yan uwanta da yawa suna ganin cutar da ita muke yi ta hanyar hade mata kai da yi mata tawaye tare da fito da kishi muraran. Idan zan kwana ina rantsuwa da Allah kan cewa ba ni yi mata hassada da b'akinciki babu wanda zai yarda."

Haka dai muka yi sallama cikin yanayi na damuwa da tashin hankali.

Baban Saude ya kira ni yana tabbatar mini da cewa suna kan hanya suna da d'an yawa.

Na kira Babanmu ya ce mini shi ma sun taso su uku har da Ummansu Hadiza.

Wanka na yi na kintsa na fita falo cikin hijabi har kasa na samu Baba Tabawa itama cikin hijabin da carbi ta kammala abin kari da d'an dama. Da asuba na ce ta yi abinci da yawa saboda bakin da suke tafe. Muka gaisa tare da sake yi wa juna gaisuwa. Masa'udu tare da

Sale suka shigo da akwati kafin shigowar Hajjan Kamalu ne ya fara shigowa tukkuna suka shigo Hajja da Gwaggo da Hamusu a biye a bayansu.

"Bakin kofar na isa da sauri ina yi musu barka da zuwa. Na kar'bi jakar dake hannun Hajja ina fad'in."" Gwaggo sannunku da hanya Hajja kun yi sauri sosai fa kamar a hanya kuka kwana."""

"Suka zauna a kujera tana fad'in."" Kina fad'in rasuwar na ce Kamalu ya sanar da Gwaggo maza ta shiryo mu taho kuma dai Garba ya k'ure gudu sosai shiyasa Allah Ya kawo mu."""

Na nutsu sosai muka gaisa a tsanake Hamusu dake can saman kujera mai cin mutum d'aya ya gaishe ni na amsa tare da tambayar iyalinsa da yaronshi Arif da bai wuce shekara uku ba ya ce mini duk suna lafiya. Baba Tabawa bayan sun gaisa da yi wa juna ta'aziyya na ce ta kawo musu abinci domin bayan karin kummalon da ta yi da yawa har ta kammala na rana

Na dubi Kamalu dake gefe a tsaye jikin labule ya sake girma da fad'i sosai suffa ta mazantaka ta bayyana a tattare dashi har da gemu ya fara ajiyewa. Yatsansa makale da carbi mai lamba yana ta rarraba ido a kanmu yanayinsa gabad'aya kamar mai nazarin wani abu damuwa da tashin hankali sun gama bayyana a tattare dashi. Ganin mun had'a ido dashi ya sanya ni janye nawa idon. Ina jin wani abu na taso mini da tashin hankali. Kawai zuciyata ta fara raya mini cewa ni ma haka zan fadi na mutu yarana su sake kasancewa cikin maraici.

"Ya gurfana a gabana cikin kula da ladabi ya furta.""Mama ina kwana ya muka ji da hakurin wannan rashi."" Na amsa da ""Alhamdulillahi mun gode Allah."""

"Ya furta."" Allah Ya jikan Momi Ya gafarta mata."" Gabad'aya muka amsa a falon."

"Na dubi Hajja tare da fad'in."" Yusi bai samu zuwa ba ne "

*GARKUWAR MATA.*

*BINTA UMAR ABBALE*

https://chat.whatsapp.com/E8JgnaAUG13CRwJbYeXImE?mode=gi_t

*TALLAH!*

*DA MAGANI A GONAR YARO!!*

*08089965176*

*07084653262*

"*Dayawa akwai matan da suke da matsala ta lalacewar nono yamushewa da kuma fad'uwarsa. Wasu ma 'yan mata ne basu kai ga matakin aure da shayarwa ba amma sai su samu matsalar faduwar nono. To gaskiya akwai magani sai dai kawai idan ba a yi dace ba. Wasu zasuyi ta faman kashe kudi amma buk'ata bata biya ba, wasu kuma zasuyi ta fargaba kada su je garin neman gira a rasa Ido, ma'ana su sayi abinda zai cutar dasu da kudinsu. Kuma yanzu dai tsakani da Allah rijalu sun riga sun gama nuna abinda suka fi karkata a kansa a jikin 'ya mace kirji da kuma baya. Wasu Allah ya hallice su dashi har ya yi musu yawa, wasu kuwa basu dashi kuma mai saurin zubewa ne. To mu dai duk wanda ya san maganinmu ya san ingantacce ne, kuma Yana aiki kwarai da gaske wurin dawo da daraja da martabar nono da izinin Ubangiji. Sahihin magani ne da ya samu sheda da lambar yabo, kuma Islamic ne da akayi masa hadi mai inganci domin gyara jikin mace ba ma iyakacin nono kawai ba. Babu nadama haka zalika babu dana sani da asarar dukiya wurin sayan maganinmu. In sha Allah matsalar ki zata gushe idan kin jarraba amfani dashi. Ba mu tsaya ina nan ba, muna da na gyaran hips sahihi dana k'iba idan kina fama da matsalar rama. Haka zalika muna dana tumbi, da kuma maganin sanyi mai mugun kyawun da yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye wanda zaku hadu da maigidanki kuyi amfani tare. Akwai ingantattun supplement wad'anda basu da illa balle su cutar da GARKUWAR jiki. Sai dai su gyara su kuma tayar da komad'a ina nufin inda ya samu nakasu a jikinki. Muna sayar da sabulan gyaran jiki dilka da man gyaran gashi, muna kuma bayar da sari a fad'in najeria da nijar muna tura kayanmu kowane gari da ikon Allah.*"

*Muna garin kano duk inda kake za mu aika maka da kayanmu. Domin neman karin bayani sai a yi mana magana ta Whasap ga lambobin da za a same mu a kai.*

*07084653262 ko*

*08089965176*

*SIYAN NAGARI!!!!!!*

*A JARRABA A SAMU BIYAN BUKATA DA YARDAR ALLAH*

*PAID BOOK 2K COMPLETE ON TALGRAM WHAT'S APP GRUOP KUMA 1K VIA 0542382124...BINTA UMAR GTBANK*

*07084653262*

"A tsanake ta ce."" A a ai tare duk muke tafe tun a waje ya ce Garba ya ajiye shi yana can tare da Adamu."""

"Na gyada kaina ba tare da na sake cewa komai ba. Baba Tabawa ta kawo tire uku masu girma cike da abinci na taimaka mata wurin zubawa kowa Hajja ta ce ."" Hajiya Saratu tana tafe in sha Allahu mun yi waya da Alhaji Sa'idu shi da d'an uwansa Alhaji Dahiru sun ce za su yi kokarin samun jana'iza."" 'Yan uwan mahaifin maigidan ne wanda a yanzu su kadai ne suka rage musu a family din. Na gyada kaina a sanyaye na ce."" Allah Ya kawo su lafiya."

Kai na jima ban shiga tashin hankali da nadamar rayuwa ba sai a rasuwar baiwar Allah nan. Tunda gawar ta iso

gabad'aya estate din namu ya cika da motoci jama'a daga kowace kusurwa abokanan maigidan dama wasu daga ciki abokan tsohon mijinta ne. Cikin gidanta cike da 'yan uwanta da zuriarsu tare da abokanan arziki da yaranta masu yi mata hidima na shagunanta. Ana ta koke koke masu dauriyar daga ciki kad'ane. Babbar yarinyata Nusaiba sumanta biyu har yanzu ba ta gane wanda yake kanta ba. Nabila kuma tana ta iskokai a wani d'aki da 'yan uwansu sun kulle- kulle kofa don kada ta fito daga inda muke a zaune muna jin ihunta. Cikin masu yi wa Momi wankan gawa har da Baba Tabawa lallai na yaba k'warai da aniya wurin jajuecewarta da dauriyarta koda yake yadda take ba ni labari a gaban idonta mahaifiyarta ta rasu kuma itace ta wanke ta. Wannan ya kara tabbatar mini da cewa Baba Tabawa tana daya daga cikin salihan matan da Ubangiji ya ce lallai yana jin kunyarsu a gidan duniya da lahira dalilin rashin haihuwa.

Ban tashi tabbatar da cewa d'an adam ba a bakin komai yake ba sai da aka gama had'a Maryam tsaf cikin likkafani a mike cikin makara ta zama 'yar mitsitsiya a tsakiyar makarar tsabar ciwo ya cinyata

ana ta lallabata sunanta gabad'aya ya shafe daga jiya zuwa yau din wasu na kiran ta da gawa wasu na kiranta da marigayiya. Yaranta da mijinta tare da yan uwanta sun kewaye makarar yayin da masu aikinta mata da muke tare da su a gidan suke gefe sun cure kansu wuri d'aya sai shar'bar kuka suke yi. Adamu dake tare da Yusi ya can gefe daya

"kuka yake yi sosai yana fad'in."" Momi kin mutu da wa ki ka bar mu a duniya, ba mu da uwa ba mu da uba. Innalillahi"

wa'ina ilaihi raji'un!.

Sambatun da yaron yake yi ya kidima ni sosai ya kuma ba ni tausayi ainun na yi saurin d'auke kaina daga kansu Yusi yana ta rirrike shi sun kasa zuwa gaban gawar ma gabad'aya.

"Hajja da Gwaggo suka nufi bakin makarar. Na yi na yi na ja kafata domin bin bayansu na kasa don wata irin juwa da Hajijiya nake ji idona na ganinsu garagara,"

Bayan haka kuma gabad'aya a tsarge nake ga yanayin kallon da na ga wata mata da na ji suna kiranta da suna Yabi take yi mini irin na wulakanci da neman fitina.

Hawaye masu d'umi suka silalo kumatuna wanda ya yi daidai da lokacin da na yi hu'bbasa wurin sarrafa 'kafafuna amma suka doje ban san yadda aka yi ba kawai na ji ni a k'asa na zube a lokacin ne kuma naga kamar gilmawar wani abu daga sannan ban sake gane komai ba sai dana farka tukkuna na tabbatar da cewar suma na yi lokacin har an kaita makwancinta an dawo. Anti Yagana sun iso tare da Inna Uwani. Ban yi mamakin ganin yanayinsu ba domin akwai d'imuwa da tashin hankali na rasuwar da aka kwantsama. Ko baka da ji'bi da mutum fad'in Annabi ne mutuwarsa dole ta nasheka balle wannan matar da alherinta kowa yake gani.

"Hajja ta shigo d'akin da muke tana fad'in."" To alhamdulillahi tunda ta tashi da ji da ganinta da kuma lafiya mun gode Allah Yagana taimaka mata sai mu koma can gidan nasu mu yi namu zaman domin nan din zaman zai zame mana fitina."

"Gwaggo da fitowarta daga bandaki kenan d'aure da alwala ta ce."" Ni ma shawarar da na yanke kenan hakan zai fi alheri."""

"Anti Yagana ta dube ni a d'an sanyaye kafin ta ce."" Sannu ba dai kya jin komai a jikinki ko?"" Kaina na gyad'a mata a nutse na ce."" Ashe kun zo?"""

"Ta ce."" Mun zo mun tarar an d'auki gawar gidan a kacame ana ta hayaniya ke kuma gaki a sheme sai da likitanku ta zo ta dubaki fa dogon suma ki ka yi."""

"Shiru na yi ina nazarin maganarta kafin na ce."" Anti Yagana mai ya faru ne?"""

Ta'be bakinta ta yi ba ce mini komai ba. Na daga kaina na kalli Hajja dake tsaye jikin bango rumgume da hannunta a k'irji nan take na karanci damuwa da b'acin rai a saman fuskata.

"Ban sake wata magana ba na tashi zaune hijabi na da yake gefe anti Yagana ta miko mini na zura a jikina tana taimaka mini na yun'kura na tashi ta ri'ke ni. Na ce."" Ki cika ni zan iya tafiya da kafafuna. Inna Uwani ta ce."" Da dai kin bari ta rike ki jikin naki ai har yanzu bai gama daidaita ba."

Hajja da Gwaggo suka yi gaba.

"Wani irin kallo dangin marigayiyar suke mini na tsana da kyama. Anti Yagana ta juyar da kanta ba ta ce komai ba. Ni ma ban ce musu komai ba na ji ita wannan matar mai suna Yabi tana fad'in."" Kun kai ta kasa kun ji dad'i, sai ku jirayi hakki domin wallahi ba mu yafe muku ba, duk abinda za ki nuna a banza a wofi Maryam dai karshenta ya yi kyau ku kam in sha Allahu mutuwar wulakanci za ku yi."""

Maganganunta ne suka dinga yi mini amsa kuwawa! a kunne gabana ya dinga bugawa da karfi da karfi. Wannan babban kalubalen ban shirya tararsa ba a yanzu domin ba ni da hujjar da zan kare kaina Allah shine shahidi.

Muka fita tun daga haraba cike da jama'a har zuwa waje mutane cike cikin manya manyan rumfunan da aka kafa. Kafafuna suka dinga hard'ewa gabad'aya sai na tsargu domin maganganun da matar nan ta yi sun sake dakusar da duk wani karsashi da kwarin gwiwata. Shin wane irin kallo jama'a suke yi mini a yanzu dana fito cikinsu. Cikin dubara na janyo saman hijabina na rufe fuskata dashi dama rike nake a hannun anti Yagana. Ina jin sanda Hajja ta tsaya suna gaisawa da ire-iren abokanan Yallabai din na ce da anti Yagana ta yi sauri mu wuce domin ba ni da wani k'umaji da nutsuwar da zan iya tsayuwa a gaban jama'a domin kar'bar ta'azziya. Muka yi gaba muka bar su ita da Gwaggo suna gaisawa.

"K'uryar d'akina anti Yagana ta dangane da ni na zauna kan gado kamar wata sabuwar amarya na yaye hijabin da ya katange fuskata. Muka had'a Ido nan take na rushe da kuka na ri'ke hannunta katamau! Jikina na kyarma na furta."" Anti Yagana Hajiya Maryam ta mutu sanadiyar lalure-laluren da suka yi mata hijabi, ina tsoron kada 'yan uwanta da jama'a su jinginta rasuwarta da ni da Hauwa, ai kin ji abinda daya daga cikin 'yan uwanta take fad'a ko?"""

""" 'Karamin tsaki ta yi kafin ta ce.""Amina duk wanda zai alak'anta rasuwar matar nan daku to dama can ba masoyinta"

"ba ne. Su kansu 'yan uwan nata da suke ko'karin tashin husuma ba kaunarta suke yi ba tunda har suke jingina rasuwarta da wani abu daban. Kishi halak ne kuma duk gidan da aka had'a mace fiye da biyu ana samun irin wad'annan matsaltsalun. A ganina wannan ba wani abun damuwa ba ne, rigima ce suke nema kuma in sha Allah rabbi har a share makoki ba za mu tanka musu ba. Ni gidan ma ba zan sake shiga ba tunda na lura duk yawansu babu mai dattako a cikinsu. Rashi kam ba su kadai suka yi ba mutane da yawa ne domin Hajiya Maryam bango ce"

majingina kuma uwar marayu har ma da masu uban. Don haka iyakacin k'aunar da za su nuna mata su bita da

"addu'a tare da rungumar abinda ta bari shine kawai sakamakon da za su yi mata bayan rayuwarta. Don haka ki samu nutsuwa ki kuma daina tunanin kina da hannu lokacinta ne kawai ya yi kuma babu wanda ya isa ya tsalle rana da sa'in komawarsa ga Allah."""

Maganganun anti Yagana sun d'an sanya ni mini nutsuwa kad'an amma har yanzu zuciyata ba ta daina yin tsalle

akan abinda na ji yana fitowa daga bakin 'yar uwar marigayiyar ba.

"Babanmu suka iso tare da baba Sule da Ummansu Hadiza kamar yadda ya fad'a. Baban Saude ne har yanzu bai shigo inda nake ba, anti Yagana kuma ta gaya mini tare suke da Babansu Fadila har da Baba Madu wanda ya kasance babban yayansu Mamanmu, mahaifin Babandi."

Kada ki karanta mini littafi ba tare da kin biya ni hakkina ba.

Sai wajan biyar saura tukkuna suka shigo da d'an yawansu duk muna zaune a babban falo. Maigidan tare da

iyayenshi biyu 'yan uwan mahaifinsa da kuma Baban Saude Baba Madu da Babansu Fadila. Falon ya cika da sabuwar gaisuwa tare da yi wa juna ta'aziya. Ta mussaman suka yi mini gaisuwar na amsa yayin da nake jin cikowar ruwan hawaye idona. Ina jin Hajja tana tambayar Alhaji Sa'idu Hajiya saratu ya ce tana can gidan mai rasuwar tunda koda suka sauka nan ta shiga ba ta fito ba kuma har yanzu. Suna ta tattauna hirar marigayiyar yayin da maigidan ke sake basu labarin irin wahalar da ta sha na jinyya farkon zuwansu asibitin a yayin da aka dora ta akan magani an ga sauyi sosai yanayin yadda yake magana da alhini shi yake nuna mutuwar ta dake shi kwarai da gaske kwarmin idonsa ya zurma fatar lebanshi ta bushe kamar wanda ya yi azimin shekara bai sha ruwa ba. Irin wannan yanayin ya shiga a lokacin rasuwar tsohon mijinta Alhaji Amadu da kyar ya dinga cin abinci. Yanzu ma ba na raba daya da biyu rabonsa da abinci tun da aka yi rasuwar kwana da yini kenan.

Gabad'aya sun jajanta sosai kuma kafin tafiyarsu sai da Baban Saude ya jagorancemu gabad'aya muka yi mata doguwar addu'a wadda take d'auke da surorin da ake karantawa mamaci. Yamma likis suka yi mana sallama gabad'ayansu har da Hamusu da Babanmu domin cewa ya yi shi ma ba zai zauna ba tafiya za su yi tunda sun yi abinda ya kawo su. Shi kansa maigidan ya so su kwana ko daya ne amma gabad'aya suka ki har da kawunan nasa. Hajiya saratu ce kawai ta zauna ta ce sai an yi sadakar ukku tukkuna.

Yallabai din ya bada umarnin mayar dasu Babanmu gida. su Baban Saude kuma dama a motarsa suke tafe. Sai bayan sun tafi tukkuna Hajja ta dinga fad'a wai mai yasa anti Yagana ba ta jagoranci Ummansu Hadiza zuwa gidan mai rasuwar ba.

Anti Yagana ta ce mata mantawa ta yi shiyasa ni kuma nasan ba haka ba ne ita da kanta ta gaya mini k'afarta ba zata sake taka gidan ba. Gaisuwar da ta yi wa maigidan ma ta isa ba sai ta je ta yi wa 'yan uwanta ba tunda dukkaninsu taron tsintsinya ba share ne.

Sai bayan magariba Hajiya Saratu ta shigo. Ina d'aki lokacin na idar da sallah ban ka ga tashi daga kan daddauma ba ta shigo.

"Na saki fuskata sosai Ina fad'in."" Mai sunan Mamana ina yini?"""

"Ta zauna gefan gadona a nutse tana fad'in."" Lafiya lau Yayata kuma diyata."""

"Na yi murmushi a hankali na ce."" Ai tun d'azu aka ce kina can gidan marigiyar ina nan ina ta zuba idon ganin Mamana"""

"Ta dafa kafadata tana fad'in."" Ga ni na shigo ai Amina ya muka ji da hakurin Maryam lokaci ya yi Ubangiji Allah Ya gafarta."""

"Na amsa da ""Amin Ya Allah."" Cikin wata iriyar murya."

"D'akin ya d'an yi shiru wanda ya yi daidai da lokacin da anti Yagana ta fito daga bandaki daure da alwala. Ta saki fuska tana fad'in."" Hajiya kin shigo kenan?"""

"Ta ce."" E wallahi Yagana ya gida ya yaran, ya muka ji da hakuri?"""

"Anti Yagana ta ce."" Ha'kuri da godiya Hajiya Allah dai ya jikinta da rahama."" Da Amin ta amsa yayin da take sake dora hannunta a kafad'ata."

Anti Yagana ta d'auki daddauma da hijabi ta koma can gefe domin gabatar da sallar magriba.

"Ta ce."" Ai ni ban fito ba daga gidan ba sai da na gabatar da sallata tukkun."" Na yi murmushi kad'an ban ce komai ba. Sai ta ce."" Amina akwai maganganun da nake so mu tattauna dake idan babu damuwa."""

"Cikin nutsuwa na ce."" Babu damuwa Hajiya Ina sauraranki."""

"Ta sauke ajiyar zuciya a tsanake ta ce."" Duk abubuwan da suke faruwa a zamantakewar gidan nan ina da labari. Da"

"har Ina cewa tunda matsalar ta'ki ta'ki cinyewa zan wanko kafata takasan na zo naji komai daga gare ki nasan ke ba za ki yi mini karya ba, ba kuma za ki goyu da bayan mijinki ko ki goyu da bayan Hauwa ba, idan har kema kina da lefi za ki gaya mini gaskiya sanin da na yi miki tun farkon fari."

Ta nisa kafin ta cigaba da cewa. Sai gashi kuma

"rasuwar

Please Login or Register in order to submit comment