You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Zuciyata ta gama aminta da hasashen da nake yi akan cewa ya samu abinda yake so a wurina shiyasa ya rage ba ni kulawar da farko yake ba ni."

Shi ma babu sakewa a maganarsa yake cewa da ni na zo na same shi a samansa. Ban ce masa komai ba na kashe

"wayar na kai minti goma kafin na tashi da kyar na sanya hijabi na fito. Suna zaune suna kallo har da Yusi na dan saki fuskata. Hajjan ta dube ni tana tambayata bacci na yi ne, sai na bata amsa da cewa ""E"" kawai, ita kuwa inna Uwani a lalace ta dube ni kafin ta kawar da kanta."

Na d'auke kaina ni ma ban tanka mata ba na wuce zuwa saman maigidan.

Na same shi a zaune Yana aiki da computer ban ce komai ba na zauna nesa dashi. Shi ma bai dago ba har sai da ya gama abinda yake tukkuna ya dube ni muka had'a ido. Babu sakin fuska ya fara tuhumata akan abinda ya gani a tare da ni wanda ya zama sabo a wurinsa. Tuhumata yake yi akan har raini ya fara shiga tsakaninmu.

"Na dube shi zuciya na zafi na furta."" Me nake yi maka na raini, sannan kuma wane canji ka gani a tare da ni da zaka tuhume ni akan hakan? Ni na gaji rayuwarta ta baya tafi mini dadi wallahi."""

"Ya zuba mini idonsa Yana kallo kafin daga bisani ya taso ya zo ya zauna kusa dani ya ce."" Ni na kasa gane inda kika nufa a cikin kwanakin nan Amina tunda su Hajja suka zo ki ka canza mini ba kya ba ni kulawa babu tarairaya gaisuwa ma sai kin ga dama. Yau kwana takawas rabon dana had'a shimfida dake menene matsalar ki ne?"""

"Kawar da kaina na yi ban tanka masa ba. Ya sanya hannu ya juyo da fuskata muna kallon juna ya furta."" Me na yi miki umm! ki gaya mini sai mu samu maslaha ba na son fushin nan naki my love...."

*GARKUWAR MATA.*

*BINTA UMAR ABBALE*

"[6/3, 8:38 PM] matar mijinta: *Wannan littafin na kudi ne vip 1k akan telegram. Normal What'sapp group kuma #700 hanyar da za a biya kudin ita ce wannan...0542382124...Binta Umar gtbank ko kuma 7084653262. Binta Umar"

Opey bank. 'Yan nijar dala dari katin airtel za ku tura mini bayan kun kankare hoton. A tura da sheda ta wannan lambobin iya What'sapp kawai.*

*07084653262*

*08089965176*

*V-VIP AREWA PEN *

*TALLAH*



*DA MAGANI A GONAR YARO!!*

*08089965176*

*07084653262*

"*Dayawa akwai matan da suke da matsala ta lalacewar nono yamushewa da kuma fad'uwarsa. Wasu ma 'yan mata ne basu kai ga matakin aure da shayarwa ba amma sai su samu matsalar faduwar nono. To gaskiya akwai magani sai dai kawai idan ba a yi dace ba. Wasu zasuyi ta faman kashe kudi amma buk'ata bata biya ba, wasu kuma zasuyi ta fargaba kada su je garin neman gira a rasa Ido, ma'ana su sayi abinda zai cutar dasu da kudinsu. Kuma yanzu dai tsakani da Allah rijalu sun riga sun gama nuna abinda suka fi karkata a kansa a jikin 'ya mace kirji da kuma baya. Wasu Allah ya hallice su dashi har ya yi musu yawa, wasu kuwa basu dashi kuma mai saurin zubewa ne. To mu dai"

"duk wanda ya san maganinmu ya san ingantacce ne, kuma Yana aiki kwarai da gaske wurin dawo da daraja da"

"martabar nono da izinin Ubangiji. Sahihin magani ne da ya samu sheda da lambar yabo, kuma Islamic ne da akayi masa hadi mai inganci domin gyara jikin mace ba ma iyakacin nono kawai ba. Babu nadama haka zalika babu dana sani da asarar dukiya wurin sayan maganinmu. In sha Allah matsalar ki zata gushe idan kin jarraba amfani dashi. Ba mu tsaya ina nan ba, muna da na gyaran hips sahihi dana k'iba idan kina fama da matsalar rama. Haka zalika muna dana tumbi, da kuma maganin sanyi mai mugun kyawun da yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye wanda zaku hadu da maigidanki kuyi amfani tare. Akwai ingantattun supplement wad'anda basu da illa balle su cutar da GARKUWAR jiki. Sai dai su gyara su kuma tayar da komad'a ina nufin inda ya samu nakasu a jikinki. Muna sayar da sabulan gyaran jiki dilka da man gyaran gashi, muna kuma bayar da sari a fad'in najeria da nijar muna tura kayanmu kowane gari da ikon Allah.*"

*Muna garin kano duk inda kake za mu aika maka da kayanmu. Domin neman karin bayani sai a yi mana magana ta Whasap ga lambobin da za a same mu a kai.*

*07084653262 ko*

*08089965176*

*SIYAN NAGARI!!!!!!*

*A JARRABA A SAMU BIYAN BUKATA DA YARDAR ALLAH*

TEEMAH DATA SERVICES MTN

1GB @550

2GB @950

3GB @1450

4GB @1550

5GB @1700

CHECK CODE *323*4# VALIDITY 30DAYS CHAT@08112392177 CALL @08037026306

8037026306 fatima musa ibrahim opay

*15*

"Nan da nan 'kwalla ta ciko idona ta fara zuba. Ina ina jin nauyin na ce masa ba na so ya auri zabin Yaddikonsa kuma kanwarsa, abinda yake ta damuna kenan, domin na gama fahimta duk kwane kwanen da Inna Uwani take yi kenan, shi ma kuma kamar yana da burin cika mata muradinta. A tunanina idan na nuna masa rashin amincewata na so kaina da yawa. To ni kaina na kasa sarrafa zuciyata domin wani mugun kishinsa nake ji a zuciyata ba kuma na so kowace mace ta rabi inda yake."

Ganin ina kuka kashir'ban sai hankalinsa ya tashi ya rungume ni a kirjinsa yana jijjigani kamar karamar yarinya sai ruwan kalamai yake yi mini a kunne. Wannan ma yana d'aya daga cikin dalilan da suka sanya ba na so wata mace ta kusance shi domin iyakar soyayya mutumin ya iya.

"Daga rarrashin sai lamari mai girma ya gifta. Dama kuma akwai buk'atar hakan, tunda tun bayan shiryarmu ba mu taba kwana ba tare da mun kusanci juna ba. Sai gashi yau kwanaki takwas kenan babu wannan, shi din ma ya isa ya taka muhimmiyar rawa wurin dasa k'unci a zukatanmu. Ban dora alhaki akan kowa ba sai akan Inna Uwani domin itace take ko'karin rusa mana farincikinmu. To ko lokacin da muke biyawa juna buk'ata bai iya yin shiru ba. Yana gaya mini kamar yau din ya fara sanina domin ya gamsu fiye da kowace rana. Ni ma ban boye masa ba na nuna masa na yi kewarsa kwarai sa'annan kuma na gaya masa abinda nake hasashe na samuwar cikin da yake ta mafarki. Ai sai ya kara kid'imewa Yana ta addu'ar Allah Yasa shi din ne. Koda muka yi wanka muka sauka kasa kawai sai na ji yana gayawa Hajja cikine da ni. A okaci guda na diririce kunya mai karfin gaske ta kama ni."

Cikin jin nauyi da kunyarsu na yi kasa da kaina. Shi kam bai ji nauyi ba ya riko hannuna muka zauna a kujera yana

"fad'in."" Ciki ne da ita wallahi, yanzu nan ta gaya mini, Hajja wannan ranar tarihi ce wajena ku taya mu addu'a Allah Ya sauketa lafiya."

"Hajja baki a har kunne take cewa."" Addu'a ta zama dole Tajo, ai ni ma ranar ta zama tarihi a wajena ba zan manta da ita ba."""

"Budar bakin Inna Uwani ta ce."" Ina ce ita ba ta fari ba ce a wajanta ko."""

"Hajja ta ce."" Kwarai kuwa ta uku ce, ai mu kamar ta fari ce a wajenmu Uwani."""

"Sai ta yi ya'ke wanda hausawa suke kira da ya fi kuka ciwo tana fad'in."" To Allah Ya raba lafiya."" Gabad'aya suka amsa da Amin. Ban da ni, da na tafi tunanin abubuwan da suke faruwa."

"Samuwar juna biyu a tare da ni sai ya kara janyo mini k'auna da soyayya a wurin uwar mijina. Dashi kansa maigidan wanda a wasu lukutan har tausayi yake ba ni, idan na ga yadda yake kaffa-kaffa da ni, sam baya son b'acin raina. Idan yana gida baya bari na yin komai kullum muna tare da juna a cewarsa yana jin d'umin abinda zai haifa."

Wasu lukutan har b'uya nake yi na share hawaye domin tunda cikin ya yi k'wari zuciyata take ta yi mini sa'ke-sake marasa kyawu. Koda abin ya dame ni na kira Anti Yagana a waya na gaya mata ina yawan mafarkai da munanan tunanai take cewa da ni mafi akasari masu ciki sukan samu irin hakan. Amma dai na dage da addu'a. Ni kam cikin Yusi da Kamalu ban yi irin wannan wasi-wasin a raina ba.

Hajja ta samu wurin zama domin kuwa cewa ta yi ba zata tafi ba har sai na haihu tukkuna lokacin watansu hud'u da

"zuwa. Inna Uwani ta yi ta yi da ita su tafi tace mata a'a, sai na haihu. Sai kawai ita ta yanke shawarar tafiya domin dama kamar akan kaya take dalili ta tsani ta bude ido ta fa gilmawar matar gidan da ciki, da kuma yadda masu gidan suke ki'dime akan hakan. tana ganin komawarta gida shine maslaha a wajenta domin ta je su tattauna yadda za a yi, don ta fahimci kamar sai ta biyo ta bayan gida tukkuna ha'kanta zai cimma ruwa."

Tafiyar inna Uwani da kwana biyar. Anti Yagana da Hadiza suka zo. Anti Yagana sai da ta fara sauka a can gidanmu

"dalili ta kwana biyu ba ta je. Nan fa Hadiza ta ma'kale mata wai lallai sai sun taho tare. Sai a lokacin ma ta san auranta ya mutu tana cikin iddah ne. Da ta tambayata dalili duk ta kwashe komai ta gaya mata. A lokacin ta yi mata fad'a sosai irin na 'yan uwantaka. Ummansu tana zaune tana ji amma ba tace komai ba, ita bakin cikinta yadda a komai yaranta ne a baya. Kallo d'aya ta yi wa Yagana ta gane cewa lallai tana cikin hutu da jin dadi, dama kuma ko lokacin da ta auri mijinta mai rufin asiri ne."

Da sahalewar Babanmu suka kamo hanya suka taho. Maigidan kuwa ya dinga fad'a yana cewa mai yasa suka biyo motar haya daga Kano zuwa Legos ba su kira su sanar da ni ko kudin ticket sai a basu su biyo jirgi su zo.

"Duk wani abu da ya dangance ni yana mutukar daraja shi da martaba shi. Tun da ya fahimci cewa anti Yagana itace babba a gidanmu yake girmamata gashi dai ya kusa haifarta amma idan zai gaisheta sai ya dan risina. Dalilin da ya sanya ma kenan ta guji zaman falo take zamanta a d'aki, takan ce mini Amina mijin nan naki kunyarsa nake ji wallahi tallahi wani idan ya ga abinda yake yi sai ya d'auka kin wanke kin bashi ya shanye. Ba na so jama'a su gazgata zarginsu akan cewa matan barno suna asiri. Kin ga dai mutumin nan babu wani abu da muka taba yi masa na mallaka, ban sani ba ko kin yi a boye Amina abin yayi yawa."

"Na dinga dariya ina fad'in wallahi ko d'aya anti Yagana shi haka yake fa bashi da wani girman kai da ma'aikatansa sai ya zauna ya ci abinci dasu. Ni kaina dan ya durk'usa mini ba wani abu ba ne. Ta ce."" Idan ya durk'usa miki wannan tsakaninku mijinki ne, amma ni kam ina kin kunyar abinda yake yi mini. Mutumin da manya suke zube masa amma idan zai gaishe ni sai ya rankwafa."""

"Na ce."" Anti Yagana duk wanda ya dangance ni to wallahi yana da daraja a wurinsa. Karin abin ma kuma wannan cikin na jikina ya sake janyo mini girma a wurinsu da mahaifiyarsa. Wallahi ban yi masa komai na gusar da hankali ba."""

"Ta girgiza kanta tana fad'in. "" Lallai Amina Allah ya share miki hawaye sai kiji tsoron Allah , ki kyautata masa kamar"

"yadda yake kula dake, ki tsare masa mutuncinsa da dukiyarsa. Na tabbatar da cewa son da yake yi miki na Allah da Annabi ne, ki yi iyakacin bakin kokarinki wajan yi masa biyayya."""

"Na ce."" In sha Allahu Anti Yagana na gode."""

"To duk wannan zantukan da muke yi Hadiza tana zaune ba ta ce komai ba illa zare Ido ta kalli bakin wannan ta kalli bakin wannan haka ta dinga tana ta sakin ajiyar zuciya. Hadiza kenan duk wani motsi da zata yi na san manufarsa domin kuwa tare muka tashi a gida daya daki daya, babu yadda zata yi ne shiyasa ta sakar mini domin kuwa Allah ne yake ikonsa."

Anti Yagana da Hajja jininsu ya hadu sosai idan suna hira tamkar uwa da 'yarta. Halinsu ya zo daya sannan kuma

tunani da nazarinsu ya zo daya. Ina jin dadi sosai a duk lokacin da na gansu a tare suna hirarraki irin na rayuwa. Ita kuwa Hadiza dama ta samu bata aikin komai sai ci da kuma bacci abinda take so ya samu basu cika wata biyu ba ta murje ta yi bul daidai da fatar jikinta sai da ta canza. To ko yaushe tana cikin Ac ga abinci mai kyau.

Lokacin da anti Yagana ta shirya tafiyarsu sai Hadiza ta yi tsalle ta dire ta ce ba zata ta tafi ba sai na haihu tukkun. Hajja kuwa ta goya mata baya. Maigidan ma haka ya ce ta zauna tunda bata da aure. Ni dai ban ce komai ba domin

na riga na san ba don ta kula da ni ta nace sai ta zauna ba domin biyan bukatarta ce. Na yi ta dariya ina kallonta a

"lokacin da suke ta jayayya da anti Yagana tana cewa ba haka Babanmu ya bata umarni ba, don haka dole sai sun tafi tare. Maigidan ya sauko daga sama da yake asabar ce baya fita da wuri ya riski jayayya. Ya ce anti Yagana ta yi hakuri zai kira Baban namu ya yi masa bayani. Ba don ranta ya so ba ta ha'kura. Aikuwa muna shiga d'aki ta rufe Hadiza da fad'a tana cewa."" Ba zai yiwu daga zumunci mu tare musu a gida ba. Ina lefin wata biyun da mukayi ai ya isa. Tun Hadiza na daurewa har sai da ta fashe da kuka tana cewa."" Anti Yagana menene don na ce zan zauna na kula da 'yar uwata. Ba ni fa da nauyin kowa a kaina ba miji ba yara. Ko don ba ciki daya muka fito tare ba shiyasa zaki dinga nuna mini banbanci. Ko ina da wani aibu ne."""

"Cikin rashin jin dadin abinda Anti Yagana ta yi mata na ce."" Hadiza ba haka ba ne, ba ki fahimci Anti Yagana ba,"

"amma kada ki yi mata wannan fassarar don Allah, menene babu komai ki yi zamanki mana, na gode sosai da kulawarki a kaina, Allah ya bar zumunci."""

Anti Yagana tana jin mu ba tace uffan ba sai aukin tsaki da take ja. Na riga na gama fahimtar duk inda ta dosa. Tana jin tsoron zaman Hadiza ne kada ta zo ta aikata wani abin da zai sanya girma da mutunci mu ya zube a idon maigidan.

****

Duk wani shirye-shirye na tafiyar anti Yagana maigidan ya kammala mata domin cewa ya yi a jirgi zata koma gida in sha Allah dan ba kasafai ya fiye son tafiyar motar nan ba.

Gudun aure na kudi ne Hajiya kada ki karanta mini littafi ba tare da kin biya ni hakkina ba.

Saura kwana biyu ta tafi rikici ya balle a tsakanina dashi domin har ga Allah nayi iyakacin bakin kokarina wurin ganin

"na danne abin a zuciyata hakan ya gagara. Tun lokacin da muka sasanta jununmu nake masa soyayya ta tsakani da Allah irin wadda ba na so ko kuda ya kusanceshi. A zahiri tashi ce ta fito fili, amma ni gani nake yadda nake bala'in sonsa da kishinsa baya yi mini kwatankwacin hakan. Kuma ina ganin komai na rayuwata zan iya bud'a masa ya san dashi ba zan rufe masa ba, zan iya bayyana masa sirrina ganin yadda ya d'auke ni, da kuma matsayi maigirma da ya ba ni a zuciyarsa. Duk wanda zai ba'kunce mu na second guda zai fahimci cewa akwai k'auna sha'kuwa da mutuntawa a tsakaninmu. Dalilin da ya sanya ma kenan na ajiye hakan a raina cewa. Babu wani abu da ya dangance shi da zai boye mini sai gashi yau ya nuna mini cewa namiji ne fa shi kuma dabi'ar nan fa ta kumbiya kumbiya da Allah ya hallice su da ita ba zata canza ba. Hauwa dai yar uwarsa ce ni ban isa na raba tsakaninsu ba, amma wallahi ban taba tunanin suna waya ba domin bai ta'ba nuna mini hakan ba, yarda dashi ce ta sanya ma ba kasafai nake d'aukar wayoyinsa ba duk da cewa yakan ajiyesu a wurin da nake zaune ko ya tashi ya fita daga d'akin ya bar su. Da can na yi zarginsa dalilin abinda ya yi mini farkon haduwarmu, amma da zama ya yi zama a tsakaninmu sai na gazgata rantsuwarsa inda yake ce mini bai taba kusantar zina ba, kawai ya jarraba ni ne akan wata bukatarsa don samun abokiyar rayuwa. Ashe ha'kan Inna Uwani ya kusa ya cimma ruwa ban sani ba, ina ta zaune sake da baki."

"Abinda ya faru shine bayan mun gama sunna sai bacci ya kwashe ni domin ba wuya bacci haka nake yi don yanzu ko auratayya muke yi bana wani katabus shi yake kidansa da rawarsa wasu lukutan ma ina gyangyadi zai kammala. Abinda ya faru kenan bacci ya kwashe ni, shi kuma ya shiga bandaki domin yin wanka. Cikin ikon Allah kiran wayarsa da akayi wadda take saitin kaina na bud'e Ido firgit sakamakon karar da ta cika mini kunne. Na tashi da sauri idona ya sauka kan fuskar wayar wanda sunan Dr Hauwa ya fito rad'au kan screan din. Gabana na bugawa na tsirawa sunan Ido a sa'ilin kuma na nemi baccin da yake cikin idona na rasa na yi tarmazai ina ta duba sunan dr Hauwa. Ban d'auki wayar ba har sai da ta katse na d'auka na shiga wurin kira naga iya adadin kiran da tayi masa ba zai k'irgu ba. Na duba shi ma naga ya kira ta sosai. Na duba messages gasunan kala kala ta turo masa na gaisuwa da fatan alheri da kuma na soyayya Amma ba kowanne yake bata amsa ba domin kusan guda talatin bai fi uku ya rubuta godiya ba. Hakan bai sanyayar mini da zuciya ba domin na san ba kasafai ya fiye son rubutu ba ya fi kiran waya ko a Whasap ne sa'kkonin mutane sukan yi kwana da kwanaki kafin ya ware ranar da zai dubu su. Wasu ma baya reply sai dai ya kira mutum a waya."

Na ajiye wayar na koma na kwanta zuciyata na tsalle da tafarfasa. Ni kaina ban san haka nake da zafin kishi ba sai yau idona har ya ji yake yi mini wani 'kullutun abu ya danne mini makogwaro.

Koda na ji fitowarsa daga bandakin ban bude Ido ban kuma motsa ba. Ina jin lokacin da ya d'auki wayar ya zauna saitin kafafuna yana dubawa ban bud'e idona ba amma duk wani motsinsa Ina ji.

"Kawai sai na tsinkayi maganarsa yana cewa."" Hauwa ya kike, ina wanka ne lokacin da ki ka kira, Ina inna Uwani ya aikin naki."""

Ashe kiranta ya yi domin a tunaninsa bacci nake yi.

"Tana tsaka da bashi amsa na bud'e idona tare da tashi zaune Ina kallonsa. Ya dube ni yana fad'in."" Bari zan kira ki an jima sai mu yi maganar oke."""

"Ya kashe wayar ya ajiye yana fad'in."" Madam tashi ki yi wanka mana."""

"Na dube shi fuska a turbune "" Menene na katse waya da sauri kana cewa za ku yi magana an jima. Hauwa ce fa, to"

"menene abin boye mini, ko ni din na isa na hana ka ka aureta ne "

*GARKUWAR MATA.*

*BINTA UMAR ABBALE*

"[6/3, 8:38 PM] matar mijinta: *Wannan littafin na kudi ne vip 1k akan telegram. Normal What'sapp group kuma #700 hanyar da za a biya kudin ita ce wannan...0542382124...Binta Umar gtbank ko kuma 7084653262. Binta Umar"

Opey bank. 'Yan nijar dala dari katin airtel za ku tura mini bayan kun kankare hoton. A tura da sheda ta wannan lambobin iya What'sapp kawai.*

*07084653262*

*08089965176*

*V-VIP AREWA PEN *

*TALLAH!*



*DA MAGANI A GONAR YARO!!*

*08089965176*

*07084653262*

"*Dayawa akwai matan da suke da matsala ta lalacewar nono yamushewa da kuma fad'uwarsa. Wasu ma 'yan mata ne basu kai ga matakin aure da shayarwa ba amma sai su samu matsalar faduwar nono. To gaskiya akwai magani sai dai kawai idan ba a yi dace ba. Wasu zasuyi ta faman kashe kudi amma buk'ata bata biya ba, wasu kuma zasuyi ta fargaba kada su je garin neman gira a rasa Ido, ma'ana su sayi abinda zai cutar dasu da kudinsu. Kuma yanzu dai tsakani da Allah rijalu sun riga sun gama nuna abinda suka fi karkata a kansa a jikin 'ya mace kirji da kuma baya. Wasu Allah ya hallice su dashi har ya yi musu yawa, wasu kuwa basu dashi kuma mai saurin zubewa ne. To mu dai duk wanda ya san maganinmu ya san ingantacce ne, kuma Yana aiki kwarai da gaske wurin dawo da daraja da martabar nono da izinin Ubangiji. Sahihin magani ne da ya samu sheda da lambar yabo, kuma Islamic ne da akayi masa hadi mai inganci domin gyara jikin mace ba ma iyakacin nono kawai ba. Babu nadama haka zalika babu dana sani da asarar dukiya wurin sayan maganinmu. In sha Allah matsalar ki zata gushe idan kin jarraba amfani dashi. Ba mu tsaya ina nan ba, muna da na gyaran hips sahihi dana k'iba idan kina fama da matsalar rama. Haka zalika muna dana tumbi, da kuma maganin sanyi mai mugun kyawun da yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye wanda zaku hadu da maigidanki kuyi amfani tare. Akwai ingantattun supplement wad'anda basu da illa balle su cutar da GARKUWAR jiki. Sai dai su gyara su kuma tayar da komad'a ina nufin inda ya samu nakasu a jikinki. Muna sayar da sabulan gyaran jiki dilka da man gyaran gashi, muna kuma bayar da sari a fad'in najeria da nijar muna tura kayanmu kowane gari da ikon Allah.*"

*Muna garin kano duk inda kake za mu aika maka da kayanmu. Domin neman karin bayani sai a yi mana magana ta Whasap ga lambobin da za a same mu a kai.*

*07084653262 ko*

*08089965176*

*SIYAN NAGARI!!!!!!*

*A JARRABA A SAMU BIYAN BUKATA DA YARDAR ALLAH*

TEEMAH DATA SERVICES MTN

1GB @550

2GB @950

3GB @1450

4GB @1550

5GB @1700

CHECK CODE *323*4# VALIDITY 30DAYS CHAT@08112392177

CALL @08037026306

8037026306 fatima musa ibrahim opay

*16*

"Ya girgiza kansa yana ce wa."" Ba ki isa ba, muddin ina da ra'ayinta. iko kuma ina dashi, bayan hud'u har 'kwarkwara zan iya yi."""

"Na ce."" Haka ake son namiji ai, dama ai na jima da sanin target dinka Yallabai, don girman Allah ka auro ukun a lokaci daya to me zai dami Amina."""

Ya jima yana kallona da fuska irin ta b'acin rai. Yana da juriya a wasu lukutan idan sa'insa ko rigima ta had'a mu yakan sakar mini ya share duk maganganun da zan ya'ba masa kuwa. Amma a wasu lukutan yakan yi fushi ya kuma nuna mini b'acin ransa. Yadda na fahimta tsayayayyar da nake masa ta fara tunzura shi.

"Ya furta."" Ki shiga hankalinki fa Amina, ki daina ganin kamar na mayar da kaina sauna akanki ki nemi ki yi mini rashin kunya zamu sanya kafar wando daya a tsakaninmu. Tabbas ina sonki amma hakan ba zai sanya na zuba Ido kina cin kasuwa a kaina ba, ke ba ki da aiki sai bakin kishi, motsi kad'an sai kin tuhume ni, haifata ki ka yi da zaki dinga

Please Login or Register in order to submit comment