You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da matsalar rama. Haka zalika muna dana tumbi, da kuma maganin sanyi mai mugun kyawun da yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye wanda zaku hadu da maigidanki kuyi amfani tare. Akwai ingantattun supplement wad'anda basu da illa"

*PAID BOOK 2K COMPLETE ON TALGRAM WHAT'S APP GRUOP KUMA 1K VIA 0542382124...BINTA UMAR GTBANK*

*07084653262*

Kirana da aka yi a waya shi ya tashe ni wajejan goma da ashirin da biyar na safe. Koda na duba lambace babu suna na daga tare da sallama sai na ji muryar Idiris mijin Sahura nan da nan na daidaita yanayina. Domin zahirin gaskiya ni ma haushinsa nake ji dangane da abinda yake ahirin aikatawa. Tabbas nasan kiran nasa baya rasa nasaba da matsalarsu. Muka gaisa jikinsa a sanyaye ya fara yi mini bayanin halin da ake ciki Sahura ta rufe gida sannan ta tattara yara da kayansu ta kaiwa mahaifiyarsa bayan tasan bata da k'oshin lafiya. Yanzu haka sai a shagon dake jikin

gidan ya kwanta shagon da yarana suke d'inki kenan yana jadadda mini a cikinsu ya kwanta cike da alhini da

"damuwa. Ban katse shi ba har sai da ya kammala tukkuna na ce."" To wallahi ni dai Idiris ba ni da tacewa akan wannan lamari. Ina ganin ka kyaleta kawai tunda tafi buk'atar rabuwar sai ka je ka yi rayuwarka da sabuwar amaryarka yara kuma ai duk sun girma babu wanda za a yi wa wahala a cikinsu."""

"Da damuwa ya ce."" Saboda fa kusancin da yake tsakaninku ya sanya na kira ki Amina, me yasa za ki gaya mini haka ke don Allah idan na ce zan rabu da Sahura ba za ki yi mamaki ba?"""

"Na d'an yi murmushi babu nisha'di na ce."" Babu mamakin da zan yi Idiris abinda aure na mutum biyu ne idan ka gaji da ita zaka sawwa'ke mata mana ko kuma ka nemi hanyar da za ka k'untata mata."""

"Ya ce."" Yanzu dai don Allah ki rarrasheta wallahi ba wai don na wulakantata zan yi auran nan ba. Ina son Sahura ina kuma buk'atar cigaba da zama da ita ki rarrasheta ki bata ha'kuri ta dawo mu cigaba da zama in sha Allahu babu abinda zai faru domin itama yarinyar da zan aura bata da matsala 'yar gidan tarbiya ce wallahi bata da fitina."""

"Na yi dariya ina mamakin maganarsa tun bai zauna da yarinyar ba yana shedar halayenta tabbaci kenan ba zai janye ba. Na ce."" To shikkenan zan yi magana da ita zuwa an jima in sha Allahu."""

"Da sauri ya furta."" Zan kira ki domin na ji abinda ku ka yanke amma don girman ki tausheta ta dawo na ware mata turmi biyu daga cikin lefen da nake had'awa sannan zan bata dubu hamsin sai ta sayi kayan kwalliya."""

"Na ce."" To shikkenan. Da takaici na katse wayar ban tsaya na kàrasa sauraran karshen maganarsa ba. A tunana ai Sahura tafi karfin turmin atamfa biyu da dubu hamsin, ita wahalar nawa ta yi masa tunda suka yi aure har yanzu ma cikin yi masa hidima take."

Da yammacin ranar muka yi waya da ita na gaya mata Idiris ya kira ni a waya akan abinda yake faruwa. Kamar yadda

"ya buk'ata din na fara rarrashinta da kawo mata misalai ta yi shiru tana saurarena don har ina murna ina cewa ta sauko a zuciyata sai da na gama maganata tukkuna ta ce ."" Ba ni buk'atar atamfofinsa ya ri'ke har da k'udin ya k'arawa amarya Amina, takarda zai aiko mini da ita yanzu zaman da nake yi kenan."""

"Na ce"" Sahura akan kishiya dai idan ki ka kashe auranki na kusan shekara ashirin da wani abu wallahi kin ba ni kunya kuma na raina wayonki, ki bari ta shigo mana ki ga kamun ludayin zaman. Haba don Allah ki jure mana."" Kashe mini wayata ta yi ta barni ri'ke da tawa a kunne da mamaki."

Bayan magriba Idiris din ya dinga kira wayata ina kan daddauma ina jan carki kamar yadda na saba. Koda na duba na

ga shine na ajiye wayar kawai na cigaba da abinda nake yi shi kuma bai fasa kira ba. Hakan ya yi daidai da shigowar maigidan wanda shi ma tunda ya fita da asubahi bai sake shigowa ba.

"Ya d'auki wayar yana dubawa sai ya kalle ni kaina a sunkuye kawai sai ya daga tare da sanyata a kunnansa jin muryar namiji na ji yana fad'in."" Wanene?"" ban ji abinda Idiris din ya ce masa. Na ji yana fad'in."" Mijin Sahura ne to bari ta kammala tana azkar ne zuwa an jima sai ka kira."""

"Ya yi shiru na d'an wani lokacin kafin na ji yana fad'in."" Amin Ya Allah, ma sha Allah, ka kira zuwa an jima kadan."" Daga haka sai ya kashe wayar ya ajiye har na kammala na juyo ina dubansa ya ce."" Mijin Sahura ne ya kira ki a waya ina fatan lafiya?"""

"A tak'aice na ce."" Lafiya ba lafiya."""

"Ya dube ni sosai yana fad'in."" Suna da matsala ne?"""

"Ina ko'karin cire hijabin jikina na furta."" Aure zai ka'ra shine take bore har ta tafi gida."""

"Ya yi d'an jim kafin ya furta."" Na kan rasa inda tunaninku yake tafiya wataran Amina, daga zai kara aure domin raya sunna sai ta ta tafi ta bar dakinta menene amfanin hakan."""

"Cike da takaici na ce."" Ai ba a ce kada ya kara ba, ya bari ya tsaya da k'afafunsa tukkuna bashi fa da cikakkiyar"

"sana'a, wallahi Sahura wahala take sha a hannunsa kuma ta yi masa hallaci tunda suka faru a gidan haya suke shekara kusan ashirin da uku da auransu buge-buge yake yi itace karfin kula da gidan tun kafin ma ta samu aiki a kamfaninka haka take gwagwarmaya. Amma shine daka kawai an yi musu rabon gado ya samu miliyan takwas ko wata biyu fa ba a yi da raba musu kudin ba ya fara yun'kurin karin aure har yana tara lefe a dakinta. Ita kuwa ta kulle gidan ta gudu ta kai masa yaransa wurin Babarsa."""

"Dariya ce ta sub'ce masa ya dinga yi har ina mamakinsa na d'auka ai zai cigaba da goya masa baya. Ya ce."" A lallai bai kyauta ba kuma da gaske bai yi adalci ba. Yadda ki ka gaya mini yanzu ai ita ta yi masa hidimar da ta zarce ta miliyan takwas to me yasa tunaninsa bai kai ya saka mata da alheri ba sai da kishiya. Bai kyauta bai kuma yi daidai ba, in banda rashin tsinkaye ai ba aure ya kamata ya yi ba a yanzu ko?"""

"Da sauri na ce."" Kwarai kuwa abinda itama take ji wa haushi kenan zai bata turmin atamfa biyu da dubu hamsin abinda ya kara ba ni haushi dashi kenan."""

"Ya ce."" Kin ga kira mini Sahurar yanzu na yi magana da ita."""

"Na zauna gefansa ya miko wayata na lalubi lambata bugun farko ta daga cikin bala'i ta fara fad'in."" Amina ki kyale ni"

"don Allah idan har kin san ba maganar arziki za ki gaya mini ba, na gaya miki na gama yanke hukunci, idan kema za ki goyu da bayan Idiris din sai nasan a wani aji zan ajiye ki."""

Ina binki bashi idan kin karanta ba ki biya ni hakkina ba

"Na ce."" Yi ha'kuri mai da wukar sis, Yallabai ne zai yi magana dake."" Ta yi shiru ba ta ce komai ba sai na mik'a masa"

"wayar da sauri ya kar'ba a nutse ya kira sunanta ""Sahura."" Ina ji ta amsa cikin ladabi."" Na'am ranka ya dad'e ina yini?"" Ya ce."" Lafiya lau ya kuke ina yara?"""

"Ta ce."" Kowa lafiya lau Sir."""

"Shiru ya d'an biyo baya kafin ya yi gyaran murya ya ce."" Kin san abinda nake so dake?"" Ta ce."" A'a. """

"Ya ce."" Amina ta yi mini bayanin duk abinda yake faruwa, ki yi hakuri ki koma dakin mijinki ki cigaba da kula da yaranki, shi kuma ki kyale shi idan har kina da hakki sannu a hankali Allah zai saka miki. Ni kuma zan yi miki alheri domin ki zauna a wadace cikin walwala zan canza miki gida mai kyau sannan zan baki kudi ki dinga wata sana'ar a gefe sannan ki cigaba da zuwa aikinki kina taimakon yaranki da 'yan uwa, kada don mijinki zai kara aure ki yi fushi ki dasawa kan ki k'unci yaranki su shiga damuwa ki daure na wani lokaci komai zai wuce ."""

"A sanyaye ta ce."" Na gode ranka ya dad'e, Allah Ya saka da alheri, shikkenan in sha Allahu zan koma kamar yadda ka buk'ata."""

"Cike da jin dadi kuwa ya furta."" Ni ma na gode sosai Sahura, zan yi magana da Jamilu sakatare na nan kamfanin naku duk abinda yake da akwai zai yi miki bayani in sha Allahu maganar abinda na ce zan baki kuma za ki gani a daran nan."""

Ta dinga godiya har muryarta tana rawa. Ya mik'o mini wayar na kar'ba a d'an sanyaye na ji dad'i sosai da ya shiga lamarin gashi har da alherinsa ko babu komai yana da lada a wurin Ubangiji.

"Muka yi sallama da ita tana fad'in."" Na kara yi masa godiya. Na dube shi a hankali na ce."" Mun gode sosai Ubangiji Allah Ya saka da alheri."""

"Bai kalle ni ba ya ce."" Ba ni details dinta yanzu ."""

"Ya miko mini wayarsa na kar'ba na sanya masa kamar yadda ya ce. Ya ce."" Ke nawa ki ka bata gudummuwa?"""

"Na ce."" Gudumawa kuma?"""

"."" Dannar kirji kuke cewa ko?"""

"Dariya na yi na ce."" Ban bata komai ba wallahi."""

"Ya d'an Harare ni yana fad'in."" To yaushe kuwa za ta saurari rarrashinki irin wannan ana had'awa da hasafi sai ki ga an shawo kan matsalar."""

Na dinga gyada kaina ina dariya lallai ne kudi suna iya sayan komai amma ban da rai da rayuwa.

"Miliyar biyar ya tura mata bai gaya mini ba amma yana tura mata da kamar minti goma ta kira ni a ki'dime har da rawar murya ""Amina don girman Allah ki kara yi mini godiya yanzu nan na ga sa'ko 5m na gode na gode na gode Allah Ya saka da alheri ga sabon gida an ce za a ba ni."""

"Dariya ta kama ni na ce."" Sahura yanzu don Allah ina rantse-rantsen da ki ka dinga yi, Idiris fa aure zai ka'ra ko kin manta."""

"Ta ja tsaki tana fad'in."" Wallahi tallahi Amina saboda Yallabai ya saka ba ki a maganar nan zan koma zaman aure da Idiris amma wallahi ba don haka ba sai dai ya aiko mini da takardata."""

"Ta kashe wayar ba tare da ta jira ta ji abinda zan ce ba."""

"Ya dube ni yana fad'in."" Ba ki kyauta ba Amina."" Ina dariya sosai na ce."" Don ba ka ji rantsuwar da ta dinga yi ba shine abinda ya ba ni dariya da mamaki."""

"Ya gyad'a kansa Shima da d'an murmushi a saman fuskarsa ya ce."" Ai tace saboda na sanya ba ki zata koma. Kuma wallahi na ji dad'i sosai tuntuni na fahimci cewa ai tana da kirki da saukin hali."""

"A tak'aice na ce."" Hakane kam Sahura mutum ce har da rabin mutum mun gode sosai ta ce na sake godiya ina yi akan kaina da ita Ubangiji Allah Ya sa kafi haka."""

Ya amsa da Amin suma Amin yana kallona.

"Na dan sauke ajiyar zuciya kafin na ce."" Sai mu yi maganar Hauwa tunda mun sasanta wannan auran."" Ya bata rai yana fad'in."" Za ki bata mini rai kenan ko?"""

"Na ce."" B'acin rai kamar yaya?"""

"Cikin 'kosawa ya ce."" Maganar Hauwa ta ishe ni a gidan nan Amina, ya kamata ke ma ki bar ta kamar yadda na bar ta"

"ba na son abinda zai rikita mini gida dama can itace husumiya yanzu da bata nan ba gashi kuna zaune kalau da Maryam ba."""

Haka kawai sai na ji rashin jin dadin maganarsa. A ganina kamar Hauwa bata cancanci haka daga wurinsa ba duk da bai gaya mini abinda ya faru ba a wajan sulhunsu amma na lura haushinta da yake ji ya sake ninkuwa. Zaman da na yi da ita na fahimci macace mai taurin kai da girman kai har shi eanda ya ajiyeta yi masa take kuma a cikin ayyukan da ta dinga yi a gidan nan da gadara da iko take gudanar da komai dalili tana ganin kamar ta fi kowa dangantaka mai karfi bayan ta aure duka na fahimceta. To amma ni wannan baya damuna tunda nasan matsayina a zuciyar mijina ko bai fito ya fad'a ba. Ba na sha'awar a ce sun rabu gabad'aya ga zuria a tsakaninsu mai k'arfi kamata ya yi a ce sun sulhunta junansu sun yi hakuri sun cigaba da zama.

Ganin yadda ya had'e rai da nuna baya buk'atar sake maganar Hauwa sai na shigo da maganar zuwa maiduguri tunda shi ya yi mini alkawari ya ce za mu je a karshen wata amma daga mun dawo za mu tafi legos tunda Alhmdullhi jikin matar tasa ya yi sau'ki.

***

Abinda ya faru kenan kamar yadda ya yi mini al'kawari cikin karamci da kara da kulawa muka je maiduguri tare. Ya bi dangin Mamana da alheri mai yawa. Baban Saude bayan gari a lokacin da muke je garin. Da yawa wad'anda ba su ta'ba ganinsa a zahiri ba suka yi tozali da shi tare da alherinsa. Ni kuma na sayawa Fadila sabuwar freezer 'katuwa da kenan d'inki domin yin sana'ar sayar da ruwa da 'kan'kara.

Kwananmu biyu kacal a maiduguri muka yi sallama da su.

A ranar da muka dawo a gidan Momi ya kwana washe gari ya shigo mini a hargitse yana gaya mini jikinta ne ya sake

tashi jiya ba su yi wani baccin kirki ba suma ta yi sai gefan asubahi ta dawo.

Ya ba ni tausayi sosai itama haka domin da gaske ne duk mai zuciyar imani idan ya ga halin da take ciki zuciyarsa sai ta motsa. Dole shiryin tafiyarmu Legos ya rushe yadda hankalinsa ya tashi da ciwon komai nasa tsayawa ya yi

Kwana biyu a tsakani ya sake kwasarta suka sake koma can kasar hindu din asibitin da suka kula da ita a wancan

karon domin sake duba lafiyarta.

*GARKUWAR MATA.*

*BINTA UMAR ABBALE*

https://chat.whatsapp.com/E8JgnaAUG13CRwJbYeXImE?mode=gi_t



*TALLAH!*

*DA MAGANI A GONAR YARO!!*

*08089965176*

*07084653262*

"*Dayawa akwai matan da suke da matsala ta lalacewar nono yamushewa da kuma fad'uwarsa. Wasu ma 'yan mata ne basu kai ga matakin aure da shayarwa ba amma sai su samu matsalar faduwar nono. To gaskiya akwai magani sai dai kawai idan ba a yi dace ba. Wasu zasuyi ta faman kashe kudi amma buk'ata bata biya ba, wasu kuma zasuyi ta fargaba kada su je garin neman gira a rasa Ido, ma'ana su sayi abinda zai cutar dasu da kudinsu. Kuma yanzu dai tsakani da Allah rijalu sun riga sun gama nuna abinda suka fi karkata a kansa a jikin 'ya mace kirji da kuma baya. Wasu Allah ya hallice su dashi har ya yi musu yawa, wasu kuwa basu dashi kuma mai saurin zubewa ne. To mu dai duk wanda ya san maganinmu ya san ingantacce ne, kuma Yana aiki kwarai da gaske wurin dawo da daraja da martabar nono da izinin Ubangiji. Sahihin magani ne da ya samu sheda da lambar yabo, kuma Islamic ne da akayi masa hadi mai inganci domin gyara jikin mace ba ma iyakacin nono kawai ba. Babu nadama haka zalika babu dana sani da asarar dukiya wurin sayan maganinmu. In sha Allah matsalar ki zata gushe idan kin jarraba amfani dashi. Ba mu tsaya ina nan ba, muna da na gyaran hips sahihi dana k'iba idan kina fama da matsalar rama. Haka zalika muna dana tumbi, da kuma maganin sanyi mai mugun kyawun da yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye wanda zaku hadu da maigidanki kuyi amfani tare. Akwai ingantattun supplement wad'anda basu da illa balle su cutar da GARKUWAR jiki. Sai dai su gyara su kuma tayar da komad'a ina nufin inda ya samu nakasu a jikinki. Muna sayar da sabulan gyaran jiki dilka da man gyaran gashi, muna kuma bayar da sari a fad'in najeria da nijar muna tura kayanmu kowane gari da ikon Allah.*"

*Muna garin kano duk inda kake za mu aika maka da kayanmu. Domin neman karin bayani sai a yi mana magana ta

Whasap ga lambobin da za a same mu a kai.*

*07084653262 ko*

*08089965176*

*SIYAN NAGARI!!!!!!*

*A JARRABA A SAMU BIYAN BUKATA DA YARDAR ALLAH*

*Gudun aure paid book complete 2k akan telegram normal What'sapp group 1k via 0542382124...binta Umar

gtbank* 07084653262

Tun bayan tafiyarsu sau biyu muka yi magana dashi kamar dai wancan lokacin da suka tafi muna had'uwa ne ta What'sapp mu yi vidiyo call abinda ya kasance kenan amma wannan karon babu nisha'di da annashuwa a tare da shi muka yi magana. Idan na tambaye shi yanayin jikin nata sai ya ce mini da sauki. A wancan lokacin yi yayi kamar sabon angon da yake watayawa da amaryarsa ya yi fresh dashi don har na dinga tsokanarsa wannan karon kuwa akwai firgici da damuwa a tare da shi ko bai fad'a ba yanayinsa ya gama nunawa.

"Na kasance cikin yanayi na tunani da zullumi domin yau tafiyarsu kwana goma sha daya kenan kuma a cikin kwanakin sau biyu kacal ya ta'bo ni, tun daga ranar ma ban sake ganinsa a WhatsApp din ba. Idan na kira waya ta yanke ko na ji busy. Gaskiya na damu sosai hakan ya sanya mini rashin nutsuwa domin sai zuciyata take ta yi mini sa'ke-sa'ken mugun abu bayan mafarkin da nake yi wai gani ina da dariya da ita mara lafiyar muna hira muna ta k'yalkyala dariya. Masana mafarki kuwa suna fad'in yin dariya a mafarki ba alheri ba ne."

Gaza ha'kuri na yi na sanar da Baba Tabawa halin da ake ciki itama ta taya ni zullumi tana ta addu'a Allah Ya sa

lafiya ina amsawa da Amin.

Idar da sallar magribata kenan na d'auki wayata dake saman dirowa ba na iya minti ashirin yanzu ban bud'e data na duba ba. Cikin ikon Allah kamar iska sakonshi ya shigo. Hoton Momin ya turo mini cikin mawuyancin hali gabad'aya duk ta 'kare ta yi fiyat da ita tana kwance a tsakure a gado hancinta da abin taimakawa numfashi. Na tsorata ainun da ganinta duk da ba a zahiri ba ne hoto ne sai da na ji wani irin tashin hankali ya rintsa da ni a lokacin zuciyata ta karya na kasa jimirin jure danne hawayen da suke danno mini. Suka fara sauka a kumatuna. Wannan ciwon ya gama cinye matar nan manya cutuka sun zagaye rayuwarta.

"Vidiyo call ya kira ni ina goge hawaye na danna da ya ga ina kuka ya fara tambayar menene. Na ce."" Ni dai daka sani ba ka turo mini hoton nan nata ba hankalina ya tashi wallahi."""

"Ya girgiza kansa yana fad'in."" Tana jin jiki sosai Amina ku taya ta da addu'a gabad'aya bata gane wanda yake kanta numfashi kuwa sai da taimako."""

"Na goge hawayen da yake tsiyaya ina fad'in."" Allah Ya saukaka mata. Kai kuma Allah Ya baka lada."""

"Ya furta da ""Amin."" A tak'aice kafin ya cigaba da cewa."" Kwana biyu mun d'an yi rashin service a garin. Sai jiya da daddare ya daidaita ban kuma samu sukunin ta'bo ki ba sai yanzu ina fatan kuna kafiya."""

"Na ce."" Wallahi lafiya lau, ni ma ina nan hankalina a tashe gabad'aya na kasa nutsuwa ina ta tunanin halin da kuke ciki."""

"Ya d'an yi murmushi kafin ya kanne mini ido ya ce.'' Ni kuma mafarkin ki na dinga yi kullum na kwanta sai kin zo mini har na yi wanka da asuba."""

"D'an harararsa na yi na ce."" Kai kam ka daina haka don Allah."""

"A sakarce ya ce."" To ya za a yi ne Amina da gaske nake wallahi kin san kuwa ba zan yi miki rantsuwa akan son rai ba."

"Mafarki nake yi ina tara dake duk dare kuma na yi wanka."" Na ce ""Allah Ya kyauta."""

"Ya amsa da ""Amin.'' Kafin ya ce."" Bari zan ta'bo ki kafin na kwanta sai mu yi hira ko?"""

"A sanyaye na ce."" To."" Ina mamakinsa duk yanayin alhinin da yake ciki halinsa na fitina yana nan."

Na ajiye waya tare da yin kasa'ke gabana sai ya buga da k'arfi idan na tuna halin da naga matar nan a ciki. Wayar na d'auka na yi saurin goge hoton ba tare da na sake kuskuran sake gani ba.

To har na kwanta ban ga motsinsa ba. Da asuba kuwa ina gama ibada kamar koyaushe na bud'e data sakon shi ya

shigo kamar iska.

"""Innalillahi wa'ina ilaihi raji'un! dana fara gani tun kafin na bud'e sakon shine abinda ya assasa mini 'barin jiki da kakkarwar hannu. Na bude gabana na bugawa da karfin gaske..."

"_""Allah Ya yi wa Maryam rasuwa a daran nan ki sanar da duk wanda ya kamata Amina.""_ Abinda yake rubuce kenan"

"Wani irin tsananin tashin hankali da d'imuwa na shiga ina daga zaune na dinga jin tafin kafata na wani irin yammm! hannuna da ke ri'ke da wayar ya sandare wayar ta fad'i saman cinyata. Ni kaina saukar hawaye na ji a saman dakalin fuskata suna kasa tsare da babban sauti na furta."" INNALILLAHI WA'INA ILAIHI RAJI'UN! Allah Ya jikanki Maryam, Ubangiji Ka yafe wa baiwarka, ashe ciwo ba na tashi ba ne."""

"Wani mahaukacin kuka mai gunji ya taho mini a guje! Na sanya tafin hannuna na toshe bakina ina fad'in."" Mun shiga uku a wannan duniyar da bata da tabbas Ya Allah!!"""

Wayar na laluba da saurin gaske tabbas wannan shi zai zama izna ga Hauwa ya nuna mata cewa babu abinda yake cikin wannan duniyar face rikici da firgici tashin hankali da rashin tabbas

"Bugu d'aya wayar ta yi ta daga cikin kukan da na kasa jimirin danne shi na ce."" Hauwa Momi ta rasu."" Cike da rikicewar murya ta furta."" Wac...wace Momin kike nufi Amina?"""

"Yadda ta fad'i maganar shi ya tabbatar mini da cewar a ki'dime take... Na ce."" Momi dai da kika sani matar mijinki Hajiya Maryam."""

"Dif ta yi sai sautin shuhhh! ne yake tashi a kunnana. Na daga wayar na duba tana ta tafiya. Sunanta na kira ta amsa a sanyaye ""Na'am. Na ce."" Ki sanar da inna Uwani halin da ake ciki Hauwa kin ga dai duniyar ko ita kenan fa."""

Ta yi shiru dai bata tanka ba. Na ja ajiyar zuciya ina jin yadda wani kutittiran abu ya tokare mini a wuya ba komai ba ne face damuwa da tsananin kidima da tashin hankali.

Jin ta yi shiru ba ta ce komai ba sai kawai na datse kiran na nemi lambar Hajja domin ba na tsammanin ta san da rasuwar tunda a sa'kon da ya rubuto mini ya ce na gayawa wanda ya dace.

Sosai Hajja ta gigice da ta ji labarin rasuwar dan har sai da na yi dakacen sanar da ita tunda ita kanta ba ta da koshin lafiya. Kasa jimirin sauraran kukanta na yi na datse kiran hannuna na rawa na ajiyeta saman cinyata hawayen suka sake zubo mini a saman fuska. Hannu nasa na sharce na sake saukar waya a karo na uku anti Yagana na kira na sanar da ita domin ta gaya duk wanda ya dace a yi jana'iza da shi. Na kira Babanmu na sanar dashi shi ma ya tabbatar mini da cewar za su kamo hanya gobe da sassafe shi da Baba Sule.

"Jiki a sabule na fita falo baba Tabawa tana d'akinta sai na bita can. Na sameta tana ninke kayanta ganin yanayina ya sanya jikinta mutuwa. Rashin kwarin kafafuna

Please Login or Register in order to submit comment