You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

nan naga ashe har da su Dada da"

anti Yagana sun samu damar zuwa bikin. Na ji takaici sosai amma haka nan na ha'kura na yi masa addu'ar samu zaman lafiya madawwami. Amma na yi masa alkawari idan na haihu lafiya takanas zan zayarci kano saboda shi.

***

Duk abinda Ubangiji Allah Ya hukunta walau mai dad'i ko mara dad'i yana da iyaka. Kuma cikar mumini kenan yarda da kaddara kowace iri ce wannan shine yake tabbatar da cewa Allah yana sane dakai kuma duk jarabtar da ya yi maka idan ka cinye ba ba tare da ka bi wata hanyar ka sa'ba masa ba to zai maka tagomashin wanda kai kanka ba ka yi tsammanin irinsa ba.

Haihuwa na yi cikin koshin lafiya haihuwar da ta sake bud'e kofofin arziki da alherai masu yawa. Duk irin zullumi da

fargabar da na kasance a ciki a lokacin da nake d'auke da cikin da haihuwar ta zo sai na yi cikin sauki da taimakon Allan da ya ba ni ajiyarsu a cikin cikina. Lafiyata lau hakan nan yaran ma da na haifa lafiyarsu lau duka ba su d'auke da kowace irin lalura daidai da irin murar nan da ake haifar jarirai da ita tagwayena ba su d'auke da ita. Tagwaitaka kuwa gadonta na yi tunda Babanmu ya yi bibbiyu sau biyu ba abin mamaki ba ne.

"Tubarkala ma sha Allah shine abinda kowa yake fad'a a kansu domin kuwa yadda Allah ya gina musu jiki da lafiya tun a ciki ba wanda zai d'auka cewa 'yan tagwayene dalili wasu akan haifesu da rashin lafiya irin ta jarirai ko yan'kwanewa da yamushewar fata, su kam kalau suka fito cikin mahaifa daya kamar kuma an tsaga kara babu ita inda suka yi bambanci. Tunda aka haifesu ake ta hasashen da wa suke kama wasu suce da ni, wasu kuma su ce da babansu. Ita Hajja ma cewa ta yi da inna Uwani suke kama mai gabad'aya kenan. Jin haka ya sanya ina Uwani kasa rufe bakinta daga zarar an yi magana sai ta ce ai da ita suke kama. Can dangin Hajja suka kwaso domin ni kaina basa kama da ni balle kuma Babansu Hajja ta ce suna kama da inna Uwani shi kuma ya ce da Samira suke kama matarsa ta farko. Ni dai dariya kawai nake yi musu domin ba ni da ta cewa ganin yaran daidai da yatsuna ba su d'auko ba. Umara ya tafi a tsakankanin haihuwar ya je ya nuna godiyarsa ga Allah subahanawu-wata'ala. Satinsa daya ya dawo ya ce zai shirya walima domin sake nuna godiyarsa ga kyautar da Allah ya yi masa. Ban so ba saboda ba na so abinda zai kawo rud'ani a zamanmu na ce masa lokacin da aka yi masa haihuwar fari ma bai yi ba sai yanzu ya kamata ya bar shi kawai umarar ma da ya yi ta isa. Fad'in haka ashe lefine a wurinsa yana fad'a na kyaleshi ya yi yadda yake so kudinsa ne kuma yaransa ne ba zan tsara masa abinda zai yi ba, Yana da kyau ya nunawa Ubangiji godiyarsa ta sigogi da yawa tunda Allah Ya yassare masa to babu ruwana idone nawa....."

Humm

Mu je zuwa dai. Tsugonan ta kare ko bata 'kare

*GARKUWAR MATA.*

*BINTA UMAR ABBALE*

"[6/3, 8:38 PM] matar mijinta: *Wannan littafin na kudi ne vip 1k akan telegram. Normal What'sapp group kuma #700 hanyar da za a biya kudin ita ce wannan...0542382124...Binta Umar gtbank ko kuma 7084653262. Binta Umar"

Opey bank. 'Yan nijar dala dari katin airtel za ku tura mini bayan kun kankare hoton. A tura da sheda ta wannan lambobin iya What'sapp kawai.*

*07084653262*

*08089965176*

*V-VIP AREWA PEN *

*77*

"Rabuwa na yi dashi kawai na daina mayar masa da martani ganin iyayensa Hajja da inna Uwani a gidan, kuma daidai gwargwado suna nuna mini kulawa da kara tare da yin tiriri da yaran mussaman inna Uwani da motsi kad'an idan ana maganar kammanin yaran take amshewa tare da tabbatar da cewa da ita suke yin kama. Dukkaninsu daga ita har Hauwan na kasa fahimtar menene a can kasan zuciyarsu domin duk yadda na kai ga so lallai sai na hango cewa abinda suke yi mini ba don Allah ba ne na kasa sun 'boye sosai kuma ko da da wani kulli a ransu ba su nuna ba, amma zahiri Hauwa ta yi kyan kai da ta iya jimirin kawar da kanta daga jin haushin d'igimin da ya d'auka adalalin samuwar yaran, don gabad'aya tunda aka yi haihuwar ya rasa sukuni haka zalika mu ma haka don motsi kad'an za a"

yi zai ce ba a yi masa daidai ba ko kuma wata daga ciki ta yi kuka ko yana sama idan ya ji sai ya sauko Yana tambayar

"dalili har kunya da nauyi nake ji wani lokacin domin inna Uwani ce take dauwaniya da su Hajja tana dan taimaka mata kadan. Gefe guda kuma Hauwa na hidimar d'orawa da saukewa yini take yi a kicin saboda ba mu da mai aiki mace sai maza, na dai kudire a raina duk lokacin da na je kano to kafata kafar baba Tabawa"

"Sannan ni kaina Hauwa hidima take yi mini ta fannin abinci ga maigidan da tsofffin iyayenta. Lokacin da ya dinga fad'a akan me zan hana shi yin abinda yake so sai da iyayensa suka ji 'kananun maganganun da yake yi sai nema yake yi ya mayar da abin rigima da na gaji kawai sai na rushe da kukan b'akinciki ya ina cikin d'aita da rintsin haihuwa a sanya ni a gaba da tijara, kawai saboda na ce kada a yi walima shine lefi da fad'in bakaken maganganu."

Hajja da inna Uwani suka shiga maganar. Akan na rabu dashi ya yi ai abin alheri ne a tara mutane a ciyar dasu a

"kuma yi addu'a, dama walima aka sani a tsarin addinin musulunci ba wani abin ba ne. Ganin yadda ya samu goyan bayansu akan hakan ya sanya ban sake wata magana ba, sai da muka yi kwana biyu ba mu yi magana ba sannan muka shirya don shine ma ya dinga neman shirin ganin da mutane a gidan na kula shi domin kada suga kamar ina da mugun hali. Amma ba wani ya'ke masa baki nake yi ba don mugun haushinsa nake ji akan abinda ya yi mini."

Amaryarsa Momi akwati biyu ta yi da kaya kowacce shake wai Hassana daya usaina ma d'aya. Wallahi rasa bakin

"magana na yi a lokacin da na bude kayan ina dubawa. Da yake duk a gabansu ne Hauwa har tana cewa kada matar nan ta rusa jarinta akan yi wa 'ya'yan miji gwaninta. Ina dariya na ce ko daya tunda ki ka ga tana irin wannan kyautar ta yi nisa ne wata'kila yadda kike d'aukarta ta wuce haka. Hajja ta ce kuma ma dai mai son yi ce domin wasu akan su bayar sun gwammace wuta ta cinye domin Ubangiji yana duba duk wanda ya azurta baya fitar da kazantar dake cikin dukiyarsa da kansa zai fita ta hanyar tashin gobara ko ta wata sigar ta daban. Ta nisa kafin ta cigaba da cewa mijinku shi yake gaya mini cewa har gidan marayu ne da ita a can garinsu jos din tana d'aukar nauyinsu bayan makarantu da massalatai da ta gina duka hobbsi ga tsohon mijinta da ya rasu. Wannan dalilin ya sanya ni jin kaunarta a cikin raina domin kuwa macace ta gari, ina kara horarku ku zauna lafiya da ita, kuma kada ku dauketa a matsayin kishi sai yayarku domin ta girmeku ku muntata da kyau."

Sosai jikina ya kara yin sanyi da sha'anin matar wato mutane suna daukarwar kansu zunubi a duk lokacin da suke munana zato akan mutum alhalin ba su da sheda kawai zargi suke yi da k'age. Sai na tuna irin maganganun da Sahura ta dinga fad'i a kanta a lokacin auransu da maigidan ya zama dole kuwa Sahura ta yi nemi gafarar Allah domin kuwa ta yanke hukunci akan abinda ba ta ta'ba ga ni ba.

"To walima ta kyau sosai, kuma ta samu halartar manyar mutane malamai da ma'aikatan gwamnati har ma da 'yan"

siyasa. Sahura ta samu zuwa itama yan gidanmu kuwa Babanmu ya samu halarta tare da Baba Sule sai anti Sakina da Fati. Anti Yagana da Yafalmata sun zo Baban Saude kuma a lokacin baya gari sai da ya kira ni a waya ya yi mini barka ya kuma kira maigidan shima ya yi masa barka. Hamusu ma ba a bar shi a baya ba ya zo shi kadai Amma domin da ya gaya mini za su zo tare da Gwaggo na ce masa a a saboda tafiyar mota ce Kuma bata da lafiya sosai na yi alkawarin idan na yi arba'in da kaina zan kai mata yaran ta sanya musu albarka.

An yi hidima sosai yara sun samu alheri irin wanda ba zai misaltuba hotonsu kuwa yana ta yawo a kafafen sadarwa

tare da yayansu Khalil da ya yi wayo har yana gudu da kafafunshi.

"A daran ranar gajiya ta kayar da ni, ana yin sallar magriba da kad'an baccin gajiya ya kwashe ni. Maganarsa ce ta"

"tashe ni na bude ido Ina kallonsa yana tsaye sai kuma ya zauna a gefana na tashi zaune ina d'an hade jikina tare da d'an matsawa. A tak'aice na ce."" Ina yini."" Ya amsa cikin kulawa yana ta kallona har na tsargu. Na ce."" Wani abu ne ya faru?"""

"Ya girgiza kansa a tsanake ya furta."" Na gode mini giwar gidana."" Murmushi na yi wanda babu nisha'di a cikinsa na ce."" Godiyar ta mecece?"""

"Ya fito da wayarsa hotonan yaran yake kallo yana murmushi kafin ya nuna mini na kalla ban ce komai ba. Sai na ji ya ce."" Kin biya ni Amina, na kuma yafe miki abinda ki ka yi mini abaya."" Ya nisa kafin fuskarsa ta sake yalwata da annashuwa ya furta."" Da ki ka tashi ba ni yara sai ki ka ba ni biyu kuma masu kama da Samira Amina na gode, na gode wallahi idan na kalli yaran nan ina jin wani irin farinciki mara misaltuwa."""

Don Allah kada ki karanta mini littafi ba tare da kin biya ni hakkina ba.

"Sosai na iya danne tsaki da harshe da gand'ar bakina ke ko'karin furzarawa. Na ce."" Na farko dai ba ni za ka yi wa"

"godiya ba Allah za ka godewa domin shine ya baka ba Amina ba. To ai yanzu ka fadi dalilin da ya sanya ka dimaucewa akan yaran bawai a karan kanka ba ne, a a saboda suna kama da wata can daban. Hakan bai dame ni ba dama hausawa sun ce kyan d'a ya gaji ubansa, ka daina gode mini ka godewa Allah ko ka je ka tashi Samiran daga kabarinta ka ce kana yi mata godiya dalili yaranka sun yi kama da ita."" Tunda na fara maganar ban tsahirta ba sai da na dire tukkuna tsakin da nake ta dankwafewa sai da na furzar dashi domin idan bai fita ba akwai matsala, na koma na kwanta abina."

"Ya jima yana kallona da yanayi na mamaki da takaici kafin ya ce.'' Yanzu ina Samiran take Amina?"" Na ce."" Oho!"

"Sai ya gyad'a kansa ya tashi yana fad'in."" Ni ba zan yi rigima dake ba domin na gane so kike ki tsinka ni a cikin mutane don haka ki huta lafiya."" Ya juya da niyyar fita. Na kuwa bi bayansa da harara ban so ya kyale ni ba a lokacin na so ya tanka na amayar da b'acin ran da ya guma mini ahe da biyu yake ta abubuwa akan yaran saboda suna kama da inna Uwani da kuma 'yarta. Hawaye suka zubo mini na haifi yaran na ci wuya kuwa ta laulayi da zafin haihuwa amma ko yatsuna babu wadda ta d'auko Allah na tuba ka yafe mini."

Gida ya watse ya rage mu kad'ai. Ni da Hauwa muka cigaba da rainon yaran a wasu lukutan kuma Hajiya Maryam

"tana aikowa a d'aukar mata su, har su d'an jima a wajenta kafin su dawo."

Kwanana arba'in da takwas na shirya zuwa kano. Amma ina jimanta yadda zan yi dawaniyar yaran ni kadai dama burina idan na isa na samu Baba Tabawa mu yi magana idan ta amince mu tafi tare domin zamanta a tare da ni zai taimaka kwarai tunda kaf gidajensa daga na Legos din har na abujan babu mai aiki mace duk maza ne. Hajiya Maryam ce kawai naga tana da masu aiki dattijuwa mai suna Taburni Mairo kuma itace take yin dawaniya da yaran idan an akaisu can wajenta.

Ya ce Hauwa ta shirya sai mu tafi tare. Sosai na ji dadin hakan kuwa ban yi nauyin baki ba na yi masa godiya sosai ya ce kwana hud'u kawai ya ba mu dama za mu yi mu dawo. Kwanakin sun yi kadan amma ban iya gaya masa ba saboda Ina gudun ya ce ya fasa ma gabad'aya tunda har yanzu yana jin haushin abinda na yi masa sharewa kawai ya yi saboda yasan idan ya ce zai rama sai mun yi dan karamin ya'ki a gidan. Ni kuma fahimtar a kusa yake ya sanya nake ta lallabawa kada ya ce ba zan je ba.

***

Alhamdulillahi lafiya lau muka sauka a kano. Gidana na sharad'a muka sauka inda muka iske shi tsaf Baba Tabawa da Yusura sun gyara ko'ina har an yi mana abinci. Na yi mamaki kwarai da gaske nasan wannan aikin ba na kowa ba ne sai Sahura domin mun yi waya da ita ana i gobe tafiyar har ta na yi mini tambayoyi ashe abinda ta shirya kenan. Hidimar tace yin cefane mai kyau ta kuma sanya a yi mana abinci mai rai da lafiya. Cikin zuciyata na sake kud'ire wani alheri da ya jima a cikin zuciyata.

Da daddare Ayuba ya shigo mana da kayan abinci ya kai a store bisa umarnin maigidan ne ya tsaya muka gaisa sosai kafin ya juya ya fita.

"Ko da na gayawa Baba Tabawa kudirina ba ta yi jayayya ba ta ce ta amince za ta bi ni duk inda zan je, yadda na nuna mata tausayi da kulawa a lokacin da take neman d'auki yanzu ne daidai lokacin da za ta biya ni. Ina dariya na ce mata ai ni don Allah na yi mata ba don ta biya ni ba. Daga ranar kuwa ta shiga hidima da yaran bakid'aya."

To duk inda ya kamata na je a tsakankanin kwanakin da ya ba ni mun je ne tare da Hauwa domin duk inda na ajiye kafata itama nan take ajiye tata. Baba Tabawa na goye da Hassana ni ina goye da Usaina ita kuma Hauwa tana ri'ke da Khalil a hannunta.

Ayuba ne ke jan mu a mota rana ta farko a gidan Gwaggo na yini sai yamma muka yi mata sallama muka nufi gidanmu anan muka yi magariba. Sannan muka nufi gidansu Sahura dake kusa damu muka gaisa sosai da mamansu ta d'auki yara ta sanya musu albarka.

Washe gari a gidan Hamusu muka yini amarya ta zama 'yar gari Hamusu kuwa ya rasa Ina zai tsoma ransa ya kai ya

kawo ya siyo wannan ya ajiye ya siyo wannan ya ajiye bayan uban girkin da ya sanya aka yi mana. Sai da na ga abin ya yi yawa tukkuna na yi masa magana sannan fa ya dan samu nutsuwa.

Dubu ashirin na bawa amaryarsa na ce ta sayi janbaki ta kar'ba tana godiya ta rako mu har bakin gate.

Da muka fito tare da shi nake tambayarsa ya ake ciki da karatun Turmizi tunda shine ya shige gaba wajan kai shi makaranta kamar yadda maigidanmu ya yi alkawari nan yake ba ni tabbacin alhamdulillahi an samu cigaba kwarai da gaske domin hankalin yaron ya fara dawowa jikinsa domin lokacin da aka kai shi makarantar ma baya hayyacinsa

dalilin irin shaye shayen da ya fara yi ya hadu da wad'anda suka fi shi wayo suka bashi kwayoyi har hankalinsa ya

gushe garkuwar jikinsa ta raunana. A Tasha aka je aka d'auko shi yana zagari da kai kawo tare da sururai. Ya ce ko wancan watan da ya je dubasu ya same shi garau kuma ya kama karatu ka'in da na'in domin malaman a tsaye suke a kansa kuma makarantar cike take da tsaro babu ta inda yaro zai haura ya gudu.

Kamalu kuwa farkon watan da zamu shiga zasu sallameshi da izinin Allah dama kuma shi mun gama magana dashi zai zauna a hannunsa domin taimaka masa da cigaba da gudanar da harkokin da muke yi na kasuwanci.

"Rana ta uku kuwa da wuri muka fita saboda gida biyu nake so mu je, gidan Sahura da gidan Alhaji Muntari can muka"

fara zuwa saboda nasan idan gidan Sahura muka je da farko bai zama lallai ta bari mu fito da wuri ba.

Alhamdulillahi na ji dadin ganin yadda anti Maimuna ta samu nutsuwa ta kafa sana'a kala uku tana sayar da itace manyan d'auri sannan ga buhuhunan gawayi anan a jibge kusa da itacen sai manja da man kulli da take sayarwa galan-galan. Lokacin da muke je duka yaran suna makaranta tunda da safe ne. Na tambayeta Salima ta ce itama ta samu koyarwa a wata nursery dake bakin titi gaskiya ne a lokacin da Babansu yake raye ya yi kokarin sanya su a makaranta da wannan yarinyar ta tsira gashi har wasu suna amfana da iliminta kuma tana samun kwabo da dari.

Na tambayeta Jamila ta ce mini ta ji dai kwanaki an ce ta yi aure amma kuma tana zaune aka zo aka gaya mata wai an ganta a wani hausa film da ta yi bincike sai ta tabbatar da itace din auran ne ya mutu ta shiga wasan hausa.

Sai abin ya ba ni dariya da mamaki cikin zuciyata na ce to Allah Ya kyauta.

**

Yini zur muka yi a gidan Sahura ta dinga yi mana soye-soye har da su wainar fulawa. Ta soya mama dubalan cikin bokiti wai mu tafi dashi. Da daddare kuma ta hana mu tafiya sai da gama awara nan ma ta cika mana fulas wai idan muje gida sai mu ci a madadin abincin dare. Sahura kenan sarakan kirki da kyauta.

*GARKUWAR MATA.*

*BINTA UMAR ABBALE*

"[6/3, 8:38 PM] matar mijinta: *Wannan littafin na kudi ne vip 1k akan telegram. Normal What'sapp group kuma #700 hanyar da za a biya kudin ita ce wannan...0542382124...Binta Umar gtbank ko kuma 7084653262. Binta Umar"

Opey bank. 'Yan nijar dala dari katin airtel za ku tura mini bayan kun kankare hoton. A tura da sheda ta wannan lambobin iya What'sapp kawai.*

*07084653262*

*08089965176*

*V-VIP AREWA PEN *

*78*

"Washe gari ranar da za mu tafi kenan da wuri ya yi waya ya ce sha biyu ta yi mana a filin jirgi domin ya gama yi ma shiri, dama na gaya masa tare muke da Baba Tabawa ya ce babu damuwa, don haka da wurwuri muka shirya na ce Ayuba ya kai ni gidan Baba Sule domin shi kad'ai ne ban je na gaishe ba, ita kanta Hadiza na so na kai mata ziyara amma lokaci bai ba da damar hakan ba, sai da na bawa Ummansu kudi na ce a yi mata siyayya a kai mata."

A gurguje muka gaisa da Baba Sule da iyalinsa na yi musu alheri daidai Gwaggwo sannan muka nufi gidan Hajja wanda daga can din sai kuma mu wuce airport.

Hajja bakinta kamar gonar audiga ganinmu a tare kanmu a had'e sannan ga 'yan jikokinta da take ta burin Allah ya nuna mata su.

"Ita kyautarta dama ta turarece domin idan ta je saudiya su take sayowa da dayawa duk wanda ya ziyarceta ta bashi, ta had'o mana da yawa na jiki dana wuta tana ta yi mana addu'a da fatan alheri cikin tsananin farinciki mara misaltuwa."

Ganin da sauran lokaci da muka fito daga gidan Hajja na ce da Hauwa mu je gidan Hajiya Saratu don ni sai na ce

"zuwana gidanta d'aya tunda nake tunda bata fiye sabga ba yaranta duka biyu maza ne kuma babban yana can Egypt yana aiki da matarsa da yaransa. Mai bin sa kuma yana chana yana aikin koyarwa a wata makaranta, da yake wanda take aure dan boko ne sosai."

Shiru ta yi mini ba ta ce komai ba yanayinta ya nuna dai kamar ba ta son zuwa. Nan na fahimci cewa har yanzu akwai rashin jituwa a tsakaninsu tun daga lokacin da suka samu sa'bani akaina basu daidaita ba. Zaman amana muke yi a yanzu dole a tsakaninmu duk wanda ya hangi kuskure daga b'angaran d'an uwansa idan har da amana bai kyautu ace ya yi shiru ba mussaman idan aka yi duba da cewa ta dalilina suka samu matsala gashi zumunci ne mai karfi a tsakaninsu.

"Tun kafin mu shiga mota na nuna mata fa yana da kyau ta gyara domin kuwa kaf Hajiya Saratu ba'asar yin ta ba ce,"

"ta wuce matsayin Yaya a wurinta sai dai uwa, gashi kuma yayar mijinta ce dole ita za ta yi hakuri ta nemi hanyar daidato domin su gyara zumuncinsu tun kafin yaranta su fahimci halin da ake ciki."

"Jikinta ya mutu sosai a lokacin da nake yi mata maganar ba kuma ta yi mini jayayya ba ta ce mu je din, dama ai ita bata d'auka da zafi ba, ita Hajiya Saratun ce ta ga kamar har yanzu bata huce ba domin koda ta haifi Khalil ba ta je mata barka ba. Na ce mata kada ta duba wannan kawai ta yi 'ko'karin gyara kuskuran da ta yi a baya."

"Takuwa ji dad'i sosai da muka je gidan nata, kuma duk yadda Hauwa take d'ari-d'ari da ita sai ba ta nuna mata komai ba a fuska ba, ta sakar mata fuska kamar babu wani abu da ya ta'ba faruwa na saba'ni a tsakaninsu. Sosai na ji dad'in ganin yadda suka samu daidaito da fahimtar juna. Muka rabu cikin girma da mutunta juna ta yi mana alheri sosai tunda dama can a sanin da na yi mata itama hannunta a bud'e yake."

***

Bayan komawarmu da kwanaki uku na kira Hamusu a waya na ce masa ya fitar da kudi ya kuma nemi kwararrun ma'aikatan da za su gyara gidana na kuntau sannan ya sayi set din kayan d'aki da kujeru da gado labuleye masu kyau ya sanya a shirya gidan. Idan komai ya kammala kawai ya kaiwa Sahura mukkulin na mallaka mata shi gabad'aya tunda dama takardun suna hannunsa sai ya bata. Shi kansa ya taya ta murna sosai ya kuma bani tabbacin zai kammala komai a cikin sati d'aya.

To mun yanke shawara har da maigidan kan cewa tare za su sake komawa da Hauwa saboda yanayin garin koyaushe

cikin ruwa ake yi duk da gidansa ya sha bam-bam da sauran gidajen da suke garin legos amma dai hankalinsa ya fi kwanciya da mu zauna anan abuja zuwa wattani shida lokacin yaran sun yi k'wari sosai..

"Na ji dadin hakan sosai kuma na yaba da yadda suke nuna mini kulawa dashi da matarsa. Sai dai tunda muka yanke wannan shawarar nake cin 'kaniyata a hannunsa duk ranar girkina nakan ji jiki kwarai da gaske baya daga

Please Login or Register in order to submit comment