You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Muka gaisa da yake a d'aki ya same ni ban kai ga fita falo ba tukkuna na ce masa ya je ya gaishe da Hauwa da Baba Tabawa ya dawo. Ya fita minti biyar ya dawo ya zauna a gefena. Na dube shi a tsanake na ce."" Jiya mun gama magana da Hamusu a waya zan sanyaku a motar haya zuwa kano sai ku dinga waya dashi kafin ku sauka. """

"Ya ce."" Na ji dadin hakan Mama, kin ga kuma Baba bai jima da tafiya kanon ba don har d'akinmu ya same mu ni da Yusi yana tambayarmu zai je kano ko muna da sa'ko wurin Baba Hamusu."

Littafin nan na kudi ne don Allah kada ki karanta ba tare da kin biya ni hakkina ba

Shiru na yi ina d'an nazari tafiyarsa kano da gaggawa irin haka tana da ala'ka da kiran Hajja dama ta ce zata kira shi

babu tamtama kuwa wurinta ya tafi.

"Na ce. "" Hakan ya yi daidai ni ma na ji dad'i, ka je ka kira mini Yusi amma kada ka gaya masa komai."""

"Ya ce."" To shikkenan. Ya tashi ya fita da sauri. Ni kuma cikin gaggawa na shiga toilet domin yin wanka. Ina fitowa su Hassana suka shigo tsaf gabad'ayansu Baba Tabawa ta shiryasu. Na ce."" Kun zo mu gaisa ne, ashe kun san ni?"" Husaina dariya ta kama yi ta haye gado ta kwanta tare da sanya babban yatsanta a baki tana totsa."

"Na ce."" Ke ba ki daina tsotsar hannun nan ba dama."" Ta yi shiru ba ta ce mini komai ba sai ma ta janyo rigar baccina da na cire da yake mai laushi ce ta dinga shafa rigar da hannunta."

"Hassana ta je ta cire hannun daga bakinta cikin tsamin baki ta ce."" Momi fa ta hana ki."""

Na dube su Hassanar na cire hannun ita kuma Husainar na mayarwa bakinta. Na juya da niyyar bude wardrobe na d'auko kaya na ji kuka da k'arfi da sauri na dube su. Husaina ce ke kuka sosai ta cukume Hassana da kokawa Minal na gefe a tsaye tana kallonsu.

"Wajan na nufa ina fad'in."" Mai ya had'aku."" Cikin tsamin bakinta tana kuka ta ce."" Dutana ta yi, ina luwanta da ni."" Dariya nasa na ce."" Ke Hassana mai yasa ki ka duteta?"""

"""Momi ta hanata tsotsar hannu."" Ta ba ni amsa tana zum'bura baki."

"Kamulu ya shigo ya ce."" Fad'a suke yi ko Mama."" Na ce."" E dama haka suke yi a gidan Momin"""

"""Wallahi yini suke yi fad'a ai Mairo tana aiki kuma Hassana ce mai zalinci. Wataran Momi idan ta gaji dai sai ta cewa da Mairo ta goya Husaina don a samu mafita nan sai ta ce ba ta yarda ba ta dira kuka. Momin da kanta take cewa a d'auko mata zani sai ta goyata ake samun zaman lafiya."""

"Na ce."" Momin da kanta take goyo."" Yana 'yar dariya ya ce."" E, ai rigimar Hassana tana da yawa fa wasu lukutan"

"Momin ce take iya sarrafata ga gaddama da rashin yarda da mutane."""

"Na gyada kaina ban ce komai ba, zuciyata ta shiga zullumi da tunanin inda matar nan ta sa gaba akaina da yarana. "

*GARKUWAR MATA.*

*BINTA UMAR ABBALE*

"[6/3, 8:38 PM] matar mijinta: *Wannan littafin na kudi ne vip 1k akan telegram. Normal What'sapp group kuma #700 hanyar da za a biya kudin ita ce wannan...0542382124...Binta Umar gtbank ko kuma 7084653262. Binta Umar"

Opey bank. 'Yan nijar dala dari katin airtel za ku tura mini bayan kun kankare hoton. A tura da sheda ta wannan lambobin iya What'sapp kawai.*

*07084653262*

*08089965176*

*V-VIP AREWA PEN *

*TALLAH!*

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/BieW3hHvRNIJLFNloG2CDl

Momyn Hajara GHT supplements

Muna da kayan gyara jiki na maza da mata munada magungunan matsalolin ma'aurata munada magungunan

kowacce irin matsala in sha Allah

Hadin Amare

Hadin Ango Hadin jego Hadin uwar gida

Hadin babbar mace

Hadin maida tsohuwa yarinya

Muna da Maganin sanyi kowanne iri

Muna da maganin ulcer Muna da maganin Asthma

Muna da maganin ciwon zuciya Muna da maganin ciwon Hanta Muna da Maganin hawan jini Muna da Maganin ciwon Ido Muna da Maganin rashin haihuwa Muna da Maganin skeler

Muna da Maganin kowacce irin cuta da yardar Allah

Sannan kowa zai iyayin register da campanynmu maitarin albarka kasari kaya kasiyar kaci riba sannan Kuma

campany yadunga biyanka albashi Duk watan da kayi aiki Saida kaya shine aikin da zakayi campany ya biya 07012621175

Register 8000 ne kachal

*86*

"""Ina Yusi din yake?"" Na tambaye shi ba tare da na dube shi ba."

"""Gashinan zuwa, amma mama kin san ba lallai ne ya shigo shi kadai ba duk inda ya ajiye kafarsa anan Adam yake ajiye tasa. Ya ba ni amsa da dan sanyin jiki."

"Shiru kawai na yi ina nazari, Adam dai ko mayya ce ta haife shi dole su rabu domin kuwa"

"babu wani dalili da a yanzu zai hana yaran nan barin garin nan. Na ce."" Je ka falo, idan sun shigo tare ka turo mini shi."" Ya amsa da ""to shikkenan. Kafin ya sanya yaran a gaba suka fita."

Gama sanya kayana ke da wuya Yusi ya shigo ya sha ado cikin yadin kufta d'inkin kansa abin kallo ne ballantana takalmin da yake kafarsa. Babu shakka matar nan ta na hidima da yaran nan kuma duk abinda za ta yi babu bambanci abinda Adamu zai sanya a jikinsa shi Yusi zai sanya duk tsadarsa kuwa. Ko turarukan da suke amfani da shi wallahi sai mai karfin jari. Jikina ya yi sanyi kalau a yayin da nake duban yaron cikin Kamala da nutsuwa tare da kwarjini fatarsa luwai alamar hutu da jin dad'i sun ratsa jikinsa.

"Kafin ya zauna a gefana sai da ya d'an risina tare da furta."" Mama ina kwana, an tashi lafiya?"""

"Na amsa a nutse ina sake nazartarsa har yanzu babu walwala da sukuni a tare dashi tabbacin abubuwan da suke faruwa na damunsa. Ya nisa kafin ya sake fad'in."" Momi ta ce tana gaisheki ta ce na gaya miki za ta shigo idan an jima."""

"Sai da nutsu sosai na dube shi babu fara'a a tare da ni na ce."" Yusi ina so ka bud'e kunnuwanka da kyau ka ji abinda zan gaya maka, hukuncin na yanke kuma babu mahalukin da ya isa a wannan ga'bar da tura ta kai bango ya dakatar da ni."" Na yi shiru Ina kallonsa yayin da gabad'aya ya shiga nutsuwarsa alamun fargaba da tashin hankali sun gama bayyana a fuskarsa."

"Na cigaba da ce wa."" Hukunci na yanke akanka kai da d'an'uwanka Kamalu za ku bar garin nan gabad'aya rikonku zai koma hannun Hamusu za ku cigaba da ri'ke mini harkokina yanzu shirin da na yi kenan domin tun jiya na gayawa Hamusu halin da ake ciki saboda haka yanzu za mu je tasha tare na sanyaku a mota in sha Allahu rabbi."""

Matsananciyar damuwa ya shiga wadda baki ba zai iya misalta irinta ba. Ina kallonsa yana ta ko'karin mayar da

"hawayen da ya cika kwarmin idonsa amma duk dubararsa sai da ruwan hawayen ya kwaranyo kumatunsa. Murya na rawa ya ce."" Mama mai yasa za ki yanke wannan hukuncin, ki dubi Allah da Annabi ki janye kada ki hukuntani akan laifin da ba nawa ba. Ki dubi k'auna da soyayyar da Momi take yi wa jininki kada ki sanya 'yan uwanta su yi mata dariya. Mama ni da Adam akwai k'auna da sha'kuwa sannan ba na so na rabu da Baba, ba zan ta'ba mantawa da hallacinsa a gare ni ba. Sannan Momi tana nan tana yi mana shirye shiryen tafiya karatu saudiya makarantar da Yaya Salim ya yi karatu, ki yi hakuri Mama, kada ki hukunta Momi da laifin da itama ranta yake soyuwa."""

Ga'bo'bina ne suka yi sanyi ganin yadda hawaye suke zarya a dakalin fuskarsa. Ya kama hannuna ya ri'ke kamatau jikinsa har karkwarwa yake yi.

"Na ce."" Yusi ba ka ji wani iri a cikin ranka ba a lokacin da Salim yake yi wa dan'uwanka sharri, abu mafi muni fa ya jingina masa. Da farko ban d'auka abin ya yi tsanani ba na danni zuciyata duk domin a zauna lafiya. Amma Yusi ba abu ne mai wahala ba a yanzu dai na tsaya da Momi da Salim a gaban alkali domin yin shari'a dasu akan wannan mummunan sharrin da Ubangiji ya halakar da wani gari kacokan akan aikatawa. Sai dai na yi hakuri ne bisa abinda uwar rikon naku take aikatawa a kanku na alheri wanda idanu suke gani sanin bad'ini kuma sai Allah. Wannan shine dalilin da ya sanya ni tausar zuciyata akan danne maganar ba tare da na d'auki matakin kare hakkin Kamalu ba. Allah shahidi ne zai bayyana gaskiya da gaggawa. Yusi kana maganar ba za ka iya rabuwa da Baba ba shin zaka iya tuna ubanka Yaya Aminu? ko ka manta dashi ne tunda yanzu ka kasance cikin daula wurin iyayen rikonka har kake ko'karin canza shi a matsayin wanda ya zama 'kashin bayan samar da kai!"""

Na yi shiru Ina mayar da hawayen dake ta yun'kurin zuba.

"Shi kam kuka yake yi sosai. Cikin rawar murya na ce."" Nasan ka manta da shi ko Yusi, ni da nake raye a duniyar ma ka manta da ni to balle babanka wata'kila jin dadi ya sanya ba ka yi masa addu'a tunda ka nunawa duniya ka yi sabbin iyaye."""

"Hawayen da nake dannewa suka goce da karfinsu duka dinga fafara gudu a kumatuna. Na ri'ke hannunsa da kyau na ce."" Ka ture maganar sabo da hallaci da kyautatawa Yusi duka nasan mutanan nan biyu sun yi mini ko da ba don Allah suka yi ba to ni ma ina rokon Allah ya ba ni ikon rama musu, amma ba na ji a zuciyata za a samu zaman lafiya da juna muddin Kamalu da Salim suna zaune inuwa daya kuma a makwanci d'aya. Kun girma da kai dashi ku tafi ku taimakawa kanin babanku ku nemi arziki ta hanyar halak, ina da shaguna da dukiya a hannun Hamusu sai mu 'bullo da hanyoyin nema domin mu gina kanmu da gobenmu, watarana za ku yi aure, za ku hayayyafa a wannan lokacin ya kamata ace kun dogara da kanku Yusi ba wai a ce koyaushe kuna ra'be-ra'be a gidajen mutane ba."""

"Kuka kashir'ban yake yi yana fad'in."" Mama na fahimci azancin ki, na gane abinda ki ke so na gane, amma don Allah Ina neman alfarma a wajanki duk rintsi kada ki yi rigima da Momi wallahi mutuniyar kirki ce, ina kaunarta kamar yadda nake kaunarki Mama, kuma duk abin nan da yake faruwa babu sanya hannunta ko da anti Nusaiba ta dawo muku da yaran nan wallahi bata sani ba lokacin tana bacci da ta tashi ta samu labari wallahi sai da ran anti Nusaiba ya 'baci da kuka ta bar gidan. Ita kanta Momi ta rasa yadda za ta yi da su. Adam ne kawai bai shiga rigimar ba, Yaya Salim da anti Nusaiba sun had'e kansu sun daina jin maganar Momi."""

"Na ce."" Sai ka ce mara hankali Yusi, ba zan yi rigima da ita ba, to akan me? ai ta yi mini alheri, abinda dai nake so da kai shine ka samu nutsuwa ka kuma kwantar da hankalinka, maganar cigaba da karatu kuma ko ba ku fita waje ba sai ku d'ora a bayaro university ku kai matakin da kuke buk'ata in sha Allahu."""

"Ya rike hannuna yana kuka."" Mama zan bi umarninki zan yi abinda kike so muddin hakan zai sanya ki daina wannan kukan. Jin dadi bai sa na mantaku a matsayin iyayena ba. Babanmu duk lokacin da na yi sallah ina yi masa addu'a, ban manta daku ba Mama, ni dan halak ne ban mance wahalar rayuwar da ki ka sha a kanmu ba. Har abada ba zan canza ku ba."""

Na sunkuyar da kaina kasa ina tsiyayar da hawaye masu zafi da 'kuna. Gabad'aya duniyar ta gama fita daga raina saboda masifa da tashin hankali.

"Tsaf ya goge mini hawayen idona yana fad'in."" Ki yi hakuri Mama ki daina yi mana kuka don Allah."" Ban ce komai ba na tashi tsaye shima ya tashi tare da dafa kafadata da hannunsa."

Lokacin da muka fito falo Kamalu da Adam ne a zaune suna magana da sauri yaron ya zame daga kan kujerar da

"yake zauna yana fad'in.""Mama ina kwana mun tashi lafiya?"""

"A nutse na amsa da kulawa sai ya koma saman kujerar ya zauna jikinsa duk a sanyaye. Hauwa ta fito daga d'aki da tawagar yaran a bayanta tana fad'in."" Kun shirya kenan?"" Kafin na amsa Adam ya gaisheta ba tare da ta dube shi ba ta amsa kamar ba ta so. Na gyada kaina tare da kallon kamalu da kansa yake sunkuye na ce."" Tashi mu tafi."""

"Baba Tabawa ta fito daga kicin hannuntà ri'ke da madaidaicin baho da dabino a ciki. A nutse muka gaisa kafin na d'ora da fad'in."" Baba zan kai yaran nan tasha zuwa kano yanzu zan dawo in sha Allahu."""

"Ta ce."" To shikkenan sai kin dawo Kamalu a gaishe da mini da Gwaggo da kyau sai kun dawo Yusuf."" Yadda take"

magana shi ya sake tabbatar mini da cewa ba ta fahimci nufina ba domin kuwa da ta gane hukuncin da na yanke sai ta yi magana akan hakan.

"Adam da sanyi jiki ya dubi Yusi yana cewa."" Za ku je kano amma babu labari Yusi babu neman rakiya, ni ma ina so na je na gaisa da Gwaggo da Baba Hamusu."""

"Yusi ya riko hannunsa ya tashi tsaye muryarsa sanyi kalau ya ce."" Wallahi ban san da tafiyar ba sai yanzu ka yi hakuri d'an uwa, idan har za ka je sai mu je ai babu damuwa."""

"Da farinciki a fuskarsa ya furta "" Zan je mana bari na sanar da Momi kai kun yi sallama ko?"" Yusi ya girgiza kansa a hankali ya ce."" Zan shigo yanzu na yi mata sallama."

"Adam na fita ni ma na kama hanyar fita zuciyata cike da zullumi da nazari nasan ba karamin gagarimin rikici ne zai 'balle a gidan ba dalilin wannan matakin da na d'auka. Amma a shirye nake da tarar komai daga maigidan koda kuwa ta rabuwa ce. Ai an yi abinda aka yi, Allah Ya shige mini gaba."

Muna fita harabar gidan Masa'udu shine babban direbanmu da ya ajiye mana domin zurga-zurga dukda ba kasafai muke fita ba amma tun farko dama ya hana mu tu'ka mota a wasu lukutan ma ya gwammace shi da kansa ya ja akan wata daga cikinmu ta ja

Ya taso da sauri tare da risinawa yana gaishe ni na amsa a gurguje domin ba na so Adam ya sake shigowa ya same mu ban san mai zan ce masa ba.

"Cike da girmamawa ya ce."" Hajiya za a fito da mota ne?"""

"Kaina na girgiza a takaice na ce."" A a.'' Ya biyo bayanmu da sauri Yana fad'in."" Hajiya ki yi hakuri na kai ku don Allah"" Ya k'arasa maganar a raunane. Na Dan dube shi sai ya ba ni tausayi sosai suke ko'karin ganin sun ri'ke aikinsu sam ba sa son abinda zai 'batawa ogonsu rai ko su sa'ba umarninsa."

"Na ce."" Yi sauri to."" Da dan gudu ya nufi wurin da motocin suke ya fito da daya da gaggawa har zuwa wurin da muke tsaye."

"Kamalu ya bude mini na shiga na zauna kafin ya dubi Yusi cike da tsare gira ya ce."" Malam shiga mota.'' Ya shiga ba tare da ya ce masa komai ba sai da akwai damuwa Mai yawa a tattare dashi don sai waige-waige yake yi."

Sai da muka hau titi sosai hankalina ya kwanta domin ni kaina ina jin nauyi da kunyar yaron ina kuma fargabar ya zo ya riskemu ba zan iya ce masa tafiyar ba zata yiwu dashi ba.

"""Hajiya Ina muka nufa..... Muryar Masa'udu ta katse tunanin da nake yi "

*GARKUWAR MATA.*

*BINTA UMAR ABBALE*

"[6/3, 8:38 PM] matar mijinta: *Wannan littafin na kudi ne vip 1k akan telegram. Normal What'sapp group kuma #700 hanyar da za a biya kudin ita ce wannan...0542382124...Binta Umar gtbank ko kuma 7084653262. Binta Umar"

Opey bank. 'Yan nijar dala dari katin airtel za ku tura mini bayan kun kankare hoton. A tura da sheda ta wannan lambobin iya What'sapp kawai.*

*07084653262*

*08089965176*

*V-VIP AREWA PEN *

*TALLAH!*

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/BieW3hHvRNIJLFNloG2CDl

Momyn Hajara GHT supplements

Muna da kayan gyara jiki na maza da mata munada magungunan matsalolin ma'aurata munada magungunan

kowacce irin matsala in sha Allah

Hadin Amare

Hadin Ango Hadin jego Hadin uwar gida

Hadin babbar mace

Hadin maida tsohuwa yarinya

Muna da Maganin sanyi kowanne iri

Muna da maganin ulcer Muna da maganin Asthma

Muna da maganin ciwon zuciya Muna da maganin ciwon Hanta Muna da Maganin hawan jini Muna da Maganin ciwon Ido Muna da Maganin rashin haihuwa Muna da Maganin skeler

Muna da Maganin kowacce irin cuta da yardar Allah

Sannan kowa zai iyayin register da campanynmu maitarin albarka kasari kaya kasiyar kaci riba sannan Kuma

campany yadunga biyanka albashi Duk watan da kayi aiki Saida kaya shine aikin da zakayi campany ya biya 07012621175

Register 8000 ne kachal

*87*

"Muryar Masa'udu ta katse tunanin da nake yi. na sauke ajiyar zuciya a hankali na ce."" Kai mu jabi park."" Cike da bin umarni ya ce."" An gama."

"Motar ta yi shiru ni da yaran duka muna cike da zullumi mussaman Yusi da nake hankalce dashi yana goge hawaye a fakaice. Ban tsawatar masa ba domin kuwa ban san mai yake ji a zuciyarsa ba, amma zahiri wannan shine iya gatan da nake ganin zan yi musu a duniya. Ba zai yiwu a ce koyaushe rayuwarsu ta kasance cikin kyara da hantara ba. Sun fara kaiwa munzali na girma a wannan lokacin ya kamata ace mun had'u ni dasu mun gina gobe dalili watarana za su yi aure su tara iyali suma. Sannan zuciyata ba za ta iya cigaba da jurar ganinsu cikin kaskanci ba, arziki Allah ne yake bayarwa su fita su nema kowa ya tsaya da k'afafunsa."

Cikin ikon Allah motar dana sanya su ta yi lodi saura bai fi mutum hud'u ba. Cike da dauriya da ko'karin kara musu kwarin gwiwa muka yi sallama na ce lallai idan sun sauka Kamalu ya kira ni tunda da waya a hannunsu.

"Ban gushe daga wurin ba har sai da na tabbatar da tashin motarsu sannan na sauke ajiyar zuciya na gyara zaman nikab din da yake fuskata tunda ban fito ba sai da na sunkufe jikina ta ko'ina dalili ba na so a gane wata ala'ka da za a yi yamadidi da ni, kuma safiya ce tashar babu wadatar mutane da yawa sosai."

Kai tsaye na nufi wajan da Masa'udu ya ajiye mota.

"Yana ganina ya taso daga inda yake ya bud'e mini na shiga na zauna sai a lokacin na ji wasu gagariman hawaye masu radad'i sun k'wace mini. Wato ni kuma haka kaddarata take, ina ro'kon Allah Ya ba ni ikon cinyeta ya kuma saukakawa yaran nan rayuwa ya basu hakurin maraici."

"Ina komawa gidan na samu Hauwa da Momi zaune a falo, amma babu cikakkiyar sakewa a tsakaninsu Hauwa ta yi zaman gadara da ki ce kule na ce miki cass domin kuwa fuskarta tamkar kunun tsamiyar da ya kwana a rufe. Kusan a tare suka amsa sallamata."

Kwarai da gaske na yi kokarin danne abinda nake ji a zuciyata game da al'amuran dake faruwa. Na nemi wuri na zauna babu yabo babu fallasa nake kallonta ina sake nazari akan al'amuranta. Ta tsuke sosai ta yi fayau abinka da mara jiki da gasken ne bata da lafiyar domin alamu sun nuna babu wani kuzari da karsashi a tare da ita.

Ita ta fara gaishe ni a tsanake na amsa ido na a kanta ina sauraran abinda take tafe dashi ta gyara zamanta kad'an tana kallona sai ta sauke ajiyar zuciya a hankali

"Ta ce."" Amina na shigo nan ne saboda ke domin mu tattauna abubuwan dake faruwa da yaranmu, Allah Ya ga zuciyata ban shigo cikin rayuwarku da wata niyya ta cutarwa ba, kuma ban had'a kai da Salim domin ya ci mutuncin Kamalu ba, asali ma abinda yake aikatawa ba ni da masaniya sai bayan ya aikata din nake samun labarin."" Ta yi shiru tana sauke ajiyar zuciya a karo na biyu kafin ta cigaba da cewa."""

"Yana da kyau a matsayinki na uwa mai hankali ki yi nazari mai kyau Amina idan hankali ya 'bata fa nutsuwa da dattako ake sanyawa domin nemansa bai kamata ace kin d'auki munanan shawarwarin da ba za su zama silar gyar Hauwa ta katse ta cikin fusata."" tana fad'in ""Ai dama ban ce kin shigo gidan nan domin ni ba Maryam, ko"

"kuma kin ji na ce miki kin shigo ne da mummunar niyya. Kin tsargu ashe ai shi mara gaskiya dama kullum cikin zullumi Hajajju ki dube ni da kyau ki ga ni, a waye nake k'warai babu wata kinaya da za ki yi mini kafin ki san Amina da yaranta ni na santa na kuma zauna da ita. Idan har mijinki ya gaya miki cewa da hannuna wurin matakin da Kamalu ya d'auka bai yi miki k'arya ba, ga ni a zaune ai ina jiran hukunci tunda ku kun iya take gaskiya da gangan."""

"Cikin rashin sukuni na ce."" Hauwa menene don Allah, duk cikinmu nan babu yaro karami tunda har ta shigo domin"

"mu tattauna magana dan samun daidaito bai kamata wasu maganganu mara dad'i su biyo baya ba kuma."""

Ta ja dogon tsaki tana fadin

"""Kina jin irin jirwayen da take yi mini ai, ai mu 'yan iska ne marasa 'yancin kai tunda mijinta haka ya nuna mata ba mu da mutunci da kima sannan ba mu da sirri komai muka yi a tambad'e ita nata sirri koyaushe cikin danda'be shi yake baya so kowa ya ji. Bazan jure d'aukar cin kashi daga 'bangaranta ba wallahi tallahi."""

"A nutse ta ce."" Ba halina ba ne raina mutum Hauwa, kuma kamar yadda ki ke hasashe hakane maigidan ya gaya mini komai ke ce ki ke ko'karin ganin lallai sai an yi 'batacciya domin kuwa abinda muke ta bunnewa dalilin gudun rikici mai muni ke ki ka gayawa mahafiyar yaron nan, kuma ki ka cire nauyi da kunya ki ka dubi tsabar idon yaron nan Kamalu ki ka gaya masa to kin fad'a kin ji dadi kuma in sha Allahu abinda ki ke fata ba zai faru ba da izinin Allah."""

"Hauwa ta mike tsaye tana huci ta ce."" Kin yarda yaronki mahassadi ne, kuma sharri ya yi wa Kamalu ko ba ki yarda"

"ba, ke yanzu don girman Allah ba ki ji kunya da nauyi ba"

"ai ita karya fure take bata 'ya'ya wallahi ni dai Hauwa Maryam ba ki isa ki siye ni da kudi da abin duniya ba. Wannan gingimeman sharri da d'anki ya alak'anta marayan Allah dashi saboda rashin adalci da son zuciyarku sai ku ja baki ku yi shiru babu wani mataki da ku ka d'auka. Sannan kuce ba za a yi magana ba, to ni na sayi rikicin don girman Allah ki d'auki mataki a kaina. Kenan wannan ya nuna

Please Login or Register in order to submit comment