You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ba domin ba na so kuma wata magana ta yi tsayi a junanmu.

"A nan din ya yi sallar Isha'i, ya ce na d'umama masa ragowar towonsa na yi masa yadda ya buk'ata ya zauna ya ci sosai ya kira Sukairaju a waya suka yi magana duk ina zaune minti talatin ya iso har kofar gidan."

"Nan na fahimci ya kira shi ne domin ya ja shi a mota. Da zai tafi bai sake tayar mini da wata magana ba, sai kuma jikina ya mutu na d'auka zai sake yi mini maganar zabar gidan da zan zauna kamar yadda ya bukata. Cikakkiyar sallama ba mu yi ba ya kama hanya zai fita, na bi shi a baya da agogonsa da ya manta a kan katifa. Ya kar'bi abinsa kawai ya yi gaba, hakan da ya yi sai ya tsaya mini a rai, ita gaskiya d'aci gare ta, ban ga abin jin haushi ba tunda iyakacin bakin kokarina na yi masa."

"Koda na idar da sallar Isha'i sai na kira Sahura na ci sa'a ta daga muka gaisa na ce."" Kin daina jin haushina kenan?' Babu annashuwa ta ce."" Ba zan daina jin haushinki ba sai kin gyara halinki."""

"Ina dariya na ce."" Wani hali ne da ni mai muni Sahura."""

"Shiru ta yi mini ba ta ba ni amsa ba, na ce."" Mutumin fa anan gidana ya kwana"". Da mamaki ta furta."" Da gaske ?"""

"""Wallahi bai jima da tafiya ba ruwan jiya da daddare ya d'an same shi?"""

"Tana jimantawa ta ce."" Amina kin samu kan bawan Allan nan wallahi ki ji tsoron Allah, ban ga namijin da yake bibikon mace kamar na ki ba, ki zauna ki yi nazari ke kanki kin san idan baya tsananin sonki ba zai ta'ba yarda ya kwana a wannan gidan na ki ba."

"Ina dariya na ce."" Haka ma Anti Yagana ta fad'a ni kuwa jinku nake yi ni nasan wanene shi, amma kin san wani abu ya ba ni tausayi ni kaina wallahi ba ki ga yadda ya sha wahala jiya ba saboda dukan da ruwa ya yi masa ya lafke zazzabi mura tari da ciwon kai da kyar muka rintsa ga uban sauro da zafi a d'akin."""

"""Humm! ki bari dai ya k'wace miki za ki yi kuka wallahi."""

"""Ba wani kuka da zan yi Sahura ha'kuri da juna muke yi ni dashi fa kuma kune kuke ganin kamar ni nake cutarsa, mu bar maganar nan haka sis tunda kin kasa fahimta amma ina so ki san da cewa amaryarsa na d'auke da juna biyu d'azu yake gaya mini."""

"""To shine me? kema Allah Ya ba ki naki rabon ba shikkenan."""

"""Sahura ba na jin fa zan yarda na sake haihuwa haka kawai ba zan yanki tikitin wahala da hannuna ba."""

"A takaice ta ce."" Shikkenan ai."" Yadda ta fad'i maganar shi ya tabbatar mini da cewa cikin takaici take ta ce."" Wanki fa nake yi ki ka kira waya zan kashe."""

"Na ce."" Da daddare wanki Sahura?' ""Ina da me yi mini ne?''"

"Ta ba ni amsa a kufule?"""

"Na ce."" Ki had'a ki bayar zan biya."" ""A a, ni menene amfanin lafiyata."""

"Na ce."" Na ga alama rigima ki ke nema Sahura a ina zan samu mai kunshi ne?'' ""Muna da su anan sosai."""

"Na ce."" To ko za ki turo mini ita ta zo ta yi mini."" ""Idan hakan ya yi miki sai na turo ta."""

"Na ce."" Duk abinki dai ba zan yarda na yi fad'a dake ba Sahura."""

"Ta ce."" Dama kin ji na ce miki mu yi fad'a, ai gaskiya d'aci ne da ita."""

Tafad'a tana d'an jan tsaki.

"Na ce."" Ai na ji shawararki shiyasa ma na amince zan cigaba da zama dashi gashi har ina neman mai kunshi haihuwa ce dai na ce ba zan yi ba."""

"""To kada Allah Ya sa ki yi, idan kin samu cikin ki zubar kawai."" Ta datse kiran ba tare da na farga ba."

"Dariya na dinga yi mamakinta ya rufe ni wai lallai sai ta gaya mini bakar magana alhalin ba ita za ta yi mini zaman auran ba, mai d'aki shi ya san inda yake yi masa yoyo."

"To ashe da ya fita daga nan mutumin nan wurin Babanmu ya je. Ban san abinda ya gaya masa ba, ni wajejen tara da"

"rabi gama wayarmu da Sahura da kadan Babanmu ya kira ni ya rufe ni da fad'a har muryarsa tana rawa yana fad'in idan na janyo masa zagi a gari sai ya yi mini Allah ya isa tunda hakki na uba ya sauke mini amma ina nema lallai sai na guji aure na yi zaman kaina, muddin wannan hanyar zan bi to zai zare hannunsa daga kaina."

"Ban yarda na yi jayayya dashi ba na dinga bashi ha'kuri har sai da ya huci na kuma yi masa alkawarin bin umarinsa. Na jima ina jajanta lamarin yadda babanmu ya hasala yana nema ya yi mini baki shine abinda ya fi daure mini kai, Ina ganin da ya tsaya mun gama magana a tsakanimu zai fi ba wai ya yi yun'kurin had'a ni mahaifina ba."

Ba ni da lokacin tambayarsa akan dalilin da ya sanya ya yi mini haka hujjarsa kawai bukatarsa ta biya ta kowace hanya bai yarda da abinda ya aikata zai bata mini rai ba.

Da takaicin hakan na kwana a raina don har na yanke shawarar kiransa a waya na tambayi jikinsa amma hakan da ya yi mini yasa na share shi ban neme shi ba.

Da safe ya kira waya na d'auka muka gaisa ya fara tambaya ina maganarmu ta kwana. Na nuna masa ban san maganar da yake nufi ba.

"Ya ce."" Maganar barin ki daga wannan gidan naki."" Na ce."" Yadda ka ce haka za a yi."""

"Ina ji ya sauke ajiyar zuciya tabbacin maganata ta faranta masa ya furta."" Zan zo da daddare saboda gudun idanun jama'a, kamar yadda na fad'a sai mu je ki za'bi gidan da za ki tare."""

"A takaice na ce."" Sai ka zo?"""

"Ya ce."" Na gayawa Hajja tare muke dake kina can gidanku idan na zo sai mu je can ku gaisa ko?"" ""To, kawai na ce masa."

"Na kasa daurewa dai na furta."" Na gaya maka duk irin abinda za mu yi ni da kai ka daina had'a ni da mahaifina menene ribarka ta yin hakan, ai ni ba na gayawa mahaifiyarka abinda zai daga mata hankali."""

"""Ni ma na gaya masa ne domin na rasa yadda zan yi dake, nasan shi kadai ne zai tursasaki ki bi umarina tunda ni kin raina ni, Amina ai ba zalinci a zamantakewar auranmu, to ni ma don Allah kada ki zalince ni, sakin da na yi miki kuskure ne da zafin kishi ba zan boye miki ba ina mutukar sonki wallahi akwai kuma wani bakin kishi da yake damuna akanki idan ya motsa mini ni kaina tsanar kaina nake yi balle wanda zai kusance ni. Maganar nan ta mutu haka kada wanda ya ji, in sha Allahu hakan ba zata sake faruwa muddin kin kiyaye faruwar hakan anan gaba."

"Maganganunsa suka kashe mini jiki, tabbas kowane dan adam yana da dabi'a, kuma yana kuskure babu wanda ya cika cif kuma ha'kuri a rayuwar duniya ya zama dole mussaman a zama na aure."

"Dukda namiji ba a cika yarda dashi dari bisa dari ba, amma a wannan karon na dan ji tausayinsa kad'an kuma kalamansa sun yi tasiri a gangar jikina ya gaji zaman lafiya yake nema."

Sahura duk da ba mu rabu da annashuwa ba jiya sai da ta turo mini mai k'unshin da kwatance ta zo har gidan tunda

bashi da wahala a bakin titi yake.

Yarinyar ta iya kunshi sosai ta yi mini kafafu da hannuwa ja da baki wanda rabona da lallai tun na haihuwar baby Khadija. Sosai na fito kamar wata amarya na bata dubu goma Yusura ta je ta rakata bakin titi.

Da ya zo bai shigo ba ya kira ni a waya ya ce na fito na same shi. Hijabi nasa har kasa na rufe fuskata da nikab da zan

fita na ce Yusura ta kulle gidan ta ciki idan na dawo sai na buga.

Can tsallake na hangi motar wata kala ce daban domin bata nuna alamun tasa ba ce wata'kila ya yi hakan ne domin kada jama'a su gane wanene tunda duk motacin da yake tu'ammalli suna da alama wannan babu wata alama sai ta lamba. Sukairaju na jingine a jikin motar shi ma fuskarsa rufe da fece mark.

Ina karasawa ya risina mini muka gaisa kafin da sauri ya bud'e mini motar na fara ko'karin shiga yana hakimce cikin k'ananun kaya da rigar sanyi mai kauri a sama. Kansa sunfuke da hula irin ta sanyi har kunne ya rufe idanuwansa sakaye da gilashinsa na ka'ida.

"Na zauna sosai kafin Sukairajun ya shiga ya ja mota. A hankali na furta."" Barka da dare, ya jikin?"""

"Yana kallona ya amsa ""Barkanmu dai ya gajiya?"""

"Shiru na yi ban bashi amsa ba, shi ma bai sake magana ba wata'kila ya yi hakan ne saboda kusantuwar Sukairaju tunda kallon da ya yi mini da farko shi ya tabbatar mini da cewa akwai magana a bakinsa."

Gudun aure littafin kudi ne. Yi kokari ki sauke nauyi muddin kina karantawa

Gidansa na unguwar sharada kwanar ganduje wajan gidan Hajiya Mariya shi ya fi kwanta mini a raina dalili akwai

"alkarya a wuraran kuma daf da titi ne, bayan haka kuma ya yi kusa da wajan gidan Sahura dukda akwai 'yar tazara amma dai ba sosai ba za mu dinga samun sau'kin ganin ganin juna mussaman daga bangaranta."

"Gidane iya gida wanda aka narka dukiya wurin gina shi, gini mai k'wari da nagarta da kuma ababen more rayuwa sabo ne ga dukkanin alamu ba a jima da gama aikinsa ba. A gyare yake ko'ina sai da ba a shirya shi da furnitures ba da sauran kyale-kyalen zamani gidan ya yi mini sosai domin bai kai girman na legos ba ya yi daidai da zama babu tsoro da fargaba."

"Ya ce tunda shi na zaba to shi ma ya yi masa gobe kuma zai sanya a shirya mini komai na ce to shikkenan. Muka shishiga ko'ina muka duba muka hau saman benan ya bud'e wani d'aki a saman wanda shi kadai ne a dan shirye shi ma ba komai ba ne sai babban kafet da tuntu manya manya irin na sarauta uku, da manyan labuleye da suka kewaye d'akin."

Muka shiga d'akin yana gaya mini watani shida da suka gabata ya yi wani bako daga kasar senegal shine ya sauke shi a d'akin a dalilin tsaro da rashin yardar mutumin wai ya ji labarin najeriyar ta lalace da 'barayi masu satar mutane shine yake jin tsoron zuwa ya kwana a hotel. Anan ya sauka tsayin sati hud'u har ya kammala abinda ya kawo shi ya tafi.

Dariya kawai na yi domin nasan mutumin yana da gaskiya najeriya ta lalace sai da ta katsan-tsanan.

"Ganin ya nemi wuri ya zauna har da kishingida a jikin tuntu na ce masa yana da kyau ya tashi mu tafi saboda dare ya fara yi goma har da minti biyar ga gari na damuna, ga kuma yarinyar mutane na bari a gida ita kadai."

"Bud'ar bakinsa sai kawai ya ce."" Ai kin zo kenan Hajiya kayanki kawai zan tura Sukairaju yanzu ya d'auko miki."" Ya fad'a babu alamun wasa."

"Da mamaki mai yawa a tare da ni na ce."" Kai ma kasan hakan ba mai yiwuwa ba ne, ko ka manta da cewa na bar yarinyar mutane a gida, kuma me yasa Sukairaju zai je ya d'auko mini kaya ba ni da sirri ne, ai ba haka muka yi da kai ba."

"Ya tashi zaune sosai yana kallona ya ce."" Ba mu yi haka ba, amma yanzu na yanke hukuncin yin hakan domin ban ga amfanin komawarki wannan gidan ba tunda babu wanda za ki yi wa sallama."""

Raina a b'ace na tsaya kawai ina dubansa gabad'aya ma bakina ya mutu da masifar takaicinsa na rasa ma wane nazari zan yi.

"ya yun'kura ya tashi yana ce wa. "" Tunda ba ki aminta da Sukairaju ya d'auko miki kayanki ba ni ne ba kya so ba huta to zan koma tare dashi zan had'o miki kayan tare da yarinyar shikkenan ko "

*GARKUWAR MATA.*

*BINTA UMAR ABBALE*

"[6/3, 8:38 PM] matar mijinta: *Wannan littafin na kudi ne vip 1k akan telegram. Normal What'sapp group kuma #700 hanyar da za a biya kudin ita ce wannan...0542382124...Binta Umar gtbank ko kuma 7084653262. Binta Umar"

Opey bank. 'Yan nijar dala dari katin airtel za ku tura mini bayan kun kankare hoton. A tura da sheda ta wannan lambobin iya What'sapp kawai.*

*07084653262*

*08089965176*

*V-VIP AREWA PEN *

TEEMAH DATA SERVICES MTN

1GB @550

2GB @950

3GB @1450

4GB @1550

5GB @1700

CHECK CODE *323*4#

VALIDITY 30DAYS

CHAT@08112392177 CALL @08037026306

8037026306 fatima musa ibrahim opay

https://chat.whatsapp.com/K944WIHnBaKHDrZS6snUky

*TALLAH!*

"*Albishirinku mata ´an ™walisa matan da suka amsa sunansu mata, waWanda suka san sirri da fa'idar gyaran jiki domin ta da komaWar sha'awarsu. To ku matso kusa kuji, wai kuna da labarin shahararren kamfaninnan na ™awa da ™awa Waya tamkar da dubu, sha ™undum, mai suna?*"

*DUNIYAR LAFIYA ISLAMIC NATURAL PRODUCT & WOMENS CONSULTATION*

*Daga aunty Fatima Buhari rijiyar lemo 7ano state*

*Cibiyace da tai fice wajen gyaran ma'aurata*

"*Wannan kamfanin basu fito ba saida suka shirya tsab domin taimakon mata ta hanyar samar musu da magunguna ingantattu nagartattu wanda aka haWa da natural kaya cikin tsabta da inganci, komai a kwali yake ´ar uwa cikin tsabta da nutsuwa aka shirya muku*"

"*ina masu son soma kasuwanci ku matso Anty Fatima tana bada kaya a sari akan farashin da zaki gode mata, tana raba kayanta ga manyan shagunan saida magunguna dake cikin kasuwar kurmi dake kano, tana tura kayanta izuwa gari_gari ™asa_™asa. Kayan sari kona miliyon nawa kike da bu™ata zasu iso hannunki a cikin kwana biyu da izinin Allah*"

"*Ni Badiat Ibrahim Mrs Bukhari ™awar Sabuwan maigogul, Aminiyar Iyabo, uwar Wakin Tani Shanono na gwada na san amfaninshi, kema ´ar uwa ki kwada zaki bani labari siyan nagari maida kuWi gida.*"

*Mun sani yanzu yana da kyau duk abinda zamu siya musan ingancinshi da nagartarshi bawai muita siyan magungunan mata kara zube ba.*

"*Wannan kamfanin kayansu babu algus ko almundahana a ciki, da tsoron Allah da ™warewa gami da gogewa ta sanin* *yadda ake sarrafa magunguna suke aikinsu, cikin nagarta da gangariyar tsabta.*"

*Abu mafi sha'awa komai a cikin kwali yake a rufe kirib*

*ga kaWan daga cikin abubuwan da kamfanin yake samarwa*

*Tsumin dadi har Madiga tareda gunbarshi*

*Tsumin no excuse mela™abin bita zaizai*

"*Gumbar dare daya wanka goma, dana gari da zumarta da tsuminta duk muna dashi*"

*Zumar hana bacci gumbarta da garinta*

*Munada Arabian sabaya tare d Sudanese sabaya*

*Da zumarta*

"*Sabaya ce dake cuko da ´a mace duk ramarta, da ™anjamewarta*"

*Itama da zumarta*

*muna da mummuna da aiki*

*Akwai tsumi da gumbar ta da zaune tsaye*

*muna da kogin daWi*

*Abangaren sanyi sun samar ma mata maganin matsolilinsu*

*muna da fitattun maganin sanyin da yake fata_fata d sanyi yayi mishi korar kare*

*Khanzur Rahman herbal formular*

*Sanyi clear syrup*

*7 days for chronic infections flusher*

*Sannan kuma muna da* *Package amarya*

*Package Uwargida*

*Package irin na zawarawan da suke shirin sabon aure*

"*Bugu da ™ari wannan kamfani yana sarrafa magungunan maza ba a iya na mata ya tsaya ba, wannan kamfani magungunan da yake samarwa suna da yawa wannan tsakurene daga cikin kayansu*"

*Da sauransu da sauransu wanda bamu ambata ba.*

*Ba fa a iya haka muka tsaya ba muna d cancada cancadan zannuwan Gado da carpet*

*Domin neman ™arin bayani ku tuntuSeta a kan lambar wayarta kai tsaye*

+2348032089456

*49*

"Zuwa la'asar gidan ya shiryu ta ko'ina har kicin komai ya ji, da alama masu aikin sun jima suna murza zaransu domin ni na d'auka za su iya kaiwa dare basu gama ba."

Suka tattara kayan aikinsu suka tafi lokacin ma shi maigidan yana bacci saboda ya sha magani. Ni da Yusura muka zagaye ko'ina dakuna ukun da suke falon dukkunnsu a shirye kowane da set din gado kewaye da labuleye masu kyau falon set din kujeru biyu ya ci masu kyau da tsada da labuleye wad'anda suka dace wurin tibi ma yasha ado mai d'aukar hankali ko'ina hasken fitilu irin na zamani sun shirya mini kicin dina tsaf duk abin buk'ata babu wanda babu da alama kamfanin sun jima suna yi masa aiki.

Sukajiru ya dinga shigo da kayan abinci yana jibgewa a store din dake cikin kicin din da yake da yalwar gaske.

Gidan ya ba ni sha'awa sosai kuma daidai misali domin bai cika girma na d'aukar hankali ba sai dai an tsara shi sosai daidai zaman da babu tsoro kuma babu takura.

Da fargaba na tashe shi domin yin sallar la'asar ganin hud'u har da rabi ta yi nasan ba a yi masa gwaninta wani

"lokacin to amma ai babu biyewa son rai wurin take umarnin Ubangiji ina ganin idan har na bar shi ya cigaba da barcin lokacin sallar ya kure ina da lefi, bayan haka kuma shi kansa baccin gabanin la'asar ko bayanta Annabi ya yi hani dashi."

Ya tashi kuwa da d'an sau'ki jikin nasa don har gumi yake yi yana gabatar da sallar ya nemi abinci don da alama cikin magunguñan akwai wanda ya ke bud'a ciki kuma wai towon dawa irin wanda na yi masa a gidana.

Ban yi masa jayayya ba na fita na duba cikin store din duk kayan masarufin da Sukairaju ya zube babu na towo babu dawa balle alkama sai samovita sai shinkafar towo.

Na fita na sanar masa Ina dasu a gidana zan kira Hamusu yanzu sai ya je ya kawo mini. Da yake yana buk'ata bai ce a a ba.

"Na kira Hamusu na yi masa bayani sosai yadda zai fahimta na kuma bashi kwatancen gidan, da yake dan halak ne awa daya da yan mintoci sai gashi a babur dinsa ya kawo mini komai."

"Sosai ya ba ni tausayi saboda hidimar da yake yi a kaina ko ciki daya muka fito iyakacin abinda zai yi mini kenan. Ya kuma ki tafiya wai lallai yana so ya gaisa da magidan kafin ya tafi. Sai na nufin saman zuciyata na dan bugawa na same shi yana waya da wani mutum na dan tsaya kimanin minti goma ya kammala kafin ya dube ni kadaran kadahan na ce."" Hamusu ne yake so ku gaisa yana kasa na ce bari na nema masa izini."""

"Ya d'anyi jim kafin daga bisani ya ce."" Ya shigo mana."""

"Na juya babu k'wari a jikinsa. Na same shi a falo suna dan hira da Yusura na ce .'Ka hau saman d'akin da yake kallonka yana ciki.."""

"Ya tashi da sauri yana fadin."" Bari na sauko yarinya sai kin gaya mini sunan saurayinki tunda ni ba kya sona."""

"Na dube shi da mamaki yana hawa benan na dawo da kallona kanta sai sinne kanta take yi na ce."" Cewa ya yi yana sonki ne?"""

"Ta daga kanta tana dariya kafin ta ce."" E, mana, ni kuwa na ce masa ai ina da saurayina."""

"Murmushi na yi da cewa."" A Ina saurayin naki yake ko shine dan gidan Yayar babanku wanda Sahura take gaya mini."" Ta daga kanta da kunya mai yawa a tare da ita. Na ce."" Hamusu kenan shi ma ai da alkawarin auran wata a wuyansa ko ta biyu zai yi dake ne?"""

"Da sauri ta ce.'' A a mama ni fa ba na son kishiya."" Ta fad'a har muryarta tana rawa nasa dariya ina fadin."" To shi wanda kike so din kina da tabbacin ba zai yi miki kishiya ba."""

Shiru ta yi bata ce komai ba. Sai kawai na girgiza kaina na wuce kicin da tunanin halin kuruciya yarinyar.

Cikin nutsuwa na fara gudanar da aikina gefe guda kuma ina cigaba da nazarin yanayin rayuwar nan ta duniya wato dai muddin kana raye ka dinga ganin abubuwan al'ajabi da ban mamaki kala kala.

"Muryar Hamusu na ji a kicin din yana fad'in."" Anti ni zan tafi?''"

"Na juyo Ina dubansa yanayinsa ya nuna mini ba a nutse yake ba domin damuwa muraran ta bayyana a tattare dashi. Cikin nutsuwa na ce."" Shigo ciki mu yi magana."""

"Ya shigo yana sunkuyar da kansa kasa, tausayinsa ne ya kama ni har na ji kwalla ta cika idona tabbas mutumin nan akwai maganar da ya gaya masa wadda ta sosa masa rai da wahala ka ga Hamusu cikin irin wannan yanayin mutum ne mai ha'kuri da yawan fara'a ba ka taba gane yana cikin damuwa koda kuwa akwaita a tare dashi."

"Na ajiye rariyar da take hannuna na ce."" Ko ba ka gaya mini ba nasan abinda yake da akwai amma ina so ka sani ban goyi da bayan wannan zargin da ake yi maka ba, kuma duk inda za mu je ina nan akan bakana ban goyi da bayan a tozartaka ba a shirye nake da kare ka a ko'ina ba zan yarda a wulakantaka ba Hamusu na zauna dakai nasan halinka kiyashi ba zaka kashe da gangan ba balle har ka yi yun'kurin kashe mutum. Bincike dai ban hana shi ya yi ba,"

"amma rashin sanin wanda ya aikata ba zai sanya a gazgata cewa kaine ba, ai alheri ba ya zama sharri Hamsu ka"

samu nutsuwa kuma kada kada damu gaskiya zata bayyana.

"""Wallahi anti gabad'aya a cikin fargaba nake ya za a yi na aikata wannan mummunan aikin me ya yi mini da zan yi yun'kurin kashe shi a yake gaya mini fa wai lallai da sanya hannuna wurin faruwar hakan, wallahi tallahi anti ban aikata ba, ai mutumin nan alheri ya kamata mu yi masa duba da abubuwan da yayi mana na sadaukarwa da taimaka ko k'aunar jininmu da yake yi ya cancanci sadaukarwa ta kowane fanni, shiyasa hidima idan tasa ce wallahi ba na gajiya koda kuwa zan kwana a tsaye. Na yi mamakin jin wannan furucin daga bakinsa anti duk da duniya ta lalace akan samu irin hakan amma wallahi ni ba na daya daga cikin butulayen mutane."""

"Na ce."" Kada da ka damu Hamusu ka shige ka je ka cigaba da sabogiginka hankalinka kuma ya kwanta barazana yake yi maka domin akan bincike yake har yanzu shi ma bai gama tabbatarwa ba."""

"Ya girgiza kansa a sanyaye ya ce."" Shikkenan anti ni ma kuwa ba zan bari ba wallahi zan tsananta bincike na kuma sanya ido domin tonuwar asirin wad'anda suka aikata hakan."""

"Na ce."" Shikkenan hakan ya yi amma don Allah kada ka gayawa kowa maganar nan Hamusu ka barta cikin ranka."" Ya ce."" Na yi alkawarin yin hakan in sha Allahu rabbi anti."

To har na gama aikin zuciyata ba ta daina tsalle ba. Nasan idan na tunkare shi da maganar tutsiyar da ya yi wa

Hamusu cibi ne zai zama 'kari dama mai neman kuka ne aka jefe shi da kashin awaki sai kawai na share shi ban nuna masa cewa nasan abinda ya yi ba.

Sai da na hada masa komai tukkuna na sauko daga saman na samu Yusura ta yi wanka ta shirya tsaf na ce taje ta d'ebi abinci wanka zan yi tukkuna.

Littafin gudun aure na kudi kada ki karanta ba tare da kin biya ni hakkina ba.

Na shirya cikin doguwar riga ta atamfa duka kala shida na zo dasu hud'u sun yi datti saura biyu kacal itama Yusuran

nata sun yi datti na ce da safe sai ta wanke mana tunda akwai na'uwarar wanki a gidan.

Sai komawa na yi saman a karon da ba zai lissafu ban ji matsalar hawa tunda kamar ina motsa jikina ne

Please Login or Register in order to submit comment