You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

shi ba saboda bai nemi hakan ba. Ina nan a tsaye ban kai ga zama ba ya sauko yana cewa ya ki ka tsaya anan Amina.

"Ban ce masa komai ba illah ido da na zuba masa. Akan wanene dalili zan bi shi ai yana da kyau a ce ya fara shiga ya sanar mata tunda ba a san a halin da take ciki ba. Idan shi mijinta ne ni kuma fa, wata'kila hakan bai zai yi mata dad'i ba."

"Bayansa na bi muna hawa benan yana sake tisa maganar wai na tsaya ina ta d'ari-d'ari na'ki sakin jikina. Na yi masa shiru ban tanka masa ba. Da dai naga ya'ki ya bar maganar daf da zamu shiga d'akin na tsaya Ina dubansa babu fara'a a tare da ni na ce ."" Don Allah maganar nan ta isa haka fa, ina dalili sai maimaitawa ka ke yi, ai ba daidai ba ne kai tsaye kawai mu kutsa mata d'aki idan kai babu lefi hakan ni kuma fa, ai ba mu san halin da zamu same ta ba."" Yadda na nuna 'bacin raina akan hakan ya sanya bai sake wata magana ba muka shiga d'akin. Na yi kokari sosai wajan ganin na daidaita yanayin da nake ciki."

Tana zaune gefan gado sanya da kayan bacci masu taushi a jikinta. Wata kujera dake can gefe ya nufa ya je ya zauna shi kadai nasan ya yi hakan ne domin mafitarsa yana tsoron ya zauna kusa da wata daga cikin hakan ya zama lefi shiyasa ya ke'be kansa waje daya.

"Sosai muka gaisa cikin sakewa tunda dama ita din macace mai fuska da iya hurd'a da mutane. Babu wani abu na kishi da ganin kyashi da na karanta a tattare da ita. Sai dai na hangi tsantsar soyayyarsa a cikin idanunta. Domin kuwa motsi kad'an za ta juya ta kalleshi ta dinga kokarin janyo shi cikin maganar da muke yi a tsakaninmu ni da ita amma ya'ki ya sake ya dai 'kyalemu muna hirarmu. Daga karshe ma sai ya sauka kasa ya bar ni tare da ita. Anan na dinga nazarinta duk da dare ne na fahimci tana jin jiki kuma murar ta kama ta da k'arfi. A lokacin sai kawai zuciyata ta dinga raya mini wani abu wai ko ciki ta samu domin sai nake ganin yanayinta kamar na mai karamin ciki. Kirjinta ya ciko ko bireziya ce oho, ni dai sanin da na yi mata zaman makokin mijinta bata da wadatattun kirji"

ita kanta ma gabad'aya ta murmure ta yi ki'ba amma ba sosai ba. Sai jikina ya k'ara yin sanyi da al'marin Ubangiji. Lallai ciki ne da ita kuma shine dalilin da ya sanya duk ya gigice tunda abinda yake nema ne ya samu.

Duk da ban tabbatar da hasashena ba amma tun a lokacin na ji na fara tausayin kaina. Zuciyata ta dinga yi mini munanan tunane-tunane. Idan ma har na samu cikin na haihu yarana ne za su tashi daban a gidan masu d'auke da wata lalura idan da k'arar kwana kuma d'aya bayan daya duk su mutu.

Da wannan tunanin na kasance har muka bar gidanta daurewa kawai nake yi amma gabad'aya zuciyata ta kasa juriya sai da na buya a toilet na ci kuka na 'koshi na dinga yin istigifari da rokon Allah ya sassauta mini abinda nake ji a cikin zuciyata.

"Washe gari da safe sukuku na tashi babu karsashi a tare da ni. Haka kawai abinda ba ni da tabbas akai ya ke nema ya daga mini hankali. To menene ribar auran ne haihuwa ce, mai yasa nake jin b'akinciki dan matarsa ta samu ciki. A ganina ai abin murna da farinciki ne a gare mu bakidaya, kamar yadda nake jin dad'in haihuwar Hauwa yana da kyau itama wannan din na yi farinciki idan har hasashena ya zama gaskiya. Amma sa'i guda na ji duk tawakkalin da na fara dangane da al'amarin ya ruguje, wani mahaukacin kishi yana nema ya zautar da ni."

Shirun da ya yi mini bai gaya mini matarsa tana da juna biyu ba shine abinda ya yi mini ciwo a ganina menene abin

"boye mini, idan ba yana nufin wani abu ba. Ko yana gudun ya gaya mini na ji haushi ko na nuna b'akincikina. Duk da bai zama dole a ce ya gaya mini abinda ya shafe shi da matarsa ba, amma ai idan da fahimtar juna da zama na amana ba lefi ba ne don ya gaya mini sai mu had'u mu yi farincikin tare gabad'aya."

Na yi ta ko'karin ganin na danne damuwar da nake ciki amma ina sai da ya fahimci wani abu yana damuna.

"Ya dinga bibiyata duk domin son ya ji abinda yake damuna kawai na ce masa babu komai. To ne zance masa ni ban iya 'karya ba balle na yi masa, babu kuma dad'i na fito fili na nuna jin haushina dan matarsa tana da ciki."

Kwana biyu a tsakani ya gaji da tambayata ya kyaleni kawai ya zuba mini ido tunda ya lura da cewar ba na son doguwar hira sai ya daina nema da ita. Amma baya fashin kwanciya da ni duk ranar girki na. A haka ya yi kwana biyu

a wajena ya koma gidanta a washe garin ranar ya shigo da safe lokacin ma ban ma tashi ba tunda na yi sallar asubahi

bacci ya d'auke ni mai nauyi. Shine ya tashe ni da farinciki yana gaya mini yanzu nan Hauwa ta haihu.

Ganin yadda yake cikin annashuwa da murna ya sanya ni dole ni ma na ara na yafa ina tambayarsa abinda aka samu namiji ne kuma gabad'aya suna cikin koshin lafiya.

Fatan alheri na yi musu gabad'aya tare da addu'ar Allah ya raya abinda aka samu. Ya kuma bada lafiyar shayarwa. Ya ji dad'i kuwa ya dinga amsawa cikin jin nishadi.

"A ranar ya shirya tafiya bauchi da nufin zuwa ya je ya dawo duk a ranar tunda tafiyar jirgice. Ban damu ba tunda ba kwanana ba ne, na yi masa addu'a da fatan alheri ya tashi ya fita domin zuwa ya kintsa."

Don Allah kada ki karanta mini littafi sai kin biya ni hakkina

Sai bayan ya tafi tukkuna na shiga tunanin da na sani na kar'bi lambar wayarta a wurinsa sai na kira ta na yi mata

"barka tunda rantsuwar nan da na yi tana nan ba zan sake taka k'afata garin ba sai dai duk abinda za a ce an jima ba a fad'a ba, wannan duniyar idan har mutum ya ce sai ya farantawa wani rai yana tare da wahala domin kuwa wasu lukutan ma wanda kake kokarin ganin ka bashi farinciki shine na gaba gaba wajan ganin ya jefaka a masifa. Baban Saude ba irin nasihar da bai yi mini ba akan zama lafiya da abokanan zamana, na kuma d'auki nasiha da shawararsa duk wadda ta shirya zaman lafiya da ni, to ni ma a shirye nake dana zauna lafiya da ita, amma wadda take ganin ta fi karfin ta ba ni girmana na babba a cikinsu sai ta yi rayuwarta ni ma na yi tawa."

Wannan shawarar na yanke a zuciyata wani sashe yana gaya mini cewa da duniya zata zageni hakan zai sake tabbatarwa da masu zargina cewa ina hassada da ciki da haihuwar. Tunda ai tun farkon samuwar cikin an sha rigima da ni akan wani dalili.

"Ni ba zuwan ne matsala ba a wajena ba, Ina gudun kallon banza da habaici shine kawai abinda nake tunani, ba na so a yi mini abinda zai hasalani na kasa jurewa na aikata abinda bai da ce ba."

To daga cewa zai je ya dawo a yini sai gashi sai da ya share kwanaki uku tukkuna kafin ya dawo sauran kwana

dayan Hajiya Maryam da kwana biyuna ya yi su ne a tare da Hauwa.

Ban damu ba saboda nasan hakan da ya yi shine daidai yana da kyau itama ya zauna da ita sosai domin su tattauna abinda ya shafe su.

Da daddare ya dawo wajan goma da rabi har na kwanta ya shigo yanayin dana gan shi ya nuna mini cewa ya d'an jima da dawowa domin jallabiya ce a jikinsa. A can gidanta ya sauka zai cike mata cikon kwana dayanta.

"Ya zauna gefena ni kuma na tashi zaune Ina laluben hulata data fadi na mayar kaina a nutse na gaishe shi ya amsa yana yi mini wani irin kallo. Hakan ba sabon abu ba ne a wajena domin ni kaina na kan rasa me yake kallo a jikina babu dai abinda bai sani ba, babu kuma sabon abu."

Saukar hannunsa na ji saman kirjina. Da sauri na ture ina dan hararsa. Ya sake matsowa jikina na matsa da baya Sai ya tsaya yana kallona kafin ya gyad'a kansa kamar wadda ta yi masa mugun lefi.

"Na daure tare da ce wa."" Ina Hauwa da jariri suna nan lafiya?"""

"""Lafiyarsu."" Ya fad'a yana duba wayarsa kafin ya miko mini wayar yana fad'in."" Kin ga hoton jaririn."""

"Na kar'ba da sauri ina dubawa. Kamarsu daya wallahi, ina dariya na ce."" Kamarku daya fa Baba, wannan yaron hotonka ne."""

"Da d'an murmushi a fuskarsa ya ce."" Haka mutane suke ta fad'i Hajja tana gaisheki yaushe za ki je ne?"" Shiru na yi ban bashi amsa ba, ina ta duba hotonan yaron da yake cikin wayarsa."

Sai ya sake maimaita tambayarsa.

"Ba tare da na dago kai ba na ce."" Gaskiya ba zan rufe maka ba babu inda zan je."" Ya dube ni da wani irin yanayi kafin ya furta ."" Akan wane dalili, mai aka yi miki?"""

"""Ba a yi mini komai ba."" Na fad'a cikin mamakin yadda aka yi ya manta irin wulakancin da suka hadu suka yi mini har da shi. Hauwa na je garinsu cikin gidansu amma bola ta fi ni daraja suka mayar da ni abar nunawa da yi wa dariya ita da 'yar uwarta."

"""Idan kuwa hakane babu wani dalilin da zai sanya ki ce ba za ki je ba Amina muddin zan bada umarni ki bi shi."""

"Hawaye ya ciko idona na ce ."" Don Allah kada ka takura mini, ka kyaleni na ji da abinda ya dame ni, ba zan je fa domin kuwa ina da dalilina, idan kai ka manta ni ban manta ba."""

"Ya gyara zama yana kallona tare da cewa."" Ni ban manta komai ba Amina, ki fito fili ki gaya mini abinda yake damunki ba ki zauna kina barin shi a cikin ranki ba, na lura kwana biyu nan tun kafin Haihuwar nan ba ki da walwala ina alkawarin da muka k'ulla dake?"""

"Hawayen dake cikin kwarmin idona ya d'igo. Na sanya hannu na goge tare da ce wa."" Ai ni ban k'ulla alkawari da kai"

"ba saboda na san ba iya cikawa za ka yi ba, kawai mu yi ta zama a haka cikin munafurtar juna."""

Sai kawai ya yi sakare da baki yana kallona. Ni kuma ina ta kuka kamar wadda aka yi wa rasuwa. Gadon ya hayo sosai

"ya riko hannuna kafin ya ce."" Munafurci na yi miki?"""

"Shiru na yi ban tanka masa ba. Ya ce."" Ki tona mini asiri kawai ba wai ki dinga b'oyewa ba, ki gaya mini hak'kinki dana take tun zuwanmu nan, ashe duk takatsantsan din da nake akan kada wadda ta zarge ni a cikinku wato hakan bai yi miki ba, kina yi mini wani irin kallo."""

"Hanci na ja, na cire hannunsa da yake cikin nawa na ce."" Idan zaman gaskiya da amana muke yi menene na 'boye mini matarka tana da juna biyu, ai na gane nufinka kada ka gaya mini, na ji haushi ko na yi mata hassada ko?"""

"Da wani irin yanayi ya furta."" Wace matar tawa ce take da ciki?"""

"Kallonsa na yi, muka had'a ido, sai na d'auke kaina ban ce masa komai ba"

"Yasa hannu ya dago kaina ido cikin ido ya ce."" Ki gaya mini wacece take da ciki."" Na ce.""Amaryarka?"""

"""Ita ta gaya miki tana da juna biyu?"""

Shiru na yi domin ba ni da amsar da zan bashi sai na ce masa alamar hakan na gani. Sai a lokacin ma na fara jin kunya da nauyin abinda nake yi wanda hakan zai sanya shi saurin gano cewa kawai zafin kishi ne yake damuna...

*GARKUWAR MATA.*

*BINTA UMAR ABBALE*

"[6/3, 8:38 PM] matar mijinta: *Wannan littafin na kudi ne vip 1k akan telegram. Normal What'sapp group kuma #700 hanyar da za a biya kudin ita ce wannan...0542382124...Binta Umar gtbank ko kuma 7084653262...Binta Umar Opey bank. 'Yan nijar dala dari katin airtel za ku tura mini bayan kun kankare hoton. A tura da sheda ta wannan lambobin iya What'sapp kawai.*"

*07084653262*

*08089965176*

*V-VIP AREWA PEN *

*74*

"Ya jima yana kallona jin ban bashi amsar da ya tambayeni ba sai ya gyad'a kansa a nutse ya ce."" Ni ne dai mijinta Ina ganin kafin ta gayawa kowa tana da juna biyu ni za ta fara gayawa, amma tunda maganar ta fito daga bakinki tabbas nasan ba 'karya ba ne, zan je na tambayata na ji dalilin da ya sanya ta 'boye mini abina."""

"Ri'ke hannunsa na yi a sanyaye na ce."" Kada ka tambayeta don Allah."""

"""Akan wane dalili?"" Ya fad'a cikin wani irin yanayi. Shiru na yi ban iya ce masa komai ba. Sai ya sake maimaita tambayar da ya yi mini a karo na biyu."

"Na daure cikin daburcewa na ce."" Ni ma fa ba gaya mini ta yi ba kawai ina hasashene."""

Ya zuba mini idonsa 'kuri yana kallo. Nauyi da kunya ya sanya na yi kasa da nawa idon. Sai ya yi murmushi.

"mai sauti kafin ya ce."" Momi ba ta da ciki Amina, domin kuwa da tana da shi nasan ba zata rufe mini ba zata gaya mini tunda tasan abinda nake nema ne ido rufe, daga yau ki daina yanke hukunci akan abinda ba ki da tabbas akai."" Na yi shiru ban tanka masa ba, domin kuwa ni kaina nasan ba ni da abin fad'a kuma ya fi ni gaskiya to idan ma cikin ne da ita menene abinda ya dame ni."

"Kamar yasan tunanin da nake yi kenan ya matso kusa da ni sosai yana cewa."" Ni zan fi so ma ki fara samun cikin Amina."""

"Kallonsa na yi. Sai ya daga mini kai da wani yanayi ya cigaba da cewa."" Momi ta kwana biyu shakararta arba'in da uku fa, ina tsammanin idan ba tsananin rabo ba a wannan matakin za ta iya wuce haihuwa don dai tana da karamin jiki ne."""

"""Humm."" Kawai na ce masa ina nazartarsa sanin halin maza akwai wahala, sun iya dadin baki da yaudara amma in ba haka ba yaushe zai zo ya zauna yana tsara mini magana. Shekara arba'in da uku shine ta wuce haihuwa muddin tana yin jinin al'ada bai d'auke ba za ta iya d'aukar ciki."

"Fuskata ya dago da hannunsa muka kalli juna sai ya matso da bakinsa daf da nawa yana so ya sumbuta gabad'aya yanayinsa ya canza da sha'awa. Ban yarda na bashi damar da hakan ba, ya gama lalube mini jiki da hannusa ya tashi ya tafi da sanyi jiki domin ga dukkanin alamu yana cikin wani yanayi na buk'ata. Bai fito ya gaya mini ba amma ina"

"zargin ba wata cikakkiyar gamsuwa yake samu daga wajenta ba, koda kuwa ita tana gamsuwa da shi, to ta"

bangaransa dai sai a hankali. Ina kuma

gane hakan ne a duk lokacin da kwana ya dawo hannuna. Yakan nuna d'oki da murnarsa.

Washe gari da safe ina nad'e a gado ya shigo mini. Yanayin yadda ya shigo a hargitse ya sanya na gane akwai

"matsala. Na tashi zaune da sauri ina gaishe shi. Ya amsa a gajarce kafin ya ce."" Ki shirya zuwa bauchi gobe in Allah Ya kaimu."""

"Kallonsa na yi naga babu nishadi a tare da shi. Sai na daidaita yanayin fuskata ni ma a nutse na furta."" Na gaya maka fa ba na tsammanin zan je gaskiya saboda Ina gudun wulakanci, tunda a wancan karon ni na je, to mai zai hana wannan kuma ita ta je."""

"""Ba na son jayayya da taurin kai fa, kada ki 'bata mini rai, baki da wata hujja anan Amina"""

"D'auke kaina na yi ban ce masa komai ba. Ya girgiza kansa yana fad'in."" Bari na kira Baban Saude na sheda masa tunda ba za ki yi yadda nake so ba."""

"Cikin dauriya na ce."" Na fa gaya maka irin wulakancin da ta yi mini a wancan lokacin Hajiya Saratu ce kawai ta goyi da bayana, ya za a yi ka tursasani zuwa wurin da za a tozarta ni a wulakantani"""

"Ya zauna kusa ni a hankali."" Zuciyata ba dad'i Amina, ke ma kada ki 'bata mini rai, ki yi abinda na ce dake kin ji ko, kada ki duba kowa ki duba ni Amina."""

"Yadda yake magana da yanayi na damuwa shine abinda ya sanya mini kasala. Na goge ragowar hawayen da yake idona na ce."" Ba na gudun zargi da zagin mutane Baba, amma ina kishin kaina, kuma wasu lukutan ba ni da juriya idan aka nemi a ci zarafina sai inda karfina ya kare ba na so na je garin mutane a yi rigima da ni."""

"""Na fahimceki tuntuni Amina, amma ina so ki sani wannan zai zama abin zargi da gutsiri tsoma, ba na so na ji ana zaginki, ko a fadi mummunar magana akanki, duk abinda za ki yi ki yi shi domin ni kin ji matata."""

Tausayi ya ba ni sosai gabad'aya a hargitse yake ga dukkanin alamu akwai abinda yake dannewa bai fito ya fad'a ba. Ni ma kuma ba zan so na ji ba tunda tsakaninsa ne da iyalinsa.

"Zan je dominsa kamar yadda ya nemi alfarma, amma ba na tunanin zan kwana don ban ga dalilin yin hakan ba. A wannan matsayar muka tsaya na ce masa ba zan kwana ba kuma sai dai mu je tare ya ce ya amince da hakan."

To na d'auka shikkenan magana ta 'kare har ya juya zai fita sai kuma ya dawo ya sake zama a kusa da ni kawai ya zuba mini ido.

"Ni ma sai na zuba masa nawa mun jima muna kallonsa juna kafin a kasalance ya furta."" Ba ki gane ina da matsala ba Amina?"""

"Na ce."" Ban gane ba, ai na d'auka matsalar muka warware yanzu."""

"""Ke ce matsalata."""

"Ya fadi haka yana bin sassan jikina da wani irin kallo. Cikin zuciyata na ce ka gama zagaye-zagayen kenan, wata'kila ma ko karyawa bai yi ba ya tashi da fitina."

"A nutse na ce."" Ai ba girki na ba ne?"""

"""Na dawo hannuki tunda yau na gama yi mata kwana biyunta, kuma haka na wanzu cikin buk'ata domin ita ba ta cika lafiya sosai ba."""

"A hankali na ce."" Lallai to ai a haka za ta saba, ni ba zan yarda mu fara 'yar haka ba gaskiya ya kamata ta zama mai"

"juriya, tunda ni ma da haka na horu."""

"""Duk da haka dai ai hallitarku ba d'aya ba ce, Amina ni fa kina saurin tayar mini da hankali motsinki kadai yakan jefa"

"ni a wani hali balle kuma na kasance a kusa dake giwar matana, kuma zinariyar gidan Tajudeeni"""

Mamaki ya kama ni jin yau wanda ake yi banbad'anci shine shi ma yau wani dalili ya sanya ya shi yana yi. Na yarda

namiji a gaban mace yakan zama sahorami koda kuwa mai mulki ne mai dukiya ne ko gawurtaccen malami akwai wajan da izza da jin kai basa tasiri.

"Ya sa hannu ya janyo ni ya matse a jikinsa yana kyarma yake fad'in."" Jiya na dauka mutuwa zan yi Amina, da tsananin bukata na kwana ki tallafe ni masoyata."""

"Na ce."" Ni fa ka daina gaya mini sirrinka Baba, dan gaskiya ni ma ba zan ji dad'i ba idan na ji kana gayawa wata abinda yake tsakaninmu."""

"Hannunsa a cikin rigata ya furta."" Babu ma wanda zan gayawa, to me ki ka yi mini, ni kullum cikin sanya miki albarka nake saboda Ina tsananin gamsuwa dake gimbiyata, Allah Ya ja zamaninki."""

"Murmushi na yi amma ba mai sauti ba na tashi daga jikinsa. Ya bi yo ni da kallo idonsa a kankance. Na ce.'"" Na ji"

"amma gaskiya ka bari sai zuwa dare a lokacin ne ka fita daga hannunta, amma har yanzu maganar nan da muke yi da kai a cikin hakkinta ne."""

"Sai ya tur'bune fuska yana fad'in."" Wallahi ba ki isa ba, ba zai yiwu na zauna cikin lalura saboda wani lissafi na banza ba, ita ban samu gamsuwa ba da ita ba, ke kuma kawai sai na zuba miki Ido saboda Ina jin tsoronki ko."""

Shiru na yi masa. Ganin haka sai ya cire jallabiyar dake jikinsa ya ajiye da sauri zan sauka daga gadon ya riko hannuna har yana murd'ewa.

"Cikin zafi na ce."" Zaka targada mini hannu Baba."""

Kada ki karanta mini littafi ba tare da kin biya ni hakkina ba

Bai ce komai ba ya kwantar da ni ta karfin tsiya ya danne tare da bankare mini hannu ya rirrike da hannuwansa yana

"fad'in."" Ku ba yara k'ananu ba ayi ta fama da ku, ki 'kwace idan kin isa, ko kin d'auka na yi tsufan da ba zan iya yi mini irin wannan danniyar ba."

"Ina dariya na ce."" To duk mai ya kawo haka, ka sassauta mini don Allah ka cika mini hannu ka kwalmade mini su. Sassautawa ya yi amma bai cika ni ba, ya ce."" Yadda nake ji na garau ko saurayi matashi ba abinda zai nuna mini, ke kullum idan za a neme ki, ko kina so sai kin yi jayayya haka da'biarki take Amina."

"Cikin jin ciwo domin hannuna ya k'age wajan hammatata na ce."" Na ji don Allah ka sakar mini hannu wannan a zabtar da ni kake yi da gangan wallahi."""

"Ya sake ni ya zauna gefan gadon yana kallona."" Cire kayanki."" Yafad'a cike da bada umarni."

Baki na zum'bura tare da juyar da kaina. Bai sake cewa komai ba sai ya sanya hannu a jikina da kansa ya tube riga da siket din material din dake jikina ya cire rigar maman ya jefar a ki'dime ya had'a ni da jikinsa ya matse yana sakin wani irin numfashi ya dinga bin ilahirin jikina da sumbata kamar zai cinyeni.

****

"To kamar yadda muka tsara tafiyar abinda ya faru kenan. Mun je bauci kuma cikin ikon Allah muka dawo a ranar da muka je din. Na kuma yi mamaki kwarai da gaske da naga canji mai yawa wurin Inna Uwani da ita kanta maijegon da 'yan uwanta, sun tar'be ni sosai cikin sakin fuska da kulawa ba kamar yadda na yi tsammani ba. Inna Uwani duk ta watsar da wannan kiyayyar da take yi mini yau har tana yi mana fad'a da nasiha ni da Hauwa akan mu zauna lafiya da juna, haka zalika kuma kada mu yi zaman gaba, mu had'e kai mu zama tsintsinya madaurinki d'aya irin abubuwan da aka yi a baya kada su sake faruwa. Sosai na yi mamakin hakan. Cikin zuciyata na ce dama ai karya fure take yi bata 'ya'ya kuma duk mai gaskiya zahiri shine a sama. Abinda nake ta gudu bai faru ba, wata'kila dana biyewa zuciyata dangane da abinda ta tsara mini na shiga bakin duniya kenan na kuma zama abar kallo da tofin alatsine. Yaro tubarkalla ma sha Allahu wanda tun ranar da aka haife shi babansa ya yi

Please Login or Register in order to submit comment