You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

titsiye ni da maganganu irin wannan. Na gaya miki ina da ikon mata hud'u a yanzu. Ba zai yiwu Allah Ya halasta mini abu ba wata mace ta tsorata ni ba. Ni ba sakaran namiji ba ne. Hauwa k'anwata ce, kuma ina da damar auranta a yanzu muddin inda ra'ayin hakan so ki samawa kanki nutsuwa tunda ban tauyeki ba."""

"Na ce."" To ka fito fili ka fad'a mana zaka auri Hauwa sai me? Ai ni dama ban ce ni din 'yar'uwarka ba ce, to me ya"

"had'a ni da kai dama in banda k'addarar aure. Me ya hanaka auran Hauwan tuntuni. Matar da ita da uwarta suka guje ka a baya sai yanzu zasu dawo rayuwarka saboda wata manufa. Idan zaka auro duk 'yan gidansu Hauwa bai dame ni ba wallahi."" Na kàrasa maganar ina buga cinyata da yin wani irin nishi!"

Cikin fusata ya buga katifar gadon na dan tsorata kuma gabana ya buga na matsa gefa. Fuskarsa ta canza sosai da

"fushin da ban ta'ba ganinsa a ciki ba. Ya ce."" wallahi kin ci arzikin abinda yake cikin ki amma da ba don hakan ba sai na sa'ba miki, ni za ki dubi tsabar idona ki gayawa magana dan Ubanki, ban haifeki ba. Inna Uwani sa'arki ce, ko ni zan iya duban tsabar idon mahaifinki na gaya masa magana. Na taba cin zarafin wani a halinki baki da mutunci ko Amina, kin ga damata kina gaya mini duk abinda kike so zan baki mamaki."""

"Duk maganganunsa ba su yi mini ciwo illa zagin da ya yi mini hawaye ya b'alle mini ina kuka nake ce wa. "" Ni kake zagi ko? Ai duk a cikin maganganuna ban yi maka sharri ba, gaskiya na fad'a kuma ban zage ka, amma ka dubi tsabar idona ka zagi Ubana, ka haife ni ne?"""

"Tsaki ya ja mai karfin gaske ya tashi ya fara hidimar sanya tufafi a jikinsa. Lokacin Hauwan ta sake kiran wayar amma bai yi yun'kurin d'agawa ba, na ce."" Ka zo ka d'auka mana 'yar uwarka jininka tana kiranka a waya, ni bana son munufarci."

"Bai saurare ni ba sai da ya gama shiryawa tukkuna ya zo ya zauna a kusa dani ya d'auki wayarsa ya kirata. Muryar da ni kadai yake yi wa amfani da ita idan muna bargo daya da ita ya yi wa Hauwa magana. ""My love menene"

"uhmm! ki samu nutsuwa za a yi, in sha Allah akwai maganganu masu muhimmanci da zan tattauna dake in sha Allahu idan na samu sukuni karshen watan nan zan zo bauchin sai mu tattauna ki gaishe mini da Inna Uwani."""

Tana bashi amsa ya tashi da wayar a kunnansa ya kama hanyar fita. Cikin gaggawa da mugun sauri na yi nufin dirowa daga gadon bargon da yake kafafuna ya tad'e ni na fado rigib!

"Ya juyo a razane a lokacin ni kuma na yun'kura na tashi duk da ciwon da jikina yake yi mini hakan bai hana ni tunkararsa ba. Da sauri ya bude kofar ya fita dan yadda ya nuna mafisar ta ishe shi haka in ba haka ba ya tsaya mu yi mana. A baranda na riske shi don bai kai ga sauka ba. Na ri'ke shi ta baya kamar mai shirin yin kokawa. Zuciyata sai tunzura ni nake yi, na rasa wane hukunci zan yi masa kuka kawai nake yi na ri'ke shi katamau! Hankalin Hajja da Anti Yagana ya yo saman domin gunji nake yi ba kad'an ba."

"Shi kuma duk ya diririce! Sai kamo ni yake ko'karin yi yana cewa."" Ki bi fa komai a hankali, kin ga an yi ne? da za ki tayar da hankali, ni dai ban cuceki ba."""

"Ganin Hajja tana nufo benan na fara cewa."" Don zaka yi aure sai ka sanya ni a gaba kana zagin ubana, me ya yi maka? Ina lefinsa da ya haife ni, ni ka zage ni mana amma ka daina ambato sunan mahaifina kana zagi ai bai nema a wurinka ba, a wurin Allah yake nema, wallahi Hajja na gaji ba zan iya ba."" Na kàrasa maganar da kuka mai karfin gaske...."

Hajja ta dube shi da mamaki a tare da ita ta. Kafin ma ta furta wata kalma anti Yagana da take ta jefo mini harara ta

"ce."" To idan auran zai yi ai ba za ki hana shi ba, wane irin wulakanta kai ne wannan Amina."" Hajja ta ce.'"" A a Yagana a yi magana ta hankali mana, iyaye ai ba abin wasa ba ne, kina jin fa abinda ta fad'a."""

"""Wallahi tallahi idan duk jikina kunnene ba zan yarda da cewa ya zageta ba, Hajja na san halin kayata."" Hajja ta girgiza kai tana dubansa ta ce."" Tajo ashe aure za ka yi ba labari."""

"Yar dariya ya yi irin ta takaici yana ko'karin cire rigarsa dake ri'ke a hannuna ya ce."" Ban tashi yin ba dai kawai ta ji muna waya da Hauwa shine ta daga hankalinta."

"Sai ta dube ni tana dan murmushi wanda na kasa tantance ko na menene ta ce."" To ki yi hakuri kin ga kina tare da lalura, kishi a yanzu ba na ki ba ne, fatan mu dai ki sauka lafiya."""

Sai na yi kasa'ke ina kallonta. Anti Yagana taja tsaki ta bar wurin na san haushina take ji kan abinda na yi.

Ganin haka sai shima ya silale Ina kallonsa ya sauka da saurin gaske. Hajja ta fara rarrashina akan na nutsu kada na daga hankalina tunda ai banga an yi ba.

Sai a lokacin kunya da nauyin matar suke kama ni. Idan na ce zan yi irin wannan dibar albarkar to zahiri zan bata kwa'bar da na yi.

"Hakama ina shiga d'aki anti Yagana kamar ta dake ni tana cewa. Wallahi kada ki bari ki kai mutanan nan karshe Amina, in banda rashin mutunci da samun wuri ina ruwanki da shiga lamarinsa da 'yan uwansa, idan auran ma yace zai yi menene abin damuwa, mutumin da bai tauyeki ba shine zaki tona masa asiri har da cikwukwuye masa riga saboda kawai kin ga suna sonki, ko kuwa sa'anki, babba dashi irin haka, waye ya gaya miki yanzu ana irin wannan kishin na hauka, ba ki ta'ba ban haushi ba irin yau wallahi."

"Na nemi gefan gado na zauna jikina a sabule hawaye na silalowa daga idona na ce."" Anti Yagana zagina fa ya yi wai don ubana, ina ga duk rikicin da za mu yi dashi idan cin zarafin iyaye ya shigo sai inda karfina ya kare wallahi."""

"""Bango ki ka kaishi, ai tunda na zo gidan ina fuskantar irin zaman da kuke yi, wasu lukutan kamar kece kike auransa"

"abinda kika ce shi za a yi, dama ai mai ha'kuri bai iya fushi ba."

"Na ja hanci raina na cigaba da suya domin na gama fahimtar cewa anti ba zata saurari uzuri na ba, kuma har yanzu ta kasa gane abinda nake ji a zuciyata game da maganar Hauwa. A dake ka kuma a hanaka kuka. na kwanta kusa da Hadiza da take ta bacci duk maganganunmu bai sai ta motsa ba, anti ta cigaba da maganganu tana fad'in. "" Ina ce ba daga gidan kishiyoyi ki ka fito ba, Alhaji Muntari wannan bagidajen mutumin ba matansa biyu ba, kece fa ta uku kin san ba kya son kishiya me yasa ki ka aure shi, sai wannan saboda kin fahimci lagonsa akanki kike dabdala a kansa. Wallahi ki ki yayi fushin irinsu, kuma idan ki ka ce ta irin wannan salon za ki dinga nuna kishinki zaki fice masa daga rai. Ko waye ya gaya miki anayi wa namiji irin haka ya cuceki idan zaki farka ki farka."""

"Cikin kuka na ce."" Anti Yagana don Allah ki kyaleni haka ba ki san abinda nake ji ba ne, shiyasa kike yi mini wannan maganganun lamarin bai zo kanki ba ne."""

"""To shikkenan ki yi mini rashin kunya don na gaya miki gaskiya ba sai kin kara ganina a gidan naki ba, duk abinda za ki yi, ki je ki yi rayuwarki ce, ke za a yi ta lissafawa aure, ace kowane d'a da ubansa."""

"Hawaye ya kara shararo mini shiru na yi mata ban sake cewa komai ba. Ita tunda ta ce haka ba ta sake wata maganar ba, ta fita falo wajen Hajja."

Ko'karin daure zuciyata na yi duk da abinda yana sasakata ban nuna ba ina so mu rabu lafiya don ganin yadda take

"ta jin haushina tana fushi da ni, na dinga bata ha'kuri har sai da huce tukkuna, na hada mata abubuwa masu yawa da kudi haka ma maigidan dubu dari biyu ya bata wai ta sayawa yara alawa. Koda zata ta tafi kasa daurewa na yi kuka na dinga yi haik'an! kamar 'kan'kanuwar yarinya Ita kam bata wani nuna alhini a zahiri ba amma dai na san cikin zuciyata tana jin rashin dadi. Ina kallo su Hadiza da Yusi suka tafi rakata filin jirgi, ni kuwa ya ce na zauna kawai a gidana. Haushinsa ya kara nauyi a zuciyata. Ita kanta Hajja sai da ta goge kwalla domin gaskiya sun shaku sosai da Anti Yagana."

Duk yadda na so da na manta da abin kasawa na yi domin sai nake ganin kamar ni ya takewa hakki. Akwai cin fuska

"a cikin abinda ya yi mini, dalilin ma da ya sanya kenan na yanke shawarar akan ba zan sake lamunta yayi waya da wata mace a cikin gidan ba koda kuwa ma'aikatansa ne. Idan har yana so ya zauna da ni lafiya. Ni ba namijin da zan zauna ya zagi Ubana gobe kuma na washe masa baki wallahi sai na nuna masa kuskuransa ba ruwana da kudi da shekarunsa iyaye ba abin wasa ba ne. Tare nake zaune da mahaifiyarsa ban ta'ba gaya mata bakar magana balle har na dubi tsabar idonsa na zageta. Ubana bai yi masa komai ba, ba kuma zan yarda ya saba da zaginsa ba ai kud'i ba hauka ba ne."

Sati biyu babu jituwa a tsakanina domin duk yadda ya so da ganin mun shirya naki bashi fuskar hakan. Gaisuwa ce

kawai take hadamu idan na sako daga samansa ba na sake komawa sai wata safiyar ina kula sosai domin kada Hajja ta fahimci akwai matsala a tsakaninmu.

Tun yana rarrashina har dai ya ha'kura ya zuba mini ido. Muka cigaba da zama a hakan. Ranar wata lahadi na tashi da ciwon kwankwaso domin tunda cikina ya shiga wata na bakwai nake jin sauye-sauye a tare da ni. ji nake yi kamar haihuwar fari don ba karamin wahala nake ci ba.

Da kyar na yi wanka na zura jallabiya wajejen takwas da kwata na nufi saman nasa.

"Na same shi yana ta waya na zauna na yi kasa'ke ina sauraransa ya kammala ya dube ni. Uffan bai ce mini ba. Na turbune fuska da kyar na ce."" Ina kwana.''"

"Ya yi mini shiru bai amsa ba."""

"Na ja hanci takaicinsa kamar ya kashe ni domin dai na fahimci da Hauwan yake magana da sassafe 'yar iska ko uban me take gaya masa oho."""

"Na ce."" Wai me kake jira ne kai ba yaro ba haka zalika itama ba yarinya ba tsohuwar guzuma ce fa ko yau a d'aura muku aure sai muga k'aryar wayar sassafe."""

"Babu sukuni ya ce."" Saurin me kike yi madam an kusa in sha Allahu rabbi."""

"Sai na ji kamar ya soka mini mashi a wuya. Na ja tsaki tare da kawar da kaina gefe."" Ya ce.'"" Wai ke daman haka ki ke ne, ba ki da kunya?"""

"Shiru na yi ban ce masa komai ba."""

"Ya sake girgiza kai a karo na biyu ya furta."" Ba tsoronki nake ji ba, kuma duk take takenki na gane wallahi ba zan rabu dake ba dan zan yi aure, kuma zan fito miki da asalin kalata tunda baki da mutunci."""

"Hawaye suka 'kwace mini na ce."" Ni ce ma ba ni da mutunci ko? Wallahi idan kuwa kana son zama da ni cikin salama sai ka bi dokokina domin kuwa ba zan zauna ka dinga raina mini hankali ba. Ka zage ni ka zagi Ubana akan wane dalili. Ni bana asiri amma zan had'aka da Allah idan har rabuwarmu itace alheri Allah Ubangiji ya tursasaka ka ba ni takardata. "

*GARKUWAR MATA.*

*BINTA UMAR ABBALE*

"[6/3, 8:38 PM] matar mijinta: *Wannan littafin na kudi ne vip 1k akan telegram. Normal What'sapp group kuma #700 hanyar da za a biya kudin ita ce wannan...0542382124...Binta Umar gtbank ko kuma 7084653262. Binta Umar"

Opey bank. 'Yan nijar dala dari katin airtel za ku tura mini bayan kun kankare hoton. A tura da sheda ta wannan lambobin iya What'sapp kawai.*

*07084653262*

*08089965176*

*V-VIP AREWA PEN *

*TALLAH!*



*DA MAGANI A GONAR YARO!!*

*08089965176*

*07084653262*

"*Dayawa akwai matan da suke da matsala ta lalacewar nono yamushewa da kuma fad'uwarsa. Wasu ma 'yan mata ne basu kai ga matakin aure da shayarwa ba amma sai su samu matsalar faduwar nono. To gaskiya akwai magani sai dai kawai idan ba a yi dace ba. Wasu zasuyi ta faman kashe kudi amma buk'ata bata biya ba, wasu kuma zasuyi ta fargaba kada su je garin neman gira a rasa Ido, ma'ana su sayi abinda zai cutar dasu da kudinsu. Kuma yanzu dai tsakani da Allah rijalu sun riga sun gama nuna abinda suka fi karkata a kansa a jikin 'ya mace kirji da kuma baya. Wasu Allah ya hallice su dashi har ya yi musu yawa, wasu kuwa basu dashi kuma mai saurin zubewa ne. To mu dai duk wanda ya san maganinmu ya san ingantacce ne, kuma Yana aiki kwarai da gaske wurin dawo da daraja da martabar nono da izinin Ubangiji. Sahihin magani ne da ya samu sheda da lambar yabo, kuma Islamic ne da akayi masa hadi mai inganci domin gyara jikin mace ba ma iyakacin nono kawai ba. Babu nadama haka zalika babu dana sani da asarar dukiya wurin sayan maganinmu. In sha Allah matsalar ki zata gushe idan kin jarraba amfani dashi. Ba mu tsaya ina nan ba, muna da na gyaran hips sahihi dana k'iba idan kina fama da matsalar rama. Haka zalika muna dana tumbi, da kuma maganin sanyi mai mugun kyawun da yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye wanda zaku hadu da maigidanki kuyi amfani tare. Akwai ingantattun supplement wad'anda basu da illa balle su cutar da GARKUWAR jiki. Sai dai su gyara su kuma tayar da komad'a ina nufin inda ya samu nakasu a jikinki. Muna sayar da"

"sabulan gyaran jiki dilka da man gyaran gashi, muna kuma bayar da sari a fad'in najeria da nijar muna tura kayanmu"

kowane gari da ikon Allah.*

*Muna garin kano duk inda kake za mu aika maka da kayanmu. Domin neman karin bayani sai a yi mana magana ta Whasap ga lambobin da za a same mu a kai.*

*07084653262 ko*

*08089965176*

*SIYAN NAGARI!!!!!!*

*A JARRABA A SAMU BIYAN BUKATA DA YARDAR ALLAH*

TEEMAH DATA SERVICES MTN

1GB @550

2GB @950

3GB @1450

4GB @1550

5GB @1700

CHECK CODE *323*4# VALIDITY 30DAYS CHAT@08112392177 CALL @08037026306

8037026306 fatima musa ibrahim opay

*17*

"Ya dinga kallona kafin daga bisa ni ya ce."" Na rasa wace irin macece Allah ya had'a ni da zama da ita. Ana ga gabas kina ga yamma An gaya miki kishi hauka ne, mahaifinki fa mata biyu gare shi, to ni me yasa zaki ce ba zan yi ba, ko kina yi mini bakinciki na samu abinda na rasa a baya ne."""

"Na ce.'"" Na gaya maka duk abinda za mu yi kada ka sako mahaifina a ciki, shi ka raina ko? Kwanaki ka zage shi yanzu kuma kana so ka gaya masa magana. Akan wane dalili? Na rantse da zatin Allah ba zan jure hakan ba zan d'auki mataki."""

"Maganata sai ta bashi dariya ya dinga yi yana kallona daga bisani ya girgiza kansa yana fad'in."" Ki d'auki duk matakin da za ki d'auka, ina jiranki, a dake dai ba zan daku ba, kuma ni sharri ki ka yi mini ba ta inda na ambaci sunan mahaifinki na zage shi, yarinyar nan har yanzu ba ki san wanene Tajo ba, amma Humm!"""

Kada ki karanta littafin nan ba tare da kin biya ni hakkina ba yar uwata.

Tashi na yi na fita daga d'akin domin Ina ganin zamana ba zai haifar da d'a mai Ido ba. Da daddare misalin sha daya

da wani abu ya kira ni a waya don har na kwanta ma muna hira da Hadiza kad'an kad'an bacci Yana fizgata yace na same shi a samansa. Ba na so Hadiza ta gane muna fad'a dashi na tashi nasa hijabina na fita.

"Yana tsaya a bakin kofa ina shiga ya murza mukulli. Na dube shi babu fara'a."" Gani.'' Sai ya kamo hannuna ya ja ni muka nufi gado."

Tunda na ga taketakensa na fara janyewa domin ba na jin dad'in komai rayuwata a takure nake yin ta. Ga kuma takaicin da yake k'unsa mini.

"Duk daburunsa suka kare jikinsa ya dinga kyarma, domin ya kai makura wajan bukatuwa kuma ya kasa samun hadin kaina. Duk inda ya ta'ba a jikina zan ce wayyo, ko na d'auki hannun na cillar dashi. Ya kasa sarrafa ni domin na cure wuri d'aya tamkar alkaki. Sai ga kwalla mai yawa a cikin kwarmin idonsa saura kiris ta zubo."

"""Ki bari na yi ko kad'an ne a hankali zan yi na gaya miki, ba ni da wata iyalin sai ke, ki daure kada ki jefa ni a cikin matsala, Amina ke kanki kin san na yi juriya sati biyu ban nemeki ba ba na so na gwada miki karfi."" Wad'annan maganganun yake furtawa jikinsa yana rawa yayin da gumi keta keto masa. Ya kai hannusa ya dora a kirjina yana shafawa. Na cire da sauri na juya masa baya. Sai yake matso ni yana shashsheka."" Kashe ni kike so ki yi ko? Me na yi miki ki ke shiga hakkina, kin san bala'in da nake ciki kuwa amina."""

Shiru na yi masa don har yanzu bai fara ba ni tausayi ba.

"""Okey ki gaya mini nawa zan saya tunda ba zaki ba ni nayi don Allah ba, na ce ki gaya mini nawa zan siya."" A hankali na ce."" Ba na siyarwa ba ne.'"""

"Ya riko kafadata tare da dora fuskarsa a tawa Yana cewa.'' To na ji, ki bari ko ban shiga wannan wurin ba na yi wasa"

"da wannan kin ji ko."" Ya kara kai hannunsa kirjina. Na ture shi na tashi zaune tare da matsawa can karshen gado."

"Ya tashi zaune shima na kalleshi gabad'aya duk ya firgice girmansa ya fito sosai. A ki'dime ya ce."" Wallahi tallahi zan gwada miki rashin Imani yanzu. Ke wace irin muguwa ce ne? me na yi miki, ko ke yarinya ce karama?"""

"Shiru na yi masa ban tanka ba. Sai yanzu zuciyata ta fara sanyi domin ganin yadda na samu damar rama abinda ya yi mini."""

"Ya danna kafadata da k'arfi zai kwantar da ni. Na kuwa bude baki da k'arfi na tsala ihu! Ina fad'in."" Wayyo cikina."""

"Ya cika ni da saurin gaske yana gyara mini cinyata data lan'kwashe. Na d'ora hannuna kan cikin ina hawaye. Shi ma ya kai hannunsa kan cikin daidai lokacin da yake ta motsi. Kusan minti biyar ya cire hannunsa. Ya lalubi gajeran wandonsa ya sanya. Ina kallonsa ya sauka daga gadon kamar mara laka a jiki ya nufi bandaki, tsaki na ja na tashi zaune."

"Tunda haka ta faru a tsakaninmu bai sake nema na a shimfida, bai kuma 'kullace ni ba. Ni din ce ma na tsiri gaba"

"dashi duk da na san ta wani gefan ya fi ni gaskiya amma ban yarda na nuna masa ba, domin zahirin gaskiya na ji ciwon zagin da ya yi mini."

"Ban sake hawa samansa ba run ranar da abin ya faru sai na bari ya sauko tukkuna muke gaisawa, itama babu cikakkiyar sakewa a tsakaninmu Ita da kanta Hajjan ta fahimci akwai rashin jituwa a tsakaninmu. Wataran ta same ni a d'aki don kwana na yi ciwon mara ban kuma gayawa kowa ba ko ita Hadiza gajiya ta yi da tambayata ta rabu da ni. Tana shigowa na yun'kura na tashi zaune Ina dan yamutsa fuskata. Ta zauna kusa da ni muna kallon juna na sake gaisheta duk da cewa da safe mun gaisa. Hadiza dake gyara kayanta a kwati itama ta sake gaisheta. Sai ta ce."" Yau na ji ku shiru baku fito ba har ke Hadiza tun bayan da muka gaisa da safe na ce yau ba kwa jin hirar ne."""

"Hadiza ta ce."" Wallahi ni na tsaya gyaran kayana ne Hajja ni ma yanzu nan nake zancen a zuciyata. Sai ta dube ni a nutse ta furta."" Ai na d'auka ko wani abin aka yi muku."""

"Yar dariya na yi gyara zama na ce."" Hajja waye zai yi mana abu kuma, na d'an tashi da ciwon jiki ne wallahi shiyasa"

"ban fito ba."""

"Cikin nazari irin na manya ta ce."" Ai wannan ya zama dole tunda kina kan ga'ba, amma dai na fahimci akwai damuwa a tare dake tsakaninki da mijinki akwai matsala ko Amina?"""

"Girgiza kaina na yi da sauri na ce.'' Babu wata matsala Hajja me ki ka gani?"""

"Ta ce."" Na ga abubuwa da yawa a cikin satin nan to na yi miki uzuri ne dalilin lalurar dake tare dake ni kaina ba na son abinda zai daga miki hankali."""

"Shiru na yi ban ce komai ba, amma maganarta kamar ta famo mini abinda yake damuna. Kwalla mai zafi ta zubo"

"mini."""

"Ta dubi ni tana girgiza kanta ta ce."" Maganar Hauwa tana damunki Amina, me zai sanya ki tashi hankalinki akan abinda ba ki ga an yi ba."""

"Na yi shiru ban ce mata komai ba, don gaskiya ina jin nauyinta sosai. To ya zan yi ne na yi kokarin ganin na danne"

abin a raina smma ya faskara ni kaina ban san ina da zafin kishi ba sai akan d'anta.

"Ta riko hannunawana a nutse ta furta."" Kada lamarin Hauwa ya daga miki hankali Amina, ni ina son tarayyarki da Tajo, kuma muddin ina raye ba zan bari ki wulakanta ba, kada ki ga Hauwa 'yar uwasa ce ki sanya a ranki cewa ko ya aureta zaki wula'kanta ko d'aya. Dake da ita duk daya kuke a wurina. Tajo ko bai auri Hauwa ba ai ba mu isa mu hana shi auran wata ba tunda Allah ne ya halasta masa, kada ki bari ya fahimci gazawarki ta wannan gefan kin ji ko."""

Hawaye masu rad'adi suka fara ambaliya a fuskata kuka nake sosai domin yanzu na sake gazgata lamarin tunda gashi

"mahaifiyarsa tana gaya mini akwai fa auran ko mu dade ko mu jima, to ya zanyi da tsananin tashin hankalin da yake yun'kuro mini a zuciyata. dama wai haka ake kishin, ni fa tsakani da Allah ban ji kishi ko kad'an ba a lokacin da nake tare da Alhaji Muntari. Ban san yadda aka yi nake masifar tsanar na ji ana danganta shi da Hauwa ba sai duk hankalina ya tashi."

Rarrashina sosai ta yi da kalamai tausasa don ba ta fita daga d'akin ba sai da ta tabbatar na sake na daina kuka sannan ta fita da zummar yin sallar la'asar.

"Hadiza ta dube ni tana tabe bakinta ta ce."" Aure ko shekara ba a yi ba zai miki kishiya to ke yanzu haka za ki zauna"

"babu wani taimako da za a yi mini. Ni fa wallahi ban yarda da Inna Uwani nan ba, gani nake kamar da sanya hannunta wurin sanya miki tsana da kiyayyar mijinki har ma da zafin zuciyar da kike ciki."

Kallonta na yi ina auna maganarta. Idan na fahimci inda ta dosa tana so na bi malamai da zummar a taimaka mini

kada mijina ya yi aure ko kada na yi

Please Login or Register in order to submit comment