You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ce komai ba sai dai zuciyata cike take da farincikin ganinsa cikin walwala da kyawun yanayi tare da lafiya da suttura irin ta 'ya'yan manya a jikinsa.

"Ga gida har gida babu abinda babu a ciki ko 'diyar shugaban kasa za a iya ajiyeta a gidan amma kash babu mace a cikinsa asalima ya tanadi gidan ne kawai domin idan ya zo garin ya sauka a cikinsa tunda karfin zamansa ya fi legos. Ya d'an ba ni tausayi kad'an domin kamar yadda ya fad'a cewa Allah bai tauyeshi da komai ba na jin dad'in duniya sai ta bangaran iyali, Ina ganin da zamansa anan yake dindindin zan iya ha'kura da can na zauna tare dashi to karfin zamansa ba anan yake ba, ni kuma gabad'aya zaman legos din ne ya fice mini daga raina."

Wajan cin abinci cike yake da cima kala kala da kayan marmarin dogon daning ne mai d'auke da kujeru takwas gaba da baya tsarin gidan gwanin ban sha'awa kuma a gare cikin tsabta kasancewar akwai masu aiki maza da suke yi hidima a gidan koda baya nan.

"Sama ya hau nan turarkarsa take Ade ya shigo da akwatina ya ajiye ya fita, Yusi ya tashi da sauri ya bi bayan shi yana kiran sunan shi na bi yaron da kallo da alama akwai sabo a tsakaninsu."

Ajiyar zuciya na sauke a nutse nake bin falon da kallo ya tsaru ainun ya ji kujeru da labuleye na alfarma hotonsa dana iyayensa gasu nan birjik a falo can na hangi na baby Nana kato a wata kusurwa a jingine ba a kafe shi a bango ba.

Na jima tsaye ina duba hoton na share kwallar da ta ciko a idona na d'auka a gidansa na legos kadai ya ajiye hotonta ashe yana dashi a nan d'in ma.

Yana ba ni tausayi sosai a wasu lukutan domin shi din abun tausayi ne....

Sai da na d'an samu nutsuwa tukkuna na tashi na hau saman tunda nan naga ya nufa ai nasan wulakanci da shan kamshi zansha shi nasan sai dai na kai zuciyata nesa.

D'akuna hud'u ne kowanne a rufe sai guda daya da naka key a jikinsa ta waje hakan ya tabbatar mini da cewa yana cike ina ta'ba kofar kuwa ta bude na shiga da sallama a bakina.

"Ya fito daga bandaki daidai lokacin da na shiga d'akin wanka ya yi ya ce."" Shigo ciki sosai mana."""

Na kàrasa na zauna gefan gado ina dubansa da gaske fa ya rame yanzu na sake gazgatawa da babu riga a jikinsa sa towol da ya dauro.

"Ya dube ni yayin da yake ko'karin zama kusa da ni yana fad'in."" Ya gajiya?"""

"Na daure a hankali na ce."" Alhamdulillahi ya jiki ashe da gaske dai ba ka da lafiya Baba."" Ya ce."" Lafiyata lau me ki ka gani?"""

"Kai tsaye na ce."" Ramewa na ga ka yi?''"

"""Fargaba ce kawai wallahi na jima ban ga ciwon da ya tayar mini da hankali kamar na Alhaji Amadu ba sam ya'ki jin magani, yana nan fa sai dai a kwantar a tayar na gaya miki yana asibiti a yanzu amma jibi za a yi masa transfer zuwa asibitin makka."

"Cike da alhini na ce."" In sha Allahu zai samu lafiya kaima ya kamata ka cire damuwa daga ranka kada wani ciwo ya sameka ka rame fa sosai Baba dama kai ba jiki ba."""

"Yana yi mini wani irin kallo ya ce.""Abin har da zolaya Amina."""

"Girgiza kaina na yi a hankali na ce."" Ban isa ba, kawai dai ramar taka ce ta d'an tsorata ni Yusi kuwa kamar wanda ake hurawa."""

Ai irin jikinki ne dashi na gaya miki ke ce ki ka gada masa 'kiba.

"Ya tashi ya nufi wardrobe yana fito da kayan da zai sanya ya ce."" Da daddare idan kin huta za mu je ki duba shi ko?"" Na ce."" In sha Allahu rabbi."" D'akin ya yi shiru na mintina shi yana ta hidimar shirya jikinsa yayin da ni kuma nake bin d'akin da kallo karaf idona ya sauka kan dirowar dake gefan gadonsa karamin hoton Samira ne irin wanda ya ajiye a gidansa na legos wanda na sanya ya cire shi."

"Kishi na ji ya soke ni, ai ta riga ta mutu shekara da shekaru ya kamata ace yanzu ya cire ta a ransa amma ace kowane gidansa da hotonta a ajiye ban san menene amfanin hakan ba."

Ya juyo yana kallona ni kuma na janye idona daga kan hotonta ina ko'karin danne abinda nake ji.

"Bai ce mini komai ba ya zauna gefan gadon tare da gyara zaman hoton dukda ba abinda ya yi ganin haka ya sanya na tashi tsaye sai ya yi saurin fad'in."" Ki yi wanka sai mu sauka mu ci abinci ko?"""

"Ban ce komai ba na nufi bandakin zuciyata babu dad'i hotonmu ya fi kamata a ce ya ajiye gefan gadonsa ba na wadda bata raye ba, na fahimci har yanzu akwai sonta a cikin zuciyarsa hirarta ne kawai ba ya yi mini tunda ya fahimci ba na so."

Muna cin abinci yake gaya mini Yusi a gidan abokin nasa yake kwana tare da yaranshi da yake matarsa daya Hajiya Maryam auran saurayi da budurwa suka yi kuma da yake 'yan boko ne sun tsara rayuwarsu haihuwa uku sukayi suka dakata sun fara da mace mai suna Nusaiba wadda suka aurar da ita shekara biyu da ta wuce anan abujan tana auran babban ma'aikaci a central bank. Sai kuma Salim wanda yanzu yake matakin shekara ashirin Adam kuma sha bakwai.

Hajiya Maryam yar boko ce kuma muguwar 'yar gayu ce irin matan nan ne masu kyawun jiki da ado da kwalliya shekarunta sun buya sosai idan ka kalleta sai ka d'auka bata fi talatin ba amma ba haka ba ne shekarunta arba'in da d'aya a yanzu tsabar gyaran jiki ya sanya komai nata yana nan cif mussaman kirjinta sai da basu da wani girma amma dai tana kula da jikinta ainun.

kuma yar kasuwa ce domin manyan shop ne da ita garin abuja da kano da kuma reshenta a jos tunda asali nan ne mahaifarta amma dai harkokinta sun fi yawa a Abuja tana fita kasashen larabawa mussaman dubai da Qatar da India domin sarin kaya dogwayen riguna takalma sari irin na indiya da kayan maza Pakistani da kuma bangaran sarkoki abin hannu agoguna da sauransu. Yar kasuwa ce sosai wadda arzikin mijinta bai sanya ta nemi wuri ta zauna ba. Da yana gaya mini Yusi ya sha'ku da yaranta dalilin gidajensu na ma'kotaka da juna ban yi mamaki ba domin na tabbatar da cewa Yusi zai iya zama da kowa saboda yana da hankali da kuma iya mu'amula shi ma kuma Allah ya sanya masa kwarjini da farinjini a duk inda ya shiga.

Bayan Isha'i ya d'auke ni a mota da kansa ya yi direving din motar muka nufi asibiti a can muka samu Yusi tare da matasan yaran suna zaune kusa da gadon da mahaifin nasu yake kwance ko'ina na jikinsa sa'kale da na'ura yana ta kokawa da numfashi

Gaskiya dan adam ba abakin komai yake ba idan ma kana d'aukar kanka kai wata tsiyane wallahi gwara ka yi karatun ta nutsu domin Allah ne mai sarrafa al'amura gashi dai da kudin wanda da yawa muke ganin kamar sune karshen jin dadi bayan ba haka ba ne mai lafiya shine d'an gata domin kuwa duk wanda Allah ya wadata da lafiya shi ya yi wa arziki..

Ita da yaranta sun ba ni tausayi kwarai da aniya kuma yanzu na sake gazgata maganar da ya yi mini jiya a waya cewa suna mugun tsananin son junansu shiyasa gabad'aya ta susuce! Ta kasance kullum cikin zubar da hawaye...Da kyar ta iya amsa gaisuwata hankalina gabad'aya na kan maigidan nata da ko yatsansa baya motsi shi kansa na lura da kid'imewarsa da likita ya shigo suna magana yake tambayarsa ya ga an sake sanya masa oxygen bayan jiya aka cire ta kuma numfashinsa ya daidaita likitan ya ce masa ciwon ne ya sake tashi d'azu da yamma amma kuma numfashin ya fara daidaita ba kamar d'azu ba. Ya sake duba shi ya fita shi ma da yake likita jikinsa a mace balle ga mu da muke zaune.

Sai wajan goma da wani abin muka bar asibitin cikin damuwa da zullumi domin kukan da Hajiya maryam din take yi ya ta ba mu gabad'aya har dashi gabad'aya yanayinsa ya canza shi bai yi na hawaye ba yana na zucci irin mai mugun cin ran nan.

Na d'auka damuwar da yake cike ba zata bari ya nemi wata buk'ata ba. A daran bai iya bacci ba sai da ya kwanta da ni irin kwanciyar da na ji jiki a hannunsa har abin ya fara ba ni tsoro ganin yadda ya 'kirkiro wani style wanda ba mu ta'ba yin irinsa ba. Ban fahimci komai ba sai wahala saboda bai jima yana yi mini wassanin soyayya ba ya fara gudanar da abinda ya kud'irce a cikin ransa wanda tun ina yi masa kawaici har dai na gaza ha'kuri na gaya masa fa bana gane komai sai zafi da ciwon cinya. Ya ce shi kuwa atafau ta haka yake so ya yi don ya fi jin dadi. Haka nan na ha'kura na kyaleshi ya dingi yi tamkar wani sabon angon da ya jima yana shan sassa'ke. Wallahi kasa juriya na yi don duk fitinata wannan lamarin ya sha kaina kamar da zalinci a ciki. Ashe lumbu lumbu ya yi mini na zo hannu ya yi mini 'keta kuka kariris na dinga domin ya rabu da ni yana fad'in bai gama ba tukkuna. Da ya gama kuwa sai da na yi

ruwan d'umi sannan na ji sasaauci na nemi waje can nesa dashi na kwanta cinyoyina suna ta ciwo. Na jima kafin

bacci ya kwashe ni ina ta kallonsa yana baccinsa hankalinsa a kwance.

"Can gefin asubahi kiran da ya shigo wayarsa ya tashe mu gabad'aya a zabure ya lalubi wayar yana dubawa da sauri yasa a kunnansa yana fad'in."" Alhaji Jamil ""Innalillahi wa'ina ilaihi raji'un! wannan kalmar ce ta fito daga bakinsa"

bayan ya gama sauraran maganar mai kiran wayar wanda na ji ya kira shi da Alhaji Jamil.

Dama a wasu lukutan mutuwa takan nuna kama kafin wa'adin ya cika. Ni dai dama ganin da na yi wa Alhaji Amadu a

wannan dare na sare domin gwiwata a sanyaye muka fito daga asibitin lokaci kawai yake jira amma alamun sallama da duniya ya gama bayyana a tattare dashi. Alhaji Jamil k'anine ga Alhaji Amadu tare suke ta tiriri dashi shi k'aninsa ne uwa daya uba daya shi kuma abokinsa ne tun na 'kuruciya abokin da akayi gwagwarmayar rayuwa.

Mutuwar Alhaji Amadu ta dake shi mutuka gaya domin ni sai na ce tunda na tashi daga kuruciya da girma ban ta'ba ganin kukan babban mutum kariris irin haka ba.

Na fahimci ya yi kokari sosai wurin ganin ya danne kukan amma hakan bai samu ba kuka ya dinga yi sosai amma ba mai gunji ba yana nanata Innalillahi wa'ina ilaihi raji'un! lamarin ya tsoratani sosai wanda hakan ya sanya ni ni ma fashewa da kukan domin na rasa yadda zanyi na rarrashe shi

*GARKUWAR MATA.*

*BINTA UMAR ABBALE*

"[6/3, 8:38 PM] matar mijinta: *Wannan littafin na kudi ne vip 1k akan telegram. Normal What'sapp group kuma #700 hanyar da za a biya kudin ita ce wannan...0542382124...Binta Umar gtbank ko kuma 7084653262. Binta Umar"

Opey bank. 'Yan nijar dala dari katin airtel za ku tura mini bayan kun kankare hoton. A tura da sheda ta wannan lambobin iya What'sapp kawai.*

*07084653262*

*08089965176*

*V-VIP AREWA PEN *

*57*

"Shine akan gaba wajan shirya Alhaji Amadu har aka kaishi gidansa na gaskiya, haka ya dinga kai kawo har ya ba ni tausayin da na ji kwalla ta cika kwarmin idona. Tabbas Alhaji Amadu ya wuce aboki a wurinsa sai da d'an uwa, domin tun a daran kafin gari ya waye ya dinga gaya mini irin gwagwarmayar da suka sha duk domin tsayuwa da kafafuwansu. Marigayin ya riga shi auran fari kusan shine ma ya yi masa rakiya ta angonci kuma tare suka dinga jigilar zuwa jos neman auran Maryam din har dai Allah Ya tabbatar da auran. Shekaru kusan goma sha biyu da auransu ne shi kuma ya yi auran fari Samira kenan Allah kuma ya dinga wanzar da ikonsa."

Ni kam da babu sha'kuwa a tsakanina da Hajiya Maryam ban nuna bak'untata ba mijina abokin mijinta ne sannan

yarona yana tare da nata yaran ta ri'ke gabad'aya dalilin da ya sanya kenan na shiga cikin 'yan uwanta na zauna tare dasu har dare muna kar'bar gaisuwa a tare. Na sake yin karatun duniya sosai domin mutuwa wa'azi ce ga duk wani mumini na kuma tausaya mata kwarai da aniya ganin yadda ta zabge ta ki'dime a lokaci d'aya babu shakka mutuwar miji wani babban rashi ne da har abada ba za a ta'ba maye gurbinsa ba.

Sai wajan tara da arba'in tukkuna na shiga gida tunda muna kusa da juna amma ban tafi ba tukkuna sai da na tabbatar da cewa ta ci abinci domin yini guda babu abinda yake cikinta babu irin rarrashin da ban bakin da ba a yi mata ba tace ba zata iya cin komai ba. Itace babba a cikin 'yan uwanta shiyasa da suka gaji da rarrashinta suka ha'kura dalili duk ta girmesu iyayensu kuma basa raye itace ke ri'ke da ragamarsu gabad'aya ni ma na tabbata don tana jin kunyata ya sanya ta kar'bi abincin da na hada mata da hannuna ta dinga ci kamar magani tana goge hawayen da suka ki daina fita daga idonta.

Bai shigo ba sai wajan sha biyu saura shi Yusi yana can dama lokacin da ya shigo din har na yi shirin kwanciya amma ban kwanta ba din tukkuna ina dakkon shigowarsa.

Littafin gudun aure na kudi ne kada ki karanta ba tare da kin biya ni hakkina ba.

Wanka ya fara yi tukkuna ya same ni a zaune a gefan gado ya zauna kusa da ni. A nutse nake dubansa gabad'aya

"bashi da kuzari na ce."" Sannu baba ya karin ha'kuri?"""

"Ya amsa da ""Alhamdulillahi yana dan duba wayarsa ya ce."" Gobe su Hajja suna tafe tare da Hajiya Saratu da sauran 'yan uwan mahaifina."""

"Na ce."" Ubangiji Allah ya kawo su lafiya amma ka ci abinci kuwa?"""

"A nutse ya ce"" Na ci amma ba mai yawa ba."""

"""Ko kana buk'atar wani abu yanzu wanda sai sanya cikinka ya dan yi nauyi."""

"""Wannan towon naki nake sha'awar ci irin wanda ki ka yi mini a gidanki amma dare ya yi yanzu za mu bari da safe sai ki yi mini ko?"""

"Cike da kulawa na ce."" Muddin da akwai duk abun bu'kata yanzu ma sai na yi maka har da d'umame ai ba wani abu ba ne."""

"Ya girgiza kansa yana yi mini wani irin kallo ya furta."" Ba ni da imani sai na sanya ki aiki da wannan dare duba lokaci fa sha biyu har ta gota."""

"A nutse na ce."" To ai aikin lada ne?"""

"Ya d'an jima yana kallona kafin ya girgiza kansa da cewa."" Ki huta kawai na gode."""

Jikina ya d'an mutu da yawan kallon da yake yi mini wanda na kasa tantance na menene na soyayya ne ko na wani abin ne.

"Wayarsa yake latsawa kafin yasa a kunnansa ban tsammaci da Hauwa yake waya ba sai da na ji yana fad'in."" Kin fi kowa sanin matsalar hakan tunda ma'aikaciyar lafiya ce ke to me zai sanya kuma ki aikata, idan kika zubar da cikin ai mun huta gabad'aya tunda ke ba za ki yi aiki da abinda ki ka sani ba."""

"Ban ji abinda take ce masa ba. Ya ce."" Ina cikin jama'a ne sosai muna kar'bar gaisuwa abokin nan nawa Alhaji Amadu ne ya rasu nasan zuwa yanzu kin samu labari ko ta kafafan sadarwa ne dalilin da ya sanya kenan ban samu damar amsa kiranki ba gashi yanzu da na nutsu na kira ki da kaina."""

"Shiru ya yi yana sauraranta har ta gama yi masa magana cikin kuka wanda nake jin sautinsa kad'an kad'an. Ya ce."" To shikkenan a d'aure mahaifar idan hakan shine solution ai kin fi kowa sanin hakan tunda ajikinki take gobe ki je asibiti da wuri ayi miki aikin Allah Ya sawwa'ke."""

Ya kashe wayar da damuwa a tare dashi. Ni ma sai na ji hankalina ya tashi wato dai muddin kana raye a duniyar nan ba zaka huta ba.

"Bai gaya mini ba amma na fahimci kadan daga cikin abinda suka tattauna cikinta ne yake barazanar zubewa. Na gaza ha'kuri na tambaye shi ya ce."" Wai fita suka yi suka yi tare da Sadiya tafiyar kasa mai tsayi saboda rashin hankali tasan tana da karamin ciki bayan sun dawo gida shine take ganin jini kad'an kad'an wai tana tunanin cikin zai iya zubewa dole sai an yi d'aurin mahaifa."""

"Da damuwa a tare da ni na ce."" Aikuwa dai yana da kyau ta yi gaggawa zuwa asibiti gobe wata'kila tana da matsalar mahaifa bata da k'wari shine dalili amma kuma itama ta yi ganganci yin doguwar tafiya a k'afa tana da karamin ciki kamar ba ma'aikaciyar lafiya ba."

"Ya ce."" Abinda take zargi kenan idan cikin ya zube ai ta huta."" Ya k'arasa maganar cikin takaici da jin haushin lamarin."

Haka kawai na ji na damu da hakan domin har ga Allah bana so wani abu ya samu cikin Hauwa ba don komai ba sai don ganin tabbatuwar farinciki da walwala a fuskarsa. A yanzu dai zuria itace karshen abinda yake nema a wannan duniyar bayan Allah Ya wadatashi da komai a duk lokacin dana kalleshi na tuna har yanzu bai ajiye magaji ba hankalina yana tashi sosai kuma nakan zubar da hawaye masu yawa domin jarabawar da ta same mu ni dashi na riga nasan ko na saki zuciyata da gangar jikina na haihu za mu sanya rai ne akan abinda muka samu bayan kuma ba mai d'orewa ba ne. Astagfirullahi wannan shine babban dalilin da ya sanya nake ji a cikin raina ko cikin na samu zan iya zubar dashi ba tare da ya sani ba don gudun shiga damuwa matsananciya bayan na bari na haihu muna ji muna gani mu rasa abinda muka samu kamar yadda muka rasa babynmu ta farko.

Abin mamaki da daure kai a wannan daran ma na jigatu kwarai da aniya a hannunsa don ban ta'ba tsammanin ma zai neme ni ba ganin irin jimawar da muka yi jiya muna abu daya. Abu na biyu kuma a tunanina gagarimin rashin da ya yi zai dakusar dashi kewar komai na jin dad'in duniya ashe ba haka abin yake ba fahimtata ma kamar idan yana cikin damuwa ya fi kulafucin lamarin washe gari na tashi da ciwon jiki matsananci domin irin sarrafuwar da na yi a hannunsa a daran jiya Ina ganin ko ko kwa'babbiyar fulawar borodi ba ta kaini buguwa ba.

Ina kwance gado bayan na yi wanka na kasa tafiya gidan rasuwar Yusi ya shigo yana gaya mini wai anti Nabila kanwar Hajiya Maryam tana kira na zo ko zan iya rarrashin antin nasu ta karya kumallo. Na ce masa ya je ganin zuwa yanzu. Da kyar na rarrafa na tashi na sanya hijabi saukata kasa ta yi daidai da shigowarsa hannunsa da ri'ke da carbi da alama daga wurin kar'bar ta'aziyya ya taso ya ce mini na je maza wurin Hajiya Maryam na zauna tare da ita yanzu Adam yake sanar dashi an yi an yi da ita ta ci abinci taki ci.

Na ce yanzu Yusi ya zo ya sanar da ni. Na fahimci tunda aka yi rasuwar yake bawa abinda ya danganci matar muhimmanci don jiya ma shine ya k'arfafa mini gwiwar zama a kusa da ita a cewarsa zan deba mata kewa bayan 'yan uwanta. Ban ta'ba kawo komai ba a cikin raina abinda dai na ajiye shine bai ajiye lamarin Alhaji Amadu a nesa

ba domin kuwa Allah ne kadai yasan irin taimakekeniyar da suka yi wa juna ba a lokacin da suke neman rufin asiri na

duniya.

Hajja suka sauka kamar yadda ya fad'a Hajiya Saratu da kannan mahafinsa su biyu Maza a ciki akwai mahafin matashi ta biyu wato Aysha wadda ta rasu sakamakon zazzabin typhoid kafin ta tare a gidanshi.

"Ba sosai na sansu ba duk da kasancewar suna da yawa kad'an na sani daga cikinsu, hakan yana da ala'ka da rashin zamanmu a gari tun bayan aure dangin Hajja ma in banda rasuwar da aka yi ta kanin mahaifin Hauwa babu wanda nasani daga cikinsu."

Wannan karon mun sake sosai da Hajja da alama sihirin da aka yi mata ya warware babu wani kallo na baibai a tsakanina da ita sai mutunci da girmama juna.

Haka aka yi zaman makoki na kwanaki bakwai mutumin nan bai daga kafa ba. Kullum da safe zai fita cikin jama'a ya kar'bi gaisuwa da daddare kuma sai ya rikid'e ya koma jarababbe na bugawa a jarida.

Wannan dalilin ya sanya na yanke shawarar guduwa ba zan iya ba don ban san abinda ya zama ba kuma idan zai jima anan din bai koma legos din ba Hauwa sai ta zo ta kar'bi lamarinsa domin dai sha'aninsa ya fara ba ni tsoro da mamaki.

"Ban sanar dashi maganar data assasa mini zuwa ba sai bayan an share makoki kwanaki tara da rasuwar tukkuna na gaya masa amma ta sigar da ba zai zarge ni ba ai taimako ne kuma duk wanda ya taimaki wani Allah zai taimake shi sosai na gaya masa yadda alhaji Muntari ya dinga fad'i tashin akan lamarin yarana kuma ya rike mini su ba tare da ya bambamtasu da wanda ya haifa ba, na kara jadadda masa cewa abinda ya asassa mutuwar aurena dashi akansa ne saboda rubutun da na yi a fece book akan abinda ya faru wanda ya danganci Kamalu dashi."

Bayanin da na yi masa cikin nutsuwa ya sanya ya fahimce ni ya kuma tausaya mutuka da gaske koda yake dama shi mai tausayi dalilin da ya sanya mini fargabar gaya masa saboda tsohon mijina ne ban san fassarar da zai yi mini ba. A take a lokacin ya ce na yi waya da Baba Sule duk abinda muka tattauna sai na sanar dashi zai taimaka in sha Allahu.

Ban yi kasa a gwiwa ba kuwa na kira Baba Sule a waya ya gaya mini har yanzu dai ba kai ga kar'bar kudin gidan ba domin duk wanda zai zo tayin wulakanci yake yi. Na ce masa to abar batun sayar da gidan za a biya masu hakki hakkinsu insha Allah rabbi duk wanda yasan yana bin Alhaji Muntari kudi ya yi mini list din sunansu a takarda tare da asusun ajiyarsu idan na dawo sai ya kawo mini ni kuma zan tura masa sunayensu ta whasap sai a biya su hakkinsu.

Na sanar dashi yadda muka yi da ya ce hakan ya yi amma fa na ajiye maganar tafiya don su Hajja ne kadai za su tafi bi ba yanzu sai nan da kwana talatin lokacin Alhaji Amadu ya yi arba'in da rasuwa shi ma kuma

Please Login or Register in order to submit comment