You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sanin cewa matsala ce kwance-kwance. Cikin 'yar damuwa na ce."" Na kawo maka abinci ne?"""

"Ya girgiza kansa alamun a'a. Na ce."" Saboda me?"" ""Ke kadai za ki iya gamsar da ni yunwar cikina."""

Na yi shiru dai. Ina jinsa ya matso sosai tare da janyo ni jikinsa yasa hannu a dokin wuyana yana tatta'ba wajan da ya zama guru-guru kafin yasa baki ya sumbata. Shi kuma wuyana yana bashi sha'awa ko sunna muke yi ya dinga sumbatar wurin kenan har dasu sanya harshe.

Ya dora hannuwansa biyu duka a saman kirjina. Ajiyar zuciyarsa na ji a saitin kunnena. Ganin ya fara ki'dimewa

sai na dan ja baya tare da jan hanci domin na ma kasa cewa komai sai zare ido nake yi.

"Ya sake matsowa yana fad'in."" Menene haka, yaushe rabon ma da na nemi wani abu Hajiya ko ba ki yi kewata ba ne "

*GARKUWAR MATA.*

*BINTA UMAR ABBALE*

"[6/3, 8:38 PM] matar mijinta: *Wannan littafin na kudi ne 1k akan telegram hanyar da za a biya kudin ita ce wannan...0542382124...Binta Umar gtbank ko kuma 7084653262. Binta Umar Opey bank. 'Yan nijar dala dari katin"

airtel za ku tura mini bayan kun kankare hoton. A tura da sheda ta wannan lambobin iya What'sapp kawai.*

*07084653262*

*08089965176*

*V-VIP AREWA PEN *

*TALLAH!*

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/BieW3hHvRNIJLFNloG2CDl

Momyn Hajara GHT supplements

Muna da kayan gyara jiki na maza da mata munada magungunan matsalolin ma'aurata munada magungunan

kowacce irin matsala in sha Allah

Hadin Amare

Hadin Ango Hadin jego Hadin uwar gida

Hadin babbar mace

Hadin maida tsohuwa yarinya

Muna da Maganin sanyi kowanne iri

Muna da maganin ulcer Muna da maganin Asthma

Muna da maganin ciwon zuciya Muna da maganin ciwon Hanta Muna da Maganin hawan jini Muna da Maganin ciwon Ido Muna da Maganin rashin haihuwa Muna da Maganin skeler

Muna da Maganin kowacce irin cuta da yardar Allah

Sannan kowa zai iyayin register da campanynmu maitarin albarka kasari kaya kasiyar kaci riba sannan Kuma

campany yadunga biyanka albashi Duk watan da kayi aiki Saida kaya shine aikin da zakayi campany ya biya 07012621175

Register 8000 ne kachal

*94*

"Na ce."" Ba haka ba ne, kawai dai ina so na gaya maka ne cewar ba ni da tsarki."""

"Sai ya yi sakato yana kallona har ya so ya ba ni dariya domin wata kala ya zama kamar wani sakarai. Na yi kasa da kaina na ji yana cewa."" Ina ce 24 ga kowane wata na bature kike yin al'ada ko ba haka ba ne, yau nawa ga wata?"""

"Ya fad'i maganar yana tsatstsare ni da ido. Ban dube shi ba na ce."" Yau shida ga watan aprilu."" ""To mai ya kawo jini kuma?"""

"Shiru na yi domin kuwa zahiri ba na so na yi masa k'arya amma da sai na ce ai lokaci ya kan canza sa'i, da lokaci mussaman idan shekaru suka tura."

"Tambayarsa ya sake maimaitawa idonsa a kaina. Cike da shahada da kundubala na ce."" Dama ina so na gaya maka"

"ban san yadda za ka kar'bi lamarin ba, amma ni Allah ne shaidata, shine kuma zai tsaya mini a ko'ina, wallahi shekaran jiya cikin da nake d'auke da shi ya fita. Amma na alak'anta faruwar hakan da wannan rikicin da muke ciki, alhamdulillahi babu wata matsala domin Hauwa ta sanya Masa'udu ya sayo mini magunguña masu kyau sun taimaka mini k'warai wurin wanko mini mahaifata."""

"Lokaci k'ankani yanayinsa ya daidaita babu wani rausaye-rausaye da lumshe-lumshen Ido irin na fitina, zahirinsa ne ya bayyana ya 'kura mini idonsa da wani irin yanayi na mussaman tattare da shi."

"Kasa jimirin kallonsa na yi sai kawai na yi 'kasa da nawa idon cikin zuciyata ina fad'in 'Duk abinda za ka yi, ka yi wanda ya fi shi a baya kaddara ce."

'Dakin ya d'auki shiru na tsayin mintina bai tanka mini ba amma a jikina na ji cewar har yanzu bai cire kwayoyin idanuwansa daga kaina ba.

"Cike da ko'karin ture rauni da kasalar dake ko'karin dabaibayi ni na dago idona. Karaf idonsa ya shiga cikin nawa, gabana ya fadi ganin cikowar k'walla a dukkanin kwarmin idonsa don sauran kad'an ma ta fara tsiyaya."

"Gwiwa ta sage cikina ya sake murdawa. Cikin gaggawar na sake yin k'asa da kaina ban yadda na sake kallonsa ba domin ji na yi gabad'aya na sare lamarin har ya kai a ce za a zubar da kwalla. Na san a yanzu abinda ya fi buri da buk'ata bai wuce ganin gidansa cike da yara ba. To ni ba budurwa ya aure ni ba, balle ya ce, sannan kuma shekaruna sun yi nisa dukda dai ban wuce haihuwar ba, bayan haka kuma ni dashi muna da matsala wadda ya taketa da k'afafunsa na kuma yi hakuri na bi shi a yadda yake so. Ba ni da niyyar sake zubar masa da ciki tunda alkawari na d'auka tun lokacin sulhunmu da Baban Saude. Idan zan samu ciki ya kasance duk yaron da zan haifa yana da matsala zan jure dalili alkawari da rantsuwar da na yi wa Baban Saude Allah ne mai yin yadda ya so."

Kuma wallahi ni kaina na ji b'akincikin fitar cikin to don babu yadda zan yi ne kawai ya sanya ni ha'kuri ne tare da barwa Allah ikonsa. Ba ni jin ko da wasa duk irin rikicin da za mu yi dashi zan sake yun'kurin zubar masa da ciki da gagan domin tun farkon fari na gane hakan lamari ne mai mutukar hadari daka iya janyo babba matsalar da za a yi wahalar shanyo kanta dalili na ci wuya 'barin da na yi sakamakon shan kwayar zubar da ciki shiyasa gabad'aya lamarin ya fice mini daga rai na ajiye a zuciyata cewa zan haihu idan Allah ya kaddara mini koda yaran za su kasance masu rauni ta kowace siga.

Gyaran muryarsa ya dawo da ni daga dogon tunanin da na tafi. Dubansa na yi sai na ga babu kwallar gogeta ya yi ko

mayar da ita ya yi Allah ne masani.

"""Ta shi ki ba ni wuri kawai Amina, Allah Ubangiji ya yi mini sakayya."" Wannan maganar ya furta mini babu sukuni a tare da shi."

Ban ce masa komai ba kuwa na tashi na kama hanyar fita daga d'akin kamar yadda ya buk'ata. Allah ai al'musauwiru kuma da zuciyar bayi yake aiki.

Jikina gabad'aya duk a sanyaye ban san kuma mai ya taka ba tunda zahiri yanayin da ya shiga ya nuna mini cewa ya ji zafin abin.

"Bayan kwanaki biyu gidan na mu ya kasance kamar kufai. To babu motsin yara shiru. Hauwa kuma ta tsiri zaman d'aki sai na yi, na yi da ita ta fito falo ta'ki. Sai yamma muke zama ni da Baba Tabawa mu d'an yi hira. Shi kuma maigidan tun shekaran jiyan da ya fita bai sake leko mu ba."

Baba Tabawa tana kicin domin d'ora sanwar dare na fito falon da waya a kunnena.

"Bikin Yusura ne ya tashi kuma abinda ya kawo tsaiko a wancan lokacin balagorun da saurayin ya yi libiya domin neman kudi dalilin da ya sanya iyaye suke ce a bari ya dawo sai a d'aura auran tunda duk gidana. Mun gama magana da ita akan kada na ga ta sayi ko cokali domin tun da aka kawo kudin nake jadadda mata. Wancan karon ma na sanyata ta yi amfani da maganin sanyi hakan ba zai 'ki ba tunda ai 'ya macace, ita kuma duk inda take 'yar gyara da kula ce. Kuma koyaushe ba'a rabata da maganin sanyi domin shine tushen gyara aure da lalatashi. Garkuwar mata itace mai magunguñan Islamic din da na aminta da ita, dukda ita Hauwan ce ta had'a ni da ita, amma dalilin yawan sayan kayanta da nake yi ya sanya muka yi sabo da ita sosai. Duk wani nau'in magani na gyaran mace tana sayarwa masu kyau da inganci. Na ce ta sake yi mata magana akan ta hadawa amaryar set din amare kamar dai wancan karon zata hada mata magangunan sanyi da na gyaran nono sannan ta kuma yi mata budurwar kaza da sauran maganin gyara idan sun gama zan tura mata kudin daga nan, in sha Allahu 08089965176 duk wata 'ya mace da take neman sahihan magunguña masu kyau marasa cutar da GARKUWAR jiki to ta nemi GARKUWAR MATA domin kuwa kayanta duka babu na kaico ana samun biyan buk'ata."

Bayan mun gama maganar sai na kashe wayar na nufi kicin domin anan nake jin motsin Baba Tabawa na sameta

"tana ta buga sakawara a turmi. Na ce."" Sannu da aiki Baba."" Ta juyo da sauri tana amsawa. Na ce."" Baba ko dai a samo miki wadda za ku dinga aikin nan tare, dukan sakawara na mai k'wari ne."""

"Tana dariya ta ce."" Ni ma da kwarina ai, kuma aikin duka duka guda nawa yake. Yara ba anan suke cin abinci ba, ku biyu ne fa sai ni ta uku sai Masa'udu sai masu gadi biyu shikkenan fa, to sai kuma mai gayya mai aiki idan ya shigo gidan shi ma kuma sa'i da lokaci ne."

"""Na ce."" Hakane amma duk da haka za a cigita wadda za ta taimaka miki koda da wanke wanke da shara ne ke kuma sai ki ji da girkin ko.''"

"Ta gyada kanta tana fad'in."" To hakan ya yi babu lefi, yau na ce bari na yi sakawara an kwana biyu ba a yi ba. Na ce."" Hakane kin ga ma tana daya daga cikin abinda maigidan yake so bayan towon da kike masa."" Tana bud'e leda ta ce."" Ina kuwa fatan Allah Ya sa ya shigo gidan yau."" Na amsa da amin a takaice kafin bar kicin din jin alamun motsi a falon."

Khalil ne tare da Usaina sai wata matashiyar budurwa da bata haura shekaru ashirin da biyar ba.

"Rige-rigen gaishe ni suka fara yi har da tsugunawa ""Mama ina yini."" In ji Khalil na amsa ina dariya tare da nazartarsu yaran suna cike da walwalarsu da annushuwa gasu nan cikin suttura mai amince. Itama ta tsuguna ""Mama ina yini."" Usaina kenan. Dariya ta kama ni na ce."" Ina yini Usai ina Hassana da Minal"" Ta tashi tsaye tana ce wa."" Suna can gida."" Khalil ya ce. Momi ce ta ce wai ga mai lallan da take yi mata..."

Littafin kudin aure na kudi yar uwata kada k8 karanta mini ba tare da kin biya ni hakkina ba.

"Na ce."" Aikuwa ka ce mata mun gode sosai."" Suka juya za su fita sai na ce."" Kai Khalil dawo ku shiga ku gaida"

"Mamanka mana."" Ya ce."" To. D'akinta suka nufa tare da Usaina tana bin sa zugwi-zugwi a baya. Na sauke ajiyar zuciya bayan shigewarsu na juyo kan mai lallan cikin nutsuwa ta gaishe ni na amsa ina fad'in."" Wane iri za a yi mana ja ne ko baki?"""

"Tana fito da kayan aikinta daga cikin wata 'yar jaka ta ce."" Duk biyun Ina yi wanda kuke so za a yi."""

"Na ce."" To a yi mini duka ja da bakin. Amma dai ba na son dogon zama. Ta ce."" In sha Allah daga nan zuwa magriba komai ya kammala."""

"Khalil ne ya zo ya gifta ni yana goge fuska. Da sauri na ce."" Kai menene ."" Bai ce mini komai ba ya wuce yana dafe idonsa. Kawai na ji fashewar kukan Usaina cikin gwarancinta tana ce wa."" Mama ta dake shi a fuska."""

"Da wani irin yanayi na ce ."" Mai ka yi mata?"""

"""Ba komai."" Ya fad'a da sauri ya kama hanyar fita kamar ma a tsorace yake Usainar ta bi bayansa itama da sauri. D'akin na shiga na ji motsinta a bandaki tana ta kakarin amai. Can na bita sai da ta gama tukkuna ta wanko fuskarta ta fito koda ta gan ni a tsaye a bakin kofa ba ta ce mini komai ba ta nemi gefan gado ta zauna. Laulayin ne ya dawo mata sabo da kuma hatsaniyar nan da muke ciki gabad'aya duk yanayinta ya canza ga wani uban haske da ta yi fau sai wasu k'ananun kuraje da suka feso mata a fuska."

"Na ce."" Wai ba ki da lafiya dama Hauwa."""

"Tabe bakinta ta yi kafin ta girgiza kai ta ce."" Amai ne ya takura mini wallahi cikin 'yan kwanakin nan, amma in banda shi babu abinda ya dame ni."""

"Na gyad'a kaina a sanyaye na ce."" Allah Ya bada lafiya."" A takaice ta amsa da Amin."

"Na ce."" Khalil ya fito yana kuka Hauwa ba kya neman zaman lafiya ko, kin fi kowa sanin abinda mutumin nan ya tsana a rayuwarsa a daki yaran nan mussaman shi Khalil din daga gaisuwa kuma sai duka fisabillahi , ai ba shi ya yi miki ba."""

"""So na ke a yi ta take ai, shiyasa na dake shi. Ni ma ai iyayene suka haife ni. Ya dake ni a fuska kwanaki yanzu kuma yana dukan zuciyata da iyakacin karfinsa. Bai isa dai ya canzawa towo suna ba."""

"Shiru na yi Ina nazarin maganarta kafin na ce."" Duk wannan bai ta so ba, za ki dasawa yaron nan k'iyayyarki da jin tsoronki a cikin ransa. zai kara yin nesa dake tunda tsakaninku duka ne da kyara da hantara, don girman Allah ki daina."""

"Hannu ta daga mini sai kuma hawaye suka k'wace mata ta ce."" Kin san irin rad'adin da nake ji a zuciyata kuwa Amina"

"? wai Yaya Tajo shine yake fifita wata bare wadda ba su had'a dangantakar komai ba akaina. Na haihu dashi Bata haihu dashi ba. Jinina ne shakiki. Ita kuwa a duniya suka had'u, amma ya tozarta rayuwata a kanta. Wallahi har na mutu ba zan yafewa matar nan da alhalinta ba."""

"""Kai! Innalillahi! don darajar Allah Hauwa maganar nan ta mutu haka na rantse da Allah ta ishe ni. Ki gyara tsakaninki da shi kawai ki daina duba wata dangantaka namiji ne za ki ga abinda ya fi haka fa."""

"Shiru ta yi ba ta ce komai ba, na ce."" Ga mai lalle ta zo za ta yi mana, ki fito falo."""

"Ta dube ""Kin ga na yi kama da wadda za ta yi wani lalle yanzu?"""

"Na ce."" Kwarai kuwa, ai ke ya kamata ma ki yi kitso da lalle domin jan hankalin mijinki ku daidaita har ya janye abinda ya ratsa tsakaninku."""

"Ta ja tsaki tare da gyara kwanciyarta tana fad'in."" Kada Allah Ya sa ya janye wallahi babu abinda zan yi, ai ke ce matar gida "

*GARKUWAR MATA.*

*BINTA UMAR ABBALE*

"[6/3, 8:38 PM] matar mijinta: *Wannan littafin na kudi ne vip 1k akan telegram. Normal What'sapp group kuma #700 hanyar da za a biya kudin ita ce wannan...0542382124...Binta Umar gtbank ko kuma 7084653262. Binta Umar"

Opey bank. 'Yan nijar dala dari katin airtel za ku tura mini bayan kun kankare hoton. A tura da sheda ta wannan lambobin iya What'sapp kawai.*

*07084653262*

*08089965176*

*V-VIP AREWA PEN *

*TALLAH!*

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/BieW3hHvRNIJLFNloG2CDl

Momyn Hajara GHT supplements

Muna da kayan gyara jiki na maza da mata munada magungunan matsalolin ma'aurata munada magungunan

kowacce irin matsala in sha Allah

Hadin Amare

Hadin Ango Hadin jego Hadin uwar gida

Hadin babbar mace

Hadin maida tsohuwa yarinya

Muna da Maganin sanyi kowanne iri

Muna da maganin ulcer Muna da maganin Asthma

Muna da maganin ciwon zuciya Muna da maganin ciwon Hanta Muna da Maganin hawan jini Muna da Maganin ciwon Ido Muna da Maganin rashin haihuwa Muna da Maganin skeler

Muna da Maganin kowacce irin cuta da yardar Allah

Sannan kowa zai iyayin register da campanynmu maitarin albarka kasari kaya kasiyar kaci riba sannan Kuma

campany yadunga biyanka albashi Duk watan da kayi aiki Saida kaya shine aikin da zakayi campany ya biya 07012621175

Register 8000 ne kachal

*95*

"Na gyad'a kaina ba tare da na sake yin wata magana ba na juya na fita daga d'akin gabad'aya zuciya sam babu dadi, abin nata kuma ya fara ba ni haushi ya daga gyara kayanka sai ba'kar magana. Ai duk wanda ya sayi rariya ya san za ta zubar da ruwa. Ni ban ce Hauwa shigar rigima ba domin tun lokacin da na ga ta dage tana ta tsalle akan hatsaniyar nasan lallai da akwai abinda zai faru. Ta sha gaya mini ita ta gaji da auran to yanzu kuma an sake ta tana kuka. Ni tausayinta ma nake ji wallahi ga ciki ga rashin zaman lafiya da miji dalilin da ya sanya kenan nake tausarta ta"

yi hakuri akwai takaici kwarai da gaske da ciwo namiji ya nuna baka da wani amfani a wurinsa domin dai sakin da ya

yi mata ko a kwalar rigarsa bai damu ba ya dasa mata k'unci yana gefe yana cigaba da gudanar da rayuwarsa. Wadda take yi domin ita tana can hankalinta a kwance mijinta yana neman hanyar da zai faranta mata da tun farko ta yi amfani da shawarwarina da duk hakan bai faru ba ta lallaba ta zauna a dakinta.

Yarinyar ta iya lalle sosai tana da zane mai ban sha'awa ganin kamar ta d'auki mai wahala da jinkiri ya sanya na ce ta takaita domin ba ni son zama shine dalilin ma da ya sanya ban fiye yin k'unshin ba.

"Baba Tabawa ta kammala aikinta ta fito ta zauna a falon muna hira jefi-jefi har yarinyar ta kammala tsaf ta had'a kan kayanta. Na ce."" Ai kina da acct ko?"""

"Ta ce."" E, ina dashi amma Momi ta ce da ni kada na kar'bi komai."""

"Cike da mamaki na ce."" Saboda me?"" Tana murmushi ta furta."" Da farko antina ce take mata lalle sai ta yi aure ni ma dama tana koya mini shine na kar'bi sana'ar duk k'arshen wata nake shigowa cikin estate din nan naku akwai wad'anda nake yi wa bayan Momi din. Mun saba k'warai da ita ta yi wa antina komai haka zalika ta samawa babban yayanmu gurbi a daya daga cikin shagunanta dake garin nan, gashi nan har ya yi aure shekara daya kenan matarshi ta haifi mace ya sanya mata sunan momi din wato Maryam muna kiranta da Sahiba."""

"Da murmushi a fuskata na ce."" Duk da haka dai ai ni ma alheri zan yi miki ganin irin yadda ki ka b'ata lokaci wurin yi mini ado da zananan henna mai kyau, shin ko ba kya so mu saba ne?"""

"Dariya ta yi kafin ta ce."" Kai anti wannan ba komai ba ne akan wanda nake yi don na ji kin ce na takaita ne shiyasa amma da wanda zan yi miki sai ya fi wannan tsaruwa."""

"Na ce."" Wannan din ma ya burge ni sosai na gode miki, amma ai ko turare kya kar'ba ko."""

Ta yi kasa da kanta tana murmushi. Ni ma murmushi nake yi can kasan zuciyata kuma ina tunanin idan har mutane za su dinga yabonka tun kana raye tabbas babu abinda zai hana ka sha'kar rahamar Allah idan ka gushe! wato ita dai Momi ko'ina alherinta zagayawa yake yi duk wanda ala'ka ta had'aka dashi muddin ya santa to alherinta zai fara gaya maka.

Muna nan zaune muna hira da ita budurwar wadda take gaya mini sunanta Lad'ifa iyayenta yan asalin jalingo ne aiki ya kawo mahaifinsu nan abuja amma k'aramin ma'aikaci ne..

Ta duba agogon da yake tsintsinyar hannunta na dama wanda nake hasashen tana d'aura shi ne domin duba lokaci a sa'in da ta d'aurawa mutam lalle da kwance shi.

"Ta ce."" Yanzu sai a cire tunda ya samu awa biyu cikakku. Dama dalilin da ya sanya ban tafi ba kenan.. ta d'auko wata leda babba da cokali mai dan fadi daga sama cikin nutsuwa ta fara cire lallen kafin ta d'aye salatif din zanen ya fito d'au ya yi bala'in kyau da kamawa. Baba Tabawa fadi take yi ""Ashe haka kike da cin lalle Amina amma ba kya damuwa da yi."""

"Na ce."" Duk da haka dai ai lallensu daban yake suna yi masa hadi na mussaman."""

"Da kaina na cire na hannun ya tafi da ni sosai nan da nan na ga ba dawo mace har ina jin dadin duba hannuna. Na ji tana ce wa."" Sai gobe zai sake fitowa sosai."" Tsaf ta goge mini kaf ta shafe duk inda lallen yake da wani abu sannan ta sake had'a kayanta a karo na biyu. Baba Tabawa da kanta ta d'auko mini takalmin da da nake amfani da shi a d'akina ta kawo mini na sanya na tashi ina fad'in.'' Ladifa alwala ai ta zama dole da fatan babu matsala ko."" Tana murmushi ta ce."" Babu matsala anti."""

Kai tsaye d'aki na wuce na had'o mata Turaruka da sabulai.

"Fitowa ta yi daidai da lokacin da ya shigo yana daga bakin kofa suna magana da yarinyar kamar sun d'an saba da juna ko da yake shi din ba ma'abocin shariya ba ne idan yau kuka hadu to zai mu'amulanceka kamar kun yi shekara da sanin juna, mutum mai sau'ki hali da nuna shi ba wani ba ne a rayuwa."

Wannan dabi'un nasa na zahiri sune suka danne ba badi'ini wanda mu da muka dangance shi kuma mafi kusa dashi yake yi mana. Amma kaf jama'a da ma'aikatansa yana mu'amulantarsu ciki sau'ki babu wata izza da nuna ni wani ne. Abinda anti Yagana take fad'a kullum kenan domin ita kanta ladabi yake yi mata ko magana suke yi baya iya had'a ido da ita wai ai yayata ce wasu lokacin har anti Yagana yake ce mata kamar yadda nake kiranta abin ya yi ta bani takaici da b'akinciki. Makirci sai kace babbakakken dan duniyar da ya gaji da yawon bariki kaf ya saye mini dangi har da Baban Saude domin sai da ya san yadda ya yi ya 'kulla abota da shi mai karfi. Amma nasan Baban Saude mutum ne mai tsinkaye da hangen nesa kuma ba zai ta'ba take gaskiya ya d'auki karya ba idan duk duk duniyar nan za a ba shi yana da taurin kai da ra'ayin rikau!

"Ledar hannuna na mik'a mata ina cewa ""Ki gaishe da mutan gidan, tunda kin ki kar'bar kudi ga wannan sai ki yi"

"amfani da su, na gode kwarai."""

"Ta kar'ba tana godiya sosai kafin ta kama hanya ta fita cike da nutsuwa. Baba Tabawa ta wuce dakinta itama. Sai mu biyu a falon na daure na ce."" Barka da shigowa."""

Don girman Allah kada ki karanta mini littafi ba tare da kin biya ni hakkina ba.

A takaice ya amsa kafin ya nemi hanyar matattakalar samansa. Ban yi kasa a gwiwa ba na bi bayansa. Ya shiga

"bandaki nasan alwala zai yi ya fito yana gyara hannun rigarsa dake tattare. Kallo daya ya yi mini ya kama hanya zai fita na ce."" Idan babu damuwa Ina son magana da kai."""

"Bai juyo ya dube ni ba ya furta."" To, bari na dawo daga massalaci."" Ya fice a gaggauce."

"Na samu gefan gado na zauna babu wani karsashi a tattare da ni, nasan da ban yi masa magana ba, bai zama lallai idan ya fita ya dawo ba, shigowar nan ma nasan ya yi ta ne akan dole domin sanin halin da muke ciki. Idan yana

Please Login or Register in order to submit comment