You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

masa huduba da Ibrahim Khalil sunan kakansa kenan sai uban ya ce a dinga kiransa da suna Khalil. Ya sha gata kwarai da gaske daga wajan Babanshi da abokansa kuma ni ban ji haushin duk irin hidimar da zai yi akan haihuwarsa ba, komai yana da lokaci kuma amfanin dukiyar kenan."

Ba su shirya wani gagarimin taron suna ba don maijegon tana d'an fama da ciwon kafafu da yake sun yi kumburi irin

"na ciki, amma suna sacewa a hankalina. Ma'aikaciyar lafiya ce ita dalilin da ya sanya ma kenan ta ce babu wani gagarimin taro da zata yi iya family dinsu ma kadai sun isa tunda suna da yawa. Hakan ma don ba yadda za ta yi ne domin wani ko ka ce masa babu suna to sai ya zo shiyasa inna Uwani ta ce dangi ba za a hana su zuwa ba, ita kuma yanayin jiki da lafiyarta baya buk'atar hayaniya saboda jininta ya d'an hau kad'an bayan haihuwar amma dai ya daidaita yadda ake bukata yanzu."

Hidima sosai ya yi musu don gaskiya ya 'batar da kudi ko ga yanayin irin mahaukatan kayan da sayawa yaron ita kanta maijegon ya saya mata sutturu sannan ya bata kud'i. Haihuwar fari ce a wajensa itama haka babu lefi a cikin dukkanin abinda ya yi

*GARKUWAR MATA.*

*BINTA UMAR ABBALE*

"[6/3, 8:38 PM] matar mijinta: *Wannan littafin na kudi ne vip 1k akan telegram. Normal What'sapp group kuma #700 hanyar da za a biya kudin ita ce wannan...0542382124...Binta Umar gtbank ko kuma 7084653262. Binta Umar"

Opey bank. 'Yan nijar dala dari katin airtel za ku tura mini bayan kun kankare hoton. A tura da sheda ta wannan lambobin iya What'sapp kawai.*

*07084653262*

*08089965176*

*V-VIP AREWA PEN *

*75*

"Da gaske dai maleji yake yi da amaryarsa domin tun yana 'boyewa yanzu a fili yake nunawa. Ita dai macace wadda ta kware wajan iya kalamai romance amma fa a shimfida sunanta sorry raguwa ce. Wata'kila hakan kuma yana da ala'ka da rashin sabo domin kuwa kowane namiji da irin hallitarsa zata iya kasancewa tsohon mijinta ba shi da karfin sha'awa da fitina irin nasa. Shekara da shekaru ta riga ta ginu a haka, ga shekaru sun tura tana sake yin rauni gefe guda kuma ga hidindimu na yau da gobe harkokinta na kasuwanci wannan kadai ya isa ya cire mata na ci da k'ulafucin d'a namiji. Shiyasa aka ce mata suna suka tara kowace mace akwai ta inda tafi kauri akwai kuma ta inda ta gaza, wasu matan kuma duka sai ka ga Allah Ya had'a musu mazajensu suna amfanuwa dasu ta kowane sashe. Tabbas ba yabon kai ba. Ni kaina na tabbatar da cewa Ubangiji ya yi mini baiwa da ba kowace mace yake yi wa irinta ba. Bai fito ya gaya mini ba a fili ba amma na tabbatar da cewa ni ce giwa kuma zinariyar zuciyarsa da kuma cikin gidansa."

***

"Kwanan Hauwa arba'in da shida da Haihuwa ya zo yana gaya mini za ta dawo amma ya nake gani domin ya bari ne ta gama wanka sai ya koma legos bayan mun yanke shawara. Na ce kawai ya bari ta zo nan 'din sai mu yanke shawara a tare domin ni har yanzu ban gama aminta da tsarin da ya yi ba, tabbas idan za mu raba wata shida shida ni da Hauwa to kuwa ban ga amfanin auransa da Hajiya Maryam ba domin kuwa idan ya ce zai biye mata akan abinda take so saboda wani dalili to kuwa babu shakka akwai gyara a cikin auransu. Ba zai yiwu a ce saboda mu kad'ai ne za mu dinga d'aukar lalurarsa ba. Itama ai matarsa ce tsakani da Allah kenan ni na yarda zan d'auki wata shida idan ya so su kuma su raba wata uku uku a tsakaninsu."

Da kansa ya je bauchi domin ya d'auko Hauwa da yaronta. Tabbas idan a da can babu soyayyarta a zuciyarsa to

"yanzu kuwa ba za a rasa ba, ba don komai ba sai dalilin abinda ya ratsa tsakaninmu wato yaron da suke haifa a tare. Ban ji haushinsa ba dangane da duk rawar kan da yake nunawa akanta da yaronta domin kuwa na riga na tabbatar da cewa hakan sai ta faru to damuwa da bakincikin hakan zai iya haddasa mini ciwo ne don babu wani abu da zan iya hanawa, matarsa ce kuma uwar yaronsa. Babu dalili mai k'arfi zan ce masa abinda yake yi ba daidai ba ne. A wasu lukutan ma ni da kaina nake taya shi mu had'u gabad'aya mu yi ta kallon hoton yaron wanda kamaninsa ke k'ara fitowa sak kamar ya yi kaki ya tofar."

Ranar da ta dawo tare da ita ya kasance domin gidane mai yalwa wadataccen zaman mace hud'u kuma cikin sakewa babu takura balle wata ta ce an matseta.

Washe garin ranar da ta dawo da yamma muna tare falon Khalil yana hannuna muna hira da ita cikin kulawa kamar babu wata matsala da ta taba faruwa a tsakaninmu yadda na lura ma ba ta fiye so mu had'a ido ba ko magana take yi kanta a 'kasa ko tana kallon wani waje daban a haka muke yin hirar. Cikin zuciyata na godewa Allah da bai sa na cuceta a zamantakewarmu ba abinda suka yi a can baya shine yake damunta

"Towol din goyansa ta d'auko mini na goya shi a bayana, cikin kankanin lokaci bacci ya d'auke shi. Ina daga tsaye ina dan jijjigashi tana gaya mini irin rigimar da ya dinga yi kafin su yi arba'in har yanzu bashin baccin da ta tara bai sake ta ba."

Maigidan ya shigo amaryarsa a bayansa ta nade jikinta da wata lafiyayyar lifaya irin ta manya. Duk shigar da za ta yi da gayu ba abin mamaki ba ne domin ko bata auran mai dukiya ita kanta hajiyar kanta ce ga uwar dukiyar da aka mutu aka bar mata da yaranta.

"Fuskarta a sake ta zauna kan kujera tana dariya yayin da take kallon Hauwa tana ce wa."" Maijego ina fatan ba ki yi fushi da ni ba ko?"""

"Hauwa ta dan yi murmushi irin wanda babu nisha'di a takaice ta furta."" Ban yi ba Hajiya ai maigidan ya ce ba ki ji dad'i ba ya jikin naki?"""

"Ta ce."" Wallahi kam a lokacin na yi ta fama da zazzabi da mura har da ciwon kai, dalilin da ya sanya kenan ban samu zuwa ba."""

"Ta ce."" Allah Ya sawwa'ke abinda ake ta fama dashi kenan."""

Na kwanto yaron fuska a sake na mik'a mata shi ta kar'ba da walwala a fuskarta. Ko ba a fad'a ba ita din macace mai

masifar son yara ko ba na bata ne wallahi irin rikon da take yi wa Yusi ko ni albarka duk abinda yaranta za su sanya a jikinsu za su ci babu bambanci wannan kad'ai ya kan sanya ni jin kunya da nauyin yin tutsu akan lamarinta. Kuma sam ba ta da fitina a haka dai tana zaune da kowa lafiya ban ta'ba ganin kishi a idonta ba.

Dad'in ganinmu mun sake muna hira gabad'ayanmu ya sanya shi kashingida kan kujera yana ta murmushi tunda

suka shigo bai ce komai ba sai kallonmu yake yi yanayinsa ya nuna ya ji dadin ganin yadda muka fara fahimtar juna. Sai bayan mun nutsu tukkuna ya gyara zamansa domin mu tattauna tare da samun matsaya akan yadda za mu shirya zama. Legos ne kowacce bata so a cikinmu amma kuma tilas ya kama mu duka saboda babu yadda za a yi ace mu bar shi a can shi kadai alhalin duka muna raye adalci shine a ce a raba.

"Ni ya bawa damar magana tunda ni ce gaba dasu gidan cikin nutsuwa na ce."" Ni na amince zan dau'ki wattani shida idan ya so ku kuma sai ku raba kowacce wata uku ina ganin hakan zai fi."""

"Hajiya Maryam tana murmushi cikin nutsuwa ta ce."" Anya kuwa ni zan iya akwai abubuwa da yawa da suka sha kaina anan din wallahi ba na so na yi nesa yanzu ko kad'an shi Yallabai din ya sani da za ku yi mini alfarma sai na ce ku barni a nan babu damuwa ta b'angarena in sha Allahu."""

Falon shiru ya yi bayan maganarta. Yana zaune bai ce komai ba alamu sun nuna tun a gidanta sun gama maganarsu ya d'aukota ya kawota ne don ya wanke kansa kada mu zarge shi.

"Na dubi Hauwa da tun da muke maganar ba ta ce uffan ba na ce."" To ke me ki ke ga ni Hauwa."" A takaice ta ce."" Duk yadda kuka tsara ya yi mini sister."""

"Sai na dube shi a nutse na ce."" To ka ji abinda kowa ya fad'a menene ra'ayinka?"""

"""Ra'ayina shine naku giwa, ku tsara yadda kuke ganin za ku zauna babu takura idan kun yi mata alfarmar da ta nema ni a wajena daidaine amma kada wadda ta kalubalanceni anan gaba. 'Yar uwarku ce ta kuma fito ta gaya muku dalilanta nasan zamanta anan din cikinku duk kun sani, idan kun goya mata baya to duk 'karuwar ta mu ce bakidaya."""

"Ban yi mamaki da sunan da ya kira ni ba, domin a wasu lukutan da sunan yake kira na mussaman idan yana so ya rarrashe ni idan mun yi fada ko neman wata buk'ata. Zai ce giwa ko zinariya"

"Cike da takaicin maganganun da yake yi na ce."" To wa ka ji ya ce bai amince ba, na d'auka ai zaman da muka yi gabad'aya don mu samu matsaya ne a junanmu, ni ta b'angarena babu damuwa tunda har na iya d'aukar rabi na basu rabin na ce su raba a tsakaninsu Allah Ya taimake ka duk wannan maganganun ba su taso ba."""

"Hauwa ta zum'buri baki tana fad'in."" To ni ma dai haka na ga ni."""

"Ita kam dariya ta yi tana fad'in."" Na gode sosai, Allah Ya daidaita zamanmu ya kuma amfani zuriyarmu, na gode ni zan koma."" Ta mike tsaye tana gyara yafen lifayar da take jikinta."

"Na ce."" A haba Hajajju ai babu buk'atar godiya duka taimakon kai ne wallahi kada ki damu an zama daya gabad'aya Allah Ya shige mana gaba."""

"Ta amsa da ""Amin."" Fuskarta yalwace da fara'a ta kama hanyar fita tana fad'in."" Sai na sake zuwa mu gaisa da yarona yanzu bacci yake yi ba mu gaisa sosai ba."" Hauwa ta ce."" To shikkenan sai an jima."

"Tana fita Hauwa ta dube shi kamar za ta fashe ta ce."" Gaskiya zan gaya maka irin yadda kake nunawa matar nan"

"kamar itace take auranka ya yi yawa. Ina lefi akan kawaici da karar da muka yi mata har sai ka fad'i wasu maganganu, ai sai ta d'auka hassada muke yi mata, kuma macace mai mutunci da sanin ya kamata gatanan babu wata matsala a tare da ita."""

"Ya ce."" Mai na yi muku kuma, shikkenan daga na fad'i magana sai ku juya mini, halinta na fad'a tana da sau'kin kai"

"gashi dai duk ta girmeku amma bata nuna muku gadarar hakan. Sannan duk da dukiyar da take da ita bata d'auki kanta a wata tsiya ba, ta sake daku sosai ta daukeku 'yan uwa daga fad'in haka sai ya zama lefi."""

"Na ce."" Mu ai dama ba muce maka wata tsiya ba ne, kuma duk abinda take yi ai ba a sanyata ba gani ta yi zata iya,"

"abinda dai zan gaya maka idan zama ya sake hadamu irin wannan muddin kasan zaka goyu da bayan b'angare daya to kawai ka yi shiru da bakinka domin kuwa yin hakan zai janyo maka bacin rai za ka rikita gidanka da kanka."""

Don girman Allah kada ki karanta mini littafi ba tare da kin biya ni hakkina ba.

"Ya ce."" Tunda kece Hajja sai ki ba ni umarni kin ji ko, ku abu kad'an mutum zai yi sai ku zarge shi Allah Ya sawwa'ke."""

"Yana rufe baki Adam da Yusi suka shigo janye da wata madaidaiciyar akwati gaban Hauwa suka ajiye Adam ya ce."" Momi ce ta ce wai gashi na Khalil ne."""

"Ta ce."" Ku ce mata na gode sosai Allah Ya kara arziki."""

"Suka juya za su fita muka had'a ido da Yusi sai yasa dariya ya rike hannun Adam na d'auke kaina ina fad'in."" Taka zata kawo ka wurina ne yaro."""

"Har za su fita sai ya kira su ya dubi Yusi yana fad'in."" Mai ka yi mata take harararka?"""

"A hankali ya ce."" Babu komai Baba, ai muna shigowa kullum mu gaisa da ita ko ?"" Ya fad'a yana kallon Adam da yake"

"murmushi. Ya amsa da ""E Muna zuwa."" Ya ce musu ku tafi abinku rigima take nema."" Suka bud'e kofa suka fita kamar wasu 'yan tagwaye komai na jikinsu iri d'aya ne."

Kaya ne na waje irin wad'anda take sayarwa cike da akwati kayan nan kudinsu zai haura dubu dari uku domin duka

"babu k'ananu har da takalma da tarkace dai kala kala. Tare muka duba kayan yana zaune bai ce mana komai ba, har muka gama dubawa muka rufe akwatin bai tanka ba daga karshe ma sai ya tashi ya haye ya sama ya barmu a falon mu biyu."

To ganin yadda muka k'ulle muka zama tsintsinya madaurinki d'aya ya sanya shi shiga hankalinsa sosai. Tun ranar da

"muka yi zaman nan bai sake yin wata magana da ta danganci matarsa ba saboda ganin yadda muka nuna masa ba mu yarda ba a tun farkon fari. Dama neman magana ne kawai tunda na farko ai bai ga mun ware ta ba, sannan bai ga muna neman fitina da ita ba, maganace a ka zauna ana tattaunawa wadda kowa yake da hakki akai to babu dalilin da zai sanya shi ya budi baki ya yabe ta a gabanmu bayan alfarmar da muka yi mata. Macace mai nagarta kuma wadda take amfani da ilminta a inda ya dace. Duk irin kushe da kiyayyar da mutum zai yi a kanta wallahi kyawun halinta sai ya sanya wataran mai kushiya akanta ya yaba mata......"

Muje zuwa

*GARKUWAR MATA.*

*BINTA UMAR ABBALE*

"[6/3, 8:38 PM] matar mijinta: *Wannan littafin na kudi ne vip 1k akan telegram. Normal What'sapp group kuma #700 hanyar da za a biya kudin ita ce wannan...0542382124...Binta Umar gtbank ko kuma 7084653262. Binta Umar"

Opey bank. 'Yan nijar dala dari katin airtel za ku tura mini bayan kun kankare hoton. A tura da sheda ta wannan lambobin iya What'sapp kawai.*

*07084653262*

*08089965176*

*V-VIP AREWA PEN *

*76*

"Ina jin kunya da nauyinta sosai, ba don komai ba sai don yadda take k'aunar abinda ya jib'anceni. Na jima ban ga mutum mai kara da kawaici irinta ba."

Daf da zamu tafi Legos muka yi waya da Sahura take gaya mini an kawo kudin Yusra an kuma sanya rana shekara

daya mai zuwa. Na ce har saurayin ya gama ginin kenan ta ce mini saura kad'an. Daga sanda muka yi waya da ita na ce zan yi magana da garkuwar mata wadda dama tun asali Sahurar ce ta had'a ni da ita tun lokacin aurana da Alhaji Muntari tun daga sannan da na fahimci magangunta suna da inganci muke zumunci da ita domin daga zarar na bukaci abu zan yi mata waya zata sanya a kawo mini abinda na buk'ata din.

kano take kuma tana aika kayanta kowane gari dole za ta hadawa yarinyar maganin sanyi domin shine abu na farko da ya kamata a fara dashi sannan Yusura bata da cikar kirji sosai har dana gyaransu zan sanya ta had'a mata duka domin kafin zuwan lokacin ta murmure

Na ce da ita idan sun gama magana da ita ni kuma zan tura mata kudin in sha Allahu.

Ta dinga godiya har sai da ta sanya ni na ji haushi na ce ta bari ba na so domin kuwa Yusura haihuwarta kawai ta yi amma na fi ta cin moriya kuma ban yafe mata ba muddin ta sayi ko cokali akan sha'aninta kawai ta bar mini hidimata ta ce. Ta dinga dariya tana fad'in Lallai abin har ya kai haka. Na ce ya wuce hakama a wajena domin kuwa abinda ya shafeni.

"Kafin mu tafi sai da na kira Babanmu duka na yi masa bayanin abinda yake faruwa amma ban sanar dashi matsalar da ta kaini wajan Baban Saude ba, sosai ya yi mini addu'a da fatan alheri. Ya kuma tabbatar mini da cewa ana samun cigaba ta bangaran Ummansu Hadiza domin yanzu hankalinta ya fara daidaita ta dawo hayyacinta ta ha'kura da kaddara ta barwa Allah komai. Amma har yanzu Hadiza na can gidan gyaran hali a ajiye ba a kai ga yanke mata hukunci ba ana ta neman ita wadda suka had'a kai suka yi aika-aikar wato Hajiya Alili."""

Mun yi waya da anti Yagana na gaya mata za mu wuce legos ban rufe mata komai ba duk na gaya mata irin yadda muka tsara zamantakewar gidan. Ta ce mini hakan da na yi shine daidai a matsayina na babba daga cikinsu dole ni zan dinga 'kokarin d'aukar girma saboda tabbatuwar zaman lafiya.

Sati uku da komawa legos na fara laulaye-laulaye. Ciki fa ya samu abinda ake nema ban gaya masa ba da kansa ya

fahimta ya dinga murna kamar me ni dai dariya kawai nake yi masa amma can 'kasan zuciya cike nake da zullumi da

fargabar abinda zai kasance bayan na haihu. Shi kuma maganarsa daya Allah Ya sa tagwayene. Kullum abinda yake

cewa kenan sai dai kawai na yi murmushi gefe guda kuma na tsananta addu'a akan Allah Ya ba ni d'orarre.

"Ban yi tsammanin zai gayawa kowa ba kawai watarana sai Hajja ta kira ni a waya muka gaisa dama kuma sa'i da lokaci takan kira ni, ko kuma ni na kira ta mu gaisa har ta tambayeni zamanmu na ce mata komai lafiya. Cike da farinciki take magana ai maigidan ya gaya mata na samu ciki. Ta dinga ba ni shawarwari akan na kula sosai kada a sake samun matsala irin ta baya. Idan ma ina so sai ta zo ta zauna mini irin na goyon cikin baby Nana aish."

"Na ce mata in sha Allahu zan kula sosai amma ta yi zamanta tunda bata da wadataciyyar lafiya bayan haka kuma abun zai zama wani iri muddin Hauwa ta ji labari ba zata ji dad'i ba, abinda haihuwa ba ta farko ba ce, babu wata matsala da za ta faru."

Da wannan na rufe bakinta ta ce mini shikkenan amma dai za ta sanya a rubuce mini al'kur'ani maigirma. Godiya sosai na yi mata muka yi sallama. Hajja macace mai dattako kwarai da gaske tana k'aunata fiye da tunanina don ma an yi yun'kurin shiga tsakanina da ita a baya.

***

"Watanni shida ciki ya bayyana ya fito sosai duk wasu gwaje-gwaje da scanning an yi mini tagwayene duk mata. Ya rasa ina zai sanya rayuwarsa duk fitina irin tasa ha'kura ya yi a sati bai fi ya kwanta da ni sau biyu ba wai kada yaran dake cikina suga kamar an takura musu. Acewarsa yawan motsa ni da yake yi zai sanya su dinga shan wahala. Abin sai ya ba ni dariya da mamaki. Tun suna ciki basu fito ba yana nuna musu k'auna irin haka, ai ni ma 'yar wani ce mai yasa bai duba hakan ba, a lokacin da ban samu cikin ba yake galabaitar da ni, wato kenan kowa nasa ya sani."

"A haka na yi wata shida a tare dashi a legos babu wanda bai san ina da ciki ba domin kuwa duk ya sanar da iyalinsa Hauwa har bidiyon call muke yi da ita musha hira Khalil ya yi wayo sosai yana koyar zama. Wasu lukutan ma idan na tambayeta yana Ina sai ta ce yana can wajansu Yusi idan ba nono ya buk'ata ba a can yake yini idan ba makaranta. Idan kuma da akwai idan za su tafi sai su mayar mata dashi. Da kanta ba tambayarta na yi ba take gaya mini yadda suke zaune lafiya domin a wasu lukutan ma takan shiga wajanta su hira itama kuma takan shigo. Na ji dadin hakan sosai da sosai, yanzu dai hankalinmu ya kwanta babu wani kishi na jahilici bayan haka kuma dukanninmu ba yara ba ne iyaye ne masu yi wa na kasa dasu nasiha."

Tare muka koma da shi abujan sai da ya yi sati biyu tukkuna suka juya shi da Hauwa da yaronta. Duk dauriyar da ya

"dinga nunawa sai da na gane hankalinsa gabad'aya yana kan abinda yake cikina kawai don ba yadda zai yi ne ya dawo da ni, ya d'auki Hauwa domin babu irin rarrashin da bai yi mini ba akan na zauna na haihu a can a gabansa a cewarsa sai hankalinsa ya fi kwanciya na ce masa a a, mun riga ai mun gama magana tuntuni babu dalilin da zai sanya yanzu a warware idan har za a yi mini adalci a lamarin wattani uku kacal za su yi a can shi da ita ta dawo a lokacin ma na haihu in sha Allahu rabbi ko da ban haihu ba to kad'an ya rage. Da haka ya ha'kura smma ba don ransa ya so ba."

Littafin nan na kudi ne kada ki karanta ba tare da kin biya ni hakkina ba

Bikin Hamusu ne ya tashi gadan-gadan domin kuwa yarinyar da ya jima yana nema burin mahafinta ya cika ta

kammala karatunta wannan dalilin ya sanya uban ya ce a d'auki wata biyu kacal a yi a gama komai

Ya kira ni yana gaya mini duk abinda yake faruwa. Na ce masa duk abinda yake bukata ya nemi Usaini domin shi yake kula mini da shagunana ya had'a lefe abinda babu ya fitar da kudi ya saya amma ya yi mata akwatina shida ya kuma sanya mata kaya masu quality. Godiya ya dinga yi mini sosai na ce babu buk'atar hakan domin kuwa duk abinda na yi masa babu fad'uwa hakkinsa ne tunda dukiyar tare muke nema. Gini kuwa dama ya kammala abinsa can unguwar maidile ya sayi fili ya gina irin na zamani tuntuni gidan ya kammalu har bidiyo ya yi ya turo mini. Na ce masa idan sun tare ya nemi solar mai girma ya saya sai a sanya masa a gidan tunda na lura unguwar kamar sabuwa ce bata gama cika ba babu wutar nepa.

***

Bikin ya matso sosai daga can suna ta shirye-shiryen a lokacin cikina watanshi bakwai da satika. Da kyar nake gudanar da abubuwan da suka zame mini dole saboda nauyin da cikin ya yi mini ya yi girma sosai ya kara sanya ni na d'unkule. Amma ina da burin so na ga na samu halartar bikin Hamusu dalili kuwa anan shine yaron ya wuce komai a wurina ni ce uwa kuma uwar dakinsa.

Daga tambayarsa akan ya barni na je tunda ai tafiyar jirgi ce ba mota ba kuma zan motsa jikina na shiga cikin jama'a.

Sai abin ya zama rigima saboda ya san ma ba bari na zai yi ba ya mayar da abin tashin hankali ya dinga sakin maganganu har sai da ya fusata ni dama haka yake so na ji haushi mu yi fad'a na kashe wayar raina a b'ace cikin zuciyata Ina fad'in idan ba zaka bari na je ba menene kuma na yin tijara kawai a ce ba zan je ba shikkenan sai magana ta mutu.

"Haka aka ci aka cinye bikin Hamusu babu ni uwar biki, sai hotona da ya turo mini

Please Login or Register in order to submit comment