You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Usaini ya shigo. Ganinsa ya sanya ya risina yana fad'in."" Barka da dare ya kuwa sanya hannu ya dago shi ganin yana ko'karin tsugunawa ya dinga mika masa hannu domin su yi musabaha yaron yana nok'ewa ya'ki kar'bar hannun cikin girmamawa sai sinne kai yake shi kuma yana yi masa dariya tare da tsokanarsa ango na amarya."""

"Ya rike hannunsa sosai Yana fad'in."" Allah Ya sanya alheri ka ji ko, ka kula na so na samu zama da kai kafin d'aurin auran Allah bai nufa ba, yanzu gashi mun had'u na yi maka murna kwarai domin ka yi dace da yarinyar arziki ka kula da amana da kuma hakkinta Ubangiji Allah Ya taya ka riko."""

"Ya dinga amsawa da Amin ya rabbi na gode ranka ya dad'e Allah ya saka muku da alheri Ubangiji Allah Ya biya bukatu."""

"Ya amsa da Amin Ya Allah babu buk'atar godiya Malam Usaini ai kai dan'uwana ne?"" Ya fad'a tare da kallona Yana cewa."" Ko ba haka ba ne?"""

"Na gyad'a kaina jikina a d'an sanyaye na ce."" Tabbas."""

"Usaini ya dube ni yana cewa."" Anti za mu tafi sai mun yi waya Allah Ya saka da alheri."""

"Na yun'kura na tashi a hankali itama ta tashi na rika hannunta ina fad'in."" Na gode da ziyara Hajara a gaida gida ki kuma kula da shawarwarin da na baki."""

"Ta ce."" In sha Allahu rabbi anti."""

"Suka juya wajan da yake tsaye yana murmushi shima suka yi masa sallama. Ya fara laluban aljihunsa ya fito da kudi yan dubu sabbi kar da su ba su dai da yawa ba su wuce dubu ashirin ba ya mi'kawa mata yana fad'in."" Ga shi a sayi jan baki da hoda."" Ta'ki kar'ba da sauri ta bi bayan mijinta sai ni na kar'bi kudin na bi bayansu da sauri."

Koda na dawo cikin falon baya nan ya hau saman don haka sai na bi shi a daddafe na kàrasa hawa na same ya cire rigar jikinsa yana zaune da singeliti da dogon wando agogon hannunsa yake ko'karin cirewa.

"Ya zuba mini ido har na kàrasa kusa da shi na zauna ya furta."" Hajiya Giwa manya."""

"'Dan juyar da kaina na yi a gajarce na furta."" Ya hanya amma ba ka gaya mini kana tafe ba."""

"Ya ce."" Hakane tafiyar ta same ni bagatatan ai kin san Alhaji sammani ko mutumin nan da ya cutar da ni shekarun baya."""

"Na ce."" Na dai ji labarinsa. Ya ce."" Mahaifiyarsa ce ta rasu kin san mutanan Dambatta ne kuma tare suke da Hajja kawaye ne tun lokacin k'uruciya ni da shi kuma abokai ne na unguwa an tashi tare har dai ya zama amintaccena a wancen lokacin kafin ha'inci da son zuciya ya shiga."""

"Na ce."" Allah sarki Ubangiji Allah Ya gafarta mata."""

"Ya amsa da ""Amin a takaice. D'akin ya d'auki shiru na d'an wani lokaci kafin ya dube ni ya ce."" Ya yara na ina fatan suna lafiya."" Ya fad'a idonsa kan cikina."

"Na ce."" Suna nan kalau sun ce a gaisheka."""

"Ya saki fuska kuwa yana cewa."" Ina amsawa amma ai gaisuwar iri-iri ce ko?"""

"Na yi shiru ban ce masa komai ba illa ido dana sanya masa ganin yadda ya kara haske fatar jikinsa ta yi kar har kumari ya yi a cikin wannan satikan da ban gan shi ba idan ba gizo idona yake yi mini ba, ban hangi wata kewa da damuwa a tare da shi ba ban sani ba ko wata ga'ba ya d'auka domin daina nuna mini so da rawar jiki. Jikina duk ya yi sanyi na kasa janye idona daga kansa iina Jin wani bala'in kishi a cikin raina sabon gida sabuwar soyayya tunda nake da shi ban ta'ba zama a gefansa bai ta'ba ni ba hannuwana suna shan mutsika idan ya rike haka zalika ya dinga"

sumbatar wuyana kenan yana shishshige mini yanzu da muka yi kusan sati biyu bamu ga juna ba babu wani abu na

"kewa da marari dana hanga a tattare da shi. Ya furta."" Bari watsa ruwa ki ba ni abinci ko?"""

"A takaice na ce."" Ban yi girki ba."" Na yi na yi na ha'kura kada na nuna jin haushin abinda yake yi na kasa jurewa. Ya ce."" Ba ki yi girki ba kamar Yaya da me ki ka ciyar da ba'kin da ki ka yi?"""

"Na ce."" Na dare ne ban yi ba dama daga gidan Gwaggo Hamusu ke kawo mini towo ba kasafai nake girkin dare ba."" Ya d'an yi jim yana kallona na wani lokaci kafin ya ce."" Ko ni zan yi miki girkin ne Hajiyata."""

"""Idan za ka yi zan ci."""

"Ya ce."" Zan yi kuwa yanzu jira ni na yi wanka."""

Ban ce masa uffan ba ya tashi ya nufi toilet na bi shi da kallon takaici da b'acin rai.

Daidai lokacin da ya fito kira ya shiga wayarsa ya zo ya zauna da babban towel a jikinsa ya d'auki wayar sai da ya kalle ni kafin ya d'aga a sake ya amsa sallama.

"Sai kuma ya yi shiru na wani lokaci kafin ya ce."" To Allah Ya sawwa'ke ki samu bacci sosai ciwon kan zai yi sau'ki maganar masu aikin nan kuma ki ajiyeta yanzu abinda za a yi shine zan yi magana da Hajja anan Dambatta ba za a rasa wadda za ta taimaka miki ba, da safe idan Allah ya kai mu zamu tattaunar maganar sosai, ki kula da kan ki, Allah Ya sawwa'ke."""

na kudi ne kada ki karanta ba tare da kin biya ni hakkina ba.

"Shiru na d'an wani lokaci yana sauraranta kafin ya sauke ajiyar zuciya ya furta ."" To babu damuwa sai na dawo."""

Daga haka sai ya kashe wayar ya ajiye saman dirowar gefan gado...

"Ya sake tashi dai ya je ya d'auko basiline ya zauna da shi a hannunsa yana fad'in."" Hauwa ce bata jin dadi tana mura da ciwon kai na dai fi tunanin ciki ta samu itama haka take zargi."" Ya fad'i maganar yana d'an kallona."

"A takaice na ce."" Allah Ya sawwa'ke."" Ya amsa daga haka sai d'akin ya d'auki shiru Ina kallonsa ya gama shafa basiline din ya shirya cikin jallabiya mai yankakken hannu ya dube ni yana fad'in."" Wane aikin zan yi miki a kicin Hajiya."""

"Da mamaki nake kallonsa ya gyad'a kansa yana cewa."" Menene a ciki manzon rahama ma ya taimakawa iyalinsa ni kuma wanene ko dakan sakwara ki ka ce na yi miki a wannan dare na shirya ke ce fa."""

"Murmushi na yi a hankali na girgiza kaina tare da cewa."" A a ka huta kawai to wai ma ka iya girkin ne?"""

"Ya furta."" K'warai kuwa mu je kicin din naki ki ga yadda ake yi wani abin ma zan koya miki wanda ba ki iya ba."" Na ce."" Lallai naga alama amma mu je din indomi kacal za ka dafa mini."""

"Ya ce."" Ai ni ba ni cin indomi Amina da gaske kuma yunwa nake ji na d'auka zan samu abinci."""

Jin ya fadi haka sai na gazgata gaskiyarsa babban abinda ya tsana zuwa gidan abinci ya jima yana fad'in tozarta kai ne ga maigidancin da yake sayan abinci a waje.

"Na tashi tsaye da kyar ina fad'in."" To me za ka ci sai na yi maka yanzu.'' Ya riko hannuna yana cewa."" A a mu je dai kicin din tare sai mu yi aikin ko?"""

Na gyad'a kaina ban sake cewa komai ba muka sauka kasan tare yana yi mini labarin yara da yadda suke hira kullum da masu aiki su Baba Tabawa. Na gama gane so yake yi mu yi maganar komawata can amma ya'ki yarda ya fito kai tsaye ya fad'a sai kame-kame yake yi.

"Muka tsaya akan dafa jallof din taliya na kunna masa gas din ya d'auki tunkuya zai tari ruwa ni kuma na d'ebo kayan miya domin marka'dawa ya ciko tukunyar taf da ruwa ya d'ora kan gas din. Ina kallonsa ya rufe da murfi yana fad'in."" Sai me za a yi?"""

"Na ce."" Da wannan kurmemen ruwan za a dafa rabin taliya? Ya ce."" Ya yi yawa ne?"""

"""Sosai kuwa kuma mai ake fara soyayya tukkuna a zuba kayan miya a soya tunda za mu yi amfani da busashen kifi idan mun gyara shi mun wanke sai mu zuba mu d'an soya tare da kayan miya nan sannan mu tsayar da ruwan sanwa."""

"Ya sauke tukunuwar tare da zubar da ruwan da ya mayar da ita kan gas din ya d'auki mai ya tsiya mai mugun yawa don wanda ya zuba zai yi gwangwani biyu ko fiye da haka."""

"Na ce."" Kenan da mai za mu tsayar da ruwan taliyar ko soyayyiya za mu yi ne Allah Ya taimake ka."" Ya ce."" Ana yin soyayyiya ne dama?"""

"Ina dariya na ce."" E, amma ba ita za mu yi yanzu ba kuma mangyad'ar da ka zuba ya yi yawa."

Gabagad'i kuwa ya kai hannunsa zai sauke tukunyar da ta d'auki zafi man yana suyuwa. Ya cire a zabure ya matsa har sai da murfin tukunyar ya fadi kasan k'afafunsa. Ya rikice sosai yana duba yatsunsa.

"Dariya kamar cikina zai yi ciwo na kashe gas din na jingina jikin wardrobe Ina kallonsa ina dariya sai zare ido yake yi. Ya nuna mini yatsun yana fad'in sun toye Amina kin ga yadda suka yi jaaa ashe haka abin yake dama?"""

"Na ce."" To kai wanene ya ce ka kama tukunya haka kawai, kuma ka ce ka iya girki ashe baka iya ba."""

"Ya ce."" Idan hakane bayin Allah nan suna aiki Amina wanene yasan iya adadin yadda suka 'kone garin sauke tukunya."""

"Na d'an 'bata rai cikin shagwaba na ce."" Su kadai kenan, ni ma ai ina yi maka girki."""

"Ya rikice kuwa ganin yanayin yadda na yi masa magana a sangarce da shagwaba ya matso ni yana cewa."" Har dake mana kuna kokari gaskiya Allah Ya saka da alheri."""

"Na amsa da Amin a takaice tare da d'an zame jikina ina cewa."" To zo ka ga yadda ake yi ko don gaba."

Ya kuwa taho ya tsaya a bayana yana murmushi na fara gudanar da aikin cikin nutsuwa yana yaba mini har da addu'a da tukwici sumba a wuya da kumatu a haka na yi masa jallof din taliya da dankali da kuma bushshen kifi ya ce a yi masa da manja ta yi kyau sosai tana k'amshi mai dad'i.

Kusan tare muka ci amma dai shine karfin cin kuma yadda ya zage ya ci da yawa ya tabbatar mini da cewa yunwa ce mai yawa a tare da shi.

Ban zaci zai iya d'auke kansa daga kaina ba a daran salin alin muka kwana bai nemi yin wata mu'amula da ni ba. Sai washe gari da rana gatse-gatse ya fara kame-kame da ya ga na'ki nuna na gane abinda yake nufi ya kamo ni wai na yi masa dabaru ta yadda zai gamsu yana tsoron ya kusance ni a haka na yi nauyi a cewarsa tausayina yake ji.

Ya fad'i hakane kawai don ya kare kansa amma shi kansa ya san babu wata dubara da take kwantar masa da buk'atarsa face sai wannan abin ya faru.

ban ma yi nisa wajan yin dabarun ba ya fice daga hayyacinsa maganar tausayi kuma sai ta kau ya fara ko'karin ganin ya samu hanyar zai mutunta kansa sai da na dinga ankarar da shi halin da nake ciki tukkuna a haka lamarin ya faru kamar wani sabon tuburarran mara hankali

*GARKUWAR MATA.*

*BINTA UMAR ABBALE*

*ZA MU KAMMALA A CIKIN SATIN SALLAH IN SHA ALLAHU*

"[6/4, 3:03 PM] Hauwa Galadima: *PAID BOOK VIP 1K ON TALGRAM WHAT'S APP GRUOP KUMA #700 VIA 0542382124 BINTA UMAR GTBANK*"

*V-VIP AREWAPEN*

*07084653262*

*158*

"Haka muka kasance cikin kula da juna mussaman daga b'angaransa wata sabuwar kulawa na dinga samu a wurinsa bini bini sai ya ce tausayina yake ji amma hakan ba ya hana shi da daddare ko kuma dai duk lokacin da lambarin ya bijiro masa ya kwanta da ni, a wannan gefen sai ya manta da tausayi girki kuwa bai sake cewa zai yi ba dalili ya ji babu sugar domin yatsunsa da ya kama tukunya sai da suka ruruce suka ja ruwa. Sai dai duk lokacin da zan shiga kicin zai bi bayana ina aiki yana damuna da runguma da ta'be-ta'be lamarin nasa dai kamar na sabon ango ko kuma wanda ya koyo wani sabon darasi ai soyayya ya iya babu karya kamar sabuwar balaga ba dattijo mai yawan shekaru ba."

Ranar sadakar uku ya ce na shirya mu je ya kai ni gaisuwa. Na shirya kamar yadda ya buk'ata din muka nufi dambatta a mota Ade direbansa ya ja mu.

"A gidan rasuwar na samu Hajja tare da jama'a tunda shi daga waje ya tsaya sai daga baya tukkuna ya shigo gidan. Hajja ta dinga nuna ni ga jama'arta wasu sun san fuskata wasu kuma ba su san ni ba dama fadi take itace uwargidan nasa ai Amina sunanta, itace wadda aka dauro auransu a saudiya. Sai na zama abin kallo na dinga jin nauyi da kunya domin na kasa tantance kallon da yawancin jama'ar wajen ke yi mini."

Da la'asar muka fito daga gidan a kafa muka taka zuwa gidan Hajjan tunda babu nisa.

Ta sanya Iyami mai aikinta yi mini towon shinkafa miyar zogale domin dai ko kad'an na kasa cin abincin da aka ajiye mini a gidan rasuwar dafadukan shinkafa ce amma sun yi amfani da wani irin curry ya yi rabad'au dashi 'kamshin babu dad'i.

Wajan biyar iyami ta gama aiki ta kawo mini sannan Hajja ta ce ta zuba mini wani a fulas sai mu tafi dashi na huta girki.

"Na kuwa ji dadin hakan sosai. Sai da na yi sallar magriba tukkuna ta fito daga cikin dakinta da turaman atamfofi guda uku manya ta miko mini tana fad'in.'' Kada na manta kar'bi wannan Amina bari na nemo leda."""

"Ya juya da sauri ta koma d'akin ta bar ni ina juya atamfofin tsala-tsala masu tsada. Ta dawo da leda viva mai zurfi tana fad'in wannan ai zata d'auke kayan ko?"""

"Na kar'ba Ina fad'in."" Eh za ta isa."""

"Ta zauna saman kujera tana cewa."" A kar'ba da hakuri ban samu zuwa biki ba amma wannan a bawa amarya Hajara idan na sanya rana Yusi zai kai ni gidan na yini in sha Allahu."""

"Na sa dariya ina fad'in."" Kai Hajja an yi abu ya wuce fa don Allah da kin bar atamfofinki ki dinka abinki."""

"Ta girgiza kanta tana murmushi ta ce."" A a dama na yi niyya Amina sai ki sanya Ayuba direbanki ya kai mata ko kuma angonta ya zo ya kar'ba a ce babu yawa kuma ina yi musu fatan alheri."""

"Na ce."" To shikkenan Hajja Allah Ya saka da alheri ya kara girma Ubangiji Allah Ya sa a fi haka, mun gode sosai."" Ta amsa da kulawa tana kallona kafin ta ce."" Ya gaya miki Kamalu zai tafi karatu can Madina ko?"""

"Eh ya gaya mini."" Na fadi haka duk da har yanzu bai ce mini komai ba."

"Sai ta gyada kanta tana cewa."" Ki kara yi wa yaron nan addu'a akwai alamun haske a cikin al'amarinsa in sha Allahu za a amfana dashi."""

"Na furta."" In sha Allahu rabbi Hajja na gode Allah Ya saka da alheri."""

"Ta yi murmushi ba ta ce komai a daidai lokacin ne kuma ya shigo yana waya ya tsaya tsakiyar falon duk muna kallonsa har sai da ya kammala tukkuna. Ya dube ta yana fad'in."" Hauwa ce ta kira waya wai Sultan baya jin dad'i."" Hajja ta ce."" Ashsha me yake damunsa?''"

"Ya gyada kansa da Yar damuwa ya ce."" Ciwon ciki abinda dai tace kenan ya kwana biyu bai yi bayan gida ba yana ta kuka uwar rainon nasa ce ta je tana gaya mata halin da yaron yake ciki amma ya sha magani a cewarta."""

"Hajja ta ce."" Wata'kila wani abin ya ci ya dam'ke masa ciki sai an kula da abinda za a dinga ba shi ya ci mussaman abinda ya danganci madara da fulawa."""

"Ya furta."" Sauyi ne kawai tunda yaron ya fara cin abinci bai ta'ba irin wannan ba ko ba haka ba ne?"""

"Ya fad'a yana kallona na ce."" Sosai kuwa kuma Baba Tabawa na kula kwarai da gaske da abincin da zai ci, tana kokari a kansa gaskiya."

"Ta ce."" To shikkenan Allah Ya sawwa'ke ai tunda ya sha magani da sauki cikin zai saki zuwa dare sai ka kira waya ka tambayi jikin nasa."""

"Ya ce."" Hakan za a yi in sha Allahu, ni ma ai ina tunanin jibi zan koma."""

"Ta gyad'a kanta tana cewa to babu lefi ai tunda an yi uku sai kowa ya koma bakin aikinsa."" Ya dube ni cikin kulawa yana fad'in."" Tashi mu tafi."""

"Na tashi da bismillah tana fad'in."" Sannu ai gwara ki zauna nan din Amina ki haihu ni kaina hankali zai fi kwanciya."" Da sauri ya ce."" Ai ba sabuwar haihuwa ba ce Hajja."""

"Ta ce."" In ji wa? au! haihuwa dama akwai sabuwa da tsohuwa ina ce idan ta yi nisa ne ma ake jin jiki, ko makaho ne ya dubi yarinyar nan ya san tana cikin ibada."""

Ya yi shiru bai ce komai ba amma gabad'aya jikinsa ya yi sanyi a haka muka yi sallama ta rako ni har farfajiyar gidan lokacin shi tuni ya shige mota.

Ade ya bude mini kusa da shi na zauna da ledar atamfofin Hajara da madaidaicin fulas din towona. Ina zama a gefansa ya kar'bi ledar ya ajiye kasan k'afafunsa saboda kayan sun yi mini yawa a hannu

Ade ya shiga mazauninsa muka d'auki hanya.

Har muka isa gida bai yi magana ba. Ya rage walwala da nishadi ya yi shiru abinsa tabbacin akwai abinda yake damunsa.

Na daure na fara tambayarsa ko ba ya jin dadi ne ya ce dani 'kalau yake gajiya ce kawai.

Ko da na yi masa tayin towon ma kafin mu kwanta ya ce a a shayi kadai zai sha shima cikinsa ya b'aci.

Na kyale shi kawai na zauna na ci towona na koshi na sauka da kayan na dawo na same shi yana waya da Hauwa jikin yaron yake tambayarta ga yanayin fuskarsa amsar da ta ba shi ba mai dadi ba ce.

"Raina ya ba ci sosai wai shin ya ma aka yi Hauwa ta san yaron ba shi da lafiya ne abinda ba tare suke ba, ba fa da gaske ba ne karya take yi ta mayar da shi shashasha tana daga masa hankali saboda ta gane lagonsa akan yara yake yau tace wannan gobe tace wancen kwanaki ta bugo waya tace bata da lafiya yau kuma ta kirkiri ciwo ta d'orawa yaro wane irin jahilci ne wannan. Ta gama gane damuwarsa akan yara shiyasa take amfani da wannan dama. Gashi muna cikin farinciki da soyayya da kulawa lallai sai ta rusa hakan ta kira shi ya dawo wajenta shine hankalina zai kwanta."

"Na bude baki ina fad'in."" Idan ba ka farga da wuri ba wallahi Hauwa daf take da ta mayar da kai sakarai ko ma nace ta mayar da kai tuntuni shashasha take kallonka."""

"Ya dube ni da b'acin rai yana cewa."" Wace irin magana ce wannan Amina ana 'karyar ciwo ne?"""

"Na ce."" Tunda ba ta da hankali ita don ta yi hakan ai ba abin mamaki ba ne, watarana za ta iya kiran ka ta ce wane ya mutu tunda jahila ce."""

"Ya yi sakato yana kallona ni ma ina kallonsa na ce."" So take yi ka koma gare ta domin ku cigaba da cin amarci a sabon gida, na gaya maka Hauwa ba za ta ta'ba canzawa ba kuma ba zata zauna da ni tsakani da Allah ba sai ta yi mini bita da 'kulli a rayuwata me na tsare mata."""

"Ya yi shiru kawai yana kallona na cigaba da cewa.""Ka yarda ko kada ka yarda Hauwa 'karya take yi Sultan lafiyarsa"

"lau."""

"Ya ce."" Na ji, ke yanzu abinda ki ka yanke a ganinki daidai ne na gaji da wannan abin da ki ke yi mini ni nake auranki ko ke ki ke aurana?"""

"Da mamaki a tare da ni na ce."" Me kuma na yi maka yanzu, gaskiya na gaya maka na ce ka farka ka kuma yi aiki da tunani akan abinda matarka take yi."""

"Ya ce."" Ni ba wannan ne damuwata ba so ki ke na kwanta ki taka ni shine karshen so da kulawa da tarairaya me zan yi miki kuma abinda ya rage kenan."""

"Sai kawai ya kwanta ruf da ciki ya mike sosai yana fad'in."" Ta shi ki hau ki bi ta kaina kawai Amina, hakan zai kara tabbatar miki da cewa kin gama da ni, sai abinda ki ka gindaya mini."""

"Dariya ta kama ni amma na danne ban yi ba sai na kasa gane dalilin wannan rikicin da ya bijiro da shi a yanzu ban sani ba ko maganar da mahaifiyarsa ta yi a d'azu ce ta 'kara fusata shi shine ya sar'kafe maganar ya had'ota da wata a ganinsa kenan na mallake shi juya shi nake yi."""

"Na sassauta sosai tare da cewa."" Ni dai don Allah ka tashi kada ka sanya mala'iku su tsine mini me ya yi zafi zaka kwanta kace sai na taka ka."""

"Ya ce."" Kin san Allah ba zan tashi ba Amina sai kin bi ta kaina kin wuce hakan zai kara tabbatar miki da cewa kin gama da ni, haba don Allah na gaji wallahi rayuwarki kawai ki ka sani ni ko oho, ki tashi kawai ki yi yadda na umarce ki."""

"Na yi kasa'ke ina kallonsa har yanzu yana kwance ruf da ciki. Na ce."" To ai kamata ya yi ka gaya mini abinda na yi maka sai na baka ha'kuri ba wai ka kwanta ka ce na taka ba, akan wane dalili."""

"Yana daga kwancen ya ce."" Sai na gaya miki ga abinda ki ka yi ke din yarinya ce, ai duk abubuwan da ki ka jima kina aikata mini kin sani, tunda ba k'ank'anuwa ba ce."""

"Na yi shiru kawai ina kallonsa saboda bakina ya mutu ma gabad'aya ya juyo da fuskarsa yana kallona har yanzu babu wasa a tare da shi ya ce."" Ba za ki tashi ki taka ni ba."""

"Na girgiza kaina a tsanake na ce.""Babu halin hakan me yasa zan taka ka Allah kada ya nuna mini wannan rana."""

Na kudi ne wannan littafin kada ki karanta ba tare dà kin biya ni hakkina ba.

Ya gyad'a kansa tare da tashi zaune yana fitar da numfashi sama-sama ya jima a haka kafin ya tashi ya shiga bandaki

na bi shi da kallo ina girgiza kaina ya fito d'aure da alwala ya hau dadduma.

Haka muka kwana ko hannuna bai ri'ke ba. Da safe na gaishe ya amsa a dakile ya koma ya kwanta bacci ya yi sosai sai wajan sha biyu ya sakko kasa.

Lokacin na gama had'a kayan sanyawata dana ware domin aikawa da Fati na fito da akwatin kayan domin kiran Ayuba na same shi zaune shi kad'ai ya kunna tibi abinda ba dabi'arsa ba.

"Ya dube ni muka kalli juna kafin ya ce."" Wannan akwatin ta mecece Amina?"" Na ce."" Ayuba zan aika gidan 'kanwata Fati."""

Ya yi shiru bai ce komai ba yana kallona na ajiye akwatin na bud'e kofa na fita domin kiransa.

Sai da na shigo tukkuna ya biyo bayana na ce masa ya d'auki akwatin ya kai mata sannan na ya gaya mata zan kira ta a waya zuwa dare.

Bayan fitarsa na je na zauna kusa da ni bai kalle ni ba da romot a hannunsa yana duba tashar da zai k'alla.

Na matsa kusa da shi a hankali na ri'ke hannunsa ya dube ni babu yabo babu fallasa ya mayar da hankalinsa kan tibin.

"Bakina nasa a kunnensa cikin k'aramin

Please Login or Register in order to submit comment