You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

aka gama wannan kacaniyar ba ta ce ga abinda aka yi mata ba."

"Shi kuma daga nasa bangaran babu yabo babu fallasa ya ce muna damunsa da maganar Nabila zai fita daga harkar kowacce domin da akwai abubuwan da suke gabansa ba mu isa mu raba masa hankali ba. Da gasken ne sabgogi sun yi masa yawa domin tunda suka dawo daga umara shi da Khalil bai fiye zama a gida ba. Ya je Kano kusan sau uku a kasa da sati hud'u. Ba ma shi da lokaci sosai idan ya dawo da daddare ya ci abinci ya dinga lissafi kenan yaran ba kasafai yake zama da su sosai ba, na yi wankan tsarki tuntuni amma bai lura ba saboda abubuwan da suka sha kansa a tunaninsa har yanzu ina cikin jinin 'biki bai ta'ba nema na ba sai dai 'yan ta'be-ta'be kafin a kwanta."

Order na yi daga kano wurin GARKUWAR MATA 08089965176 package irin na masu jego na ce ta had'a mini na aminta kuma na gazgata sahihancin maganinta shiyasa ba ni shakka da shakku a ko'ina zan yi mata TALLAH da k'umaji da karsashi. Ta kuwa yi mini delivery har garin Abuja na sanya Masa'udu ya je ya kar'bo komai cikin girma da arziki nannad'e da salatif. Na durfafi gyara jikina domin bahaushe ya ce wai idan kana da kyau ka kara da wanka.

Yau da yake girkina ne baya gari ya tafi kano Amma ya ce lallai a gida zai kwana. Na yi tatul ta ko'ina kuma buk'ata na ke ji. Sosai yau kwana hamsin da shida da haihuwa na dawo Amina sosai

Ado da kwalliya na yi mai kayatarwa don an sake yi mini wani sabon lallen ma baya wanda aka yi mini na bikin suna ba. Sai yanzu na sake gazgata alfanun raba gida hankalina a kwance yake sosai a yanzu Hauwa na can gidanta ni ma ina nawa duk ta ta zame mini jiki amma wallahi watarana har mancewa nake yi da ita mussaman yanzu da muka sake yaiwata a gidan ko ta ina babu kad'aici akwai kuma fahimta mai kyau da masu aikina muna girmama juna

Na kudi ne littafin nan kada ki karanta ba tare da kin biya ni hakkina ba.

mutuntawa tabbas da maza da yawa za su gane jin dadin da kwanciyar hankalin da yake tattare da rabawa iyali

mazauni da dayawa ba a sa samu rikici da rabuwar kai ba. Khalil ne yakan d'an je gidan jefi-jefi wataran kuma idan babu makaranta ya ja 'yan uwan su je su d'an zauna mata babu kuma wata matsala da ta ta'ba faruwa dalilin zuwansu nasu domin yadda na fahimta so take itama ta ja su a jiki ta samu irin soyayyar da suke mini har sultan yanzu ya daina tsoronta da shi suke zuwa idan za su tafi hakan yana yi mini dadi sosai yaro ne Khalil amma mara mantuwa shiyasa ake cewa idan za ka yi sharri ko wani abu na rashin kyautawa kada ka yi a gaban yaro dalili baya mance abu. Yanzu da ya fara girma ya gane cewa mamansa itace matsalar gidansu gashi a aikace cikin hikima yana ta ko'karin ganin ta gyara ta dawo mutuniyar kirki tunda ba zai mance abubuwan da suka dinga faruwa ba.

A bakin yaran nake jin Ladidi suna yawan kiran sunanta sai da na tambayi yaron wacece ita yake gaya mini mai aiki ce da ta zo daga bauchi sunanta Ladidi take wasa da su tare da yi musu tatsuniya ashe kenan an kawo mata mai aiki wata'kila ma ta jima domin lokacin da ta jibgi danyen naman nan na yi ta mamakin yadda za ta yi dashi Ashe tana da mai yi mata hidima ko tare suka zo da inna Uwani Allah ne ya sani.

"Sai dare ya dawo bayan ya yi wanka ya ci abinci ya bukaci ganin yara har saman suka same shi ya kuwa kasance da su na tsayin mintina talatin ana ta gaisuwa masu hawa jikinsa na yi masu tsokanarsa na yi Usaina ce me jan gemunsa tana fad'in ya yi fari furfurar ce bata iya fadi ba har tana nuna masa sabon kitson hannu da Taburni ta yi musu tana cewa."" Ka ga nawa ba'ki naka kuwa fari baba ka goge ya dawo irin nawa."" Tana ta jan gemun yana dariya kallonsu kawai nake yi har suka gama ya ce su sauka k'asa zai huta da suka fita d'akin ya rage mu biyu ya ce."" Na ga lokacin da zan huta Amina, wallahi jikina ciwo yake mini ga shekaru ga wahalhalun rayuwa."""

"A takaice na ce."" Sai sai shekarun amma kai yanzu har wata wahala kake Sha?"""

"Ya d'an harareni yana fad'in."" A a ba na sha a kwance nake samun kudin tunda mafia nake yi."" Dariya maganarsa ta ba ni na yi a takaice ban ce komai ba sai kallonsa da nake yi masa"

"Ya yi kwafa yana cewa."" Yarinyar nan Nabila nema take yi ta matsanta mini fa wai zuwa ta yi can wajan Hajiya Ayya"

"mahaifiyar Alhaji Ahmadu akan na aureta."" Ban ce komai ba sai Ido mu je dai zuwa."

"Jin ban yi magana ba ya sanya ya ja goron numfashi kafin ya furta."" Ni yanzu karfina duk ya 'kare kun karar mini da shi bana ji jin zan iya ajiye mata uku a yanzu kuma kowacce tana jira na kwanta da ita ni na fara gajiya wallahi."""

"Duk yadda na kai ga dannewa sai dariya ta subce mini na ce."" Haba kaine fa na ji kana fad'in babu abinda ya fi wannan sabga dadi a duniya kuma sai kace ka gaji."""

"Ya furta."" Da gaske na gaji Amina duk da sunna ce mai kyau ai duk fafutukar da na dinga yi a baya wallahi ina son haihuwa ne, Ubangiji Allah Ya ba ni sai godiya yanzu ma ban ce ba ni so ba ina neman kari ina nufin abinda aka yi a baya yanzu ba za a yi ba."""

"Na girgiza kaina ina kallonsa kafin na ce."" To sai ka ce mata me?"" ""Na ce sai na yi shawara tukkuna."""

Na yi 'kasa da kaina ban sake cewa masa komai ba saboda takaici wace shawara kuma ya fito fili ya gaya musu gaskiya daga ita Nabilan har wadda ta yi kamun k'afa da ita tunda babu buk'atar aurenta a ransa babu amfanin yi mata yawo da hankali.

A daran dai wani lamari ne ya kasance a tsakani na dashi mai armashi da wahalar mantawa. Soyayya bata tsufa muddin za mu had'u muka zama tamkar sabbin ma'aurata ah to me za a fasa tunda da rai da lafiyar da kuma sauran kuruciyar shima duk fadi yake yi ai yana shiga hannu ya fara makyarkyata tamkar wani d'an magyaru! GARKUWAR MATA ta gama gigita lissafin attajiri sai ya dawo ustaz a daran yabo da kalaman soyayya a cikin harshen labarci ya dinga zuba a yayin da jikinsa yake tsananin neman abinda duniyar ta ginu a kai. Allah Ya sa mu dace Amin.

***

Kwana biyu haka muka dinga gwangwajewa Muna shan soyayya a kuma wannan lokacin ne dana samu dama na gaya masa bukatata kan kyautar da ya yi mini da farko ya ce a a bai ba ni don na sayar ba yanzu haka ana ko'karin sabunta takardun wajan da sunana don haka babu niyyar sayar da shi a tsarinsa.

Na yi ta ko'karin ganin na ganar da shi nufina ya ki ya ce idan ba ni so kawai na gaya masa ba zai yi mini kyauta ba kuma na canza masa tsari ba ana cigaba da gudanar da abinda ake yi a kamfanin duk abinda ya kama na shiga da fita mallakina ne.

Ganin bai amince ba sai na kyale shi. Da yaje ya yi kwana biyu a gidan Hauwa ya dawo na ce masa ina so ya ba ni rancen kudi tunda dama wanda na samu na wurin larabawan nan suna hannunsa bai sa mini cikin acct dina ba. Babu wata fargaba ya tambaye ni abinda zan yi da kudi kuma nawa nake buk'ata. Na ce miliyan hamsin.

"Ya jima yana kallona kafin ya furta."" Me za ki yi da su?"" Da mamaki sosai a tare da shi ya yi mini tambayar."""

"Na ce."" Kasuwancina zan kawo nan garin zan kama shaguna cikin wuse market na zuba kaya tunda yanzu raba 'kafa ake yi."""

"Ya ce."" Yaushe za ki biya ni?"""

"Na ce."" Mu yi a rubuce shekara uku ko hud'u, in sha Allahu rabbi zan biya ka kudinka."""

"Ya gyad'a kansa yana kallona kafin ya furta."" Ki ce kawai na baki kudi Hajiya kai tsaye amma ai kin san babu rance a tsakaninmu ko?"""

"Na gyad'a kaina ina fad'in."" Da akwai mana idan da yarda da amana ko kana ganin ba zan iya biyanka ba?"""

"Girgiza kansa ya yi kafin ya ce."" Za ki iya tunda me nema ce ke amma ki bari zan yi shawara akan hakan. Zan kuma sanya miki kudinki da suke hannuna."""

"Na 'bata rai tare da cewa."" Tunda sai ka yi shawara za ka ba ni me yasa ba za ka amince da shawarata ta farko ba abin nan ni ka ce ka bawa to me yasa ba za ka bari na yi iko da shi ba ashe kyautar ba har zuciyarka ka yi mini ba tunda ka hana ni na yi iko da shi."""

"Ya furta.'' Ai ni ban baki don ki sayar ba, kin ga kuwa babu wani dalili da zai sanya ki ce mini na ba ki umarnin sayarwa, amma dai yanzu tunda na ji hanzarinki ki bari na yi tunani tukkun ko an gaya mini haka ake tafiya kai tsaye komai yana buk'atar nazari da tunani."""

"Shiru na yi ban sake yi masa wata magana ba, muka cigaba da tafiya a haka shima bai sake tashin maganar ba ya kuma sanya mini kudina da suke hannunsa kamar yadda ya fad'a."

Ranar wata lahadi da sassafe na hau saman na same shi da yake a d'akina nake kwana wataran ya biyo ni mu kwana tare ranar da yake da ayyuka kuma ko ya biyo ni yana fita idan muka kammala uzurinmu.

"Na same shi suna bidiyo call da Kamalu shigowata d'akin na ji yana fad'in."" To ga tanan ma ta shigo Amina zo ga Ustaz sunan da yake kiransa da shi kenan tun lokacin da ya dawo daga makarantar horon da muka kai shi ni da Hamusu."


Downloaded From https://tknovels.com.ng


Please Login or Register in order to submit comment