You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

akan telegram. Normal What'sapp group kuma #700 hanyar da za a biya kudin ita ce wannan...0542382124...Binta Umar gtbank ko kuma 7084653262. Binta Umar"

Opey bank. 'Yan nijar dala dari katin airtel za ku tura mini bayan kun kankare hoton. A tura da sheda ta wannan lambobin iya What'sapp kawai.*

*07084653262*

*08089965176*

*V-VIP AREWA PEN *

*TALLAH!*

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/BieW3hHvRNIJLFNloG2CDl

Momyn Hajara GHT supplements

Muna da kayan gyara jiki na maza da mata munada magungunan matsalolin ma'aurata munada magungunan

kowacce irin matsala in sha Allah

Hadin Amare

Hadin Ango Hadin jego Hadin uwar gida

Hadin babbar mace

Hadin maida tsohuwa yarinya

Muna da Maganin sanyi kowanne iri

Muna da maganin ulcer Muna da maganin Asthma

Muna da maganin ciwon zuciya Muna da maganin ciwon Hanta

Muna da Maganin hawan jini

Muna da Maganin ciwon Ido Muna da Maganin rashin haihuwa Muna da Maganin skeler

Muna da Maganin kowacce irin cuta da yardar Allah

Sannan kowa zai iyayin register da campanynmu maitarin albarka kasari kaya kasiyar kaci riba sannan Kuma

campany yadunga biyanka albashi Duk watan da kayi aiki Saida kaya shine aikin da zakayi campany ya biya 07012621175

Register 8000 ne kachal

*87*

"Muryar Masa'udu ta katse tunanin da nake yi. na sauke ajiyar zuciya a hankali na ce."" Kai mu jabi park."" Cike da bin umarni ya ce."" An gama."

"Motar ta yi shiru ni da yaran duka muna cike da zullumi mussaman Yusi da nake hankalce dashi yana goge hawaye a fakaice. Ban tsawatar masa ba domin kuwa ban san mai yake ji a zuciyarsa ba, amma zahiri wannan shine iya gatan da nake ganin zan yi musu a duniya. Ba zai yiwu a ce koyaushe rayuwarsu ta kasance cikin kyara da hantara ba. Sun fara kaiwa munzali na girma a wannan lokacin ya kamata ace mun had'u ni dasu mun gina gobe dalili watarana za su yi aure su tara iyali suma. Sannan zuciyata ba za ta iya cigaba da jurar ganinsu cikin kaskanci ba, arziki Allah ne yake bayarwa su fita su nema kowa ya tsaya da k'afafunsa."

Cikin ikon Allah motar dana sanya su ta yi lodi saura bai fi mutum hud'u ba. Cike da dauriya da ko'karin kara musu kwarin gwiwa muka yi sallama na ce lallai idan sun sauka Kamalu ya kira ni tunda da waya a hannunsu.

"Ban gushe daga wurin ba har sai da na tabbatar da tashin motarsu sannan na sauke ajiyar zuciya na gyara zaman nikab din da yake fuskata tunda ban fito ba sai da na sunkufe jikina ta ko'ina dalili ba na so a gane wata ala'ka da za a yi yamadidi da ni, kuma safiya ce tashar babu wadatar mutane da yawa sosai."

Kai tsaye na nufi wajan da Masa'udu ya ajiye mota.

"Yana ganina ya taso daga inda yake ya bud'e mini na shiga na zauna sai a lokacin na ji wasu gagariman hawaye masu radad'i sun k'wace mini. Wato ni kuma haka kaddarata take, ina ro'kon Allah Ya ba ni ikon cinyeta ya kuma saukakawa yaran nan rayuwa ya basu hakurin maraici."

"Ina komawa gidan na samu Hauwa da Momi zaune a falo, amma babu cikakkiyar sakewa a tsakaninsu Hauwa ta yi zaman gadara da ki ce kule na ce miki cass domin kuwa fuskarta tamkar kunun tsamiyar da ya kwana a rufe. Kusan a tare suka amsa sallamata."

Kwarai da gaske na yi kokarin danne abinda nake ji a zuciyata game da al'amuran dake faruwa. Na nemi wuri na zauna babu yabo babu fallasa nake kallonta ina sake nazari akan al'amuranta. Ta tsuke sosai ta yi fayau abinka da mara jiki da gasken ne bata da lafiyar domin alamu sun nuna babu wani kuzari da karsashi a tare da ita.

Ita ta fara gaishe ni a tsanake na amsa ido na a kanta ina sauraran abinda take tafe dashi ta gyara zamanta kad'an tana kallona sai ta sauke ajiyar zuciya a hankali

"Ta ce."" Amina na shigo nan ne saboda ke domin mu tattauna abubuwan dake faruwa da yaranmu, Allah Ya ga zuciyata ban shigo cikin rayuwarku da wata niyya ta cutarwa ba, kuma ban had'a kai da Salim domin ya ci mutuncin Kamalu ba, asali ma abinda yake aikatawa ba ni da masaniya sai bayan ya aikata din nake samun labarin."" Ta yi shiru tana sauke ajiyar zuciya a karo na biyu kafin ta cigaba da cewa."""

"Yana da kyau a matsayinki na uwa mai hankali ki yi nazari mai kyau Amina idan hankali ya 'bata fa nutsuwa da dattako ake sanyawa domin nemansa bai kamata ace kin d'auki munanan shawarwarin da ba za su zama silar gyar Hauwa ta katse ta cikin fusata."" tana fad'in ""Ai dama ban ce kin shigo gidan nan domin ni ba Maryam, ko"

"kuma kin ji na ce miki kin shigo ne da mummunar niyya. Kin tsargu ashe ai shi mara gaskiya dama kullum cikin zullumi Hajajju ki dube ni da kyau ki ga ni, a waye nake k'warai babu wata kinaya da za ki yi mini kafin ki san Amina da yaranta ni na santa na kuma zauna da ita. Idan har mijinki ya gaya miki cewa da hannuna wurin matakin da Kamalu ya d'auka bai yi miki k'arya ba, ga ni a zaune ai ina jiran hukunci tunda ku kun iya take gaskiya da gangan."" Cikin rashin sukuni na ce."" Hauwa menene don Allah, duk cikinmu nan babu yaro karami tunda har ta shigo domin mu tattauna magana dan samun daidaito bai kamata wasu maganganu mara dad'i su biyo baya ba kuma."""

Ta ja dogon tsaki tana fadin

"""Kina jin irin jirwayen da take yi mini ai, ai mu 'yan iska ne marasa 'yancin kai tunda mijinta haka ya nuna mata ba"

"mu da mutunci da kima sannan ba mu da sirri komai muka yi a tambad'e ita nata sirri koyaushe cikin danda'be shi yake baya so kowa ya ji. Bazan jure d'aukar cin kashi daga 'bangaranta ba wallahi tallahi."""

"A nutse ta ce."" Ba halina ba ne raina mutum Hauwa, kuma kamar yadda ki ke hasashe hakane maigidan ya gaya mini komai ke ce ki ke ko'karin ganin lallai sai an yi 'batacciya domin kuwa abinda muke ta bunnewa dalilin gudun rikici mai muni ke ki ka gayawa mahafiyar yaron nan, kuma ki ka cire nauyi da kunya ki ka dubi tsabar idon yaron nan Kamalu ki ka gaya masa to kin fad'a kin ji dadi kuma in sha Allahu abinda ki ke fata ba zai faru ba da izinin Allah."""

"Hauwa ta mike tsaye tana huci ta ce."" Kin yarda yaronki mahassadi ne, kuma sharri ya yi wa Kamalu ko ba ki yarda"

"ba, ke yanzu don girman Allah ba ki ji kunya da nauyi ba"

"ai ita karya fure take bata 'ya'ya wallahi ni dai Hauwa Maryam ba ki isa ki siye ni da kudi da abin duniya ba. Wannan gingimeman sharri da d'anki ya alak'anta marayan Allah dashi saboda rashin adalci da son zuciyarku sai ku ja baki ku yi shiru babu wani mataki da ku ka d'auka. Sannan kuce ba za a yi magana ba, to ni na sayi rikicin don girman Allah ki d'auki mataki a kaina. Kenan wannan ya nuna kun sake bawa yaron lasisin ci gaba da aikata abinda yake yi dalili kun nuna masa akan daidai yake, ke da mijinki kun daure masa gindi saboda kun tara abin duniya kuna ganin kun fi karfin hukuma ko? to ku d'aukaka k'ara don Allah allura ce zata tono garma menene ba mu sa ni ba Maryam na fad'a din idan ta yi miki zafi ki kaini 'kara ko kisa tsinken tsire ki tsire ni!"""

Na tashi tsaye da sauri

na tare ta tare da mayar da ita kan kujera na zaunar sai huci take yi tabbacin a fusace take kuma a shirye take da duk abinda zai faru.

"Hayaniya ta fito da Baba Tabawa daga kicin tana fad'in."" Mai yake faruwa ne don Allah ku yi aiki da hankali da girman shekarunku kada hayaniyarku ta d'auki hankalin yaranku k'ananu har su fahimci abinda yake faruwa, kun san dai yaro da ri'ke abu a zuciyarsa..."

"Littafin gudun aure na kudi ne, don Allah kada ki karanta ba tare da kin biya ni hakkina ba."

Cikin numfasawa Hauwa ta koma ta zauna tana huci! ita kuma Momi ta yi 'kasa da kanta k'walla cike a kwarmin

"idonta. Alamu sun nuna cewa ba ta iya fad'a na cacar baki ba koda fad'ansu ya yi tsayi da Hauwa ita za ta kaita kasa. Har cikin zuciyata ban ji dad'in abinda ta yi mata ba duk da cewa duka su biyun ban san menene a cikin zuciyoyinsu ba don haka ba daidai ba ne abinda ta yi tsinka na k'asa da kai ma tozarci ne ballantana wanda yake sama da kai ashekaru. Ni da ita duka haihuwa ce ta janyo mana domin kuwa da yara ba su had'a ba ina ganin babu wani dalili da zai sanya na yi sa'insa da ita akan namijin da ba shi da wani tabbas. Tun farko itama Hauwan da ta d'auki shawarata abinda yake yi akan matarsa ba zai dameta ba tunda ta san tafi amfanarshi fiye da ita ko a wurin tarayya ta aure ne. Kuma ita ce uwar mai sunan mahaifinsa Ibrahim Khalil, uwa uba kuma 'yar uwarsa ta jini. Hauwa ba ta fi ni kishi ba wallahi kawai na fita ha'kuri da juriya ne dalilin gwagwarmayar da na yi a rayuwa ita ba ta yi irinta ba."

BabaTabawa ta koma kicin jikinta duk a sanyaye bayan cikin hikima irin ta manya ta yi mana nasiha aka ci sa'a kuma Hauwa bata k'alubalanceta ba.

Falon ya yi shiru bayan gushewar baba Tabawa daga wurin babu wanda ya sake magana. Ita Momi din tunda ta sunkuyar da kanta kasa ba ta sake d'agowa ba tabbatacin ta ji ciwon irin tijarar da Hauwa ta yi mata.

"'Dagowar da za ta yi kuwa sai ya yi daidai da kwaranyowar ruwan hawaye a dakalin fuskarta. Ba ta yi yun'kurin gogewa ba sai ta kalleni ta fara magana cikin karaya da zullumi."" Amina ni na haifi Salim amma wallahi ba na goyon bayansa akan irin abubuwan da yake aikatawa na rashin kyautatawa. sannan na sake jadadda miki babu yawuna ka haifi d'a ne kawai amma ba ka haifi halinsa b Hauwa ta yi saurin cewa."" Kuka ai yanzu ki ka soma in sha Allahu"

rabbi Hajiya kina

"fama da gagararan d'anki da ki ka kasa sarrafawa ina ke ina iya yi wa yaran wasu tarbiya wallahi ki ji tsoron Allah da Annabi, ga shi dai da bakin ki kin fad'a cewa Salim baya jin maganar ki, sannan nan Nusaiba ta shigo har gida ta yi mana rashin kunya, ina tarbiya anan kina so ki lalata mana yaranmu ne, ko kuma kina so su yi koyi da abinda yaranki suke yi duk a had'u a yi mutuwar kasko gabad'aya ko ba haka ba ne."""

Shiru ta yi ba ta ce mata komai ba. Na dube Hauwa da ta kasa zaune a kan kujera sai zabura take yi kamar ta yi tsalle a gabanta ta rufe ta da duka.

"Gyada kaina na yi ban ce komai ba na mayar da hankalina kanta domin sauraran abinda take cewa."" Na nunawa Salim takaici da 'bacin raina na kuma gargade shi akan kada ya kuskura abu mafi muni ya sake faruwa irin haka. Ina"

kwance cikin ciwo jiya na samu labarin doki-in-doka da ya shiga tsakaninsu. Wannan shine abinda ya fi tayar mini da

"hankali na ce kina ina har hakan ta faru. Ban haifi Kamalu da Yusi ba, amma yau zan gaya miki wani abu da nake ji game da yaran nan a zuciyata wallahi ina sonsu fiye da yadda ki ke tsammani. Yadda nake jin yaranku gabad'aya a raina haka nake jin wanda na haifa. Ina rokonki da Allah da annabi kada ki yanke kyakykyawar ala'kar dake tsakaninmu. Kada ki yi yun'kurin datse k'akkarfan zumuncin da yake tsakanin Adamu da Yusuf domin kuwa d'azu Adam ya je mini cikin damuwa cewa kin tura yaran nan kano, ki yi hakuri yara su dawo mu cigaba da rayuwa cikin aminci na yi miki alkawari wani abu makamancin wannan ba zai sake faruwa ba. Kuma in sha Allahu Salim zai shigo ya baki ha'kuri komai ya shige da izinin Allah."""

"Ta gama maganar tana sanya hannu domin share hawayen da yake ta tsiyaya a fuskarta. A nutse na ce."" Ki yi hakuri"

"ki daina kuka akan wannan lamari Momi wallahi ban k'ullaceki ba, kuma ni har abada akan yara ba zan yi rigima dake ba, amma ina so ki sani ce wa muddin Kamalu da Salim na tare a Inuwa daya to sa'bani ba zai daina giftawa a tsakaninsu ba. Abinda ba na fatan ya sake faruwa. Ba wai ba ki isa ba ne, kin fi karfin komai a wurina domin ban mance alherinki ba, ki yi hakuri yara dai har abada sun bar nan in sha Allahu suna can hannun dangin Babansu sai dai su zo da ziyara. kuma ban isa na yanke zumuci da ala'ka ba tunda ai ba ni na had'a ba. "

*GARKUWAR MATA.*

*BINTA UMAR ABBALE*

"[6/3, 8:38 PM] matar mijinta: *Wannan littafin na kudi ne vip 1k akan telegram. Normal What'sapp group kuma #700 hanyar da za a biya kudin ita ce wannan...0542382124...Binta Umar gtbank ko kuma 7084653262. Binta Umar"

Opey bank. 'Yan nijar dala dari katin airtel za ku tura mini bayan kun kankare hoton. A tura da sheda ta wannan lambobin iya What'sapp kawai.*

*07084653262*

*08089965176*

*V-VIP AREWA PEN *

*85*

Babu wanda ya ce komai sakamakon saukowar maigidan daga sama ya canza kaya amma ga yanayin yadda fuskarsa ta ke a cude nasan duk ya ji maganganun da Kamalu yake furtawa. Bai ce mana komai ba haka zalika bai kalli inda muke ba ya kama hanyar fita cike da tsananin b'acin rai a tare da shi.

Yusi da sauri shi ma ya bi bayansa ba tare da ya yi wa kowa sallama ba.

"Hauwa ta ja tsaki tana fad'in."" Haba ai ni yau kwanan farinciki zan yi wallahi, irin wannan mutanan rashin mutunci da tijara shine daidai da abinda ya kamata da su."""

Muka yi shiru babu wanda ya tanka mata. Ta dubi Kamalu da har yanzu yake huci yana numfarfashi.

"A nutse ta ce."" Kada ka wani damu Kamalu abinda ka yi shine daidai domin idan har da ni da uwarka za mu zauna mu zuba ido akan abin nan to wallahi tallahi babu wani mataki da uban rikonka zai d'auka. Abinda ka aikata a yanzu shine ya tabbatar mini da cewa kai dan halak ne ka haifu kuma kana kishin kanka, sannan kuma ya nuna cewa Salim sharri ya yi maka baka aikata ba, kada ka sare ko ka tsorata don suna da kud'i wallahi ba za su yi nasara a kanka ba."

"Idan har Salim da uwarsa sun ce za su bi kadin jinin da ka zubar masa ni zan biya su zan kuma shige maka gaba tsayuwa gaban alkali masifa yanzu aka fara wallahi."""

"Na jima ina kallonta tare da yin nazari a kan maganganunta. Yadda ta d'aukaki lamarin take sake zuzuta shi shine abinda yake sanya ni tunani. Ita da Momi din duka na kasa gane inda suka sa gaba. Masifa yanzu aka fara. Wannan maganar tata ita nake ta nanatawa a cikin raina. Tabbas k'azafin da Salim ya yi wa Kamalu mai muni ne sosai, to amma ni ban shirya tsayuwa gaban alkali akan hakan ba. Kamalu dai duk da ba a shedar mutumin yau ina da tabbacin bai aikata ba. Ba ni son bala'in ya yi tsayi domin shaidan ya samu mafaka."

"Tunda ni da yaro mun tauna tsakuwa shikkenan nasan duk daran dadewa gaskiya zata bayyana. Ba zan tsaya da ita domin yin shari'a akan yara ba, ba kuma zan ce mata komai ba domin bata isa ba, mijinta da ya daure mata gindi shine daidai da ni. Sai dai yadda Hauwa take zafafa lamarin da ko'karin sake rura wutar rikicin shine na kasa gane azancinta na yin hakan shin soyayya ce ko kuma da wata manufa a zuciyarta. Ba ni so akan abinda ya shafe ni auranta ya samu tangard'a amma na lura ita ba wannan ne abinda ya dame ta ba. Tunda har na riga na yanke hukunci na kuma gaya mata ya kamata ace itama ta sassauta saboda gudun afkuwar abinda zai sanyata ta shiga nadama tare da danasani."

"Yusi ya sake dawowa a karo na biyu daga bakin kofa ya tsaya yana fad'in."" Ka zo in ji Momi."""

"Hauwa ta kalle shi sama da kasa kafin ta ja tsaki ba ta ce dai komai ba. Sai harara da ta ke wurga masa. Ya sake maimaita maganarsa ""Momi ta ce ka zo."""

"Ya ce."" Ka je ka ce mata gani nan."""

"Har ya juya zai fita na ce."" Yusi zo nan."" Ya juyo yana kallona na ce."" Zo."" ya zo ya durkusa kusa da ni."

"Na ce.""Ka za'bi Momi ko?"" Ya yi shiru bai ce mini komai ba. Cikin tsawa na sake cewa."" Momi ce uwarka ba ni ba ko Yusi?"""

"Sai ya sa kuka yana cewa."" Mama don Allah kada b'acin rai ya sanya ku yi abinda zai janyo muku nadama, Momi duk abin nan da yake faruwa wallahi ba ta da laifi, tana sonmu dukanmu na yarda Yaya Salim ya yi laifi amma kada abin ya shafeta itama cike take da takaici da b'acin rai."""

"Hauwa ta ce."" Idan abin ya dameta tunda farko mai yasa ba ta shigo an tattauna ba."" Da sauri ya ce."" Bata da lafiya wallahi, shiyasa bata shigo ba a kwance take."""

Yana rufe baki Nusaiba ta shigo da tawagar yaranmu a bayanta ta ci kuka ta k'oshi domin kuwa fuskarta har ta d'an

tasa idonta ya yi ja wata'kila d'an uwan ne ya kira ta a waya a gaya mata. Yaranmu kaf tun daga kan Khalil Hassana da Usaina Minal suna bayanta.

"Ba tare da ta gaishe da kowa ba tana daga tsaye take ce wa."" Mun gode bisa abinda aka yi mana, Allah Ya saka da alheri, mu ba mu gaji fitina da tashin hankali ba domin tarbiyar da iyayenmu suka yi mana kenan, koyaushe Mominmu cikin yi mana nasihar mu zauna lafiya da kowa take yi. Mahaifinmu kafin ya rasu k'arshen maganarsa shine mu ri'ke Babanmu Alhaji Tajo a matsayin uba. Wannan dalilin ya sanya ba za mu yi fad'a daku ba domin muna kallonsa a matsayin ubanmu, kuma Shima ya rike mu a matsayin 'ya'yansa. Bayan haka kuma muna buk'atar nutsuwa kwanciyar hankalinsa, shine dalilin da ya sanya Mominmu tace mu yi hakuri. """

"Ta sauke ajiyar zuciya kafin ta cigaba da ce wa."""

"Sannan yaranku ga su nan Momi ba ta da lafiya, dama kokari ne kawai irin nata ni kuma na ce kowacce ta raini abinta."""

"Da sauri Hauwa ta ce."" Sannu uwar iya, sarkin kitifi da makirci 'yar na gada idan ba ki yi ba ai baki sha nonon uwarki ba, mu so muke mu kwantar da uban rik'on naki ciwo ya kama shi shiyasa muka hana shi sukuni. Wato ke baki ga abinda dan'uwanki ya aikata ba ko har kina da bakin magana saboda ba ki da kunya ko."

"Yara dama ai ba mu muka sanyata ta ri'ke ba, ita taga zata iya, mu ai taimakonmu ki ka yi da ki ka dawo mana da su dama fin karfinmu aka yi, rashin lafiya kuwa kowa ma a cikinta yake mara kunyar k'arya sakarai, wannan tabarmar kunya ki ke nad'ewa da hauka. Wanene musababbi idan ba d'an'uwan naki ba. Shi za ki jawa kunne a matsayinki na wadda take gaba da shi, cikinmu dai babu sa'arki da za ki zo ki yi wa d'ibar albarka, sai me dan yara sun dawo gidan ubansu dama ai ita ta nema ni da Amina dai babu wadda take da sha'awar barin yaronta a hannun uwarki."""

"Nusaiba cikin rawar murya ta furta."" Kin ga ni ba sanya ki a cikin maganata ba, ko dana shigo kin ji na ambaci"

"sunanki, wai shin ma ina ruwanki ne naga ai ba ke ce ki ka haifi yaron ba da har ki ke fuffuka duk fa abinda ki ka ji da shi wallahi daidai nake dake, ai dama an ce ke ce ki ka rura wutar ba kowa ba."""

"Hauwa ta zabura da sauri ta tashi tsaye tana fad'in."" Ubanki zan ci la'ada waje don uwar uwarki ita data turo ki itace sa'ar yi na, duk wanda ya gaya miki ni nake turara wutar bai yi karya ba da gaske ni ce kuma sai na rurata ta ruru! ta cinyenku matsiyata masu kisan mummk'e."""

"Sai ta fashe da kuka mai karfin gaske ta sanya hannu ta toshe bakinta. Hauwa kuwa ko a jikinta. Na tashi na je na zaunar da ita ina fad'in."" Menene haka Hauwa yarinyar nan ba sa'arki ba ce kamar yadda ki ka fada me yasa za ki biye mata."""

"Tsaki ta ja da k'arfi tana fad'in."" Iskancin banza da wofi wai har wani fadi take yi an zalincesu su ba suga zalinci da suka yi ba kenan, ko shi wannan din ba mutum ba ne?"" Ta fad'a tana nuna Kamalu dake zaune a kan kujera. Na ce."" Ya dai isa abar maganar don Allah."""

Ta yi shiru ba ta sake magana ba sai tsaki take ja. Ina juyawa ita kuma Nusaiban ta kama hanyar fita jikinta duk a

sabule. Sai kuka take yi 'kasa-kasa tana jan hanci.

Ban ce komai ba na koma saman kujera na zauna kaina na sarawa tsabar tunani da zullumi.

Duk da abinda suka yi wa Kamalu sai da na d'an ji wani iri a zuciyata. Gabad'aya ma yaran ba su iya fad'a ba daga ita har Salim din domin kuwa da sun iya fad'a ina ga da ba su fara ko'karin neman sulhu ba shi karamin cikinsu ma

Adam kenan tunda ake hatsaniyar bai ce komai ba sai dai kuka da share hawaye da tissue shine kadai abinda yake

yi gwara Yusi ya zo yana kalubalantar d'an uwan nasa.

"Da zai tafi kiran da Momin take yi masa ban hana shi ba, amma hukuncin da na yanke a zuciyata yana nan ban janye shi ba sai yaran sun bar gidanta da garin ma gabad'aya domin kuwa ba zan iya ba da wannan masifa ba na shirya tarar kowane irin kalubale."

Washe gari da safe Kamalu 'kalau ya shigo mini tsaf dashi cikin Pakistani yana ta kamshin turaransa da ya riga ya

zauna masa a jiki

".

Please Login or Register in order to submit comment