You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

na gaya masa shirina. Ina da tabbacin ba zai bijire mini ba."""

"Ta ce."" Misali na yi miki ai idan ta yi tsalle ta nuna d'anta sai a nuna mata ke kuma uwar dakinsa ce a kasuwa sanadinki har yake saya mata atama super ta daura ta yafa mayafi mai tsada ."""

"Dariya ta kama ni ina fad'in."" Anti Yagana kenan, to kin ji dama dalilin da ya sanya nace bari na gaya miki kafin na yanke hukunci Babanmu bashi da matsala hakan zai yi masa dad'i."""

"Ta ce."" Ni ma na baki goyon baya amma kafin nan ki fara tambayarsa genotype dinsa da blood group idan ya sani shikkenan idan kuma bai san matsayin jininsa ba sai ya yi maza yaje a yi masa"

"Na ce."" To shikkenan haka za a yi in sha Allahu anti Yagana a gaishe mini da masu jegon."""

"Ta ce."" Gasu nan suna bacci gabad'aya tunda aka yi wankan safe suka kwanta."" Na yi dariya ina fad'in."" Fadila manya a shafa mini kan Shahida."" Sunan anti Yagana aka sanyawa yarinyar sai uwar tace tana so a dinga kiranta da Shahida a lokacin da ta fad'i hakan na ce wata shekarar sai ki haifo Shahid. Kunya kuwa ta kamata na ce to idan ba rashin kunya ba duk muna zaune ita zata za'bawa 'yarta suna ai ta yi kara ta bari a samu sunan da za a dinga kiran yarinyar tunda ai dole a sakaye dalilin sunan uwarta ne."

Goma da sha biyu ya kira ni a waya ya shigo gate amma maigadi ya hana shi shigowa. Na sanya hijabina na fita harbar gidan suna daga can bakin gate har da Ayuba direba.

"Ganin fitowata ya sanya ya kafe babur dinsa Yana kallon Ayuba yake cewa."" Idan shi zai ce bai gane ni ba ai kai za ka sheda fuskata ko ba kai ba ne direban da ka dinga zurga-zurgar kai su asibiti a lokacin da Babanmu ya kwana rashin lafiya."""

"Ayuba ya dinga fad'in."" Tabbas ni ne yanzu na sheda fuskarka ka yi hakuri wallahi d'ayan muka fi ganewa."" Yana"

"nufin Hamusu. Shi kuma Usaini haushi ya ji yadda suka tsayar dashi a bakin gate suna tuhumarsa domin ba mu yi kama ba ko daya gashi kuma ya ce musu shi kanina ne kuma zuwansa daya gidan shiyasa suke yi masa wanna titsiyar Hamusu suka fi shedawa."""

Ayuba ya biyo shi a baya yana dan bashi ha'kuri na ce ya je kawai babu komai suma suna kan aikinsu ne babu lefi don sun ga bak'uwar fuska sun nemi dalili.

"Da yake safiya ce ko ruwan da na ajiye masa bai sha ba muka gaisa sosai da bayan rabuwa zafin nemansa ya sanya shima ko gidana na Abuja bai taba zuwa ba kullum yana kasuwa a sanin da na yi masa tun Yana yaro manemi ne baya zama duk wasu lissafe-lissafe da za mu yi ta waya muke yin komai kamar dai yadda muke yi da Hamusu abinda ya gaya mini shima Usaini haka zai gaya mini sun yi bala'in cirar tuta a wajena dalili kuwa anan shine ni kaina sai dai na ce dukiyar itace tawa ta farko kenan da na zuba domin gudanar da kasuwancin abinda zai ru'banya daga baya kuwa duk kokarinsu ne kuma duk inda suka hango cigaba da sauri za su gaya mini a jarraba ko za a samu nasara. Shekara na yi kuwa za a yi lissafi a fitar da riba da uwar kudi a sallami kowa hakkinsa. Usaini yana tura kayanmu gari- gari ta hanyar yanar gizo an san shi sosai kamar dai yanzu da yake gaya mini ba'ki sun zo daga nijar domin sayan kaya ba ni tamtama a online suka had'u."""

"Ya dinga jan Minal da wasa tana janyewa na rashin sabo har sai da ya samu nutsuwa tukkuna na dube shi a tsanake na ce.""kasan dalilin kiran ka da na yi?"""

"Ya girgiza kansa a hankali yana fad'in. A a anti amina Allah ya sa lafiya."" Na ce."" Lafiya lau kuma alheri ne."""

"Sai ya saki fuskarsa sosai har da gyara zama yana fad'in."" To Ina jinki anti ko za mu sake bude wani shagon ne?"" Na ce."" A a matar aure na yi maka."""

"Saranda ya yi ya zare ido yana fad'in."" Matar aure anti a ina take kuma? ban gama gini na ba dalilin da ya sanya kenan na janye idona daga kan 'yan mata domin ba ni so na fara soyayya da budurwa iyayenta su ce na fito. Ni kuma nafiso sai na kammala komai a tsanake sai na nemi mai hankali daidai da ni na aura."""

Murmushi na yi Ina kallonsa yana ta jero mini bayani wanda na tabbatar da cewa gaskiya ce tsantsa kuma duk maganar da ya furta tana fitowa ne da can kasan zuciyarsa.

"Na ce."" Maganar gini mai sau'ki ne Usaini don ma dai ka d'auki irin na zamani da kyale-kyale ai da tuni ka gama ko ba shine wanda ka ta'ba turo mini ta waya ba kwanaki."""

"Ya ce."" Eh shine gidan anti amma yanzu aiki ya kara nisa."""

"Na ce."" To alhamdulillahi Usaini wata yarinya ce na yi maka sha'awarta nutsatstsiya kuma 'yar Malamai idan har Usaini ya samu nasarar mallakar yarinyar nan ina yi masa albishir da cewa ya gama dacewa da ma'aratussaliha."""

"Ya yi murmushi yana fad'in.'' Kai anti Amina wannan yarinyar a ina take yadda na ji kina kwarzantata wallahi har kin kwadaita mini ita a cikin raina."""

"Nasa dariya ina cewa."" Ka ji d'an gari ko, sai ma ka ganta doguwa chocolate color ga ka farar fata yaranku za su zama wata kala masu kyau."""

"Ya sunkuyar da kansa yana murmushi."""

"Na ce."" Ka amince kuma ka bar mini wuka da nama a hannuna?"""

"Ya gyada kansa yana fad'in."" Na amince anti Amina wallahi ba ni da ja kuma ba ni da haufi a kan ki na yi farinciki da wannan zabin da ki ka yi mini tun banga yarinyar nan ba har ta zauna a zuciyata."

"Fuskata ta kara yalwata da annashuwa na ce."" Aikuwa na gode sosai na ji dadin wannan alfarma da ka yi mini amma yau din nan nake so ka sanar da Ummanku duk abinda yake faruwa kuma ina son sanin matsayin jininka."""

"Ya ce."" Zan gaya mata a yau din in sha Allah. Matsayin jinina kuwa( O) ne genotype (AA)"""

Wani irin sanyi ya sauka a zuciyata shikkenan an samu yadda ake buk'ata ta wannan bangaran akwai dacewa da cancanta wancan bangaran ne kuma ban san wainar da suke toya ba. Gabana ya fadi na daga kai na dubi agogo sha daya saura kuma yadda suka tsara jadawalin d'aurin auran bayan an yi sallar Juma'a ne.

"Na saki ajiyar zuciya ina fad'in ."" Ma sha Allah ta kowane bangare an samu daidaito idan har Allah Ya kaddara wannan auran Usaini ina yi maka murna sosai domin ka yi mata."""

"Ya ce."" Na gode sosai anti Allah Ya saka da alheri ya kuma kara girma abinda ki ke yi mana na zumunci Ubangiji Allah sanya miki a mizani Allah Ya jikan iyaye da kakanni."""

"Na dinga amsawa da Amin Amin Allah Ya taimake mu gabad'aya."""

Muka yi sallama kafin kafin ya tashi na gaya masa zuwa dare zan kira shi domin karin bayani.

Ya kama hanya ya tafi na zauna cike da nazari da zullumi hankalina kuma yanzu ya yi can garin bunkure ko a wane hali ake yanzu bai kira ni ba nasan kuma tuntuni ya isa garin tunda babu wata nisa.

Na d'auki wayata gabana na d'an fad'uwa na lalubi lambarwa wayar na shiga sai dai har ta katse bai daga ba. Na

"sake kira a karo na biyu nan ma bai daga ba jikina ya mutu na ajiye wayar da rashin kuzari."""

BUNKURE.

Cike gidan yake zuri'ar Malam D'aha 'ya'ya da jikoki kadai sun isa gayya ba sai sun gayyatowa kowa ba. Amma da yake wannan sha'anin na mussaman ne a gare shi gidan cike yake da nau'in ba'ki daga gari gari nasa da na matayensa mussaman uwar bikin uwargidansa mahaifiyar amarya wato Inno.

An gama towon d'aurin aure suna ta malmale shi a leda ana zuba shi a manyan kuloli gefa guda kuma kirigar tukuwanan miya ne guda biyu kan murhu suke ta cin wuta suna zab'abbaka da tashin kamshi mai shanana a saman miyar.

Yaran mata surukan gidan suna can bakin turgijejiyar bishiyar darbejiya da ba a samu nasarar tun'buketa ba a lokacin da aka sabunta gidan suna ta d'aura zobo a leda suna zuba shi a wani mazubi mai girma. Kowa ka gani cike yake da annashuwa da farinciki daka kan iyayen 'ya'yansu da jikokinsu da surakansu.

Zaure malamin kuwa daga can bayan gidan akwai kofar da aka yi masa ta mussaman domin ba'kinsa wanda Malam Rabi'u ya buk'aci da a yi hakan dalilin gidan akwai matansu babu cancanta maza ma bambamta na shiga gidan kai tsaye duk da sashen malamin daban yake amma dai tilas ta tsakargidan za a bi kafin a isa zauran nasa kuma wasu lukutan iyalansu na fitowa.

Ta wannan kofar suka shiga zauran malamin shi da Dr Iliyas ba kowane ya san da zuwan na su ba.

Malam D'aha na sanye da manya kaya babbar riga da 'yar ciki shadda mai kyau daidai gwargwado da d'inki manya cike yake da Kamala da nutsuwa amma kana duban fuskarsa za ka gane cewa lallai yana cikin farinciki dalilin wanzuwar wani lamari da wata'kila ya jima da shi a zuciyarsa.

Tun bayan gaisuwar da suka yi da shi sai jikinsa ya kara mutuwa kwarai da gaske ya ji a ransa baya buk'atar wannan annashuwar da take fuskar malamin ta dusashe domin kuwa lamarin da suka zo dashi gare shi babba ne wanda zai iya rushe duk wata walwalarsa.

Lallai ne akwai buk'atar zama akan wannan mas'alar mai sark'akkiya kamar yadda mai d'akinsa ta gaya masa ya makara a yanzu ba lallai ne malamin ya yarda da uzurinsa ba tunda ai ya jima da bashi yarinyar mai yasa bai kawo tasgaro ba sai yanzu da aski ya zo gaban goshi

Jikinsa ya yi tubis bakinsa ya mutu d'akin ya d'auki shiru bayan gama gaishe-gaishe daga shi har Dr Iliyas din sai zare ido suke yi domin dai malamin bai fito ba sai da shirya Kuma yawanci irin wad'annan malaman masifar kwarjini ne da su da cika ido.

Dr Iliyas duk 'kumaji da karsashinsa na k'wararran likita sai da jikinsa ya mace ganin yadda wanda ya gayyato shima jikinsa ya yi la'asar sai rarraba Ido yake yi yana sinne kai wannan lamari yana da wahalar fahimtarwa a wajen irin wad'annan mutanan da tauhidi ya yi wa k'awanya da kuma rashin samun ilimin boko mai zurfi ga kuma rayuwar karkara abin dai goma da ashirin

*GARKUWAR MATA.*

*BINTA UMAR ABBALE*

"[6/4, 3:03 PM] Hauwa Galadima: *PAID BOOK VIP 1K ON TALGRAM WHAT'S APP GRUOP KUMA #700. VIA"

0542382124 BINTA UMAR GTBANK*

*V-VIP AREWA PEN*

*07084653262*

*151*

Suka yi shiru gabad'aya jikinsu a mace kamar ba wad'anda suka zo d'aurin aure ba mussaman shi angon da gabad'aya rashin nutsuwa ya gama bayyana a tare da shi. Ana haka Malam Nuhu ya shigo shine babban d'a ga malam D'aha daga shi sai Rabiu amma shi ba a cikin gidan yake zaune ba yanzu da can dai ya zauna dai a gidan kafin daga bisani ya gina nasa a gaba da gidan Malam din da kad'an

Sa'ida lokaci yakan tafi cira ni Katsina idan an samu amfanin gona ya je ya kasa ya sayar matansa hud'u daya ta rasu sai uku yanzu da yara ashirin da bakwai. D'aurin auran ya kawo shi ya kuma kwana biyu cikin iyalinsa kafin ya koma. Akwai sanayya a tsakaninsu tun lokacin kuruciya amma dai ba kamar yadda suke da Malam Rabi'u ba domin dai shine sa'ansa. Malam Nuhun ya d'an girme shi tunda sakon Malam Rabi'u ne girman dai ba wani mai yawa bane sai dai da yake shi mutumin karkara ne duk ya manyata sosai ya tsofe ga d'auwaniya da lissafin rayuwa ga hidimar iyali duk mai mace uku a yanzu da yara sama da ashirin da biyar kuma yana ciyar dasu kowace rana babu tangard'a lallai shi ya kamaci da a kira namiji dalili anan shine da yawa maza mace daya ma suna gaza ri'ke ta balle mace biyu da yaranta. Suna nan birjik a gari wad'anda jima'in kawai suka sani duk dare babu fashi sai sun yi amma ba su san

hanyar da za su kula da abinda jin dadinsu ya haifar musu ba domin kuwa jin dadin ai shi yake kawo albarkar 'ya'ya

bayan an rabauta da shi.

"Aka shiga gaishe-gaishe da tambayar bayan rabuwa. Daga lokacin ne ya dan samu nutsuwar bud'e bakinsa da ya yi masa masifar nauyi kasantuwarsu da malamin a d'aki ya kasa duban wajan da yake zaune saboda tsabar jin nauyi da kunya tare da zullumin abinda zai biyo bayan uzurinsa. Ya zurawa Malam Nuhu ido yana nuna Dr Iliyas cikin ko'karin jaddada jarumtarsa ya ce."" Wannan sunanshi Dr Iliyas Musa k'wararran likita ne da ya karanci fannoni da dama yana aiki a babban asibitin nan kano wato Malam Aminu."""

Malam D'aha ya sake mikawa Dr Iliyas hannu suka yi musabaha a karo na biyu bayan wadda suka yi da farko a lokacin da suka same shi shi kadai a zauren nasa. Malam Nuhu Shima ya mik'a masa hannu baya suka sake yin musabaha cikin dai karamaci da kulawa.

"Wajan ya d'auki shiru na d'an wani lokaci. Kafin ya yi gyaran murya ya cigaba da cewa."" Wato Malam Nuhu na ji dadin zuwanka a yanzu saboda wani babban uzuri wanda ya assasa mini rashin nutsuwa da kwanciyar hankali da tunanin yadda zan tunkari Malam da wannan uzurin da duka ya shafe mu gabad'aya."""

"Shiru ya sake ratsa wajan a karo na biyu babu wanda ya tanka Malam Nuhu dai kacokan ya mayar da hankalinsa gare shi yana sauraransa. Ya nisa kafin ya sake tattago jarumtar da neman rinjaye dangane da abinda yake faruwa ya cigaba da cewa."" Wani abu ne da ya zama ruwan dare ko kuma na ce babban kalubale da rikicewar tunani ga ma'aurata wad'anda Allah Ya jarabta da hakan. Kasancewarku mutanan karkara nasan dai da wahala a ce wasu da suke rayuwa a wannan garin ba su gazgata cewa rigafi ya fi magani ba. Kuma hausawa suna cewa taya Allah kiwo ya fi Allah na nan."""

"Malam Nuhu ya ce."" Yallabai ya kamata ka yi magana kai tsaye domin wallahi gabad'aya ka sanya ni cikin nazari da zullumi."" Ya dubi malamin yana fad'in."" Ko ba haka ba ne Malam?"""

"Malam D'aha ya gyad'a kansa cikin nutsuwa ya furta.""Tun zamansu a wannan wurin na fahimci da akwai abinda yake tafe da su domin dai tunda aka fara hidimar nan Alhaji Tajo bai ta'ba bugo mini sammako irin yau ba sai kwanaki biyu da suka wuce da ya zo da kansa ya d'auki Hajara ya ce da ni za su je asibiti a zaman da nake yi a yanzu ina sauraran ji daga gare shi ne ko Hajara tana d'auke da wani ciwo wanda mu ba mu san da shi ba sai yanzu."""

"Malam Nuhu ya ce."" Ya Malam Hajara kalau take domin tunda aka haifeta a gidan nan bata ta'ba kwanciya wani mummunan ciwon da zai gigita mu ba. Kusan a yanzu ma duk ta fi yaran gidan kuzari da hankali."""

Ya gyada kansa amma bai ce komai ba. Suka dai zuba masa cikin yanayi na damuwa gabad'ayansu domin ga yanayin yadda ya fara yi musu magana sun san lallai akwai matsalar da take shirin faruwa.

"Ya sauke ajiyar zuciya kafin ya cire shakku da jin nauyin malamin ya dubu idonsa sosai ya ce ."" Malam a gafarce ni idan har na yi lefi ina neman afuwa. Ban zo nan na d'auki Hajara na kaita asibiti domin a yi mata wani gwaji na mummunan ciwo ba face samun nutsuwa da ita domin ingantuwar auranmu da kuma samun yara masu albarka da wadatar lafiya."""

Na kudi ne littafin nan kada ki karanta ba tare da kin biya ni hakkina ba.

"Ya gyada kansa yana fad'in."" Babu cutuwa ko cin zarafi tsakanina da zuri'ar Alhaji Ibrahimu kai din daidai kake da"

"wannan da yake zaune a gefanka."" Ya nuna Malam Nuhu. A daidai lokacin Malam Rabi'u ya shigo da daurikan goro kusan bakwai ya jibge a gefe d'aya."

Yazo ya zauna a ka gaisa da shi yanayin da ya gan su a cikin na alhini da zullumi ya sanya ya fara tambayar d'an uwansa lafiya.

"Malam Nuhu ya furta."" Lafiya ba lafiya amma dai mu saurare daga Alhaji Tajuden."""

"Duka suka zuba masa ido sai ya cigaba da cewa."" Ina godiya Allah Ya gafarta Malam wannan da yake zaune da na gabatar muku da shi shine likitan da ya yi mana gwajin jini da yarinyar nan Hajara cikin kwarewa da irin hikimar da Allah ya huwace musu ya tabbatar mini da cewa akwai matsala domin kuwa jini na dana yarinyar nan bai yi daidai da yadda ake buk'ata ba. A irin hasashen da suke yi da kuma yadda muke gani a kan wasu da Allah Ya jarraba da samun yara masu d'auke da wannan cutar mai kisa farar d'aya ya sanya shi din ya ba mu shawara a matsayinsa na jami'in lafiya dakatar da abinda ake shirin yi a yanzu dalili anan kuwa shine za mu kasance ni da yarinyar nan cikin yanayi na damuwa da tashin hankali a duk lokacin da Ubangiji Allah Ya ba mu rabo na haihuwa yaranmu za su zo d'auke da wannan lalura ta sikila wadda take kisa a take ta kuma wahalar tare da jirkita hallita da matsancin ciwo mabambamta idan kwana bai k'are ba."""

Shiru kamar an yi ruwa an d'auke babu wanda ya ce uffan amma gabad'aya jikinsu ya yi sanyi ban da malamin da wani murmushi ne ma na mussaman a saman le'bansa.

"Dr Iliyas ya yi kundubala ya dubi malamin da wasu takardu guda biyu a hannunsa yana bud'a su ya ce."" Ya Malam a"

"matsayin mu na likitoci muna yin iyakacin bakin kokarinmu akan kowace irin ma'asala domin mu dora jama'a akan hanyar da za su samu mafita da kuma wadatar lafiya. Babu nufin yi wa Allah shishsigi domin shi Ubangiji shine ya d'an sammana sani daga cikin abinda mu ba mu sani ba sanin abinda yake kudira sai shi buwayi gagara misali."" Malam D'aha ya zuba masa idoo yana sauraransa. Ya cigaba da cewa.""Yawaitar wannan ciwo da yadda masu d'auke dashi ke shiga gagari da k'unci na rayuwa da azaba mai tsanani a duk lokacin da ya motsa ya sanya kungiyar manyan likitoci daga 'kasashe daban-daban mahukunta da kuma gwamanti had'a karfi da k'arfe domin yin bincike akan dakile hanyar da wannan lalurar za ta cigaba da yaiwata a kowane sassa na fad'in duniyar nan gabad'aya."

Binciken da k'wararru suka yi tare da taimakon Allah Ya sanya suka gane cewa mataki na farko da za a d'auka domin dakushe yad'uwa da haihuwar yara masu d'auke da wannan lalura yin gwaji na jini domin sanin matsayin namiji da mace a duk lokacin da za a k'ulla auratayya wanda muke kiransa da (genotype) Ta wannan hanyar ne kawai za mu duba mu ga cancanta da dacewa wad'anda suke so kulla aure domin yin rayuwata ta din-din tare da samar da yara masu ingantaciyar lafiya.

Daga lokacin da muka fahimci cewa As da As na da mutukar had'ari a matakin jini ko Ss da Ss Muna yin iyakacin bakin kokarinmu wajan ganin mun hana su kulla aura ba don komai ba sai don gujewa 'kin juna da tsanar junansu da za su yi a nan gaba dalili kuwa anan shine suna fara haihuwa za su ci karo da jinyya mai tsanani daga albarkar da suka samu. Iyaye na kasance tamkar majinyyata marasa nutsuwa da fargaba a duk lokacin suka dubi abinda suka haifa a kwance cikin mawuyancin hali na ciwon ga'bobi da kumburi da 'konewar jini zafin jiki da koke-koke Mu likitoci muna yin misali da ciwon nakud'a irin na mata ga yaro ko yarinyar da suka tsinci kansu a cikin wannan yanayin. Nakud'a idan Allah Ya sau'kakawa mace cikin dan k'aramin lokaci zata haife abinda yake cikinta sa'banin mai d'auke da wannan ciwon a duk lokacin da ya motsa masa yana ficewa ne daga hayyaci tare da jefe zukatan iyaye rayuwar ce ko mutuwa.

"Ya nisa cikin sauke ajiyar zuciya ya cigaba da cewa."" Ita wannan cutar ana gadonta daga iyaye biyu wato uwa da uba kamar yadda na yi muku misali da farko idan ya kasance an samu rashin daidaituwar jini uba ya kasance As uwa ma ta kasance As to akwai yiwuwar su samar da yara masu dauke da cutar kuma mafiakasari yaran da za su haifa duka za su rinjayi masu lafiyar yawa. Akwai misalin Ss da Ss shima kamar As din ne akwai buk'atar ha'kuri da juna tare da neman mafita daga kowane bangare domin gujewa samar da abinda zai zama damuwa da zubar hawaye a gaba."

Kamar yadda Yallabai ya yi bayani da farko kafin ba ni damar magana ni likita ne massanin fannika da dama da suke da ala'ka kowace lalura kuma ina yin iyakacin bakin kokarina wajan ganin na bayar da shawara akan abubuwan da su kawo rud'ani da cutar da wani bangare.

Shin yaya ake gane cewa an haifi yaro da wannan cutar dalili anan shine yaro yana karami ba shi da bakin da zai fad'i cewa ga wajan da yake masa ciwo sai dai kuka da kumburin jiki kafafu da cikinsa da kuma jirkitar launin idanu daga fari zuwa ruwan dorawa (yellow) alamu na farko kenan sai yanayin suffa da rashin kuzari ta wani gefan tafiyarsu ma tana bambamta da irin ta masu cikakkiyar lafiya.

"Abu na farko da za a yi shine idan yaro ya nuna irin wad'annan abinda na lissafa da farko ayi maza a kai shi asibiti domin auna shi don tabbatar da lafiya mu kuma a matsayinmu na likitoci daga lokacin muke fara namu taimakon da shawarwari ga iyaye akan yadda za su kula da yaronsu don kiyaye tashin ciwon a kai kai."""

"Ya yi shiru yana sauke ajiyar zuciya kafin ya nisa cikin nutsuwa."" Ya cigaba da cewa."" Allah Ya gafarta Malam ban zo nan wajan domin katse sunnar manzon rahama ba face bada shawara a matsayina likita amma ina ji Malamai da yawa na fad'in cewa akwai maganinta mu dai a likitance wannan matakin muka d'auka domin dakushe k'ara yawaitar haihuwar masu dauke da wannan lalura."""

"D'akin ya d'auki shiru na wani lokaci kafin ya yi gyaran murya a nutse ya furta."" Babu wata cuta da Allah bai yi maganinta ba Iliyasu ban katse maka hanzari ba kuma ban raina sanin da Allah ya yi muku ba a matsayinku na masu taimakawa. Kafin na bawa Alhaji Tajo auran yarinyar Hajara na nemi zabin Allah na kuma yi istahara akan lambarin a kuma duk sanda zan wayi gari nakan tsinci kaina cikin farinciki don ganin zuriata da ta abokina za ta had'u waje daya domin haifar da wata zuriar da ba za mu iya iyakance adadinta ba. Mu bar wa Allah

Please Login or Register in order to submit comment